Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 8

Post

Kida a ruwa Book 3 page 8

.....I will give her the injection, if I drink GOD it will take a few minutes for her to regain her composure, so far what happened has not left her brain completely. Not sure she will find herself in that, so I didn't give her the injection earlier." He didn't say anything, but he was satisfied with her explanation, so he grabbed Nimrah by himself and lifted her up. She was whispering and wanting to grab the needle. Almost together, he and the Doctor calmed down after a few minutes when Nimrah started to calm down. But he woke up inside, and the doctor was visible. Knocking on the door made the Nurse and Doctor look at the door, and the Nurse went to look. Dabo was carrying things, after they greeted him he handed her the things, took the rest and went to Imran's room. After putting the clothes in the right place, the doctor ignored the order to rub Nimrah's body, which was again taking pain. Standing up, Dada did what he did, since he had the injection, he laid Nimrah on his side, now she is not in his body. He had to close the door and close the nurse who was following him and looked down at Nimrah. The Doctor smiled, but she heard the Nurse show her compassion...

Standalone post1,658 words

8

.........Nurse data fahimci yanayin Nimrah ɗin cike da son birge shi ta zabura tana faɗin, “Yallaɓai bari na sanar da Doctor, dan kam akwai matsala a firgice take. Dama Doctor tayi magana ɗazun data farka akan ALLAH yasa kada ta shiga yanayin...” Yanda bai tanka ba a ɗazun yanzu ma hakan ne. Itama bata jira amsar tashi ba ta fice a hanzarce. Ai ko babu jimawa sai gasu sun shigo. Har yanzu kuma Nimrah ta hanashi ko motsi tsabar yanda ta cukuykuye sa. Dan zuwa yanzu gaba ɗaya rabin jikinta akan nashi yake. Cikin lallashi Doctor tai magana tana kamo hannunta. Amma sai ta fisge tana fashewa da kuka da sambatu irin na tabbacin bata cikin hayyacinta... Doctor ta rasa yanda zatai aikinta saboda yanda take jikinsa. Gashi maganar duniya Nimrah taƙi ɗagowa.... “Miye matsalar?”. Dada ya faɗa yana ɗan kallon likitar a karo na farko. Sai kuma ya janye idanun nasa duk a lokaci guda. Itama ba iya kallonsa take ba, dan haka ta fara masa bayani yanda zai fahimta...... Da ga ƙarshe ta ce, “Yanzu akwai allurar dazan mata, in sha ALLAHU ƴan mintuna ne nutsuwarta zata dawo, dan har yanzu abinda ya faru bai bar brain ɗinta bane gaba ɗaya. Rashin tabbacin zata tsinta kanta a hakan yasa ban mata allurar ba tun ɗazu.” Bai ce komai ba, sai dai ya gamsu da bayanin nata, dan haka ya kama Nimrah da kansa ya ɗagota sosai. Tana mutsu-mutsu da son ƙwacewa dai akai allurar. Kusan a tare shi da Doctor suka sauke ajiyar zuciya bayan wasu mintina ganin Nimrah ta fara nutsuwa. Sai dai shi a ciki yay tashi, doctor kuma a bayyane. Knocking ƙofar da akai ya saka Nurse da Doctor kallon wajen, sai kuma Nurse ɗin taje ta duba. Dabo ne ɗauke da kaya, bayan sun gaisa ya miƙa mata kayan, ya ɗauki sauran ya nufi ɗakin Imran. Itama bayan ta ajiye kayan inda ya dace doctor ta bata umarnin gogema Nimrah jikinta dake sake ɗaukar zafi. Miƙewa Dada yay abinsa, dan tun da akai allurar ya kwantar da Nimrah gefensa yanzu ba'a jikinsa take ba. Sai da ya maida ƙofar ya rufe Nurse ɗin dake binsa da kallo ta ƙasan ido ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana nufar Nimrah. Murmushi Doctor tayi, sai ma taji Nurse ɗin ta bata tausayi...

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷

Wani wawan birki Malam Buba yaja yana waro idanun mamaki ganin wanda ke ƙoƙarin tsaida shi. Duk da ya rufe fuska da handkachiff ga p-cap hakan bai hana shi gane shi ba. Wuff Dagger ya buɗe motar kuwa ya shigo. Ya furzar da iska mai nauyi yana janye handkachiff ɗin daya rufe fuska da shi... “Amma Oga wannan gangancine da mu duka zai iya sakamu a haɗari. Mizai sa kazo har nan anguwar, gari da haske kuma irin haka?”. Harara Dagger ya jefama Malam Buba kafin ya janye handkachiff ɗin da yake goge fuska yana gyara zama. “To faɗa min ya kake so nayi Mole? Tun randa ka kirani an ɗauke Nimrah ka sake nemana? Tsabar rashin mutunci ma waya ka kashe min gaba ɗaya. Jiya da shekaran jiya duk naje gidanka ance baka dawo ba. Sai da na kira Ari akan ya bincika min tunda na tabbatar bazai rasa huɗɗa da wani a gidan ba ya tabbatar min kana nan anan ma kake kwana. Mole mi kake nufi? Mi kake shiryawa? Ko Nimrah na hannunka?”. “Amma Oga wannan wace irin magana ce? Kasan dai duk wuya bazan ci amanarka ba, duk abinda zakaga nayi ina da dalili na, ko bakazo ba zan zo na kawo maka dukkan bayanai. Na farko dai kwana a gidan nima a gareni tilas ne, dan yarinyar nan Ruƙayya ce babu lafiya, sai kuma wajen jiyyarta ɗayar matar waɗannan ƙannen nasa ta faɗi akan ciki sai ta akai mata tiyata aka riro jaririn. Hakan yasa inata kai kawo na jigilar kai abinci da abubuwa. Sannan wlhy hankalina ba'a kwance yake ba, ina nane da su ko zanji bayanin an sami Uwa dan har yanzu mutumin nan bai sake dawowa gidan ba daga shi har Imran....” “Amma ba waya ya kamata ka kashe min ba, tunda nima ina buƙatar son jin abinda ke faruwa ko.” “Itama fa wayar ba kashewa nai ba oga. Wannan wawan Sanda ɗin ne ya ara ya shiga bayi saboda fitilar bayin ta lalace shine ya tsumbulata a ruwa, yanzu haka inda zan kai gyara nake nema”. “Mtsowww!”. Dagger yaja tsaki. Sai kuma ya miƙa masa hannu da faɗin, “Bani wayar.” Ba musu Malam Buba ya cirota ya bashi, Dagger ya ɗan jujjuyata a hannunsa sai kuma ya saka a aljihu. Wata ƙarama ya ciro ya bashi. “Ga wannan, daga yanzu na dinga sanin halin da ake ciki”. “Amma Oga ya batun Nimrah? Wlhy abin ya fara bani tsoro.” “Nima a tsoracen nake, dan itace rayuwata. Amma ina kan bibiyar iyayen yaron can da suka daka a makaranta satin daya gabata”. “Tsohon shugaban ƙasa fa naji ance”. “Eh su. Dan ina zarginsu gaskiya. Musamman matarsa bata da mutunci daman.” “To amma ta yaya Oga?”. Wata dariya Dagger ya kece da ita. Sannan ya ce, “Humm Mole har yanzu kanka a tukunya yake kai kam. Baka san waye Dagger ba a ƙasar nan. Kodan kai kana ganina arhar banza ne. To bara kaji, wannan damar ina baka ita ne saboda Nimrah. Za kuma ka iya samun fiye da hakan. Kai dai bari na aureta”. Harga ALLAH sai da ƙirjin Malam Buba ya jijjiga. Har ya kasa dannewa cikin suɓutar baki ya furta, “Aure Oga?”. “Eh mana, ko bazaka bani ba?”. Dagger ya faɗa cikin tsatstsareshi da idanu. Yawu mai kauri Malam Buba ya haɗiya, zuciyarsa kuwa wani irin dukan take yi. Cikin rawar baki ya ce, “Ba..b...ba haka nake nufi ba Oga. Kawai dai naga ita ƴa take a wajen ka”. “A'a a wajenka dai, dan kai ka haifa. Ni masoyiya ce, kuma uwar ƴaƴana. Sai dai idan baka son bani” Yawu mai ƙauri Malam Buba ya sake haɗewa. “Oga ai kaima mai aurama wani ce. Kawai dai kasan ance wannan mutumin yana au.....” Cikin katseshi Dagger ya ce, “Oh kai harma ka ɗauki wannan auren aure? Shi jakin wace ƙasa ce zai aure ta babu iyayenta. Sannan ma wannan tsohon da aƙalla ma zai iya girmarka ne bakinka ke iya jinginawa da ƴarka. Jibeshi mutum a murɗe kamar ɗan damben turawa, dan ni banga abinda ya rage ba a zaman prison ɗin shiyyasa bamma yarda a can yake shekara takwas ba......” Sam Malam Buba ba jin Dagger yake ba a yanzu. Dan tsakani da ALLAH hankalinsa ya tashi. Ai koda rayuwa ta maidashi haka baya fatan yarsa ɗaya tilo ta auri mutum irin Dagger da babu sbinda ya sani a rayuwarsa sai mugunta da kisan kai. Ga neman mata kamar ɗan bunsuru. Tabbas baya ƙaunar Zak-Shadow, kuma ko zai rasa ransa wannan auren bazai bari ya tabbata ba akan ƴarsa. Amma kuma bazai so Dagger ya maye gurbin Zak-Shadow ɗin ba a rayuwar Nimrah. Dole ne yayi wani motsi a wannan gaɓar, kuɗin nan da su Oga suka bashi gida zai nema ya saya a wata ƙasa cikin maƙwaftan ƙasashen nan, ya ɗauke ƴarsa ya maida can, ya sama mata ma'aikata masu kula da ita, ya biya mata ta cigaba da karatunta har ta samu miji irin wanda yake fata a gareta amma ba Dagger da Zak-Shadow ba..... “Wai tunanin mi kake yi?”. Dagger ya faɗa cikin tsawa-tsawa. Ajiyar zuciya Mole ya sauke yana girgiza kansa. “Ba komai Oga, babbar damuwata kawai ina ta shiga? Waye ya ɗauke ta? Saboda mi ya ɗauke tan?”. “Karka damu zata dawo. Yanzu haka su Ayu nakan aikin nemanta. Bari naje yau inada meeting dasu oga aiki zai fara da zafinsa saboda kayan aiki sun iso, duk halin da ake ciki dai na dinga sani. Kaima kuma ka zama cikin shiri, idan ta kama kazo dole zaka zo”. Kai Mole ya jinjina masa. Daga haka sukai sallama ya fita a motar anata kiran sallar magrib shi kuma yaja motar ya ƙarasa gida. Dan dama daga asibiti yake yakai abinci. Sai da ya dakata wata mota da Malam Almu ya buɗe ma gate ɗin ta fito sannan ya shige, har yay parking idanunsa akan Nabeeha dake komawa ɓangarenta da alama motar data fita baƙinta ne.....

°°°°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°°°

Kusan mintina ashirin Nurse ɗin ta ɗauka tana gogema Nimrah da barci ya ɗauka jiki. Ta canja mata kayan da aka sako marasa nauyi. Dan simple doguwar riga ce sai hula. Tana ƙoƙarin saka mata hular ne ta buɗe idanun ta da sukai jazur tana yamutsa fuska. Hannu takai ta dafe kan. Dan haka Nurse ɗin ta dakata daga saka mata hular tana tambayarta kanta na ciwo ne?. Kan ta jinjina mata tana lumshe idanu, a lokacin Dada ya sake dawowa ɗakin. Tunda ya iso gaban gadon Nimrah ta buɗe idannunta a kansa, sai kuma tai narai-narai da su hawaye na taruwa a ciki. Cikin muryarta dake fita ƙasa sosai ta ce, “Dada kaina”. Bai wani jita da ƙyau ba, sai dai a motsin lips ɗinta ya fahimci abinda take faɗa. Maimakon zama a kujerar gaban gadon sai ya zauna a bakin gadon kusa da ita sosai, bayan hannunsa ya kai saman goshin nata. A dai-dai lokacin Nurse ɗin ta fito daga bayi hannunta ɗauke da ƙaramar tasa da ruwa a ciki, sai towel ɗin data goge mata jiki data ɗaurayo. Cikin in-ina take sanar masa zata sake saka mata towel a kanta. Hannu kawai ya miƙa mata alamar ta bashi, ai ko da hanzarin ta ta matso towel ɗin daga ruwan ta miƙa masa. Amsa yay batare daya kalleta ba, ya janye hannun Nimrah data riƙe kan ya ɗora towel ɗina. Sosai ta sauke ajiyar zuciya, tana mai ɗora hannunta akan nashi da yake ɗan daddana towel ɗin. Idanun su ne suka shige cikin na juna a hankali. Tai saurin janye nata tana rufesu. Shi ko ya cigaba da kallon fuskarta da tai fayau..........✍️

[1/14, 2:32 PM] Zeenaran 😘: