Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 9

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 9

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 9: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 9. Sai bayan awa guda kana muka shiga ciki, aka baibayeta kowa na mata…

4,472 words

Sai bayan awa guda kana muka shiga ciki, aka baibayeta kowa na mata barka. Ta kalle ni muka haɗa ido da ita, murmushi na sakar mata ita kuma lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya daga farin cikin da take. Sai da ƙyar aka bani yaran na ɗauka, don nunawa ma suka yi basu san ina wajen ba, sai da Innarta ta karɓeta su ta miƙo min tukunna. Kallon yaran kawai nake yi ina jin kamar kar wani ya karɓe su, na yi adu'a sosai na tofa musu, haka kawai naji soyayyarsu ta rufe ni, ma sha Allah kyawawa da su farare tass, ga hanci har baka irin na mahaifinsu, dukansu kamar su ɗaya da mahaifinsu ni dai ban ga ta inda ma suka yi kama da Babarsu ba banda haskenta da suka ɗauko.

Na shagala a kallonsu Yaya ta zo ta karɓe su daga hannuna tana faɗin ai daga haihuwar yaran ba'a dinga jagwalgwala su ba. Haka ina ji ana ta yada min magana, wata cikinsu na cewa da Zahra'un tayi mamaki da taga duka mata, da aka yi scanning ai mace da namiji aka ce.

Sai wata da bata jima da zuwa ba kamar ma Yayarta naji suna cewa, tace,"To kin manta kishiya ce da ita, kishiyar ma juya, ai dole za'ai ƙulla ƙullar ganin an hana haihuwar namijin. Irin basu da imani, basa zama kullum a tafe suke cikin jeji, kuma fa tun da ta samu cikin nan nake cewa da ita ta dage da adu'a kar tayi sakaci don yanzu kishiyar zata iya hanata haihuwar ma, kinga dai irin baƙar wuyar da ta sha ai kwana kusan goma ana naƙuda, nayi imani asiri tayi mata ta so kwantar da cikin, to sai Allah yasa mu ƴan uwanta ba zaune muke ba tafe muke muma".

Maganar ta soki raina, nayi ƙasa da kaina ina ambaton Allah. Ina jiyo ana kwaɓarta da cewa tayi shiru gani can zaune, sai ta kallo ni tana cewa,"Au wai ita ce ma kishiyartata? Ni wallahi ce nake wata cikin ƴan aikin gidan ne. Tabɗijam".

Iyam ma ta kawo ruwan rubutu tana cewa a bawa Yaran wai saboda mahassada kar su cutar da su, tun da ba kowa ke murna da zuwan na su ba. Gaba ɗaya sai naji na tsani kaina, kamar na tashi na fita to amma me amfanin fitar? gwarama na zauna tun da magangunsu dai ba fito min a jiki zasu yi ba. fatana ɗaya kar Nazifi yace anan zai barni na kwana don ban san ya zan yi ba. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR12FT5* Wuri na samar mana can gefe da su Fati muka zauna kan wata kujera. Zamanmu Rumana ta takura akan muci gaba a game ɗin, ni kuma gaba ɗaya raina a dagule yake, sai ji nayi Anty Aisha da su Basira na faɗin,"Yo dama juya ai bata da wani daraja a wurin miji".

Na ɗago ido na kalli ɓangaren da suke, ban san wacece ɗayar ba amma dai naga har da ƴan uwan Zahra'u su uku da na sani. Suka ɗora da maganar da Anty Aisha ta dire. "To ai kinga ita yanzu duk wata dukiya da aka mallaka tata ce. Me haihuwa da mara haihuwa darajar ai ba ɗaya ba ne, ita fa me haihuwa gaje gida take yi, ta mallake miji da komai nasa, soyayyarsa ta zama tata gaba ɗaya, kuma a dangin miji za ki ga ita ce ƴar lele, kinga dai ita Zahra'un ai ko mutuwa yay ƴaƴanta sun mallaki komai ɗinsa, kuma ko a yanzu dai kinga ƙiri ƙiri ai ya na nuna yafi damuwa da ita akan uwar gidan".

Ni kam jin su kawai nake yi zuciyata nata min ba daɗi, A wannan lokacin na samu kaina cikin tsananin son haihuwa. Sai dai a gefe ɗaya cike na ke da tsoron duniya da mamakin halin ɗan adam, wato shi yana maraicin rashin ƴaƴa, yanzun kuma da Allah ya ba shi amma har an fara maganar mutuwarsa da gadonsa, ba ma ƴan uwan matar ba kawai har da nasa ƴan uwan, lallai duniya. Sai dare Nazifi yazo muka tafi, haihuwan da kwana uku aka sallamo su, cikin wannan kwanakin kam na aikatu, abincin safe rana dare duk nice, jama'ar Iyam a ƴan barka duk ni ke ɗawainiya da su. Ban taɓa nuna ɓacin rai ko gajiyawa ba, ni ina yi ne ma ina roƙon Allah da nima ya dube ni ya bani ko da ɗaya ne.

Sai bayan dawowan na su na samu ɗan sararawa hakan ma ban wani hutawa kawai dai aikin ya ragu, tun da suka dawo kuwa ban ɗauki yaran nan ba duk sona da na ɗauke su, tsakanina da su kallo ne daga nesa, ko kusa da su na tunkara Kakarsu ta ɗaga min murya, sau ɗaya ne ma na shiga ɓangaren Zahra'un sai ce tayi yanzu suka gama shan nono suka kwanta, kuma ba'a ɗaukarsu idan sun sha nono saboda tumbuɗi suke yi. Kullum da anyi musu wanka ake miƙa su wurin Kakarsu, ita kuma ko Uban ne ya dawo sai tace ya ɗauke su iya nan ɗakinta kar yaje can wani waje da su a cutar mata da jikoki, to yanzuma in ya dawo har sai nayi bacci bai shigo ɗakin ba, abinci ma can ɗakin Iyam ɗin yace na ke ajiye masa, tun da ba ya rabuwa da yaran sai kusan sha biyu ƙarfe ɗaya yake kaiwa uwar su.

Ummani da Maman Yasmin da Anty Khairi suka zo barka, a wajenta kuwa an musu tarbar mutunci don wata Yayar Mamarta da Inna suka yi ta godiya da kayan barka, riguna ne set biyu sai turmin atamfa guda biyu amma kace akwatun kaya guda aka kai musu. Da muka je wajen Iyam kuwa haka ta nuna tamkar bata san Ummani ba, kamar ba Iyam ɗin da shekara goma baya ba ta laƙabawa Ummani Ƙawata ƙawata, ta ɓata fuska tana faman amsa musu gaisuwarsu a wani daddaƙile kamar waɗanda suka zo neman taimako wurinta, sosai zuciyata ta sosu, na tabbata da ace jariran ma suna wurinta ba lallai ne ta basu ba, har wani cewa take da Fati tayi sauri ta kunna hayaƙi saboda masu zuwa ba'a san da irin manufar da suka zo ba, Maman Yasmin tsabar ɓacin rai sai da ta so ta gaggaya mata magana Ummani ta hanata.

Ranar suna kuwa wani shagalin taro aka haɗa zan iya rantsewa tsayin rayuwata ban taɓa ji anyi shi ba da dai sunan wai taron haihuwa, duk kuwa irin kuɗin masu kuɗi, duk irin tarukan sunan da nake jin labarin ana yi. Waterfall event center aka kama da naji ana batun miliyoyin kuɗi aka saka a iya kama wajen kawai ban da kuɗin abinci da sauransu, ni ban ma san da cewa ba'a gida za su yi taron ba sai da azahar na shiryo na fito naga suna tafiya, sai kuma ga Rumana tana ce min na bata sabon kaya wai za su tafi wurin suna. Kuma sai da na shiga IG ne ma na ke ganin vedio har ya fara trending, abun ya ƙayatar da ni matuƙa da ke zuciyata babu baƙin ciki, ga shigar da aka yiwa yaran ma sha Allah kamar ka sace ka gudu, ni dai sai naji na ƙara jin sonsu a raina, jama'a a hall ɗin kuwa tamkar kaji an cika maƙil, shi da matar shigar kaya kala ɗaya suka yi, kowanne fuskarsa da annuri yana riƙe da ɗaya itama tana riƙe da ɗaya, shi ya saka shadda dakakkiya ita kuma ta sanya wani arnan less da shi ɗaya ya isa ɗaukan ido a wajen, ina kallon bidiyon ina murmushi ina hawaye.

Ina sama sai na sakko ƙasa saboda gidan ni kaɗai ce, sai da na sakko ne ma naga ashe su Marawiyya sun dawo, na samesu suna faɗin irin watsi da nerar da uban ya dinƙa yiwa yaran da uwarsu, kyauta kuwa da aka dinga bawa yaran ba'a magana, shi kansa sai da ya bada atamfofin chiganvy aka rarraba. Har yaywa mahaifiyar yaran kyautar mota dalleliya. Haka kawai naji ba zan iya ci gaba da zama ina jin labarin na su ba, na wuce ɗakina na ƙasa ina jin kamar ina so nayi kuka, ina shiga na kashe wayata kawai na kwanta ina ta tasbihi cikin raina saboda kawar da abin da shaiɗan ke neman dasa min.

Basu fara dawowa ba sai bayan isha'i, lokaci ɗaya gidan ya kacame da hayaniya. suna kan hanyar dawowa ya kira ni yace na shirya zamu je akaiwa Malam yaran, nace masa to. Bai ma shigo gidan ba ya turo aka kira ni, na isa motar na sameta hakimce a gaba, sai naga ai cin fuska ne ace ni na zauna a baya, don haka na tsaya daga bakin motar har ya dawo daga sallamar wasu ƴan ƙauyensu, Iyam ta aiko masa a basu kuɗin mota.

Ya dube ni yana hararata yace,"Ba ki je wurin suna ba motar ma ba za ki shiga ba?".

Nayi guntun murmushi na ce,"Ina da muhimmancin da za'a ce naje suna ne? Ko ina da arziƙin da za'a faɗa min abin da aka shirya? Rashin zuwan nawa ai bai hana kun yi yanda kuke so ba. Ita kuma kayi mata magana ta dawo baya".

Ganin zai ɗaga min murya yaci mutuncina gabanta gaban mutanen unguwa na ɗaga masa hannu kawai na buɗe bayan na shiga. Da muka je gidansu ashe can mutanen ƴan uwan Iyam gayya guda ta gayyato, Ah to kuwa Nazifi ya shekara goma da aure bai haihu ba ai dole ayi shagali ban ga laifin su ba. Ni na ɗauki Noor me sunan Iyam da ubanta ya miƙo min ita da muka shigo, Iman ɗin kuma tana hannunta, abin sha'awa idan ka kallemu sai naji inama ace kanmu haɗe yake kamar ya da ƙanwa. Wurin Gwaggoje muka fara shiga muka gaida ita, sannan muka je ɗakin Amarya kai matar nan da mutunci yana yawa zancen kirkinta yay yawa. Ummaa kuwa dama a falo muka sameta ita ce ma taje ta isawar da Malam cewa mun zo, da ke ita ke da girki, ni tun da na gaida itama bata ƙara bi ta kaina ba sai karɓar Noor ɗin tayi tana cewa ga yanda ake ɗaukar yaro hakan da nayi ai sai wuyan yarinyar yay ciwo, kuji haɗin masifa don Allah.

Ana haka kuwa Yayan Shago ya iso wurin, cikin barkwancin nan nasa da zolaya yake cewa Hassana da Hussaina matan Alhaji Ƙarami uwayen Hassana da Hussaina. Ni dai murmushi na ke muka gaisa da shi, ita kuwa ta haɗe rai da ƙyar ma suka gaisa. Bata san shi ɗan ba ruwansa ba ne yana tsokanarta ya ce,"Amma dai Amarya kin bawa Yayar taki ɗaya ko?".

Kanta a gefe tana ƙara haɗe gira sama da ƙasa tace,"Wace Yayar tawa? Kuma akan me zan ba da abin da ba'a tayani naƙuda ba, ita ma macece ai ta haifi nata mana".

Da yake shi ba baƙon zafi ba ne yay ƴar dariya yana ce mata,"Maida wuƙar Amarya, Allah ya raya mana sai an kawo min kwanon nama na".

Yana barin waje na ce da ita,"Kiyi haƙuri fa shi haka yake da wasa".

Bata tanka min ba sai faman kallon ƴarta da ke hannuna take. Sosai Malam yayi murnar ganin yaran, ya tofe su da adu'oi kafin ya miƙo mana su, bayan mun gama gaisawa ne sai muka ji ya fara faɗa, ya tasa Nazifi a gaba kamar zai cinye shi ɗanye, wallahi ni ban taɓa tsammanin ba zai yi masa mugun duka ba, dama shi mutum ne me zafi, Ƴaƴan duk tsoronsa suke yi, bana mantawa da ko hira ake aka ji sallamarsa sai kowa yay ɗif, gyaran muryar Malam kawai zaa ji a natsu, shi kansa Nazifin tun kan aurenmu yasha faɗa min da ka aikata laifi Malam ya sani gwara baka ma fara aikatawa ba, ga fadansa ba ya wucewa.

Kuma yana da sakin jiki da ƴaƴansa kawai dai yana da faɗa. Ni Iyam ce dai da ta fanɗare masa yanzu, amma ko ita da ai mugun tsoronsa take ji, kuma duk rashin lafiyar nan da yay ne yay sanyi dan ni dai nayi mamaki ace Malam ya iya barinta zama a gidanmu. Haka yay ta faɗa jikina har rawa yake, yana cewa ashe zaluncin da ya ke bugawa a cikin gidansa babba ne, to an same shi an zayyana masa from A-Z.

Yana nuna shi yace,"To Nazifi idan shiryawa tashi ranar ƙiyama da shanyewar ɓarin jiki kayi to kaci gaba da duk abubuwan da kake yiwa matarka. Ita kuma uwar taka da taje can ta tare ta zama fitina a tare da ku, zata zo har inda na ke ta same ni, wallahi Nazifi ka sani sai na mugun saɓawa mahaifiyarka, ka dai san sarai waye ni".

Muka haɗa ido da shi, ko bai ce ba na san tunaninsa ni na kai ƙararsa, gabana naji yana ta faɗuwa don ni har ga Allah ba'a taɓa faɗa irin haka a gabana ba, kuma ban taɓa ganin ana yiwa babba kamar Nazifi faɗa ba don haka duk sai nake jin tsoro. Malam ɗin ya kira sunana yana cewa,"Ke kuma Sa'ida me yasa ba ki taɓa zuwa kin faɗa min abubuwan da yake miki ba? Da ba sai ki bar masa gidansa ba don ubansa tun da shi ɗin me rama alkhairi da sharri ne. To daga yau duk abin da Nazifi yay miki na rashin kyautawa na sahale miki kai tsaye ki kirani a waya, zan tabbatar masa da ni Bala Mai Kalwa ubansa ne kuma mijin uwarsa".

Ya ƙara komawa kan Nazifin da cewa,"Ina iliminka Nazifi? Kaf ƴaƴana babu wanda na ke alfahari da shi irinka ashe zaka bani kunya, ashe kayi watsi da addininka, har abun duniya ya iya rufe idanuwanka, ita uwar taka idan tayi tsufan da ya ɗebe tunanin yakamatanta ba sai ka nusar da ita daidai ba. To wallahi kaji na rantse idan baka saita zaman gidanka ba ka zama adali tsakanin matanka ba zaka sha mamakina, domin ina mai tabbatar maka da akan yarinyar nan Sa'ida zan iya yafe ka. Ai ni ban mancewa da halacci".

Kuka na saka kaina a ƙasa na ce,"Don Allah kayi haƙuri Malam, duk ba haka ba ne, ba yanda aka faɗa maka ba...".

Katseni yay da ɗaga murya,"Rufe min baki, saboda kina da tsananin haƙuri shine za ki kare shi, ki zauna suna cutar da ke".

Ni ban ma san yanda zan kwatanta maku irin faɗan da Malam ke yi ba. Nazifin ya hargitse sai haƙuri yake ba shi, da ƙyar ya sassauto ya shiga yi mana nasiha mai matuƙar ratsa gaɓaɓan jiki, wanda ni dai irin yacca wa'azinsa ke shigata hawaye kawai na ke yi, shi kansa Nazifin muryarsa tayi rauni, ga irin ayoyi da hadisan da yake janyowa sai da na mugun jin tausayin Nazifi, take kuma naji a zuciyata na yafe masa duk abubuwan da yay min, to nawa rayuwar take ma? Allah kawai ya yafe mana gaba ɗaya.

Malam ma nunawa yay kamar bai san wata Zahra'u ba, muka baro gidan ran kowa babu daɗi, ta karɓe yarinyarta a hannuna tana yi masa kuka wai ana so a shiga tsakaninta da mahaifinsa, shi kuma ya ƙara rikicewa da kukan nata yana faɗin tayi masa shiru don Allah da wanne take so yaji. Tace ita dai koma waye yaje ya ɓatata wurin Malam bata yafe masa ba, sarai na san shaguɓe ta min, ni kuwa har muka isa gida ban kulawa lamarinsu ba, shi ɗin ne ma dai da muka shiga wajen rabuwa zan yi ɗakina yace wallahi matsawar ya bincika yaga da sawar hannuna wajen kai ƙararsa gun mahaifinsa to aurena na yiwa, tun da nake rayuwa da Nazifi a irin uƙubar nan bai taɓa yin furucin da ya dake ni ba irin wannan, wai aurena na yiwa! Kenan zai rabu da ni!

Washe gari ƴan taron suna duk suka watse, gida ya dawo yanda muke da, sai Innarta dai tana nan wacca aka bari zata dinƙa yi mata wanka. Daga baya Mamanta ta zo itama tana da kirki gaskiya domin uwa ce ta gari, tasa aka kira ni tayi mana nasiha, tace kuma ƴaƴan da aka haifa bana Zahrau ba ne kawai nima na ɗauka nawa ne, don duk macen ƙwarai tana ɗaukar ƴaƴan miji matsayin nata ne, don Allah mu haɗa kanmu mu zauna lafiya fitina ba wata abar so ba ce kar mu biyewa sharrin zuciya.

To ni dai zatona samun yaran nan zai kawo canjin zama me daɗi, sai dai ina ashe ba haka ba ne. Zahra'u da Iyam sun mayar da ni muguwa abar tsoro, ban da ikon tunkarar in da yaran suke za su farga suna maganganun marasa daɗi, har cewa suke suna gudu ne kar na lashe kurwar yaran, kullum in har zanga Zahra'u sai tayi min gorin haihuwa, sai ta nuna min ita ke da gida da miji yanzu, ni kuma haka kawai Allah ya ɗora min tsananin ƙaunar yaranta, ko wa naga ya ɗauke su sai na ce zan karɓe su in dai ba hannun Iyam suke ko kuma uwarsu ba.

Da naga abun yana yawa sai na haƙura kawai na kame kaina daga yaran, na kama kaina sosai ko ubansu ne ya ɗauko su bana sha'awar ma na kallesu balle ɗauka. Hakan kuma sai ya janyo wata sabuwar maganar a wajensa shima, wai nasa baƙin ciki a raina shiyasa duk na lalace ina ta ƙarewa, to koma dai me na ke nufi na ke kuma ƙullawa Allah ya fini, yana yiwa ƴaƴansa adu'a kuma yana yiwa mahaifiyarsu, nan da lokaci kaɗan ma zan ƙara ganin ta samu wani cikin. Ni kuwa ina kallonsa a nutse na ce Allah ya bada masu albarka bana baƙin ciki.

Wata ɗaya bayan nan ina zaune ina haɗa kayan wankinsa ya shigo, yana goye da Noor Iman kuma tana hannunsa. Ya zo ya kwantar da su kan gadon, tun da na kalle shi sau ɗaya na ɗauke kai naci gaba da abin da nake yi. Can sai jinsa nayi yana faɗin,"Sa'ida me yasa ba kya son ɗaukan yaran nan?".

Na kalle shi hankalinsa na kan yiwa yaran wasa, ni mamakin ma maganar tasa nayi, yo idan ya zo da su ba ya ji ba ya gani, idan zan masa magana dubu da wuya ya amsa min ɗaya, dama zaman namu da shi gashi nan ne dai wai ai ance masa asiri na ke neman yi akan yaran. Jin nayi shiru ya ɗago ido ya kalle ni, sai ce yay,"Zan shiga wanka ki tafasa min shayi kafin na fito. Anjima kuma zan yi baƙi ki san me za ki tanadar musu".

Na ce masa to amma ya karɓo lemu wajen Iyam da kansa. Fita yay ya barni da yaran, naci gaba da aikina ina jin Noor tana kuka amma ban juya kai na kalleta ba, ya shigo ya ganni ina abin da nake sai ya kama faɗa akan rashin ɗaukar yarinyar na lallasheta. Nace,"To so kake na ɗauketa Iyam ko Uwarta su zo su ganta hannuna su ce nayi mata wani abun".

Harara ya watsa min yana faɗin na ƙware a kimtsa magana, ya ɗauki yarinyar ya kaita aka bata nono ya dawo da ita har tayi bacci ma, dama ita Iman ɗin bata fiya kuka sosai ba barta da bacci. Shigarsa wanka ba daɗewa Noor ɗin ta farka da sabon kuka, na kalleta kamar zan ɗauketa kuma sai na ƙyaleta. Ya buɗe ƙofar banɗakin ya leƙo yana cewa,"Yanzu tsakani da Allah kina ɗakin saboda rashin imani kina jin yarinya na wannan kukan ba za ki iya ɗaukarta ba. Dilla Malama ɗauketa ki rarrashta, banza me baƙar zuciya kawai".

Kallonsa nayi kawai na girgiza kai bayan na ce na gode da zagi. kukan yarinyar ne ya taɓa ni naje da sauri na ɗauketa ina jijjigata, haka kawai sai naji kamar tawaz da naga taƙi yin shiru na ɗau ruwan fida na bata tasha, kukan nata ya tsagaita na goyata a bayana har ta koma bacci. Ina aiki a kicin yarinyar ta fara mutsutsu a bayana, da alama dai nono take so sai na sakkota, na fito zan kaiwa Babarta sai wata zuciyar tace da ni kul don haka nayi ɗaki in bawa ubanta shi da ya ɗaukota.

Sai da na shiga na lura da Idanun yarinyar sun juye, jikinta kuma ya saki, haka nan naji zuciyata ta amsa. Sai na nemi wuri gefen gado na zauna ina jin sanyi na ratsa ƙafafuna, a hankali na shiga bubbuga bayanta ina jijjiagata duk sai naga bata motsi, hankalina ya tashi na ɗaga ido na dubi bakin ƙofar banɗakin. Na ambaci innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe da ƙarfi na faɗa ma ban sani ba, ai kuwa sai ga shi ya fito daga banɗakin a guje yana tambayar lafiya.

A ruɗe na ke nuna masa ita ina cewa,"Kaga idanunta naga sun juye".

Karɓarta yay yana kallonta kafin yasa yatsansa a hancinta. "Ya naji bata numfashi?". Ya faɗa yana ɗora hannu saman ƙirjinta, sai kuma yasa tafin hannu ya rufe mata idanu. A kiɗime ya ɗago ya kalle ni yana daka min wata razananniyar murya da cewa,"Me kika yi mata Sa'ida?".

Ido na zuba masa ina kallonsa cikin kaɗuwa, da ƙyar na iya buɗa bakina na ce masa,"Me kuwa zan yi mata Hubbi, wallahi babu abin da nayi mata, goyata nayi kawai har ma tayi bacci sai take ta mutsu mutsu a bayana, na sakkota zan kaiwa Zahra'u na ce bara na bari ka kaita da kanka. Kawota na bata ruwa muga...".

Fizgewa yay ya fice fuuu, na bi bayansa da sauri, ɗakin Zahra'un na bi shi na kasa haƙuri na cusa kaina ciki, ya duƙa gabanta ya kama nono yana ta sakawa ƴar a baki bakinta a datse taƙi kamawa, na tsaya daga gefe ƙirjina sai lugude yake, uwar tuni ta fara hawaye tana ƙwala kiran Inna Zulai, sai gata itama ta zo da gudunta, tana zuwa ta karɓi ƴar ta jujjuyata a hannunta, ina kallon yanda ta bimu da kallo dukanmu kafin a sanyaye tace,"Wannan ƴar ai ta koma".

"Kamar ya ta koma Inna?". Na faɗa cikin rawar baki ina kai hannu na taɓa yarinyar.

Innar ta maimaita,"Haƙuri za'ai Allahn da ya bayar ya karɓa, ina Iman ɗin?".

"Kina nufin ta mutu Inna?"...

Ƙarar da Zahra'u ta ƙwala ita ta katse sauran maganata, ni kuma a kiɗime na durƙushe a ƙasa ina ɗora hannaye saman kaina, Tsautsayi! a hankali cikin harɗewar harshe na ke faɗin innalillahi, jikina sai rawa yake yi, idona cikin na Nazifi da ke kallona da wani kalar ƙwayar idon da ban taɓa saninsa da ita ba. Sai girgiza masa kai na ke kafin na shiga ranse masa da cewa ban yi mata komai ba.

"Kin kashe min Ƴa Sa'ida, sai da kika san yanda kika rabani da ƴata, duka biyun kika kashe?".

Kuka na fashe da shi ina cewa,"Akan me zan kashe maka ƴa, akan wanne dalili, wallahil azim ban mata komai ba, ka yarda da ni wallahi banyi mata komai ba".

Inna da ke kan Zahra'u tana yi mata firfita tace,"A'a kai kuwa me ya kawo magana irin haka".

Takowa yay wanda ban taɓa tsammanin ba takeni zai yi ba saboda yanayinsa, ya wuce ya fita a ɗakin. Ya bar ni da kuka ina jin wani bala'in tiriri na fitowa ta ko'ina a jikina. Bango na dafa na miƙe da ƙyar, bana iya gani da kyau na ke laluba hanya, kaina na ke jin yana bala'in sarawa, wannan wacce iriyar ƙaddara ce? Daga ɗaukan yarinya sai mutuwa! A yau kam nasan zamana ya ƙare a gidan nan, ni da wannan halin da na ke shiga wancan zuwa wannan a irin rayuwar nan tawa gwara ace na faɗi na mutu, gwara na mutu da wannan bala'in, yanzu wa zai yarda ba ni na kasheta ba? Ko kotu aka je sai akai har busa ƙaho ba'a gama shari'ar ba tun da bani da shaida. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR11FT5* Haka suka yi ta yada min magana me zafi, na nuna kamar ma ban jin su duk da kowanne harafi na maganarsu sai ta taɓa zuciyata, ita kuma sai zugata suke yi akan kar tayi saken wata ta nemi tayi mata rainon ƴaƴa, daga haka me ake raba uwa da ƴaƴanta. Iyam kuwa sai albarka take saka mata tana ta faɗa mata wai duk abin da take so zata yi mata shi ai tunda har ta bawa Shalelenta ƴaƴa.

Sai ƙarfe ɗaya Nazifi ya dawo ɗakin, ce nake ma ko ya tafi gida ganin dare ya tsala haka, ashe yana can wurin likita yana ƙarasa biyan bill. kowa ya tashi ya fita aka barmu daga ni sai shi sai Zahra'u. Kujera yaja ya zauna gaban gadon, ita kuma tana daga kwance yaran na kusa da ita. Ya shiga yima yaran wasa yana cewa da ita,"Sannu uwar ƴaƴana, fatan babu in da yake miki ciwo ko?".

Ta ce,"Ciwo akwai shi kam uban ƴaƴana, Kaima kuma sannu domin tare muka sha wahalar naƙudar nan, Babies sun wahalar da mu Honey".

Ya shafo fuskarta yana cewa,"Ke dai sannu da ƙoƙari. Kinga scanning ɗin sai bai zama gaskiya ba". Ya faɗa da sanyin murya daga ji ba yanda zai yi ne amma ya so shima ace da namiji aka haifa.

Hannunsa ta riƙe tana cewa,"Kar ka damu da wannan Daddyn Twins, cikin da ya baka mata biyu shi zai ƙara baka maza ko nawa kake so in sha Allahu. Ni ai farin cikinka na ke so don haka zan cika maka gida da yara har sai ka ce sun isheka, ni ba zan hanaka haihuwa ba Honey".

Cikin nuna jin daɗi ya ce,"Na gode Sweety Allah yayi miki albarka. Nayi musu huɗuba da sunan Iyam da Momi, Salamatu da Shema'u".

Take annurin fuskarta ya canja. "Haba Honey kuma don Allah sun zo a zamani sai ka saka musu sunan tsofaffi. Ni kam gaskiya ba za su ke amfani da wannan sunayen ba".

Tayi maganar muryata na nuna rashin jin daɗi sosai, shima turus ɗin da yay na bai ji daɗin abin da ta faɗa ba, amma sai ya kaudar yana cewa,"Kin gane su kuwa? Wacece Babba wacce ƙarama?"

A kumbure tace,"ina zan sani abu iri ɗaya ba banbanci".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull