
Post
KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 5
.....n quarrel like this with the mother. Muhammad Hunaif is the son of Abuja Minister Alhaji Mahmud Mijinyawa and Hajiya Kaltume Muhammad (Mami). His mother Mami is a lawyer, and she does humanitarian work, she has an organization called Kaltume Women And Youth Initiative here in Abuja. Muhammad Hunaif is the second son in the list of six children of Alhaji Mahmud, Hamza is the eldest, then Hunaif, then AbdulHameed, then Yusuf, then the younger two children Inara and Inaya. Hamza and Hameed studied Business Management, and now they are running their father's companies. Hunaif studied medicine and surgery, but now he is a footballer because ball is what he loved since his childhood, the medical field he went to was his parents' choice. Yusuf also followed Mami's footsteps, he is in his final year at the University of Abuja studying Law. The two children are already sss1 as there is a long birth gap between them and Yusuf. Hamza and Hameed are married with children, Hamza's two children are both boys, Hameed's two children, one female and one male. Back to story... After about an hour, Hunaif got up, switched off the TV, went upstairs, went to his room, took a bath and got ready in
Page 5
Aguyi Irinsu Street
"Hunaif! Hunaif!" Sunan da wata dattijuwar mata ke kira kenan cike da ɓacin rai tana saukowa daga stairs, Hunaif dake buga PS a falo ya ɗago dara-daran idanunsa ya kalleta da murmushi yace; "Mami wannan kira haka, Allah ya sa lafiya?" Daƙuwa ta yi mishi, tace; "Uwar ka ce ba lafiya ba, yanzu tsakani da Allah ban isa na saka ka abu ba sai ka ɓata min rai?" Ajiye controller ɗin hannunsa ya yi, ya kama hannun Matar ya zaunar da ita a gefe, yana wannan shu'umin murmushin nasa yace; "Zauna mu yi magana Mami, wani laifin na kuma aikata ne?" Ya tambaya kamar bai san abinda ya yi ba. Mami ta harare shi tace; "Tambaya ma kake? Ina na ce ka kai Inti?" Sosa kansa dake cike da gashi ya yi, yace; "Afuwan Ammi, yarinyar ta dameni da surutu ne a hanya shi yasa na sauketa a hanya."
"Ka kyauta." Mami ta faɗa cikin ɓacin rai, sannan ta tashi ta koma ɗakinta dake sama. Murmushi Hunaif ya yi, ya ɗauki controller ɗinsa ya cigaba da buga game ɗinsa hankali kwance, don sun saba irin rigima haka da Mamin.
Muhammad Hunaif kenan ɗan Ministern Abuja Alhaji Mahmud Mijinyawa da kuma Hajiya Kaltume Muhammad (Mami). Mahaifiyarsa Mami mai Shari'a ce, kuma tana humanitarian work, tana da organisation mai suna Kaltume Women And Youth Initiative a nan cikin garin Abuja. Muhammad Hunaif shine ɗa na biyu a cikin jerin ƴaƴa shida na Alhaji Mahmud, Hamza shine babba, sai Hunaif, sai AbdulHameed, sai Yusuf, sai auta ƴan biyu Inara da Inaya.
Hamza da Hameed su yi karatu ne a ɓangaren Business Management, yanzu haka suna riƙe da companies ɗin Babansu.
Hunaif ya karanci Medcine and surgery ne, amma yanzun haka shi footballer ne saboda ball shine abinda yake so tun yarantarsa, Medical field da ya tafi ma zabin iyayensa ne wannan.
Yusuf kuma shi ya biyo ƙafar Mami, yana final year a University of Abuja yana karantar Law.
Ƴan biyu kuma tukun suke sss1 kasancewar akwai tazarar haihuwa sosai tsakaninsu da Yusuf.
Hamza da Hameed suna aure da ƴaƴa, yaran Hamza biyu dukka maza, yaran Hameed ma biyu, mace ɗaya namiji ɗaya.
Back to story...
Bayan kusan awa ɗaya Hunaif ya miƙe, switch ɗin TV ya kashe, ya haura sama, ɗakin shi ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin wani expensive pant baƙi da ash designer t-shirt, ya feffesa turaruka masu ƙamshi sosai, wayoyinsa ya kwashe a gaban mirror ya fita daga ɗakin. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Mami ya yi kafin ya tura a hankali ya shiga da sallama ɗauke a bakinsa, Twins na kwance a lallausar rug dake shimfiɗe a ƙasar ɗakin, suna buga Ludo a iPad ɗin su, suna jin sallamr Hunaif suka gyara kwanciyarsu, yana shiga suka gaida shi, a taƙaice ya amsa da "Lafiya." Ya ƙarasa bakin gado, ya zauna a gefen Mami dake aiki a laptop ɗinta, Yana mai ɗora kanshi a kafaɗarta. A hankali ya furta; "Aiki kike haka?' Ba ta kula shi ba ta cigaba da aikin ta, ƙasa ya yi da murya, a marairaice yace; "Mami I'm not feeling too well." Kallonsa Mami ta yi, ta gan yanayinsa ya canza all of a sudden, ta saka hannu a goshinsa, tace; "Your temperature is not high, me ke damunka?" Kanshi ya yi pointing mata yana lumshe ido. "Ka sha magani?" Mami ta tambaya sounding very worried. Girgiza mata kai ya yi, ya ce; "I can't take drugs on an empty stomach." Mami ta kalle Twin da suka mayar da hankalinsu kan yayansu, tace; "Inara get your brother some food." Da sauri Inara ta miƙe ta fita, Inaya kuma ta ƙaraso kusa da Hunaif tana yi masa sannu.
Sinasir biyu Inara ta Kawo a plate, da bowl cike da cow head pepper soup, ta ajiye a kan side drawer ɗin gadon, kaɗan Hunaif ya ci ya ture kwanon, Mami ta buɗe side drawer ɗin ta ɗauki sachet ɗin paracetamol ta ɓala masa biyu ta bashi da ruwa.
A gadon Mami ya yi kwanciyarsa, Mami ta lulluɓe shi da bargo, ta lalle su Inaya, tace; "Ku tafi dakinku, your brother need rest." Allah ya ƙara lafiya suka yi masa kafin suka fita daga ɗakin, Mami kuma ta ɗauki laptop ɗinta ta cigaba da abinda take yi. Minti-minti take kallon Hunaif da ya lumshe ido kamar mai bacci, shi kuwa Hunaif he is trying hard kar ya fashe da dariya ganin yadda Mami ta shiga damuwa don yace bashi da lafiya, where as lafiyarsa ƙalau, Yana neman hanyar da zai lallaɓa Mamin ta yafe masa laifin da tace ya yi mata ne, kuma ya san yadda Mami ta damu da lafiyarsu shi yasa ya yi amfani da wannan damar.
Intisar ƴar kawar Mami ce, tazo gidansu Hunaif ta yi weekend, shine Mami tace Hunaif ya kaita ta ɗan yi shopping kafin ya dropping ɗinta a gida. A hanyar tafiyarsu Inti ta rinƙa yi wa Hunaif hira, a tunaninta ta yi gwaninta, sai kawai ta gan ya gangara gefen hanya ya yi parking, rafa ɗin dubu ɗaya ya miƙa mata, without looking at her ya ce; "Ki je ki yi siyayyar ki, sai ki wuce gida daga nan." Inti ta kalle shi sannan ta kalli kuɗin hannunta, confusingly ta ce; "Ban gane ba." Kai tsaye ya ce mata; "I mean you should get out of my car." Intisar ta kalle shi da mamakin yadda ya canza lokaci guda, ta buɗe baki za ta yi magana, yace; "Get out please."
Ba ta ƙara ce komai ba ta fita daga motar gently, tace; "Thanks for the halfway ride." Hunaif bai kulata ba ya ja motarsa ya barta a tsaye a wajen tana neman taxi.
Mamakinsa ne ya kusa kashe Intisar a tsaye a wajen, ko da ta samu abin hawa ta koma gida, ko da ta koma gida mamakin abun ya sa ta faɗawa Yayarta Teema abinda ya faru, ta duba mata ko ta yi wani laifi, ashe duk hirar da suke yi Mommynsu na bakin ƙofar ɗakin tana jin su, shine ta kira Mami ta ji ko wani laifin Inti ta yi wa Hunaif ɗin.
Tun Hunaif na pretending har baccin gaske ya ɗauke shi. Alarm ɗin wayarsa da ya buga ne ya farkar dashi, a hankali ya buɗe idonshi ya sauke su a kan Mali da ke zaune a kan ɗaya daga cikin couch dake ɗakin tana shan banana smoothie, sauka ya yi daga kan gadon ya je ya zauna a kusa da ita, smoothie ɗin ta miƙa masa ta ce; "Za ka sha?" Girgiza mata kai ya yi. Yana kallonta har ta gama shan smoothien, ta ajiye cup ɗin a kan table dake tsakiyar jerin set of couches dake ɗakin, sai riƙe hannunta, ya kwantar da murya yace; "I'm sorry Mami, What I did to Inti is not intentional, kin gan jiyan mun yi loosing match, ba ta bar ni na ji da abinda ya dameni ba, ta wani cika min kunne da surutu."
"This is still not enough reason na sauke ƴar mutane a bakin titi, ka saka yarinya shigar taxi, abinda ba ta taɓa yi ba a rayuwarta, You just portray that ban isa na saka ka yi abu ba kenan." Cewar Mami tana mai tsare shi da idanu. Hunaif ya sake hannunta, ta kama kunnensa ya ce; "I'm sorry Mami."
"Zan hakura only if Inti ta ce ta yafe maka."
Murmushi Hunaif ya yi wadda ya kasance al'adar sa, yace; "This won't be a problem In Sha Allah." Sannan ya miƙe, yace; "Zan tafi stadium."
Mami ta harareshi ta ce; "Da ciwon kan za ka je stadium?"
Langwaɓar da kansa ya yi, yace; "Kan ya daina ciwo, don't stop me from going please."
Mami ta ce; "Allah ya tsare, ya dawo da kai lafiya."
Hunaif ya kissing hannun Mami ya ce; "Ameen my Mami."
Ɗakinsa Hunaif ya koma ya canza kaya zuwa jersey, ya ɗora dogon wando akan jersey short ɗinsa, ya kwashe wayoyinsa da car key ɗinsa ya fita daga ɗakin, a falo ya wuce su Inara suna buga PS ɗinsa, bai ce musu komai ba ya fita zuwa compound ɗin gidan, motarsa porshce 918 spider ya shiga, Maigadi na buɗe masa gate ya ja motar da speed ya fita daga gida.
Yana shiga stadium ɗin ya yi parking a parking area, yana sauko daga motar hankalin mutane ya dawo kanshi, ya fara tafiya cikin izza yana taku ɗaiɗaya kamar ɗan sarki. Changing room ya shiga, ya cire dogon wando da ya ɗora a saman jersey short ɗinsa, sannan ya fito zuwa cikin field. Excersice suka fara yi suna zagaye field ɗin kafin lokacin buga ƙwallon ya yi. Training match suka yi na upcoming AFCON qualifiers da za a buga. Daga stadium ɗin gidan su Inti ya wuce direct, yana parking, ya cewa Maigadinsu ya yi masa sallama da Intisar. Intisar dake kwance a cinyar Mommynta, sai ƙawarta Zee tana zaune a gefe suna kallon maimaicin Kwana Casa'in suka ji sallamar Maigadi, Mommy ta ja mayafinta dake gefenta ta lulluɓu dashi.
Bayan sun gaggaisa da Mommy ya sanar da ita Hunaif na sallama a waje, Mommy tace ya shigo.
Bayan ya shigo har ƙasa ya tsuguna ya gaishe da Mommy, sannan yace; “Mommy I'm here to take my sister out, ki zan wanke laifina.“
Mommy ta yi murmushi tace;“Kun fi kusa.“
Hunaif ya lalle Inti dake kwance, yace; “Get dress I will be waiting for you outside.“
Intisar na zumɓure-zumɓure ta tashi ta ta shige ɗaki don yin shiri.
#Jikargarba