Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 3

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 3

.....for wanting to avenge their father. That's dirty math. Yay the little one, looking back and looking at the box that T-Dalha gave him yesterday. After five minutes, he went to where the box was on the table. He put the coffee cup down, then took the box and sat down. Jijjuyashi started working, and for the first time he tried to open it. But what refuses to open. He tried three times, but he just let out a small smile, turning away and putting the box away. Just then Daddy Imran's call came into his phone. He looked at the phone for a while and then picked it up. "See here coming to you". Imran said after Dadah greeted him. "Okay". Dadan also answered briefly. Then the phone was disconnected. In less than 20 minutes, the same train that brought them yesterday brought him. After they were settled, he crossed over to their Dadah. Dadah, who was looking at him, said, "You just swear you won't leave me alone." Imran was looking at him speechless, then he laughed and sat next to him. "Humm, why is this man starting to scare me? My daughter hasn't finished conquering you?". "Oh, what are you thinking about?". Dadah added to his debt.....

Standalone post2,000 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 3_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Ba sunan Baba kawai ba, a labarin Kawu Tanimu ya shinshino wani abu game da mahaifin Nimrah. Idan lissafinsa yayi dai-dai mutumin nan ya jefa kansa a wannan musifar ne saboda son ɗaukar fansar mahaifinsu. Gurɓataccen lissafi kenan. Yay ƙaramin tsaki, tare da waiwayawa ya zubama dan box ɗin jiya da T-Dalha ya bashi idanunsa. Fin mintina biyar ya nufi inda box ɗin yake a saman table. Kofin coffee ɗin ya ajiye, sannan ya ɗauki box ɗin yana kaiwa zaune. Jijjuyashi ya shiga yi, sai kuma a karo na farko yayi yunkurin buɗe shi. Sai dai me ya ƙi buɗuwa. Ya gwada har sau uku amma yaƙi, sai kawai ya saki ƙaramin murmushi yana kauda kansa da ajiye box ɗin. Dai-dai nan kiran Daddy Imran ya shigo wayarsa. Ido ya ɗan zubama wayar sai kuma ya ɗauka. “Gani nan zuwa wajenka”. Imran ya faɗa bayan Dadah ya amsa masa sallama. “Okay”. Shima Dadan ya amsa a taƙaice. Daga haka wayar ta yanke. Cikin abinda baifi mintuna ashirin ba jirgin jiya daya kawosu yanzu ma shine ya kawo shi. Bayan an daidaita su ya tsallako zuwa na su Dadah. Dadah dake kallonsa yay wani ɗan murmurshi da faɗin, “Kai dai ka rantse bazaka barni nai angwacina hankali kwance ba”. Cikin sakin baki Imran ke kallonsa, sai kuma ya kwashe dariya yana kaiwa zaune a kusa da shi. “Humm Mutumin nan ka fa fara bani tsoro. Anya Daughter ɗina bata gama mamaye ka ba?”. “Oh da mi kake tunani?”. Dadah ya ƙara bashi amsa yana ɗage gira. “Wlhy Zak... Kai ɗan iska ne.” Dadah ya sake murmusawa. Cike da basarwa ya ce, “Su Faro fa?”. Shima Imran sai ya saki wancan zancen ya bashi amsa da, “T-Dalha ya fita kan maganar gawar nan. Faro kam yana barci.” Kai Dadah ya jinjina. Daddy Imran kuwa ya fara zubama kansa coffee. “Kunyi waya da wani a gida ne?”. “A'a wani abu ya faru ne?”. “Humm mutumin nan ya dawo gidan fa? Harda kawo musu tsaraba. Abin ya bani mamaki, da yazo a gaggauce fiye da shirin mu. Mi kake tunani?”. Dadah yay shiru na kusan mintuna biyu kamar bazai ce komai ba. Imran da ya san nazari yake shima sai yay shiru ya fara shan coffee ɗinsa ma. Sai can cikin firzar da huci mai nauyi Dadah ya miƙe, jikin ƙarfen jirgin ya koma, ya dafe shi da hannu ɗaya, idanunsa akan ruwa ya furta, “Dama nasan zai dawo, sai dai ba a wannan gaɓar ba. Gaggawarsa na nufin akwai mai sarrafa tunaninsa bayan mu. Kuma dole yana a cikin gidan ne. Akwai kuma burin da yake son cimmawa shima”. Miƙewa shima Daddy Imran yayi, ya isa inda Dadan yake. Sai da ya kurɓi coffee sannan ya furta, “Wata sabuwa, to amma ko waye mizai sa yay hakan? Tunda alamu sun nuna basu da alaƙa da juna?.” Dadah ya furzar da huci mai nauyi. “Hasashenka nakan dai-dai basu da alaƙa, hasalima irin salonmu ne wannan.” “Salon mu? Zak.. ka fara bani tsoro fa. Idan fa wannan hasashen naka ya zama gaskiya dole ɗayan biyu ne. Munafuki ko ɗan leƙen asiri”. “Hakan sabon abu ne a aikin tsaro Imran?”. Kalaman sukai masifar dukan zuciyar Daddy Imran har ya kasa bashi amsa. Dadah da yasan halin kayansa yace, “Cool down my Boss. Komai mai sauƙi ne. Ka kira Dabo yanzun ya tura min dukkan bayanan Ojo dake UNIT ZERO”. “Okay”. Dadah ya cigaba da faɗin, “Abu na gaba bayan kama wannan mutumin a shirya yanda za'a kama Ojo. A gefe ka saka Garba cikin tsoro, ta hanyar kafa committee ɗin binciken kuɗaɗen makamai da sukai ɓatan dabo a gwamnatin data gabata. Ko kuwa yaka gani?”. “Tabbas hakan yayi. Duk da nasan tun a bayyanar mutuwar mutumin nan abubuwa zasu fara kwace musu”. “Ai sun ma fara kwace musun, dan a yanzu haka a haukace suke da binciken inda suke zaton ka ɓoye musu yaransu ne, duk da tunaninsu ya fara rabuwa akan akwai ɓoyayyen jami'i dake maka ayyukan. Shiyyasa ma suka dakatar da duk wani shiri nasu. A wannan komawar tasa ne suke son yin zaman shimfiɗa sabbi domin bamu ƙafa”. “Hummm ƴan wahala. Basu san mu tuni muka basu ƙafar ba. Ai naga kwana biyu sun rage bibiyarka. Inaga sun fara cire zargin kana ɓoyayyen aikin da suke hasashe a kansu”. “Nima na fahimci hakan, sai na lura sun fara maido zarginsu kanka ɗinne shiyyasa. Sai dai Garba ya fara zargin Faro ma. Shiyyasa nake son a tsorata shi hankalinsa yabar kansa, dan nasan yana da naci idan yaso yin abu, sannan shegen kansa ne yana da basira”. “Mara amfani ba. Miye amfanin basira irin ta Garba Zak... Sune fa idan suka gawurta suke zamewa duniya musifa. Dan wlhy Garba ya samu dama tsaff zai zama ɗaya daga cikin basawan duniya masu shirya yaƙe-yaƙen ƙasa da ƙasa”. “Miye banbanci ma yanzu. Tunda abinda suke shiryama ƙasar tamu kenan. Babban burin su kawai ta hargitse, ban sani ba ko su suna tunanin za'a barsu gadin duniyar ne”. “Wlhy suna sane. Gurɓatacciyar zuciya ce kawai da tsabagen son kai ke ɗawainiya da su. ALLAH dai ya shiryemu baki ɗaya.” “Amin ya rabbi”. “Mi kake tunani game da Baba ɗin can kuma?”. “Humm Imran kaina ya kulle matuƙa. Shiyyasa ma kaga na sakin zancen jiya.” “Baka buɗe box ɗin bane?”. “Na gwada hakan baiyi ba”. Juyawa Imran yay yana kallon box ɗin. Sai kuma ya nufi inda yake ya ɗakko shi. Jujjuyashi shima ya shiga yi amma babu wani wajen da za'a iya buɗe shi, duk da kuwa akwai tsagar dake nuna murfi a samansa.. “Mi hakan ke nufi?”. “I don’t know…” Cewar Dadah yana ɗage kafaɗa da taɓe baki. Shiru ne ya biyo baya, Daddy Imran nata dai ƙoƙari amma baiyi ba. “To ko zamu fasashi ne?”. “Inaga mu ƙara zanari dai. Dan tunda ya bada shi a haka akwai saƙon da yake son isarwa.” “Haka ne kuma na fahimta..”

{×××}{××××}{×××}

Anan ɓangaren First Lady number Rayhana ta saka Nanah ta samo mata. Da farko da tai mata magana ta WhatsApp bata kulata ba. Kuma ta buɗe saƙon. Abinda yasa kuma Rayhana bata kulatan ba saboda bata yarda First Lady ɗin bace da gaske. Itama First Lady ɗin shiru bata sake magana ba. Sai washe gari gata tazo gidan. Rayhana ɗin ce kawai a gidan, Hajiya Hasiba ta fita biɗiɗinta na kasuwanci. Da yake First Lady ɗin tasan Hajiya Hasiba bazata dawo a lokacin ba shiyyasa tazo. Rayhana ta gaisheta da girmamawa kamar yanda suka saba. Sannan ta saka mai aikinsu kawo mata ruwa da lemo tana faɗin. “Gashi Momy ɗin bata nan. Dan nima ban tashi barci na sameta ba”. “Karki damu, wajenki nazo dama ba wajenta ba”. Da mamaki Rayhana ta ce, “Wajena kuma Mom?”. (Dan haka suke kiran First Lady ɗin). “Tabbas wajenki Rayhana. Amma mu shiga daga ciki”. Rayhana bata musa ba, sai dai a ɗarare take. A bedroom bayan sun zauna First Lady ta kama hannunta ta riƙe. “Rayhana ina son ki bani hankalinki nan magana zamuyi mai muhimmanci. Sannan ki faɗa min gaskiya a dukan abinda zan tambaye ki. Na miki alƙawarin zan taimake ki akan koma miye”. Mamaki ya sake kama Rayhana. Sai dai kafin tace wani abu First Lady ta katseta. “Kar kice komai ki saurare ni kawai. Miya haɗaki da Nabeeha? Har kukai rigima?”. “Ba komai”. “Dole akwai. Dan komai na rayuwa yana da dalili Rayhana. Kar kiji tsoro ko ki ɗauka Momyn ku ce ta sakani. Sam ba haka bane, hasalima bata san zan same ki da batun ba. Nima kuma ba ina son ji bane saboda rarrabe mai gaskiya, ina son ji ne kawai dan na taimake ki, nima kuma akwai taimakon da zakiyi min da zai kasance sirri tsakani na da ke.” Numfashi mai nauyi Rayhana ta sauke, sai dai bata ce komai ba. First Lady ta sake jeho mata wata tambayar. “Wani ne ya sakaka ki?”. “A'a”. “Kina son mijinta ne?”. Rayhana ta ɗago da sauri tana kallonta. First Lady tai murmurshi, dan ko Rayhana bata faɗa ba ta samu amsar tambayarta. “Shike nan ma basai kince komai ba. Na samu amsata. Rayhana zan taimake ki, zaki samu Haysam a hannunki. Sai dai da sharaɗi biyu. Zaki min nawa aikin nima. Sannan zaki shirya ɗaukar duk wata cakwakiyar da zaki fuskanta a wajen su. Idan kin amince aikin mu zai fara”. Rayhana ta ɗan ja numfashi ta fesar. “Mom bana jin tsoron duk wani ƙalubale. A kansa zan iya tunkarar komai ma. Sai dai aikin da zaki bani ɗin ne matsalar....” “Ba matsala bane shima. Domin mai sauƙi ne a gareki. Hasalima dole sai kinyi sa in har kina son shiga gidan Haysam. Domin kema yaƙin ki ne, saboda aikin ya shafi duka matansa biyu”. “Har Aunty Nabeeha?”. “Tabbas har ita. Dan itace mafi haɗari a gareki. Tunda in tana ciki ke bazaki shiga ba, dole sai ta fito ke ki samu waje. Waccan ko tana ciki ai zaki iya shiga”. “Haka ne”. “Yauwa ƴar gari. Yanzu nizan wuce. Ki shirya zuwa anjima zan sa azo a ɗauke ki. Kinga sai ki nunama Momyn ku saurayinki ne kawai”. “Shike nan ba damuwa”..........✍️

(Dole ma na dagema ƙawata Nabeeha da addu'a 🥲, irin wannan maƙiya kaca-kaca a gari ina dalili😏🚶🥺.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*