Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 11

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 11

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 11: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 11. Na shirya cikin kayan da Maa ta bani nayi kyau sosai, lokacin ne…

4,442 words

Na shirya cikin kayan da Maa ta bani nayi kyau sosai, lokacin ne take ce min,"Kun samu magana da Onochie?". Kamar ta san Alla allan da nake kenan tayi maganarsa, na rasa wa zan tambaya shi to, ai kuwa ban san lokacin da na amsa da sauri ba nace"A'a ina ta kiran wayarsa ba ya tafiya tun jiya". Na faɗi hakan da muryan damuwa.

Sai bayan nayi maganar ne kuma kunya ta lulluɓe ni, itama murmushi tayi da sautinsa ya fito sosai tace,"Yana lafiya kwantar da hankalin ki, za ki saba ne a hankali". To ni kowa sai yace min in kwantar da hankalina, ta ya kenan alhalin su kansu ba su ji daga gare shi ba.

Muna zaune tana ɗan jana da hira wanda duk tambayoyi ne take min game da rayuwana, har tana tambayana mun dai gama magana da Salim akan asibitin da zai nema min ko na ce mata ehh, tace sai ranar da zan je ganin gida zamu tafi har da ita su gaisa da iyayena. Wani dogon saurayi me kama da ita ya shigo ɗakin, ba zai wuce 20years ba. Da fara'arsa muka gaisa suna kama da Maa ɗin sai dai shima ingarman jikin Sir yayi, over over ya miƙa mata yace Brother ne yake magana yace a bawa matarsa. Idona akan abar ina mamaki wai ta nan ake magana mutum kuma yaji, abar da nake gani a film sai gata gaban idona har zan taɓa kuma zan yi magana da wanda na sani ta ciki, ina wannan tunani kuwa na jiyo muryansa na faɗin,"Nnọọ(Hello)".

Ita kuma tace masa,"Ibolachi(Good morning)". Dama iya abinda na sani kenan a yaren shima kwanaki ne da muna chart da shi ya ɗan koya min, yo wa ya san ma ko zan iya ni da na zo rayuwar dindin a cikinsu, yaren da na ke jinsa da wahala.

Sai da suka gama magana da Maa kafin ta miƙo min, na karɓa kaina a ƙasa, fita tayi sai naji daɗin hakan ko don na samu sakewar magana da shi. Na riƙe a bar a hannuna ina zuba mata ido, a baki zan sa ko kuwa a kunne? Don lokacin da Maa ke maganar da shi ban lura da yanda tayi ba, muryansa nan da ke kashe min jiki naji yace,"Ola’m (My Diamond)".

Wani yanayin daɗi naji ya ratsa ilahirin ɓargona, idanuwana a lumshe ina sauke ajiyan zuciya, wallahi na azabtu da rashin jinsa Allah ma ya sani, ashe haka na ke mugun sonsa ban sani ba. "Myyy are you there?". Kawai sai naji na fashe masa da kukan gaske, kuka har ina jan numfashi. Hankalinsa ya tashi ya shiga jero min tambayan mene? Me ya faru?, cikin shagwaɓan da ban taɓa sanin na iyata ba a duniyana na ce,"Tun jiya ban ji muryanka ba, ina ta kira bana samu, ban san wanne hali kake ciki ba, zuciyana nata min zafi, hankalina duk ya tashi".

With low voice da ke fita da amon damuwa da tsantsan kulawa yace,"Am so sorry Ola’m, banda yanda zan yi ne, duk abinda na ke hankalina na kanki, kowa sai da ya gane bana cikin natsuwata, har kwaɓa nayi a confrence meeting, ni kaina zuciyana bai samu salama ba sai yanzun da naji muryanki, amma kuma hankalina ya fi da tashi dalilin jin kukanki, kiyi haƙuri kin ji ina nan lafiya, ki daina kukan please bana son zubar hawayenki masu tsada, kukan yana taɓa min zuciya kar kisa ta samu matsala".

Na ɗan ja numfashi nace,"To yaushe za ka dawo?".

A hankali yace da ni,"Muna Abuja right now amma na gama shiryawa tahowa kawai zan yi, ba zan iya ƙara yini ba tare da na jini tare da ke ba. Kin yi breakfast?".

Kaman ina gabansa na girgiza kai da cewan,"Na kasa cin komai tun jiya, kai kawai na ke son gani".

Ya furzar da iska wanda na tabbata sai da ya shafi goshi kamin yace,"Ki yi haƙuri kin ji, zan iso gareki nan ba da jimawa ba, amma ki daure ki ci abincin ko kaɗan ne idan na zo sai na ƙara ba ki".

Na ƙara shagwaɓe masa da faɗin,"Ni ba zan iya cin komai ba sai na ganka, baki duk babu ɗanɗano kuma kasan kai ne ɗanɗanon bakin nawa".

Haka yay ta lallashina da soyayyarsa, na amsa masa da to zan ci abincin amma ba da yawa ba. Ya tambaye ni ya naji yanayin nan ɗin, banda wata matsala ko? Sun min tarba me kyau? Ya makwancina? Na takura? Garin da daɗi?".

A hankali na ce masa,"Naji daɗi sosai da yanda aka karɓe mu hannu bibbiyu, abinci har sai da muka bar shi, wurin kwana kuwa ai ƴan gida muka zama ba baƙi ba, garin kuma akwai daɗi duk da babu inda na fita".

Duk na ba shi labarin abun da ya wakana daga jiya zuwa yau, sai naji yayi farin ciki musamman da na ce masa family ɗinka suna da kirki kuma naji daɗin kasancewana cikinku, su Maman Khairi ma kowa yaji daɗi yanda ba su nuna mu ɗin ba nasu ba ne suka rungume mu da soyayya, Ina basa labarin irin adu'an da Sir ya dinƙa min sai naji kaman na tsoma shi cikin kogon nishaɗi.

"Myy dama na fada miki ai, Family na ba za su nuna miki banbanci ba, kowa zai so ki, nima suna sona sosai kuma suna son duk abinda na zo musu da shi, wani gatan ma tukunna dai, wataran Maa sai ta kusa goya ki saboda soyayya, za ki ga gata iya gata a wajen family na, an kai ki wurin Granny?".

Na ce masa,"Ehh mun je, Mommi ma duk ta raka ni na gaida su Uncles".

"Ohh wan nan tsohuwa sai da ta ja min ke yawo kenan ta wahalar min da ƙafan mata, ita bata zama da anyi baƙo ta dinƙi kaisa wuri tana aikin masa bayanin mutane, kema haka ta miki ko?".

Ina ƴar ƙaramar dariya na ce masa,"Ehh amma tana da shiga rai babu ruwanta".

Kaman ina gabansa na ji sanda ya ke jijjiga kai da cewan,"Uhmm da kike ganinta masifaffa ce, ke ma ɗokin ganinki ne na sabunta, ita ko wasan jika da Kaka bata yi, kowa a gidan shakkarta yake, amma idan kika iya zama da ita bata da damuwa sam, ta dungure miki kai?".

Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata da ce masa a'a. Mun jima muna magana da shi kaman ba zamu rabu ba, haka kamar ma ba zuwa zai yi ya ɗauki kayarsa ba. Wallahi sai naji ma ashe idan ina tare da shi nafi missing ɗinsa, kaman na bisa ta cikin abar haka na ji, haka na ɗauka waya na masa text me daɗin gaske, kai wani hanin ga Allah ma dai baiwa ne. Ina zaune ina ta juya over over ɗin a hannuna Maa ta dawo, tace to naje can wurin ƴan uwan nawa nan da ƙarfe biyu dai za'a fara taro. Nace mata to na tashi na fita tana ta cewa na yi kyau sosai a shigan kayan.

Da ƙarfe sha biyu ina kwance ni ɗaya a ɗakin da aka sauke mu, wayata ce a hannuna ina ta kallon hotunan ɗaurin auren da Yashaik ya saka a status, bana kallon kowa da kyau sai mijina, nayi nisa cikin kallon wani hotonsa naji an faɗo kaina, na razana zan kurma ihu sai aka toshe min baki, ido warwaje na ke kallonsa, yaushe ya shigo ban ji motsi ba? Mutsu mustu na shiga yi zan ture shi ina tsoron kar wani ya shigo ya ganmu, sai naji yace,"Nasa key a ƙofan fa".

Mirgina ni yay na zamana a samansa, yay min peck a goshi kafin ya shiga bawa fuskartawa kiss ta ko'ina, ina ta kakkaucewa ina ce masa ya bari wani zai iya shigowa ni ya ƙyale ni bana so. Sai kawai yay min wata runguma da har sai da ƙashin bayana ya amsa. "Myyy kin san yanda na ƙagu na mallake ki kuwa? Halalina ce fa ke yanzu ko waye ma ya shigo ya ganmu a haka babu abin da zai ce, wuri ma za'a bamu kuma mutum shi zai ji kunya".

Sai ya kulle ido yana cika bakinsa da iska ya hure min a fuska, na lumshe ido shi kuma ya buɗe nasa yana ta kallona kaman zai cinye ni. "I missed you so much matar Soja, kaman zan mutu fa haka naji".

Ina haɗiye yawu da ƙyar na ce,"Plss ka daina zancen mutuwa, yaushe ku ka dawo?".

"Yanzun muka shigo, wurinki na yo direct, kowa sai kallona yake don na tambayi ina amaryana suka ga na taho kai tsaye, laifi nayi hakan?".

"Ko wurin Maa baka je ba?". Yay wani killer smile ya ce,"Na leƙa ɗakinta naga ba ki nan, na san kuma ta ganni don naji sautin fitar murmushinta".

Ɗan marin wasa nayi masa ina kwantar da kaina a ƙirjinsa na ce,"Salim ka ba ni kunya".

Yana nutsa yatsunsa cikin gashina yace,"Har an ɗaura aure ma ba ki daina faɗin sunana ba gatsal ko, oookkk na ma gane so kike sai anyi abin kana ki sama min suna".

Ni dai da ace da hausa yake magana sai na fi jin kunya, fuskata na ɓoye a ƙirjinsa. "Ka san yanda ka tashi hankalina kuwa? Da sai dai ai kaji labari a media ana wata matar soja taje neman mijinta fadar shugaban ƙasa, don shi zan je na tsare da tuhumar ina ya kai min abin ƙaunata".

Dariya sosai yayi wadda ta bayyana haƙoransa dukka a waje, dariyar da sautinta yay min mugun daɗi, ya daɗa rungume ni yana cewa,"Sai ki ce masa me idan kika je?".

"Na ce mijina da ka aika a jirgi can wani waje na zo ka bani abina mu tafi, don na fiku buƙatarsa".

Na faɗi hakan ina murmushi ina kai hannu na taɓa sumar kansa, fuskansa ya shiga gogawa da nawa muka yi shiru ni da shi sai fitar numfashinmu kawai da kake ji. Da wani kasalalliyan muryasa yake ce min,"Myyy wannan Ƙamshin na ki, ko naje na faɗawa Maa a fasa taron mu wuce kawai? Ni ba zan iya ƙara jiran lokaci ba".

Lumsassun idanuna na buɗe ina kallonsa, sai dai ni kaina a yanda na ke jina jikinsa ko maganan ba zan iya ba, ni fa gaba ɗaya a yacca na ke jin soyayyarsa da feelings ɗinsa tamkar ban taɓa sanin komai ba a game da soyayya da aure. shi yay ƙarfin halin da ya raba jikinmu yana sauka akan gadon yace,"Myy ba zan yarda ki ƙara kwana ba, zan faɗa musu yau zamu wuce kin ji".

Knooding kaina kawai na masa, ya fita yana faman shafa kansa, na bi bayansa da ido har lokacin ina jin rungumar da yay min wadda naji kamar muna manne ne still. Babu jimawa sai ga shi ya dawo da tray na abinci, ya zauna yana cewa da ni na sakko, na dube shi na ce,"Wai kai Salim baka jin nauyin mutanen da ke kallonka ne?".

Shiru yay min sai da ya gama zuba faten doya kana ya dube ni yace,"Kina cin Teba?". Gyaɗa masa kai na yi nace,"Jiya da aka kawo ya bani sha'awa". "Oya to sakko".

Na zamo akan gadon yace alalle sai dai na zauna saman cinyarsa, naƙi babu yanda bai da ni ba, yace ya ɗaga min ƙafa ne kawai saboda ba gidanmu ba ne, ina masa dariya na kai hannu zan fara ci ya riƙe hannun nawa, da kansa ya ke bani na tambaye shi miyan menene yace min sunanta Ogbono soup, yana sonta sosai na dage na iya zan mallake shi da ita. Sai da ya tabbatar na ƙoshi kafin ya bar ɗakin har yana zolayana,"Da ga cin teba sau ɗaya har kin zama ƙatuwa".

Na ce masa ko dai daga ci har gari ya tsotse ni. Yay dariya yana ƙwafa wadda na san ma'arta. Karfe biyu wata budurwa ta shigo ɗakin sa'ilin muna magana da Safiyya, wadda ke ta bani tips na kula da miji, tana ce min ko da naji ana matan ƙabila na ƙwace miji ba da asiri ba ne ba kuma makirci ba ne, kawai tsantsan iya kula da buƙatunsa ne da iya tattalinsa su mayar da shi kamar jariri, babu batun kuma an girma an aje ƴaƴa shikenan batun soyayya ya tashi, riƙe abinsu suke da ladabi da biyayya jin kai duk a aje a gefe ayi ta gurzar lamura, har tana faɗin banda dai aure rubutaccen al'amari ne da ita dai bata ga me zai sa Salim ya ƙara aure ba, domin Kudrat kat ce wajen sanin zamantakewar aure, naji haushin maganar ma Safiyya har zuciyata na ɗarsa min ko kishi take taya Kudrat ɗin, to nima dai za su ga salon nawa mallakar mijin ne babu boka babu Malam.

Budurwan da ta shigo tace Maa ta turota ta shirya amarya, lokacin bamu jima da gama cin wani abincin ba, duk da cikina a cike yake da wanda Salim ya bani, to saboda kar Hajjo ta tsare ni da tambayan inda na ci na ƙoshi dole haka nasa hannu, ni kam har na gaji da ganin abinci ma. Duk wanda muka zo tare sai da aka basa kayan shigan partyn ya saka, ni kuwa ban san ta yanda zan faɗa muku haɗuwar da nayi cikin shigar da aka min ba, Safiyya ta ƙwala wani ihu tana tafi da tsalle tana cewa,"Ke kam ai zam igbo ɗin, wallah wanda bai san ki ba zai rantse ba bahaushiya ba ce". shigan blue akan min ni kai na da na kalla madubi sai da naji na burge kaina, ku kuwa dama sai dai na barku da haskowa idanunku kawai.

Lokacin da aka fito da ni Mommi ta riƙe ni ta tsayar da ni gefen Salim, wanda kaɗan ya rage ban sume ba saboda yacca ya tafi da ni a kyan da yay cikin shigarsu. Ga wata sanda ta ƙarfe ta ya riƙe, kai ba ka ce sojana ba, fuskarsa sai annuri take fiddawa. Ranƙwafo kansa yay saitin kunne na yana cewa,"Baby kyan da kika yi kaman a sace a gudu, to Allah ya so ma ni zan ɗauke kayata ba kuma me hana ni, nan gani nan bari ɗumamen maya".

Na waro ido ina ce masa,"Har da su karin magana ka iya, lallai ne Onochie".

Ƙuguna ya matsa yana murmushi. Tab lallai arziƙi na inda yake, haka talauci ma na can inda ake kukan babu, ashe duk girman compaound ɗin nan akwai inda ya fishi, ta can ciki wani wawakeken fili ne anan suke shagulan bikinsu babu ruwansu da kama event center, an ƙawata wajen ka rantse wani mashahurin event center ɗin aka kama, plate na abinci ne kawai ke haske maka ido da drinks. ni dai kaina na ƙasa amma ba ƙarya kowa a wurin abun kyau da burgewa ne, Musamma yaransa da aka yi musu shiga iri ɗaya suna zaune a gabanmu kan kujeran da muka zauna, suma kamar ni hannayensu duk da ƙananan mafitai me gashi.

Hoto kawai ake ta ɗasa mana, sai naji ina ma acan gida ne nayi hoto da mahaifiyata da ƴan uwana, ba shakka Yaya Imam ma zai kyau cikin irin shigar nan, sai dai na san ko me za'a masa ba zai saka murjani a wuya ba. Taro yay taro, duk ba wasu mutane ne da aka yi gayya ba iya Family ne kawai, Safiyya ce ta gabatar da ni ta faɗi tarihina tun daga haihuwa har kan matakin aikina, Kudrat ma ta zo masha Allah wallahi da na ganta sai da na raina kaina, ashe kyan da na gani jikin ƴaƴanta da wanda ake faɗa min ba komai ba ne.

Nayi ta mamakin me ya kai salim ƙara aure shi kuwa yana da wanga zuƙeƙiyar mata. Babu ruwanta sakaraftunta kawai takeyi cikin farin ciki kamar ba wadda miji kewa kishiya ba, ni da ka aka kawo ma na fita kishin miji, har da su zuwa tayi mana liƙi, haka ta zo tana ta yaƙe min haƙora hoto kuwa mun yi da ita yafi a ƙirga, tun ban sakin jikina da fuska da ita sai da na rissina, kowa na ta rawa ni dai na kasa saboda kunya, Salim kuwa ya zage yana ta abarsa shi da ƴaƴansa da matarsa, Kudrat ɗin ce ma ta kamo hannuna ta shigo da ni tsakiyar su tana rawar tana aikin watsa mana kuɗi dukkan mu.

Ba'a watse a wajen ba sai ƙarfe bakwai Granny ya aiko a kashe kiɗa aje ayi ibada, sai lokacin naga Salim ya murmusa, don tunda ya gama rawarsa yaci magani sai zungurana yake wai ana ta ɓata lokaci salon aja masa ƙin tafiya da ni yau, ni dai dariya kawai nake ƙasa ƙasa, kunya na ke ji na biye masa yanda idon kowa ke a kanmu. Fakar ido yay ya fige ni muka shige wani ɓangare, yace min da na koma ciki kawai in cire wannan kayan hayaniyar na shiryo na fito, nace masa ni kam ban iya rashin kunya ba, sai ya matse bakina na samu dai na zilla masa ganin abinda yake ƙoƙarin aikatawa.

Ai kuwa ana can ana nemana duk sai naji kunya, ina jin wata mata ina ga inlaw ce a gidan tana faɗin a bawa Onochie matarsa su wuce yau, Kudrat ma ta hango ni ta taho da hanzarinta tana ce min a yau fa zamu tafi gaskiya ba za'a kuma barinta kwana a gida ita ɗaya ba tunda dai mijina ba barinta kwana anan zai yi ba.

Nace da ita,"Tafiya da wannan daren?". Ranta fess tace,"Mene dare? Shi bai faɗa miki babu nisa ba, 2hours ne fa kawai zuwan".

A hankali na ce mata,"Da dai mu bari sai goben ma tafi da safe". Hannuna kawai ta kama muka yi ciki sai ɗakin Maa. Ita ta kira shi a waya tana faɗa masa wai ya shigo ya shirya ni mu tafi, ni duk sai ta bani mamaki sosai, kamar ba kishiya aka mata ba, to ko ba auren soyayya suka yi ba ne? Ko kuwa dai dama matan arewa ne kawai ma su kishi?. shi kuwa sai ce mata yayi to idan ni ban son tafiyan ta kwaso masa yaransa su tafi yana jiransu a waje idan ya so gobe ni na kai musu kaina.

Yanda yay maganar sai da nayi dariya don a fusace yayi ta. Can ɗakin da muka sauka na koma, Umman su Safiyya ita ta shirya ni, tayi min shigarmu ta hausawa kamar dai jiya swizz less ne na saka blue sai faran lafaya, haƙƙun nayi kyau ko a faɗa ko kar a faɗa, duk wanda yace ban ba to ɗan hassadata ne. Yo idan ka ganni ma ina zaka taɓa cewa Sa'ida ta taɓa aure? Ina zaka taɓa cewa ba tsaleliyar budurwa ba ce a gabanka? Rantsuwa kuwa idan za'a kwana ana maka da labarin irin rayuwar da nayi a baya ba zaka taɓa yarda ba, to ina ma wani alama da zai nuna na fuskanci ƙabulace me raɗaɗi a rayuwata, canjin rayuwar fa ba ƙaramin canji na samu ba sai dai godiya ga me sama kawai, shiyasa aka ce haƙuri ba yawa, me haƙuri ba ya tawaya, haka kuma me haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa, ga matakin nasarar da haƙurin ya kawo ni nan.

Sai da naga dai an gama shirya ni da gaske tafiya zamu yi sai kuka kamar daga cikin gidanmu za'a ɗauke ni, Nasihan da Hajjo ke ƙara min ita ta sake karyar min da zuciya, hatta Maman Khairi da Maman Yasmin sai da suka yi hawaye, na ce a bani waya na kira Abbaa, kaman kuwa yana jiran kiran nawa shima don bugu ɗaya ya ɗaga, na ce masa gani yanzu za'a wuce da ni can gidana, nan yay ta min adu'a yana ƙara jaddada min nasiharsa gare ni, muka yi sallama da shi sabon kuka na ƙara zuwar mini.

Sai da su Gwaggo Abula suka fara fita kafin Umman su Safiyya ta fito da ni kaina na ƙasa. Falon Sir aka kai ni, a can na tarar da Salim ɗin shi da Kudrat, dukkanmu Sir ya haɗe yay mana faɗa da nasiha, nasiha me tsuma zuciya. Daga nan aka kai ni can wajen Maa wannan karon kuma da gani sai shi ne, Itama tayi mana nata adu'oin irin na kowacce mahaifiya ta ƙwarai, musamman shi da take faɗa masa ya zama me adalci tsakaninmu, kar ya taɓa bari wani abu da zai haddasa ƙabilanci a tsakaninmu ya afku. Har Maa aka rako mu compound tana riƙe da hannuna ita ta saka ni cikin mota, su Hajjo na ta yi musu godiya da irin karramawar da aka yi mana.

A motan da na ke Mama A'i ne da Hajjo sai Gwaggo Abula da Safiyya, ɗaya kuma su Maman Yasmin ne a ciki, ɗayar kuma Salim da iyalansa. To a motar ma tun ina kuka har na gaji na daina, na biyewa hirar da ake, yo tafiyar ba ta minti goma zuwa talatin ba ce, awa uku ne babu kaɗan, zuwa sha ɗaya na dare dai mun isa, Kamar dole Salim da rigima dai da yay haƙurin. Naji ƙaran shigowar message a wayana, ina dubawa na ga lambar Lubabatu ne, mamaki ya mamaye ni ita kuma message da wannan daren haka? Me zan mata? Ni fa bana ƙaunar wani iri na Nazifi Bala Mai Kalwa ya ƙara gifatawa a rayuwata, Tun ban buɗe ba kuwa nayi regretting bata lambar tawa, sai dai ko da na duba saƙon magana yake akan.

_"Don Allah ki yafe min Sa'ida, hakkinki ba zai bar ni ba, ban da idon da zan zo gaban ki na fuskanceki na nemi yafiyarki, don Allah ki ce kin yafe min, na gode sai naji daga gareki, ba ni da waya ne a hannu"._

Tsaki nayi na goge message ɗin, can kuma sai zuciyana tace na mayar masa da amsa tunda shi bai da hankali bai san menene aure ba, kar ya zo ya ƙara turo min saƙo mijina ya gani ya rikita min zama ya tashi hankalin farin cikina.

_"Idan ba so kake ka ƙare rayuwanka a gidan yari ba to kar ka ƙara turo min saƙo, domin kuwa mijina ba zai ƙyale ka ba. Yafiyata ka jira mu haɗu a kotun Allah gaban alƙalin da ba ya zalunci"._

Mun isa Delta State lafiya, na shiga gidana da ƙafar dama, wata faɗuwar gaba da ban ji ta ba tun ranar ɗaurin aure sai yanzu ta ziyar ce ni, jiki a sanyaye fuskana na rufe haka na tako cikin falona, Umman Batula na faɗin shiga da Bismillah, suna biyo min ayoyin da zan karanta, kai yanda ake tayi da ni fa kamar auren budurwa b abazawara ba.

Suna kai ni cikin ɗakina duk suka watse aka bar ni daga ni sai Safiyya. Ganin har lokacin ina hawaye ta daki kafaɗata tace,"Beb wannan hawayen ya isa sai kace wacce ta auri wanda bata so? Bafa auren farko bane na biyu ne balle kice min kina tunanin first night, haba mun fa girma Beb". Ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya ta shakiyanci.

Sai kuma ta tsuke fuska taja tsaki tace,"Allah ya isa da mai kalwa ya same ki a banza, ina ma ɗan uwana ne ya aureki tun farkon farko ba mai kalwa ba shege matsiyaci". Sai ta sake sakin fuska tace,"To ya za'ayi da ƙaddara ce Allah ya riga ya rubuta. Ke ki kwantar da hankalinki ki kwashi soyayya, wallahi Salim ba shi da matsala na san kin sani, ki cire batun fargaban zai sameki wani ya riga shi shiga hanyar, yo dama ai a yanda ya ganki ya ce yaji ya gani har sai da ya amso ki hankalinsa ya kwanta. Anty Kudrat kuwa zan ta nanata miki sauƙin kanta ya wuce tunaninki, matar nan dabance, don ni ko yau aka ce an samu matsala to wallahi Beb ke zan fara ɗorawa ayar tambaya".

Ni dai kallonta kawai na ke yi, cikin raina tunani kawai na ke yi akan sabuwar rayuwar auren da zan fara a karo na biyu, shin ya zama zai gudana tsakanina da Salim? A yanzu ni dai ba za'a kira ni mara ilimi da rashin wayewa ba, haka ba za'a kalli kayan da iyayena suka zube min a cikin gidan ba a goranta min da ɗiyar talakawa, fatana na samu ɗorewar farin ciki, sai dai a ko da yaushe ina hangen wani nakasu da na ke tare da shi, nakasun rashin haihuwa wanda shi ne maƙasudin lalacewar zaman aurena, ban sani ba, ban kuma san ta ya wa'annan ahalin za su karɓi lamarin ba, shin za su nuna min banbanci ne ɓaroro da matar gidan da ta riga ta ƙyanƙyashen ƙwai ba ɗaya ba ba biyu ba? Ko kuwa za su zama masu goranta min ne da hantarata kamar waɗancan?, duk ba wannan ba shi wanda ya ɗakko ni ya aje ya rayuwar tamu zata tafi da shi idan muka haura wasu shekaru ban samar masa da haihuwa ba, ko kuma zai mayar da ni bora ne soyayyarsa, mutuntawarsa da darajartawarsa na ga uwar ƴaƴansa? Ban san ya ubangiji ya tsara rayuwata ba, wataƙila ina ɗaya ne daga cikin bayinsa da ya jinkirtawa haihuwa ne, ko kuma ina daga cikin waɗanda bai rubuta suna da rabon samun haihuwar ba har su koma gare shi.

Safiyya ta kalla agogo sai ta miƙe ta ɗauki mayafinta da jakarta tana ce min,"Sai ki yi ta aikin tunani da hawaye kin ji, ke da ba ki jin shawara, ni dai zan wuce sai da safe, wajen Anty Kudrat zan tafi, babu ke ba zan iya kwana cikin su Hajjo ba".

Na gyaɗa mata kai kawai, ai dai tare zamu kwana da ita a cikin gidan na matuƙar jin daɗin hakan. Har ta nufa hanyan fita sai ta dawo ta sake zama kusa da ni tace,"In yazo yaga kina wannan kukan ba zai ji daɗi ba fa, zuciyansa zai so su duk ki saka shi a damuwa, dan Allah ki daina ki saki jikinki komai zai tafi dai dai da izinin Allah".

Sai kuma ta dungure min kai tana faɗin,"Munafuka me kukan gulma, nan da anjima sai dai in jiyo na tashi, to earpiece zan saka ba zan kawo ɗauki ba".

[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR15FT5* Cikin dare ciwo ya tasar min, tun ina dauriya ni ɗaya abu har yaci tura, gurnani na ke ina nishi ina wani irin miƙa, da kwance na ke kan benci haka har na faɗo ƙasa ban sani ba, malelekuwa kawai nake yi har ta kai ga na fara mawahalcin kakari kamar zan yi amai. Ɗan sanda da ke tsare da ni ya leƙo yana buga min tsawa tare da faɗin na ishe su na kiyaye na natsu.

Ina kuka cikin ƙarfin hali na ce masa"Ka taimaka min da ruwa".

Sai ya ƙara doka min tsawa yana cewa,"Ba za'a bayar ba".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull