Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 58

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 58

..... I also stopped looking." Dada just smiled and turned his eyes to his laptop screen...... ★←★→★←★→★ "Mole, why are you looking for me so quickly?". "Oga, there is a problem, no matter how I think of saving it, I know the truth that it is impossible. There was a guest who was in this house last year, and my heart couldn't calm down because they came with Imran." "A guest! With Imran?". Dagger said while staring at Mole with his eyes. "Of course, how are the members of the family treating him? I put a question mark on him." "Mole, I need to see Nimrah right now." "Right now, it's not possible. Even though I'm at school, I'll take them, but she's not the only one. This girl is a twisted person. If she doesn't grow up, there's nothing." Hot air Dagger screamed at me, he knew the truth Mole said about Nimrah. See, since they met one time, this girl did not look for him again. In all the videos that her followers bring to him, there is not a single one of her worried. He lost what kind of devilish girl she was. In a bit of pain, he looked at Mole and said, "But Zak-Shadow, how can you not understand him now?"......

Standalone post1,675 words

58

........“Daga ina ka fito da wannan kayan, kamar mai shirin kai lefen aure?”. Dada ya katse dariyar tasa. Cikin shanye dariyar Daddy Imran ya ce, “Kayan lefen Nimrah ne dan gara ta tar......” Ai bai ma kai ƙarshe ba Dada yay wata kalar ɗagowa ya watso masa firgitattun idanunsa. Ai ko Imran ya sake fashewa da dariya harda kwanciya. Sai da yay mai isarsa ya tsaigata da faɗin, “Haba Zaki irin wannan kallon ai saika gigita ni, maida wuƙar wasa nake maka. Nima ba kare ya cizan ba da zan baka yarinyata tun yanzu ka halaka min ita yanda ka shekara takwas ɗin nan kana mafarke-mafarke.” Kai kawai Dada ya girgiza batare da ya tanka zancen ba... Imran yasan iyakar amsar kenan. Shima sai ya saki zancen dan dama tsokanarsa yake ya fara masa bayani akan kayan cewar nasa ne da aka ɗinka. Sai takalma da dai duk wani abin buƙatarsa daya saba na yau da kullum.... Dada yasan wannan kaɗan daga aikin Imran ɗinsa ne, sai kawai ya zuba masa ido yama kasa magana. Cikin ƴar Harara shima Imran ya ce, “Malam nima daina kallo na.” Dada ya ɗan murmusa kawai yana maida idonsa ga screen ɗin laptop ɗin sa......

★←★→★←★→★

“Mole miyasa kake nemana da gaggawa haka?”. “Oga akwai matsala ne, duk yanda nai tunanin ajiyewa har na san gaskiya hakan ya gagara. Akwai fa baƙo da akayi a gidan nan shekaran jiya, kuma sam zuciyata ta kasa nutsuwa da shi saboda tare da Imran suka zo”. “Baƙo! Tare da Imran?”. Dagger ya faɗa yana tsatstsare Mole da idanu. “Tabbas, yanda kuma ƴan gidan suke masa ya saka na ɗora ayar tambaya a kansa”. “Mole ina buƙatar ganin Nimrah yanzun nan”. Yanzu kam sosai Mole ke kallonsa kafin ya girgiza kai”. “A yanzu haka kaima kasan bazai yiwu ba, duk da makaranta zani ɗaukarsu, amma kasan ba ita kaɗai bace. Ga yarinyar nan murɗaɗɗiyar kanta ce, idan ba ita taso abu ba akwai daru.” Iska mai zafi Dagger ya furzar yana kaina sitiyari duka, dan yasan gaskiya Mole ya faɗa akan Nimrah. Duba da tunda suka haɗu sau ɗayan nan yarinyar nan bata sake nemansa ba. A duk videon da masu bibiyarta kuma ke kawo masa babu ko ɗaya daya ganta a damuwa. Ya rasa wace irin sheɗaniyar yarinya ce ita. Cikin ɗan zafi-zafi ya kalla Mole da faɗin, “Amma ai kasan Zak-Shadow, taya zaka gagara ganesa a yanzu?”. “Oga! Idan na gagara ganesa fa banyi laifi ba. Karka manta sanin da nai masa wancan karon sani ne na sama-sama. Yanzu kuma wannan baƙon harda ƙasumba a fuskarsa”. “Mtsoww! Mole dolene naga Nimrah, dan na fara fahimtar kai wawa ne a wasu lokutan. Kayi duk yanda ma zakayi gobe mu haɗu.” ya ƙare maganar yana jawo jotter da pen a cikin drower ɗin motar, rubutu yayi mara tsayi ya miƙa masa. “Ka bata wannan yau, a yanzu kuma”. Komai Mole bai sake ce masa ba ya amsa takardar, dan kalmar Wawa daya kira shi da ita ta ƙona masa rai, dama ga Mole da shegen zuciyar tsiya. Shima Dagger cikin takaici ya sake faɗin, “Fita min a mota”. Kallonsa Mole ya juyo yayi cikin ido, sai dai nan ma baice komai ba ya buɗe motar ya fita. Ta gidan su Nimrah da zai je ɗaukarsu ya koma. Sai da ya bar wajen sannan ya buɗe takardar da Dagger ya bashi.... (Ki gaggauta haɗuwarmu daga gobe zuwa jibi, dan akwai magana mai muhimmanci. Jinkirin ki zai iya zame miki dana sani da kukan rashin Ruƙayya ko Mamanku). Laɓɓa Mole ya cije tare da yin ƙwafa. Saboda irin wannan dama ya nutsu ya koya karatu da rubutu a wajen Dagger ɗin, gashi kuwa amfanisa ya fara zuwa masa a gaɓar data dace. A baki ya saka takardar ya taune ta, sai da ya tabbatar ta narke ya tofar a titi ya cigaba da tafiyarsa zuwa makarantar tahfiz ɗin su Nimrah......

★Idanu sosai Malam Buba ya zubama Nimrah da suke fitowa ita da Ruky, yanda suke dariya zaka tabbatar wata hirar farin cikin suke yi. Mu'azz ya ƙaraso inda suke yana miƙa musu leda, hannunsa da ince na leda yana sha alamar shine a ledar da suma ya basu. Wani murmushi ya saki a karo na farko. Zuciyarsa na ayyana masa lokaci fa yayi da shima zai ci arziƙin wannan wahalar tasa. Dole ne yay ma Dagger juyin mulki ko su zama sarakuna biyu a fada guda. A yanzu fa ƴar nan tasa itace IGIYAR FITO da kowa zai buƙata wajen samun nasarar kaiwa GAƁAR ruwan kodan ceton rai ba DUKIYAR da aketa kai-kawo a kanta kawai ba. Domin kuwa shi shaida ne, mutumin nan da gaske shi ne DODON mutanen nan duk ƙarfin su da damar da suke da ita a hannu. Gashi kuma a salon daya dawo zai iya zame musu KIƊA A RUWA... kenan washi dama ce a yanzu da zai murza kambunsa fiye da kowa, ta yanda gaba ɗaya manyan ƙungiyar ma zasu koma tafin hannunsa sai abinda ya faɗa musu, dan yana da abubuwa fiye da Dagger da suke ganin shi kaɗai ne shegen su. Kai-kai shi kam yau sai yaji ma yana alfahari da abinda Hassatu tai masa na bada Nimrah ga Zak-Shadow... Karo na farko a rayuwarsa ya ayyana (ALLAH ya jiƙan ki Hassu na. Kin haifa min ƴar gudalliya ta zame min alkairin tsanin yin kuɗi da zan fantama a rayuwa ni da ita.....) Isowar su Nimrah ya katse masa tunani, duk suka gaisheshi kamar ya da suka saba sannan suka shiga mota. Mu'azz na gaba suna baya. Duk sun cika motar da hirar su har suka iso gida....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

“Wai nikam yau lafiya? Sai nake ga kamar kanata ɓoye-ɓoye. Musamman idan ka kimanci lokacin fita massalaci. Sai yanzu kuma nake ganin kamar kana yin haka ne saboda baƙon nan na jiya.” Wata shegiyar harara Sanda ya zabgama Malam Almu da faɗin, “Oh ido ka saka min kenan ban sani ba?”. “A'a wlhy taya zan saka maka ido ni kuwa. Kawai dai ina ganin ya kamata idan da wani abu ne ka sanar min nima sai na kiyaye gudun kwaɓa aiki. Bana son nayi wani kuskure da ƴar uwata zata cutu a dalilin sakaci na shiyyasa. Saboda ni kaina dai da jiya kawai na fara ganin baƙon nan sai na jini kamar a tsorace. Dan daga ganinsa kaga BARDEN NAMIJI da baya buƙatar wargi. Irin waɗan nan kuma yana da ƙyau kasan su wanene su kodan ka kiyaye musu”. “Mtsowww! Malam Almu tashi ka bani waje kafin na canja maka kamanni, ka cika min kunne da shegen surutunka fa mara amfani”. “ALLAH ya baka haƙuri, ya huci zuciyar ka. In dai nine kaga tafiya ta”. Maigadi ya faɗa yana fita a ɗakin yabar Sanda dake binsa da kallon harara. Fitar tasa ce kuma tai dai-dai da isowar Malam Buba ɗauke da su Nimrah. Dan haka ya buɗe masa gate al'amarin Sanda na cigaba da masa kai-kawo.......

______★

Matuƙar farin ciki su Nimrah sukai da samun su Aunty Mimi yau ma a gidan. Duk da su kaɗai ne babu yara ko ɗaya sai Baby Nawal dake ɗakin Mammah tana barci. Bayan sun gama rungume Mammah da mata shagwaɓa suka gaida iyayen nasu. Dai-dai suna cire hijjabai Ruky ta makama Dayyan daya zuba musu ido kamar tsohon maye harara. Maimakon yaji haushi sai ya sakar mata murmushi. Ita Nimrah bata lura ba, hankalinta nakan magenta dake matuƙar shan gata a gidan kamar ƴar mutum. Tayi girma abinta tayi ƙyau kai kace magen turawa ce. Ta ɗaga ta tana mata kiss da rawa Ruky ta ƙaraso inda take. Dai-dai nan kuma Daddy Imran ke sakkowa daga upstairs Dada a bayansa. Sai dai da yake Daddy Imran ɗin ne a farko shi suka fara gani, sai dai shima sai da yay magana tsabar yanda su duka hankalinsu ke kan magen da suke kira da suna Mishi. Wani lokacin kuma suce Peppy. “Halan yaran nan yau basu ganni bane”. Muryar Daddy Imran ta shiga cikin kunnuwansu a bazata. A tare suka juya inda yake, sai kuma Ruky ta zabura ta rungumeshi. Sai dai Nimrah batai hakan ba, dan tun suna ƙanana ma sosai ko tazo rungumesa kamar Ruky cikin wayo yake hanata yin hakan, tun bata fahimta harta fahimta, bayan sun ƙara girma a islamiyya ta fahimci kuma dalilinsa na yin hakan, shiyyasa bata taɓa damuwa ba sai ma kima da daraja daya ƙara a idonta. Kusa da shi ta matso tana masa sannu da zuwa itama, sai kuma ta juya a hankali jin motsin kamar mutum a kusa da su. Da sauri ta janye saboda saukar idanun nata akan Dada dake ƙoƙarin ɗaura agogo. Sai dai kuma tamkar walƙiya hoton agogon ya gilma mata a brain, da sauri ta kuma ɗagowa ta kalla hannun nashi. (Wlhy agogon ne fa na ɗakin Mammah) Wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata. Sai dai gaisuwar da Ruƙayya kema Dadan ta katse mata lissafi. Cikin satar kallon agogon ƙasa-ƙasa itama ta gaishe shi. Kamar yanda ya amsa ma Ruƙayya a taƙaice itama a taƙaicen ya amsa mata. Daddy Imran dake kallonsu ya ce, “Halan yanzu ma kuka shigo gidan?”. “Eh Daddy ko ɗaki ma bamu shiga ba.” Nimrah tai maganar cike da shagwaɓa tana ma magenta wasa. Ƴar dariya Daddy yayi da faɗin, “To aje ai wanka a huta, ALLAH dai ya bada ilimi mai albarka. Mishi ina gaisuwa”. Ya ƙare maganar da taɓa kan magen. A tare suka amsa da amin. Suna nufar hanyar ɗakinsu. Ta ƙasan ido Dada ya bisu da kallo, can ƙasan zuciyarsa yana nazarin kallon da yaga Nimrah nama agogonsa a sace. Sai dai bai kawo komai a ransa ba tunda bai san ta gansa a ɗakin Mammah ɗin ba suka ƙarasa cikin falon. Dan zasu ɗan fita ne zaga gari kamar yanda Dadan ya buƙata. Duk da Imran yaso ƙi Dadan ya nuna masa sai fa sunje, tunda a mota ne wazai wani ganshi tunda yasan abinda suke gudun dai kenan. Shi kuma a yanda yake jin ransa ma bashi da dalilin wani hutu aiki kawai yake son fuskanta..........✍️