Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 5

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 5

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 5: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 5. Nayi murmushi na ce,"Kiyi haƙuri Iyam, amma ko akwai wallahi ba zan…

4,421 words

Nayi murmushi na ce,"Kiyi haƙuri Iyam, amma ko akwai wallahi ba zan bayar ba, haka ko da babu wallahi ba zan dafa saboda ita ba. Jikin aiki na fita? Ko kuma iya dafawar ne bata yi ba da ita ba zata girkawa kanta ba? Ita har mene ma na sha'awar abun hannun kishiya da zata taro jama'a su zo su ƙwatar mata? To kunu da awara ne nayi nawa ne babu kuma wanda zan bawa a cikin gidan nan wallahi...".

Maganata ta katse ganin Nazifi ya ɗaga hannu zai sauke min mari, Iyam tayi saurin dakatar da shi da cewa,"A'a ƙyaleta Shalele, ai ba komai take ba sai baƙin cikin Amarya ta samu ciki ita ta nan sai ci da kasayarwa, daga yarinya ta samu ciki kuma sai ki hau baƙin ciki da hassada".

Ina hawaye na ƙunar zuciya sosai na ce,"Ni kuwa akan me zan yi baƙin ciki da abun da Allah ne ke bayarwa, ina da ilimi kuma ina aiki da shi don haka wallahi ko kusa don wata ta zo a bayana ta samu ciki ba zai dame ni ba...Kiyi hakuri ba da ke nake ba amma baƙin ciki ai sai wurin wanda bai san alƙur'ani da hadisi ba, ni kuwa na san kamar yanda Allah ya bawa wasu ariziƙi a dare ɗaya haka nima ciki idan ina da rabo zai ba ni, Allah kaɗai ya san me tsara min a rayuwata".

Shigowar Atika yasa nayi shiru, ta dubi Iyam tana ce mata,"Anty Amarya na kuka wai cikinta".

Iyam ta fita da sauri tana cewa,"Innalillahi, wato mace dai idan ba taɓa samun ciki tayi ba bata da imanin tausayawa me laulayi, to Allah ne ma ya san manufar jaki da bai ba shi ƙaho ba".

Ta na fita na wurgawa Nazifi banzan kallo na ce,"Kaima ka samu damar fice min daga ɗaki".

Yatsa ya daga yana nuna ni da shi ya ce,"Na san ba komai ya ba ki lasisin iya buɗe baki ki farfaɗi abin da kika ga dama ba illa wannan munafukar ƙawar taki da ke baki shawara. To daga yau zan yanke alaƙar ki da ita".

Ina kallonsa kai tsaye na ce,"Safiyya ce tare ka ganmu, haka kuma zaka buga ka barmu, da na rabu da Safiyya gara na rabu da kai Nazifi, domin kuwa ita ba butulu ba ce, Safiyya tafi min kai sau dubun dubata Nazifi Mai Kalwa...Kuma dai ka sani duk lalacewar goma tafi biyar, kafin wancan ni ɗin dai mara ilimin ni ka sama kuma ni ɗin dai silar matsayin da kake fariya da shi a yau".

Yana fita naje na sakawa ƙofar maƙulli, a gefen gado na zube ina fashewa da kuka soai, na jima a haka kafin na kai hannu na ɗauko wayata, yau kam gani na ke gwara na kira Abbaa na faɗa masa dukkan halin da nake ciki, sannan na faɗa masa suyi min haƙuri da uzurin nemarwa kaina mafita, ba zan iya ba, ba zan iya jurar sabon wulaƙanci akan cikin da Zahra'u ta samu ba.

Lambar Abbaa na danna sai bayan da ta fara ringing kuma na shiga tsoron abin da zance masa. Kamar yanda ya saba bai ɗaga kirana sai ta katse kana ya biyo baya. Yanzun ma sai bayan ta yanke kana ya kira. Na saita natsuwata ina ɓoye yanayina a natse nayi sallama, maimakon jin muryan Abbaa sai naji Ummani ta amsa. Kuma jin muryan mahaifiyartawa idona suka ciko da ruwan hawaye.

Ta kira sunana jin nayi shiru, na amsa ina ta ƙoƙarin danne kukan da ke son ƙwace min, saboda ko kusa ba na so ta gane a halin da nake ciki ta shiga damuwa, ni yanzu ɓoye mata komai na ke yi saboda yanda duk taƙi kwantar da hankalinta, kullum tunaninta na inda na ke da halin da nake ciki, har ta kai yanzu sai dai ta sanya abinci a gaba ta kasa ci.

Duk yanda na so ɓoye kukan abun yaci tura, kawai na fashe da kuka saboda na san hakanne kawai zai sa na samu salama, in yisa a kunnen da za'a lallashe ni da kalamai tausasa.

"Ya su hanallah Sa'ida lafiya?". "Ummani ba komai".

"Wanne irin ba komai, haka kawai za kiyi kuka don kiji daɗi, ana haka dama? Ko wani abun farin cikin ne ya same ki?".

Cikin kuka sosai na ke ce mata,"Ummani ni kawai na gaji da zama da Nazifi ne, na gaji Ummani so na ke ya rabu da ni, umarninku na ke nema in ce ya bani takardar sakina".

"Kul kar na ƙara jin wannan furucin a bakinki, idan na ƙara jin kin faɗi haka sai nayi mugun saɓa miki Sa'ida. Ba na ce miki kici gaba da adu'a ba Allah yana sane da ke kuma zai kawo miki mafita".

"Ina ta Adu'a Ummani, ina yi amma kullum babu sauƙi, babu sauyi, Ummani wani sabon shafin ci min mutunci ne ya buɗe saboda Zahra'u na da ciki. Yanzu shikenan da gaske banda rabon haihuwa, matsalar daga ni ne ba zan taɓa haihuwa ba Ummani, shekara takwas da ɗoriya ban taɓa ɓarin wata ba amma ita wata huɗu ta dauki ciki...Ummani ki bar ni na roƙi Nazifi ya sakeni don Allah don Annabi". _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR07FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ "Kwantar da hankalinka babu abin da zai same su kaji. Yanzu shiga ɗakina ka ɗakko wata jarka yaluwa ka kawo min, jiya ne Adamu bai sami kawo rubutun da wuri ba sai bayan ta rufe ƙofa".

Kaina na jingina da bango ina hawaye, ina jiyo su duk tashin hankali yasa ma sun rasa me ya kamata suyi, ita kuma sai kuka take yi sosai, sai can kuma saboda baƙin munafurci da iya kirsa ta shiga cewa da shi. "Derling ban san matsalar cikin nan ba, ni da akwai hali da an ciro Baby haka, in ya takura min ni kaɗai ba damuwa ba ne Derling, ko kuma idan kana wajena duk ba matsala ba ne, amma kar Sa'ida taga kaman da gangan na ke shiga hakkinta, ban san ya zan yi ba Honey".

Tsintar kaina nayi da share hawaye na fita zuciyata na tafarfasa, ina zuwa na kamo hannunsa ina cewa. "Wuce mu je".

Iyam ta tsaya galala tana bin kayan jikina da kallo tace,"Wacce irin fitsara ce wannan zaki fito a haka? Ko kin manta da cewa ina cikin gidan".

Ban bi ta kanta ba na ƙara cewa da shi,"Hubbi magana na ke maka. Ai ciwon nata ya lafa yanzu tun da har ta iya gane tana shiga hakkin wata. So lets go ina so zan koma bacci".

Zai magana na kai hannu na rufe bakinsa, ina kallon yanda ta rumtse ido alamun abun ya bata takaici sai ta kama cewa. "Ke kam kiyi haƙuri Sa'ida ba laifina ba ne, ban da cikin nan haka kawai ai ba zan hana kaina bacci a irin lokacin nan ba, to Babyn ne har ya san Daddynsa tun yana ciki, idan bai kusa duk sai naji yana karkartata ya hana ni sakat".

Wani kallo na watsa mata ina cewa,"Kinga dakata ban nemi jin wani ba'asi daga bakin ki ba. Ciwo ke ya dama, abun da na sani miji a wajena yake kuma ba zai yiwu sai muna tsaka da jin daɗin rayuwarmu ba wani can da bai riga ya zo duniyar ba ya dinga shiga lokacina...".

Wa ni kallon fusata Nazifi yay min yake faɗin,"Keeee ya isheki haka, kar ki ce za ki banzar kishinki akan ɗana, a hakan da kike ganin bai zo duniyar ba to ni yafi min ke, kuma zan fi ba shi lokacina fiye da ke ɗin, idan baccin kike ji akwai wanda ya hana ki ne ki wuce kiyi kayanki mana".

Nima cikin fusata na ce da shi,"Kai ne ake rainawa hankali amma wannan abun da take ƙarya ne wallahi, kai kuma saboda son ɗa ya rufe maka ido ka gagara ka gane...amma ka sani wallahi ba zai yiwu muna tare a dinga zuwa ana katse min bacci ba, ba zai yiwu ta dinga shiga lokacina ba, don haka ka zaɓa ko ka dawwama a wajenta har sanda zata haife maka ɗan naka ko kuma duk lokacin da kake wurina babu ita babu shiga huruminka".

Gigitacciyar ƙara ta sake saki tana dafe mara. Duk su biyun suka yi kanta ita kuma ƴar aikin ta tsaya gefe tana jera mata sannu, can kuma sai ga Innarta da Ƙannenta sun sauko suma suka rufa kanta sai sannu suke jera mata.

Iyam ta dube shi tana faɗin,"Kaga ɗauko maƙullin mota mu wuce asibiti kawai, ai bamu ga ta zama ba, shi dama ciki in ya shiga wata bakwai ai ana iya haifarsa. Bamu san ko Allah ne ya kawo haihuwar yanzu ba. wannan susutacciyar matar taka ma kaɗai ta isa tasa a haihu babu shiri. Ban da rashin imani ma na juya ana zancen ciwo kina ke ina ruwanki, da ike bata san zafin ɗaukar cikin da rainonsa ba. Allah ne ma ya san manufar jaki da bai ba shi ƙaho ba, Allah ya baka matar da zata cika maka gida da iyali tana baƙin ciki da hassada saboda ita bata haihuwar wata ba zata haihu ba, to aniyarki ta koma miki duk baƙin cikinki sai naga jikina jinin Shalele".

A wannan furucin na Iyam kam tuni idanuna suka ƙara tara ruwan hawayen baƙin ciki, wani rauni ya baibaye ni, raina ya kai ƙololuwar ɓaci har na kasa haƙuri sai da na tanka. "Ni ba na baƙin ciki da abin da Allah ne ke bawa bawansa, cutar hassada kuma ban ɗorawa kaina ba don Allah kar ki ƙara alaƙanta ni da ita. Kuma idan hakan da kuke ke da ɗanki kuna ganin daidai ne kuci gaba da zaluntata, Allah yana ji yana gani zai saka min".

Tass naji saukar mari a fuskata, na dafe wurin cikin jin raɗaɗin zafin, Nazifi na nuna ni da yatsa ya ce,"Idan mahaifiyata na magana kina yi sai na yi fatali da ke, ƙarya aka yi akan ki ke ba juyar ba ce, idan kin ji haushi ki ɗauki cikin mana ki haife kiga idan ba'a so ki ba, karo na uku da zan ƙara faɗa miki wallahi da na san ba ki haihuwa Sa'ida ba zan taɓa aurenki ba, juyar banza da wofi kawai".

Ƙurii na masa da ido ina kallonsa, da yanda yake maganganunsa cikin kwanciyar hankali, a duk kalaman da yake faɗa min a baya ba su ƙona min rai ba kamar yanda wannan yay min ba, a maimakon zubar hawaye sai na tsinci murmushin da ban shirya masa ba a fuskata, ban ƙara cewa komai ba na juya na koma ɗaki, da shigowar tawa shima ya shigo ya saka jallabiyarsa tare da ɗaukar maƙullan mota ya fita.

Yana fita na saki marayan kukan da nayi dauriyar riƙewa, jikina rawa kawai yake yi, Allah ya sani yau na ƙara jin na daɗa gajiya da zaman auren Nazifi, tabbas aka ci gaba da tafiya a haka zaciyata zata iya bugawa, wanda a yanzu haka yanda na ke jin jinina yay zafi kamar zan shiɗe haka na ke jina. Wallahi ban da mahaifina ban ga abin da zai hanani tattarawa na bar gidan Nazifi ba a gobe da safe, kuma bari na har abada, ai ban haifa ba balle na tafi da tunani da damuwar barin ƴaƴana, aure ne dama yama fita gaba ɗaya akaina ba iyaka aurensa ba kawai.

Tun daga wannan ranar lamari ya ƙara sauyawa, hankalin Nazifi ya tattara gaba ɗaya ya koma kan Zahra'u da abin da ke cikinta, wai ai likita ya ce tana da buƙatar a kula da ita sosai, don haka ko fita yay bini bini ya dawo, haka idan muna tare bini bini ya tashi ya tafi wajenta ya dubata, kuma da ke muguwa ce ta ƙarshe sai ta koma cewa ita abincina kawai take iya ci ta zauna lafiya, don haka dole na koma girkawa ina bata tana ci, idan naƙi girki kuwa ta dinƙi ciwon ƙarya kuma duk abin da aka bata taci sai tayi amansa, sai taci nawa ne kawai take zama lafiya, a hakan ma duk bai mata ba sai abun da take so na ke dafawa, idan ma na ce zan yi son raina to fa idan raina yayi dubu sai ya ɓaci. Nazifi har da min kashedin kar hakan ya bani lasisin zuba wani abu a abinci da zai cutar masa da mata da yaro, in bar ganin matarsa ce ni yin shari'a da ni abu ne me sauƙi a wurinsa.

Kusan kullum ba ni da aiki sai kiran mahaifiyata ina shaida mata abubuwan da ke faruwa, nayi ta mata kuka ina shaida mata na gaji, banda burin da ya wuce na ganni kusa da ita a ƙalla ko da a kafaɗarta ne na zubar da hawanyen kuma nayi hira da ita naji sanyi, haka zata lallashe ni ta turo min su Hindatu da Ƴaƴan wurin Yashaik su ɗebe min kewa, ita kuma ko da yaushe sai dai tayi ta ƙara jaddada min muhimmancin haƙuri, juriya da ƙara dagewa akan adu'a. Ga shi har yanzu ban ƙara zuwa gida ba tun wannan case ɗin da akai na su Atika, don ko da Kaka yasha jinya Abbaa ce yay na zo masa gida bai yafe ba. To daɗin ma da nake ta ji dai wata guda ya rage a cika shekara. Amma tabbas ina da buƙatar duk san da na shiga damuwa irin haka naje gidanmu wurin mahaifiyata, don ma dai Allah yasa yanzu makarantar koyon turanci ta online da na shiga karatunta duk ke ɗebe min kewa, haka kuma zan ta ganin Safiyya na live vedio a IG akan harkar lafiya wannan ma duk sai yake sawa ina jin daɗi.

Kar ku so kuga irin kuɗin da Nazifi ke kashewa wajen siyayyar kayan jariri, duk wasu kayan haihuwa ya siya ɗakinsa yay maƙil da akwatuna kamar me haɗa lefe, ko zama muka yi sai ya kama tambayata me zai ƙara siya, ba ɗakinsa kawai ba ita kanta can ɗakinta ya cikata da kaya nata da na jariri, Haka ba dama suyi waya da wani cikin mutanensa da yaji mutum yace bai ƙasar zai ce a taho masa da kayan jarirai masu tsada, gidan kuwa har yasa ana gyaransa wasu wuraren ana sabunta su. Ana haka Iyam tayi tafiya ƙauye, tana tafiya kuwa na samu damar sararawa, don kwanciya nayi ciwon ƙarya ko motsawa ban yi, ni kam na gaji da bautawa matarsa na ciyar da ita da kula da ita, saboda haka gidanmu nima aka turo min Saudatu ƴar wurin Baba Tijjani wacca da ƙyar uwarta ta barta, itama kuma Zahra'un sai ga shi an turo mata ƙannenta har biyu da wata tsohuwa.

Ƙaton cikin Zahra'u a gaba ya fito turtsetse haihuwa yau ko gobe, a kitchen take tana kaiwa da kacaniya da tukunya, kunnenta sanye da earpod tana magana da alama waya take yi. Ƙanwarta Mubina da ke can gefe tana yanka salad ta dube ta tana faɗin,"Yaya shi kawai za'a yanka?".

Kai ta ɗaga mata alamar ehh kana a hankali tace mata,"Je ki sanya turare a ɗakin Honey, kuma ki haɗa salad ɗin kisa a friedge ɗin ɗakina".

Mubina ta fita ita kuma taci gaba da maganar da take yi. "Ki bari ke dai wani abun ma sai Unborn ya sauka anan zan ƙara ƙwace shi ya zama nawa ni ɗaya".

Sai kuma tayi dariya sosai kafin ta ce,"Kai ƙawata! To ai na faɗa miki nima sai da na gama shishshigewa jikinta na gane sakarya ce sanyinta yay yawa kana na ce to bari in karkata in san yanda nayi na dawo da shi tafin hannuna gaba ɗaya. Kin san ina faɗa miki yarinya ce gaba ɗaya bata da wayewa, da ke ma naga yanzu ta fara baki in anyi tana iya mayarwa, amma tana abu komai irin na ƴan da, kuma like tayi rayuwan ƙauye ne i think so, kin san wani abu ma? Idan fa muna gado sumbatun da yake min haka za kiji yana ta faɗin shi a wajena kawai yake jin daɗi, can ba'a masa komai, bata iya salon komai ba salam takee".

Ta ƙara yin dariya bayan gajeran shirun da tayi tace,"A'a ni ba zan koreta daga gidan ba, ai so nake ta zauna tayi min rainon yara ni kuma naji da aikina. Kin san tana da addini da kuma tarbiyya dan ba ki ga yaran da suke wajenmu ba yanda ɗayar ke da karatun ƙur'ani a baki da ibada".

"Hhhh Allah ko ƙawata to ya kamata dai ki dawo ɗin gaskiya don kam dai ɗanku ya kusa fitowa, a yanzu haka ji na ke kamar zan haihu ƙarfi hali kawai na ke. Kin san na gama wancan wasan na ƙyaleta ta huta kar ɓakin cikina ya kasheta a rubuta min zunubi, amma dai kam har yanzu bana barinta runtsawa idan ya koma wajenta".

Nazifi ya shigo kitchen ɗin a lokacin, daga bakin ƙofa ya tsaya tare da harɗe hannayensa yana ta kallonta, jinta yake har can ƙuryar zuciyarsa, yana mata wani irin so ne da shi kansa bai sani ba, a duk lokacin da yake tare da ita sai ya ciji yatsar rashin samunta tun da daɗewa, ban da zanen ƙaddara ma da me zai kai shi haɗa layi da auren Sa'ida? Sai dai wani ɓari na zuciyarsa kan faɗa masa cewar ko da a wancan lokacin ya samu Zahra'u ba lallai ta aure shi a irin matsayin da yake ba, don a yanzu wataran yana ganin ɓacin ranta idan ƴan gidansu na masa magana da turanci yana kasa mayarwa, ranar nan har magana ta yaɓa masa ya kuma ji zafin maganar amma haka ya shanye saboda yana mutuwar sonta.

Zahra'u kuwa ƙamshinsa tuni ya sanar da ita zuwansa, don haka a hankali tace da ƙawarta ta kashe wayar, sai taci gaba da aikinta tana ta murmushi kamar bata san yazo ba. tana son Nazifi sosai shiyasa take so ta ƙwace shi gaba ɗaya babu boka babu Malam, kuma bata so ta kori Sa'ida tafi so ta zauna ta zamar mata ƴar aiki. Amma Allah ya gani duk ranar da Nazifi bai wajenta ji take tamkar tayi hauka saboda bala'in kishinsa da take yi.

Da sanyayyan muryata ta kira sunansa cikin salo na jan hankali.

"Derling". Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Shi kuma ya tako ya iskota yana me rungumeta ta baya tare da ɗora haɓarsa bisa kafaɗunta.

"Derling lafiya dai ka dawo da wuri haka?". Lumshe ido yay yana shaƙar ƙamshin da ke fita daga jikinta yace,"Na kasa samun natsuwar yin komai ne Swty, hankalina duk yana kanki ke da Unborn".

Ya faɗi hakan yana ɗora hannayensa saman cikinta ya shiga shafawa. Tana murmushi ta janyo towel ta goge hannayenta tare da juyowa ta fuskance shi, in da hannayensa suka koma kan ƙugunta. "Sannu da dawowa". Kafin yay magana ta ƙara cewa,"Amma Derling anya ayi haka kuwa, shikenan kuma sai ka dinƙa baro office ba zaka zauna kayi aiki ba, yanzu idan Babyn ya zo ya ke nan?".

Ta ƙarasa maganar a shagwaɓance wanda hakan ke ƙara narkar da zuciyarsa akan sonta don shi bai ganin hakan akan Sa'ida, idan ma tana yi to bai masa kyau kaman na Amaryarsa.

"Hmm Swty kin san yanda na ke azabtuwa da rashinki kusa da ni kuwa. Kinga da ban san in fita aiki nayi ta zumuɗin dawowa gida ba sai yanzu da na sameki. Balle kuma da tunanina ya yawaita akan ajiyata, ke dai madallah da ƙoƙarin samar min abin da aka kasa samar min shekaru da shekaru".

Shafo fuskarsa tayi tana cewa,"Ina sonka ne da yawa shiyasa nayi iyaka ƙoƙarina wajen ganin na sama maka farin ciki, kuma in sha Allahu ba tare da gajiyawa ba zan ta haifa maka yara har sai kace Swty sun isa haka".

"Godiya na ke Allah yayi miki albarka". Ya faɗa yana ƙara janyota jikinsa da cewa,"Ina son wannan kwalliyar. Kin san Unborn yasa kwalliyar na ƙara yi miki kyau sosai".

Tayi murmushi me sauti da cewa,"Wato ma ɗanka ne ke sawa nayi kyau?".

Hannunsa na shafa cikinta yace,"Tukunna ma wai me ya kawo ki kitchen?".

"Ina ƙoƙarin ƙarasa girki ne na bada akai maka office ashe ma kana hanya. Ban ji daɗi ba da ka dawo ban gama ba, kuma kaga Sa'ida ma...".

Ya ɗan ɓata fuska cikin nuna rashin jin daɗi ya ce,"Haka zamu yi da ke idan na fita ki ke satar baro ɗaki kina shigowa aiki? Ko kin manta likita yace ki huta ne, Swty ke da Unborn Baby kuna da buƙatar hutuwa, don Allah ki daina takura kanki, ga ƴan aiki nan da za su dinƙa miki duk me kike so, bacin nan ga Babaa Zulai da su Mubina, Sa'ida kuma ai ƙanwarta tana wajenta akan me za ki damu kan ki da ita. Ki daina don Allah kinga ko wanka ba na bari kiyi da kan ki so ban lamunce da shigowa kitchen ba daga nan har ki haifa min farin cikina".

"Derling ni gaskiya bana so ne kake cin girkin ƴan aiki, ko su Mubina kishi na ke da su akanka. Ka bar ni na samu lada tunda na sami lafiya ai, yanzu bana jin wani ciwo sosai, haihuwan ma a sauƙi zata zo in sha Allah".

"Ni dai ki huta, idan ba kya so naci abincin ƴan aiki zan kira gida idan sun yi abinci suke aiko mana, idan kuma Sa'ida taji sauƙi shikenan".

"A'a Honey ya kamata fa mu bar Sa'ida ta huta haka da ɗawainiyarmu. Kaga babu daɗi kar ta zo ta ƙulla ce ni ka jawo min baƙin jini a wurinta".

Bai sake cewa komai ba ya kama hannunta ya riƙe suka fita a kitchen ɗin, tana ta roƙonsa akan ya barta ta ƙarasa ta kusa gamawa amma bai saurareta ba. A falo ya tsaya yana ƙwala kiran Marawiyya ƴar aiki, wacca ta zo da saurinta tana duƙawa gabansa. Yana kallonta da faman kanainaye jiki a mayafinta yace,"Ki ƙarasa aikin da ke kitchen, Idan kika ƙara bari naga matata a kitchen tabbas zan sallameki ne".

"Kayi haƙuri Alhaji hakan ba zai ƙara fauwa ba".

Kamar zai duƙa ya ɗauki Zahrau sai ya fa tuna ba Sa'ida ba ce da yake rarumarta farat ɗaya, wannan da nauyinta sosai da har ƙirjinsa ke ciwo idan ya ɗauketa. Suna shiga ɗaki ya zaunar da ita kan gado. Ya wuce ya ɗauko magungunanta ya kawo ya bata da kansa kafin ya shiga mammatsa mata jiki wai alallai tayi aiki ta gaji. Ita kuwa tana yi masa wani irin kallo ta kwanta kan gado tana janyo shi jikinta.

"I am missing you Derling". Ta faɗi hakan wanda tuni jikinta ya fara tsuma domin sun jima ba'a je ga majiyar daɗi ba, tun satikan baya da jini ya ɓalle mata har akai tunanin ma ko ɓari ne amma da suka je asibiti sai likita yace da Nazifi ya ɗan barta ta huta, to tun sannan duk son Nazifi da ayi harka itama duk sonta sai dai su haƙura, dama ita ta fishi naci da ƙulafucin abun, gwara shi ma yana samu a wurin Sa'ida wanda hakan ke sosa ranta.

Cikin wani salo na kashe jiki tace da shi,"Honey wasa kawai, ina kewarka da yawa".

Lokaci guda kuma ta sauya labarin yanayin na su, ta birkita Nazifi ya rikice, shifa baƙaramin godiya yake ga Allah ba da ya ba shi Zahrau matsayin matarsa, Nazifi yana matuƙar bala'in son kasancewa da ita ko da yaushe. Yana iya rantsewa bai san daɗin aure ba sai da ya sameta, domin duk wasu wasanni na tarwatsa ƙwaƙwalwa da jin kamar zai mutu sai da ya mallaketa ya san su, ita ce kawai take masa irin yanda yake buƙata, amma ita Sa'ida ko da yaushe a cikin jin kunya take da rashin sanin irin abubuwan da zata masa wanda za su fasa kwakwalwarsa, har ta barsa da tunani idan ya fita office ya kasa sakat sai ya dawo gareta.

Sai yanzu ya daina ganin laifin wata Malama da ke lecture tana cewa mata namiji yana tsananin son mace me kunya, ki zama me kunya da zarar an zo ga abin nana ki nuna masa ba ki san wata aba kunya ba, ki zama fitsararriya a wajensa idan aka zo harka, yauwa ina nufin karuwar gidan Oga. Kuma tun da ta gama yi masa wasannin sai ɓacin rai ya maye gurbin baƙin cikinsa,saboda tunawa da yay yau zai koma wajen Sa'ida. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull