Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 6

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 6

.....he ended there. Hanu pulled the phone from Faro's ear. He turned around and took a gun to his stomach in the style of a fully trained officer. Seeing Dadah made Faro lower his eyes and shake his head and quickly turned around and took the gun. Dadah one guarded the eyes and removed it. The phone screen looked. Biebah was struggling to say, "Hello Love! Love, what do you call me?". Relaxing, Dadah took the phone to his ear. One of his hands in his pocket, he corrected his voice. "I saw the phone". Biebah's Dada's voice was so loud that she closed her eyes and closed her mouth. She said in a trembling voice, "I entered three Dadah". A chill went through Dadah's heart, along with the love of her younger sister. Biebah entered to greet him with her dancing voice. "Yes?". "I'm fine, Dad. But I miss you." "Lie or not?". "Allah Dadah". She fell into a frenzy. The little one replied, the idiot who didn't say anything again handed the phone to Faro and rushed at him. He answered and laughed. He said, "Biebalo next, don't let your brother slaughter the lamb". She smiled at him. He also hung up the phone while recovering. So he opened the driver's seat and entered. Dadah's son even enter

Standalone post1,966 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 6_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........A bakin ruwan ya samu Faro dake jiransa. Sai dai sam baiga isowarsa ba saboda ya juya baya a jikin motar daya iso da ita yana waya da Biebah. Dadah dake taku a nutsensa ya ƙaraso wajen. Hannu yakai ya zare wayar daga kunnen Faro. Ai ko yay wata kalar juyowa yana kai masa bindiga gafen ciki cike da salon jami'in daya samu cikakken horo. Ganin Dadah ne ya saka Faro runtse idanunsa da dafe kai ya juya da sauri yana ɗauke bindigar. Dadah daya tsaresa da idanu ya kawar. Screen ɗin wayar ya kalla. Dai-dai Biebah na faman faɗin, “Hello Love! Love baka jina wai?”. Hankali kwance Dadah ya kai wayar kan kunensa. Hannunsa ɗaya a aljihu yay gyaran murya. “Nayi seezing wayar”. Biebah da muryar Dada ta dake ta ta waro idanu tare da dafe bakinta. Cikin rawar murya ta ce, “Na shiga uku Dadah”. Wani sanyi ya ratsa zuciyar Dadah, tare da ƙaunar ƴar ƙanwar tashi. Biebah ta shiga gaishe shi muryarta na ɗan rawa. “Ykk?”. “Ina lafiya Dadah. Sai dai ina kewar ku”. “Ƙarya ko?”. “ALLAH Dadah”. Ta faɗa cikin shagwaɓa. Ƙaramin murmurshi yayi, batare da ya sake cewa komai ba ya miƙama Faro wayar yana hararar sa. Amshe abarsa yay yana gimtse dariya. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Biebalo next kada yayanki ya mun yankan rago”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi. Shima ya yanke wayar yana murmurshi. A haka ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Dan Dadah har ya shige gefen mai zaman banza. Sai da ya tada motar har suka fara barin wajen sannan Faro ya juyo ya ɗan kallesa. Kan Dadah a duƙe yake yana danna waya. Dan haka Sai ya sake maida kansa ga titi. “Yanzu asibitin zamu je?”. Wayar Dadah ya ajiye yana ɗan furzar da iska. Sai da yay crossing ƙafafunsa sannan ya bashi amsa da. “Ba Imran na tare da shi ba?”. “Eh suna tare”. “Kira su kawai mu haɗu acan”. “Okay”. Faro ya faɗa yana ɗaukar waya. Cikin ɗan raba hankalinsa tsakanin wayar da titi yay kiran Imran. Bugu ɗaya ya daga. Yasa wayar a hans free. Daga can Imran yace, “Yaya kun taho ne?”. “Eh gamu nan a hanya. Kuna asibitin ne?”. “No mun fito. Yanzu haka gamu a hanyar gidan.” “Oh har yazo kenan?”. “Tun ɗazu ma. Kawai mu haɗe daku a can”. “Okay”. Wayar ya yanke. Shiru ya ɗan ratsa motar, sai kuma zuwa can Dadah ya katse shirun. “Ya jikin yaran nan guda biyu?”. “Humm ka bari kawai sai a hankali wlhy. Brain ɗin yaran baida ƙarfi. Shiyyasa hodar iblis ɗin tai musu illa da yawa.” Dadah ya ɗan taune lips. Cike da takaici. “Ina zaton akwai abinda suke haɗa musu a ciki. Ya kamata ayi gwaje-gwaje a kanta”. “Nima nayi wannan tunanin. Dan har nake ma Imran bayani. Dama dawowarka muke jira”. “No wannan ba abinda za'a jirani bane. Kawai a aiwatar”. “Shike nan, in sha ALLAHU muna komawa”....

%==%==%==%

Nimrah data gama ƴan koke-kokenta falo ta koma. Ta hau kujera ta zauna tare da ɗaukar mayafi ta rufe ƙafafunta dan akwai sanyi. Ga skirt ɗin jikinta ƙarami. Koma ace kayan duka. Damma Dadah ya saka mata Safa a ƙafa da kansa bayan sun idar da sallar magriba. Television ta kunna, ta saka ƙarar can ƙasa. Sai kuma ta ɗauka bowl dake cike da grapes ta sa a cinyarta. Sai da takai ɗaya baki sannan ta ɗauki wayarsa ta fara ƙoƙarin kiran Mammah. Yau dai cikin sa'a ta shiga. Wani farin ciki ya tsarga mata. A take murmurshi ya ƙawata fuskarta. Damuwar da Dadah ya barta a ciki ta gudu. Cikin ƙaguwar a ɗaga mata tace, “Mammah ɗaga Mammah”. “Ai na ɗaga Autar Mammah”. Mammah ta faɗa daga can tana dariya. Itama Nimrah dariyar ta ƙyalƙyale da shi da faɗin, “Mammah na i miss you irin mai cika duniya ɗin nan”. Anan ma Mammah sai da ta dara. Ta ce, “Auta ƴar Mammahn ta. Ina fatan kina lafiya?”. Da sauri Nimrah ta fara gaishe ta. Mammah ta amsa da kulawa tana tambayarta yaya take?. “Mammah ina lafiya. Sai kewar ku. Ina jin kamar nayi tsuntsuwa na zo na ganku. Mammah ina su Yaya Mu'azz?”. Kafin Mammah ta amsa karaɗin su Ruky ya cika falon ita da Mu'azz. Suna kitchen ne dama wai suna wainar fulawa. Dan yanzu anan su bayan la'asar ne. Su kuma Dubai na jiran isha'i ma dan bakwai ta gota sosai. “Kin gansu nan ma sun ishe mu da rigimarsu tunda ke ALLAH ya hutar dake ta kwana biyu”. Cikin dariya Nimrah tace, “Mammah Yaya Mu'azz ɗin ne sai a hankali. Rinton sa yayi yawa ne”. Mammah bata kai ga bata amsa ba Mu'azz ya iso wajen yana kawo ƙarar Ruky data zabtare waina wai ita da Ninah. Dan yanzu tsabar fitina idan za'a raba abu sai tace sai an raba da Ninah, kuma itace mai cin gadonta. Mu'azz na jin an ambaci Nimrah ya saki batun faɗa yana matsowa kusa da Mammah da kwalama Ruky kira tazo. Ai dole Mammah ta miƙa musu wayar ganin suna shirin hayeta. Su Kulu na kwasar dariya da Gwaggo Khadijah data fito.....

»»««»»««»»««

A hanya su Dadah suka haɗe da su Imran dake cikin wata zuƙeƙiyar mota baƙa wulik. Dan duk da tasu Dadan ma nada shegen ƙau wadda su Daddy Imran ke ciki ta fita. Leƙowa kawai Imran yayi ta window ya miƙoma Dadah tab. Daga haka kowa ya maida gilashinsa ya zuge suka tafi a jere. Gida ne kyakkyawan gaske, sannan katafare bana wasa ba, dan kai tsaye zamu kirashi da Mansion ne. Yanda suna isowa aka wangale musu gate zai baka tabbacin an san da zuwan su. Akwai securitys a gidan sai dai ba masu yawa ba. Dan da'alama gida ne na sirri. Security ɗaya dake tsaye a ƙatuwar ƙofar shiga cikin gidan ya matso gaban motocin, dan basu tsaya a ko ina ba sai gaban ƙofar. Ido suka haɗa da Dadah. Yay masa signal da nashi idon da ake gani kaɗai. Dan akwai facemask daya sanya. Dadah ya kawar da nashi idanun sannan ya fito dan security ɗin harya buɗe masa. Suma su Imran dun fitowar sukai. Sai dai yanzu ɗaya ya ƙaru a cikinsu. Su duka sun rufe fuskokinsu da mask suma. Dan shima Dadah ya saka, sanda yake fitowa kuma ya sake ɗora baƙin gilashi daya lulluɓe ainahin ƙwayoyin idanunsa. Dama ga kayan jikinsa komai baƙi, hatta hannayensa akwai safar hannu a jikinsu. Zaratan mazajen huɗu suka rufa masa baya. Dan ɗayan da ya sake ƙaruwa a cikinsu yasa su zama huɗu bayan Imran, Faro, T-Dalha. Sai dai kasancewar fuskokinsu a rufe suke bazamuce waye shi ba. Suna isowa ƙofar ta rabe biyu a hankali. Wani azababben luxury parlor ya bayyana. Kai da gani kasan kuɗi sun jigata. A bakin ƙofar computer ce zatai searching nasu kafin su wuce, ai ko Dadah ya danna agogonsa a kaikaice. Na'urar ta gama zuƙe-zuƙenta ta sanar da babu komai a tare da shi tana danna green danja. Hakama su Imran ɗaya bayan ɗaya sai da ƙofar tai musu. Suma kuma babu wani damuwa suka wuce. Wata kyakkyawar doguwar farar mace dake sanye cikin jar doguwar riga da akai ma wata shegiyar tsaga tun daga ƙasa har ƙarshen cinya ta taso tana wani kalar juya siririn jikinta mai kama dana tarwaɗa. Daga sama kuwa rabin ƙirjinta a bayyane yake. Cikin wani kallo dake bayyana ainahin fitinar dake ranta tabi Dadah da kallo. Shi kam bamace kallonta yake ba ko a'a. Dan idanunsa na cikin gilashi. Cikin yarfar da hannu da karya jiki tai musu baraba da zuwa da harshen turanci. Dadah ya ɗaga mata yatsu biyu kawai. Sai ta saki wani mugun murmushi. Sannan tai wani juyi da jikinta ta fara tafiya. Babu wanda yay magana suka take mata baya. Ƙayataccen staircase ɗin dake tsakkiyar falon ta fara takawa, daga gani kasan akwai zinari a kwalliyar dake wajen. Ta tsaya a step ɗin farko tana juyowa. Cikin wani irin kaɗa yatsunta a jikin gilashin staircase ɗin da salo irin na iskanci ta ce “Shi kaɗai zai haura”. A take Imran ya zaburo zai yi magana amma sai Dadah ya ɗaga masa hannu. Wani alama yay musu da yatsunsa batare da yace komai ba yay mata nunin suje. Tayi murmurshi mai haɗe da lumshe idanu. Sai kuma ta botsare ta fara wata banzar tafiya. Dadah ya kawar da kansa cike da takaici yana jan tsaki a zuciyarsa. Eh shi mai yawan buƙata ne. Amma a kan halattacen nama. Shifa ko mace zatai zir a gabansa in har ba halak ɗinsa ba koda yana cikin yanayi ne baya jin ta birge shi. Dan a rayuwarsa zina da shaye-shaye suna cikin abubuwan da yafi tsana a ruhinsa. Sai dai hakan baya hana shi yin addu'a ga masu yi da musu fatan dainawa idan suna da rabo. Tare da nema wa wanda basayi da shi kansa kariya wajen UBANGIJI na har abadan. Dan wasu mummunar ƙaddararsu ce ke musu jagora fara aikatawar. Shima mutum ne kuma kamar kowa bashi da tabbacin tsallakewa sai da yarda da kariyar ALLAH...........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*