Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 57

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 57

"Daddy's wife's aunt is not here". Now look, she was adamant that Daddy wouldn't let me stay in this house, but why did they sell it to me because I didn't listen to Aunty Jiddah at first. I don't believe this, I bring you good news, but I don't confirm its validity." Trying to get down, Nabeeha lay on the bed in a careless state, saying, "What about me? "Hummm Aunty Nabeeha, this gossip is so true that you will give it to me." I heard a certain disgust from the Imam as if Dada had returned home". Nabeeha who was trying to join the servants stopped, then she quickly turned around and looked at Ismat who was smiling. She raised her eyebrows and said, "I'm not sure, that's why I'm coming to let you know. I thought that the Imam was going to the house, but I saw that they passed the tahfiz, and Umm was not planning to go out. What happened that day made me afraid to come. This Nimrah is not ashamed of her and Ruqayya" Nabeeha was not listening to her anymore and now she has already returned to the bed and sat down. She looks like a confused person.....

Standalone post1,577 words

57

.........“Aunty! Aunty Nabeeha! Aunty please ki tashi”. Da ƙyar Nabeeha ta iya buɗe idanunta da sukai mata nauyi saboda barci. Dan ko sallar asuba da ƙyar ta tashi tayi ta wajen ƙarfe shida ta sake komawa gado. Yanzu kuma ga Ismat tazo tana tashinta. Akan Ismat ɗin ta sauke su, sai kuma ta sake lumshewa da buɗewar dai. “K kuma daga ina da safiyar nan?”. “Daga gida mana. Ina su Momy naji gidan shiru”. Cikin yamutse fuska Nabeeha tai hamma tana tashi zaune da ƙyar, sai da taja wayarta ta duba agogo. Ganin goma harta wuce ta maida ta ajiye tana bama Ismat amsa. “Momy tayi tafiya, suna Chaina ita da Aunty Amo.” “Uhmm ita Momy ai bata gajiya da yawo a jirgi kamar ƴar sama jannati. Taita biye ma matar nan, sun sauka a mulkin ma bazata ƙyaleta ta huta ba. Su Amima fa?”. Baki Nabeeha ta taɓe alamar amsa zancen farko kenan, kafin ta amsa na ƙarshe da faɗin, “A club suka kwana. Ina ƙyautata zaton kuma yau Momy zata dawo ma. Ke dai da gaske kin bar gidan nan ko? Ko takaicin zama da wannan shegiyar matar ta Daddy baƙya yi”. “Hummm wlhy Aunty Ummu nada kirki, kawai dai bamu fahimceta bane. Yanzu fa ki duba, badan tayi tsayin daka ba Daddy bazai barni na zauna a gidan nan ba, amma wlhy har faɗa saida sukayi a kaina saboda ƙin sauraren Aunty Jiddah da yayi a farko. Ni bama wannan ba, labari na kawo miki mai daɗi, sai dai ban tabbatar da ingancinsa ba.” Koƙarin sauka Nabeeha tayi a gadon cikin halin ko'in kula tana faɗin, “Labarin mi? Uwar kwashe-kwashe”. “Hummm Aunty Nabeeha wannan kwasha-kwashan fa indai ya tabbata gaskiya wlhy har ƙyauta zaki bani. Wani ƙishin-ƙishin fa naji a wajen Imam kamar Dada ya dawo gida”. Cak Nabeeha dake ƙoƙarin shiga bayi ta tsaya, sai kuma ta juyo da sauri tana kallon Ismat dake murmushi. Gira ta ɗaga mata da faɗin, “Bani fa da tabbas, shiyyasa nazo sanar miki ma dan ki bincika. Nayi tunanin su Imam zasuje gidan ne ma sai naga sun wuce tahfiz, Ummu kuma banga tana wani shirin fita ba balle nace zan bita na sami tabbaci. Dan abinda ma ya faru waccan ranar yasa wlhy tsoron zuwa nake ji. Nimrah ɗin nan ba kunya ce da ita ba ita da Ruƙayya” Nabeeha daba wani saurarenta take ba a yanzu tuni ta dawo bakin gadon ta zauna. Kamar wadda ta ruɗe ta kalli Ismat ɗin da faɗin, “Ismat kar ki saka naji kamar zan haukace dan ALLAH da gaske?”. “Aunty shiyyasa nace miki ban tabbatar ba ai. Amma mu bincika dai”......

<<<<<<<<%>>>>>>>>

A gidan Mammah kusan ƙarfe uku na rana Daddy Imran ya iso gidan. Su aunty Ummi duk suna nan, dan su Ja'afar ma yau basu je kasuwa ba. Dama su Bilal ma'aikata ne yau ranar hutu. Suna zagaye da Mammah da Dadansu cike da nishaɗi mara misali. Ga Uncle Nasiru yazo gidan shima kusan tare suka yini. Uncle Jamilu ma da su Gwaggo Khadijah sun tabbatar da suna tafe in sha ALLAHU. Dan yau ɗin ma duk sunyi magana da Dadan ta waya. Itama dai Ammie matar Daddy Imran tun ɗazun tana gidan, sai dai ita kaɗaice yara sun wuce islamiyya. Rashin yaran ya saka gidan zama babu hayaniya dan baby Nawal ce kawai data kasance ana goyo. Duk da Dada bamai jimirin hira bane bai ji ya ƙosa da wannan zaman ba. Dan ma su Lailah sun kasa sakewa saboda kunyarsa, shiyyasa ko hirar basa iya saka baki sosai sai jefi-jefi. Sai da ma suka ɗan shiga yin girki kitchen da su aunty Mommy sannan. Sanda suke kammalawa su Dadan suka tafi sallar azhar. Wannan fita salla ita ta saka Dada da su maigadi yin kiciɓus na farko, dan da asuba dukansu kaucewa sukayi dan ma shi Malam Buba ba gidan yake kwana ba. Yanzu kam babu wannan damar. Koda yake sun fito ne a bazata daga sashen Mammah ɗin, shi Malam Buba daya fara hangoshi har ya miƙe zai gudu cikin bayi sai akai rashin sa'a Ammar ya tsaida shi ta hanyar ƙwala masa kira. So yake ya bashi aikar amso masa saƙo wajen wani abokinsa. Daburcewa Malam Buba yayi, sai dai ganin da sun riga sun ƙure masa ya aro jarumtar dole. Haka ya iso inda suke da sassarfa yana kaucema idanun Dada, dan yasan a waccan haɗuwar tasu ta shekarun baya babu daɗi.

Shi Dada ma hankalinsa ba kansu yake ba, waya yake yi da Imran ne daya kira shi. Har yayi kamar zai wuce su dan Ammar daya tsaya na bama Malam Buba saƙon ne. Sai dai me, kamar gilmawar inuwa a cikin ƙwaƙwalwa ya lura da malam Buba dake cikin yanayi na tsarguwa. Karo na farko ya ɗan zuba masa ido, dai-dai Malam Buba na gaishesu su duka. Sai akai sa'a kuma a lokacin Bilal ya furta, “Kun shigo kun gaida baƙo kaida su Malam Almu kuwa?”. Malam Buba da ya runtse ido irin na naga takaina ɗin nan yay murmurshin ƙarafafa kai da faɗin, “A'a Alhaji, ai bamu san akwai wani baƙo ba, mun zata Alhaji Imrana ne ya dawo daga tafiya. A gafarce mu. Alhaji barka da zuwa ina yini”. Dada dake kallonsa cike da nazari hannu kawai ya ɗaga masa. Sai kuma yay wucewarsa yana cigaba da wayarsa hankali kwance kai kace babu wani abu daya ma lura da shi. Dada mutum ne mai taku. Shiyyasa ko a gidan soja suke faɗin suna tsoron shirunsa. Dan ko kai waye baka isa a tashi guda ya maka magana ko nuna maka wani yanayi akan wani abu naka ba. Idan ma kana da ƙaracin tunani saika ɗauka bai san dakai ba a waje, a wannan silen yanayin nasa yake ma mutane da yawa illa batare da sun farga ba. Dan shi yanda kasan iskar dake gurɓata yanayin ƙasa haka yake shiga jiki a hankali batare da an ɗauki al'amarin da girma ba a zahiri.. Ganin abinda Dadan yayi ya bama Malam Buba nutsuwa da tunanin ai bai ganeshi bane, to taya ma zai gane shi a wannan yanayin ɓadda kamar tasa. Amma duk da haka dole ne yaje wajen Malaminsa ai masa aiki akan mutumin nan, dan lokaci yayi da za'ai wasa mai ƙyau da shima yake ganin zai zama wani abu a wajen manyansu, ba wai cigaba da zama ƙarƙashin Dagger ba kullum yana sammusu daga uwar dukiyar da ake basu. Ya tabbatar Dagger ya jima yana cutar su, kawai dai suna ƙyalesa ne tunda shine yasan manyan arnan, ta hannunsa suke samun umarninsu. Bayan sun dawo sallar ya sake iske Malam Buba ya ɗakko su Afrah daga makaranta, ya kaima su Nimrah abinci kuma. Anan ma ta gefen ido ya gama ƙare masa kallo dan ya kawo saƙon Ammar ne daya amso. Falon suka sake zama aka cigaba da ƴar hira, duk da dai shi ba wani magana yake mai tsaho ba ko da yawa. Hasali ma ya gaji da surutun amma bazai iya tashi ba saboda farin cikin ƴan uwansa dake zagaye da shi da yake ciki. Balle ga su Ayyan da aka ɗakko daga Islamiyya sun zagaye shi da labarinsu da a magana ɗaya biyu sai ance Aunty Ninah, aunty Ruky. Tun baya fahimtar wacece suke kira Ninah ɗin har ya gane. Dan tun jiya yake jin sunan a bakunan ƴan gidan bai tantance dawa ake ba sai yanzu. Kusan 2:30 ya tashi ya haura sama.

★Mintuna kusan talatin da shigowar tasa yana zaune kawai a sofa da laptop akan ƙafafunsa daya miƙe saman table, aiki sosai yake, sun fara shiri da yawa, shiyyasa yake jin bashi da wani lokacin hutu. Dan a nan kusa yake son ganawa da su Faro da sukai waya ɗazun ya sanar masa baya babban birni yaje wata jiha aikin gaggawa. Goran ruwa ne daya sha fin rabi a kusa da ƙafafun nasa, sai takardu daya baza a kusa da shi saman sofa ɗin da jikinsa. Koda akai knocking ƙofar bai ɗago ba balle dakatawa da abinda yake yi a haka ya bada iznin shigowa... Daddy Imran ya turo akwatin hannunsa Ammar da Bilal na biye da shi da wasu akwatinan suman. Sallamarsu da ƙarar tayoyin akwatinan ya saka Dadan a karo na farko ya ɗan kallesu. Sannu da aiki Bilal da Ammar sukai masa, ya jinjina musu kai kawai idonsa dai akan akwatinan da suke ajiye wa. Sai da suka juya zasu fita ya jefa musu tambayar da ta sakasu dakatawa... “Ma'aikata nawa ne a gidan nan?”. Batare da tunanin komai ba Ammar ya ce, “Su biyar ne Dada, sai mata biyu dake aikin cikin gida. Kulu da Asabe, maigadi Malam Almu. Sai driver malam Buba. Akwai mai sharar tsakar gida da bama flowers ruwa sunansa Sanda ƙanin Malam Almu ne mai gadi. Sai kuma can ɓangaren su Yaya Ma'aruff, akwai maigadi ta gate ɗin can ma, da mai kula da flowers”. Dada dake ɗan jinjina kai ya lumshe idanu yana sake buɗe su. Da hannu kawai yay musu alamar suje kafin ya maida idanunsa ga laptop ɗin. Sai da suka tura ƙofar batare da ya ɗago ba ya furta, “Malam ka dameni da kallo”. Murmushi Daddy Imran dake tsaye ya riƙe ƙugu yayi, sai kuma ya zauna a bakin gadon yana faɗin, “Ba dole na kalleka ba. Kwana ɗaya ko gama hutawa bakai ba ka fara tambayar ma'aikatan gida. Anya kuwa Zak... Baka da aljanu?”. “Tsamiya ce da kuka ba aljanu ba”. Fashewa da dariya Imran yayi sosai.........✍️