Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 6

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 6

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 6: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 6. #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR06FT5* _Hohoho wani girkin…

4,462 words

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR06FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ "Ke dakata!".

Ummani ta tsawartar min da maganar da na ruɗe ina yi. Kafin a hankali kuma ta shiga faɗa min kalaman kwantar da hankali kaman yanda ta saba a ko da yaushe, tare da ƙara faɗa min cewa na dage da adu'a komai me wucewa ne. Sai da ƙyar na samu na iya tsayar da kukana, muna gama wayar na kwanta kan gado saboda yanda naji kaina na bala'in sara min, baccin ma sai ya gagara zuwa kamar yanda na ke so ta ƙarfi da yaji ya ɗauke ni.

Ina cikin juyi cikin tunane tunane wayata tayi ringing, ganin lambar Safiyya nayi saurin ɗagawa, tana jin yacca nayi sallama a sanyaye ta danna ashar da cewar,"Wato sun kuma guma miki ko?".

Na ce,"Hmm Safiyya lamarin nan fa kwata kwata babu sauƙi". Nan na kwashe duk abin da ya faru a ɗazu na faɗa mata, ta dingi zage zagenta da cewa,"Wai ke ba zaki iya nunawa Nazifi ƴar daba ba ce ke, ki nemi abu ki ce zaki sassara shi idan bai sawwaƙe miki ba, haba wannan bala'i na kullum yaƙi ci yaƙi cinyewa, haihuwa ke za ki bawa kan ki ne. To wallahi ki nunawa Nazifi ke mahaukaciya ce, kuma har mahaifiyar tasa ki bar ɗaga mata ƙafa yanzu idan ya so ko mai zai faru ya faru kin dai ji me na faɗa miki ko, mata ƴar bala'i da miji a raye tazo gidan ɗa ta tare saboda dai ta hana ki sakat".

Nayi shiru ina jin sabbin hawaye na sakkowa ta gefen idona. "Ni dai shawara na ke ba ki Beb, ki nemarwa kanki mafita tun wuri wallahi, ba zai yiwu kici gaba da zaman wannan ƙasƙantacciyar rayuwar ba, haba Miji yay maka, Uwarsa ta maka da ƴan uwansa, yanzu ta kai ta kawo ma lamarin ya haɗa har da kishiya. To wallahi gwara tun wuri ki zama mahaukaciya a cikin gidan nan, kiyi haukan da za ki hana kowa kwanciyar hankali, rashin mutunci waye bai iya shi ba, idan ma baka iya ba a wannan zamakin koyarsa kake, don haka ki daina barin miji yana taka ki son ransa Beb".

"Hmmm ba za ki gane ba ne Safiyya, ni fa duk faruwar wannan lamuran ba na so igiyar aurena ta girgiza, Safiyya idan Nazifi ya rabu da ni wa kike tunanin zai auri macen da bata haihuwa? Shima fa rashin haihuwar ne yasa ya juya min baya har yake ganina banza a wofi, yau idan ace na aje masa ɗa zai kalle ni ne yace ni da babu ɗaya a wurinsa? bayan haka Safiyya ba ki ganin irin rayuwar da zaurawa ke yi ne? Irin tarin ƙalubalen da suke fuskanta ba daga waje ba har da cikin gidan iyaye, a wannan ƙananun shekarun nawa ina zan kai zaman zawarci ni da na ke ɗorawa kaina damuwa da surutun mutane. Na gaya miki fa Kaka ya rantse aurena ya mutu zamana a gidanmu sai in faɗi yay ya mutu. Ko kaɗan mutuwar aure ba ta da daɗi Safiyya, yayin da zuciyarmu ke tafasa ne kawai muke ganin gwara rabuwa da ci gaba da zama, ke dai kawai ki tayani da adu'a ubangiji ya saita dukkan al'amura, ya kawo min sauƙi cikin wannan musibar".

Muryan Safiyya a sanyaye tace da ni,"To Allah ya kawo sauƙi ya saita tsakaninku. Amma lamarin kam sai dai ke ɗin uwar haƙuri, idan ni ce sai dai Baba ya kore ni a gidansa amma sai na kashe auren billahillazi, kuma ba zan bar gidan ba sai na fasa ƙoƙon kan mijin yasin, da irin rayuwar gidanki ai gwara yawon zawarcin ina tafe ana zagina, ina ce dai ba fitowa zai ajikina ba...".

Dafe goshi nayi ina girgiza kai nace,"Safiyya ya isa haka mana. Don Allah kike adu'a Allah ya sanyaya miki zuciya. Anyway yanzu dai ya ake ciki, kiran nan da kika min har naji sanyi a raina".

Numfasawa tayi kana tace,"Dama zan faɗa miki ne wannan ƙwararriyar chef ɗin zata fara classes na girki amma online zata yi, kinga kin samu dama sai kiyi joining ko? Gwara kema ki koyi girke girken zamanin nan da ake na larabawa kike girkawa kanki ke ɗaya kina ci kina barin ƴan iska da shaƙar ƙamshi da tsinkewar yawu".

"Uhmm to Safiyya ni kam don wa zan koyi girkin idan ba don shi ba, ai gwara na iya yaci na wuce gori. Amma nawa ne kuɗin da ake biya?".

"7k ne kuma kar ki damu da wannan zan biya miki, dama i want hear from you ne if kina so kar nayi azarɓaɓin biya miki ki gwanya ni".

Ina murmusa kunci na ce,"Alright na gode sosai ƙawar arziƙi, Allah barmu tare ya baki miji na gari. Sai batun spices na abinci da kika ce shima za ki haɗa ni da wacca zan ke siya a wurinta".

"Amin ya Allah na gode da adu'a. Ehhh spices kar ki damu akwai Mrs Arab zan haɗaku, ba lambarta ne a wannan wayar da sai na ba ki yanzu...Ai in sha Allah kwanan Nazifi zai raina kansa, sai yay danasanin duk abubuwan da yake miki, ke dai kike riƙe duk tips ɗin da na ke ba ki, ƙananun kayan ma zan sako su a mota jibi a taho miki da su, saura idan an kawo kike ƙin sakawa kin ji, wallahi Beb kayan da na siya miki kika saka kika gimla ta kusa da Nazifi na rantse miki da kansa zai kawo kansa ɗakinki, bar shege da mu yake zancen, itama matar tasa zata ci uwarta ne".

"Ƙawata ta kaina, shikenan to ina godiya kuma in sha Allah duk shawarwarinki gare ni zan ke amfani da su. Naji kin ce za ki yi aiki bara na barki haka sai da safe".

"Ok Beb bye bye take care. Allah kuma ya saka miki nan kusa. Zan tura miki lambar chef ɗin sai kiyi mata magana tayi adding naki group".

Ta kashe wayar ni kuma na tashi naje na ɗauro alwala nayi sallar isha'i da ban yi ba. Ƙarar wayata na shigowar text na ɗauka ina duba lambar da Safiyya ta tura mini, 09030398006. Take ko nayi saving na shiga whatsapp na aje mata saƙo. Cikin kwanaki biyun da suka biyo baya abubuwa sai ƙara faruwa suke, ƴan uwan Zahra'u kuwa sai shige da fice suke a gidan ana zuwa dubata da jiki, yanda suke ta nan da ita sai abun ya burgeni da bani sha'awa, ina jin ina ma ace ni ce, wato ashe haka me ciki ke zama ƴar gata ta kowanne ɓangare.

Nazifi da ƴan uwansa kuwa sun maida ita kamar ɗanyan ƙwai sai riritata suke yi, ni dai ina ta ganin abubuwan da yanzu ko kusa basa damuna ma sai dai nayi murmushi na girgiza kai, haka za suyi ta yada habaici idan suka zo, to ni kalmar juyan ma yanzu jinta na ke kamar iska bata taɓa zuciyata. Shi kuwa da gayya sai ya shigo min ɗaki yana tambayata wai ina da abu kaza Baby ta kasa cin komai, ai na nake ganin za'a samu abu kaza, haka dai ni kam ban bi ta kansa ya gama surutunsa ya fice. Ranar ma da yana wajena sai ce yay in taimaka duk sanda nayi tuwo in ke zuba mata na ce ba zan iya ba, shine ya hau fushi wai a tunaninsa zan fishi farin ciki da samun cikin nan amma sai yaga akasin haka, bai taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba kuma yayi mamaki sosai, amma na sani yaron da za'a haifa shine farin cikinsa sama da komai a duniya, saboda haka gwara na koyawa zuciyata sonsa tun kafin yazo duniya idan ba haka ba kuma zaman mu da shi zai fi na baya muni.

Cikin ikon Allah da na ƙara dagewa akan adu'a sai na ɗan fara samun kan Nazifi, yanzu zai zauna da ni har mu ɗan yi magana, kuma ko ban je ɗakinsa ba zai neme ni, duk da ahakan ba gane masa na ke ba. Kuma wani abun mamaki hakan sai yasa Zahra'u ta tsiro da wata tsirfa ta makirci ganin cikinta ya fito sosai, wato duk ranar da Nazifi ya dawo wajena ba zata bar ni da shi ba, sai mun kwanta sai kiranta ya shigo waya tana yi masa kuka ita cikinta, Small Baby yana takura mata, amai take tayi ta kasa bacci, zata ci abu kaza, tana ga haihuwa zata yi, abubuwa dai iri daban daban da ba ya iya haƙura shi kuma sai ya farka yaje wajenta, haka zai zauna ba zata barsa ya dawo ba sai asuba.

Lamarin tun bai damuna sosai har ya zo ya dame ni, na kira Ummani na faɗa mata sai ta shiga bani haƙuri kamar kullum tana faɗa min dama a irin wannan gaɓar akwai wahala, sai dai na ƙara haƙuri da kawar da kai, aduar nan dai kawai naci gaba kar na fasa. Da dai naga abin ya ishe ni muka yi waya da Safiyya na ke faɗa mata, sai ce tayi nima in fara yi masa ƙaryar ciwo wala yana wurina wala bai wurina, ita zama ta haɗa ni da likitan da zaa ce ciki ne da ni, cikin ƙarya ai ba akaina aka fara ba. Ban dai ɗauki wannan shawarar ba kawai na yanke abin da na ke ganin yafi min, dama da ya kwanta gado sai bacci shine kawai sai na samu na saka wayar a silent, haka kafin nayi bacci zan ta ganin kiranta na shigowa, asuba nayi kuma zan riga shi farkawa na cireta a silent, sai da safe idan yaga kiran sai ya kama tambayata wai kwana biyu wanne irin bacci muke yi ne, sai in masa shiru bana tanka masa.

Yauma muna kwance mun ma yi nisa a bacci, kamar a mafarki naji ana ƙwanƙwansa ƙofa. Na kasa motsawa daga kwancen da na ke saboda mamakin da ya kama ni haka kuma kaina ya ɗaure, na tafi tunanin wa ye da bugu a daidai wannan lokacin haka? mirginawa nayi na ɗauko wayarsa don duba lokaci sai naga kiran Zahra'u na shigowa, ikon Allah kawai sai na kasa aje wayar na tsaya kallo har kiran ya katse, ƙarfe biyu lokacin. Tsaki nayi na aje wayar na koma na kwanta, can kuma sai aka ƙara ƙarfin bugu ka ce an biyo sahun karɓar bashi.

Ina kallonsa ya tashi zaune yana ɗaukar wayarsa ya duba, sai kuma naji yana magana shi ɗaya. "Allah yasa lafiya". Ya faɗa yana sauka akan gadon ya tafi ƙofa yana tambayar waye. Wallahi tsammanina duk Iyam ce ko kuma ita Zahra'un, amma sai naji muryar ƴar aikinta na cewa.

"Alhaji Anty ce bata da lafiya".

Ai lokaci guda baccin ya bar idonsa da sauri ya buɗe ƙofar, yana niyyar fita na kasa haƙurin cewa da shi,"Ina zaka je kuma?".

Ya juye ya kalle ni fuska duk ta gama bayyana da damuwa yace,"Ba ki ji ba Amarya ce babu lafiya, ko za ki taso muje ki ɗan taimaka mata".

Iya shaƙa na shaƙa har naji kamar na miƙe na wanke shi da mari. A yau kam bana tunanin zan musu uzuri, na gaji da cutarwar da ake min, Na ɓata rai ban miƙe daga kwancen da nake ba na ce,"Amma dai kasan hakan shiga hakki ne ko? Ita ciwonta ba ya tashi kullum sai taga kana wajena, a wajen nawa ma sai muna tsaka da bacci, wato kiran wayar ma da ta saba duk bai mata ba sai ta koma haɗawa da buga ƙofa? Wannan ai zalunci ne, mutum yay magana kuma ace yana baƙin ciki da hassada".

Wani kallo ya shiga yi min wanda na kasa fassara shi. Sakkowa nayi a gadon na isa bakin ƙofa zan mayar da ƙofar na rufe na ke cewa da ƴar aiki,"Ki koma kiyi jinyartata ko ki faɗa mata tasha magani".

Kafin na kai ga rufe ƙofar sai jiyo ihunta muka yi a falo, tana kiran,"Wayyo cikina, wayyo marata, Derling ka zo ka taimaka min don Allah, Derling mutuwa zan yi".

Ai kafin na ƙifta ido Nazifi ya fice, idona ya ciko da ruwan hawaye, ina tsaye naji Iyam na faɗin.

"Ki yi haƙuri Amarya ciki dama ya gaji haka amma ki daina kiran za ki mutu, mutuwa ba yanzu ba in sha Allahu. Zafin ciwo ne kawai sannu kin ji, ai kina ma ƙoƙari wallahi Allah ya ba ki da sauƙi".

Shi kuma hankalinsa a tashe yake cewa da Iyam,"Yanzu me zamu yi mata? Ko asibiti zamu tafi? Iyam ba na son abin da zai taɓa min yaro, ba na son abin da zai taɓa Zahra'u, ina son su dukansu sune rayuwata". [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR09FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Washegari ban farka ba sai ƙarfe tara. Hakanma da ƙyar na iya tashi saboda zazzaɓi da ciwon kan da na kwan da shi. Ga ɓarin zuciyata da ya dinƙa min ciwo don ko da asuba da nayi sallah haka nayi ta nishi ina jin zuciyata kamar ana soya min ita, shi kansa farko yay banza da ni yana ji ina ta faman kiran sunan Allah cikin wahala, ashe zuciyar tasa da sauran tausayina sai ya tashi ya samo min pain relieve wurin Matarsa, naƙi karɓa na sha a ganina akan me zai karɓo min magani wurin kishiya, kuɗin siyo min me bai da shi? Asibiti kuwa dama bana saka rai don rabon da nayi ciwo yace naje asibiti har na mance, idan na buƙaci zuwa sai ya kama ƙorafin na fiya ciwo da raki, in nemi paracetamol na sha asibitinma ko naje shi zasu ba ni.

Duk sanda yay furucin nan sai dai na girgiza kaina, Namiji ne shi Ƙayar Ruwa, amma ban da rashin adalci irin nasa ko da muna zaman lafiya sarai yasan irin ƙarfin hali na ciwona, sai nayi ciwo ma na gama ban bari ya gane ba. Kuma idan shine ke ciwo mura wannan ya dinƙa kwakwazo, sannan a hakan Zahra'un da ta zo kafin ta samu cikin ma kusan duk sati suna hanyar asibiti bata da lafiya, amma bai taɓa ƙorafi ba. Ai har sai da na ga ciwo na neman kashe ni kana na karɓa maganin na sha baƙin ciki na daɗa tokare min zuciyata, danasani da nadamar ƙin tsayawa nayi karatuna na baibaiyeni, don duk da wannan tarin baƙin cikin ban fuskance shi ba, a ƙalla da ina aiki ko ba'a biyana da yawa nafi dai ƙarfin na ce da Nazifi ya siya min magani balle har ya ƙuntata mini.

Ni dai maganin ma da na sha sai naji tamkar ana ƙaramin zafin ciwon, haka nayi ta malelekuwa a ƙasa ina hawaye, ga zafin ciwo ga fargabar tunanin Allah sa ba ciwon zuciya ne ya kama ni ba, shima dai abun sai ya ba shi tsoro ya shiga binciken paracetamol ya kawo min, ƙarshe dai sai ruwan zamzam ya tsiyaya ya tofa min bismilla ƙafa sha tara ya ban na sha tukunna na samu sukuni na koma bacci.

Agogo na kalla naga har goma saura, rashin ganin Nazifi a ɗakin banji wani mamaki ba, don na san dama yau ba lallai ya bi ta kaina ba idan zai fita, kuma ba saboda tausayin ciwon da nake ba, sai saboda na faɗa masa Allah ya saka min katse min baccin da yay akan biyan buƙatar wata can da alhakin ci da ita ba akaina yake ba, har ina faɗin ba zan yafe ba shine yace kar na yafe na ce dama ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne ko ban ce ya saka min ba zai saka min ne. Shine har ya na ƙara faɗa min shi fa bai ƙaunar duk wanda ba zai so ƴaƴansa da uwar ƴaƴansa ba, kuma akan hakan yana iya ɓatawa da kowa.

Na sakko a gado cikin ƙarfin hali, ɗakin na gyara anan nayi wanka kana na koma ɗakina na shirya. Saudatu na kallona tace,"Yaya Sa'ida ba ki da lafiya ne?".

Na ce da ita,"Lafiyata lau". "Naga idonki yay jawur". Ta faɗa tana taɓa jikina sai ta ƙara cewa,"Kuma kin ji jikinki ma zafi".

Bance mata komai ba na buɗe wadrobe ina kwaso kayan wanki, sai sannan idona ya kai kan Rumana da ke bacci. Na kalli Saudatu ina cewa,"Lafiyar ƴar nan bata je school ba?".

Saudatu tace,"Nima ina bacci ta ƙwanƙwasa ta shigo naga tana hawaye".

Rigar da ke hannuna na ajiye, na yaye bargon da ta rufa da shi ina taɓa jikinta, babu wani zazzabi don haka na shiga tashinta. Ta buɗe ido tana miƙa ganina kuma tayi firgigi ta miƙe zaune tana micimici da idanu. Ina mata kallon shiga taitayinki da ni na ce,"Rashin lafiyar ƙarya saboda kar kije makaranta ko? A haka kike so mu shirya da ke? Salon ki jawo min zagi da cin mutunci ace ni nake hana ki saboda ina baƙin cikin ban haifa ba, koma me za'a gaggaya min ai kin sani dai tun da gaban idonki ake komai. Ina ce har alƙawari kika min akan ba za ki ƙara yin abin da zai jawo min faɗa ba. To saukar min a gado ki ficen kije can, kuma kar na sake naji kin ambaci sunana a bakinki".

Ƙasa tayi da kanta kafin ta sauka ta fita jiki a sanyaye. Na ci gaba da haɗa kayan Saudatu sai magana take min akan na kwanta na huta kuma akwai kuɗi a wurinta ko taje ta siyo min magani nace mata a'a. Haka na gama na shiga banɗaki ina wankewa tana tayani ɗauraya, babu yanda bata yi da ni ba akan na barta tayi ita ɗaya, ni kuma bana so ne ciwon da nake ji ya kwantar da ni shiyasa gwara na motsa jikin nawa. Yau ɗin dai haka na ke jina sukuku babu wani daɗi, Da ace akwai injin wanki ne sai na ƙyale mata, to tun zuwan Iyam ƴan uwansa suka lalata shi, kowacce ta tashi zuwa sai ta yayibo uban kayan wanki, dama ni ba damuwa nayi da amfani da shi ba dan ko da na ke wankin Iyam ma ban taɓa yi da shi ba.

Mun fita shanya kawai na ga Rumana durƙushe gefen ɗaki ta kifa kai sai shashshekar kuka take yi a hankali a hankali. Ban saurareta ba nayi gaba, sai kuma duk naji zuciyata ba zata iya watsi da yarinyar ba na barwa Saudatu shanyar na dawo. Kanta na tsaya na kira sunanta ta ɗago tana kyarmar jiki.

"Don Allah Anty kiyi haƙuri".

Harara na galla mata nace,"Rufe min baki ni, ba damar ayi miki faɗa sai ki kama kuka, idan kinje makarantar zan miki faɗan ne? Ke ba ki san ni kike bari na kwana a ciki ba, ni kike jawa maganganun ɓacin rai".

Ta saka kuka tana rungume ni tace,"Anty ai ba ƙin zuwa nayi ba, yau ba ki zo kin tashemu ba kuma da Atika ta tashi bata tasheni ba. Sai da ta gama shiryawa na farka, kafin na shirya an tafi kaita shine Anty Amarya tace zata aiki direba na haƙura da zuwa ko na karɓo kuɗin mota ko na tafi a ƙasa".

Tausayi naji ta bani, duk sanda na kalleta sai na tuna wahalar da suka bani, haka sai na tuna wulaƙancin da iyayensu suka yi min, da wanda ake kan yi har yanzu, don na kasa mantawa da dukan da Uwayensu suka min, haka na kasa mantawa da a dalilin sharrinsu watana goma sha ɗaya cif ban taka gidan ubana ba. To amma ita yanzu duk ta maƙale min, ko shareta nake ta dinga kuka kenan tana bani haƙuri, kuma wai saboda ta daina wancan mugun halin Iyam sai take tsangwamarta, itama ƴar uwartata da ta samu ɗaurin gindi sai ta daina kulata, shi kansa gogan saboda Rumanan a wajena take bai fiya lura da lamarinta ba, Atikar dai ita ce ƴar gata a wurinsa tunda tana wurin amaryarsa, ni Rumanan ma har tausayi take bani nayi nayi ta koma can wajen Zahra'un taƙi ita tafi son wajena.

Na ce,"To kin yi breakfast?".

Kaɗa min kai tayi alamar a'a. Muka sauka naje na dafa mata indomie don ni ban jin ma zan iya cin wani abu kam, Saudatu kuwa tana azumi da yake alhamis da alhamis bai wuceta.

Da rana muna falo muna kallo sai ga su Ummaa sun zo. Da fara'ata na miƙe ina musu sannu da zuwa, fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata, ina cewa ga wurin zama sai ce tayi. "A'a ai ba wurinki muka zo ba, ba ki ga kayan hannun mu ba ne, me ciki muka zo dubawa da kayan barka kafin a haihu mu ƙaro wasu".

Nayi murmushi na ce,"Allah sarki to an gode. An zo lafiya ya Malam?".

Tana jefa min banzan kallo irin wanda Iyam ke min tace,"Malam na lafiya".

Suka wuce ina bin su da kallo, irin set ɗin robar kayan wankan jarirai ne sai ƙatuwar baƙar leda da na san ba zai wuce kayan yaro ba. Abin na ta dai ba na Allah ba ne don ta ƙara samun shiga wajen Iyam ne da shi kansa Nazifin. Dama ai ita da Iyam ɗin kansu a haɗe yake sun ware Amarya a gefe baiwar Allah da babu ruwanta, ita kam zuciyarta fess babu datti. Sama suka nufa, kuma nayi musu shiru ban shaida musu cewar tana ƙasa ba, tun da ba wurina suka zo ba ina na ke da hurumin faɗa musu kuwa, gwara nayi shiru kafin a ƙara faɗa min magana, ile sai ga su sun sakko suna raba idanu.

"Sa'ida ai babu kowa a wurin nata".

"Ta nan ƙasa ai". Ta bini da kallo wanda ke shaida taji haushi, ta kama faɗin,"To da ba sai ki shaida mana ba amma kika barmu muka hau. Ko don na ce ba wurinki na zo ba, to me zan zo nayi a wurinki ke da ba ƴaƴa ba balle na ce na zo ganin ƴaƴan Nazifi".

Ta gama maganganunta suka wuce, nan ma dai haka ta gama bin ɗakunan ƙasan ta dawo tana ce min. "Ina ne wajen nata ne, wannan ƙasan naku masu surƙuƙun waje duk a kasa gane masa".

Kamar na ce,"ki kira wayarta ki tambayeta". Sai naga hakan kuma ai zama da rashin girmamawa, ko ba komai matsayin uwa take, ni kuma ban da halin rashin kunya wa manyana. Na kalli Rumana zan ce ta tashi ta raka su sai naga ta ɓata fuska tana kaɗa min kai a hankali alamar bata son zuwa, kawai sai nayi musu nuni da hanyar dama ta jikin lungun tsakanin ɗakina da nasa ne.

Saudatu tace,"Wallahi Yaya Sa'ida idan da nice ba zan faɗa mata ba. Mtswww mutanen nan ba su da kirki ko kaɗan".

Nayi guntun murmushi bance komai ba. Ni dai hankalina duk bai ga kallon da muke yi, domin kuwa lokaci ɗaya naji gabana na ta faɗuwa kamar ƙirjina zai faɗo, na shiga adu'a amma inaa. Tuni kuma sai na fara tunanin can gida, kwana uku kenan bamu yi waya da Ummani ba saboda wayarta ta lalace, wanda rashin jin nata ya haifar min da rashin kwanciyar hankali duk abin da nake ina daurewa ne kawai. Jiya ma sai Yashaik na kira yace idan ya shiga gidan zai haɗamu, Yaya Al'amin kuma haushi naji don ko a shekaranjiyan sau huɗu ina kira ina cewa ya haɗa ni da ita sai yace in kashe zai je ya kai mata amma sai inji shiru, ni kuma nayi zuciya na ce ba zan ƙara kiransa ba.

Kasa haƙuri nayi na kira Maman Yasmin, muka gama gaisawa muka yi ƴar hira sannan nace ko zata taimaka ta bayar akaiwa Ummani wayar. Tace min to bara ta duba ko zata sami yara don yanzu duk sun tafi Islamiya. Shiru shiru bata kira ni ba har na ƙara kira tace bara kawai taje ta kai da kanta, na ce a'a ta bari ko su Yasmin suka dawo ta basu, ni dai kawai don Allah ta haɗamu. Bayan gama wayar tamu na kwanta, a raina ina jin ina ma ina da kuɗi in siyawa mahaifiyata sabuwar waya, da haka bacci ya ɗauke ni.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull