Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 11

Post

Kida a ruwa Book 3 page 11

.....they have not been married for a long time, maybe she has given birth, so why? Especially now that she is in the city, she is getting good food. I don't think you have to be with her, but you know her every move since these people started this style. And don't forget that Nabeeha has also returned to the house now. She herself, if you continue to take Nimrah as a girl, she will grow up with you. But if she confirms that you are really here, then everyone will fight for herself. Kaifa, you are telling me now that Nimrah has finished telling you that you have a wife, and she has not forgotten to cut her off. So who is Nimrah in the absence of hearing? You still see their small actions, but since she hasn't forgotten about the slaughtering thing I'm telling you, she has to do something. But thank God, Nimrah Zakanya is real. The simple thing is that she doubts you since you are still a stranger in her eyes. But you should also prepare, if it is fear, Nimrah does not know anything called fear". Now if she leaves me before I go out, I don't even have anything to do. If.....

Standalone post1,688 words

11

.........“Amma mutanen nan ƴan iska ne Haysam. To taya ma suka san ka auri Nimrah? Nifa abin nan na bani mamaki”. Dada dake zaune a kujerar kusa da gadon jiyyar Daddy Imran ɗin yaɗan furzar da iska yana jan ƙaramin tsoki. “Imran ba abin mamaki bane dan nasan mutanen nan dama dole suna zagaye damu. Kawai yanda suka gaya mata wannan zancen ne sai na fahimci akwai manufa, akwai kuma abinda suke son isarwa ga yarinyar musamman da suka ce taje ta bincika mijin da kanta...” “Tabbas nima na fahimci hakan, tunda kaga harta kasa riƙewa ta faɗa maka. Indai haka ne to ya kamata mu zauna da ita a mata bayani. Dan a yanzu ni kaina banga amfanin cigaba da ɓoye mata kai mijinta bane. Sannan dolene fa ta koma kusa da kai gaskiya.....” “Imraaan!”. “Haysamm!”. Shima ya tari numfashinsa. Sai kawai suka zubama juna idanu. Babu wasa sam a idanun Daddy Imran ya cigaba da faɗin, “Wai mi kake shakku ne? A tunaninka Nimrah bata san komai bane? Kana ganin lafiya-lafiya idan tana hannun iyayenta ne zuwa yanzu basu jima da mata aure ba, maybe ma ta haihu to wlhy. Balle yanzu da a cikin birni take tana samun abinci mai ƙyau. Ni bance dole sai ka kasance da ita ba, amma ta zama kana sanin duk motsinta tunda har mutanen nan suka fara da wannan salon. Sannan karka manta Nabeeha ma ta dawo gidan a yanzu. Ita kanta idan taga kana cigaba da ɗaukar Nimrah yarinya har yanzu zata tsiro maka da wasu fitinu ne. Amma idan ta tabbatar da fa da gaske kake shike nan sai kowa tai yaƙin kanta. Kaifa kake gaya min yanzu Nimrah ta gama faɗa maka tasan kana da mata, harma bata manta ta yanke ta ba. To kasan waye Nimrah kuwa a rashin ji? Har yanzu ƙananun ayyukansu kake gani wlhy, amma tunda har bata manta wannan batun yankan ba ni nake faɗa maka sai tayi wani abu.....” Yanda Dada ke masa kallon mamaki yasa shi yin ƴar dariya. “Hummm sa wasa, kai dai ka saka ido kawai a kanta. Amma kasan ALLAH Nimrah Zakanya ce ta gaske. Kawai sauƙin abun tana shakkarka ne tunda baƙo kake a idanunta har yanzu. Amma ka ma shirya, dan in dai tsoro ne Nimrah bata san wani abu wai shi tsoro ba”. Hararasa Dada yayi da faɗin, “Duk baku kuka ɗaure mata take yi ba. Yanzu haka idan ta sakani gaba da fitina rasa ma abin yi nake yi. Ina ga ta dawo kusa dani, ai wannan aikin ma bazai yiwu ba, dan bazan iya haɗa rikicinta da aikina ba gaskiya. Kana maganar ta girma, to yanzu take cemin ai idan malamai sukai addu'a ko ba'ai aure ba ana samun Baby, ina hankali anan Imran?”. Duk yanda Daddy Imran yaso gimtse dariyarsa ya kasa, sai da yayi mai isarsa. Sai kawai Dadan ya kuma zuba masa harara. “To miye abin dariya anan kuma?”. “To kai miye na tsarguwar? Ko kaji nace wani abu?. Tunda dai in malamai sukai addu'a ana samun Babyn kai ba sai ka zama Malamin nata ba. Miye abin wahala a ciki ba koyar da karatu bane kawai ta fahimci baƙaƙe da wasilla”. “Wlhy kaji kunya uban banza”. Dada ya faɗa yana miƙewa ya nufi hanyar fita. Shima Imran miƙewar yayi yana ƙyalƙyala dariya dan an sallamesu har Nimrah ɗin ma. Duk da bakwai sun zama normal bane gaba ɗaya musamman ma shi mai rauni akai. Kawai dai zaman asibitin ne bashi yiwuwa a wannan gaɓar.....

©©©©©©©©©

A ɓangaren shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida ƴan jam'iyya sun bala'in saka rayuwarsa gaba ta ƙarƙashin ƙasa akan naɗin muƙamai. Dan tun suna ƴar percentage har sun fito masa ƙuru-ƙuru da sunayen waɗan da suke buƙatar a bana manyan muƙamai. Hankalinsa ya tashi, duk da kuwa wanda suka kawo ɗin shi bazai ce suna da wani baƙin hali na zahiri bane. Amma a muƙaman da suka riƙe a baya a bayyane take su masu rauni ne ga sauke haƙƙokin talakawa. Babu abinda suke yi sai raya kansu da iyalansu da dukiyar ƙasar. Shiyyasa babu wani ayyukan cigaba na zahiri da suka fito daga yankunan su a sanda suke mulki na shugabanci ko na wani office da suka riƙe. Rasa wazai tunkara yay shawara yayi. Gashi kwanaki uku kacal suka bashi. Yau hatta office yaƙi fita da wuri har kusan sha ɗaya. Wani gefe na zuciyarsa keta kawo masa Zak-Shadow da Imran. Kuma tabbas yana jin gamsuwa da yaran. Dan wannan rikitaccen mulkin baya yiwuwa sai da ɓoyayyun mashawarta. Wlhy badan fidda Haysam da yayi ba da yace shi wannan mulki baiga amfaninsa ba, dan rikicin cikinsa da kitumurmura sun wuce tunanin mai tunani. Wanda ke waje shike kallon shugaban ƙasa a mai zartarwa sama da kowa. Amma a zahiri hotone kawai a kujerar mulki shugabancin ƙasar nan. Ainihin masu mulkar ƙasar suna gefe ne kawai suna busa sigari kalar wadda suke buƙata. Sai abinda suke so, sai abinda sukace dole za'ayi, idan kace zaka bijire su ƙasƙantar da kai a idon talakawan ƙasar a bayyane, a ɓoye su raunana lafiyarka da kuzarinka. Duk mai baka goyen baya su siyesa da kuɗi, idan yaƙi bi shima su ɓatar da shi ko su tsigesa a kusa da kai ɗin. Wannan itace zahirin ƙasar da talaka bai sani ba, wata shari'ar dai sai anje can kawai. Wayarsa ya ɗauka da mutane masu muhimmanci ne kawai a ciki yay gajeren text ya tura. Daga haka ya miƙe domin shirin fita office.....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Saƙon shugaban ƙasa ya shigo wayar Dada ne a dai-dai lokacin da motar su ke hawa kan babban titi bayan fitowarsu a cikin asibiti. Dabo ne ke driving ɗin, gefensa Imran. A baya Nimrah sai Dada dake ta aiki da laptop a kusa da ita. Tana lafe ne jikin ƙofa idanunta a lumshe, ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a gida saboda ɗoki. Duk da dai akwai ajiyayyar damuwa dake danƙare da zuciyarta da brain ɗinta. Amma kamar yanda tai alƙawari zata bi komai a sannu kamar yanda ta fara. Dan a yau ta sake fahimtar gane ainahin Dada ba abune mai sauƙi ba. Dole ta dake, dole ta shirya, dole ta jajirce, dole ta ƙara wayo da taka tsantsan. Sai dai duk da haka maganar auren nan na ɗaga mata hankali. Tana son taji tabbaci a bakin Mammah da sauran Uncles ɗinta da Daddy Imran. Harga ALLAH indai da auren nan batama san yanda zata fassara shiga ukun da take ciki ba. Waye wannan miji? Tana son ta sanshi, ta ƙagara ta sanshi. Duk halin da take ciki Dada na lure da ita. Dan yanda take yamutsa fuska, ta cije lips, ta matse idanu yasa shi fahimtar akwai abinda take tattaunawa da zuciyarta. Kuma ko minene yana da girma da rikitarwa a gareta. A lokacin da yake ajiye wayarsa dake tsakkiyarsu bayan kammala karanta saƙon Mr President sai yaga tasa hijjab ta share hawaye. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa. Baiyi magana ba ya cigaba da aikinsa yana sauraren tattaunawar Imran da Dabo akan Ojo da suke ƙoƙarin gano inda yake yanzun... Gidan Daddy Imran suka fara zuwa domin sauke shi. Nimrah nason shiga taga Ammie tana kuma zumuɗin zuwa taga Mammah. Sai kawai ta saka a ranta tunda weekend za'a shiga zasu zo ita da Ruky. Isowar su gate ɗin nasu gidan sai taji ƙaguwar a buɗe, dan badan Dada bane a motar da tuni ta ɓalle murfin ta shiga da gudu. Amma jikinta sai tsuma yake ta yanda har shi ma ya gane. Aiko Dabo na tsayar da motar ta buɗe ta fice dan haƙurinta yakai maƙura. Dada ya bita da kallo kawai, dan kamar ƙyatawar ido har taje ƙofar falo. Kansa ya ɗan girgiza yana miƙama Dabo daya buɗe inda yake laptop ɗin daya rufe. Daga haka ya sakko ƙafafunsa ya fito gaba ɗaya. Sauran kayan Dabo ya tattauro, dai-dai kuma isowar maigadi da malam Buba dake noƙewa a baya wajen. Cikin girmamawa suka fara gaida Dadan. Dada ya janye idanunsa daga kallon da yay ma malam Buba na seconds, kafin ya amsa gaisuwar tasu. Suka ɗora da nuna farin cikin dawowar Nimrah, sunata ambaton godiyar ALLAH. Shi dai wajen yay ƙoƙarin bari. Amma sai maigadi ya miƙo masa abinda ke hannunsa yana faɗin, “Af naso na manta. Ranka ya daɗe dama ga saƙo yanzun nan babu jimawa wani ya kawo shi a baka. Dan zanje nakai ciki ne ma kuka iso na dakata buɗe muku ƙofa.” Idanu Dada ya ɗan zubama hannun maigadi, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da yace komai ba. Yana barin wajen Malam Buba ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da har sai da maigadi ya kallesa. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru suka koma bakin gate. Sanda da ya shige ɗaki wufff tun buɗe gate da akai ya fito shima sum-sum yana leƙa hanyar sashen Mammah da har Dada ya shige....

Yanda Dada ya samu falon ya kacame da murnar ganin Nimrah sai yama tsaya kawai yana kallonsu. Dan Ruƙayya na rungume da ita tana kuka ana lallashinsu. Su duka biyun suna jikin Mammah. Mu'azz ma sai sharar hawaye akeyi na farin ciki. Shigowarsa tasa su Bilal dake zagaye da su maido hankalinsu kansa. Sai kuma duk suka zaburo cike da farin cikin ganinsa suma. Mammah kanta yau ta kasa dannewa kallonsa take farin cikinta a bayyane. Gwaggo Alawiyya tazo ta kama hannunsa tana faɗin, “Sannu kaji Haysam, ALLAH yay maka albarka. Maza zo ka zauna ansha fama kwana biyu”. Murmushi kawai yayi yana kaiwa zaune. Ya gaida Mammah sannan su Gwaggo Khadijah. Suma su Ja'afar suka gaisheshi. Kafin wani lokaci Aunty Mimi ta kawo masa ruwa. Dan suma duk suna gidan daga asibiti suke duba Lailah. Mammah tasan duk yanda suke son jin yanda aka samo Nimrah bazai faɗa ba, dan haka ta tambayesa a shirya masa abinci ne. Miƙewa yay yana amsa mata da zai yi wanka tukunna. Ya ɗan kalli Nimrah da Ruƙayya ke bama abinci a baki itama yana bata ya wuce abinsa. Dai-dai Ammar na sakkowa daga kai kayansa ɗaki da Dabo ya kawo. Umarnin kawo masa coffee ya bashi yana wucewa...........✍️