Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 8

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 8

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 8: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 8. "Ka gane finka sanin ya kamata nayi da aiki da ilimin shiyasa na…

4,480 words

"Ka gane finka sanin ya kamata nayi da aiki da ilimin shiyasa na baro cikin yara, kai a ganinka kana faɗa gabansu hakan na maka daɗi ba burgewa da cinyewa ba ne, domin kuwa zasu daina ganin girman da kake da shi a idonsu ko da ace ɗan da ka haifa da cikinka ne, hakan ma ba tarbiyya ba ne, ƴaƴa mata aka baka kuma wataran aurar da su zaka yi ka kai wa wani...kuma kana ƙara daga murya ne saboda matarka taji, ai gani a ɗakin da gani sai kai kana iya kiranta tazo nan ɗin ba sai ta tsaya iya ji ba, gani da ido ai ya kori ji. Sannan kar ka ƙara alaƙanta ni da kalmar girman kai don ni ƴar Aljanna ce kaima ka sani".

Wai ƴar wannan maganar da nayi sai ta zama ciwo, har yana nuna ni da yatsa yana cewa,"Wato kin yi bakin da ba zan faɗa ba sai kin faɗa kema, to na rantse da Allah zan koya miki hankali, zan baki mamaki dan na lura har yanzu ba ki gama sanina ba".

Nace,"Ina kuwa zan gama saninka Nazifi, ai har yanzu ma ban sanka ba domin kasha gaban tunanina. Kuma duk wannan Bala'in dai da kake akan ka baro wajenta ne, to ka koma mana ai ban riƙe ka ba, ƙarƙarina nayi kallo ranar ƙiyama, wanda ya shiga kwanan wata ai ya san makomarsa Nazifi Mai Kalwa".

Hankaɗa ƙofar yay ya rufe har sai da na tsorata, ya wuce ni fuuu zuwa banɗaki. Na taɓe baki na zauna kan kafet, ai yanzu kam sam bana tsoronsa bana shakkarsa, na daina masa shiru ina ƙyale shi yay duk bala'insa da zai yi, barazana ce kawai na ke jira ya fara kafin itama ya aiwatar. na ɗauko wayata na kunna data, kai tsaye group na ajin koyar da english na shiga don ni yanzu ya fiye min komai da ke cikin gidan nan. Hasalima ina mancewa da ɓacin rai muddin na shiga ina karatuna.

Sai bayan ya fito a wanka yay shigar bacci kana ya zauna yana ce min,"Abincina fa?".

Kamar ba zan tanka shi ba can kuma na ce,"Ina naga lafiyar da zan iya wani girki".

"Kamar ya? Ba kin ji sauƙi ba". "Da na ji sauƙin ban gama hutawa ba ne shiyasa". "Duk ba abin da ku ka ci kenan?". "Mun ci mana". "Kuma sai wanda za'a dafa min ya gagara ba? Da ban kawo na ajiye ba kuma a kira ni da azzalumin miji".

Wani kallo na masa sai kawai na aje wayata na miƙe na fita, ba jimawa na dawo riƙe da ɗan ƙaramin flask na miya da cokali duk a hannu, kan teburin da ke gabansa na ajiye na ce,"Ga sauran da muka rage". Na faɗa yayin da na ke buɗe masa flask ɗin, wata ƴar guntuwar shinkafa ce bata fi cokali huɗu ba, ko ƙaramin yaro yaci ba ƙoshi zai yi ba, ta ƙandashe sanyi ƙalau, Saudatu ce da ƙiwa yau tayi jallof babu cikakken mai da kayan miya, su kaɗai suka ci abinsu don ko ni sai indomie na dafa.

Miƙewa yay bayan yaja tsaki ya fice a ɗakin, nayi guntuwar dariya ina rufe murfin. Sai kusan minti biyar ya dawo da ƙatuwar leda hannunsa, Biredi ne ya fita ya siyo babu shiri, in banda haka sai da sassafe yake aikawa gidan biredi a siyo sabon yi me zafi, ina kallonsa ya buɗe friedge ya ɗauko lemu. Kallona yay nayi saurin ɗauke ido don na san saboda yaji babu sanyi ne, kamar ba zai magana ba sai kuma ce min yay,"Me ya samu firij ɗin?". Ya faɗa yana duba socket.

Ni kuwa ina sane na kashe yau da safe, ai na rantse sai na guma masa a kwanaki biyun nan da zai yi, abinci sai dai ya siyo na waje amma na bar yi masa girki ko yaje can ya karɓo a wajenta. Duk da naga kamar bai jin daɗin girkinta, don ranar nan tana min baƙaƙen maganganu wai idan ma asiri nayi akan ya daina jin daɗin girkinta to nayi kaɗan na rabata da shi. Ni dai ban kulata ba don nafi ga na bawa banza ajiyarta, wayewartata da ake ta faɗa a banza a iska tunda har tana iya faɗa da kishiya, a wannan zamanin wa ke wannan shirmen? Bokon nata ma ai na banza da wofi ne.

Shi kuma sai ya tsiri cewa irin girkin ranar kaza zan yi, don kam dai Alhamdulillah naji daɗin koyon girkin Leemars Mandi, kuma koyon yay min rana sosai. Waya naji yana yi yana cewa da me gadi ya siyo masa leku me sanyi, shi kuma yace masa ai masu shaguna duk sun rufe yanzu. Haka nan bai iya shan lemun ba don ba ya iya shan abu mara sanyi. Naga ya buɗe wadrobe ya ɗauko jakar takardunsa ya zo ya bajesu yana dube dube, nan dai na barsa har na kwanta ma. Sai can cikin barcina naji ya tashe ni, ina farkawa na dube shi da tausayin yanayin fuskarsa na ce,"lafiya?".

Yay ɗan jim kafin yace,"Ko za ki taimaka ki soya min wainar ƙwai don Allah".

Agogo na kalla naga ƙarfe uku da rabi, sai naji ya ban tausayi don duk me imani dai ya san illar yunwa balle shi da ba ya jure mata. Na sauka na fita naje babu daɗewa na dawo da soyayyar wainar ƙwai ƙatuwa har da ɗauko masa lemu me sanyi a ɗakina. Amma saboda mutumin nan baida imani babu Allah a ransa ashe Zahra'u ce ta kirasa a lokacin wai tana son cin wainar ƙwai, ina kallo ya ɗauka ya fita cikin rawar jiki da sassarfa, ji nayi kamar na tashi na iske shi na kifar da wainar ayi duk bala'in da za'ai, amma sai ɗayan ɓarin zuciyata ya hane ni da cewa,"Kauda kai lokaci ne".

Haka nan na kwanta riƙe da gefen zuciyata ina hana kaina kukan da ke son ƙwace min. Ban san san da ɓarawon bacci ya ɗauke ni ba kuma. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar

[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR10FT5* Tsawon kwanaki muna ta fama da jikin Abbaa, Asibitin Aminu Kano suka bamu gado da taimakon Baba Tijjani da wani mutum da ke siyan kaya wurin Abbaa aka samu na biyan gado da sauran abubuwan da likitoci suka nema. Abinci kuwa na kullum Ummansu Hindatu ita ke dafowa ana kawo mana na safe, Maman Yasmin tayi na rana, Anty Khairi tayo na dare, ni da Ummani da Abbayo mu ke kwana a asibitin, ba kullum muke zuwa gida ba saboda yanayin kuɗin mota. Idan ba Yaya Imam ko Yashaik ba ne suke da kuɗi a hannu sosai shine zasu ce muje muyi wanka sai mu dawo.

Ba Abbaa kaɗai da yake ciwon ba hatta mu da muke jinyarsa duk mun rame mun fita a hayyacinmu, don abun biyu ya haɗe mana, shima Kaka jikinsa ya tsananta sosai duk da shi nasa ciwo na tsufa ne. Su Yaya Imam na ta in koma gida abun zai zama da hauka har kwana shida, gwara in ke zuwa ko bayan kwana ɗaya ne, Babanmu ya ce ai tun da mijin ya barni su ƙyale ni, cacar kuɗin mota ma aiki ne. Sannan idan ina gida zan fi damuwa har wani ciwon yazo ya iya kamani. Ba su san ma ni rashin dama ce dama tasa na ke zaune acan ɗin ba, a hakan dai da hankali ba a kwance yake ba nafi jin daɗin zaman akan na koma wancan kurkukun.

Ni dai ban iya cewa da su komai, don na san idan suka yanke magana akaina ko Ummani ba ta iya cewa ba haka ba. Nazifi ya zo sau biyu ya duba Abbaa da jiki, haka wani sa'in da daddare zai kira ya tambaye ni ya me jiki yana magana kamar na tursasa shi. Uhmm sai yanzu ai na ƙara yarda da ake cewa idan iyayenki basu da kuɗi miji ba ya musu kallon daraja musamman in ace shi bana arziƙi ba ne, ga dai shi na gani kan Nazifi yana ganin bamu da komai, wanda kamata yay ace ko bai zo kullum ba ya ke kirana kullum yaji yanda jikin mahaifin nawa yake, haka ma ya taimaka mana da ko na magani ne tun da ai yasan halin da muke ciki, amma duk ba ɗaya tun zuwan dai da yay a gida ya bada dubu goma ɗin nan bai ƙara zuwa ma ko da ruwa ba yace ga shi. Ranar ƙarshe da ya zo yana faɗa min itama Zahra'un sun koma gida wai haihuwar ba yanzu ba sai nan da sati ɗaya, idan bata haihu da kanta ba zasu yi mata aiki.

Iyam ma naji ta dawo amma bata ko kira ni balle zuwa dubiya, gidansu Nazifin ma dai kaf babu wanda yazo min sai jiya ne Lubabatu da Yayan Shago da Amarya suka zo, naji daɗin zuwan na su sosai da kayan dubiyarsu da zasu tafi har dubu biyu Yayan Shago ya bawa Ummani. Da muka yi waya da Safiyya Babansu ya haɗamu da wani babban likita a asibitin, ita ma Ummar tasu ta turawa Ummani dubu biyar tace basa Nigeria da sun zo dubiya.

Yau da muka tashi jikin Abbaan da sauƙi, haka yana ɗan magana yace ayi masa kaza, ko kuma yana son kasa. Har ma da yaji maganata yake cewa har yanzu ban tafi gida ba, Ummani ranta a dagule tace,"Kai dai kaji da ciwon da ke damunka".

Ummani kam yanzu haushin Nazifi take yi sosai, haushin da na san ba lallai ta taɓa daina ganinsa da abubuwan da yake min ba, don ita tana da ruƙo, na faɗa muku a baya tana da tsananin haƙuri amma idan ta ƙullaci mutum akan abin da yaywa ƴaƴanta tofa sai ta Allah. Balle yanzu da ya ƙara nuna mata su ɗin ba komai ba ne du da suna iyayen matarsa. Yau ɗin da Abbaa yaji daɗin jikinsa sai ga ƴan dubiya nata zuwa, wannan ya shigo wannan ya fita, kowanne ya zo da ɗan alherinsa. Dama ciwon nasa na damuwa ne kwana biyu kasuwa shiru idan ya fita haka yake dawowa, shi kuma ba ya iya fitowa yace da ƴaƴansa su taimaka masa ko ya faɗa musu ga halin da yake ciki, a bikina kawai aka yi hakan, amma Ummani ce min tayi sun sha yini da yunwa sai idan Maman Yasmin ta kawo abincin rana da ke kullum sai ta aika, to shine suke tattala shi aci har dare.

Dukanmu ba ƙaramin daɗi muka ji ba da har yace a tayar da shi ya zauna, na saka masa pillow a baya ya jingina da shi. Ya buƙaci na zuba masa tuwon masara da miyar kuɓewa ɗanya da Anty Khairi ta zo da shi. Da kaina na ba shi yana ci ya kuma ci sosai dan ƴar kaɗan ya rage malmalar, yasa Abbayo ya kama shi ya taimaka masa zuwa banɗaki yayo alwala, haka yazo a lokacin nan yay ta ramakon sallolin da ke kansa, bai tsagaita ba sai da ya rama sallolin kwana shidan da yay a kwance.

Ummani dai sai ta kalle shi in ga ta kaɗa kai ta faki idonmu tasa hannu ta share ƙwallarta, cuta ba mutuwa ba amma ni kaina har na sallama da Abbaa, don ko yanzu irin abubuwan da yake tamkar mai yi mana bankwana. A hankali na ke sa gefen hijabina na goge hawayena. Abbaan da kansa yake jan mu da magana har dai muka saki jikinmu saboda yacca yaga duk mun ƙara damuwa jikkunanmu sun yi laƙwas.

Da zolaya yake cewa da Ummani,"Hajiyar Salman ana tsoron zaman takaba ne".

Tace da shi,"Kaga ni dai rabani da wannan zancen. Naga alamun ma ka samu lafiya bara na yiwa likita magana ya zo ya bamu takardar sallama".

"Ehh fa dai kirawo shi ɗin su bar cin kuɗin Ƴaƴana haka. Amma kafin nan kunto kuɗaɗen da ke bakin zaninki".

"Ehh lallai kaji sauƙi tun da har ka iya saka ido. Mutum duk ya ɗagawa mutane hankali, ga ƴarka nan duk ka ramar da ita, ko da yaushe a kuka take abinci bata iya ci".

Abbaa ya zuba idanuwansa akaina ko ƙiftawa bai yi, ni kuma ina ta ƙoƙarin gusar da tsantsar damuwar saman fuskata ta dole, don bana so ya hangi abin da zai ɗaga hankalinsa tun da gaskiya rabon da nace na zauna irin haka gabansa yay min kallon ƙurilla da fahimta irin wanda yake min yanzu anfi shekara uku, kuma don dai yaji daɗi sai na ɗago ido ina kallonsa da murmushi na ce,"Sannu Abbaana Allah ya ƙara maka lafiya".

Ya amsa da amin yana saka min albarka gaba ɗayanmu da su Anty Khairi. Ya kalli Ummani yana ce mata,"Kinga da Sa'ida ta zama likita irin wahalhalun asibitin da muka sha da duk mun samu sauƙi, to Allah bai nufa ba".

Ummani tace,"Umm Kana naka Allah na nasa, bai rubuta faruwan hakan a kundinta ba ne".

Nasa hannu na goge hawayen da ya zubo min. A hankali naji Abbaa na cewa,"Shi fa gidan aure gida ne na yaƙin neman Aljanna, sai mace ta yi haƙuri bana wasa ba kana take iya jin daɗinsa har ta iya samun Aljannarta. Na jima ban miki kallo irin wannan ba Sa'ida, sai dai yau ɗin fuskarki ta shaida min kina cikin wani hali a matsuguninki, wannan ramar taki ba ta sauƙi ba ce, na tsorata da ita ƙwarai, ina ga ba kiga yanda kika ƙare ba ne ko? Na san mahaifiyarki na sane da duk irin halin da kike ciki, nima kuma daga baya duk na fuskanta, na san kin san waye mahaifinki a ɓangaren iya takun yin bincike. To kamar yanda na ke faɗa miki ko da yaushe a baya yanzun ma zan ƙara nanata miki. Ki ƙara haƙuri akan wanda na san kina yi, kiyi haƙuri kiyi adu'a sune kawai jin daɗinki, haƙuri ba ya yawa ba ya janyo danasani da nadama, haka adu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza, Sa'ida babu wanda ya yake nasara ba tare da yay haƙuri da juriya ba, don haka ki zama me tawakkali da duk halin da kika tsinci kanki kin ji. Sauƙi a wurin ubangiji ya ke, tsanani da akasinsa basa dawwama, da sannu labarin zai canja komai ya shuɗe".

Ina hawaye sosai na ce,"To Abbaa ka yafe min, don Allah ka yafe min akan...".

"Ni ai tuni na yafe miki. Amma a dinga kulawa, a dinga kai zuciya nesa, a daina ɗaukar huɗubar shaiɗan, in ka cutar kaima za'a cuceka. Allah yay miki albarka, Allah yay miki albarka ya lulluɓe dukkan rayuwaki da farin ciki mara yankewa".

Na ce,"Tom Abba, na gode Allah ƙara lafiya yaja kwana".

Shiru na ɗan sakanni ya ƙara cewa,"Ya wajen abokiyar zaman na ki, kuna dai zaune lafiya ko?".

Na kasa riƙe kukan da ke maƙale, ina fitar da shi na ce,"lafiya muke Abbaa".

Sai naga ya ɗan murmusa yana jijjaga kai kafin yace,"Ma sha Allah, sai aci gaba da zama lafiya kin ji".

Da magriba sai ga Nazifi ya zo duba Abbaa, ni na fita na shigo da shi. Ummani dai babu sakin fuska ta amsa gaisuwarsa sama sama, Abba yace da shi ya zauna. Yanda yake yi dai irin a gurguje yake don ina lure da shi, tun da yake zuwa bai taɓa zaman minti biyar ba, da ya zo an gaisa yace ya me jiki aka ce da sauƙi zai ce to ya tafi. Abbaa ya shiga tambayarsa akan zancen plazarsa yace ai Alhamdulillahi adu'arsu ta amsu komai yanzu ya daidaita, Abbaa na nuna jin daɗinsa yake ta jero masa adu'a da fatan alkhairi.

Yana daɗa dubansa yace da shi,"Amma dai baka samun wata hatsaniya daga wurinta ko? Yanzu ba ita kaɗai ba ce kuma nasan lamarin ƴaƴanmu a zama irin haka".

Kansa a ƙasa yana juya muƙullin hannunsa, wani abu yake so yace da dukkan alama, to ƙila sharrin ne bai gama haɗuwa a ran nasa ba shiyasa yay murmushi kawai bai ce komai ba. Abba ya ƙara cewa,"Hakan ya shaida min akwai matsalar kenan, dama na san dai kana haƙuri ne, to ai na faɗa maka duk san da tayi maka laifi ka zo ka sameni hakan umarni ne ba ƙararta ka kawo ba, idan tana ganin tafi ƙarfinka ai mu bata fi ƙarfinmu ba. Allah yay maka albarka, haƙurin da ake Allah ya bada lada, sannan ayi ƙoƙarin kwatanta adalci nauyin da ke kanka yanzu yafi na baya, tsakiyar mata biyu kake don haka sai kayi da gaskiya saboda lahirarka".

Kansa na ƙasa yake cewa da Abbaa zai wuce. Ba dan idon Abbaa ba da bai isa na bi bayansa da kallo ba, ba da son raina ba ha na miƙe na fita raka shi, ko ƙofar ward ban ƙarasa ba na juyowata dama yana gaba ne ina bayansa kuma da nisan tazara tsakaninmu. Ina komowa Abbaa yace da ni,"Ba tare zaku wuce ba?".

Maƙot na haɗiye dunƙulen yawu na ce,"A'a Abbaa, ai da yake gidan ma babu kowa itama an kwantar da ita a asibiti zata haihu".

Ashe tsautsayi ne ya ɗebe ni nayi wannan maganar, Ummani nata min sigina ban lura ba. Sai ce yay to ai wannan rashin hankali ne ace abokiyar zamana na asibiti zata haihu ban je na dubata ba kwata kwata, ban da abuna ma ai sai ace baƙin ciki na ke da haihuwartata. Saboda haka na tattara abin da zan tattara na bi bayan mijina shi kam ya yafe zaman kula da shi ai yaji sauƙi. Idona ya cika da tarin hawaye, babu abin da zan ɗauka dama, Ummani na kallona da tausayawa tace,"Abbansu da ka barta sai ta tafi da safe. Ko abinci ma bata ci ba".

Ai fa nan Abbaa ya hauta da faɗa sosai akan me yasa ita bata san abun da ya dace ba, dama su iyaye mata sune ke ɗaurewa ƴaƴa gindin yin abin da suka ga dama a gidan aure, kuma sai auren ya mutu su zo suna kuka ana ganin laifin miji. Faɗa fa kamar ba majinyacin da ke kan gadon asibiti ba. Ni dai ina ta kuka na ce,"Ummani sai an bani kuɗin mota na san yanzu ya rigada tafiya. Kuma ma ban san asibitin da suke ba wayata babu kuɗin da zan kira shi na tambaye shi".

Ana haka Abbayo ya shigo, Abbaa ya kalle shi yace,"Kai da kuɗi a hannunka?".

Yace,"Ehh akwai". Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ɗebo kuɗi.

Abbaan yace da shi,"Nawa ne?". Ya shiga ƙirgawa kafin ya ce,"Dubu ɗaya da ɗari uku ne".

Abbaa yace,"To ara min ka bawa wannan yarinyar. In wayarka da kuɗi kira mata mijinta".

Abbayo yace,"Ai da zan shigo na gansa bakin motarsa, ina ce ma ko ita yake jira".

"Ehh kira mata shi ɗin dai".

Abbayo ya miƙo min wayarsa na saka lambar na kira, kamar me jiran kiran kuwa bugu ɗaya ya ɗauka duk da na san baida lambar, ya ɗaga yana sallama, na amsa ina cewa da shi,"Ka tafi ne?".

Jin muryata munafuki sai ce yay,"Ya za'ai na tafi kema ai kin san jiranki na ke yi. Kin san an kusa shiga da ita ɗakin tiyatar ya kamata muje da sauri".

Ƙit na kashe wayar kafin ya ƙara karanto abin da zai haɗa ni da mahaifina, na miƙawa Abbayo wayar hannuna na karkarwa ganin kallon da Abbaa ke watso mini. Nayi msu sallama zan wuce ina maidawa da Abbayo kuɗinsa sai Abbaa ce yay.

"Rike kije da shi. Kuma kar da ki tafi ki ɗorawa kanki damuwa, ni na warke gobe ma a gida za ki jini".

Ummani ta rako ni har waje ranta duk babu daɗi, tana ta bani haƙuri da ƙara yi min nasiha. A bakin mota na same shi yana ganina ya murmusa da cewa,"Ai dama ma san Abbaa zai ce ki biyo ni. To ki ga hakan ai yafi, rashin zuwanki ɗin sai a fara ƙananun maganganu kin san halinku na mata, yanzu ace kina baƙin cikin haihuwar ne".

Na ce,"Ai ba su kaɗai ba kaima kana iya faɗa, yanzun ma ai shaguɓe kayi".

Sai yaji haushi akan me zan faɗi hakan. Tun da muka shiga motar ban ce da shi ƙala ba, duk da yana ta jana da magana yana ta faɗa min irin wuyar da Zahra'un ke sha. Wai ai har sai da aka haɗa da saukar ƙur'ani saboda an ce asiri aka yi mata akan karta haihu ana so a kwantar da cikin, yana faɗar hakan na ɗago na kalle shi, ban iya yin magana ba yaci gaba da bayani wai so ake ma a raba auren asirin dai da ake tayi babba ne. Ni kuwa kamar na tambaye shi sai kawai nayi shiru. Sai da muka ɓata wajen awa ɗaya akan siyesiye da yake tsayawa yi, ya saya wancan ya siya wancan, ni ko bana ganin laifinsa dole yayi ɗoki tun da ya jima bai samu haihuwar ba, Ya tambaye ni ko ya siya min abinci nace a'a na ƙoshi.

Wani babban asibitin kuɗi ne a nasarawa GRA, haɗuwar asibitin kaɗai zai shaida maka asibiti ne na masu hannu da shuni, haka yake faɗa min kwanciyar duk kwana ɗaya dubu ɗari yake biya. Na ce to Allah ya ƙara horewa yace amin.

Su Iyam muka fara gani a ƙofar ɗakin tsaye da alama ma sun dawo daga rakiya ne, sai da suka gama gaisawa da ɗan nata kana nima na gaisheta ina cewa sun dawo lafiya, fuska babu annuri ta amsa kamar nayi mata dole.

"Sai yau kika ga damar zuwa kenan".

Banyi mamaki da furucinta ba, sai na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na san ta girgiza da shi, na rasa me zan ce ma, tabbas da na san zata yi min wannan furucin ko gaisheta ba zan yi ba wallahi. Sai shine yace da ita,"Ina ga kin sha'afa na faɗa miki an kwantar da Babansu a asibiti".

Ni kuwa idan yana Babanku ko mahaifina mamaki yake ba ni, da yanda na ke kiran mahaifina haka shima yake kiransa, Abbaa sama Abbaa ƙasa. Tahowar nan tamu da suka yi waya da Baban Zahra'un tamkar zai yi masa sujjada, amma ni da yaje wajen mahaifina gaisuwar ma ina ga so yay Abbaan ya gaida shi.

Iyam tayi min wani kallo tace,"Oh anyi haka yo na mance ne, Allah shi sawwaƙe. Amma ai da ko sau ɗaya kya leƙo ki duba ita me naƙudar ba wai ki nemi wuri ki zamanki ba".

Ina murmushi me ciwo na ce,"Da yake abin da ya shafeka shi ya dameka".

Yaya na tsaye ita dama ban ma yi karambanin gaida ita ba, muna shigowa da ta ganmu da shi ta ɗauke kai. To me zata ba ni? Don haka ban ce mata komai ba, haka ko ya mai jiki itama bata iya ce min ba duk da taji ana zancen. Ya bani leda yace na shiga ɗakin na kai musu ƴan uwan Zahra'un na ciki, na shiga na samesu da yawa sunata hira da dukkan alama ma sun mance a halin da ƴar tasu take ciki. Muka gaisa suka amsa min kadaran kadahan, na ajiye musu ledar nace in jishi sannan na juyo na fito don ba zan juri irin kallon banzan da suke yi min ba, haka na zauna can gefe kan wata kujera ni ɗaya, idan ka ganni sai kayi zaton marainiya ce gaba da baya.

Shi kuma yana ta kai komo zuwa ofishin likita, hankalinsa duk yaƙi kwanciya, daga baya kuma sai ga shi ya dawo ya zauna wajena yana ta roƙona in ke yiwa Zahra'u adu'a. ƙarfe goma da rabi ana shirye shiryen shiga da ita ɗakin tiyata sai ga wata Nos ta zo wajenmu, ganinta muka miƙe a tare da shi ita kuma tana tambayar,"Kune ƴan uwan Zahra'u Abdullahi?".

Da sauri ya ɗaga kansa da cewa,"Ehh mune, an shiga da ita tiyatar ne?".

Kafin tayi wata magana tuni su Iyam suka ƙaraso wajen, ban san me ta gani ba ta dafa kafaɗata tana murmushi tace,"Ta haihu an samu ƙaruwar ƴaƴa biyu duka mata, ina taya ku murna".

Ai ji nayi kamar ni aka ce na haihu, don ban san lokacin da na kama murna ba, haƙorana talatin da biyu du a waje. Su Iyam aka yi hamdala su Yaya ma sai murna aka tafi sanar da ƴan uwanta don su suna cikin ɗakin ba su san wainar da ake toyawa ba.

Shi kuma yana ƙara tambayar Nos ɗin,"Babu namiji duka mata ne?".

Ta ce,"Ehh duka mata. Ba da jimawa ba za'a fito muku da yaran ana gyara su ne".

A iya zamana da Nazifi ban taɓa ganinsa a cikin tsananin farin ciki ba kamar yanzu, don zubewa yay kawai ya miƙa sujudu shukur. Bayan ya ɗago kuma sai ya dube ni yana,"Kinga lamarin Allah ko, mahaƙurci mawadaci, da nayi haƙurin kinga lokaci guda ya bani har guda biyu, nan gaba kuma na san zai bani abokin me taimaka min in sha Allahu. Ki tayamu murna Sa'ida".

Ina murmushin jin daɗi dan na mance ma ni da wata damuwa na ce,"Ina tayaka murna Allah ya raya mana, yay musu albarka".

Kowa dai a wajen murna yake, sai dai duk ana ce musu babu namiji sai naga jikinsu yay la'asar, haka ma Iyam tun da aka ce duk mata ne fuskarta ta sauya alamun ba hakan ta so ba. Ba'a jima ba sai ga Nos biyu tare da yaran, ya tafi da sauri ya karɓe su, bakinsa yaƙi rufuwa yanda ka san gonar auduga, wato Allah ɗaya yasan farin cikin mutum ke riskar kana a ciki idan ya sami haihuwa, haka ga wanda Allah bai ba shi ba Allah ɗaya yasan irin abin da yake ji a tare da shi, da taimakon Nos ɗin ɗaukan yaran ya daidaita a hannunsa. Likita yazo yace da shi,"Zasu nuna muku ɗakin da aka sauya mata, sai dai a yanzu mutum ɗaya ne zai iya ganinta sai nan da wani lokaci kowa ya iya shiga".

Muka ɗunguma duk muka bi bayan Nos ɗin da ke mana jagora zuwa ɗakin, Shi dai ya kasa ma bawa kowa yaran duk suna hannunsa, bayan ya gama yi musu kiran sallah ne yay musu huɗuba tsautsayi yaja ni na miƙa hannu zan karɓi ɗaya sai ce yay min,"Yi haƙuri bari su fara jin ɗumin jikin mahaifiyarsu tukunna".

Ya faɗi hakan yana shigewa ciki, Na jiyo Iyam na faɗin,"To ai ko saboda ma ta tofe yaranta da adu'a gudun masu cutarwa wani ba ya ɗauke su ba ita bata ɗauka ba". Sai lokacin na dawo cikin hayyacina na shiga hankalina na daina ɓarin jiki, don haka na koma gefe na rakuɓe. Ta glass ɗin tagar ɗakin na ke hango yanda Nazifi ya haɗa yaran da uwarsu ya rugume yanata sumbatarta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull