Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 3
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 3: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 3. Kullum zai fita amma haka zai je ya dawo babu wani ƙwarin jiki, ya…
4,398 words
Kullum zai fita amma haka zai je ya dawo babu wani ƙwarin jiki, ya buga duk ta inda zai buga ya rasa wata sana'a da zai kama, sai dai ya fita haka yaje wajen su Yayan Shago inda suke leburanci ya zauna wajensu ya ɗan taya su wani abun, su kuma a kuɗin sallamar da ake basu a ciki suke sammasa, to ɗan kuɗin ba wani me yawa ba ne idan yazo da su basa kaiwa ko'ina, iyaka abin da za'aci na lokaci ɗaya ne kawai ake samu, to don ma Allah yasa babu yara da damuwar da zamu shiga sai tafi haka.
Rayuwa taci gaba da tafiya har aka zo gaɓar da kullum sai dai ya fita haka ya dawo babu komai, ɗan na garin kwakin ma da ake siyowa aci yanzu ba ya samuwa, ƙanzon da muka shanya duk ya ƙare, muka koma sai dai wata rana muci watarana kuma haka zamu yini mu kwana da yunwa, ruwa kawai muke sha. Wannan hali da muka shiga na tsananin babu ita tasa na koma yin waya gida ina yin dabara na ce ni abincin gida nake so ci idan anyi a aiko min da shi, har aka fara zargin ko ciki ne da ni, to fa da wannan ne ma muke samu muci rana da dare, dama na safe ba'a batunsa, wataran kuma idan na tashi sai in je can gidansu na yini to acan zanci na rana idan dare yay kuma a zubo mana mu taho da shi, kuma duk wannan hali da muke ciki babu wanda ya sani domin kuwa muna da wadatar zuciyar da babu wanda zai ganmu ko ya zo gidan ya gane halin da muke ciki, fes fes zaka ganmu cikin annuri da walwala, gidanmu ɗasɗas babu wani alamar tsanani.
To abu fa yaci tura babu wani sauƙi sai tsanani, talauci yay mana ƙatutu, ko lalura muke sai dai mu roƙi Allah ya bamu lafiya magani kau biyar ɗin siya ma babu. Da haka dai na bawa Hubbi shawarar ko in nemi sana'a ko da aikatau ne nake yi, yace bai amince ba sam, zai ci gaba da jajircewa wajen neman abun yi. Kullum cikin hawayen tausayin halin da muke ciki na ke, ga mijina me tsananin tawakkali wanda ko bacci cikakke baya iya yi haka yake kwana yana gayawa Allah ya kawo masa ɗauki da mafita. Watarana kawai na yanke shawara ni ɗaya domin ba zai yiwu muci gaba da zama a haka ba, ba tare da sanin Hubbi ba na nemo dillaliya ta siya kayan ɗaya ɗakina da sabuwar kujerata guda ɗaya.
Hubbi ya dawo da daddare na damƙa masa naira dubu talatin a hannunsa. Ya kalle ni yana tambayar Habibity ina kika samo damin kuɗi haka sannan ne nake sanar da shi yanda aka yi. Tsabar farin ciki har da ƙwallarsa, ya rungume ni jikinsa yana saka min albarka da godiya. A washegari kuwa yaje kasuwa ya siyo buhun garin masara da shinkafar hausa, yasa kuma aka yiwa tiredarsa ƴan gyare gyare, ya fara aunar da garin masara da shinkafa dama babu irin masu awo a cikin layin sai anje titi, ai ko kan kace me wannan ƴan unguwa an ganewa wajen, ni kuma cikin gida sai na ke sana'ar wanki da guga, haka zanyi wanki me uban yawa, idan dare yayi Hubbi ya tayani guga, kuma ɗan abin da za'a samu bai kai ya kawo ba amma a hakan dai babu laifi, haka muka haɗu da taimakon juna muna rufawa kanmu asiri.
Muna cikin wannan rayuwar dai Allah ya kuma kawo mana jarabawa, shima awon da Hubbi ke yi aka zo aka sace tiredar, rana ta farko da na taɓa ganin hawayen mijina wanda yay matuƙar ɗaga hankalina ranar har ban yi bacci ba. Tun daga nan kuma Hubbi ya sare yace shi ya gaji, ta kai ta kawo idan ma ya fita da anga ya dosa waje za'a fara ƙusƙus ana maula ta kawo shi, masu shago kuwa duk sun sauya masa fuska saboda basa son ba shi bashin kayan abinci don ba'a samun damar biya da wuri. Duk ƙarfin hali irin na Hubbi haka zuciyarsa ta mutu yace kawai ubangiji yay ikonsa akanmu, har ta kai ga ya kusa yin saɓo sai da na rufe masa baki.
Tsaka da wannan tashin hankalin da muke ciki na kwashi kujeruna duka naje na siyar, kayan kicin ɗina ma haka duk na tattara masu kyan na siyar da sitturuna masu kyau, don har ga Allah na gaji da ganin mijina na zaman jugum yana hawaye, na gaji kuma da jin yana fita mutane na gulmarsa suna gudunsa. Don haka kuɗin da na haɗa dubu arba'in da biyar na kaiwa maƙocinmu na ce don Allah ya nema mana aron adaidaita sahu ga wani abu zamu rage, a hankali kuma sai a dinƙa cikawa, amma don Allah kar ya bari mijina ya san nice na zo da zancen kawai yace shine ya taimaka masa.
Mutumin da ke yana da mutunci a washe gari kuwa sai ga shi ya kira Hubbi, suka je can wurin karɓar babur ɗin aka saka hannu da komai tare da yarjejeniyar cikin shekara guda zai gama biyan kuɗin babur ya zama na shi, ya dawo yana ta farin ciki yana shaida min yanda akai, ni dai ko kusa ban nuna masa ma ina da sa hannu a lamarin ba, haka muka kwana cikin farin ciki da adu'ar Allah sa zuwan ƙarshen komai kenan.
To a ranar farko da Hubbi ya fara fita da babur ɗin yay hatsari babba don babur ɗin sai da yay raga raga, shi kuma ya samu karaya har biyu a cinya. Ya sha wuya ba kaɗan ba, a wannan lokacin ne kuma aka fara fuskantar halin da muke ciki bayan dawowarmu daga asibiti, Ummani taga bata ga kujeruna ba ko da ta tambaye ni nace mata ai ina so a sauya min su ne mun kai wajen gyara. Hubbi na tsaka da ciwo jikin Iyam ma ya tsananta, ciwon nono da sikari ya tsananta mata sosai, har ana tunanin sai an yake nono ɗaya, tashin hankalin da muka shiga a wannan lokacin Allah kaɗai ya bamu ƙarfin tawakkalin sake karɓar jarabawar a karo na barkatai.
Sama da wata uku Iyam na kwance a asibiti anata fama, nan gida ma haka karayar Hubbi da ake ta fama sai tayi sauƙi sai ciwo ya koma gidan jiya, ni da shi duk muka fita a hayyacinmu muka rame kamar kuɗin guzuri. Ni dai a hakan na ci gaba da jajircewa a wanki da guga wajen tallafa masa, ban taɓa nuna masa na gaji ba, haka ban taɓa nuna bana tare da shi ba. kullum ma ni ce me tausarsa da kwantar masa da hankali, ƙarfen da yake dogarawa da shi ya lalace magungunansa suka ƙare, muka rasa ya zamu yi, ga can ana fama da Iyam wadda itama cukucuku ake tayi wajen neman kuɗi nata magungunan.
Ana haka Abbaa ya turo min dubu saba'in yace in je nayi rijistireshon na jamb da na waec, abun da yay saura kuma na adana su da kyau idan jarabawar ta fito na ci sai na biya kuɗin makaranta da su, ya san ba zasu isa ba amma zai ke turo min wani abu ana tarawa a hankali a hankali. To da yake ba'a ma fara registration ɗin ba da saura kusan wata biyu, Hubbi yace to na ɗauko kuɗin mu siyo kayan abinci, a siya maganin Iyam shima a siya nasa, kafin lokacin in sha Allahu za'a mayar da kuɗin. Hakan kuwa aka yi cikin ikon ubangiji kuma sauƙi ya samu, sai dai ba ya wani iya fita kullum yana gida. Iyama jikinta yay sauƙi sosai don dubu talatin da ake nema duka muka ware aka kai asibitin.
To da haka muka ci gaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, idan nayi wanki shi zai guga, ya fara karɓo mana kalwa ma a gida ina siyarwa. Watarana da rana muna zaune a tsakar gida muna sauraron rediyo muka ji labarin wani attajiri da ke taimakawa talakawa, aka faɗi sunansa da adireshinsa. Na kalli Hubbi naga kamar ma bai ji abin da aka ce ba, da daddare muna cin abinci na taso da maganar, ya girgiza kansa yace ba zai je ba shi yanzu yana tsoron zuwa neman taimakon wani. Nayi ta tausarsa sam yaƙi amincewa yace shi fa ba zai je ba, haka muka kwanta zuciyata fal da saƙe saƙe.
Ana kiran farko na tashi nayi alwala na shirya, na ɗauki takarda da biro nayi rubutu na ajiye kusa da Hubbi, a ciki na faɗa masa cewar zanje can wajen mutumin ko Allah zai sa a dace, idan ya farka yaga zai iya biyo ni to. Yana ta barci bai ma sani ba na tsallake na fita cikin mamakon ruwan saman da ake ta zugawa tun bayan isha'i, ga ban da kuɗin mota amma ban karaya ba sam haka na taka tun daga Yakasai har Nasarawa GRA, tun ƙarfe huɗu da rabi na dare ba ni na isa ba sai ƙarfe shida da rabi saura, ba tare da naji tsoron gamuwa da komai ba hasalima ban tunanin wani abun cutarwa ba, ni dai ina cikin adu'a da zullumin fatan Allah sa zuwan nawa ya zama alkhairi.
Ni ce ta uku a layin mata kuwa, Alhaji Isma'il Fari bai sami fitowa ba sai ƙarfe takwas, ban ma san layi ya zo kaina ba saboda ina can ina gyangyaɗi, sai da wata ta zungure ni kafin nan na miƙe da ƙyar saboda ciwon jiki da kuma yacca nake jin cikina a ɗaure. A kallon farko da na yiwa mutumin a raina naji in sha Allahu za'a dace, haka na zauna ina faɗa masa matsalar da muke ciki, tun ina hawaye a hankali har na koma kuka sosai, matarsa tana kusa da shi itama ta tausaya min, ya jinjina kansa yana faɗa min cewa in sha Allahu zai yi mana abin da zai iya.
Ya kalli matarsa ya ce ta lissafo dubu ɗari biyar ta ba shi, ni dai kaina na ƙasa zuciyata na ta bugawa, tausayin kanmu na ƙara lulluɓe ni. tunanin da na ke ya katse lokacin da naji Alhaji Fari na cewa,_"Iyakar abin da na ke iya taimakawa da shi matsayin jari dubu ɗari da hamsin ne, to amma tsakani da Allah duk a cikin masu zuwa neman taimako matsalarku tafi taɓa ni, don haka ga wannan dubu ɗari biyar na muku domin Allah"._
Yay furucin a daidai lokacin da Hubbi ya shigo ciki wanda aka yi masa iso, tsananin farin ciki ban san lokacin da na miƙe daga gaban Alhaji Fari ba riƙe da kuɗin a hannuna ina ta karkarwa jiki naje gaban Hubbi ina nuna masa. Na kama hannunsa na damƙa masa ina faɗin,"Hubbi ga shi na ka ne halak malak, Allah ya amsa adu'armu Hubbi yaji kukanmu, Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan yasa kuma silar ɗumbin arziƙinka ne mara yankewa".
Kuma maganar da Alhaji Fari ya ƙara yi ita tasa na juya gare shi ina jin furucin da yake kamar a mafarki, faɗa yake wai ya bawa Hubbi shago ɗaya kyauta a ɗaga daga cikin plazar da yake da ita a janbulo. Don haka yasa rana zai sa ayi masa iso zuwa shagon, abun da ya rage masa kawai ya zuba kaya. Tsabagen farin ciki sai muka rasa da wanne kalami ma zamu yiwa Alhaji Fari godiya, ga kayan abinci ma da yasa aka haɗo mu da shi, buhun shinkafa biyu, katan na taliya biyu, sai galan ɗin manja da man gyaɗa, haka muka dawo gida da murna sosai mara misaltuwa, Hubbi ya dinƙa min godiya dasa min albarka.
Kuma a wannan ranar ne da muka je duba Iyam Hubbi ke labarta mata duk abubuwan da suka faru tun daga farko har wa yau, Iyam taji na ƙara shiga ranta, ta kasa ɓoyewa sai da ta sanar da Malam da Yaya, waɗanda suma suka dinga min godiya da irin halaccin da na nunawa ɗansu, wanda in ace wata ce tuni ta rabu da shi amma ni haka na rayu da shi cikin tsanani da wahala, ba tare da na taɓa fallasa sirrin matsalar mu ba.
Allah alqawiyu ashe wannan shine silar arziƙin Hubbi, domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci da zuba kaya da yay a shagon Allah yasa masa nasibi shagon ya bunƙasa, dama shaddodi yake siyarwa nan da nan sai ga shi yana rufa riba da wasu ɗaruruwan kuɗaɗe, kuma kafin kace me wannan Hubbi ya zama Alhaji, da yana sawa a shigo masa da kaya daga baya kuma sai ya koma fita da kansa yana shigo da su. Tashin farko ya ƙerawa iyayensa sabon gida na gani na faɗa, bayan ya gama da su muma ya tamfatsa mana namu anan ɗorayi salanta link 3, gida na haɗuwa, gata iya gata na gani domin kuwa gwalagwalai ya dinƙa siya min, Yayyuna na roƙe shi duk ya bisu da jarin naira miliyan ɗai ɗai.
Da nayi masa maganar ci gaba da karatuna ya nuna shi kamar ma bai san da zancen ba, ga Abbaa na ta min magana akan naje nayi registration yaji an fara, shi kuma da na masa zancen sai ya ɓata rai har ma yace min kar na ƙara tambayarsa wani kuɗin makaranta, wannan kuma shine ƙalubale na farko da na fara fuskanta daga gare shi bayan canjin rayuwar da muka samu, kafin ƙalubalen rashin haihuwa ya biyo baya daga ta ɓangarensa da ƴan uwansa har kawo lokacin yanzu da ya ƙaro aure.
*DAWOWA LABARI.* _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR03FT5* Ummani ta fito ta sameni durƙushe ina kuka, ta shiga tambayana dalilin kukan, ni dai ko da na ɗago ido na zube akanta sai na rasa amsar bata, domin ni kaina ban san dalilin kukan nawa ba, na dai san kawai zuciyata babu daɗi. Ta matsa min da tambaya ban san lokacin da na ce mata,"Yaya ne yaƙi min ƙari saboda yaci gyarana a karatu".
"To ai maganinki, Sa'ida jiya kaf ba ki duba karatunki ba, ba na so ki fara saka wasa a karatu wallahi. Kuma ai da gaskiyarsa idan kin iya ya ƙara miki. Yanzu yana ina?".
"Wai yaje ya dawo". Na faɗa ina goge hawayen fuskata.
"To ga abincin idan ya zo sai ya tafi da shi. Nasa yana cikin ƙaramin flask naga magriba tayi ba lallai ya tsaya ci anan ba, babbar kular kuma ya kaiwa Iyam. Ni zan shiga daga ciki zan yi lazimi".
Tana gama faɗin hakan ta wuce ɗakinta. Nafi ƙarfin minti goma sha zaune ni ɗaya ina ta jira in ga ko zai dawo amma shiru. Tashi nayi na ɗauka ledar kayan abincin na shiga ɗakina, na je ɗakin Ummani na ɗauko wayarta na dawo na zauna na kira tasa wayar har sau uku bai ɗaga ba. Daga ƙarshe na yanke shawarar tura masa message, sai ya dawo min da reply ɗin cewa zai aiko Adamu ya karɓar masa yanzu yay nisa. Da magriba kuwa Adamu ya zo ya karɓa dama ina ta gudun kar Ummani ta shigo ɗakin ta gani.
Tun daga wannan ranar kuma shikenan sai Yaya Nazifi ya ɗauke ƙafa daga gidanmu, zuwa gaida Kaka ma da ya saba duk ya daina, kowa kuma sai cigiyarsa yake yi a gidanmu, da an tashi sai a tambaye ni, nima sai na rasa amsar da zan ke ba su. Abbaa yake cewa ƙila ko yanayin kasuwar tasu ne don ranar nan yaje can wajensa sun gaisa, Wata rana ma sai Yaya Al'amin ya ce mana ai sun haɗu can shagon yake ya faɗa masa yanzu ba ya samun lokaci shiyasa bai leƙowa, amma ya gaidar masa da kowa.
Ni dai duk sai na takura kullum cikin tunani, kawai abin da zuciyata ta gama yankewa shine zan sanarwa da su Abbaa a mayarwa da Salim kuɗinsa, domin a kaf nazarin da na zauna nayi Salim shine zai yanke alaƙata da Yaya Nazifi, ni kuma ko kusa bana son abunda zai raba zumuncinmu domin kallo ɗaya na ke masa da yayyena maza waɗanda muka fito ciki ɗaya, don haka zan sanarwa da Salim tun wuri Yaya Nazifi, idan yaga zai iya ɗaukar alaƙarmu da shi ko bayan aure shikenan, idan bai iyawa to ni bai isa ya raba ni da shi ba.
Bayan watanni sai ga Salim ya zo gidanmu, ranar da ƙyar Abbaa ya amince na fita wajensa domin cewa yay ai ba haka aka yi da shi ba, yanda aka yi ko da zai fara zuwa muna gaisawa sai nayi candy tukunna, Abbaa yay ta faɗa sosai yana cewa shi baya son irin haka dalilin da yasa yaƙi karɓar kuɗinsa kenan amma Kaka ya matsa. Ranar kuwa na sami damar nunawa Salim duk wata shaidar da zai fahimci ba na sonsa ko kaɗan balle sha'awar zaman aure da shi, ban fito da baki na faɗa masa cewa bana sonsa ba, amma in dai shi me hankali ne zai gane inda na dosa, haka ya zo da manyan ledojinsa na sahad store guda biyu amma naƙi karɓa.
Kuma ban san ya akai ba bayan kwana biyu da zuwan nasa sai Ummani ke ce min Iyayen Salim sun zo sun karɓi kuɗinsu, wai shi yana so yay aure yanzu don haka idan ni matarsa ce komin daɗewa zai mallake ni amma a yanzu ya samu wata yarinyar da iyayenta suka shirya aurar da ita.
Ranar kamar nayi me don farin ciki, dama ni har ga Allah ko ba don Yaya ba zan aure shi ne kawai saboda zaɓin mahaifina. Washe gari da muka je makaranta Safiyya ƙememe taƙi kula ni, na damu da fushinta sosai, kuma ko da na takura da roƙonta akan me na mata sai tace bata yi zaton zanƙi wani ɗan uwanta ba, na ce ai ba ƙinsa nayi ba shi yace ya sami wata matar, tace ƙarya ne dama akan me ba zai ce haka ba tunda na nuna masa bana ƙaunarsa. haka dai tayi ta maganganun rashin jin daɗin abin da nayi, tace kuma ta san ba kowa ne sila ba sai Yaya Nazifi don haka wallahi ta tsane shi, ba don ya shigo rayuwata ba tana da tabbacin babu dalilin da zai sa in ƙi Yayanta ko don amintar da ke tsakaninmu, ta san zan so shi ko saboda ita.
Ni dai nayi ta bata haƙuri da ƙoƙarin fahimtar da ita amma taƙi saurare na sam, har da cewa ni munafuka ce dama can son Nazifin na ke yi kuma ba zan burgeta ba sai na aure shi. Sai ma ta bani dariya, ni dai abin da na sani tsakanina da Allah bayan son ƴan uwantaka da nake masa bana masa irin son da suke tunani, amma kowa ya gagara fahimtata, sun kasa ganewa cewa Allah ne ya haɗa jinina da shi, ranar ko da aka tashi makaranta ƙin tsaya ni tayi tai tafiyarta, ni kuma tafiyar nata ma sai yay min daɗi domin kuwa ina son zuwa shagon Yaya Nazifi sai dai in har da ita ban san ya zan yi na je ba.
Na hau adaidaita sahu ya kai ni Jakara kasuwa, da tambaya na je har Shagon Yaya, lokacin yana alwalar azahar na isa ƙofar shagon, tun kallo ɗaya da yay min bai ƙara ba ya ci gaba da alwalarsa, sai dai na san ko bai faɗa ba yay mamakin zuwan nawa domin naga hakan a ƙwayar idonsa a kallon farko da yay min. Ina tsaye gabansa har ya kammala alwalar, ya miƙe ya shiga ciki ya bar ni tsaye, ina jiyosa yana cewa da yaran shagon da suke tare su ɗan ba shi aron wajen yay baƙuwa, sai da suka fito dukansu kana yay min wani duba da cewa.
"Bismillah". Na taka a hankali zuwa ciki, yay min nuni da wata kujerar katako na zauna, yana warware hannun rigarsa da ya naɗe ya ce,"Zan je masallaci ina dawowa".
Ina ta kallonsa dai ban ce komai ba ya fita ya turo ƙofan shagon, sai naga duk ya faɗa idanunsa sun yi loko kamar ma yay jinya. Ina zaune shiru ni ɗaya ina ta kallon kayayyakin shagon, ma sha Allah akwai kaya sosai kuma shagon babba ne da alama ana ciniki ba kaɗan ba. Bayan wasu mintuna ya dawo hanunsa da leda baƙa, ya aje kan glass ɗin gabana yana cewa.
"Ga lemu. Akwai pure water a ciki ko za ki alwala". Ya faɗa yana miƙo min wani botiki gabana, a ciki nayi alwalar ya shimfiɗa min sallaya daga ciki nayi sallar, sai yace na zauna anan ba sai na dawo bakin ƙofa ba saboda masu wucewa. Ni dai duk bana jin daɗi saboda rashin sakin fuskarsa, ya kuma nuna bai murna da zuwan nawa.
Nayi shiru shi kuma yana ta karatun ƙur'aninsa, yana cikin yi kuma wata mata ta shigo siyan kaya, bayan ya sallameta ne murya can ƙasan maƙoshi na kira sunansa. Ido ya ɗora akaina ba tare da ya amsa ba, idona ya kawo ruwa ina cewa,"Yaya laifin me na maka?".
Sai ya bagarar da zancen nawa da cewa,"Bamu gaisa ba ma".
"Na gaidaka ai amma sai ka nuna kamar baka ji ba".
"Ki yi haƙuri ban ji ba. Ya su Ummani?". "Suna lafiya. Ya kasuwa?".
"Kasuwa Alhamdulillah, ga shago nan yau kin gani, sai ai mana adu'a". "Allah ya bada sa'a Yayana".
"Amin na gode ƙanwata. daga makaranta kika biyo nan?". Na ɗaga masa kai ya ce,"To me yasa?".
"Kawai na zo na ganka ne, ka daina zuwa gidanmu gaba ɗaya".
Sai ya shafo gashinsa yana cewa,"gaba ɗaya babu wani lokaci ne yanzu amma in sha Allahu ina nan tafe, zan samu wannan lahadin ma in zo ki faɗawa Ummani".
Nayi shiru ban ce komai ba. Sai kuma ya ce,"Ƙanwata akwai damuwa ne? Na ga yanayin na ki wani iri".
"Kaima Yaya naga duk ka rame, rashin lafiya ka yi?".
Fuskarsa ta murmusa yana kallona sosai kafin ya ce,"To ƙila ko don kin jima ba ki ganni ba ne, amma ni da na ke jina ma kamar zan fashe saboda ƙiba, yanzu hankali ya kwanta an sami sana'ar yi, mutane basa ta surutun kana zaman banza ba, haka gida ma kullum ana samun wadatuwa da abinci".
Murmushi nayi da sautinsa ya fita kaɗan na ce,"Alhamdulillah Allah ƙara rufa asiri. Ai dama Yaya na faɗa maka komai zai wuce ya zama kamar ba'ai ba. Kuma Yaya kace kayi ƙiba, kalla fa wuyanka yanda ya ƙara zugewa, wannan sai dai karyewa ba fashewa ba kam".
Hularsa ya cillo min yana faɗin,"Za ki fara tsokanar tawa ko".
Kawai sai na tsinci jin daɗi a raina saboda yanda naga fuskarsa ta washe da dariya, ya miƙe yana cewa,"Tashi to na raka ki kar aga kin jima, ko za ki faɗawa Ummanin kin zo?".
Nayi shiru sai ya ƙara cewa,"akwai me wainar fulawa a baya na siyo miki?".
Girgiza masa kai nayi alamun a'a, ji na ke kamar kar na tafi amma haka dole na tashi ina jin kewarsa tana cika ni. Leda ya ɗauko me layi layi shaƙe da kaya ya miƙo min, na karɓa na duba sai naga kayan kwalliya ne a ciki masu yawa da su man shafawa da under skirt, na dube shi cikin jin daɗi ina cewa,"Yaya na waye?".
"Na ki ne, tuntuni na ke ta cewa zan bawa Al'amin ya kawo miki kuma sai bai fiya biyowa ta nan ba. Akwai wata baƙar ledar a ciki wannan na Ummani ne. Wannan kuma ki bawa yaran gidan".
Ya ƙarashe da miƙo min ledar biscuite. Ganin nayi shiru ina kallonsa ya hure min ido da iskar baki. Nayi murmushi ina ta miƙa masa godiya, sai da ya fara fita ya tarar min adaidaita sahu kana ya dawo yace na fito, kuma sai bayan na shiga motar ne yake ce min.
"Ki gaida sirikina, kice inji wani Yayanki na kalen dangi".
Ina murmushi me faɗi kamar dama jiran maganar na ke na ce,"Wanne sirikin? Yaya Al'amin bai faɗa maka maganar ta rushe ba? Yaya babu maganar aurena akan kowa yanzu".
Sai naga ya waro ido yana kallona da mamaki sosai bayyane a fuskarsa, haka rashin jin daɗin furucin a ƙwayar idonsa, kafin kuma ya sauke numfashi yace min. "Ki gaida gida". Yana faɗin hakan ya juya ya koma shagonsu ina kallonsa. Bayan kwana biyu na dawo daga makarantar magriba zan shiga gida kawai naji an dakatar da ni, da mamakina kuma Hamisu ne abokin Yaya Nazifi, muka gaisa da shi yana ce min wurina ya zo zamu yi magana amma in shiga gida in fara sanarwa tukunna.
Na shiga gida na sanar da Ummani, tace to nayi sauri kar Abbaa ya dawo ya tarar da ni naja mata faɗa. Batun da Hamisu ya zo min da shi yay matuƙar girgiza ni har na kasa tantance ma wanne irin abu naji a tare da ni, wai faɗa min yake Yaya Nazifi yana sona kuma har jinya yay akaina, ya rasa ta yanda zai faɗa min ne tuntuni har wani yayi masa shigar sauri. Har dalilin janyewar da yay min duk sai da ya faɗa min wai saboda kar ya zama ya haddasa fitina don ya lura akansa zan iya cewa na haƙura da auren wancan iyayena kuma ba za su ji daɗi ba, shima kuma ba zai juri ganina da wani ba, amma tabbas yana tsananin sona kuma da gaske aurena zai yi duk da bai san ya zan karɓi maganar ba, amma idan na amincewa soyayyarsa yana roƙon da na basa damar gabatar da soyayyarsa kafin wani ya ƙara riga shi.
Lokacin da Hamisu ya gama isar min da duk saƙon Nazifi ban iya cewa da shi komai ba na koma gida. Har raina ban ji daɗin batun da ya zo min da shi ba, ban kuma taɓa tsammanin wannan maganar daga bakin Nazifi ba, hasali ni ban taɓa hasaso shi matsayin wanda zamu yi soyayya ba balle aure. Kawai sai naji ina jin haushinsa sosai, amma wataƙila yana so ya yanke alaƙarmu ne kwatakwata shiyasa ya ɓullo da maganar soyayya tsakaninmu, ni soyayyar Yaya da Ƙanwa na ke masa kuma ita zan ci gaba da masa, ba irin wadda yake nema a yanzu ba soyayyar saurayi da budurwa.