Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 1
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 1: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 1. [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR1FT5*
4,487 words
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR1FT5*
__________________________________ A lokacin da na buɗe idanuwana cikin tsanani da raɗaɗin ciwo akan fuskar da ban taɓa sani ba na sauke su wato fuskar SJ wanda yay min rumfa a ƙoƙarinsa na taimako ga likita da ya buƙata na a rirriƙe ni. Kuma wannan shine mafarin shigowar rayuwar Sadiƙ Abubakar Jadda gare ni, kamar yanda silar siyan rake ya zama mafarin haɗuwata da Nazifi Bala Mai Kalwa. Na sha jinya a sanadiyar hatsarin da nayi kamar ba zan rayuwa ba don har sai da aka yi tunanin fitar da ni ƙasar waje domin a duba ƙwaƙwalwata a cewar likitoci ba ƙaramin buguwa nayi ba, hankalin ahalina ya tashi, natsuwa tayi ƙaura daga garesu domin ba su da kuɗin da za su fidda ni ba su da dalilin su, tsananin damuwar ne ma silar kamuwa da hawan jinin mahaifina domin shi a lokacin ce yay kawai a bari ubangiji yay ikonsa, shi kam ya cire rai da ni, duk da Amb Jadda ya ce ba su da damuwa su ne za su yi komai tun da sune sanadi, kuma kan ka ce mene wannan SJ da ke matuƙar ba ni kulawa har ya tattara bayanan komai zuwa ƙasar da za'a fitar da ni, sai ga shi kuma cikin hukuncin ubangiji a irin adu'oin da iyayena ke ta min da faɗi tashin ɗawainiyar asibiti da iyalan Amb Jadda ke ƙara yi akaina sai komai ya zo da sauƙi cikin ikon ubanji kuma na sami lafiya.
Ahalin Amb Jadda mutanene ma su tsananin mutunci da karramawa da sanin darajar ɗan Adam, Dr Hassana Abubakar Jadda macece ta gari wadda ta fita daban a cikin mutane, akwai ta da tsananin tausayi gami da kyautatawa, haka shima mijinta Amb Jadda mutum ne me tausayin talaka da son taimaka masa shi dai illarsa ɗaya shan sigari da har aka ce tayi masa illa ta taɓa lafiyarsa amma duk da hakan bai daina sha ba sai ma ƙari, wanda shan sigarinsa shi ne sanadin rashin jituwa tsakaninsa da Ɗansa SJ da ko magana bata haɗa su. Idan har magana wa junansu ta zama dole to suna isar da ita ta rubutun takarda ko kuma a waya, idan kuma a gida ne Maamee ita ce me aika saƙo a tsakanin uba ga ɗan, amma Amb Jadda in har zaka faɗa masa gaskiya akan shan sigari to zaku ƙulla gaba ne da shi.
Ko bayan sallamata a asibiti da aka yi Maamee bata watsar da mu ba, ta kan zo gidanmu ta gaishe da mahaifana nima kuma ta duba ni tana me ƙara bada haƙuri akan afkuwar hatsarin. Wanda a kowanne lokaci Ummani da Abbaa ke nuna mata babu komai hakan tsararran lamari ne da ubangiji ya shirya faruwarsa ko da bata sanadinta ba. Silar hakan kuma sai ya zama zumunci ya ƙullu tsakaninmu da ahalin Amb Jadda musamman ma ta ɓangarensu, don ana mu ɓangaren mu kan ja da baya da su duba da cewa ba tsararmu ba ne su, suna da kuɗin da ko da kaf zuriyarmu aka siyar ba za'a haɗa kaso biyu na daga dukiyar da Allah ya ba su ba, kuma su ɗin manyan mutanene da duniya ma ta san da zaman su.
Ta ɓangaren Nazifi me rake shima mutum ne me tsananin kirki na gaban kwatance, rashin zuwa makarantar da na ke yi ya tambayi su Safiyya dalili suka faɗa masa, a ranar ya zo duba ni da ledar kayan dubiyansa daidai ƙarfin talaka, sai ka rantse wani ɗan uwa ne na kusa. Kuma ba'a cika sati ba sai ga shi sun zo da ƙannensa maza da mata, suma zuwan na su da kayan dubiyarsu suka zo, haka aka dafo min miya da kaji da kayan marmari a leda. Kusan kullum sai ya zo duba ni, kuma ba ya zuwa haka kawai sai da kayan dubiya.
Daga nan kuma shikenan sai zumunci ya ƙullu a tsakaninmu domin kuwa bayan an sallame ni daga asibiti hatta Yayar Nazifi da Mahaifiyarsa sai da suka zo har gida duba jikina, da yake mahaifiyarsa macece mai faran faran yini ɗaya sai suka zama tamkar dama can an san juna ita da Ummani har Abbaa ke musu tsiya, ita dai tana ba su labarin ai Nazifin kan yi mata hirarmu ni da su Safiyya akan yabon hankalinmu da tarbiyarmu.
Tun daga wannan ranar kuma ko abincin gargajiya Iyam tayi sai ta aiko an kawowa Ummani duk da nisan da ke tsakaninmu da unguwarsu, aiken alkhairi duk ita ce, idan ta tashi haka zata ciko ƙaton kwano da daddawa ta ce a kawowa Ummani. Itama Ummani haka duk sanda ta samu abun arziƙi ta bani in kaiwa Iyam, idan na je gidan yini na ke sai Yayan Shago ya dawo ko Yaya Nazifi tukunna Iyam tasa a rakoni gida.
Tafiya tayi tafiya wata rana na dawo daga islamiya, na tarar da sabuwar mota kar a ƙofar gidanmu, zuciyata cike da mamakin su waye baƙin da muka yi, sai da na shiga gida na tarar da Maamee ita da Marfu'a da Madam waɗanda zuwansu babu jimawa kenan. Bayan gaisawarmu na wuce ɗan tsukukun ɗakina domin cire uniform, ina ciki Ummani ta ƙwala min kira nayi saurin ƙarasawa na fito da hanzari, a kicin na sameta ta dube ni tana cewa.
"Sanyo gyalenki ki kaiwa me suke ce masa ruwa yana waje".
Nayi ɗan jim sai can na ce,"ohh Bayya ko?".
Ta gyaɗa kanta,"ehh shi, yaƙi shigowa gidan kin san bai da sakewa kamarsu".
Na koma ɗaki na sanyo ƙaramin gyalena na zo na karɓi ɗan ƙaramin farantin robar hannunta, wanda aka sanya pure water masu sanyi guda biyu akai, fita nayi inda na tarar motar bata ƙofar gidanmu kamar ɗazu, nayi leƙe leƙena ban ganta ba hakan yasa na juya domin komawa sai kuma sai naji anyi fakin, na waigo naga motar ce ta dawo. ƴan sakanni kana na taka na ƙarasa ɓangaren mazaunin direba na ƙwanƙwasa gilashin. A hankali aka zuge gilashin, tsammanina ma Bayya ne ashe Na-Madam ne sarkin tsokana. Yana kallona da murmushi ya kira ni da sunnan da kaf gidan na su ke faɗa min.
"Dimple".
Murmushi nayi inda malotsan gefen bakina suka lume ciki, na rissinar da kaina ƙasa ina cewa da shi. "Ina wuni".
Ya amsa min da fara'arsa,"lafiya lau Dimple, ya su Ummani da Abbaa".
"Lafiya ƙalau. Ga ruwa ta ce in kawo maka".
Ya kalli farantin hannuna wanda har naji wani iri saboda na roba ne kuma duk yasha jiki. Ya miƙo hannu ya ɗauka ruwan cikin tare da faɗin an gode. Sallama na masa zan wuce nan yake ce min,"ba ku gaisa da Bayya ba".
Sai sannan ma idona ya kai cikin motar in da na hango shi zaune idonsa zagaye da baƙin gilashin da bai rabo da shi, da ƙananun kaya a jikinsa kamar ko da yaushe don ni dai ban taɓa ganinsa da manya ba, yay kyau sosai p-cap na ɗaukar fuskarsa, shi irin masu kyan da ake kallo ne aji kamar a sace a gudu. haka ɗaya sai naji gabana yay mugun faɗuwa nayi saurin ɗauke ido daga barin kallonsa, a hankali kuma na ce,"Ina wuni Bayya".
A kaikaice ya dube ni ta cikin gilashin, kamar ba zai amsa ba saboda yanda yaja lokaci can kuma sai ya ce,"lafiya lau, ya kike ya mutanen gida?".
Yay maganar cikin birkitacciyar hausarsa da bankinsa bai gama ƙwarewa da ita ba, don ba ya dogon zance ba tare da ya saka faransanci a ciki ba, har sha'awar hakan na ke ni kam, sai naji ina ma ni ce na iya wani yaren bayan hausa.
Ina gyara gyalena da ke neman zamewa na ce masa,"duk suna lafiya ƙalau, Ummani ta ce a gaishe ka".
Kansa ya gyaɗa wajen amsa min. Na-Madam cikin zolaya ya ce da ni,"Hajiya Dimple sanyi ƙalau, ke dai sam ba ki son magana, yanzu idan na ce ki tayani hira fa sai ya zamar miki jan aiki. To ai shikenan ki gaida mutan gidan".
Ina murmushi na wuce, ina gab da sanya ƙafata cikin soro maganar SJ ta dakatar da ni, haka kawai kuma sai naji kiran sunan nawa da yay a karo na farko ya amsa a gaba ɗaya ilahirin jikina, haka kuma naji tamkar sunan a bakinsa aka raɗa shi tun usuli duk da cewar kana jin yanda ya faɗi Sa'ida ba muryar bahaushe ba ne.
Ni kam ban san dalili ba amma tabbas na kan tsinci kaina cikin wani yanayi da na ke kasa fassara shi balle gane masa in har na ga SJ ko naji ƙamshinsa, don hatta ƙafafuna kan yi rawa a irin wannan lokacin hakazalika in rasa natsuwata. A hankali na juyo hannayena na karkarwa riƙe da farantin na kai ƙwayar idona kansa, ya cire gilashin idanuwansa, idanun a ƙanƙance kamar basa gani da kyau, ganin na tsaya yay min alama da kansa na in zo. Na tafi sannu a hankali ina jin kamar zan faɗi ba tare da sanin dalilin wanzuwar hakan ba.
"Ya wuyan na ki?". Idona a ƙasa na haɗiye yawu kafin na iya cewa,"Da sauƙi".
"Es-tu sûr?". Ɗago ido nayi na dube shi, ganin na tsare shi da ido sai ya kulle ido ya kaɗa kansa kaɗan kafin ya ƙara buɗe baki da ƙyar ya ce min,"kin tabbata?".
Na ɗaga kai da cewar,"Ehh yay sauƙi ba kamar da ba".
"Zan iya gani?". Gyalena na ɗaga ina yaye wajen tare da nuna masa, ina ga ganin sacewar kumburin wuyan yasa ya kai hannu ya taɓa babu shiri na wani zabura ina ja da baya saboda yanda zafin ciwon gun ya ratsani da kuma jin hannunsa kamar shokin na wutar lantarki. Ƙwayar idonsa akaina bayan wucewar ƴan sakanni ya ƙara cewa,"kina iya zuwa school?".
Na sauke numfashi tare da cewa,"Ehh yanzu ma daga islamiya na dawo".
Kallona ya tsaya yana yi, wucewar minti ɗaya yay min alama da hannu na in matso kusa, na matso kusa da ƙofar motar da ya buɗe ya ziro ƙafafunsa waje. Ya kai hannu ya ware idanuwana yana duddubawa irin yanda likita yake min, sai da ya gama bincikensa matsayinsa na likitan da ya ajiye aiki saboda saɓanin da ke tsakaninsa da mahaifinsa kana ya ce min.
"Jinin ya ɗauke gaba ɗaya, kar kina wasa da magani please".
Sai kuma yay shiru kafin ya ƙarasa maganar,"Ki yi haƙuri kin ji".
Kai na sunkuyar ƙasa, ni kam wannan kalmar ta ban haƙuri da ke fitowa daga bakinsa ko da yaushe da ace tana tsiro da tayi a jikina. Haƙurin nasa duk yana bayarwa ne saboda mahaifiyarsa, Marfu'a ta taɓa ce mana in ace Mahaifinsa ne ya buge ni da mota to SJ zai iya tayamu shigar da ƙara kotu, kuma ba zai tsaya akaina ba don ganin na sami lafiya kamar yanda ya ke a yanzu, hasalima zai ce ina ruwansa shi shan sigarin mahaifin nasa ne ya janyo masa ba wani ba, ai anyi anyi ya daina shan sigari yaƙi ji.
Muryana kamar an shaƙeni na kalle shi ina jin gabana na tsananta faɗuwa saboda kwarjininsa na ce,"Bayya ka daina ba ni haƙuri don Allah...".
Ban ƙarasa ba ya ɗaga min hannu alamar in dakata, sai kuma ya ce da ni,"SJ not Bayya". Bayan ya huta da wannan ɗan guntun furucin ya ƙara cewa,"Su ƙannena ke kuma wata ce daban, just call me with me my name Sadeeq or SJ".
Kai na gyaɗa a hankali don tuni na fahimci bai son wancan sunan kam yafi so a kirasa da SJ ko Sadeeq, ƙannensa ma da suke faɗin Bayya ba so yake ba, shi a kirasa da zallar sunansa kawai, su kuma ƙannensa na ganin idan suka kira sunansa gatsal tamkar aikata zunubi ne, nima kuma gaskiya a irin yanda na taso da tarbiyar gidanmu ba zan iya faɗar sunansa ba domin ya girme min nesa ba kusa ba.
"Ƙafan na ki yana takuwa sosai yanzu?".
Ina ɗaga kai na ce,"Ehhh, ta daina ciwon".
Ya gyaɗa kansa sau biyu, bai kuma ƙara cewa da ni komai ba ya mayar da ƙafafunsa cikin motar ya rufe ƙofar, ni dai ina tsaye kawai kamar me neman gafara duk a tsorace na ke ina jin jikina na kyarma, sai satar kallonsa na ke ina jin wani abu na motsawa a tare da ni.
Ji nayi suna magana da Na-Madam cikin yarensu wanda ban san me suka ce ba, sai kuma naji Na-Madam ya ce da ni.
"Idan kin shiga ki ce da Maamee su fito mu tafi".
"To".
Na amsa a hankali ina barin wajen da sauri. Yanda na shiga gidan kamar wadda taga wani mugun abun, na faɗa ɗakina ina haki tare da dafe ƙirjina da ke ta bugawa. Sai da na natsu kana na fito na shiga ɗakin Ummani, daga gefe na tsuguna na sanarwa da su Maamee saƙon su SJ na cewar su fito.
Ni dai tun daga wannan ranar wani sabon Al'amari ya sauka akaina, gaba ɗaya na rasa me ke damuna mene kuma dalili, domin kuwa tunanin SJ ya samu muhalli a cikin raina, komai na ke yi duk abun da na ke yi da tunanin SJ, haka idona a kowanne bugawar sakan da minti sai na tsinci haskawar hoton surarsa, bini bini kunnena ya jiye min sautin muryarsa, gaba ɗaya sai na rasa gane kan dalilin hakan, abu ɗaya kawai da na sani tunda na taso nayi hankali ban taɓa jin wani abu irin haka ba, kuma ban taɓa jin namiji ya burge ni ba har ina son wani abu nasa sai akan SJ.
Yawaitar faɗuwar gaban da na ke a duk lokacin da na ayyana kamar bayyanarsa a inda na ke sai na fara ramewa, ramar har tayi min yawa saboda rashin sake ganinsa da banyi ba tun wancan zuwan da suka yi gidanmu, sai wata rana ne ma Ummani ke ce min taje gidan zuwa yi musu godiyar ƙara turo kuɗin magunguna da suka yi da aiken da akayowa Abbaa na kayan abinci. Ranar ji nayi tamkar na fashe da kuka domin ko babu komai da taje da ni zanga SJ mutumin da na rasa dalilin tsaya min a rai da yay. Ban taɓa sanarwa da kowa halin da na ke ciki ba hatta Safiyya da ta gallazeni da tambaya ganin duk na sauya.
Bayan wucewar kwanaki masu tsayi ina daɗa girma da wayo da hankali na farga da cewar na kamu da son SJ, so kuwa me tsanani tun da har yana wahalar da ni duk da ƙarancin shekaruna, du da cewa so ba shekaru ba ne, don in ace a ƙauye muke tuni an min aure ba kuma zan kawo ya wannan shekarun ba ma ban fara tsayawa da saurayi ba, sa'annina kowacce da yaronta. Kuma tun daga lokacin da na fahimci na kamu matuƙa da soyayyar SJ na yiwa kaina faɗa akan dole na yakice tunaninsa da sonsa a raina domin SJ ba tsarana ba ne ba ajin aurena ba ne, shi mai kyau ne, mai ilimi, mai kuɗi, mai ji da kansa, ɗan manyan mutane, to ina gamin haɗi tsakanina da shi daddawa a kunu? Shi kam ai sai manyan mata da suka amsa sunansu, masu ilimi ƴaƴan masu kuɗi ba irina ƴar Malam Salman me teburi a kasuwar rimi ba, wadda bata da komai ɗin da namiji kamar SJ me aji zai gani yace yana so, sai dai tabbas da ace zan samu wata dama da zan isar da saƙon zuciyata ga SJ lallai da nayi hakan, to amma ban san hakan me zai iya haifarwa a gare ni ba, ba na son wulaƙanci haka ba na son abin da zai haifar da matsala tsakanina da iyayena, amma tabbas ina son SJ kuma zan so rayuwar aure da shi.
Ganin fa ni kaɗai na ke kiɗa da rawata akan soyayya, tuni na miƙe da adu'a, na duƙufa akai babu dare babu rana akan Allah ya cire min son SJ ya kuma ƙara nisanta tsakanina da shi ta yanda ba zan gansa ba balle ya zame min famin ciwo, sai na fara samun salama domin kuwa babu abin da yafi ƙarfin adu'a, a hankali a hankali yawan tunaninsa da jin motsawarsa a zuciyata duk ya tafi sai jefi jefi, nayi hamdala na gode Allah don hakan ba ƙaramin alkhairi ba ne a gare ni na sani, tunda ba taɓa samun SJ zan yi ba, ba zai taɓa zuwa yace yana sona balle har ya furta zai aure ni.
Tambayar ma da na kewa kaina har kullum garin ma ya akai na kamu da sonsa? Shi son dama haka ya ke babu shawara babu neman izini? Sau tari na kan yi murmushi takaicina idan na tuna kwanciyata a asibiti, wato lokacin a haukar tunanin da nake yi irin rawar jikin bani kulawa da tsananin nuna damuwa gami da tausayi akaina da SJ yay sai na tsammaci ko sona yake yi, tun ma da naga yanda ƴan gidansu kowa ke haba haba da ni kamar wata shaƙiƙiyarsu ba tsintuwar hatsarin titi ba, ashe duk ina cin alfarmar mahaifiyarsa ne da kuma kyan zuciyarsa ta masu imani, ba yanda na ɗauka na soyayya hakan yake a ɓangarensa da ɓangaren ƴan uwansa ba, hasalima yana da matar da zai aura wacca ba'a ƙasar nan take ba, naji hakan ne a bakin Ummani, wadda itama na san hira ce tayi hira tsakaninta da Maamee har ta san hakan, ranar kuma na ga rashin hankalina don kwana nayi ina kuka, har ina ayyana ina ma ace SJ ya fasa auren kowacce mace ya dawo gare ni, sai dai babu yanda zan yi haƙura da shi ya zama dole, silar ciwo ya haɗamu da su kuma samun waraka ya rabamu da su, don tun da na gama wartsakewa likita ya tabbatar musu da bani da wata matsala ta ko'ina muka bar jin ɗuriyarsu haka suma suka daina jin tamu ɗuriyar. Sai ma in wataran ana zaune ne haka Abbaa ya tuna su ana faɗin kirkinsu. ____________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR02FT5*
*Advert!* _Ina masu son koyan kalolin abincin ƙasashen waje? Kamar irin su mandi rice, Chinese rice, chicken biryani, Afghani rice, eggs rice, chicken kabab, chicken biryani da sauran abincin labarawa da indiyawa masu daɗi da kwantar da hankali tun daga jin ƙamshin su. akwai kalolin salad irin su patoosh salad, normal salad, macaroni salad da sauran su. Baku da labarin Leemars_mandi zatayi class don ta taimakawa mata ta koya musu kalolin abincin ƙasashen waje wanda mu bamu san da su ba...?. Ta ƙware indai a wannan b'angaren ne shiyasa ake mata take da "Home of delicious and Arabian foods." ni na shaida Leemars_mandi ta ƙware a wajan sarrafa d'anye ya koma dafaffe. Ka da ku sake ayi babu ku class d'in zai zo muku nan bada jimawa ba akan naira 7k kacal, akwai ragi mai auki ga wad'anda suka fara biyan kud'in su. Domin neman ƙarin bayani nemeta akan wannan number 09030398006, ko DM a Instagram @Leemars_mandi._ __________________________________ A gefe guda kuwa Allah ya haɗa jinina da Nazifi Bala Mai Kalwa, nagartar Yaya Nazifi ita ta sanya muka yi shaƙuwa ta ban mamaki, ya zama tamkar ɗan gidanmu, kuma yanda ake zumunci da gidanmu da gidansu in ba sani kayi ba zaka ce ko dama can ƴan uwan juna ne mu. Kowa nawa ya san shi, ba shi da shamaki da ko'ina a cikin gidanmu, abota me ƙarfi ta ƙullu tsakaninsa da Yayyuna, ƙwarai shi kam mutum ne me shiga rai saboda kyawun halinsa da ɗabi'unsa ga uwa uba kuma addini, yayi haddar ƙur'ani har sau uku banda manyan littafan addini da ya haddace, duk wani mutum na ƙwarai zai so ace yay mu'amala da Yaya Nazifi, kai ba ma shi kaɗai ba zuri'ar Malam Bala Mai Kalwa kaf babu na yarwa, ko kwatance ake a unguwarsu na matasa na gari za'a sako sunan Yaya Nazifi a farko haka za'a sako maka sunayen samarin gidan Malam Bala Mai Kalwa.
Tun da har Abbaa na ya yarda da mu'amalarmu da Yaya Nazifi na san kuwa lallai ya samu lambar yabon shaidawa, ya iya mu'amalantar mutane ga kyautatawa da son taimakawa, haka bai da abokin faɗa, shiga shirgin abokai ma bai dameshi ba, indai ba fita neman na kansa ba to yana gida tare da mahaifiyarsa ko kuma yana wajen mahaifinsa ɗaukar karatu. Abbaa da kansa ya yarje min mu'amala da Yaya Nazifi domin yay masa duk wasu jarabawowi sannan kuma ya karance shi sosai, duk da baka ba wa mutum dukkan yardarka kamar yanda ba'a barin ƴa mace sakin jiki da namiji, amma ko da yaushe cikin masiha da ankarar da ni ake. Abbaa har roƙarsa yay da ya ke zuwa gida yana min karatu duk sanda ya samu lokaci, ya damƙa masa amanata domin ya yarda da shi bai da haufi akansa.
Tsakanina da Yaya Nazifi mutunci da girmama juna ne, bama ɓoyewa juna komai, duk wata shawara da ta shafi rayuwarmu da juna mu ke yi, yana matuƙar bani gudunmawa wajen ganin rayuwata ta inganta, bayan mahaifana shine mutum na farko da zan ce yana ɗora ni akan daidaitacciyar hanya, wanda kai tsaye kuma zai faɗa min gaskiya komin ɗacinta, ya kuma tsawatar min da bin hanyar da take ba daidai ba.
Lokaci guda sai ya zamana in har zaka zauna da ni to ba zamu rabu ba sai ka san Yaya Nazifi a bakina, shima ta ɓangarensa duk wanda ya ke tare da shi ya san sunana a bakinsa, haka har ta fara kaiwa ga mutanen da ke kewaye da mu sun fara zargin ko soyayya muke yi, sai dai ko kaɗan babu hakan daga zuciyar kowannemu, ni dai matsayi ɗaya ne a zucciyata Yaya na ɗaukesa kuma aboki, tamkar yanda shima ya ɗauke ni matsayin ƙanwa kuma abokiya, Yaya Nazifi sam ba ya banbanta ni da ƙannensa, ko abun faɗa na yi da gyara zai fito min a matsayin wa na gari yay min faɗa sosai, ina basa girmansa matsayinsa na wanda ya girme min sosai.
Sai dai fa ko kusa an ƙi yarda da cewar babu soyayya a tsakaninmu, tun daga kan ƙawayena har shi kansa ƴan gidansu kan tsokane ni wataran su ce budurwar Yaya Ƙarami ta sirri. Iyam kuwa sau tari idan yana mata hirata sai tace uhmm lokaci dai, Hatta mahaifiyata sai da ta taɓa tambayata anya babu wata alaƙa ta daban tsakaninmu, na tabbatar mata da babu wannan kamar yanda su ke tunani, ta kuma yarda da ni domin ta san bana mata ƙarya bana mata ɓoye ɓoye kuma ta sanya ido akan hakan sosai taga saɓanin zarginta, wasu da basa iya tantance soyayya da mutuntaka ne dai suka kasa gasgata yanda muka ɗauki junanmu.
Lokacin da muka zo term ɗin ƙarshe a SS2 lokacin manema aurena su ka fara fitowa kamar dama jiran lokacin su ke, caaaa wannan ya zo wancan ya zo, daga yamma tayi an fara sintiri kenan a soron gidanmu wai ana sallama da Sa'ida, kuma manyan mutane ba ƙananu ba, duk da ba fita na ke ba idan aka zo amma na kan yi mamakin inda har suka ganni ma suka biyo sawu, haka kuma mafi yawancin masu zuwan sai in tuƙe maƙura a mamakin me suka gani tattare da ni da kamar su masu kuɗi zasu zo neman auren ƴar talaka kamata, yau ace me mota kaza, gobe ace kalar mota kaza, anjima ace wani babban mutum da mota kaza shine babba a wuri kaza, ni ranar da aka ce ma wani ya zo da kaki sai da nayi mugun tsorata ce nake laifi na yi.
Lamarin ya fara bawa Abbaa haushi, da ka ji Abbaa na tsaki to akan hakan ne, har gargaɗina yay akan ya soke min ko zuwa unguwa da Ummani, daga makaranta sai gida. Shi kam so ya ke ko zai aurar da ni sai nayi nisa a karatun jami'a kamar yanda ya ke fata, don haka duk wanda ya zo da maganar aurena Abbaa zai saita masa hanya da cewar ba yanzu zai aurar da ƴarsa ba domin karatun likita zanyi ba ya so a gurɓata min tunani da soyayya. Ta ɓangaren mahaifiyata ma hakan take don sosai take sanyani gaba da faɗa akan kar na sake in faɗawa tarkon namiji, in tsaya na natsu na tsayar da hankalina wuri guda in yi karatu shine burinsu, kuma shine babban gatan da zasu tafi su barni da shi, wannan ita ce babbar damata in moreta tun da ƙuruciyata kafin girma ya riskeni al'amuran duniya ma su sha kaina.
Na kuma yi masu alƙawarin hakan domin nima banda ra'ayin soyayya ko kaɗan, ko da ina da shi zan ajiye saboda farin cikin iyayena da cikar burinsu, ko son SJ da nayi a baya da ace zuciyata tayi shawara da ni da hakan ba zata soma faruwa ba, to godiyar da na yiwa ubangiji ma har nayi yayin son nasa na gama babu wanda ya sani hatta shi kansa, a yanzu kuma da na ƙara hankali da wayo sai na gane bama sonsa na ke ba burge ni kawai ya ke yi, abin da mutane da dama basa ganewa kenan banbanci tsakanin so da burgewa.
Wata ranar juma'a bayan la'asar muna zaune a tsakar gida ni da Ummani ina tayata tsinkar zogale, muna ta hirarmu ta ƴa da uwa, aka yi sallama daga soro, jin muryar kuma ya saka ni sauke sanyayyen murmushi ina kafe hanyar shigowa da ido, Ummani kuma ta warware ɗaurin ɗan kwalinta ta yafa kafin sannan ta ce,"To shigo mana Nazifi ka tsaya daga nan, gidan ai ba baƙonka ba ne ko".
Har ya sanyo ƙafarsa tsakar gida ban ɗauke idona ba akan hanyar shigowa, shima ɗin shigowar tasa ƙwayar idonsa akaina ta sauka, ya murguɗa min baki da hararar wasa ni kuma sa'adda da na ɗauke kaina zuwa gefe ina murmushi me faɗi don sosai ya bani dariya, yanda mu ke abu da shi kamar ƙawa da ƙawa. Yau kam yayi kyau sosai cikin farin yadinsa me sauƙin kuɗi, ga shi sai ƙamshi ya ke yi me daɗi, suna gaisawa da Ummani take ce masa.
"Yanzu mu ke maganarka na ce kyan miyar zogalen nan da zan yi ace ka samu kaci. Mutuniyar taka sai ce tayi ai ka daina shan miyar zogale, tuwan ma ka daina ci wai ka zama ɗan gayu".
Yana murmushi sosai yace,"Ai Ummani yarinyar nan ƴar adawata ce, buƙulu ne irin nata kawai kuma ko me zata yi sai na ci tunda ba cefanenta ba ne".
Duk sai muka yi dariya ina gaida shi, bai amsa gaisuwar ba yace,"Ke da kike buƙulun na ci tuwo nayi dumurmur kamarki, to alqur'an duk baƙin cikin tanda sai mun ci waina, Yarinya ko za ki bindiga sai nayi ƙibar nan da kike baƙin cikin na yi".