Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 11

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 11

..... she even had to ask him about their trip. Dan hears her saying what time they and Ninah will get off?. But he didn't seem to mind and he hugged her. She was going to speak again and he covered her mouth with his own. Then the story changed. After finding out how he wanted her to help him, he had to prepare for the office since he prevented them from going down a bit. The breakfast schedule in Mammah department has not changed for them yet. They go there to break and go to work. Just as Shariffa accompanied Jaafar to give them food themselves, so Ruqayya and Asma'u joined the system. Now Ruky and Ammar came out holding her hand and teasing her. Asma'u and Bilal also came out holding each other's hands. Asma'u, the king of shame, removed her hand from Bilal's and greeted Ammar. Ruky knows how she wants to remove her own Ammar. She had to wait for him then. Bilal acted as if he did not see them. But he laughed in his heart unlike Asma'u who was always smiling. Ruky also greeted Bilal as usual, she also greeted Asma'u. After that, they joined the Mammah section, today they are the only exporters of Ja'afar and Ma'aruff who do not go out to the market. They even got to Kulu and pr

Standalone post1,979 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 11_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Da ƙyar Ammar ya haɗiye bai gayama Ruky dawowar su Nimrah ba. Dan ya tabbatar yana faɗa bazai samu abinda yake so ba da safiyar nan. Dan haka yay gum da bakinsa. A hakan ma sai da ta ɗakko masa batun tafiyar tasu. Dan yana jin tana faɗin ko ƙarfe nawa su Ninah zasu sauka?. Amma yay kamar bai jiba sai ma rungumeta da yay. Zata sake magana ya rufe mata baki da nashi. Daga haka labarin ya canja. Bayan samun yanda yake so ta taimaka masa dole yay shirin office tunda ya hanasu su ɗan runtsa. Har yanzu tsarin yin breakfast a sashen Mammah bai sauya musu ba. Can suke zuwa su karya sannan su wuce aiki. Kamar yanda su Shariffa ke raka su Ja'afar su basu abincin da kansu haka Ruƙayya da Asma'u suka hau tsarin. Yanzu ma Ruky da Ammar sun fito yana riƙe da hannunta yana tsokanarta Asma'u da Bilal suka fito suma nasu hannun cikin na juna. Asma'u sarkin kunya, ta cire hannunta daga cikin na Bilal tana gaida Ammar. Ruky kam duk yanda take son cire nata Ammar yaƙi saki. Sai da ta mintine shi sannan. Yi Bilal yay kamar bai gansu ba. Sai dai yayi dariya a zuciyarsa saɓanin Asma'u datai murmushi. Itama Ruky ta gaishe da Bilal kamar yanda suka saba, ta gaida Asma'u ma. Daga haka suka rankaya sashen Mammah dan yau su kaɗai ne masu fitar Ja'afar da Ma'aruff basa fita kasuwa. Sun samu har su Kulu sun shirya breakfast. Suna zama sai ga Lailah tare da yara cikin Uniform. Zuwa suka rungume Uncle's ɗin nasu da Auntys tare da gaishe sun. Suma su Bilal suka gaida Lailah da girmamawa. Haka ma su Ruky. Daga haka suka fara kari su da yaran. Ruky da Asma'u na zuba musu. Lailah kuma yanzu girma yazo tunda an samu masu tayo. Bedroom ɗin Mammah ta nufa domin gaisheta ita da Gwaggo Khadijah...

Bayan wucewar su Ammar Mu'azz ya fito. Shima yau bazai je school ba. Shine ya fasa ma su Ruky ƙwai akan dawowar su Nimrah. Ruky tai wani kalar rikicewar farin ciki harda tsalle. Sai da Gwaggo Khadijah ta riƙeta tana faɗin banda tsalle dan basu sani ba ko jikansu na kwance. Bata wani fahimci dalilin hanata tsallen ba ta wuce kitchen. Acewarta tana da girki na musamman da zatai ma Ninah. Babu wanda ya hanata. Sai ma bin bayanta da suma su Shariffa sukai dan suma akwai nasu shirin, duk da sai a lunch zasuyi dai. Tuni kuma sun kira su Aunty Ummi sun baza musu har Biebah. Yo a gayama ƴaƴan Mammah gayya. Balle wannan da sukai ma shiri na musamman. Ai tuni sukace suna tafe suma. Dan hatta Biebah ta shirya lallaɓa Faro da son laɓewa da yima Dadah sannu da zuwa dan bazata yarda ayi babu itaba. Ina ba wannan maganar yau ranar show ce. Ta san dole ne a baje haja yanda ya dace. Mammah da Gwaggo Khadijah dai basu san mi suka shirya ba. Dan wajen goma Ma'aruff da Ja'afar suka shigo suma, sai kawai suka hau hira. Mu'azz daya tashi cikin mata dama harda shi ake a kitchen saboda tsabar cin kai...

[]%[]%[]%[]%[]%[]

Nabeeha da bata san Dadah ya dawo ba sai wajen goma na safe yay kiranta a waya. Cikin barci ta ɗaga da ƙyar batare data duba mai kiran ba. Sai da yay sallama ta miƙe a zabure da faɗon, “My D.” “Uhmm ƴar gata barci ma kike yi” “To D. ai gari bai gama waye ba”. “A wajen ƴan gata irinki ba. Ki kawo min Coffee”. “Coffee! Ka dawo ne?”. “Uhmm surprise nai miki”. “Imyimm zan rama. Yanzu dai ka bani mintuna kaɗan”. “Ba damuwa”. Ya faɗa yana yanke kiran. Duk da tana jin wani abu mai nauyi yana tiƙaƙo mata zuciya tayi farin ciki da dawowar tasa. Guntun text ta turama Jiddah tana sauka a gadon. Minti biyu sai ga kiran Jiddah ɗin. Sai kawai ta ɗauki wayar ta wuce bayi da ita tana amsawa. Bayan sun gaisa Jiddah ta ce, “Dan ALLAH ki sama ranki nutsuwa. Kada ki nuna masa komai. Sannan ki dafa coffee ɗin da kanki bawai mai aiki ba”. “Mtsoww! Wlhy ji nake kamar bazan iya dauriyar nan ba Jiddah. Yaje ya gama abinda yaso da ƴar cikinsa zai zo ni yanzu yana min daɗin baki”. “Humm Aunty Nabeeha wannan sune MAZAN ai. Kima godema ALLAH shi da matar auren sa yayi. Akwai irinsa da yawa, ke wasu ma zasu haife sa na waje suke bi kuma yara ƙanana wasu ma basu kaita ba. Aunty Nabeeha, yanzu dama na hannunki, ta karɓe Yaya Haysam ko barinsa ya suɓuce miki ƴar cikin ki ta ƙarɓe. Dan Namiji tamkar abin kiwo yake. Inda ake kulawa da shi da bashi abinci kawai ya sani, anan kuma yake burin zama. Idan kwana bibbiyu zakuyi kinga weekend ɗin nan taki ce, sai ki ajiye kowa da komai ki fanshe kwanakin ki. Amma fa sai kin cire ma kanki yarinyar nan”. “Naji”. Ta faɗa kawai tana yanke wayar. Sam Jiddah bata damu ba, dan tasan daman yaƙine a gabanta babba, sai kuma ta ya haɗa da addu'a dan wannan yayar tata ƴar sai a hankali ce. Sai da Nabeeha tayi wanka tai shiri sannan ta fito. Kitchen ta nufa. Sai dai batayi yanda Jiddah tace ba. Nanah ta saka ta haɗa mata Coffee powder a cikin coffee maker ɗin. Sai dai ta tsaye tana kallon komai dan kar a maimaita irin ta waccan ranar. Maimakon tai tunanin ya kamata bayan nan ta nema masa wani abun breakfast ina. Kamar an jeho Rayhana da kwana uku kenan da dawowarta sai gata ta shigo. Da mamaki take kallon Nabeeha da taci kwalliya. “Aunty fita zakiyi?”. “A'a mi kika gani?”. “Naga kin ci kwalliya da uwar safiyar nan. Keda nasan lokacin tashin ki barci ma baiyi ba”. Ƙaramin tsaki tayi, batare da tunanin komai ba ta ce, “D. Ne ya dawo zai sha coffee”. Wani kalar masifar bugawa ƙirjin Rayhana yayi. Cikin rawar lips ta ce, “Wai Yaya Haysam?”. “Akwai wanda nake kira da wannan sunan bayan shi?”. Nabeeha ta bata amsa tana ɗaukar kayan da Nanah ta haɗa ta fice abinta. Cikin takaici Rayhana ta kwaikwayi abinda Nabeehan ta faɗa a zuciya tana rakata da harara da gatsina baki....

\\××\\××\\××\\××\\

Sai kusan sha ɗaya hajjaju Nimrah kuwa ta farka. Bayan ambaton addu'ar tashi daga barci ta buɗe idanunta. Sai kuma ta yunƙura ta tashi zaune. Wata irin kewar Dadah ce ta shiga saukar mata. A irin wannan yanayin tana tashi takan ganshi ne a kusa da ita yana barci ko yana zaune. Amma yau ya mata nisa, duk da gasu a muhalli guda. Tabbas sati biyu ta bar mata babban tarihi da bazai gogu ba, al'amuran da suka faru a cikinsa bazasu lissafi ba. Sai dai ta shirya maimaita wanda suka fisu tare da Dadanta. Dan ta riƙe kenan babu sakaci babu ɗaga ƙafa. Bazata shiga hurumin daba nata ba, amma kuma zata tsare gidanta da mugayen securitys ta kowanne kusurwa.... Ƙarar wayarta daya bata mamaki ya katse tunaninta. Ta ɗauki wayar ta jujjuya, duk da dama dai matsalar buɗewar Data take tunanin ta samu bana kira ba. Ganin zata tsinke ga shi Ummu ce yasa ta ɗaga kiran. (Aunty Mommy) gaisheta ta shiga yi cike da farin ciki. Daga can Aunty Mommy ta ce, “Nimrah barci kike yi?”. “Eh Ummu tunda nai salla na koma”. “A ina?”. Cikin rashin damuwa ta ce, “Ummu ɗakin da kika kai ni waccan ranar”. Kallon jun Aunty Ummi da Aunty Mimi dama su Shariffa sukayi, aunty Ummi taima Aunty Mommy alamar ina Dadah?. Dan haka Aunty Mommy tace ma Nimrah. “Ina Dadah fa?”. Anan ma kai tsaye Nimrah tace, “Ummu yana ɗakinsa.” “To yi sauri ki shirya muna sashen Mammah”. Wani ihun farin ciki Nimrah ta saki tana jefar da wayar batare data kashe ba ta nufi bayi. Dama neman dama take ya kuma ta samu. Haba sati biyu bataga Mammah da Ruky da iyayenta ba ai magana ta girma. Ta kuma yi babban haƙurin daya dace ai mata jinjina a haɗa da award. A gaggauce tai wanka ta fito. Sauri-sauri ta hau shiri cikin atamfa doguwar riga. Ko ɗan kwali bata tsaya ɗaurawa ba ta yana gyale ɗankwalin a hannunta ta fito. Hajjaju Rayhana shugabar rashin aikin yi ta ƙasa ce kawai a babban falo tana dakon jiran fitowar Dadah ko Nabeeha. Amma bulum babu wanda ya leƙo. Sai kuma ga amarya ƴar garari ta fito. Ko kallon inda take Nimrah kuma batai ba. Hasalima ita bata ma ganta ba ta fice. Sumar zaune Rayhana tayi, har numfashinta na sama da ƙasa saboda kiɗimewar ganin canjin dake a bayyane ga Nimrah duk wanda ya kalleta. Yarinya tayi wani fresh kamar irin eutopian mutane ɗin nan. Jiki na ɓari ta miƙe zuwa gaban window tana leƙen Nimrah da tuni tayi nisa zuwa sashen Mammah... “Babbar bala'i. A sati biyu kawai? Tab ɗi jan. Shi ke nan na mutu ni Rayhana”. Wasu wahaye musu shegen zafi suka shiga rige-rigen sakko mata akan fuska. Ƙirjinta kuwa ya mata nauyi na rashin gaira balle dalili..........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*