Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 2

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 2

.....s aware of your every move.” "When did he give me this message?". "On the day of your feast is your celebration". "I need to look like him". "Since childhood I have known him, he does not show his face. He is always wearing a turban." Dadah didn't speak again. For ten minutes. Then he left where he was and came back to where he got up and sat down. The conversation was the only thing he got together and he didn't say anything about Baba. He took his laptop from the side, held it tight and handed it to Imran. "This is his location. He will arrive tonight. It lasts seven days at the end of each month.” Imran bowed his head and lowered his eyes on the laptop screen, then he handed it over to Faro and said, "May God help me." Now who is the target?” “He will die physically, but he will be alive in our hands.” Faro laughed and said, "Did he see me?" So what about leaving a dead body? I don't know how he is tied to the waist for the nobles of his country, they must want to celebrate him." "We have to produce a new body that will match his body." "Does that mean we have to start production before the operation?". "That's the plan." Dadah answered briefly. Uncle Tanimu who was listeni

Standalone post1,968 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 1_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........“Wannan shine mafi wahalar al'amari Sir!. Dan Baba ko waya baya amfani da ita. Amma tunda har kaga ya bada saƙo a baka, duk sanda yaso zai bayyana a gareka. Dan tabbas yana sane da duk motsinka.” “Yaushe ya bada wannan saƙon ka bani?”. “A ranar da akai walimar bikin ku ne”. “Ina buƙatar kamaninsa”. “Tun ƙuruciya da na sanshi baya bayyana fuska. A koda yaushe yana cikin naɗin rawani ne”. Dadah bai sake magana ba. Tsahon mintuna goma. Sai kuma ya baro inda yake ya sake dawowa inda ya tashi ya zauna. Zancen ainahin abinda ya tarasu ya ɗakko batare daya sake cewa komai akan batun Baba ba. Laptop ɗinsa dake gefe ya ɗauka, yay danne-danne sannan ya miƙama Imran. “Wannan shine location ɗinsa. A daren yau zai iso. Yana ɗaukar kwanaki bakwai a kowane ƙarshen wata.” Imran ya jinjina kai yana sauke ajiyar zuciya idonsa akan screen ɗin laptop ɗin, sai kuma ya miƙama Faro yana faɗin, “In sha ALLAHU yazo hannu kenan. Yanzu miye target ɗin?”. “Zai mutu a zahiri, amma zai kasance rayayye a hannunmu.” Dariya Faro yayi, tare da faɗin, “Ashe yaga boni. To ya batun barin gawa? Dan nasan yanda yake da ɗaurin ƙugu ga manyan ƙasar sa dole zasu so yi masa bikin biznewa”. “Dole zamu samar da sabuwar gawa wadda zatai dai-dai da jikinsa”. “Hakan na nufin sai mun fara samarwa kafin Operation?”. “Tsarin kenan”. Dadah ya amsa a taƙaice. Kawu Tanimu dake saurarensu sai yaji sun ƙara birgeshi. Ya miƙe ɗauke da laptop ɗin da shima ya gama kalla ya kai gaban Dadah ya ajiye. Dai-dai Imran na tambayar Dadah “Samar da gawar nan zaifi komai bamu wahala nake ga. Yanzu wane plan ne a ƙasa?”. Shiru babu wanda ya amsa, dan haka a karo na farko T-Dalha ya ɗan ɗaga hannu alamar neman izinin magana. Su duka kallonsa sukai. Kafin Dadah yay masa alamar yayi. Faro kuma ya gyara zama yana zuba musu shayi tare da ɗaukar dabino dake cikin wani kyakkyawan bowl yakai bakinsa. T-Dalha ya ce, “Thank you Sir. Ina ganin kubar komai a hannuna game da samar da gawar”. “Ka tabbatar?”. “In sha ALLAHU”. “Okay mu sai muje step two. Akwai cemaras a gidan tako ina, muna baƙatar dakatar da su awa biyar kafin ɗaukarsa”. “Shiga gidan fa?”. Faro ya tambaya yana miƙama Dadah da yay maganar kofin shayi. Sai da ya koma ya zauna a mazauninsa, Dadah kuma yay ma shayinsa kusan sha uku kafin ya bashi amsa. “Akwai yarinyarsa itace zata mana jagora”. Sosai mamaki ya kama Imran, dan yasan Zakinsa baya amfani da Mata akan aikinsa. Cikin kasa haƙuru ya ce, “Wannan karon mi yasa?”. Dada yay ƙaramin murmushi, dan yasan ina tambayar ta dosa. Idanunsa ya ɗan zubama Imran ɗin, sai kuma ya janye a slowly. Cike da basarwa ya furta. “Dole sai da itan”. Shiru ya biyo baya. Dadah ya kalla agogon dake hannunsa. Kofin nasa shayin ya ajiye tare da miƙewa. Ya tura hannayen sa cikin aljihun wandonsa duka biyu yana kallonsu. “Little Shadow ta kusa tashi, lokacinku ya ƙare. Mu ƙarasa kwana lafiya”. Daga haka yabar wajen batare da jiran amsar kowannensu ba. Faro da Imran da suka saki baki da hanci suna kallonsa dariya ta ɗan suɓuce musu. Shi ko T-Dalha ƙasa yay da kai yana murmurshi da tsananin son ganin Zakanyar tasa matar Zakin su. Dadah kam ko waiwayensu ma baiyi ba ya shige abinsa ya barsu da gulmarsu.

Daddy Imran ya katse gulmar tasu yana miƙewa da faɗin, “Kunga tunda an koremu sai mu tattara ƴammatan ƙafafunmu mu wuce.” Cikin dariya Faro ya ce, “Idan kayi zuciya ka ƙara aure gobe kawai”. Naushi Imran ya kai masa, ya kauce yana dariya da faɗin, “Wlhy karka nakasa ni, da kuka dama Biebalo ta barni na taho.” Dariya sosai T-Dalha ke musu ƙasa-ƙasa. A haka dai suka koma ta inda suka shigo zuwa jirgin su da ke tafiya a hankali shima....

∆÷÷÷÷÷∆÷÷÷÷÷∆

Kai tsaye bayi Dadah ya nufa, ya fara watsa ruwa sannan yay alwala. Baiyi gigin tada ƴar rikicinsa ba sai da yay rakata'aynul fijir. Ya santa da nauyin barci, dan haka koda ya yaye bargon da take ciki bai tsaya jan zance ba ya ɗagata cak zuwa bayi. Ruwa ya shafa mata bayan ya miƙar da ita tsaye ya jingina da jikinsa. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana ƙanƙamesa, sai kuma ta nema fara ƙunƙunin kuka. “Shhh!!”. Ya faɗa yana shafa bayanta. Kafin cike da lallashi ya ce, “Ya isa, muje kiyi alwala”. “Dadah ka bari sai anjima”. “No. Ba wannan maganar.” Ya faɗa yana sake ɗagota daga jikinsa. Dole ta buɗe ido kaɗan cikin layin barci. Fitsari tayi sannan alwala. Ya kama hannunta ganin yanda har yanzu take layi. Dama a haka kullum yake yaƙarta suke sallar asuba. Azkar ko ai sai dai a jikinsa. Indai son jiki ne ya bata award na zama lamba ɗaya. Kamar kuwa yanda ya faɗa suna idar da sallar ta matso ta shige jikinsa. “Good morning, Dadah.” “How are you?” “I’m not okay…” Ta faɗa tana tura masa baki da sake ƙanƙamesa. Idanu ya zubama fuskarta na tsawon sakanni sai kuma a hankali ya furta, “Mike damun ki?”. “Barci”. Ta faɗa a taƙaice. Ƙaramin murmurshi ya saki da sumbatar goshinta, sai kuma ya ɗagata cak ya maida saman gadon ya kwantar. Sake shige masa jiki tayi ta nannaɗe sa kamar ƴar mage. Ya ɗan ja numfashi ya fesar. Cikin jarumtar danne rikicin dake neman tada ƙura ya zame mata hijjab ɗinta datai salla. Itama abayar ya kama ya cire. Da sauri ta ƙara ƙadandanesa saboda yanda sanyi yay wani kalar shigarta. “Akwai sanyi ne?”. Ya faɗa cikin kunenta da raɗa. Idannunta a rufe ta jinjina masa kai. Kunya na baibaye ta tare da tsoro. Dan hatta bugun zuciyarta ya ɗan canja. (Ashe jiya cika baki ne hajjaju🤣). Bargo yaja ya rufa musu, dan shima barcin yake buƙata, yasan kuma idan yace zai janye jikinsa yanda tai masa wannan ɗaurin goron rigima ce sabuwa zata tashi. A hankali abubuwa suka fara masa kai-kawo, yasan za'a rina, dan tun jiya haƙurinsa yakai wuya. Zuwan su Imran ɗin ne ma ya rage masa azabar da yake ji. Sai kuma ita ɗin daya bugar da maganin barci saboda wasu dalilinsa.. A karo na farko ya zubama fuskarta idanunsa dake a lausashe. Ya jima yana kallonta, kallon da take jinsa a jikinta da ɓargo. Dan tuni barci da take tattali ya gudu ma. Numfashi taja mai ƙarfi sakamakon saukar lips ɗinsa a kan nata. Tai ƙoƙarin janyewa amma ya hana hakan ta hanyar riƙe fuskarta da hannunsa. Tun tana tirje-turje har dai ta sallama. Sai dai yanda zuciyarta ke gudu hatta shi kansa yana ji. Tun abu nayin kamar a iya sumbata zai dakata har aka koma wani sabon layin, mai sabon shafin littafi. Rawa jikinta ya fara, gaba ɗaya alwashinta na jiya na guduwa. Sabon tsoro da tashin hankali ya mamaye ta. Daren kwanaki uku da suka shuɗe ya shiga dawo mata tamkar a taswirar allon da ake talla saman titi... “Calm down ƘAUNA”. Kai ta shiga girgiza masa. Hawaye masu gudun tsiya na sauka a jikinsa. Duk da tausayinta dake son kwatarta wani gefe na zuciyarsa ƙarfafashi take. Tabbatar masa take zata iya ɗauka kamar farko. Ya cire tausayi ya samu komai ta yanda zata kasance irinsa. Ya gamsu da tabbatarwar ɗayar zuciyarsa, dan haka salon ya sake ɗaukar sabon sauyi. Komai ya koma bigiren da zafi-zafi....

Tabbas Nimrah ta tabbatar da fami yafi sabon ciwo. Dan yau a neman ceto har Nabeeha sai da ta shigo ciki. Daga ƙarshe kamar waccan ranar dai ta sake rasa numfashinta. Sai da manya suka dawo hayyacinsu ya fahimci tarihi ya sake maimaita kansa kenan. Yaji ba daɗi, sai dai dama doctor ya sanar masa da hakan zata dinga faruwa kafin komai ya daidaita. Dan dole sai a sannu-sannu ƙarfin nasa zai koma dai-dai misalin da yake a baya da bazai cutar ba. Kamar ranar ya sa mata ruwa ta farfaɗo. Ai ko da farko da fasa masa ihun kukan daya sashi rufe mata baki da nashi ta fara. Rawar jikinta ce ta ƙaru, dan tayi tunanin sabon yaƙi ne za'a koma. Aiko da ƙyat ta tsallake rijiya da baya. Dan jin al'amarin zai sake juyewa Dadah ya janye, da hannunsa ya maye gurbinsa. Sannan ya fara jera mata kalaman lallashi. Ta haɗiye ihun kukan, amma hawaye basu dakata ba. Hakama jikinta bai samu natsuwa ba. Da ƙyar ya kauda kai ya ɗauketa zuwa bayi. Sai da ya tabbatar ruwan zafi ya ratsa mata jiki yanda ya kamata duk da magiyar da take masa da kuka sannan ya barta. Da taimakon nasa dai suka tsaftace kansu ya sake ɗakkota. Bai tsaya bi takan neman komai ba ya sauketa a gadon yaja musu duvet. Gara ma shi akwai towel... “Sleep”. Ya faɗa cikin kunenta, sai kuma ya dawo ta inda idannunta suke ya fara hura mata iska. Dole ta sake rufesu da ƙyau. Kamar abin siddabaru cikin ƙanƙanin lokaci barci yace salamu alaikum, dan dama maganin bai gama sakinta ba...........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*