Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 10
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 10: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 10. Sai ya murmusa kuncinsa yana nuna mata wacce ke kan hannunta ya…
4,472 words
Sai ya murmusa kuncinsa yana nuna mata wacce ke kan hannunta ya ce,"Ita ce Hassana Salamatu, wannan kuma Hussaina Shema'u...kin san ta yanda za ki gane su kinga wuyan Hussaina akwai tawadar Allah".
Ina ga bata san lokacin da ta saki guntun tsaki ba wanda har shi kansa sai da yayi mata duba na ransa ya sosu, ta ɗauke kai gefe tace,"Za'a dinga ce musu Noor da Iman".
Ya kaɗa kansa da cewa,"Duk yanda kike so amma dai ai ba za'a ɓoye musu suna duka ba dole a makaranta za su ke amfani da asalin sunayensu, kuma ban da abinki Salamatu fa Ummu Salma ne ƙauye ne suka ɓata shi da Salamatu".
Ranta dai babu daɗi tace,"Ni dai da kayi shawara da ni, ai ba lallai sai munyi musu takwara ba. Tsakani da Allah duk irin sunaye masu daɗi da ake sakawa yara yanzu zaka tashi ka sakawa yarana irin sunayen ƴan gidan ku".
Ko ni kaina furucinta ya ban haushi, ai ko ba komai sunan mahaifiyarsa ne ya saka to ya zata yi? To da Jummai ɗin da ake ce mata yasa fa? Ko da yake ai har da na uwarta ta nuna bai mata ba. Ransa kuwa ya ɓaci yana gaya mata cewa saboda yay mata kara ma ya saka har da sunan tata mahaifiyar shine zata dinga faɗa masa magana, nan da ya hau sama, ganin abin nasu na neman zama babbar rigima sai na tashi zan fita na basu waje, don ina ga ma ta manta ina wajen ne amma ko don kirsa bata bari hakan ta faru ba.
Waigowa yay yana dubana yace,"Zan bar ki anan ne ko tare zamu tafi?".
Nace,"A'a tare zamu wuce". "Ba za ki zauna tare da Yaran ba?".
Na ɗanyi murmushi na ce,"Ai muna tare da su". Sannan na kalleta na ce,"To Maman Ƴan Biyu Allah ya ƙara lafiya, Allah kuma yaywa yaranmu albarka, ya raya su da imani".
Bata da niyyar amsa mini sai ma nono da ta fito da shi tana faɗin ya tayata sakawa Yarinyar da take kuka a baki, wai idan ta motsa tana jin zafi sosai. Ƙafafuna suka kama rawa na nufi ƙofa da sauri zan fita naji yana cewa da ita,"Kin yi mata ya me jiki kuwa? Har yanzu Babanta yana asibiti".
A daƙile tace,"Ya me jiki, Allah ya ba shi lafiya". Na amsa da,"Amin, na gode". Kana na fita na bar su.
Ina fita ban tsaya ba ganin ana min kallon wulaƙanci kawai na zaɓi da na wuce waje na jirasa. Sai da na gaji da tsayuwa har ina tunanin ma ko mun fasa tafiyar ne zamuyi kwanan asibiti, don biyu na dare ne ke kawo kai, ina ƙoƙarin tsugunawa kana sai ga shi ya fito, ya buɗe motar zan shiga gaba sai ce yay,"Koma baya da su Iyam zamu tafi".
Iyam na gaba ni da Yaya muna baya. Sai da muna kan hanya Iyam ta tambaye shi ko ya faɗawa Malam yace a'a yana jin nauyi ne. Faɗa ta kama yi masa da cewa Allah ya baka arziƙi babba kace kana jin nauyin faɗawa mahaifinka, ko don kaga har yanzu yana jin haushin ƙarin auran naka, to shi ya zai yi da abun da Allah ya tsara?. Sai tace ya tura mata kati a wayarta, tura mata yayi ta miƙowa Yaya wayar ta danna mata lambar Malam ta kira tana shaida masa haihuwar, sai kuma naji tana faɗin ita fa ya ƙyaleta ya rabu da ita da maganar dawowa gida, banda abinsa ai gidan ɗanta take zaune ba baƙon waje ba. A daren nan haka muka kai Yaya har gidanta can Ƙwalli tukunna muka wuce, ai kuwa ƴan sanda sun tare mu yafi sau uku, duk inda muka tsaya sai dai ya basu cin hanci sannan su barmu mu tafi.
A daren nan zan iya cewa Nazifi bai runtsa ba, ni a rayuwata ma ban taɓa ganin wanda aka ma haihuwa yake tsananin farin ciki haka ba, kai ni ban ma taɓa ganin mutum da farin cikin nasa ba, motsi kaɗan sai yace Alhamdulillah, motsi kaɗan sai ya kira wayarta yace suna dai lafiya ko?. Da asuba bayan na idar da sallah har na koma saboda bacci ne fal a idona, ya zo ya tashe ni yace ga naman kai can an kawo na dafawa me jego, sannan naje wajen Iyam na karɓo garin kunun kanwa za'a dama a tafi mata da shi, kuma sai me nake ganin za'a ƙara musu?
Na ce da shi,"Ni da ban haihu ba ina na san abubuwan da me jego ke so". Kana na gyara kwanciyata ina cewa,"Bari na ɗan matse idona kaina ciwo yake wallahi".
Faɗa ya kama yi yana cewa,"Haba ke kuwa, naman kai fa na ce miki idan ba ki ɗora tun yanzu ba sai da rana kike so a kai mata? Ta shi don Allah kiyi abin da ya kamata in kin kammala kya huta gaba ɗaya, ga paracetamol can ɗauki ki sha sai kan ya daina ciwo".
Tashi nayi kawai don bana son biye masa raina ya fi haka ɓaci. Ya ƙara cewa,"Naga masu jego ana so suci nama mai ruwa ruwa ko? To ko za kiyi mata irin wanda kika yi kwanakin baya, yay daɗi sosai ina ta so ma na ce ki ƙara yi".
Wani kallo na watsa masa da cewa,"Da alama ka manta ni mutum ce ba inji ba. Haba kace wannan kace wancan, kana tunanin banda darajar ƴaƴanka ne ma zan amsa da cewa zan yi".
Sai ya sauke murya yana faɗin,"To shikenan dafa iya wannan ɗin. Ni ba kya ɓatan rai ba ina tsaka sa farin cikina. Allah yay min babbar kyauta kema ka ci albarkacin hakan".
Ina fita na tarar Iyam ta fito tana cewa,"Ya faɗa miki aikin da zaki yi ko, to kinga naman kai ba ace za'a dafa shi kan gas ba za'a ɓata lokaci, sai dai kisa itace ko gawayi ga Adamu nan nasa ya kawo babbar tukunya. Don Allah sai kiyi da jiki na ga sai faman lanƙwashe lanƙwashe kike yi, idan ba kiyi ba wane zai yi ummm? dama amfanin naki kenan aikin".
Ni ban ma ko gaisheta ba na amsa da to kawai na wuce sama. idona har ba ya buɗewa da kyau saboda baccin da ke cikinsa, amma haka dole na yaƙe shi na fito na kama aikin. Ko kusa ban ji ina ɓacin rai dan zan yi aikin ba, hasalima annashuwa na ke ji a tare da ni, banda ma yanayi na gajiya da ramakon bacci dama ina da niyyar in gari ya waye na tambaye shi me zan dafa da za'a kai musu. Shiga ɗakinsa ɗari fita ɗari sai na same shi yana waya da abokai da mutanen arziƙi yana gaya musu an masa haihuwa. Tun asubar nan bai koma bacci ba kiraye kiraye kawai yake yi, wasu kuma yana tura musu saƙo ta message. Ya kira Malam ma yace masa za'a kawo Sa a yanka ayi sadaƙa sannan kuma ayi sauƙar ƙur'ani wa yaran.
Naci wahala sosai wajen dafa naman kan saboda itacen ɗanye ne, da dukkan alama da gayya Iyam tasa aka kawo shi haka, ga Naman kan gari guda kan shanu manya huɗu. Iyam sai azalzata take yi akan nayi sauri kar rana tayi, shima ɗin kuma da nasa ƙwazzafar yana faɗin to na dama kunun in dafa shayi a fara kai musu, duk sai na bi na rikice aikin ma yaƙi yin sauri, ga ba damar ƴar aikin Zahra'u ta taya ni saboda tana ta gyaran wajensu, haka dole na rabu da naman na dawo kitchen na ɗora shayin sannan na dama kunun.
Atika ta shigo kitchen ɗin tana ce min,"Abba yace kije da sauri". Hmm yarinyar nan idan ta girma ban san ya zamu kwashe da ita ba, ko gaishe ni bata yi, magana ma idan tana min kamar wacca ta isa da ni ko kuma sa'arta. Sharewa kawai na ke saboda dai a zauna lafiya amma ko ranar nan ita da ƴar uwaratata sai da suka yi faɗa, ita Rumanan na ce mata kar ta ƙara yiwa Antynta rashin kunya in ba haka ba zata faɗa a islamiya a zaneta, ita kuma tace ai dai ta faɗawa Anty Amarya a cireta daga islamiyar a sauya mata wata.
Biredin da nake soyawa a cikin ƙwai na tsame na kashe gas na fita. Samunsa nayi ya shirya sai baza ƙamshi yake kamar sabon ango, don kayan ma da ya saka sababbi ne, bakinsa yaƙi rufuwa fuskarsa sai fitar da murmushi take yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka san a tsananin farin ciki yake. waya ce kare a kunnensa yana cewa,"Ehh dama na ce ƙila baka tashi daga bacci ba ne, sai na maka text ta whatsapp".
"Ehh wallahi Ƴaƴa biyu ne duka mata, sai ayi musu adu'a don Allah". "A'a Amaryar ce ba uwar gidan ba. Ameen na gode sosai a gaida iyalin, sai anjima".
Ya aje wayar yana dubana da cewa,"Wai har yanzu ba ki gama ba? Kinga fa har na shirya zan tafi can, ƙarfe nawa yanzu tara fa, ace kuma har yanzu me shayarwa bata ci komai ba, kin san fa ƴaƴan za su sha nono duk su zuƙeta itama ta buƙaci abinci".
Numfashi na sauke na ce,"Kafin ka fito na gama, amma Nama ba zai samu yanzu ba ka turo a ɗauka anjima. Kuma sai ka ɗauko kula a wajenta da zan zuba biredin a ciki".
Na faɗa ina juyawa na fita. Can sai ga shi ya shigo kitchen ɗin, barinsa nayi da zuba soyayyan bireɗin ni kuma na ɗauko kwando ina saka kwanukan kayan abincin. Ya ɗauki wasu yay gaba da su nima ina biye da shi da ɗaya kwandon. Shi a shirin nasa ma tare zamu tafi, sai Iyam tace ina fa zai yiwu tafiya da ni, idan naje can me zanwa me jegon me zanwa yaran? Kawai na zauna na dafa abincin rana akai musu, kuma wataƙila ayi baƙi ƴan barka basa zo gida babu kowa ba, roƙonta na tari mutane da girmamawa kar su zo na nuna musu mugun halina dan dangin Zahra'u mutane ne masu mutunci, in kula kar jakin kishina da baƙin cin haihuwa yasa na ɓatawa miji girman da yake da shi a wajensu.
Babu yanda Rumana bata yi ba akan zata bisu Iyam ta hana, wai ai tunda ta iya munafurci yanzu to ta jira ni mu tafi tare, ita Atika ai uwar wajenta ce shiyasa zasu tafi da ita, Yarinyar ta ban tausayi sosai, tana tashi ta tambayeni akan ta shirya nace to ai makaranta tace Atika ma bata je ba Abbansu yace zasu je gano jarirai, nace to itama ta shirya ɗin, na dai fahimci duk wani da zai raɓe ni ya soni Iyam bata ƙaunarsa ko da jininta ne. Sai kusan sha ɗaya na sauke naman kan, na zuba a kulolin tsakiya har biyu irin na taron biki, sannan na dafa shankafa da miya da coslow itama kwano ɗaya yace a dafa, ya turo Adamu ya ɗauka kai musu, ni kuma yace na shirya da yamma na je.
Na gaji sosai ina so na kwantar da haƙarƙarina, na ce masa naje gobe kawai sai ya kama faɗan shi ba ya son musu, kuma kar na ɓata masa rai, ko na manta ƴaƴansa zan je gani da na ke faɗin ba zanje ba. Nace masa ni fa idan yana tunanin ina jin haushin haihuwar yaran nan yama daina, domin kuwa ni zuciyata tas take babu tsatsa, idan kuma ba zai cire zargin hakan a ransa ba to yaci gaba da ɗaukar alhakina. Da Yamma na shirya muka tafi Asibitin ni da Rumana, na tarar an ƙara cika wanda ke shaida dai ita ɗin yar gata ce, don har wata likita ma naji tana cewa amma wacca ta haihu nan ta gaban goshi ce. suma kusan ƴan uwan Nazifi duk suna nan, asibitin dai sun mayar da shi kamar wajen taro su kawai ake gani. A waje na tsaya muka gaggaisa da ƙannnen nasa da Yayyensa, kana na shiga ɗakin.
Sallamar da nayi babu wanda ya amsa sai nayi musu uzuri da hayaniyar da ake tayi hakan yasa basu jini ba, sai bayan na shiga ne na ajiye kayan abincin tukunna Innarta ta lura da ni tace,"A'a Sa'ida sannu da zuwa, tun ɗazu kuwa na ke ta zuba idon ganinki".
Na amsa da yauwa ina tambayarta ya jarirai suka kwana. Tayi min nuni da wajen zama tana ce min ƴaƴan nawa an fita da su Kakansu ya zo, nace mata tom ga dai abincin dare can na zo da shi. Tayi min sannu tare da godiya sosai tana ta faɗin an barni da ɗawainiya, sannan ta juya garesu tana gabatar musu da ni, na kula kusan duk ɗinsu ba waɗanda muka bari jiya ba ne. Haka suka bini da wani irin kallo na raini da ƙasƙanci, ai suna ganin na saka hijabi har ƙasa ga niƙab da safa ga ni duk a koje, haka kuma suna jinjina ni ce kishiyar Zahra'u. Babu me niyyar min magana, ni kuma girmansu yasa na gaishe su sai dai babu wanda ya amsa min sai ɗauke kai da suka yi, ina ji suna ƙusƙus Allah masanin me suke cewa a zuciyata ni kuma ina nanata "Wallahulmusta'anu ala ma tasifun, hasbunallahu wani'imal wakil, la'ila ha'illa anta subhanaka inni kunta minazzalumin".
Me jegon ma haka na daure nayi mata magana to ni ban sani ba ta amsa ko bata amsa ba, ci kanki dai bata ce min ba kamar ma bata san ina wurin ba. Rumana ta dame ni da cewa Anty ina jariran na doka mata tsawa akan ta ƙyale ni ai tana ji aka ce an fita da su, Atika ta zo wajen tana ce mata jariran Antynta masu kyau, ita kuma ance Antynta ba zata haihu ba. Rumanan ta ɗago ta kalle ni, tabbas yarinyar yanzu tana sona bilhaƙƙi da gaskiya, sai in kuma shaiɗan ya kuma buga mata ganga, don yanzu ko wani ya ɓatan rai to sai tayi kuka musamman ma idan taga Nazifi yana min faɗa, sai tace ita bata so Abbansu na yi min faɗa.
A sanyaye tace da ƴar uwartata,"Nima Antyna zata haihu ai in sha Allahu". Tana faɗar hakan na girgiza kaina ina murmushi me ciwo, na ce da ita ta tashi su fita daga waje sai ta girgiza min kai, haka na tilastata ta fice tana matsar ƙwalla, ni kuma bana son ƙara jin bakin Atikar ne saboda zuciya zata iya ɗibana na daki bakin yarinyar.
Kiran Ummani ya shigo wayata, bayan mun gaisa na ke ƙara tambayarta jikin Abbaa tace wallahi yaji sauƙi sosai in kwantar da hankalina, gobe ma ake sa ran basu sallama. Ban dai yarda ba sai da naji muryan Abbaan tukunna, saboda na kira da safe ce min tayi bacci yake yi ni kuma sai nake tunanin ko jikin nasa ne ya dawo, tun da ko a jiyan kana ganinsa ka san ƙarfin hali yake yi, don niyyata ma da zan fito can zan wuce Yashaik yace kar na je. Ummani tace na bawa Zahrau wayar na ce ko ta bari kawai idan ta koma gida sa zo mata barka, tace a'a na bata ɗin dai kafin ta zo. Na miƙe na isa gaban gadon na miƙa mata wayar, ta bi hannuna da kallo na ce mata,"Babarmu ce zata yi magana da ke".
Karɓa tayi babu sakin fuska, kuma da mamakina sai naji tana magana da Ummani cikin ladabi da girmamawa, har tana tambayar jikin Abbaa, sai naji daɗi da hakan don nayi tsammanin zata wulaƙanta min uwa ne yanzu mu kwashi ƴan kallo, ban san me Ummanin tace mata ba naga tayi murmushi tace,"To Mama ai sai su zo har gida ma su gaishe ki". Sannan kuma naji tana jero in sha Allahu Mama, kafin ta koma jera to to, da haka na san aduo'i ne Ummani ke bata don na san wacece mahaifiyata, bayan gama wayar tasu har godiya nayi mata ko ba komai ta darajarta min Uwa.
Ina nan zaune zaman asibitin duk ya gundure ni, ba don yace lallai na tsaya sai ya zo tukunna mu tafi tare ba, niyyata muna gama gaisawa naga yaran sai na juya. Ba abin na fita daga wajen ɗakin ba duk ƙannen Nazifi ne da Yayyansa, ni kam da na zauna tare da su gwara na zauna nan ɗin suyi ta min habaicin, don nafi jin zafin cin mutuncin ƴan uwan Nazifi akan na ƴan uwan Zahra'un. game ɗin ludo na saka mana a wayata muke yi ni da Rumana, hankalina ya bar kan kowa sai dai kunnuwana ba su fasa jiye min yacca ake ta aikin yada min baƙaƙen maganganu ba ana aibata ni, zuciyata taji ba zata jura ba kawai na miƙe na kama hannun Rumana muka fice. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR13FT5* Maman Yasmin da Maman Khairi da Yaya Nusaiba wato Yayar Safiyya suna ta hirarsu, ni dai ina daga gefe ina jin su sama sama, nayi wanka lokacin na shirya cikin wasu kaya marasa nauyi da Maa ta bayar aka kawo min, hankalina duk ba ya jikina, zuciya da gangar jiki sun cika da kewar Salim, babu abinda na ke son ji a yanzu sama da muryarsa, don na san ba zan samu ganinsa ba ko da ace yana cikin gidan.
Idona na rufe Safiyya ta shigo tana faɗin,"Ke to ga ƴarki nan ta addabi mutane a kaita wurin New Mommy". Nayi saurin buɗe ido ina kallon Rofi'at ɗin da murmushi, zaune na tashi na buɗa mata ta taho da gudunta ta shige jikina, Allah ya gani tun ba'a je ko ina ba na kamu da soyayyarsu, muna can muna magana ashe yarinya har tayi bacci, gyara mata kwanciyarta nayi a jikina.
"Safiyya hanya dai lafiya ai babu matsala ko?".
Ta baro hirar da suke ta waigo tana kallona tace,"To banda abinki ba tare da security suke ba, ki kwantar da hankalinki nan da ƙarfe uku na dare za ki gansu".
"To Allah ya kawo su lafiya". Na faɗa ina kwantar da kaina kan filo, sai da muka yi dai wayar da su Mama A'i suka ce min wallahi lafiya lau suke gasu ana ta fafara gudu da su akan hanya, zuwa ƙarfe ɗaya ma za su iya zuwa. "To Allah ya kawo ku lafiya Mama A'i".
Cikin baccin da ya fara fizgata naji yo ƙarar wayata, da sauri na farka na ɗaga ina sawa a kunne ko numbern ban duba ba, can naji muryan mace cikin turanci na ce min,"Ba dai har kin yi bacci ba".
"Umm wa ke magana?". Muryarta ya bayyana irin rashin jin daɗin nan da cewa,"Kudrat ce". Fuskata a yatsine na ce,"Ayyah barka da dare". Haƙuri ta shiga ba ni kan kiran da ta min nayi bacci, na ce mata,"babu komai ai". Sai ta sake cewa,"Shi ne ba ku biyo ta nan ba kun barni ni ɗaya a gida shiru". Na kyaɓe baki ina cewa,"Kema ai sai kika ƙi zuwa nan ɗin". Murmushinta tayi wanda ke bayyana bata da damuwan komai tace,"Ki yi haƙuri shi ne yace ba sai na zo ba, yaran kawai za'a kai, amma ɗazu Maa tace gobe da safe nima na taho tunda akwai party da za'ai".
Murya a daƙile na ce,"Allah ya kaimu". Tana son jana da hira ina ga ko kaɗaicin gidan ne ya dameta, da kuma mijin nata da basu samu yin waya ba don alamun hakan ya nuna, tana ta ce min fatan dai Yarana ba su dame ni ba ko, na ce mata ga Rofi'at ma kusa da ni har tayi bacci, ni dai na nuna mata bacci na ke ji, muka yi sallama nayi cilli da wayar gefe tare da jan dogon tsaki wanda har sai da Yaya Nusaiba ta tambaye ni lafiya, kawai nayi saurin kulle idona da zummar a cikin bacci nayi, nan kuwa haushi da takaicin kiran Kudrat ne, aikin banza ita ko kishi ma bata yi zata wani kira ni da ƙatuwan muryanta ita lallai ga ta me kirki, ta bar ni inji da damuwan rashin jin Salim ɗina ma, shegen iyayi da neman suna da makirci irin na su na ƙabila, ƙwafa nayi ina janye Rofi'at a jikina na juya mata baya.
Ni fa banga ta bacci ba yau sai ta Allah kuma, babu nutsuwa sam tare da ni, kowa ya shigo yaga yanda na takure kaina sai kallo da ido sai ace baƙunta ce, Safiyya ma haka ta zo ta gama zuba min surutunta sai da ido kawai na ke kallonta, ita ce ma ta fahimci yanayin da na ke ciki tace bari dai taje ta jiyo min labarin mijin nawa wurin Sir, na zama ƴar soyayya zan mace musu tun basu kai ni ɗaki ba. bayan fitarta duk na zaƙu ta dawo ta sanar min halin da mijina ke ciki, na ɗaga waya zan kirata sai naga ashe ta bar wayan nata anan, ni dai nayi ta faman juyi akan gadon duk na rasa me ke min daɗi, su Maman Khairi ma da suka lura da ni sai suka shiga min shaƙiyanci irin na su wanda har sai da naji kunya, tun kuwa da nasa filo na rufe fuskata ban ƙara buɗewa ba.
Sai ƙarfe biyu da rabi Umman Batula suka iso, da aka tashe ni ma ce na ke gari ne ya waye jin hayaniya da hasken fitilun gidan da ba zaka taɓa cewa dare ba ne, naji daɗin ƙarasowarsu lafiya kuma ina ganin hakan na rarumi wayata na kuma kiran Salim shiru kiran bai tafiya. Hankalina sai ya tashi idona ya cika da ƙwalla, rabona da shi fa tun safe, shima magana muka yi a tsaitsaye, jiya kam dama totally banji muryansa ba, ni kuwa wanne irin horo wannan aikin na su yake min, dama haka aikin na su ya ke da barin mutum cikin fargaba da tashin hankali? Kuma babban abin da ya ɗaga min hankali da yace jirginsu ne zai kewaye a can wani ƙurgummin daji. rumtse ido nayi jin hawaye na neman sakko min na rungumo Rofi'at jikina gabana na ta faɗuwa, haka bacci ya sace ni ina ta adu'an Allah yasa dai lafiya, ya kula min da mijina a duk inda yake.
Da asuba ma da muka yi sallah ban iya komawa bacci ba, ina kallon su Mama A'i da Maman Khairi aka yi sallah aka koma bacci, kowanne to a gajiye yake sai faman miƙa suke yi, ga shi sun samu gado wawakeke da katifa me bala'in taushi. Har gari ya fara wayewa kaina na bisa gefen gado duk na kasa sukuni, zuciyata matse da taraddadi, idona kuwa na kasa ɗauke shi akan wayata ƙiris na ke jira in ga kiran Salim ya shigo. Duk yanda na so na daure na kasa sai da na kira Ummani, ko da ta ɗaga yanda taji muryana sai ta shiga tambayana lafiya, kwana nayi ina kuka?".
Nace mata,"A'a tun jiya ne bayan ɗaurin aure har yanzu bamu ƙara magana da Salim a waya ba, ko message idan na masa ba reply kuma ni har yanzu ban ji wani yace sun yi magana da shi ba".
Na faɗa da muryana tamkar zan yi kuka. Sai naji ta sauke numfashi tana tayani adu'a Allah yasa lafiya. "In Allah ya yarda lafiya, kin san yanayin aikinsu da kurɗa kurɗan shiga daji wataƙila suna wurin da babu network ne". Haka ta ɗan kwantar min da hankali, sai da ta haɗa ni da Abbaa muka yi waya shima yana tambayana ya kwanan baƙunta nace masa babu daɗi duk nayi kewarsu, shima kuma yace in kyautata zato a raina in Allah ya yarda lafiya lau Salim yake koma a'ina ne.
Wajen takwas aka turo ƙofan ɗakin, idona karaf akai kaman zan ga Salim, baccin gajiya ne fal cikin ƙwayar idona amma har ga Allah ba zan iya ba, duk wanda ya ganni ya san hankalina ba kwance yake ba, abinci ne aka kawo mana kala kala na break fast, bayan tea da soyayyan bread da ƙwai, akwai ferfesun ganda da snacks da soyayyan kaza, sai kunun tamba da ƙosai, kowanne ya bani sha'awa amma ba zan iya ci ba, ko jiya ina ganin teba da miyan kuɓewa yawuna kaman zai dalala amma na kasa ci, to da wanne teste ɗin bayan wanda ke da ɗanɗanon bakin ya tafi da shi.
Haka su Maman Yasmin suka zage suka ci abincinsu ni kuwa ban iya ko kai hannu kwanon ba, ina zan iya cin abinci ban san a wanne hali Salim yake ciki ba, ai ko ruwa ba zan iya sha ba, ba yanda ba'a yi da ni ba na ce ni na ƙoshi, har da ƙaryan amai ma na ke ji, Safiyya na min iskancin wai da an kai ni na faɗi haka sai ta ce Salim ya iya aiki, su kuma duk tsammaninsu ƙulafucin gida ne babu wanda ya kawo a ransa cewa rashin jin mijina ya jefa ni a halin ƙaramar rashin lafiya.
Safiyya ta zo muka fita tare da ita Maa ce ke kirana, a ɗakinta muka sameta cikin shiga na alfarma, tana ganina fuskanta ya washe da annuri, cike da kunya na isa kusa da ita inda take min nuni da na zauna, muka daɗa gaisawa da ita don tun sassafen da aka kai mana abinci muka fito gaba ɗayanmu muka same su a main falo ita da Mommi muka gaida su, kuma babu ɗagawa Maa da Mommi ɗin su ne suka je da kansu har ɗakin da aka sauke su Mama A'i suka gaishe su, ashe can ma haka aka kai musu tulun uban abinci, ko ina za su kai shi oho.
Tana kwanto ni jikinta take ce min,"Kin ci kin ƙoshi?". Na ɗaga mata kai alaman ehh, sai tace min to nayi wanka anan na shirya, can sai na barwa sauran suma su sami kimtsawa. Kaya ta ɗebo min a wadrobe ɗinta riga da skirt na atamfar ankara, ta aje min duk wasu kayan shiryawa, ni dai duk a kunyace na ke na so ace ta bar ni na shirya a can cikin ƴan uwana, da taga itama alaman hakan tana murmushi take dafa kafaɗana tace,"Ni fa Mamanki ce babu batun jin kunya tsakaninmu, ki saki jikin ki da ni kinji daughter nah".
Nayi murmushi kaina a ƙasa, tace min akwai towel a toilet ɗin sabo ta ajiye min, dama da ƙaton hijabi a jikina haka na shiga da shi sai a banɗakin ma na cire kayana. Har na fito still tana zaune bakin gado inda na barta, tayi min nuni da dressing mirror tace ga stool nan na zauna na gyara jikina, ga turaruka nan duakkansu na fesa. Ina shafa man ina ji suna waya da Kudrat tana ce mata tom sai ta ƙaraso. Ban san me yasa na ke jin zuciyata kamar bata son Kudrat ba, ko duk cikin kishi ne, ko ambatar sunanta aka yi sai naji zuciyata tayi bala'in motsawa da haushi, har mamakin kaina na ke yi, adu'ana ɗaya kar wannan kishin yay min illa.