Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 2

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 2

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 2: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 2. Dariya muka ƙara yi gaba dayanmu ina cewa,"Wallah Yaya kai dai ka…

4,411 words

Dariya muka ƙara yi gaba dayanmu ina cewa,"Wallah Yaya kai dai ka min biyayya kawai, don sai abin da na ce da Ummani ka dai sani".

Ummani tace,"Ke asuwa ɗan wake a hotel, wacece ke?".

"Autar Ummani mana".

Tace,"Su Autar Ummani manja, to ko da kike Auta ai ba ki samu kwatan son da nake masa ba".

Haƙoransa suka washe yana cewa,"Ahh tou, Auta daban wanda ake so daban, Yarinya ki kumbura ki fashe ni kam nasha gabanki".

Ɓata fuska nayi ina murguɗa baki kaɗan kaɗan yanda na saba yi masa. Ummani ta dube shi tace masa,"To ko ƙafa zaka sa ka hankaɗata gefe ta baka wajen zama".

Tashi nayi ina ƴar dariya na ba shi wurin zama akan tabarmar, sai faman dai hararata yake da alama nayi laifin da ban sani ba. Ledar da ya zo da ita ya miƙawa Ummani, haka yake duk lokacin da zai zo sai ya taho mana da wani abun sai in bai da kuɗi kam. haka kuma sai ya zo da alawa duk ranar juma'a ya rabawa yaran gidan da na maƙota, yaran har dakon zuwansa suke ranar juma'a, yanzu ma tuni suka baibaye shi kowa na Yaya Nazifi ba'a bani ba.

Hayaniyarsu duk ta cika ni nayi miƙewar da ban shirya ba, lokacin da na dawo ɗauke da lemu da ruwa har ya sallami yaran, na aje masa farantin a gabansa ina kai hannu cikin tsokana zan ɗauke lemun yay saurin ɗaukewa. Lemun ya fara buɗewa ya sha, daɗin ya ratsa shi har da su rufe ido. Sai da ya sauke yake cewa,"Ummani wai har kin fara lemun?".

Tace,"Au bafa ka zo ba tunda aka fara ko, ai lemu dai in faɗa maka gashi nan yanata jan kasuwa Alhamdulillah, wannan ɗin ma Allah ne yay da rabonka, don dai ta riga ta ɗauko maka ne amma na ƙawata ne a ajiye mata zaka tafi mata da shi".

Suka shiga hirarsu shi da Ummani, nan yake shaida mata ta taya shi murna kuma ta faɗawa Abbaa wani maƙocinsu ya ɗauke shi yaron shago zai ke zama a shagon kullum tun safe har dare, babban shago ne su uku aka saka a ciki amma shine oga don mutumin ya damƙa masa ragamar komai. Cikin nuna jin daɗi Ummani ta ce,"Amma kuwa naji daɗi Nazifi, kai masha Allah da wannan albishir a ranar juma'a babbar rana, ubangiji yasa hanyar arziƙi ce ya bada sa'a ya shige muku gaba. Wallahi na tayaka murna sosai, Allah kauda fitina da idon maƙiya".

Shima cikin nuna jin daɗin adu'ar tata yake ta amsawa da amin. Yana daɗa gaya mata yanda tsarin shagon nasu yake, kayan kwalliya ne da kayan jarirai a ciki. A ɓangarena kuwa bayan farin ciki har da tausayinsa naji ya kama ni, don kusan wata uku kenan yana fafutukar neman abun yi don tuni jarinsa ya karye, yanzu babu sana'ar da yake, yana gida kullum sai dai ya fita ya sha iskar gari. okacin da Abbaa ya siyowa Yaya Al'amin ice har da shi ya raba musu, amma shima yanzu babu, idan yana bani tarihin rayuwarsa a irin gwagwarmayar da ya sha har ƙwalla na ke yi masa saboda tausayi, namiji ne shi mai ƙokarin neman na kansa sai dai ubangiji bai saka masa nasibi a nemansa ba, yana da jajircewar neman amma kuma da ya fara sai abu ya lalace masa, in jari ya zuba sai ya karye, haka idan kasuwa ya fara zuwa sai wani abun ya gifta kasuwancin ya lalace, idan tafiye tafiye ya soma zuwa garuruwa itama sai tafiyar ta tsaya masa, sau tari wani aikin shine silar nema musu shi da ƴan uwansa amma kowannensu sai ya samu ci gaba shi kuma sai dai koma baya a kullum, kai a taƙaice ma idan yasa hannu a kasuwancin da ba nasa ba sai kasuwancin mutum ya lalace, shiyasa yafi gane duk abin da zai yi ya kasance nasa ne na kansa, har ya kan ce ina ma ace yayi karatun boko ko da iya sakandire ne wataƙila da ya rage zafi, to amma a hakan ma Alhamdulillah tun da a ɓangaren addinin da zai je lahira da shi babu ta inda aka barsa, kuma ya san komai lokaci ne yana adu'a haka iyaye suna masa.

Bayan sun gama magana da Ummani ta miƙe tana ce masa,"Bara in yi na kammala girkin nan ka tafiwa da Ƙawata tuwon nan kaima kuma ka samu ka ci". Har ta nufi kicin kuma sai ta dakata tana ce masa,"Kaga kuwa ma yau idan ka ci gyaranta a karatu wallahi ka zaneta don jiya yawo ta kaɗa suka tafi da ƴan islamiyarsu, taja min faɗa a wurin Abbaanku".

Da sigar tsokana na ce,"Ai Yaya da har zamu biyo maka ma sai Safiyya tace muna zuwa zaka fara mana wa'azi".

Sai naga yanayinsa ba kamar yanda muka saba da shi ba, banda haka da yanda nayi maganar nan ai ya bani amsa daidai da maganata, haka yake shikam wajen zaro maida martani, ka faɗi ɗaya ya faɗa maka talatin, ga iya baƙar magana me saka cikin mutum ya ƙulle saboda dariya. Gyara zama nayi na fuskance shi sosai, domin kuwa idan har na gansa a irin wannan yanayin to akwai matsala, domin shi ɗin mutum ne me raha, in har ka gansa saɓanin walwala to tabbas akwai damuwa babba, imma ciwon ƙafar Iyam, imma kuma a gida babu abin da za'a ci sai idan kuma ya fita yay buga bugarsa ya rasa abin yi.

Kallonsa na ke sosai da nazarin son fahimtarsa, na san babu ɗaya daga cikin abubuwan da na ke tunani, idan Iyam ce jikinta ya tashi shigowarsa za su yi maganar da Ummani, aikin yi kuma yanzu yake murna da mana albishir ɗin ya samu wajen sana'a. To mene matsalar? Hannu na saka na firfita idonsa ya ƙirfta daga kafe wuri ɗaya da yay.

"Yaya lafiya dai?".

Yasa hannu ya shafi fuskarsa yana cewa,"Lafiya lau, ɗauko kayan karatun na ki da sauri ina da uzuri".

Kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya juyo yana kallona, fuskarsa babu wani annuri ya ce,"ba ki ji ba ne?".

"Naji Yaya, kawai na damu ne da canjawar yanayinka cikin ƙalilan ɗin mintuna, kuma sai zuciyata yau duk bata yarda da lafiya ɗin da ka ce ba".

"Yanzu dai ɗauko littafan muyi abin da ya kamata".

Na miƙe jiki a sanyaye na wuce ɗaki, na dawo da jakar littafaina sanye kuma da hijabina. Dardumar da na zo da ita na shimfiɗa nayi zaman karatu ina mai fuskantarsa. Bismillah ya fara muka shiga karatun, ina jin daɗin karatunsa sosai, duk daƙiƙancin mutum ya ɗauki darasi a wajensa sai ya iya kuma sai ya zauna a kansa, bai yi min wani ƙari me yawa ba naji yana rufewa da adu'ar tashi, nayi saurin cewa.

"Yaya ko rabi fa bamu yi ba, kuma yau littafi ɗaya za'ai?".

"Ehh gwara muyi kaɗan ba zan so shiga lokacin wani". Sai kuma ya kalli agogon ƙurƙurar wayarsa da nake tsokanarsa da ita, ba tare da ya dube ni ba ya ce,"Ƙarfe Biyar da rabi yanzu, duk inda ya ke yana kan hanya sai ki shirya".

Furucin nasa yasa na ware ido ina kallonsa da kyau, sai duk naji zuciyata babu daɗi sam, na san yana yi min tuni ne, domin tuntuni yace na ɗaukar masa alƙawarin ba zan tsaya ina bawa wani namiji fuska ba, ba zan tsaya kule kulen samari ba, kuma ba zan tsaya zance da duk wanda ya zo wajena ba. Kuma waccan shekaranjiyan kawai sai ya zo ƙofar gida ya taradda ni da baƙo, dama tun a lokacin da naga yanayin yanda suka gaisa da baƙon na san bai ji daɗin ganinmu tare ba, nima kuma bai san ba'a son raina ne har na ke tsaye da baƙon ba.

Hasalima ranar ne na fara ganinsa kuma bisa umarnin Kaka, shi ɗin Yaya ne a wurin Safiyya don ɗan Yayar Ummansu ne, Saurayi ne ba wani babba ba, Air force ne yanzu haka yana cross river can yake aiki sai lokaci zuwa lokaci yake leƙowa ganin iyaye, Wai ya ganni ranar mun je gidan su Safiyya, shine maimakon ya fara tuntuɓata kawai sai ya tafi wurin su Kaka kai tsaye, kuma zuwan ma ba shi kaɗai ba har da manyansa, Abbaa ya gaya masa cewar yay haƙuri ya sanar da su gaskiya akan ba yanzu zai aurar da ni ba, amma sai ce yaji ya amince zai jira zuwa duk lokacin da aka ɗiba masa, shima dama ko da auren aka yi yanzu zai barni nayi karatuna ba zai hanani ba ko da ace aiki ne ma, Kaka yace to shikenan sun ba shi, amma da sharaɗin babu waya babu zuwa zance har sai lokacin da aka ba shi izini amma ya san da cewa kam sun basa Sa'ida, Ya ce ya yarda ya amince, Wan mahaifinsa ya dage akan za su bada kuɗin aure, dole haka aka karɓa naira dubu ɗari ba don son ran Abbaana ba sai don amincewar Kaka.

Shine ranar ya zo gida wai na gansa, Safiyya sai wani faman koɗa min shi take wai na yarda ai auren ana yi sai ƙasar da na zaɓa, kuma mahaukacin kuɗi ne da shi, yay bala'in iya soyaya, waye waye ɗinta dai, ni har ta ban haushi ma na ce ita me ya hana ta aure shi, sai ce tayi ai don bai ce yana sonta ba ne, da yace yana sonta da naga yanda ake auren miji na kece raini. Ni dai ranar da kukana na fita, fuska babu yabo babu fallasa muka gaisa da shi, tashin farko kuma tambayar da yay min wai in faɗa masa yayi min zan iya aurensa? Idan ba zan iya aurensa shi ba zai shiga hakkina ba zai haƙura yabawa wasu dama, ko da naga ya fara magana da iyaye saboda hakan shine mutuncinsa, amma ko kuɗin aure da aka bayar dama an bada ne bisa sharaɗin idan nace bana sonsa za'a mayar masa da kayansa.

Ni dai kai na ɗaga masa na amincewa kawai, don ko fuskarsa ma ni ban tsaya ƙare mata kallo ba, abu daya zan iya cewa fari ne me matsakaicin tsayi, muka gama gaisawa sama sama yana ta faman gabatar min da kansa da tarihinsa, yana aikin min tambayoyi. Ni da ina ta jinsa kawai zuciyata a matse babu daɗi, to amma ya zanyi! ni ko da naji waye shi na kuma gansa a gabana ko kaɗan ban ji bana sonsa ba, haka ban ji ina sonsa ba, ni dai kawai na san da cewa ina ƙaunar zaɓin Abbaana, kuma zan koyawa zuciyata son zaɓin Abbaana ko da ace zan cutu, ko da zan mutu ta silar hakan. wannan alƙawari ne da na ɗaukarwa kaina ba tun yanzu ba, na shirya zama da duk wanda Abbaana ya zaɓa min matsayin mijin aure ko da ace ina da wani wanda na ke mutuwar so a gefe, to balle ma yanzun babu kowa da na ke so a zuciyata, babu wani da na ke hasashen aure, don haka na san da sannu zuciyata zata amshi soyayyar lieutenant Salim Sadiq Oluwa.

Idanuwana suka yi nayi narai narai na shiga wallacewa Yaya Nazifi,"Allah Yaya ko ranar da ka zo ka taradda mu ni ban san da zuwansa ba, ina zaune ne fa kawai Kaka ya ce naje waje ina da baƙo, ina jin nauyin faɗa maka ne shiyasa amma na san Ya Imam zai maka maganar".

Kansa ya gyaɗa alamun yaji, bai ƙara cewa da ni komai ba nima nayi shiru ina jin kamar zan saka kuka. Sai bayan wucewar kusan minti goma kana ya kalle ni ta gefen ido yana sosa gemunsa ya ce,"Ki yiwa Ummani magana zan wuce?".

Na maƙe kafaɗa ina cewa,"To Yaya ai kana fushi da ni".

"Fushi kuma akan me". "To Yaya idan ba fushi ba, ɓacin ran saman fuskarka na menene?".

"Kar ki damu Ƙanwata, kawai dai banda muhimmanci ne yanzu a wurinki, matsayina kuma ya canja tun da kin samu abokin rayuwa...".

Ji nayi kamar in kai hannu na toshe masa baki, amma babu damar hakan. "Kayi haƙuri don Allah Yaya, kai fa Yayana ne muna tare har abada, kai me aurar da ni ne, kuma ni wallahi Allah matsayinka bai canja ba a wurina...".

"Ya kike wallacewa bayan ga zahiri, idan da ne ai duk yanda ake ciki kafin ki fita wajensa ma sai kin kira ni kin faɗa min, karo na farko da ba ki nemi shawarata ba, ai shikenan na gode".

"Kayi haƙuri Yaya don Allah, ba ni da wani zaɓi ne. Amma ai kace kai zaka tayani zaɓar mijin aure, idan bai yi ba shikenan".

Murmushi yay wanda bai kai har ƙasan ransa ba ya ce,"Yayi mana Ƙanwata, ai yana da kuɗi kuma yana da ƙwaƙwƙwaran aikin yi, yana da wurin ajiye ki, zai iya riƙe mace kuma ko yanzu aka ce ya fito zai kawo lefe kuma a shirya biki cikin kwanaki ƙalilan, babban ma'aikaci irin wannan ba abun yarwa ba ne".

Na ɗan juya idanuna ina daɗa jin wani iri cikin raina. Na dakatar da shi da cewa,"Yaya ni duk ba wannan ba. miji me nagarta na ke so, me ilimin addini, tarin kuɗinsa bai dame ni ba, ni dai ya so ni kawai da dukkan zuciyarsa, in dai akwai rufin asirin da zamu ci musha mu zauna a kowanne irin muhalli ya ishe ni. Kuma kaga shi fa ban san ya halinsa yake ba, ban san ɗabi'unsa ba, addininsa ya yake? Nagartarsa ya take? kuma su irinsu ka san matansu basa samun lokacinsu saboda irin aikinsu, ni kuma mijina lokacinsa, soyayyarsa, yardarsa da kulawarsa na ke biɗa. Ni Yaya miji irinka kawai na ke so kayi min adu'a Allah yasa shima haka yake".

Shirunsa yasa na ɗago ina kallon, na ce"Yaya". Sai kuma na rasa abun faɗa, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yace,"Kin san me?".

Na girgiza masa kaina alamar a'a. "Ina tsoron rabuwa da ke ne Ƙanwata saboda nayi sabo da ke fiye da tunanin me tunani".

Na karayar da kaina na ce,"To me zai rabamu kuma? Aure fa kawai zan yi".

"Au aure ne ma kawai? Tunaninki mijinki zai yarda da alaƙarmu ne? A irin wannan shaƙuwar tamu? Ko ni ina tsananin kishinki balle mijin da za ki aura, Miji ma irin wannan mutumin, daga lokacin da kika yi aure Sa'ida duk wata alaƙa da ke tsakanina da ke ta rushe babu ita".

Tsorata nayi naja da baya saboda yanda yay furucin cikin huci. Yanayin kuma da ban taɓa ganinsa a ciki ba, kawai sai hawaye ya fara sakko min nasa hannu ina gogewa ina ce masa.

"Yaya indai baka sonsa zan haƙura da shi, ni bana son abin da zai rabamu".

"Ban zauna da shi ban san waye ba amma daga yanayin da na gansa ni kaina zan iya zaɓa miki shi, to amma bai yi min ba, idan na ce bana son aurenki da shi Ya za ki da su Abbaa?".

"Nima ban sani ba amma ba zan iya bijirewa zaɓinsu ba, zan faɗa masa ya ce musu ya janye. Yaya zan fasa aure in har alaƙarmu da kai zata taɓu".

Na faɗi hakan ina kuka sosai, kuma kawai sai gani nayi ya miƙe ya zura takalmansa ya fice. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR04FT5* _Not Edited, Plss avoid error mistakes._ ________________________ Cikin sati biyu kamar yanda Abbaa ya yanke hukunci aka kawo lefena akwatu biyu maƙil da kaya, sai shinkafa kwano bakwai da dardumar sallah da ƙur'ani da littafan addini. ba ƙaramin ƙoƙarin Yaya Nazifi na gani ba, kuma sosai naji daɗi tunma da naji yanda ake ta santin kayan da ya zuba da yaba masa a irin ƙoƙarin da yay, a lokacin atamfa mai mugun tsada dubu biyu da ɗari biyar ce zuwa uku, kusan duk kayan da aka ɗaga sai Umma ta faɗi tsadarsu da ke ƴar kasuwa ce ita. Don haka murna ba ni ɗaya ba har da Ummani domin kuwa an bawa maƙiya kunya don kaf ƴaƴan Baba Tijjani da aka aurar ba wadda ta sami kaya kamar nawa.

To tun fa daga nan hidima sai ta ɓalle a gidanmu aka shiga shirye shiryen biki, shi Abbaa bai taɓa tsammanin Yaya Nazifi zai iya kawo lefe a ɗan ƙanƙanin lokacin da yanke masa ba, ya tauna tsakuwa ne domin aya taji tsoro, sai ga shi kuma yaga saɓanin tunaninsa, don haka a maimakon ya matse Yaya Nazifi sai ya zamana kansa ya ɗanawa tarko, domin kuwa dai a wannan lokacin ana cikin rufin asiri ne amma cikin jin jiki ake, sam bai da wasu kuɗin aurar da ni, na abincin gida ma da ƙaƙa ake samu, sai Ummani tayi cinikin lemo ake yin cefane da siyan abubuwan buƙata, ga lokacin jikin Kaka sai a hankali don haka duk wasu ƴan kuɗi da suka samo akan magungunansa suke tafiya, kuma kullum ana hanyar asibiti, don hatta kuɗin jarabawata na waec sai bashi Abbaa yaci ya biya acewarsa gwara na haɗa jarabawa duka biyun.

Ni dai sai ya zama gaba ɗaya bana cikin farin ciki, kamar ma ba wata amarya ba, na yi mugun shiga damuwa da ganin yanda iyayena duk suka takura, babu wani me walwala a cikinsu, ko da yaushe suna jugum sai walwalar ƙarfin hali da suke kawai. na shiga damuwa sosai hankalina ya ƙara tashi na rame domin kuwa Abbaa sam a lokacin banda gaisuwata da yake amsawa ba wani magana da ke ƙara haɗa ni da shi, Ummani ce ke ta tausarsa a hakan ma.

Ana saura kwanaki goma biki Yaya Nazifi ya zo, na saka masa kuka akan a ɗaga biki ni kam, yaga na tashi hankalina sosai to da yake shima yana da buƙatar ɗaga ƙafa sai yace zai yi magana da Malam sai su zo a sami Abbaa. Ni dai na san da kamar wuya domin mahaifina kaifi ɗaya ne, ba ya sauka akan maganarsa, shi ya yanke don haka ba zai taɓa janyewa ba na sani, amma wataƙila a wannan karan ya sauko, kuma abin da ya ɗaga min hankali naje gaishe shi da safe naji suna maganar shi da Ummani akan ko kuɗin katifa ma babu balle sauran kayan ɗaki da ake buƙata, gwara ita Ummani ma tun da jimawa an taɓa kawo mata tallan tukwane tayi dabarar siya bayan su itama bata ajiye komai na kicin ba domin duk basu tsammaci zuwan lokacin aurena yanzu ba, yanda suke kaishi da nisa ashe ba haka Allah ya shirya lamarinsa ba, aure ƙanin mutuwa ne idan ya zo babu yacca za'ai.

Malam suka zo suka sami Abbaa da batun a ɗaga aure yace sam ai shi magana ɗaya yake yi, shi dai zuwa ranar asabar zai ɗaura min aure babu ruwansa da inda Nazifi zai ajiye ni, yayi min abin da na ke so ya kuma fita hakkina. Abin da ya rage tsakaninsa da Nazifi riƙe masa ni amana da kuma cika alƙawarin da ya ɗauka na barina in yi karatu a gidansa, shima kuma ta ɓangarensa zai cika alƙawarin da ya ɗauka na ba zai bar Yaya Nazifi da ɗaukar nauyin karatuna ba shi zai ci gaba da ɗauka matsayinsa na mahaifina da hakkin hakan yake akansa, duk abin da ya shafi katatuna a gidan Nazifi shi a mahaifina shi ke da hidimarsa.

To haka dai da karime karimen abubuwa a ɗau wancan a siyar a ɗauka wancan a siyar, Yayyuna su kawo ɗan abin da suka fita suka samo da haka aka haɗa aka min kayan ɗaki, Ummani kuwa kusan duk wasu kayanta masu daraja sai da ta ɗaga ta siyar aka siya min kayan kicin.

Ranar lahadi aka ɗaura aure, ɗaurin auren da ya tara mutane da yawa. Ranar kam nayi kuka sosai na kuma yi mugun danasanin ɗaga hankalin iyayena da nayi akan auren nan, haka naji ina ma ban san Nazifi ba a rayuwata, domin ranar sai bashin kayan abinci aka karɓo aka yi abincin biki. Daren ranar aka kaini gidana bayan tarin nasihohin da na sha daga wajen mahaifina masu ratsa jiki, irin nasihar da yake ta min akan zaman aure sai naji ina ma ace a warware wannan auren. hatta shi kansa sai da yay kukan rabuwa da ni, Ummani kam da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikinta, abin da ya ƙara sakani kuka a lokacin yanda Abbaana ya dinƙa bani haƙuri akan ƴan kayan da suka yi ƙoƙari wajen siya min, yana faɗa min don Allah kar nayi fushi in sha Allahu bayan aure da ya samu kuɗi zai sauya min komai ya siya min sababbi masu kyau da ƙarko, kuma za su ƙaro min kaya da yawa indai kuɗi suka zo hannunsa, ya san waɗannan sai dai nayi maleji, kuma yasan za'a iya min dariya idan aka gani tunda tsofaffi ne aka siya amma kar na damu sa duk wanda yay min dariya, wata rana zai saka ni dariyar in Allah ya yarda, kuma fushin da yay da ni akan lamarin auren nayi haƙuri, sannan da zarar naji an fara biyan kuɗin jamb na faɗa masa ya tura min kuɗin registration, haka aka fita da ni daga gidanmu kamar zan shiɗe saboda kewar iyayena da zan yi.

Yashaik ne ya aro motar gidan da yake direba aka kaini a ciki saboda shi Yaya Nazifi ba abokai ne da shi ba, Hamisu ne shi kuma adaidata yake ja don haka shine ma yay ƙoƙarin tattaro tawagar masu adaidaita sahu aka dinga ɗiban ƴan kai amarya.

To a rayuwar gidan aurenmu babu abin da zance da ubangiji sai godiya gare shi da ya mallaka min Yaya Nazifi matsayin mijina, domin kuwa nayi dacen samun miji na gari da ya san darajar mace, wata iriyar rayuwa muke shimfiɗawa me cike da zallar soyayya da ba zamu taɓa mancewa da ita ba a tarihin rayuwarmu, Yanda Yaya yake ji da ni tamkar zai haɗiye ni da soyayyarsa, zazzafar ƙauna yake nuna min ta kowanne ɓangare, bai taɓa bari na koka ba, motsi kaɗan ya tambaye ni me nake so, me zai yi min, duk wani abu da ya san ina so sai yay ƙoƙarin samar min shi, haka idan ya fita ya tashi dawowa da ɗan namansa ko kifi ko kayan marmari, a gida ma mu girki me kyau da rai da lafiya ko gidan wasu masu kuɗin sai haka, haka idan ya fita aiki shine baro shago da rana ya zo ya duba ni sannan ya koma, kullum faɗamin yake son da yake min baida adadi, domin samun macen aure ta gari irina da wuyar samu, don haka yay min alƙawarin mutuwa ce kawai zata rabamu, kuma yay min alƙwarin zai inganta rayuwata da dukkan ƙarfinsa da ikonsa.

Ta ɓangaren ƴan uwansa ma haka, nuna min so suke tamkar zasu haɗiye ni, komai suka samo a rakito akawo min, abinci wannan sai naga damar girkawa don da wuri ake gama abinci acan a kawo min, kuma da yake bamu da nisa sosai kusan kullum ina gidan don Iyam bata da wani batu a bakinta sai na Sa'idata, Nazifi turo Sa'ida ta zauna kusa da ni idan ka dawo daga aiki sai ka zo ku tafi tare. Irin ƙaunar da sirikata ke nuna min sai nake jin kamar mahaifiyata, komai Iyam taci sai ta bani, duk wani sirri ko shawara ko damuwarta ni ɗin nan dai nice, sai ta faɗa min ma abin da ya shafeta bata faɗawa ɗanta ba, har shima yake tsokana da cewa gaskiya zai yi ƙarata wurin alƙali na ƙwace masa mahaifiya.

To haka ma babbar Yayarsu Yaya Maijidda, matar nan yanda ta ɗauke ni ko yanda ta ɗauki Nazifi da suke ciki ɗaya albarka, itama komai matar ƙaninta Ƙarami, har facalolina suka fara jin haushin hakan, bini bini ta kira waya ta tambaya ya muke, ban da wata matsala ko, kuma Ƙarami ba ya min komai ko? Idan yana min wani abu kar na ɓoye na kira na faɗa mata. To ni kuwa ƙarar me zan kai mata akan mijin da ya tattara dukkan soyayyarsa da ƙaunarsa, kulawarsa da hidimtarwasa ya ɗora akaina? Ai ni babu abin da zance da Nazifi a rayuwa.

Kamar yanda Abbaa ya faɗa min shekara guda da aurena ya canja min kayan ɗaki sababbi masu kyau, kuma ba'a kwashe tsofaffin ba yace duk na haɗa, nayi murna sosai da farin ciki tare da adu'a wa mahaifina. Dama ɗakuna biyu ne don haka sai na mayar da tsofaffin ƙaramin ɗakin, da yake kujera ɗaya ce dama duk sai ya ɗauke ɗakin bai cunkushe ba, wancan ɗakin kuma da yafi girma can na bar sababbin kujeruna har uku na bar shi a matsayin ɗakin Hubbi, don har labulaye Abbaa ya canja min, dama waɗancan wasu ajiyayyu ne na Ummani da bata saka su aka fito min da su.

Jarabawar waec da neco ɗinmu ta fito a lokacin kuma sai ban ci ba duk biyun, a waec bani da english da biology, neco kuma bani da english da maths, haka na sha kukana Abbaa yay ta lallashina yace in bari idan za'a kuma yin wata sai na ƙara zanawa, to ita kuma lokacin da ya zo sai ya zamana babu kuɗi har aka rufe biya, amma haka Abbaa yay ta ban haƙuri da cewa in jira lokaci Yashaik yace masa ana zana wata da ake biyan kuɗi masu yawa a ci, to idan za'a yi indai da kuɗi zai biya min na kwantar da hankalina.

Cikin shekaru biyu da aurenmu al'amura suka fara taɓarɓarewa Hubbi, rana ɗaya megidansa yace ya saida shagonsa, ya sallami su Hubbi da dubu tamanin tamanin yana basu haƙuri. Wannan rasa shago da Hubbi yay shine mafarin ƙalubalen da muka fara fuskanta, kuɗin sallamar da aka ba shi da su ya samu ya buɗe tireda a ƙofar gida yake siyar da provision.

Sauran kuɗin da yay saura kuma ya siyo kayan abinci na ɗan lokaci ya ajiye, sai ƴar dubu huɗu da ya bani yace na ɓoye ko da wata buƙatar ta ujila zata ta so. To yau da gobe kayan abinci duk suka ƙare, tireda kuma sai dai ace an gode Allah domin tuni itama kayan ciki suka ƙare kuma ya rasa ta ina kuɗi suka tafi, abun dai ba'a cewa komai lokaci guda komai ya tsaya masa cak.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull