Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 10

Post

Kida a ruwa Book 3 page 10

..... in the open space and went straight to the servants. After a few minutes, he came out and wiped his head to the neck, showing that he was wet. He hurriedly finished his dressing and went to the mosque inside the hospital... Nimrah's head was looking for a break and was surprised to see a sign that Dada was sleeping in the room. Although he had to come back from the mosque and wake her up. From the way she was sitting on the edge of the bed, she looked at the bottom of his white robe. Dan was not in his body last night. The correction in the voice that he put on raised her whole face and looked at him. Then she quickly averted her eyes as he was also looking at her. She straightened up like a broken egg and went to the toilet in the room. It is a small room with only two beds, everything I need is in it until fright. What surprised her was that the other bed had no sign of being slept on, why was she wondering where he slept? Shouldn't he be sitting in this chair? She didn't have a problem with this answer, so she came out to the servants, from where she was standing, she raised her eyes and stole his gaze, thinking that he would look up and quickly turn her aside. He was also

Standalone post1,745 words

10

........Iska yaɗan furzar kawai ya ɗauki laptop ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Shima zuwa 1:47am idanunsa suka fara yajin barci. Dole ya rufe Laptop ɗin ya zama a hankali ya kwanta a gadon duk da ya musu kaɗan, sai dai ya tabbatar yace zai tashi wata sabuwar futinarce kuma. Dan shi kam lamarin Nimrah da rigimarta sun fara fin ƙarfinsa. Aiko kamar abinda take jira kenan. Mutuniyar ku sai aka sake gyara kwanciya a jikin Dada ɗare-ɗare. Addu'a yayta ambata duk wadda tazo bakinsa. Har ALLAH ya taimaka tarzomar dake neman turniƙewa ta lafa cikin amincin ALLAH, daga haka shima barcin yay gaba dashi saboda yana jinsa sosai. Kiran sallar farko ya farka, baya buƙatar farkawarta taga a yanda suke kwance, dan haka cikin dabara ya zameta a jikinsa ya kwantar da ita a tsakiyar gadon yana gyara mata blanket shi kuma ya sauka. Duk yanda yaso tashi kasawa yay, sai da ya jinkirta zaune a bakin gadon hannunsa ɗaya dafe da kansa, ɗayan riƙe da cikinsa daya ƙulle masa tamau, ya ja mintuna a haka har ya ɗan sarara sannan ya miƙe zuwa bayi. Bayan wasu mintina ya fito yana goge kansa zuwa wuya alamar jiƙashi yayi, dan jallabiyar jikinsa ma ta nuna hakan kasancewarta coffee color. Sauri-sauri ya ƙarasa kimtsawa ya tafi masallacin cikin asibitin....

Kan Nimrah neman tarwatsewa yayi da mamakin ganin alamar fa Dada a ɗakin ya kwana. Duk da sai da ya dawo salla massalaci ya tashe ta. Daga yanda take zaune a bakin gado ta zubama ƙasan farar jallabiyar jikinsa idanu. Dan ba itace a jikinsa jiya da daddare ba. Gyaran muryar da yay ya saka ta ɗagowa gaba ɗaya ta kallesa. Sai kuma tai saurin kauda idanun nata dan shima ita yake kallo. Miƙewa tai kamar wadda ƙwai ya fashe ma a ciki ta nufi toilet dake a cikin ɗakin. Dan ɗaki ne guda da gado guda biyu kacal, komai na buƙata akwai a cikinsa har fright. Abinda ya bata mamaki ɗayan gadon babu alamar an kwanta akai, shiyyasa taketa wasiwasin a ina to ya kwana shi? Badai a zaune a kujerar nan ba?. Bata da mai bata wannan amsar, dan haka ta fito a bayin, daga inda take ta ɗan ɗago ido ta saci kallonsa, tana ganin zai ɗago tai saurin maidawa gefe. Shima dake binta da kallo ta gefen ido janyewa yay ya maida kan Alkur'anin hannunsa. Bata wani jimaba ta fito, sallayar data gani shimfiɗe alamar shi yay amfani da ita ta hau bayan ta ɗauki hijjab data gani ta saka. Koda ta idar sai da tayi har azkar sannan ta miƙe a wajen. Sum-sum ta iso inda yake, kanta a ƙasa takai duƙe a ƙasa kusa da shi tana faman cuɗa yatsunta cikin juna. “Dada ina kwana”. Idanunsa ya ɗago a slowly daga kan Alkur'anin ya zuba mata su, cike da nazarinta yake kallon hannun da take cuɗawa cikin juna. Ita kuma jin shiru bai amsa ba ta sake maimaita gaisuwar tana ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido. Rasama ya zatai tayi sai kawai ta tura baki gaba. Ɗan motsi lips ɗinsa sukai kamar mai shirin yin murmushi. Sai dai baiyi ɗin ba. Alkur'anin ya rufe ya ajiye a drawer gefen gadon jiyyar tata. Babu zato kawai taga ya miƙa mata hannunsa dake fari tas, ga faratan a gyare sai sheƙi suke fes-fes da su. Nata hannun ta kalla, sai kuma ta sake kallon nashi tana ƙoƙarin noƙe nata.. “Baƙya son mu samu ladan musabaha Kiddo?”. Wani irin yuuuu Nimrah taji tun daga yatsan ƙafarta har tsakiyar kanta sakamakon yanda Dadan yay magana muryarsa a shaƙe, gashi ƙasan maƙoshi kamar mai raɗa. Ya kuma kamo hannun nata cikin nasan harda ɗan matsawa yanda ya sata dole ɗagowa ta kallesa. Shima kallon nata yake da wani irin yanayi data kasa fassarawa, ya kuma riƙe idanun nata cikin nasa ta kasa janye wa. Ruwa idanun nata suka fara tarawa, har yana iya ganin ƙyallinsu. Lips ɗinta na rawa kamar zata fashe masa da kuka ta ce, “Dadahhhh”. Idanun nasa ya janye daga cikin nata. Sai kuma ya janye hannun batare daya amsa kiran da tai masan ba ya koma cikin kujerar da ƙyau ya gyara zamansa. Sai da ya tabbatar abinda ke masa kai-kawo a maƙoshi ya koma ya kwanta sannan yay magana cikin dakewa. “Yaya jikin naki?”. Sharrr hawayen da ita kanta bata san na miye ba suka zubo mata. A haka ta furta, “Na warke”. Kallonta yay da mamaki. Ganin kuka fa take bil-haƙƙi abinta. Sai kawai yakai hannu ya shafa kwantaccen gashin fuskarsa. Itama dai-dai tana miƙewa zata bar wajen. Hannunta ya riƙo kawai ya dawo da ita, sai dai yanzu tana daga tsaye ne tana sharɓar hawaye taƙi kallonsa. “Negar! bana son kukan banza fa. Ko kina son bugu ne?”. Kafaɗa ta maƙe masa tana ƙara matso hawayen. “Wani guri na miki ciwo ne?”. Nan ma kafaɗar ta noƙe. Jimm yay yana kallonta, sai kuma ya sake faɗin, “Mi kike so?”. Yay maganar yana matso da ita sosai jikinsa ta sake duƙawa cike da lallashi, har tana ɗora hannunta saman cinyarsa bata farga ba. Cikin rawar murya tace, “Ina jin tsoro”. Wani irin motsawa zuciyarsa tayi, ya dai dake ya furta, “Tsoro dai? Na miye?”. Kuka ta sake fashe masa da shi taƙi magana. Sai kawai ya miƙe itama ya miƙar da ita ya sakata a jikinsa ya rungume. Daburcewa tai gaba ɗaya, dan abin yazo mata a bazata. Kodan jiya ba cikin hankalinta take ba duk bata san mita dinga masa ba da yanda shima yayta rungumeta. “Kar kiji tsoro Kiddo. Matsoraci baya zama gwani. Kiyi addu'a, amma miyasa kike jin tsoro? Sun miki wani abu ne?”. Kanta dake kwance a jikinsa ta girgiza. Ɗagota yay ya zaunar a bakin gadon, ya matso kujerar sa kusa da ita sosai har jikinta na gogar nashi, dan ƙafafunta ma tsakiyar nashi ƙafafun daya ɗan wara suke. Idanunsa a kanta, hannayensa cikin nata ya ce, “Faɗa min tsoron mi kike ji?”. Ta kasa danne abin, dan ya tsaya mata a rai matuƙa har zuciyarta da ƙwaƙwalwa sun kasa ɗauka kamar sauran abubuwan. Tana kuka sosai ta ce, “Dada sun ce an min aure. Da wani mutumi”. Wani irin Bimmmb!! Yaji zuciyarsa ta bada sauti. Ya danne da ƙyar yace, “To shine abin kuka Kiddo. Dama duk mace dole tai aure ai ko?. Kuma kema ai kin girma.” “Dada ni dai zan zauna wajen Mammah ta. Ban girma ba. Ba'aina Small Mom aure ba da su Uncle Billa sai ni”. Murmushi yayi kaɗan a ransa yace (Kiddo ki illatani har duniya tasan halin da nake ciki kawai ki huta). A zahiri kam ɗan gyaran murya yay da faɗin, “A'a Kiddo, zama wajen Mammah kam na lokaci ne. Sai dai randa na aurar daku halan da Mammah zaki tafi?”. Jin abinda ya faɗa ya sata kallonsa, ganin ita yake kallo tai saurin janye wa tana shagwaɓe fuska da faɗin, “Ni bazan yi auren ba fa kwata-kwata bana so Dada?”. Idanunsa ya ɗan waro waje shima kamar yanda ta waro masa nata a furucin ƙarshe. “Kice malam gari su fara addu'a, Kiddo bata san aure ai asirin Dada ya gama tonuwa”. Kunya ce taji ta kamata a karo na farko, duk da dai dama dakewa kawai take tun ɗazun, dan maganar ta mata nauyi, amma tana son ta amayar ko zataji sauƙin nauyin da ƙirjinta yayi saboda girman ta a ranta. Tasa ɗayan hannuta ta rufe idannunta tana haɗiye ƙwallar da suka sake cika mata ido. Shima da yanayin ya fara masa tasiri sai ya gyara zama yana ɗan matsa hannunta da har yanzu ke riƙe a cikin nashi. “Uhmmm faɗa min miyyasa. Kinga idan naji dalilin ki mai ƙarfi ne sai nima na yarda bazan miki auren ba. Kawai muyi zaman mu muna cin tuwon Mammah kullum”. “Ai banda kai. Tunda kana da mata”. Ɗan tsai yay yana kallonta cike da nazari. Sai kuma ya basar da faɗin, “Waya gaya miki?”. “Na sani ai. Ba itace ta taɓa yankamu ba, ga tabon a cinya na ma. Ranar ma kuma ta dawo sunyi jere a part ɗinka itada masu kama da karuwan nan.” takai ƙarshen maganar tana yaye rigar jikinta cinyarta ta bayyana. Da sauri ya haɗiye yawun dake neman sarƙe shi, ya ɗan zubama tabon da ya zama dogo sosai idanunsa da suke rinewa, ga yanda fatar jikinta ke wani sheƙi da kwanciyar ɗaukar idanun mai kallo ya saka tsigar jikinsa tashi. Yanda yanayinsa ke canjawa yasa shi kai hannu da kansa yaja rigar ya maida mata. Cikin rashin damuwa ta gyara zama da faɗin, “Dada kaga nasan kana da mata ko?”. A ransa yace (Wata sabuwa, wannan ficikar fa da wayonta) a zahiri kam sai ya basar ta hanyar faɗin, “Shike nan ke faɗa min miyyasa baƙya son kiyi?”. “Saboda bana son na bar Mammah da su Uncle's, da Ruky. Da Daddy, da su Ammie. Nafi son muyita zaman mu a haka lullum-kullum muna jin daɗin mu, muna hira. Dada ƙarya suke ai ba'a min aure ba ko?”. Ji yay kamar ya kwashe da dariya saboda yanda tai tambayar cikin marairaicewa, amma ya gimtse abarsa “Uhmm ƙila da gaske suke yi dai, amma miyasa baki tambaye su waye mijin ba to tun acan?”. Baki ta sake turawa. “Wai sunce assignment ne naje na bincika kai ko Mammah zaku faɗa min”. Maimakon ya bata amsar sai ya waske da faɗin, “To amma ai naga kina son yara sosai. Kuma sai anyi aure ake haifar yara ai ko, yaya zakiyi kenan?”. Yanzu kam har cikin ranta ta ce, “Dada baga su Afrah ba. Kuma su Ammy suna ƙara haifo mana wasu, ai sun ishe mu mu duka.” “Duk da haka kema zamu so ni da Mammah da Uncles ɗinki muga naki ai”. “To kawai basai na haife su a haka ba?”. “Babu auren?”. Ya faɗa cikin ɗan waro idanu. Kawai sai abin ya bama Nimrah dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa. Shi kuma ya shagala kawai yana kallonta. A ranta ko rayawa take (Dada fa kallon ƴar yaye yake min ko? Bari muje a hakan to). Sai da tai dariyarta sosai sannan ta jinjina masa kai. Kai tsaye ta ce, “Eh, ai ko bakai aure ba idan malamai suka maka addu'a sai kawai kaga ka samu Baby”. Samun kansa yay da tsareta da idanu kawai. A ransa yace (Zakiga malamai kuwa yarinya, harda ma masu addu'ar saukar aljanu nan kusa kaɗan).........✍️

🤣🤣Zamu so ganin malam saukar aljanun nan kuwa Dada🥱🤭. [1/14, 2:41 PM] Zeenaran 😘: