Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 7
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 7: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 7. Ban jima da soma baccin ba na farka a tsorace ina salati, wani…
4,458 words
Ban jima da soma baccin ba na farka a tsorace ina salati, wani mummunan mafarki nayi wai ƙofar gidanmu cike da mutane an kafa rumfar tanfol, kuma na shiga gidan sai na tadda su Yashaik sunata kuka, na tsallake mutane na faɗa ɗakin Ummani da gudu, ina shiga na ganta itama tana kukan, na faɗa jikinta ina tambayarta me ya faru sai ta kasa ce min komai. Daga tsakar gida sai naji ana Allah yasa ya huta yasa Annabi ya san da zuwansa, ban san lokacin da na fita ba ina tsallaka mutanen tsakargidan nayi ɗakin Kaka, shima a can na sameshi shi da ƴan uwansa da su Baba Tijjani, na bi kowa da ido Abbaana ne kawai babu, ban gansa ba haka kuma fuskokin duk ɗinsu da jimami.
Sai naji kafafuna sunyi sanyi na fito a gigice nayi ɗakin Abbaa, ina zuwa naga an saka kwaɗo abin da ba'a taɓa ba, wai sai naji muryar Hajjo na ce min kiyi haƙuri Sa'ida ita mutuwa dole ce, Abbaanki ya amsa kiran mahallicinsa. Ai ban san lokacin da na ƙwalla razananniyar ƙara ba na zube a wajen ina ihu ina kiran sunan Abbaa, aka taru akaina Ya Imam shi kuma na min ihun na rufewa mutane baki.
Ina hankalina zai kwanta da wannan mugun mafarkin, ai tuni na miƙe ina cewa da Saudatu,"Tashi ke ki shirya".
Itama yanda taga na fita a hayyacina ta kama tambayana, ban tsaya sauraronta ba na haye sama suka biyo ni suna ta me ya faru. Ko da na shiga ɗaki sai na rasa abun ɗauka, duk na ruɗe na riki ce. Ta zo ta kamani ta zaunar, Tuni kuma hawaye ya fara sauka a fuskata kamar an kunna famfano, ina ta juya kai na kasa cewa komai duk da cewar magana na ke so nayi, mafarkin ne yake ta haska min a ido. Yawu naji tana tofa min wanda na fahimci adu'a ne take yi, ita kuma Rumana ta ƙanƙame jikina ganin ina kukan itama sai ta sa kuka.
Sama sama naji Saudatu na faɗin,"Kema da saka abu kike a rai, na san rashin jin Ummanin ya sa kika yi mummunar mafarki, dama shaiɗan me jiran kaɗan ɗin saƙa maka mummunan abu. bara a ƙara gwada lambar Ya Hindatun ko zata shiga".
Murya na rawa na ce,"Ba ita za ki kira min ba, kira me gidan nan ki faɗa masa zan tafi gida".
Ganin bata da niyyar kiran na ƙwaci wayar, ruwan da ya taru a idona yaƙi barina ganin screen ɗin wayar, sai itan dai na miƙawa nace ta taimaka ta kira shi. Ta kira har sau uku bai ɗaga ba, nima na karɓa na dinga kira amma bai ɗaga ba, duk da ba yau ne karon farko na rashin ɗaga min waya da yake amma na yau ɗin sai na fi jin na damu da shi, hankalina ya ƙara tashi, to kar dai mafarkin nan ya zama gaskiya Abbaa ya mutu, Ina zan sa kaina idan na rasa Abbaana a wannan gaɓar? Yaushe rabon da na gansa? kuma ya mutu yana fushi da ni? Bana so ya mutu duk da mutuwa dole ce, haka ba na so ya mutu sai ya san gaskiyar lamarin da ya faru akan case ɗina da Nazifi da yaransa.
Tunani nake akan na tafi kawai in yaso ko na ƙarasa gidan na faɗa masa, sai dai har kullum ina tsoron fita babu izinin miji duk da lalura ce ta kama a yanzun, to amma ai bani da tabbas. Zuciyata ta yanke shawarar na tashi na shirya kawai, kuma sai bayan mun shirya har mun sakko falo na tuna da kuɗin mota, naira ɗari ce da ni hagu da dama, na kalli Saudatu nace,"Nawa ne kuɗin hannunki?".
"Ɗari ce".
Shiru nayi ina tunanin yanzu wa zai ɗaukemu ya kai har makwarari a ɗari biyu? ga shi kwanakin nan na fahimci can gida ma a matse suke don haka ba na ce in munje can ma karɓa ba. Kiran wayar Nazifi na ci gaba da yi, nayi sa'a ya ɗaga a wannan karon, ko sallamarsa ban amsa ba nace,"Don Allah zan je gida".
A daƙile yace min,"wanne rainin hankali ne hakan baki san da tambayar ba sai bayan na fita, kuma tun tashinki sai yanzu za ki kira ki tambaya, to babu in da zaki je".
Roƙonsa na shiga yi, yanda yaji ina masa magiya ya daka min tsawa da cewa,"Ke ya isa, ina tsaka da aiki kin addabe ni da kira kamar me bina bashi, na kira kuma kina min kuka da faman magiya, ke wacce kalar macece ne mara natsuwa da rashin sanin yacca ake magana da miji. Me ake a gidan naku dama?".
"Kayi haƙuri, zan je naga Abbaa ne".
Hmmm zuciyata ta matse jin yana tambayata,"Waye Abbaa?". Ya faɗa kafin na bashi amsa kuma sai ji nayi yana faɗin,"Hasbunallahu ai na manta ma gaba ɗaya". Kamar an kulle masa baki sai yay shiru.
Na daɗa ruɗewa ina tambayarsa,"Me ka manta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un don Allah ka faɗa min wani abu na faruwa ne da aka ɓoye min?".
Ƙaramin tsaki yaja kafin yace"Ki shirya kije ɗin".
Na ce,"To don Allah ko zaka turo min da kuɗin mota, ɗari biyu ce da ni ba zata kaimu ba".
Sai ya ƙara cewa,"To wai dole ne zuwa gidan, ko kin manta har yanzu wa'adin da Baban naki ya ɗauka miki na rashin zuwa gidansa bai ƙare ba ne. Ko kiranki suka yi?".
A sanyaye na ce,"A'a hankalina ne yaƙi kwanciya don Allah kayi haƙuri ka taimaka min da kuɗin motar".
"Ki aika Saudatu ta karɓo miki dubu ɗaya wajen Amarya". Na rumtse ido nace,"Amma...".
Ya katse ni da cewa,"Kinga idan ba za ki aika ba ki haƙura ko ki tafi a ƙasa. Ni dai kar ki ƙara kirana kina katse min abu me muhimmanci".
Daga haka ya katse wayarsa, ina jinsa kafin ya katse yana faɗin,"Hamisu kaga na manta ina cewa zaka raka ni gidan su Sa'ida, wanne asibiti ma Al'amin yace mana?".
Sai naji hawaye ya ƙara zubo min, zuciya da jiki na rawa na miƙe. Tabbas akwai abin da ake ɓoye min, kuma mafarkin nan yana haska min ne, haka nayi watsi da takaicin karɓo kuɗi wurin Zahra'u. Ban da yanda zan yi haka dole na tura Rumana ta karɓo, sai da ta jima aka gama jan lokaci sannan aka bata dubu biyu wai ya kirata yace ta ƙara mana dubu ɗaya. Rumana tana kuka akan zata bi mu na ce tayi haƙuri saboda makarantarta ba zai yiwu mu tafi tare ba.
Muna isa gida muka tarar jikin Abbaa ba yanda yake, Yayyuna suna gefensa sai firfita suke masa, Ummani tayi jugum a gefe ɗaya ta zabga tagumi tana kallonsa, kana kallon fuskarta kaga na wacca ta sha kuka ta gode Allah. Wai ashe kwanansa huɗu yau a kwance, saboda kar na san da ciwon aka ce min wayar Ummani ta lalace, Su Yashaik suka amshe don kar zuciyarta tayi rauni ta faɗa min, hatta Abbayoma ya zo shi da yake can garin damaturu amma ni da nake nan aka gagara sanar da ni rashin lafiyar mahaifinmu saboda kar a ɗaga min hankali, a ganina ba'a min adalci ba sam. Haka na isa gefen kan mahaifin nawa na zauna ina kamo hannunsa na riƙe, bai gane ni ba kwatata kwatata, ga dai shi idonsa akaina yake ashe ba ya gani yau ne ma idon ya ɗan buɗe masa amma jiya da shekaranjiya duk ba ya gani. cikin kuka na ke jera masa sannu ina cewa Abbaa ka yafe min don Allah. Sai da yaji muryata ya gane wacece, duk da a tsananin ciwo yake amma sai ce yay,"Me yasa kika zo alhalin wa'adin lokacin da na ɗauka maki bai cika ba, karo na biyu da kika take maganata Sa'ida". Yay maganar a wahalce.
Ni dai kuka kawai na ke yi, shi kuma cikin zafin ciwo faɗi yake na tashi na tafi gidana. Sai da Kaka yay magana kana yay shiru ya haƙura. Har bayan isha'i muna kan Abbaa, ciwo babu wani sauƙi har cewa yake a ƙyale shi ko yanzu ya tafi ai ya mori duniyar kuma dama kullum cikin jiran cikar lokaci yake, muyi masa fatan dacewa da rahmar ubangiji kawai, sannan mu haɗa kanmu Yayyuna su kula da ni, kuma mu riƙe mahaifiyarmu da kyau. Wannan furucin nasa ya daɗa tsinkar da zuciyoyinmu, mazan ne kawai suka yi ƙarfin halin riƙe hawayensu a hakan ma ban da Abbayo, ni da shi kuka muke haiƙan. Sai wajen tara na dare ciwo ya lafa masa har bacci ma ya ɗauke shi.
A ɗaki Ummani ke faɗa min ai tunma a ranar da ya fara ciwon aka kira Nazifi, aka ce kar ya bani aron wayarsa ma na kira gida, mamakin da tayi da har yanzu bai zo ba kuma waya ma bai kira ba, don ɗazu ma da ana neman kuɗin da za'a yi masa scanning na hanta Yashaik yake cewa ko shi zai kira ya tambaya aron kuɗi sai ta hana.
Ko kirana bai yi ba yaji daga gare ni, ban san dalilin ma dana sa a raina cewa zai kira ni ɗin ba. Washe gari da safe sai gashi ya zo, yana bawa su Yashaik haƙuri wai ayyuka ne suka sha gabansa shiyasa, duk yanda ya so ya yakice ba yanda zai yi. Da zai tafi ya ajiye musu kuɗi Ummani tace ba za'a karɓa ba tasa Abbayo ya ɗauka zai mayar masa, ni kuwa na karɓa nace ba za'a mayar ba tunda dama cikin buƙatar kuɗin ake, Don yanzu haka wata allura aka rubuta dubu goma Yashaik da Yaya Imam na can sun fita nemo kuɗi.
Ranar cikin dare a lokacin ƙarfe uku, ina tsakiyar sallah wayata ta shiga ƙara, bayan na idar kuma ina jan carbi ta ƙara yin ƙara na kai hannu zan kashe zatona alerm ne, ashe kira ne na ɗaga ma ina tunanin kashe alerm ɗin nayi, sai daga nesa nesa na ke jin kamar ana kiran Sa'ida, wayar na ɗauka da zummar kunna fitila na haska na fita ko Ummani ce ke kira, sai naga ashe a wayar ne kira ke tafiya.
Tsaki nayi na kashe kiran na koma kan sallayar, kiran ya ƙara shigowa raina a ɓace naja tsaki na ɗaga,"Ina jinka lafiya kira ya wannan lokacin kamar wanda ke bina bashi".
Muryarsa na shaida tsananin damuwar da yake ciki yace,"Muna asibiti ne Zahrau ce ke naƙuda, kin ganmu tun tara amma har yanzu shiru. Shine na kiraki don Allah ki sakata cikin aduarki, na san sallah kike yanzu. To don Allah kiyi mata adu'a sosai kin ji bana so wani abu ya sameta ita da yaran".
Nayi shiru zan sauke wayar a kunne yace,"Don Allah Habibty, kinga shekara cikin ta goma da aure sai yanzu Allah zai bani haihuwar nan, ko ba don ita ba kiyi saboda mijinki, nima kar kiyi don ni kiyi saboda Allah Habibty".
Ido na rufe ina jin wani abu na tasowa a ƙirjina, a hankali na ce,"Tom zan yi saboda jalla wa'azza, Allah ya sauketa lafiya. Ka kwantar da hankalinka kaima ka natsu kayi mata adu'ar".
A sanyaye ya amsa da,"To nagode. Na so ma ace kina nan, ya jikin Baban na ku da sauƙi ko?".
Ban amsa shi ba na kashe wayar na ci gaba da ibadata ina roƙawa mahaifina lafiya da kawo mana sauƙi cikin halin babun da ake, Haka kuma na haɗa har da ita me haihuwar nayi musu adu'a. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR08FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Baccin yammar da bai saba kwatata shi ya ɗebe shi bayan sun gama gurzar soyayyarsu, da ƙyar Zahra'u ta raba jikinta da nasa ta tashi tana jin jikinta duk ciwo, nan ta fita ta barsa ko motsi bai yi. kuma ba shi ya farka ba tun bayan la'ar sai da aka fara kiran magriba Zahra'u ta zo ta tashe shi. A da sabon sa ne bai baro masallaci sai anyi isha'i amma tun da ya auri Zahra'u ba ya izama, ana idar da magriba zai dawo idan anyi isha'i ya ƙara komawa, lazimi da sauran karatunka da ya saba yi duk ya watsar.
Yanzu ma ko da ya dawo daga masallacin a ƙa'ida ɓangaren Sa'ida zai wuce, tun da dama shigar lokacin kowacce bayan magriba ne, amma sai yay tsaki fuskarsa na nuna ɓacin rai, sam bai son komawa can, shi da zata taimaka ma ta amince da ya jingine aurensa da ita, zai bata maƙuden kudaɗe, bacin haka ma yana duba abu ɗaya ne shiyasa yake zaune da ita har kawo yanzu, amma shi ganinta ma bai son yi kuma a wajensa batta da amfanin komai tun da har ta gaza samar masa da ɗa, yana ta faman tsaki ƙasa ƙasa ya ƙara komawa ɓangaren Zahra'u.
Ko da ya shiga ɗakinta bai sameta ba don haka ya fito ya nufi falonta, can ya iske su ita da su Inna Zulai da Iftihal, Inna Zulai ta sakata gaba da cewar sai ta tattaka yawan zaman da take yi ya isa haka kam, ya kamata take motsa jiki ko dan ta samu sauƙi wurin haihuwa. Ganinsa ɗin ita kuma ta shagwaɓe fuska tana yin narai narai da idanu, Innar ya gaida su Iftihal ma suka gaida shi kana ya juya ya koma, cikin ransa yana ta adu'ar Allah yasa kar Inna ta hana Zahra'un fitowa tun da tasan yau ya fita a wajenta.
Yana tsaye ya tsurawa ƙofa ido sai gata ta shigo, ya saki ajiyar zuciya yana tafiya wajenta cikin nuna jin daɗi da ɗoki kamar wanda ya shekara bai ganta ba, rungumeta yay yana kai hannu cikinta, idonsa a rufe yake cewa. "Ina tsananin son ku, kune farin cikina, kune rayuwata, kune komaina, Allah yay miki albarka Swty, Na gode Na gode da ƙoƙarinki na samar min cikar muradina, Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya kula min da ke da abin da za ki haifa min".
Sai ya zameta ajikinsa yana tallafo fuskarta yana ƙarema kyawunta kallo. "Nayi miki alƙawarin rabin dukkan abin da na mallaka, sauran kuma na abin da za ki haifa min ne, ni bana da buƙatarsu, babban buƙatata haihuwa kuma na sameki kin sama min ita a lokacin da na fidda tsammanin samu, don haka kin gama samuna da ni da dukkan wani abu da yake mallakina. Ina sonki so mai girma".
Ya faɗa yana sumbatarta a gefen baki, tayi murmushi kawai tana kallonsa, ya kamo hannunta suka isa bakin gado ya zaunar da ita, har ta zauna sai kuma tayi saurin dafa shi ta miƙe jin kamar an tsikareta, nan ta kama yi masa ƙorafin irin ciwon da take ji a jikinta, shi kuma sai faman lallashinta yake kamar zai ciro cikin ya mayar jikinsa. Hankalinsa ya tashi ganin ta kasa zama, ya fita a ruɗe ya kira Inna wadda tana zuwa ta dubi Zahra'u tace da shi,"Ka kwantar da hankalinka kai kam, ba haihuwar ba ce kawai dai alamominta ne na ana kan hanya. Itama dai don raguwa ce".
Innar ta ƙarasa maganar da zolaya, Zahra'u tace,"Ai ko dai Inna a irin wahalar da Babyn nan ke bani Allah ni ba ƙaramar jaruma ba ce".
Innar ta fita tana murmushi, shi kuma ya riƙe hannunta sunata kaiwa da komowa a ɗakin da yake ƙato ne gari guda, kaf ɗakunan gidan albarka, a hankali kuma sai ta fara jin daɗi har da kanta ta buƙaci zama. Ta zauna tana sauke numfarfashi, shi kuma ya duƙa a gabanta yana ta shafa cikin yana kallon fuskarta.
"Sannu Sweety".
Hararar masoya tayi masa, ya kama hannunta ya ruƙo cikin nasa sai zuba yake mata. Idonsa ƙyam kan cikin yake cewa,"Yanzu Sweety da gaske ƴaƴa biyu ne a nan?".
"Ummm kuma duk masu kama da kai ba". "A'a ai dole a samu ɗaya me kama da ke, ni nafi so ma suyo kamanninki, amma dai shi abokina kar yay gajarta irin taki".
Dariya tayi tana faɗin,"Ohh ji son kai, kana jin irin zagin da ƴan gidanmu ke min akan rashin tsayi kuma shine zaka so princess ta biyo ni. Aa itama gwara tayi tsayi kaman naka kasan fa ance doguwar mace rabin kyau. Kuma sannan ma ina so tayo irin idonka kaga ai ka fini manyan ido naka sexy eyes ne suna da kyau a wurin mace".
Dogon numfashi ya sauke yace,"Sweety kinga ni ban samu nayi karatun boko ba, wanda kuma hakan ke damuna. Sam ba zan yi saken da za'a ce Muhammad bai yi karatun boko ba, dama na addini wannan kam gidan suka tarar zan ɗora shi akai Sweety, zai gaje ni in sha Allahu, sai dai ina roƙonki da ki taimaka min wajen tsayawa akansa kiga boko ta kafu akansa".
"Honey son kai? Komai sai kace shi baka saka Pricess". "Ai har da ita na ke nufi. Kinga tun yanzu ma ya kamata muga irin makarantar da ta dace a sa su".
Wayarsa ya zaro a aljihu ya bata yana cewa,"Shiga goggle ki dudduba mana tsadaddun makaratun ƙasar nan, amma wanda ake karatu haiƙan. Ɗazu na gwada yi to ban san me zan rubuta ba, ko ana rubutawa da hausa?".
"Hmm Honey turancin nan fa babu wahala. Ka dai ƙara dagewa akan Jammaje Academy ɗin nan zaka gani har sai kazo ka fini, turanci ai yare ne kana sa kanka zaka koya. Kuma Honey batun school na su ai da ka bari sun zo duniyar tukunna ko".
Fuskarsa ya shafo yana cewa,"Kin san wani abu ma. Ki binciko ƙasar da kike so na kaiki ki sami hutu kamar na shekara guda, kina buƙatar hutawa Sweety saboda ɗaukar cikin yara biyu ba wasa ba ne".
Haka fa suka zauna suna ta lissafi da tsarawa akan rayuwarsu da yaran da za'a haifa, shaf ya mance yana da wata matar ma a gefe, wadda ko tunanin ma Allah ya iya kawo mata haihuwar bai yi, idan ta haifa ɗin kuma bai da wani abu da zai ɗaga yace ya bawa yaran wajenta don komai ya tattara ya baiwa Zahra'u, har ATM ya ɗauko ya bata yace ta ajiye a wajenta na Muhammad ne, duk wata zai dinga saka masa kuɗaɗe a ciki, ba ya so ɗansa yay irin rayuwar wahalar da yay a baya.
Ita dai sai dai tace to, sai ita ta ankare da tafiyar lokaci ma tace da shi lokacin sallar isha'i yayi, ya fita kamar ba zai fitan ba, lokacin da ya dawo ya sameta tana waya da Iyam. Dama da zai wuce masallaci ta kira shi ya haɗata da ita sai yace mata yaje masallaci, shine ita kuma ta kasa haƙurin jiran ya dawo ta ciyo bashin kamfani ta kirata, don ko iya jiran a zo a saka mata kati ma ba zata iya ba, tunda ta kira take ta tambayarta jikin nata tana faɗa mata ai ta kusa dawowa cikin satin nan ma kuwa saboda ta karɓi haihuwar jikanta.
A ƙasan zuciyar Zahra'u tace mahaukaciya ce ta haifan zan yi irin haihuwarku ta marasa ilimi, ke har tunanin ma zan haihu a gida kike da kika fara lissafin za ki karɓi haihuwata, ai wallahi ko da wasa. Dawowarki ma ni bana so don dama ba son zamanki na ke a gidan ba, lokaci ma na ke jira ki koma matsuguninki. Bayan gama wayar tasu ta ankarar da Nazifi tafiyar lokaci, ɗan tsaki yay ɓacin rai na ƙara wanzuwa a fuskarsa ya ce,"Sweety ba na son matsawa daga kusa da ke. Ko na tafi ma gangar jikina ce kawai acan, Ko in kira Sa'ida in tambayeta ta bar mana kwananta? Kinga tana da sauƙin kai zata amince".
Ta ware ido tana kallonsa, cikin ranta ta ayyano idan ita Nazifi kewa wannan ɗibar albarka ai tuni ta zagwanyar masa da fatar jiki. Ko ranar da ya mari Sa'ida a gabanta sai da taji lamarin har ƙasan zuciyarta don sosai ta bata tausayi, Sai dai a nata ganin Sa'idan ce tayi saken da har yake mata abubuwan da yaga dama, da ace tun fari tana taka masa burki wataƙila ya raga mata, wai ma har yana faɗin zai iya tunkararta ya tambayeta ta bar masa kwana akan kishiya? To ba rashin haihuwa ba ko rashin me take yi ya isa ya gwada mata haka in bata masa ɗanyan kai ba. Hure mata iska a ido yay da ƙara cewa,"Ko kin fi so na tafi ɗin? Amma dai ki sani farin cikina da duk jin daɗina anan yake, can wallahi takura kawai na ke yi. Ni dai kima bari na kirata na nemi izininta za kiji da tace da ni to".
Tayi saurin dakatar da shi da danna kiran da yake shirin yi a waya tace,"Amma Honey zamu yi hurting ɗinta ai, kayi haƙuri kaje kar mu ke shiga hakkinta. In dai Babynka ne idan ya zo ma sai kake tafiya da shi can, nima don babu yanda zan yi ne da na maƙale a jikinka mun tafi tare domin bana son rashin jin daɗin da kake yi. Kaga yanzu ita sai ta ƙullace ni take zaton ni ce na ke hanaka zuwa wajenta, kuma zuciya bata da ƙashi sai ta iya ɗarsa mata ta cutar da ni kuma ga Twins tare da ni".
Ta faɗa da nuna damuwa sosai, ai ko ya shiga jijjiga kai yana faɗin,"Ta cutar da ku? Ai kuwa da zaman duniyar nan ya gagareta wallahi, akanki da Ƴaƴana?".
Sai da ƙyar dai Nazifi ya iya tashi ya tafi ransa duk a dagule. Har sai da yaje ya faɗawa Inna kome ake ciki ayi gaggawar kiransa komin dare.
Zaune muke ni da Saudatu da Rumana muna ta hira, sosai zamanta kam ke ɗebe min kewa har bana son ma lokacin komawarta yayi, shiyasa idan aka kira ni daga gida sai na ƙara narkar da murya don su shaida sauƙi fa babu shi, don haka suma bar kiran ta dawo. Agogo na kalla naga har ƙarfe goma, na jijjiga kaina haɗe da yin murmushin takaici. sai ga kiransa ya shigo, haushi yasa nayi biris da kiran naƙi ɗagawa, ban da ya raina min hankali sai yanzu ƙarfe goma tukunna zai baro wajenta, ko da akai magriba naje ɗakin nasa ban gansa ba tsammanina ya tsaya masallaci ne , haka nayi ta zaryan hawa da sauka wai sai can dawowan da zanyi na jiyo muryarsa acan ɗakin nata yana faɗa mata shi fa yana ganin za'a ƙara yawan kwana domin gaskiya kwana biyu nayi masa kaɗan a wajen kasancewa tare da ita, ita kuma me ta faɗa masa Allah masani sai jinsa nayi yana ƙara cewa to ai ita akwai yaronsa tare da ita zama da ita yafi zaman wajena muhimmanci.
Irin wulaƙantanin da yake da nuna mata rashin darajata a wurinta sai dai Allah ya saka min kawai. Don ko satin baya sai da ta yaɓa min magana kan ai yanzu ita ce matar so a gidan, miji bai taɓa ɗaga mata murya ba balle yasa hannu ya mareta ko yay mata gorin haihuwa, idan ina taƙama da Uwar gida ai suna ne kawai domin yanzu ita ce da gida, ranar maganganunta sun ƙona min rai sosai sai dai ban bi ta kanta ba, Saboda banga laifinta ba kome ta gaya min shi yaja min, shi ya bata ƙofa.
Rumana tana dubana tace,"Abba yana kiran waya".
Ban amsa mata ba na miƙe na shiga banɗaki, lokacin da na fito sai ga shi ya turo ƙofa ya shigo yana kiran sunana, ban amsa ba rai a haɗe kamar hadari. Saudatu ta gaida shi ya amsa yana tambayarta ina ina, ta kallo ni sannan ta kallesa tace,"Dama ta shiga banɗaki ne amma gata nan ta fito".
Niko na tako kamar ban san da zuwan nasa ba ina goge ruwan fuskata na nufi wadrobe, Cikin muryar ɓacin rai yace,"Ba ki lura da ni ba ne?".
Ciki ciki na ce,"Na ganka mana". Hakan sai ya ƙara ƙona ransa ya hau bambami, zuciyata ta sosu na ɗora idona kansa, na lura yanzu idan zai yi min faɗa yaci mutuncina idan bai ɗaga muryar da matarsa zata ji ba hakan sam bai masa daɗi ba, ko kuma yayi a gabanta shine kwanciyar hankalinsa. Ko bama ita ba aganina ba dacewa ba ne ya ke min faɗa gaban Saudatu. Sauri sauri nayi wajen zarar kaya, jikina har rawa yake ban ma iya rufe murfin ba na tafi da sauri na fice a ɗakin na barsa nayi ɗakinsa, duk da cewar ba'a son raina ba don da niyyata idan ya neme ni zan faɗa masa ya koma can inda ya baro zai fi masa dan acan aka damu da shi ni bai gabana.
Ina cikin saka kaya sai ga shi ya shigo ɗakin har lokacin faɗan yake yi. "Ban san me kika taka ba Sa'ida da rashin mutunciki na raina ni ya hauhawa, har ina miki magana za ki banza da ni alhalin kina jina, kuma saboda tsabar rashin sanin darajar miji da rashin ilimi ina miki faɗa zaki fito ki barni wato ga kare na haushi ko, kin yi laifi ba zaki iya bada haƙuri ba saboda girman kai".