Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 4

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 4

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 4: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 4. Sai dai me duk yanda na so na ƙyamaci wannan batun da Yaya Nazifi…

4,457 words

Sai dai me duk yanda na so na ƙyamaci wannan batun da Yaya Nazifi ya zo min da shi abun sai ya faskara, Saboda yanda Yaya Nazifi ya nace ya dage wajen cusa min soyayyarsa, ya koma kusanta kansa da ni fiye da baya, shine rakani makaranta da ɗauko ni, kullum yana ƙofar gidanmu, a da idan ina farin ciki da ganinsa a gidanmu yanzu duk ba na yi, ina ta kaucewa faɗawa tarkon soyayyarsa amma sai da ya san yacca yay ram da ni a tarkon soyayyarsa domin yau da gobe tafi gaban wasa. Ba zan ce ba, kuma ban san taya ba, lokaci ɗaya, rana ɗaya cikin lokaci ba mai tsayi ba na aminta da soyayyarsa, Soyayya me ƙarfin gaske ta ƙullu tsakaninmu, Wani irin soyayya yake muna min tsaftatattciya, Kulawarsa, ɗawainiyarsa da gudunmawarsa akaina suka ƙara ninkuwa, ya maida ni ƴar gata a cikin ƴan mata, soyayya mukewa juna me tsanani da har muke ganin ba zamu iya rayuwa ba tare da juna ba.

Kuma ba tare da ɓata lokaci ba iyaye suka shiga maganarmu don Yaya kasa haƙuri yay yace gwara yay magana a sabon matsayinsa kafin wani ya ƙara zuwa da neman aurena, don yana tsoron sharrin samarin da ke ta kawo min hari. Ranar da ƙyar na iya sanarwa da Umman su Hindatu ta faɗawa Ummani Yaya Nazifi na so ya turo iyayensa ayi maganar aurenmu. Ranar kuwa ji nayi tamkar na buɗe ƙasa na shige ciki saboda yanda suka hau tsokanata, wai dama can ai sun san soyayya muke yi muke ta ƙaryata kanmu, Ummani ma tayi ta min tsiya kunya duk ta kamani na kulle kaina a ɗaki.

Ranar Asabar Malam wato mahaifin Yaya Nazifi da ƴan uwansa suka zo suka nema masa aurena. Kamar yanda Abbaa yaywa magaban Salim bayani haka suma yay musu bayani kan cewar karatu shine burinsu akaina a yanzu, don haka ba zasu ce ba zasu bawa Nazifi ƴarsu ba amma sai dai ba yanzu za su aurar da ni ba, idan zai iya jiran lokaci to, da yake da Yaya Nazifin aka zo ya amsa da cewar ya amince shima dama ba maganar aure yake yanzu ba tunda akwai tsare tsaren abubuwa da yake yi, sai dai yana so Abbaa yay masa alfarma ya bada kuɗin aure yanzu saboda wasu ƴan dalilai. Lamari na babbar magana su Abbaa suka fahimci nufinsa suma suka ga dacewar bayar da kuɗin auren, don haka cikin sati guda kuwa Yaya Nazifi ya kawo kuɗin aure naira dubu ashirin.

Tsakanin Ummani da Abbaa ban san wanda yafi wani farin ciki da batun auren ba, domin na faɗa muku babu wasu iyaye da za su kasa yiwa ƴarsu kwaɗayin Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin mijin aure ba, haka babu wata budurwa da ba zata so ta mallake shi ba in har ba burin auren me kuɗi ne kawai a ranta ba. Tafiya tayi tafiya soyayyarmu na ƙara ƙarfi, ina jin duk duniya babu wanda zai iya min irin wannan soyayyar tasa, haka ina ganin na gama dacewa da samun mijin aure. muna gabanin fara zana jarabawar neco sai Yaya ya fara matsamin lamba akan zancen shi gaskiya muyi aure, shi kawai zai fi samun kwanciyar hankali da natsuwa idan ina gidansa, shi yana buƙatar aure yanzu kam nan ba da daɗewa ba, karatu ne dai yay min alƙawarin ba zai tauyeni ba zai barni har in ga ƙarshen biro da takarda.

Raina ya ɓaci da wannan maganar tasa, domin ba haka suka yi da iyayena ba, an faɗa masa an jadda masa sai na kusa kammala karatun jami'a a ƙalla nan da shekara biyar masu zuwa, ya kuma ce ya amince shima yafi so sai ya mallaki wurin zama, amma shine yanzu ko shekara ba'a gama rufawa da magana ba zai fara wannan zancen saboda yaga da kuɗin aurensa akaina. Dalilin hakan ya janyo saɓani mai girma tsakaninmu, muka dinƙa rigima da shi rigimar da bamu taɓa yi ba, na nuna masa fushina da bai taɓa sanina da shi ba tsawon tarayyarmu, haka shima naga fushinsa da ban taɓa ganinsa da shi ba a sanin da na masa.

Ni dai na tsaya masa akan bakana na cewan ba zan taɓa iya tunkarar iyayena da maganar aure yanzu ba, nima ina so in faranta musu in saka musu da irin ɗawainiyar da suka yi da ni a rayuwa, kuma karatun da zan yi na likita ba ƙaramin karatu ba ne don haka damata yanzu ce, yanzu ne na ke da damar natsuwa in mayar da hankali da ban da ɗawainiyar kowa akaina, don haka yay haƙuri kawai zuwa lokacin da aka ɗiba, yama rufe maganar aure ba yanzu ba kam, shekara biyar ne kamar yanzu zai ga lokacin ya zo, kafin nan in sha Allahu ya mallaki gidan kansa ma.

Amma yanzu idan yace aure ƙarshen shekara ina zai kai batun neman gidan zama da haɗa lefe da sauran hidindimu, ɗawainiyar gida bayan aure da tunanin kuɗin gidan haya da ta yara. Duk yanda na so in fahimtar da shi sam yaƙi fahimtata, yaƙi jin shawarar da na ke ta ba shi akan ko da fili ne ya fara mallaka tukunna, amma ina sai yay min mummunar fahimta ma, yake ganin kamar na daina sonsa ne, har yake cewa Safiyya ce take neman hure min kunne saboda ɗan uwanta me kuɗi yana sona, shi kuma bai da kuɗi kuma shi ɗan talakawa ne, ya kama maganganun ashe na raina nemansa, duk irin jajircewar da yake akan sana'arsa shine na ke ganin ba zai iya riƙe ni ba, shi ariziƙi ai na Allah ne, kuma shi dama fatansa Allah ya rufa masa asiri yafi ƙarfin ci da sha, kuma idan har akan ina ganin ba zai iya riƙe ni ba ne to naci amanar soyayyarmu.

Haka muka ta fafatawa da shi tsawon lokaci, kullum cikin rigima muke da shi akan fa sai an saka rana ƙarshen shekara. da yaga na cije na kafe sai ya koma sauke murya yana lallashina, ya dinƙa roƙona yana min daɗin baki, ƙarshe kuma sai ya fara faɗa min shi yana da matsala ne, yana gudun kar ya faɗa wani halin, kaza da kaza dai, da wannan ya shawo kaina har na yarda na amince don nima a gaskiya ina jin idan ba shi ba ba zan iya rayuwar aure da wani ba.

Ranar da najewa Ummani da maganar Yaya Nazifi yace yana so a saka rana nan da ƙarshen shekara, kasa cewa da ni komai tayi sai da Abbaa ya dawo ta faɗa masa, ai kuwa raina yay mugun ɓaci, na sha kuka iya kuka saboda irin faɗan da Abbaa ya dinƙa min, yana cewa wato soyayya har tayi tasirin da zata sa karon farko in fara tirjiya da maganarsu, to idan yaga dama sai ya mayar musu da kuɗin na su auren Nazifin ma ba zan ba. Sosai Abbaa ya ɗauki fushi da ni kamar yanda ya ɗauki mugun zafi da maganar. hankalina ya tashi, shi kuma Yaya Nazifi idan naje masa da batun halin da ake ciki shima sai ya ƙara dagula min lissafi, na rasa ina zan saka raina, haka har sai da yasa na tada hankali a gida akan ni dai nan da ƙarshen shekara na ke so ai aurena, har ma na kai ƙarar Abbaa wurin Baba Tijjani lokacin kuwa ba ya gari.

Da wannan Abbaa ya fusata kuma don ya ƙure Yaya Nazifi sai ya ce shi kuma ya tsayar da auren nan da wata guda, idan har ya wuce haka to ba zai kaffara ba ya fasa bawa Nazifi ƴarsa, don haka nan da sati biyu ciff ya kawo kayan lefe. Wannan hukuncin na Abbaa duk ya ɗaga hankalinmu, musamman ma daga ni domin na san shikenan na rasa Yaya Nazifi, don kuwa a halin da ake ciki yanzu Yaya Nazifi bai da wasu kuɗi da ya aje da zai iya haɗa lefe balle akai ga tanadin wurin zama duk cikin wata guda.

Ana haka kuwa yazo min da zancen mahaifiyarsa ta ba shi aron gidanta da ta zuba ƴan haya a ciki, sai dai akwai gyare gyare a gidan sosai don ko masai sai an ƙara haƙansa, ban da gyaransa rufin kwano da su simintin ƙasa da duk ya farfashe. Amma yanzu dai zai yi iya duk ƙoƙarinsa yaga ya haɗa lefen kafin sati biyun da Abbaa ya yanke, in ya so ko wurin Hamisu ne sai ya ari kuɗin, Ranar yay ta bani haƙuri da lallashina akan in kwantar da hankalina komai zai zo cikin sauƙi, kuma in sha Allahu ko don hallacin da na masa ba zai bani kunya ba.... _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar

[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR05FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Tun daga ranar da Nazifi ya buƙaci da na siyar masa da kwanana ya ɗauke ƙafarsa daga gare ni daga inda na ke, rawar ƙafa kawai yake a wurin amaryarsa, sai shan soyayyarsu suke hankali kwance, wani abun ma na lura da gayya yake min shi, yanda yake faman rawan kai ka rantse aurensa na farko kenan. Sam ba ya ko waiwayena balle tunanin sauke hakkina, bai damu da ya lafiyata take ba haka bai damu da dukkan wata buƙata tawa ba, ya barni kawai da ɗawainiyar gidansa, yaransa da ɗawainiyar mahaifiyarsa da ke mini kallon baiwa, wacca kowanne kalar kashi ta kwaso ni take watsawa, gaba ɗayansu basu ko tunawa da hakkin cutar da ni da suke yi.

Haka har aka cika wata guda ɗin da na ɗibar masa amma mutumin nan bai yi aiki da hankali da tunanin ba, bama za'a sa ilimi ba don yanzu ni bana saka shi sahun masu ilimi kam, ranar da naje ɗaki na same shi ya na ta faman ɓata rai da cin magani saboda ya baro ɓangaren Amaryarsa, abincin ma da na kai sai ce yayi ai ya ƙoshi, ni dai ina ta bin hanyar da zata sa ba zamu samu saɓani ba amma shi neman hanyar ayi tsiya kawai yake, ni kuma ganin hakan kawai na bar masa ɗakinsa na koma nawa, tun sannan na fita sabgarsa na ce idan anyi duniya don manzon Allah bani ƙara zuwa inda yake sai idan ya neme ni, ashe shi hakan ma yake so don bai ko nuna bi ta kaina ba, ganin na fita harkarsa ya tattara ya koma wurin amaryarsa gaba ɗaya, maganar dole idan ta kama zai aiko min message ne kawai, ni kuma idan ina buƙatar abu mahaifiyarsa na ke faɗawa wanda kafin a bani ma ko a faɗa masa sai na sha jiki.

Wannan abubuwa suka ƙara gwada min da gaske Nazifi ba ya buƙatata a rayuwarsa sam, zaman dole kawai yake da ni, wanda kuma na ke ta nazari da tunanin dolen da ta gagare shi fitowa fili yace da ni ya sallama auranmu, domin kuwa yanda ya gaji da zama da ni haka nima na fishi gajiya da zama da shi.

Gaba ɗaya ya mayarshe ni wata banza shara a cikin gidan, ya gama tsinka darajata da mutuncina a wurin matarsa, Munafukin miji wama ya san me ya gaggaya mata akaina, tun da ta kai ta kawo yanzu tsakanina da ita ma kallon banza ne musamman idan ta fita aiki ta dawo, da zarar ta ganni sai kallon raini da ƙasƙanci saboda mijinta ya nuna mata ni ɗin ba komai ba ce a gare shi, don haka take wani nuna isa da gadara matsayinta na wadda miji yake so yake bawa kulawarsa, yake kuma ji da ita.

Ni dai basa ko gabana tuni na ɗauke ido akan su, harkokin gabana kawai na ke yi. Abinci ne zan girki iya cikina da na mahaifiyarsa da yara, shi da ita kuwa dama takeaway yake musu ne oho ni dai ya min text yace na bar girki da su. Kuma tuni na yiwa kaina karatun tanatsu, na kira Ummani muka tattauna akan shawarar da na yanke, ya kamata na kama sana'a wacce nasan in har Allah ya saka min albarka da ganin ina samu ma kaɗai Nazifi ya rage wulaƙanta ni, yanzun ma ai har da ganin cewa shi yake min komai shiyasa, kuma duk abin da na ke buƙata sai na jira shi dole kuwa inga walaƙanci kala daban daban.

Saboda haka na tattara duk gwala gwalaina guda uku muka je kasuwa aka auna aka siyar da tsada sosai, ina batun saro kaya irin su atamfofi da danginsu Maman Yasmin tace a'a tunda kuɗin har za su kai a siya fili to gwara a siya min filin na ajiye shi zuwa wani lokaci sai a ɗaga a siyar tunda ba kuɗin gini gare ni balle na gina, amma wannan zan ta iya juyawa da ribar ma sai in dinga ƙara siyan ƙasa ina ajewa, amma idan nace kasuwancin cikin gida zan yi to Nazifi zai iya min muguntar da zai dakusar min da shi, wannan kuwa bai ji bai gani ba kuma kar ɗokin soyayya wataran tasa nayi suɓutar bakin faɗa masa.

Ai kuwa da wannan shawarartata ne Ummani tasa Yaya Al'amin ya samo dillali aka siya min wani fili can unguwar rimin auzinawa, da yake can akwai arhar filaye, tace da shi ko Abbaa kar ya bari ya sani zata faɗa masa idan lokacin hakan yayi, nima kuma naja bakina nayi shiru ko da wasa kar Nazifi ya san da zancen siyar da gwala gwalai balle siyan fili, takardun filin kuma zata ajiye min su a wajenta.

Ranar da farin cikina na dawo gida, ko babu komai yanzu ina da kadara a ƙasa, karatuna kuma da ya tauyen hakkin ci gaba, ya kuma hana ni kuɗaɗen da mahaifina ya bani domin biyan kuɗin makaranta yaje don kansa Allah ai ba azzalumin bawansa ba ne. Sai dai na samu ajin online da ake koyar da turanci da kuma ajin biology, nayi register na shiga domin hakan zai fiye min alfanu, gwara na nemi ilim ta waya akan ya zama kullum sai dai na saka data na hau nayi chart da kalle kallen tictok a banza a wofi ni ban ƙaru da komai ba, ga shi kuma koyawar da ake babu mugunta darasi ake sosai in har ka natsu ka mayar da hankali ba zaka ce a online ne ka ke karatu ba, jinka zaka yi tamkar a cikin makaranta zaune a aji gaban Malami.

Yau ina ɗaki da yamma zaune ni da Rumana, yanzu kam ta zama ƴar ɗakina, Atika kuma ta zama ƴar ɗakin Zahra'u. Ganin lokaci na miƙe na fita don zuwa haɗa abun shan ruwa, ina sakkowa Nazifi na hayowa shima wanda ya dawo daga kasuwa. Nayi kamar ban gansa ba don tuni na ƙuduri aniyar zai sha mamakina, tabbas ko magana ce idan ba shi yay min ba ba zan masa ba, gaisuwa ma bana so ta haɗamu. Hanya na ba shi don ya wuce sai na ga ya tsaya, ganin bai da niyyar wucewa naci gaba da takawa ina sauka ya dakatar da ni.

"Me ke damunki ne Sa'ida? Za ki ce ba ki ganni ba ne da sannu da dawowa zata gagara fitowa daga bakin ki, kina nuna tamkar ni ba mijinki ba ne".

"To Nazifi sannu da zuwana zata ƙare ka da wani abu ne da ka damu da ita? Ko ba'a faɗa maka ne a inda ka nufa".

"Ni kike faɗawa haka?".

Ya faɗa yana ɗaga murya sama, ni ko ganin zai min hargowa nayi masa banza na wuce na barshi anan. Bai san ni baƙin cikin ganinsa ma nayi ba da har yake kiran nayi masa sannu da zuwa, ni kuwa yanzu ina yaga wannan darajar a idona, ai ana zaman jinginar aure ne kawai tsakanina da shi, kuma ban fidda ran zuwan lokacin da zai ce ya raba aurenmu ba.

Har na shiga kitchen ina jin yacca yake bina da kallo, dama kunu na sakko na dama saboda ina azumi, kuma ma sai naji ina sha'awar awara don haka na koma sama na ɗauko kuɗi na dawo na bawa ƴar aikin Zahra'u ta siyo min ɗanyar awara a waje. Har aka sha ruwa ina kitchen ina aiki sai sauri na ke yi.

Motsin shigowa naji na ɗago na waiga kaina ina kallon in da Zahra'u ke tsaye, har zan ɗauke kai sai kuma naga tana lalube, ban san me take nema ba, ban ma san me ya shigo da ita kitchen ɗin nawa ba, tunda tuni aka raba mana kitchen tun sanda ta nuna bata so mu haɗa girki, wai ita ba girkin kowa take ci ba, kuma in aka ce za'a haɗa girki ita zata takura da yawa. Sai ya zauna ya sauya tsari yace kowacce ta dinga girkinta amma nauyin ciyar da duk wanda yake zaune a gidan da duk wani ɗan uwansa da zai zo ya rataya a wuyana ne.

Ba tashin hankali na ke nema ba kuma ba abu ne da zan soma shi sabo ba na amince ba tare da nuna masa ko rashin jin daɗin hakan ba, lokaci ne dai yana nan tafe da zai gane gaskiya kuma Allah ya saka min.

"kina neman wani abu ne?".

Na tambayeta a mutunce, shiru tayi ta ci gaba da binciken durowa, na bita da kallon mamaki ina ajiye kofin hannuna da na ɗaga zan sha lemo. Kaf dai kitchen ɗin idan ba shi ya faɗa mata cewa duk kayan ciki nasa ba ne to banga wani abu da yake mallakinta a ciki ba da har ta zo nemansa tana min bincike haka. Na buɗe baki na ƙara cewa da ita,"Ina magana kin yi banza da ni. Ko kin mance ba ki da hurumi da nan ɗin?".

"Ba sai kin tuna min ba ai na sani, Idan ban da mallaki anan ɗin ai ba zaki ganni a ciki ba, ko kin manta kafin sama min nawa da yafi wannan girma da ƙawatuwa kayan kitchen ɗina sun haɗu da naki, so ina son bincikar abin da aka iya ɓoyewa ne".

Juyawa nayi ban saurareta ba don na fahimci neman tashin hankali take da ni, ni kuma bata isa ba tayi kaɗan, ko kusa ba zan taɓa sauraron rigimarta ba. Da farko ta nuna kamar zamu zauna lafiya da ita, tun da har hira muke zama muyi a falo, ayi wasa da dariya cikin mutunci da girmama juna, har ma a lokacin take cewa taga ina fama da halin Fati saboda haka zata gyara mana zamanta don ita gaskiya bata da haƙuri da shiru irina, ni a lokacin murmushi kawai nayi ban ce mata komai ba. Idan gari ya waye taji shiru ban fito ba da kanta take leƙowa ɗakina mu gaisa, to amma lokaci ɗaya sai naga ta fara sauyawa, muna ƴar hy hy da ita kafin kuma ta sauya gaba ɗaya wanda magana ma idan nayi mata bata ɗaga kai ta kalle ni, bar ta dai da min kallon wulaƙanci.

Na kammala duk abin da zan yi na fita na barta a kitchen ɗin. Bayan na idar da sallar magriba ina biyawa Rumana karatu sai naji an murɗa ƙofa, da tsananin mamaki na ke kallon Nazifi da ke shigowa, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai akansa, rabonsa da sanyo ƙafa cikin ɗakina har na mance wallahi. Rumana ta yi masa sannu da zuwa tare da gaida shi, nima kuma yaci darajar yarinyar na buɗi baki nace masa.

"An dawo lafiya?".

Bai amsa min ba sai ce yay da Rumana,"Je ki ɗakin ku zan yi magana da Antynki".

Kallona ta tsaya yi don yarinyar tuni ta fara tausayina a gidan, gyaɗa mata kai nayi kana ta miƙe ta fita tana ta waigena, da alama dai tana ji a jikinta ba mutunci ya kawo uban ruƙon nata ba. Tsaye yay min aka hannaye zube cikin aljihu, jirana yake na masa magana oho dai, ni ko na ci gaba da abin da na ke nayi kamar ma ban san yana cikin ɗakin ba, sai can ya nemi wuri ya zauna yana kiran sunana.

Ɗago ido kawai nayi na dube shi ban amsa ba, ya numfasa kana yace,"Wai ke me yake damun ki ne?".

"Me ko yake damuna, lafiyata ƙalau ni kam. Yanzu dai me ke tafe da kai?".

Kallon mamaki yay min kafin ya ce,"Tambayata kike hakan?". Sai kuma ya kama ɗaga murya yana faɗin,"Sa'ida so kike sai na fito na miki bayanin irin wulaƙancin da kike min ne? Ina matsayin mijinki wanda aljannarki ke tafin ƙafarsa amma ba ki ganina da daraja balle ki mutunta ni, sai in wuce ki wuce ba zaki buɗi baki kiyi min magana ba, yaushe rabonki da zuwa ɗakina? Yaushe rabonki da shiga ki gyara min makwanci? Yaushe rabon da ki dafa abinci ki ba ni? Yaushe rabonki da bani hakkina? Yaushe rabonki da gaishe da ni? Yaushe rabon da na fita na dawo kiyi min sannu da zuwa? Kina abu kamar wadda ke zaman kanta a cikin gidan, ko kina so ki faɗa min ke kika auro ni?".

Ya kai aya ya kalle ni muka haɗa ido, muryarsa ta ƙara fitowa da ɓacin rai wajen cewa,"Ina magana kin kafe ni da ido, to na gaji da wannan halin rashin mutuncin da kika tsira, idan kuma hakan kika zaɓarwa kan ki ni ban da matsala ban da damuwa tunda ba ke kaɗai na ke aure ba, a yanzu ina da wadda ta fiki komai, wacca tayi miki tseren da ba za ki taɓa iya taddota ba, Zahra'u ta fiki wayewa, ta fika iya kwalliya, ta fiki sanin yanda zata tarairayi miji da ba shi kulawa, ta fiki iya soyayya, ta fiki iya gado haka kuma ta fiki ɗanɗano, saboda haka Sa'ida kar kiyi tunanin wannan girman kan da kika ɗorawa kan ki zai dame ni domin da ke da babu ɗaya a wurina".

Rasa abin ce masa nayi, kallonsa na ke babu ko ƙifce, haka kawai sai na fashe da kukan da na jima ban yi ba, kuka na ke sosai kafin na fara ce masa. "Nazifi ni kake faɗawa waɗannan maganganun?".

Na miƙe jikina na karkarwa na ke cewa,"Ban san me na maka ba ka tsane ni? Amma kuskurena ne da na rusa farin cikin iyayena na zaɓeka, ban da haka da baka aje ni cikin gidanka kana gana mun azaba ba, da baka kalle ni kana gaggaya min magana irin haka ba, haba! me na maka a rayuwar nan Nazifi? Me nayi maka da na ke fuskantar tozarci irin haka daga gare ka?...Kuma ma idan har da gaske ni da babu ɗaya ne a wurinka menene na zuwa kayi ƙorafi akan hanyar da na zaɓa wadda na ke jin sanyi cikin raina, Mene damuwarka da rashin kulaka da na ke yi ɗin ehh Nazifi? Mene damuwarka na ce?...".

Ni gaba ɗaya ma sai na rasa me zan ci gaba da cewa, nema na ke kawai na rikice, banɗaki na nufa zan shige ciki domin Allah ya gani bana son ganinsa a gabana, ruƙo hannuna yayi ya janyo ni na dawo gabansa yana zuba idanunsa akan fuskata, ƙasa da murya yace,"Kin san me ya kawo ni wajen ki?".

Hawaye ne kawai na ke ban iya ce masa komai ba, sai ya ƙara cewa,"Idan kina tunanin na zo karɓar wata tsiya daga jikinki ne to kinyi kuskure. So idan kin gama kukan Zahra'u na so taci awara da kunu".

Ban san lokacin da nayi masa wani kallo na baka da hankali ba kafin na ce,"Me ya shafe ni da abun da zata ci to?".

Kai tsaye ya maimaita min,"Kunu da Awarar da kika dafa za ki zo ki zubawa Zahra'u tana son ci".

Na ƙwace hannuna daga ruƙon da yay min, ina goge hawaye na ce,"Saboda ita ta dafa? Ko kuma saboda kai me karɓa mata ɗin ina tsoronka?".

Buɗar bakinsa zai magana aka turo ƙofar ɗakin, muka waiga a tare, Iyam ce ta shigo da kwano tana ce min. "Ke ƴar nan ina kunu da awara da kika dafa? Zubo maza anan Amarya zata ci".

Wani murmushi nayi a ƙasan raina, duk ɗin su na gane inda suka dosa, suna so su faɗa min cewar sun samu ƙaruwa ne wanda na fahimci hakan tuntuni. Zazzafan hawaye ya ƙara sakko min nasa hannu ina gogewa, ta dube ni tana min kallon sama da ƙasa ta ƙara cewa,"Ki bar zagina cikin ranki ki bani abun da na ke tambayarki".

Na ce,"Ai ba da ita na dafa ba Iyam, azumi nayi na dafa iyaka cikina kuma na cinye".

"Iyeee lallai Sa'ida, Dama har za ki dafa abinci a gidan nan ni ba ki bani ba?".

Na saki baki ina kallonta ganin zata min sharri gaban ɗanta na ce,"Akwai wata rana da na hanaki abinci ne Iyam? Wannan awara da kunu ne nayi na shan ruwa kuma azumin nan ni kaɗai nayi".

"Ohh ni ban yi ba kenan ban isa ki dafa komai da ɗana ya siyo ya ajiye ki iya zubawa ki bani ba, da kyau. To yanzu dai ko me za kiyi ki zubo akaiwa Amarya don babu in da za'a je samun na siyarwa yanzu, idan kuma kin cinye ɗin ki fito yanzu kije ki dafa mata wani".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull