Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 12

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 12

.....he is busy. The phone started vibrating, a call was coming in. Ammar picked up the phone and put it in his ear. "How are you?" Ammar sighed and said, "She's safe, she's not among those who were kidnapped." He sighed and said, "Alhamdillah." "Yes, I'm not done, the signs show that there's still a lot to do." Ammar interrupted and said, "You have a problem Mega, this was done, there's no good appreciation, it's even doubtful if the criminal is caught. Go back, I don't know what brought you back." "No. There is something I'm following, and I didn't give his phone. It's in my hand. I want to work on it." Ammar said, "Good, keep it safe, don't you dare hand it over to them yet, stop first and see if they can run away." care" "Shikenan" He hung up the phone. ***** He is sitting under a tree, smoking a cigarette, next to him are four young adults.....

Standalone post3,997 words

MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN

SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 AYSHERCOOL

Page 12

Turus ya ja ya tsaya cikin tashin hankali, bayan da ya kunna wayarsa ya ci karo da batun sace ɗalibai da aka yi. Cikin sauri ya kira wayar Ummi. Sai dai wayar ba ta shiga. Cikin tashin hankali ya lalubi wayar Amir, sai dai ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Cikin hargowa Ammar ya fara yi masa faɗa "Wani irin iskanci ne zan din ga kiran wayarka ka ƙi ɗagawa?"

Amir ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba wayar na mota...

"Dalla ina Ummi take? Me yake faruwa ne?"

"Abin da ka ke son tabattarwa ya faru, an shiga makarantar su Ruƙayya an yi garkuwa da ɗalibai hamsin, amma Alhamdillah luckily she's not among, mun je ɗaukko ta ni da Baba Sani, sai dai tana cikin tashin hankali sosai da sosai" Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya nemi guri ya zauna yana faɗin "Amir, ka tabatta tana lafiya babu abin da ya same ta?" "Eh lafiyarta ƙalau, sai dai a tsorace take ne kawai"

"Shikenan take care, zan sake kira in sha Allah " ya kashe wayar yana hamdala. Wayar ce ta fara vibrating, kira yana shigowa. Ammar ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa. "Yaya ake ciki?"

Ammar ya numfasa ya ce "She's safe, ba ta cikin wanda aka sace"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Alhamdillah"

"Wai komawar ka sake yi da gaske?"

"Eh, ai ban gama ba, alamu sun nuna akwai sauran rina a kaba"

Ammar ya ja guntun tsaki ya ce "Ka na da matsala Mega, wannan ɗin ma da aka yi, ba wani appreciation na kirki, ana ma doubting idan mai laifin ka kama. Ka kuma koma, ban san me ya mayar da kai ba kuma"

"Ba aikinsu kawai na koma yi ba, wannan aikina ne, ina son gyara ɓarnar da na yi"

Ammar ya ce "Kuma sun san da hakan? Sun san ka koma?"

"A'a. Akwai abin da nake bibiya ne, and ban bayar da wayarsa ba, tana hannuna ina son za mu yi aiki a kanta"

Ammar ya ce "Good, keep it safe kar ka kuskura ka damƙa musu ita tukuna, ka fara tsayawa mu ga iya gudun ruwansu"

Mega ya ce "Kai na san abin da nake yi fa, idan na kammala abin da nake yi, idan na tabattar babu sauran wani abu, zan dawo soon in sha Allah"

"Anyway yadda ake ciki, ka yi mini magana. Take care"

"Shikenan" Ya katse wayar.

***** Yana zaune a ƙarƙashin bishiya, yana shan sigari, gefensa wasu manyan matasa ne su huɗu. Riƙe da manyan bindigogi su na kaiwa su na komowa. Ya ciro ƙaramar wayarsa ya duba saƙon da ya shigo. "Da alama dara ta ci gida, 'yan maza sun shiga hannu" A sukwane ya miƙe tsaye yana sake karanta saƙon. Da sauri ya fita ya sake danna lambar amma shiru. Cikin sauri ya buɗe bayan wayar, ya zaro layukan da ke cikin wayar, ya kakkarya su, ya watsar ya cillawa ɗaya daga cikin matasan da ke tsaye a kansa wayar ya ce "Ka jajjage ta yanzun nan, mu bar gurin nan dawa ta ɓaci" Nan da nan suka je inda suka ajiye baburansu ƙirar boxers, suka hau suka bar gurin.

*****

Dattijo ne da shekaru sun ja, duk da hutu da jin daɗin da ake ciki, amma yanayin tsufa ya bayyana a tattare da shi, yake zaune a kan kujera 3 seater. President Faruk Kankiya na kan kujerar da ke facing ɗin dattijon cikin girmamawa.

Dattijon ya ce "Mu na mai jajanta maka, gami da takaicin abin da ya faru a mulkinka, na sace ɗalibai 'yan makaranta. Amma ina mai tausarka da baka shawara ka bi komai a nutse sannu a hankali, kar ka yi garaje ko gaggawa ko kaɗan, idan ba haka ba lissafi zai ƙwace maka. Batun bawa rundunar tsaro kwanaki bakwai su dawo da yara ba abu ne da zai yiwu ba. Kai ba jami'in tsaro bane ba Faruku, ka ba su dama su yi aikinsu domin ceto yaran nan cikin sauƙi ba tare da an yi asarar rai ba. Duk da a rahotannin da muke samu an kashe masu tsaron yaran, da yarinya guda ɗaya, amma ba ma fatan a sake rasa rai. Batun za ka sauke shugabanin tsaro ba shi ne mafita ba. Kamar yadda ka ke faɗa aiwatarwa ne naka, yiyuwar lamari na Allah ne. To su ma hakan ne, ka ba su dama, ka toshe kunnuwanka da surutu da tashin hankalin mutane za su ruɗuka ne kawai. Sai kuma ka je ƙafa da ƙafa makarantar, ka ga halin da makarantar ke ciki ka kuma jajantawa iyayen yaran da ba su ƙwarin gwiwa, ka nuna yaran nan da aka sace naka ne"

Jiki a sanyaye Kankiya ya ce "Na fahimce ka ranka ya daɗe, na kuma gode sosai da sosai da wannan shawarwarin da ake bani, atleast na samu releif na kuma fahimci kuskuren da na so tafkawa. Na gode sosai da sosai "

"Good, a yi ta haƙuri da yardar Allah komai zai daidaita" Ya jinjina kai ya tashi suka yi musabaha da dattijon ya fice.

*****

Jikin Mama ne yake karakarwa, tamkar mai shirin hawa bori. Hafsa da Mariya sun yi mata ƙuri da ido, su na jiran su ji me za ta ce, bayan ta sauke wayar daga kunnenta. Hafsa ta ce "Mama mene ne? Me aka ce miki?"

Da kyar ta iya ƙwato "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta miƙe tsaye ta fizgo mayafinta a kan gado"

Mariya ta ce "Mama kin ƙi yi mana magana, kuma jikinki sai rawa yake yi me aka gaya miki ne?"

"Mariya Naja, Naja'atu an ce ba a ganta a cikin sauran ɗaliban ba, shiyasa dama na ce da ku bari na je a duba"

Hafsa ta ce "A'a Mama, ko kin je babu abun da zai canza, yanzu ina za ki je?"

"Gurin su Babballe zan je na sanar musu"

Mariya ta ce "Mama babu abin da za su tsinana mana, dama ki rabu da su"

"A'a ku jira ni ni dai na je na gaya musu" Ta nufi hanyar fita, sai dai ta ji jikinta ya yi mata nauyi, da kyar take ɗaga ƙafafuwanta.

YELWA

Can garin su Ramata, tuni labari ya cika garin an sace ɗaliban makarantar su Rahama. Cikin matsanancin tashin hankali Baffa ya tafi makarantar ,domin duba waɗanda ba a sace ba, ko da Rahama a ciki, sai dai cikin ɗaliban kaf babu Ramata. Jikinsa na tsuma ya fito ya samu wata baranda ya nemi guri ya zauna yana nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Shugaban makarantar ne, ya nufo Baffa jikinsa a sanyaye ya ƙaraso gefensa ya zauna. Ya dafa kafaɗarsa cikin ƙoƙarin kwantar masa da hankali, ya ce "Ka yi haƙuri, Malam Bashir mu ɗauki wannan al'amarin a matsayin ƙaddara. Mu kuma yi addu'a. Gwamnati ta bamu tabbacin yaran nan za su dawo cikin aminci. Da yardar Allah za su dawo gare mu"

Baffa ya numfasa ya ce "Na yi imani da ƙaddara, na sani ko a gida hakan za ta iya faruwa. Ni tunanina ɗaya Ubangiji Allah ya tsare mana su, ka sani ni ita kaɗai ce da ni yanzu" Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya.

"Ka yi haƙuri, mu ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za su kuɓuta cikin aminci"

Har da jami'an tsaro aka haɗu a ka din ga tausar Baban Ramata, duk da akwai sauran iyaye da aka sace wa yara. Amma duk wanda ya ga yanayin mahaifin Rahama dole ya tausaya masa. Idanunsa da farar fatarsa ta yi jawur, jijiyoyi duk su ka fito raɗa-raɗa a goshinsa saboda tashin hankali. Har tasha wani jami'in tsaro ya kai shi aka saka shi a mota, ya nufi Yelwa.

*****

Tun da Isma'il ya yi ɓatan dabo, kwana na biyar kenan, mutane na ta shigowa yi wa su Alina jaje, tare da fatan Allah ya bayyana shi. Sai dai haryanzu abin da yake ɗaure mata kai, bai wuce yadda Mamman ya nuna damuwarsa a kan ɓatan Yayanta ba. Ga shi tamkar ya yi mata asiri, ta kasa gaya wa kowa abin da ya faru. Yau ma da ya aika yaro ta zo, Nadiya ba ta ce komai ba, dan a ganinta, zuwansa na ɗan ragewa Alina damuwar da take ciki. Tun da ta fito ya tsare ta da ido, amma ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Ya nuna mata gefensa kan barandar gidan, ta nemi guri ta zauna.

"'yar ƙwalisa, kin ga ramar da ki ka yi kuwa?" Ya yi maganar daki-daki. Ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.

"Alina, wannan yanayin da ki ka shiga, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki yi haƙuri ki kwnatar da hankalinki. In sha Allah duk inda yake zai bayyana, amma wannan damuwar ba ta kamace ki ba. Tsananta addu'a yakamata mu yi a wannan gaɓar" Ta yi shiru ta kawar da kanta gefe guda.

"Alina" Ya kira sunanta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalli cikin idanunsa. A take abin da ya faru ya fara dawo mata, kuma tana da yaƙinin shi ta gani ba wani ba. Tun da Isma'il ya ɓace sai a lokacin hawaye ya samu zubowa daga idanunta. Cikin sanyin jiki ya ce "Alina kar ki yi kuka dan Allah. Ki yi haƙuri" Tamkar ya ziga ta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta tashi da sauri ta shige gida ta bar shi a gurin a zaune.

***** YELWA

Duk da yadda 'yan uwan Baffa ke jin haushinsa, na ƙin aurar da Ramata ya kai ta makarantar boko, sun shiga tashin hankali da labari ya fara bazuwa cewar an shiga makarantar su Ramata an saci ɗalibai. Ko da ya tafi dubawa ko har da Ramata a ka ɗauka, bai gaya wa kowa ba sai Juma. Ita kuwa yana tafiya ta je ta gaya wa su Maddibo. Aikuwa hankalin kowa ya tashi. Mussaman 'yan uwan mahaifiyar Ramata da babu yadda ba su yi ba, ya yi mata aure amma ya ƙi.

Sai bayan la'asar sosai sannan ya dawo gida. Aikuwa ya tarar da gidan a cike da mutane. Su na ganinsa suka yi kansa da tambayoyi a kan ina Ramata. Jiki a sanyaye ya samawa kansa gurin zama. "Kai Jibo, ina yarinya take ka dawo kai kaɗai?" Modibbo ya yi maganar cikin zaƙuwa.

"Ramata na cikin yaran da aka yi garkuwa da su" Ya ba su amsa kai tsaye, dan bai ga amfanin ɓoye-ɓoyen ba. Salati suka saka gaba ɗaya.

Cike da takaici Sambo ya ce "Ka gani ko? Babu irin abin da bamu gaya maka ba, game da kai yarinyar nan can wata uwa duniya da sunan boko, ga shi yanzu ka salwantar da rayuwarta a banza. Ita kaɗai dama ta rage maka, yanzu ga abin da ka janyo"

Maddibo ya ce "Ya isa haka, Ramata dai 'yarmu ce, yanzu tayar da jijiyoyin wuya da hayaniya ba namu bane ba, iyaka kawai mu riƙe addu'a Ubangiji Allah ya bayyana ta"..

Baffa ya kwashi takaici da miyagun maganganu a gurin 'yan uwansa, duk da halin da yake ciki. Yana ji yana gani, abinci ya gagare shi, salla sai ya sallame sau biyu, saboda rafkanuwa. Ya zauna ya ja uban tagumi, ya ji sallamar ɗan gidan Iro Yayansa Amiru, wanda aka so haɗa shi aure da Ramata, Baffa ya dage makaranta za ta yi. Baffa ya amsa masa, ya yi masa iznin shiga. Ya shiga yana sake sallama, Baffa ya yi masa iso, tare da nuna masa kusa da shi ya zauna. Jiki a sanyaye Amiru ya ce "Baffa ashe tsautsayin da ya faru da Ramata kenan?" Baffa ya sauke numfashi ya ce "Wallahi kuwa Amiru, an sace su Ramata. Duk ana ɗora mini laifin faruwar hakan, amma ni uba ne, ba zan taɓa aikata abin da zai cutar da 'yar da na haifa kuma ta kasance itakaɗai ta rage mini ba"

Amiru ya ce "Na sani Baffa, kuma na fahimce ka, sai dai mu haɗu mu yi haƙuri, mu yi ta addu'a Allah ya bayyana ta"

Amiru ya din ga rarrashin Baffa, sun daɗe tare sannan Amiru ya yi masa sallama ya tafi.

Sai dai Baffa bai karaya da lamarin ba, sai da dare ya tsala, ya tuna Ramatansa bai san a inda take ba, bai kuma san a yaya za ta kwana ba. Tsakar gida ya fito, ya tsaya a tsakiyar farin wata, ya sakawa ƙofar ɗakinta ido. Lokacin da ya kai ta makaranta, tare da shugaban makarantar primary ɗin su Rahaman, sai da aka kai shi har ɗakin da aka bata, da gadon da aka bata ya tabattar da tana kauwwame a guri ɗaya, sannan ya amince wanda tsawon shekarun nan, ko ya kaita makarantar wasu lokutan sai ya yi ta damuwa da rashinta a kusa da shi. Balle yau da ba a san ma a inda take ba. Ya ja da baya a hankali ya jingina da jikin danga, sai kuma abubuwa daban-daban suka fara dawowa kansa game da garin, baya tunanin kaf garin YELWA akwai wanda ya haɗu da masifu kala-kala kamarsa. Haka ya wanzu yana tuna abubuwa daban-daban marasa daɗi da suka faru da shi a garin.

***** Tamkar baƙin hadarin damuna, mai ɗauke da iska haka ya murtuke fuska hanunsa riƙe da waya, ya kara ta a kunnensa yana jiran a ɗaga. Yana kwance a kan doguwar kujera yana kallon talabijin, kiran wayar ya cika masa kunne. Kuma wayar da ba kowa kiransa a ita ba, sai mutane na musamman. Ya duba ya ga lamba ce babu suna, ya ɗaga kai kunnensa. Sai dai shiru ba a yi magana ba. "Wa ke magana?"

"Sadauki ne"

"Waye hakan?"

"Idan ma ka gane waye, idan ba ka gane ba, ɗaya daga cikin manyan yaranmu, ya yi ɓatan dabo, bamu san inda yake ba, kuma Kacalla Sumale na matuƙar ji da shi, dan haka ina fatan babu hannunku a cikin kama mana yaro"

"To kai ɗan samari, ta yaya ka ke tunanin zan saɓa yarjejeniyarmu ne? Bamu saka an kama kowa ba, hasali ma mu na ta ƙoƙarin ƙara gyara muku hanya ma"

Sadauki ya ja ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, ya yi ɓatan dabo ne bamu gan shi ba, mu na kyautata zaton ko kama shi aka yi, amma za mu ci gaba da duddubawa. Yaran nan su na nan a tare da mu, ku sako kuɗin Abincinsu. Sannan duk abin da gwamanati ke ciki a sanar da mu, dan idan rana ta ƙwace tare za ta ƙwace mana"

"Ka kwantar da hankalinka, ina da tabbaci a kan shirin da muka yi"

"Shikenan"

"Yauwwa ɗan samari, za a kawo muku saƙon, zan turo da lambar motar, da inda za ku je ku karɓa"

"Yayi" Sadauki ya faɗa a taƙaice ya katse wayar.

Dattijon ya yi dariya ya ce "Idan rana ta ƙwace, zata ƙwace mana mu da ku a ina? Yaro bai san wuta ba sai ya taka.

*****

Wani irin azababben sanyi ake yi a gurin, Ramata ji take yi tamkar ta fi kowa jin sanyi. Jikinta sai wata irin karkarwa yake yi. Yunwar da take ji, har ta ci ta cinye ta, abin da ake ba su sam baya isar su. Gaba ɗaya hancinta a toshe yake, da baki take numfashi saboda matsananciyar murar da ta kama ta, bayan tunanin Baffa da ya addabe ta, babu abin da ya dame ta, irin rashin suturar kirki da ke jikinsu, ga ƙarti a kewaye da su. Kumburin da ƙafafuwanta suka yi kuwa, ba su riga sun sace ba, saboda dafin ƙayoyin da ta din ga takawa. Tana zaune ko kwanciya ta kasa yi, ta duƙunƙune jikinta, tana kallonsu a zube a daji kamar dealer gwanjo. Ɗaya daga cikin maharan nasu, da suke tsaronsu, ta lura da yadda yake takura mata da yawan kallo, hakan ya ƙara takura ta, mussaman rashin cikakkiyar sutura da take jikinta.

****

Tana zaune a kan gado, tana shan tea, ta kammala ta sauka daga kan gadon ta fita falo, kawai ta tarar da shi a zaune a ƙaton falon, ya miƙe ƙafafuwansa ya jingna da jikin kujera. Kai tsaye ta nufe shi tana faɗin "Mr. President a gida zaka kwana kenan, ai ban san ka shigo ba" Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta zagaya ta zauna a kan kujera ta ce "Bikin 'yar gidan ministan al'adu da za a yi, ina son sabuwar mota gaskiya latest mai kyau. Kalli lace ɗin da zan yi order shi nake son sakawa, 5.5million wannan sarƙar ma direct daga Dubai na sayo ta"

Cike da takaici ya ce "Dan girman Allah Fatiyya ki rabu da ni na ji da abin da yake damuna. An sace yaran mutane a makaranta, na rasa ta ina zan fito na taushe su, yaran mutane na inda ba a ma sani ba, kuma duk da matsayinkii a ƙasar nan, ko sau ɗaya ba ki nuna dmauwarki ko kin yi wata magana ta kwantar da hankali ba. A lokacin da ƙasar nan ke fama da rashin kuɗi durƙushewar tattalin arziki, ga ɗalibai an sace a mulkin mijinki a gaɓar ne ki ke shirin saka kayan miliyan biyar. Ke ko gudun magana ba kya yi?"

Fatiyya ta ɓata fuska ta ce "To wai dan Allah mu muka sace su ne? Abin da zai faru ya riga ya faru, Allah ya kuɓutar da su, amma dan an sace yara kuma shikenan ba za mu yi walwala ba?"

Ya ƙare mata kallo tsaf ya ce "Anya kuwa ke uwa ce Fatiyya? Kin ga je ki ki bani guri ne, kar ki sake dagula mini lissafi"

Kwaɓe baki ta yi ta fice ta bar shi a gurin a zaune. Duk da yadda yake samun masu rarrashinsa a kan abin da ya faru, amma ya takura ƙwarai da matsin lambar da yake fuskanta daga jam'iyyun adawa, ƙasashen ƙetare da uwa uba al'ummar ƙasa da su ka fara Allah wadai da mulkinsa.

***** Laila na zaune ta idar da sallar la'asar, ta yi shiru. Sadam ya shigo da sallama ɗakin ya ɗora da kiran sunanta. "Ke Laila, amma dai da wuri yau za ki ɗora mana girkin dare ko? Dan ni wallahi ba na ganewa taliyar nan ko minti sha biyar ba ta yi a cikina, nake jin wayam ba komai" Sai dai ya ga ta yi shiru bata amsa ba. Ƙarasawa ya yi inda take, ya taɓa kanta, kawai ya ga tana sharɓar kuka wiwi. Cikin mamaki yake kallonta ya ce "Lafiya?"

Jin sheshsheƙar kukan nata, ya sanya Mama shigowa da sauri tana tambayar kukan me take yi.

Laila ta goge hawayenta cikin ƙunar rai ta ce "Wallahi tunanin 'yan uwana da aka sace nake yi?"

Sadam ya ce "Wane 'yan uwan naki aka sace?"

"Ɗaliban makarantar nan mana" Ta ba shi amsa tana share hawaye. "Ko a tarihi ban taɓa jin wannan masifar ba, yaya za a yi a ce an sace ɗalibai mata har cikin makaranta kamar wasu kayan sakawa"

Saddam ya yi tsaki ya ce "Ji banza, shi ne ki ke wa mutane kuka har haka? A gidan uban wa suka zama 'yan uwan naki? Kawai kin saka gabana ya faɗi a banza"

Mama ta ce "Ni wallahi kin bani tsoro"

Ta girgiza kai ta dube su ta ce "Sai ranar da ya zamana an sace da ni, za ku ji babu daɗi? Idan ɗalibai a makarantu ba su tsira ba, ni wane tabbaci nake da shi zan tsira?"

"Ke dalla yi wa mutane shiru da wannan falsafar banzar taki. Ba nan ki ke zama kina video kina goyon bayan gwamnatin ba. Dalla tashi ki ɗora mana tuwo"

Mama ta ce "Kai dakata mini, Laila na da gaskiya. Duk inda iyaye da yan uwan yaran nan suke, hankalinsu a tashe yake. Ubangiji Allah ya tseratar da su cikin Aminci. Ni kaina abin ya tsaye mini. Har da yarinyar wata class mate ɗinmu aka sace wallahi abin gwanin ban tausayi. Tare muka yi islamiyya da ita"

Sadam ya ɓata fuska ya ce "Ahh lallai aiki ya ganku, gara na fita tun wuri na nemi abin da zan ci, tun da naga alamar zaman makoki zaku yi yau, ba za ku dafa abinci ku bani ba"

***** Tamkar marasa amfani, haka suke hantarar ɗaliban. Su na jere a zazzaune, ana raba musu buredi a wulaƙance, mai rabon buredin ya miƙa wa Ramata. Ta miƙa hannu za ta karɓi buredin, ya haɗa da hannunta ya riƙe yana ƙare mata kallo. Jikinta ya yi sanyi ya hau rawa, ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta. Amma cike da rashin ɗa'a ya fara shafa hannun nata da ɗaya hannun nasa, har zuwa damtsenta. Jikinta ya hau rawa cike da tsoro tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ya tsare ta da ido da baƙar fuskarsa yana sauke numfashi. "Kai kar fa ka kuskura ka yi abin da ba shikenan ba, kar ka ja mana tashin hankali" cewar na kusa da shi, da suke raba buredin tare. Ya yi murmushi tare da sakar mata hannunta, yana yi mata murmushi. A hankali Rahama ta yi ajiyar zuciya, dan tsoro ne ya shige ta, ta zata wani abin zai yi mata. Ƙarar sautin kusantowar babura ce ta cika gurin, gaba ɗaya suka zuba wa inda suke jiyo sautin ido. Su goma sha biyu ne suka zo a kan babura kowannensu riƙe da miyagun makamai. Idan da sabo, ya ci a ce Rahama ta saba da ganin tashin hankali, amma a wannan karon ma sai da tsoro ya shige ta, ganin uban bindigun da suke hannun maharan kamar za su yaƙin duniya. Cikin girmamawa suke gaishe shi, ya din ga jinjina musu kai, ya din ga ƙarewa 'yan matan kallo, ya tsayar da idanunsa a kan Rahama. Ya yi shiru yana ƙara ƙura mata ido, tamkar mai son hango wani a kan fuskarta. Sai dai ita ma ta ɗan tsura masa ido, ba ta kai ga janye idanunta ba, ya tako a hankali nufo ta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta daina kallonsa. Ya ƙarasa ya tsuguna a gabanta yana kuma ƙare mata kallo, tun zuwansu ya lura da yadda take ta kare jikinta da hannunta.

"Kalle ni" Ya faɗa cikin kakkausar murya.

Tamkar zuciyarta za ta faso ƙirjinta ta fito, saboda luguden da take yi, haka ta ɗago idanunta da kyar ta kalle shi. Ta mayar da kanta ta sunkuyar.

"Kin sanni ne?" Ta girgiza kai a hankali.

Ya saka hannu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Da gaske? Kalle ni dai, na ga kina kallona kamar kin sanni ko?" Ya yi maganar yana murmushi.

Ta sake girgiza masa kai tana sunkuyar da kanta ƙasa, ba tare da ta kalle shi ba.

"A jam fullo?" (Ke Bafulatana ce?"

Ta jinjina kai alamar eh.

""ko honɗun wuro njahaa?" (Daga wani gari ki ke?"

"Yelwa" Ta faɗa a tsorace.

Ya waro ido tare da yin murmushi ya ce "Daga Yelwa aka kai ki makarantar kwana? gaskiya ne, lallai makiyayan Yelwa sun waye, an samu gagarumin ci gaba Sannu ko, ku kwantar da hankalinku babu abin da za mu yi muku, za ku koma gida lafiya in sha Allah, za mu ajiye ku ne nan da wani ɗan lokaci, domin cikar muaradanmu da na iyayen gidanmu. Da mun kammala za mu sake ku. Kun kafa tarihi a duniya, ɗalibai na farko da aka yi garkuwa da su. Ya yi maganar yana murmushi. Ba tare da ta san ita yake kallo ba, ta sake ɗagowa ta kalle shi, fari ne sai dai ba tas ba, idanunsa sun sha farin kwalli rabajau, yanayin fuskarsa da yadda yake magana, ba ka ce ko kwari da baka zai iya ɗauka ba, balle bindiga.

"Za ki ce wani abu ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ta girgiza kai da sauri tana sake sunkuyar da kanta.

"Ya sunanki?"

"Rahma" Ta furta kamar mai raɗa cikin tsoro.

"Ramata" Ya furta yana guntun murmushi, ya miƙe tsaye ta kalle shi da mamakin jin yadda ya faɗi sunan da ake gaya mata a gida, Alhalin ita ba ta san shi ba, ba kuma ta taɓa ganinsa ba...

Ayshercool 08081012143

1k ne a telegram 0069685771 Aisha Adam stanbic