
Post
KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 5
.....speed. Hanan followed her and said, "Who is Mimy?". She couldn't answer because of the jump that Ruky hit her brother. Happiness overwhelmed Biebah. She held it tightly and laughed. Just then Lailah came in and they were laughing at Rukayyan's speed. Then Biebah felt even more happy. The hall was suddenly confused with the joy of seeing each other. Biebah married Khadijah and Naseer and took them all. Hanan, who was clinging to her, was full of happiness when they touched her. "Leave it to us, Mimy." Asma'u made them laugh. Shariffa said, "Calm down, Hanan. In a few months, you will bring them to us." She jumped for joy. Biebah just mumbled. Even though there is a strong relationship between her and her aunts, this kind of talk does not come between them. It would be better this time of the festival if they give them cosmetic products so they can talk. Even though they said they were not hungry, she filled the table with cold food and bowls. Then the interview was spread. If it is true that many mentions of his person felt the fall of the front, Nimrah should have felt it at this time. Dan called a lot. They even tried to check her line on WhatsApp, but her last seen was the d
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 4_* _Chapter 5_
__________________ __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........Da gudu Ruqayya ta shigo cikin falon tana ihun kiran sunan “Small Mom! Small Mom!!”. Biebah dake kitchen tare da Hanan tana girki itako tana zuba mata surutu ta fito da sauri. Biyota Hanan tayi itama tana faɗin, “Mimy waye?”. Bata samu bata amsa ba saboda tsallen da Ruky ta buga ta ɗaneta. Farin ciki ya mamaye Biebah. Ta riƙeta da ƙyau tana dariya. Dai-dai nan su Lailah suka shigo suma suna dariyar gudun Ruƙayyan. Ai sai Biebah ta ƙara jin wani daɗi. Nan take falon ya rikice da farin ganin juna. Biebah ta haɗe Khadijah da Naseer duk ta ɗauka. Hanan dake manne da ita sai taɓasu take cike da farin ciki. “Mimy dama a bar mana”. Dariya su Asma'u suka sanya. Shariffa tace, “Kwantar da hankalinki Hanan. Nanda watanni kaɗan kuma zaki kawo mana irinsu”. Tsallen murna ta shiga yi. Biebah dai murmurshin kawai tayi. Dan duk da akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninta da matan yayun nata irin wannan maganar ba shiga tsakaninsu take ba. Garama a karon bikin nan idan zasu basu kayan gyaran jiki sun iya ɓaro magana. Duk da sunce basa jin yunwa sai da ta cika musu table da kayan sanyi dana kwalam. Daga nan aka baje hira. Idan har gaske ne yawan ambaton mutum nasa yaji faɗuwar gaba ya kamata Nimrah taji a wannan lokacin. Dan ta sha kira sosai. Har layinta suka gwada dubawa a WhatsApp amma last seen nata ma tun ranar da aka kaisu. Sati guda kenan kuma. Dole suka haƙura suka ci-gaba da hirarsu. Bayan la'asar sai ga Mu'azz. Dan daga makaranta yake ya wuto nan saboda Ruky ta tura masa gulmar suna gidan Small Mom. Nan fa hira ta ƙara daɗi. Zuwa biyar Biebah ta sake shirya musu abinci. Ta kuma dage akan sai sunci. Babu yanda suka iya dole suka zauna sukaci. Daga nan aka sake ɗora sabuwar hira. Sai da sukai sallar magriba sannan sukai shirin tafiya. Tamkar Biebah ta bisu haka take ji, idanunsa duk sun cika da ƙwalla. Dama gashi miji baya kusa. Daga ita sai Hanan, amma dai ta kira Didi ta roƙeta Sumayya ta dawo nan su zauna har Faro ɗin ya dawo. Ta kuma mata alƙawarin yau in sha ALLAHU zata turota bayan ta dawo makaranta. Abinda yasa bata zo ba har yanzu kuma maybe bata dawo da wuri bane ba. Har compound ta musu rakkiya, Hanan tayi barci ne shiyyasa aka samu sauƙi. Amma ta tabbatar da sai tayi rigima zata bisu kodan su Naseer. Yanzu Mu'azz ne ya amshi tuƙin. Ruky a gefensa. Su Asma'u sai suka haɗu a baya su uku. Ruƙayya kamar zatai kuka. Dan har ca take wai Biebah tazo su tafi kawai tunda Uncle Haydar ɗin baya nan. Su Lailah nata mata dariyar wannan shirme. Daga haka dai Mu'azz ya fice a gidan maigadinsu ya maida ƙofa ya rufe. Biebah ta share guntayen hawaye da suka cika mata ido tana murmurshi. Aure kenan yaƙin mata. Inba auren ba mizai rabaka da gidanku da ƴan uwanka. ALLAH dai ya bamu ikon jurewa da zaman lafiya da mazajen mu.. Sumayya bata iso ba sai da akai sallar isha'i. Sosai taji nutsuwa daga kewar da su Rukayya suka barta a ciki.....
{%}%{%}%{%}
Da yammaci su Dadah ne ke shan iskar ni'imar dake mamaye da tekunn.. Suna zaune ne daga waje dan haka suke jin armashin iskar da sanyin ruwan. Dadah ne a zaune Nimrah na daga kwance sai dai kanta na'a cinyarsa ne. Labari take bashi yana faman murmurshi. Dan labarin nata ba ƙaramin nishaɗi yake bashi ba. Ita kanta ta fahimci hakan dan haka taji bata jin gajiya. Wayarsa dake gefe ta motsa, koda ya ɗauka ya duba saƙon Imran ne ke sanar masa mutumin fa ya sauka yanzun nan. Komai Dadah baice ba ya maida wayar ha ajiye. Hankalinsa ya sake maidawa ga Nimrah....
^^^^^^^^^
Anan kam anayin magriba Mole ya baro gidan su Mammah. Dan saƙo ya samu daga Dagger cewar ya same shi a hotel ɗin da yake. Saboda wannan karon ba hayar gida ya kama ba a hotel Dagger ya kama masa ɗaki saboda shirin su. Ya iso hotel ɗin ana sallar isha'i. Dan ya samu jinkirin isowa saboda hold up daya ɗan riƙe shi a hanya. Kwance ya samu Dagger a gadon sa. Ya kawar da kai yana jin wani haushinsa. Sai dai a zahiri bazaka taɓa gane hakan ba. Sai ma cikin girmamawa ya fara gaishe shi da faɗin, “Sannu da zuwa Oga”. Zaune Dagger ya tashi, yana amsa masa da, “Kaima sannun ka. Ai harna fara tunanin ko baka ma taho bane”. “Ka bari kawai go slow ne ya riƙe ni.” “Okay, faka-faka zauna muyi magana dan akwai inda zanje. Ya ake ciki inata neman layinka baya shiga?”. “Network ne kawai. Amma nima fa nata nemanka tun a jiya bai je ba. Sai na haƙura saboda nayi niyyar yau naje can dama”. “Ai ba sai kazo ba, saboda ina son aikin nan ya tafi yanda ya kamata. Yanzu dai yaya?”. “An samu matsala, domin basa ƙasar ma.” “What!”. “Kwantar da hankalinka Oga. Kasan dai babu abinda zai faru. Dan malami na yasan aikinsa. Yanda ya tafi da ita haka zai dawo min da abata. Yanzu abinda nake gani mu tafi shiri na gaba kawai”. “Ba shirin bane damuwata, karfa aje a samu matsala. Dan wlhy ya taɓa min Mata naman jikinsa ma sai an tattara da cokali kafin a bizne. Kai ma kuma bazan ƙyaleka ba”. “Babu ma abinda zai faru.” “Zanfi kowa son haka. Maganar shiri na gaba ina ganin muɗan jinkirta shima. Abinda nake son ka bincika mana ranar da zasu dawo. Sai muyi amfani da wannan damar ku aiwatar. Ni kuma ina da sabon shirin da zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.” “Amma Oga......” “Kayi kawai yanda dace”. “Shike nan ba damuwa.” Mole ya faɗa yana danne ɓacin ransa. Shi kuma Dagger ya miƙe batare da ko sallama ba ya fice a ɗakin. Dan akwai aikin da zai yi. Kuma su Mr Specter ne suka saka shi. Da harara Mole ya bishi. Cikin zuciya yace (Matsiyaci, ALLAH ya kaimu. Ba kaine zaka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ba nine zan jefa. Dan daga ranar zaka rasata. Rasawa na har abadan. Bawai ita kawai ba, hatta ni daga ranar zan ɓace maka. Dan yanzu kam nafi ƙarfin zama a ƙarƙashin ka. Nima gashin kaina zan fara ci sannan lokacin cika burina a kanka yayi) murmushi mai yalwa da faɗi ya suɓuce masa. Ya cije leɓuna yana miƙewa, dan dole shima ya fara sabon shiri kenan.....
>>>>>>%<<<<<<
“Dadah wai ina zaka je?”. Nimrah ta faɗa hawaye na ciko mata ido. Jacket ɗin da ya ɗauka ya ƙarasa sakawa. Juyowa yay yana kallonta. Cike da lallashi ya furta, “Zo kiji na faɗa miki wani abu”. Kafaɗa ta maƙe masa. Hawayen da take riƙewar suka silalo. Hannu ya kai ya ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya ɗanyi hanzarin riƙota saboda yanda ta juya fuuuu zata fita. A jikinsa ya sakata, ita kuma ta shiga mutsu-mutsun son ƙwacewa. “Ni dai ba ruwana da kai. Ka ƙyale ni. Kuma sai na faɗama Mammah kullum-kullum yawo kake tafiya ka barni ni kaɗai.” Murmurshi yayi mara ƙarfi yana shafa bayanta. “Idan kika ce babu ruwanki dani ai ƙura ta tashi kenan. Ke ce fa mai kwantar da rikicin nan da babu mai iya tunkara. Kiyi haƙuri kinji Babyn Babien ta. Bazan daɗe ba, abu ne mai muhimmanci shiyyasa zanje. Dan yana cikin dalilin zuwan mu nan. Faɗa min mi kike so na sayo miki”. “Ni tsoro nake ji”. Ta faɗa murya na rawa. Fuskarta ya ɗago. Ya share mata hawayen dake zirara. “Haba Little Tiger ɗina, nasan fa ke ba matsoraciya bace. Kuma zan bar miki wayana aro ba sai ki kira su Mammah kuyi hira ba. Idan kuma cikin ma'aikatan can ɗaya tazo ku zauna to?”. “Naji to ka bani wayar”. Murmurshi yayi kaɗan, tare da rankwafowa ya sumbaci bakin da take tura masa. Idanunsa na cikin nata da raɗa ya ce, “Kin tabbatar kin haƙura ba zakiyi kukan ba idan na tafi?”. Kanta ta jinjina masa. “Good girl”. Ya faɗa yana manne lips ɗinsu. Wani kalar nutsatstsiyar sumbata ya shiga mata. Sai da yaji jikinsa na neman rikicewa ya barta. Da sauri ta juya masa baya saboda kunya. Ya lumshe idanunsa da suka canja launi ya sake buɗewa a kanta. Sai kuma ya matsa ya sake rungumeta ta baya. Hannunta ya riƙe cikin nashi. “Thank you AMANAR HAYSAM. Nayo miki tsarabar?”. Kanta ta jinjina masa. Ya sake faɗin, “Mi kike so?”. “Chocolate”. “Lips ɗin nan ne Chocolate ɗin ai.” Ya faɗa yana shafa su da yatsunsa biyu. Baki ta buɗe kamar zata cije shi. Ya janye su yana murmurshi. “Kin zama kura ko? Sai me kuma za'a ƙaro miki?”. “Ice-creeam”. “A'a banda shi. Dan akwai sanyi anan. Canja da wani abun dai”. “Komai ma to ka sayo”. Wuyanta ya sake sumbata, sai kuma ya saka mata wayarsa a cikin hannu ya sake ta. “Bye bye”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya kalleta ba, dan yasan zata iya saka masa kuka. Aiko kamar ya sani, tana hawayen ta matsa jikin window tana leƙen sa. A gaban idonta ya hau mashin ɗin ruwa aka buɗe masa jirgin ya fice da wani irin gudu na ƙwarewa...........✍️
Mubi su Dadah muga wa za'a cafko? Ko mu tsaya wajen Nimraty?.🤭🏃🏼♀️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*