Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 12

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 12

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 12: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 12. Kaina na jinginar da bango ina ta sauke numfashi wanda ma sai na…

4,499 words

Kaina na jinginar da bango ina ta sauke numfashi wanda ma sai na matse hancina na buɗe baki kafin nan na samu na shaƙi iska. Juya kaina nayi ga bakin ƙofar, idanuna a rufe ina ta so na buɗe su amma sunƙi buɗuwa, murya na fita da ƙyar na ce,"Ka taimaka min don girman Allah, ina da ruwa a cikin nan ka yiwa darajan Allah ka hasko min fitila na duba".

Ni ban sani ba ashe ya hasko ɗin, sai ji nayi yana masifa cikin ɗagawar murya yana cewa,"Ba za ki ɗauka ba ne na kashe fitila ta".

A rikice na ce,"Yi haƙuri ban san ka kunna ba, idona bana gani don Allahu ku taimaka min". Na faɗa cikin ruɗewa ina lalube da hannu.

Hasko fuskarta yay, ya tsaya na ƴan sakanni yana kallonta kafin yasa maƙulli ya buɗe ƙofar ya shigo. Naji shigowar tasa amma ban san ta ina yake ba, sai jinsa nayi yana cewa,"Me ya sami idon na ki?".

Na dinƙa ɗaga murfin idona yaƙi buɗuwa sam, tsoro da tashin hankalin da na ke ciki suka ninku, take na fara tari babu ƙaƙƙautawa, sai ji nayi ina tofar da wani abu mara daɗin ɗanɗano a harshe. Naji ɗan sandan ya furta,"Subhanallah, ba ki da lafiya dama ba kiyi bayani ba tun ɗazu".

Ba zan iya magana ba a halin da nake kam, ni dai taimako kawai na ke buƙata a lokacin, a bani maganin da zan sha zuciyata ta bar zafin da take yi, haka kuma a buɗe min idanuwana da suka kasa buɗuwa, sannan a bani in sha ruwa, fitarsa naji, take na shiga ambaton Allah ina kuka ina roƙonsa da ya buɗa min idanuwana, kafin na koma kiran sunan Abbaana. Can sama sama naji mutane akaina ana magana amma ban san me suke faɗa ba, kafin naji kuma an kinkime ni can nesa nesa naji ana batun asibiti.

*Ƙarfe Bakwai na Safe.* Abbaa ya fito daga ɗakinsa yana kiran sunan Ummani, ta fito daga kitchen da sauri ta iso gabansa da leda baƙa a hannu. Miƙa masa tayi cikin sanyin yanayi tace,"Don Allah ko na sako mayafina na bika, ina so naje naga ya ta kwana".

Abbaa yaja numfashi ya sauke, hannu yasa a aljihu ya ɗauko kuɗi. Tsohuwar ɗari biyu ce ya nuna mata yana cewa,"Ki yi haƙuri naje ni ɗaya, kinga ko ni ɗaya wannan ba zata kai ni ba balle har mu biyu, dole nima sai dai nayi rabi tafiyar ƙafa rabi ta mota".

"To ko aikawa zan yi a taso Yashaik?". "A'a don Allah mu bar yaran nan su huta haka nan, tun da ni zanje ai ba sai kin damu ba. Kuma dama sun ce yau ɗin zasu bayar da ita in sha Allahu".

"To ubangiji Allah yasa, Allah ya amince saboda sirrin la'ila ha'illallahu. ga shi nan ma na saka mata sauran awarar jiya da bamu ci ba naji bata yi yami ba. Don Allah kasa taci abincin kaga tana da ulcer".

"In sha Allahu. Bari na wuce". "Tom aje lafiya a dawo lafiya, amma idan anyi cinikin lemo zaka ganni na taho".

Kai kawai ya gyaɗa mata ya fita. Kana duban idonsa ka san ido biyu ya kwana, haka kana ganin yanayinsa kaga na me ƙarfin hali, dauriya kawai yake yi, dauriya saboda ƴarsa da iyalansa. Haka yake tafiya da ƙyar, bai jima a bakin titi ba ya samu me napep ɗin da ya ɗauke shi da taimako har ƙofar na'isa a naira ɗari.

Zone 1 shine headquater ɗin dama da case ɗin yake, ko da yaje dakatar da shi aka yi daga waje aka ce ya jira zuwa ƙarfe goma, babu irin roƙon da bai yi musu ba akan su taimaka ko abinci ne su barsa ya bata amma suka ƙi sai karɓa suka yi, sai bayan ya shafe awa guda har da rabi sannan ɗan sandan da ya shiga kai mata abincin ya dawo yana faɗa masa ai ya manta ma anje da ita asibiti babu lafiya tun daren jiya.

Ai jin wannan furuci Abbaa ya nemi yanke jiki ya faɗi, su kuma ƴan sandan babu tausayi bare imani don haka babu wanda yabi ta kansa, da taimakon ubangiji ya samu kansa, tunaninsa ɗaya me ya sami Sa'ida kuma wanne hali take ciki? duk yanda ya so su faɗa masa asibitin da aka kaita suka ƙi, har sai sha biyu na rana lokacin AIG ya shigo, sannan ne insifecta Usman wato Yayan Zahra'u ya kira shi ofishinsa.

Lokacin su Ummani da Yayyun Sa'ida kaf sun zo har da Kaka, sai da aka jira zuwan su Nazifi sannan Insifecta yake shaida musu da cewa an tura case ɗin na su gaba zuwa Fagge Shari'a Court, kuma zasu fara zama a sati na gaba in Allah ya kaimu, saboda haka sai su nemi lauyan da zai tsaya musu. Nazifi yace babu matsala suna da lauya a hannu, su Abbaa dai basu iya cewa komai ba illa ma dukkaninsu tunanin ta in da zasu fara nema lauyan da kuɗaɗen da za'a fitar suke, ga babban tashin hankalinsu an ce basu da damar ganin Sa'ida, Ummani tun tana kuka da hawaye har ma ya daina zuba sai dai ka jita tana fizgar numfashi, Abbaa ma duk ƙarfin halinsa da dauriyarsa sai da ya karaya, Ƴaƴansu ne kawai masu ƙarfin gwiwa da suke tausar su.

Malam mahaifin Nazifi zai yi maganar cewa ko za'a iya basu lauyan da zai tsayawa Sa'idan, zuwan Safiyya ya katse maganar tasa wadda ta zo ita da Antynta da kuma lauya, wacca ta gabatar da kanta wa Insifecta. Ta kuma karɓi bayanai da date ɗin fara zama, daga nan ta buƙaci a kaita wurin Sa'ida nan aka shaida mata cewa tana asibiti, haka aka haɗata da ɗan sanda wanda suka tafi da shi can asibitin.

*23-Nove-2023, Fagge Shari'a Court, Muhammad Murtala Way, 10:30am.*

Kotun bata cika sosai ba iya ƴan uwa ne na jiki wanda suka san da case ɗin sai baƙin fuska ƙalilan wanda sha'awar sauraron shari'a ya saka suka zauna. Bayan shigowar Alƙali rajistara ya tashi tsaye yace,"A yau juma'a sha bakwai ga watan nuwanban shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, wanda yayi daidai da uku ga watan jumada auwal shekara ta dubu ɗaya da ɗari huɗu da arba'in da biyar A.H. zamu saurari ƙarar Zahra'u Abdullahi wacce take ƙarar kishiyarta akan kashe mata yarinyarta da tayi har lahira". Ya faɗa yana tattara file ɗin ya miƙawa Alƙali ya karɓa yana dubawa.

Shiru kotun tayi na wani lokaci kafin Alƙali ya kalle su yace,"In lauyoyi masu kariya suna kusa su gabatar da kansu."

Wani dogon namiji baƙi mara tsaho sosai ya miƙe ya ce,"Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Mu'azzam Ibrahim ni ne Lauyan mai ƙara". Ya faɗa yana zama.

Wata Mace doguwa mara jiki ta miƙe itama tace,"Sunana Barr Zaliha Muhammad, ni ce lauyan wacce ake ƙara". Ta faɗa tana zama itama. Alƙali ya fara rubutu a kan file na wani lokaci kafin ya ɗago yana kallon su.

"Lauyan wanda yake ƙara ko yana da abin faɗa?". Alƙali ya faɗa yana kallon su.

Miƙewa yayi yace,"Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai alfarma da ta bani dama domin yiwa wacce ake zargi tambayoyi".

"Kotu ta baka dama". "Na gode ya Mai Shari'a". Ya faɗa yana fitowa ya ƙarasa inda Sa'ida take tsaye yana kallonta.

"Malama Sa'ida ko za ki iya yiwa kotu bayanin yarinyar da aka rasa wacece a wajan ki?".

Sa'ida ta haɗiye yawu ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce,"Ƴar mijina ce". Ya kalleta da kyau ya ce,"Ƴar kishiyarki ce kenan ko?".

Sa'ida ta ɗaga kai alamun eh. ya girgiza kai ya ce,"Ke ina naki ƴaƴan?".

Tambayar tashi ta motsa zuciyata, na ɗago ido ina kallonsa kafin na ce,"Bani da su". Ya girgiza kai sannan yace,"Kenan dan ba ki da su shiyasa kika kashe ƴar kishiyar ki?".

Da mugun faɗuwar gaba na sake kallonsa jin yana neman ƙara ɗaure ni. "Ina da ja Ya mai girma mai shari'a!" Barr Zulaiha ta faɗa tana miƙewa tace,"Bai kamata lauyan mai ƙara ya fara yiwa wacce ake zargi tambaya akan abin da ya shafi rayuwar ta ba. Rashin yara abu ne da ya shafi rayuwarta bai shafi case ɗin da muke magana a nan ba".

Mai shari'a yace,"Barr Mu'azzam a kiyaye". Yace,"Na gode ya mai shari'a".

Ya kalle ni yaci gaba da cewa,"Ƴar mijinki ƴarki ce Malama Sa'ida amma meyasa kika kashe ta?". Na kalle shi nace,"Wallahi bani na kashe ta ba". "To waye kasheta?".

Na share hawayen idanuna na ce,"Kawai ta rasu ne amma bani na kashe ta ba". "Me ye silar rasuwar tata shi za ki faɗa".

A hankali nace,"ban sani ba nima". Ya sake kallona yace,"Kenan da gaske ne ke kika kashe ta?".

"Wai sau nawa zan maimaita ban kashe ta ba?". "Ki daina ɗaga mana murya". "To ya ku ke so nayi, iyaka gaskiyata na ke ta faɗa muku amma kun ƙi yarda". Na faɗa ina jin tamkar zan shiɗe.

Barr Mu'azzam ya kalli mai shari'a yace,"Ya mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai adalci da tayi duba akan bayanan Sa'ida sannan tayi duba akan itace ƙarshen ɗaukar yarinyar da ta mutu, yarinyar da lokacin tana hannun mahaifiyarta lafiya lau take, amma da Sa'ida ta ɗauketa sai ta mutu alhalin bata ɗaukar yaran, To babu wuta me ya kawo hayaƙi? Saboda haka Ya mai girma mai shari'a ina so a duba halayen mata akan kishi, tabbas Sa'ida zata iya kashe yarinyar kishiyarta ko don ganin cewa ita bata da su. Don haka na ke roƙon kotu ta hukunta Sa'ida akan laifin kisan da ta aikata kamar yanda mahaifin yarinyar da mahaifiyarta ke roƙon a ƙwatar musu hakkinsu. Na gode ya mai shari'a". Ya faɗa yana dawowa ya zauna.

"Ko lauyan wacce ake ƙara tana da abin faɗa?". Cewar Alƙali.

Ta miƙe tsaye tace,"Ina da shi ya mai shari'a. Ina roƙon wannan kotu da ta bani dama na kira Zahra'u Abdullahi mahaifiyar ita yarintar da aka rasa".

Wani a cikin kotun ya miƙe yace,"Malama Zahra'u Abdullahi in kina kusa ki fito".

Tasowa tayi with confidence. Barr Zaliha ta matso kusa da ita tace,"Malama Zahra'u ya ƙarin haƙuri?".

"Haƙuri da godiya, Na gode".

Barr ta numfasa sannan tace,"Malama Zahra'u ko za ki faɗa mana hujjarki da zata tabbatar mana da Sa'ida ce ta kashe miki yarinya?".

Ta gyara tsayuwarta tana kallona, wanda ƙwayar idanuwanta ke nuna tsantsar tsanata a ciki tace,"Saboda itace ƙarshen ɗaukarta kuma goye a bayanta ta rasu".

Barr ta girgiza kai tana murmushi tace,"Wannan ita ce kawai hujjar ki?".

Ta ɗaga kai bayan ɗauke idonta akaina tace,"Zata iya kasheta saboda tana baƙin ciki ita bata haihu ba, shiyasa da ta goyata tayi mata wani abun har ta mutu".

"Kafin wannan lokacin Sa'ida ta taɓa yunƙurin kashe yarinyar?". Ta girgiza kai tace,"Bata taɓa ba".

Barr ta jijjiga kai,"Ok amma ta taɓa ƙoƙarin shaƙeta ko bata wani abun da zai iya zama silar barinta duniya?". "A'a bata taɓa ba". "Kenan akwai kyawun alaƙa ta nuna kulawarta akan yarinyar kafin ta rasu?".

Wannan tambayar da Barr tayi mata sai na saddaƙar, domin dai na san daga ita har Nazifi da Iyam babu wanda zai amsa wannan tambayar da gaskiya. Sai dai kuma mamaki ya kamani da amsar da ta bayar wanda na ke da tabbacin ubangiji ne ya matsi bakinta ta faɗi hakan.

"Ehh to gaskiya tana son yaran, farkon haihuwarsu tana nuna kulawarta akan su, hasalima ni na shiga tsakani na nuna mata bana so tana raɓar min yara, na hanata ɗaukarsu kwatakwata, to da yake tana da sanyin hali da haƙuri sai kawai ta janye jikinta da su saboda a zauna lafiya".

Barr tayi murmushi tace,"To amma kuma duk wannan kyakykyawar shaidar da ta samu daga bakinki me yasa kuke zargin ita ta kashe miki ƴa?".

Ta kalli Barr tace,"Saboa itace ƙarshen ɗaukarta, kuma a bayanta ta mutu".

"A bayanta ta mutu? Kenan kin ganta da idon ki lokacin da ta kasheta?". Ta girgiza kai alamun a'a. Barr tace,"Magana za kiyi".

Ta ce,"Ban ganta ba". Ta faɗi hakan jiki a sanyaye.

Barr ta juya ta kalli Alƙali tace,"Ya Mai girma mai shari'a ina so ayi duba a bayanan mai ƙara, ayi Nazari za'a tabbatar da babu hujjar da zata gamsar da kotu cewa Sa'ida ita ta kashe yarinyar, ko don duba da yadda ita uwar yarinyar ta faɗa na cewa Sa'ida mutuniyar kirki ce. Idan mai shari'a ya bani dama zan gabatar da insifecta Usman Abdullahi wanda shine ɗan sandan da ya isa da gaggawa gidan a lokacin da abun ya faru".

"Kotu ta ba ki dama".

Kamar ɗazu wani ya tashi ya buƙaci shigowar Insifecta Usman. Shima bayan ya zo Barr ta kalle shi ta ce,"Insifecta lokacin da kuka isa gidan Alhaji Nazifi Mai Kalwa, wanne makami ku ka samu da Sa'ida tayi amfani da shi ta hanyar kashe ƴar kishiyarta?".

"Babu". "Kace Babu? Kenan da me ta kasheta?".

Numfashi ya sauke yace,"To a iyaka duk binciken da muka yi gaskiya babu wani shaida da ke nuni da cewa kashe yarinyar aka yi, don ko hoton sawun hannaye duk mun ɗauka na inda ita Sa'ida ta tattaɓa, kuma binciken likitoci ma babu rahoton nuna cewa kashe yarinyar aka yi".

"Ok kenan har likita ma yay nasa bincike akan rasuwar?". "Ehh ƙwarai kuwa, likitoci har uku ma". "Da kyau, kun zo da rahoton?". "Ehh mun zo da shi". "Ko zaka iya bamu?".

File ɗin da ke hannunsa ya bata, ta karɓa tana faɗin,"Na gode, kana iya komawa". Daga haka ta miƙa file ɗin wurin Alƙali.

Alƙali yay rubuce rubucesa, sannan Barr Zaliha ta ce da shi,"Idan mai shari'a ya bani dama ina so na gayyato likitan da ya duba yarinyar domin yayi mana bayani yadda zamu fahimta".

Alƙali ya sake yin rubutu yace,"An ba ki dama".

Aka nemi ganin likita ya ƙaraso ya tsaya, ta ƙarasa kusa da shi tace,"Dr ko zaka iya faɗa mana sunan ka?".

"Sunana Dr Bashir Adam ƙwararre a fannin likitan ƙananun yara."

Ta jijjiga kai tace,"Me ya kawo ka zaman wannan kotun?".

"Domin bayar da rahoto akan binciken lafiyar wacce ta rasu".

"Wa ya buƙaci da kayi binciken?". "Insifecta Usman".

"To ko zaka iya mana bayanin rahoton rasuwar Salma Nazifi Mai Kalwa wato Noor, jaririya me kimanin kwana talatin da ƴan kai, wacce ka tabbatar da hukumar ƴan sanda sun baka damar yin bincike akanta?".

"Ehh zan iya domin da kaina na dubata lokacin da Insifecta Usman ya buƙaci na tabbatar musu da ta rasu ko tana raye".

Barr tace,"A yayin da kake dubata akwai shatin shaƙa ko guba a jininta wanda zai tabbatar mana da kasheta akayi?".

Likita ya girgiza kai yace,"Babu ko ɗaya a ciki, domin kuwa ta silar ciwo ta rasu ba silar guba ko shaƙa ba".

Barr Zaliha tace,"Ciwo dai?". "Ƙwarai ciwo". "To wanne irin ciwo kenan, ko zaka iya yi mana bayaninsa da kuma adadin kwanakin da ya ɗauka a jikinta".

"Jaundice shi ne ciwon da ke tare da yarinyar, wanda kuma ya kai kimanin kwana talatin da biyar a jikinta, shaidar cewa da shi aka haifeta, kuma symptom ɗinsa a bayyana yake ba'a ɓoye ba, za'a samu fatar jariri tayi yelo da idanuwansa, yelo sosai, to shi wannan ciwo dama idan ya zama chronic har yay yawa ya hau ka shi ne yake leading to death, so yawanci iyaye idan suka haifi yaro a haka tunaninsu ba ya basu ga cewar ya kamata suga likita, sai su tafi akan an haifi yaro da rana ko shawara, in da kuma sai su tsaya a iya maganin gida, wasu iyayenma suna ganin hakan amma sai suyi ignoring su zuba ido har azo a rasa jariri".

Barr tace,"Wato Dr idan na fahimceka wannan ciwon da kayi mana bayani shi ne silar barinta duniya ba dalilin hannu ko wani abu da aka bata ba?".

Ya jijjiga kai cikin tabbatarwa yace,"Ƙwarai da gaske shi ne silar rasuwarta, bayan shi gaskiya babu wani abu".

Tayi murmushi tace,"Na gode likita, zaka iya komawa ka zauna".

Ya juya ya koma itama kuma ta kalli alƙali tace,"Ya mai shari'a ina so ayi duba ga bayanan Likita da bayanai akan ciwon da ya kashe yarinyar a tabbatarwa da jama'a Sa'ida ba ita ta kashe yarinyar ba, Allah ya nuna a bayanta zata rasu ne amma bawai dan ta kashe ta ba. Haka ma idan aka ƙara duba bayanan mahaifiyar yarinya, Da wannan na ke so kotu tayi watsi da wannan ƙara domin babu komai a cikinta sai zallar ƙazafi da son cutar da Sa'ida, sannan ina nemawa Sa'ida hakkinta akan sharrin da akayi mata. Na gode". Ta faɗa tana komawa ta zauna.

Alƙali yayi rubutu kafin yace,"Shin lauyan da yake ƙara ko yana da abin fad'a?".

Barr Mu'azzam ya tashi yace,"Babu ya mai shari'a".

Mai shari'a yayi rubutu na wani lokaci, kotun tayi shiru ana jiran hukunci kafin ya ɗago yace,"Duba da rashin hujja gamsashshiya da ba'a samu daga ɓangaren masu ƙara ba, da kuma bayanai da hukumar ƴan sanda ta bayar, da rahoton likita da ya bayar zai tabbatar mana da abin da ake zargin Sa'ida da shi bata aikata ba".

Ya sake yin shiru yana rubutu kafin ya sake cewa,"Wannan Kotu mai adalci ta wanke Sa'ida Salman Madobi daga zarginta da ake yi akan laifin kisa, bata da hannu kuma bata aikata ba, duk wasu bayanai da hujjoji sun tabbatar da hakan. Sannan kotu zata ci tarar Zahra'u Abdullahi da Nazifi Bala Mai Kalwa akan ɓatawa wadda suke ƙara lokaci, da wahalarwa, da kuma ɓata mata suna da tayi, ta ɓatawa shari'a lokaci, bisa hakan kotu taci tararsu naira miliyan ɗaya da rabi. Sannan Kotu na gargaɗin Nazifi Bala Mai Kalwa da Zahra'u Abdullahi akan ko dan gaba yana da kyau su san gaban alƙali ba wajan wasan yara bane, su samu hujja mai ƙarfi kafin su shigar da ƙara in ba haka ba nan gaba kotu zata hukunta su".

Da haka alƙali ya buga teburi ko ya tashi da faɗin koootuuu. Ahalina da dukkan magoya bayana muryoyinsu da ke fitar da kalmar Alhamdulillah ita ta karaɗe cikin kotun gaba ɗaya. Ta ɓangarena kuwa zan iya cewa babu wani abu da naji a tattare da ni na farin ciki ko na murna, haka babu akasinsa domin kuwa cikin kwanakin nan da nayi a cel jina na ke tamkar wadda babu zuciya a ƙirjinta.

Safiyya ta zo da saurinta ta rungume ni tana kukan farin ciki, Ummani ma haka, ina kallon yanda mahaifina ke share ƙwalla wadda na san bata komai ba ce illa tsananin farin ciki da murna. Yaya Imam da Yashaik na can gefe suna tattaunawa da wani insifecta. A wannan lokacin ƙyam na ke a tsaye, ƙwayar idona ta gama wurgawa kan kowa da komai, kafin a hankali ta shiga haska min hoton fuskar Nazifi.

Na sani babu kalma mafi ɗaci da ciwo gami da firgici a rayuwar kowacce ɗiya mace irin kalmar ZAWARCI, to amma a yau nafi buƙata da kwaɗaituwar nayi zaman Zawarci fiye da zaman gidan miji. a yau na tsani kalmar miji, bana son auren, na kuma sha alwashin ni da aure har mutuwa, tabbas a yau ba sai gobe ko jibi ba sai in Nazifi ba ya raye amma sai ya sake ni, sai ya sakeni ko ta wanne hali. [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR16FT5* Farantin hannuna ya suɓuce ya sauka akan tiles ya bada sautin rikitacciyar ƙara, ƙarar da taja jaririyar da ke kwance razana ta farka daga baccin da take, nan kuwa ta tsanyara uban kuka wanda lokaci ɗaya gidan ya ɗauka da sautin kukanta, kan kace me wannan uwarta ta sakko daga sama, ta bangaje ni daga ƙofar ɗakin Iyam ta faɗa ciki tana ɗora hannu aka da faɗin ta shiga uku.

"Ni Jummai me ya faru da yarinyar nan take tsala uban kuka haka?".

Cikin kuka tana dudduba jikin yarinyar take cewa,"ban san me tayi mata ba Iyam, shikenan ta ƙara kashe min yarinya, na rantse da Allah a wannan karan ba zan yarda ba".

Ai kan ƙiftawar ido sai tsintar Iyam nayi a gabana, tasa hannu ta ɗauke fuskata da mari tana zazzaga ruwan bala'i. "Wanne irin rashin imani ne danƙare a zuciyarki?, Mayya ɗiyar mayu kin dawo ki kashe kowa kenan, ke ninfa ko da haihuwa kika yi ba ƙaunarki zan yi ba, kuma ko rubuce yake sai na saka Shalele ya rabu da take".

Kamar kar in tanka sai kuma na sauƙaƙa zuciyata, ko ba komai bayani na da daɗi duk da ba amfani zai yi ba, kuma ni rigima da tashin hankali ne ban so, Idona akan uwar da ƴarta na ce,"wallahi tallahi Iyam babu abin da na mata, kawai fa na ajiye miki abinciki ne na zo fita tsautsayi farantin ya suɓuce a hannuna, to ƙarar ita ta firgitata".

Rufe bakina ba wuya Iyam ta ɗau waya ta kira uban yarinyar, da kwakwazo take faɗa masa ai na zo na ƙarasa kashe masa yarinya yay gaggawar zuwa wannan karan kotun ƙoli ce zata raba mu. gabana ya faɗi jin ƙaryayyakin da take gilla masa, ga jaririyar kamar haɗin baki sai ƙara tsanyara kuka take yi kace ɗaukarta nayi na buga da ƙasa, ba'a ɗebi wasu mintuna masu yawa ba sai ga shi ya dawo, lokacin ina tsaye a parlo na kasa zama saboda fargabar abin da zai faru.

Ganinsa a furgice ba ƙaramin razana ni yay ba, kallona ya tsaya yi a fusace sai ga Uwar ta sakko tana jijjiga ƴar itama sai kuka take yi, ya tafi da sauri ya karɓi yarinyar yana duddubata, ita kuma uwar faɗa masa take yi wai asibiti zata kaita saboda kunnenta ya toshe, kuma bata san me aka tusa mata a baki ba dai maƙogoronta ya cushe ko nono ta kasa sha.

Ni dai tsabagen mamakin sharrin daskarewa nayi a tsaye, to wai uban me ma ya dawo da ni gidan?, aikuwa ban yi aune ba naji saukar duka a jikina ta ko'ina, Nazifi ne ya shiga ɗaki ya zaro belt ya ke dukana kamar an aiko shi, garin in ƙwaci kaina in guje masa goshina ya bugu ajikin ƙarfen matakalar bene, tsananin azaba yasa na kurma uban ihu ina kiran sunan Allah. jini ya fara malala, ya koma saka ƙafa yana tattakeni yana faɗin sai ya kashe ni akan lahanta masa yarinya da nayi. ba Nazifi ya ƙyaleni ba sai da ya haɗa min jini da majina, fuskata duk ta kumbura idona ɗaya har bana ganin komai da shi.

"Wannan dukan ba komai na yi miki ba, ki jira yi dawowata, ba aai burinki raba ni da farin ciki ba, to Sa'ida daga ranar yau na dinƙa dukanki kenan a cikin gidan nan har mutuwarki, sakin ki ba zan yi ba, ba zan taɓa sakin ki ba, yanda kika ƙuntata min kika kashe min yarinya wallahi nima sai na kashe ki da irin salon wuyar da zan dinga gana miki a cikin gidan nan daga ranar yau, za ki ƙwammaci ba ki taɓa sanina ba a rayuwarki".

"Wayyooooo". Na kurma wata gigitacciyar ƙara ina saurin miƙewa daga kan katifar da na ke kwance. Ƙirjina bugawa yake yana dukan uku uku, zufa kuwa tuni ta wanke min jiki, jiki na rawa nayi ƙofa ina girgiza kaina. Sai ga Ummani da saurinta tana tambayata,"Ke lafiyarki".

Numfashi kawai na ke saukewa kamar wadda ta sheƙa mugun gudu, na faɗa jikinta ina faɗin,"Ba zan koma ba Ummani, don Allah ku ƙyale ni ba zan koma ba, wallahi na koma kashe ni za su yi".

Bayana take shafawa tana faɗin,"Ke me kike faɗi ne haka? Ko mafarki kika yi ne?".

Shiru nayi ina haɗiye yawu a busashshen maƙogorona, a hankali na ke sauke ajiyar zuciya, na janye a jikinta sannan na bi ɗakina da kallo, kafin na ɗaga labule ina kallon tsakar gidanmu. Sai kuma na fara tunanin ashe fa daga kotu gida muka yo ba gidan Nazifi na koma ba, na hasko lokacin da muka fito daga cikin kotun Kaka yake maganar to ya za'ai da ni, Abbaa yay saurin cewa da shi ai gida zamu wuce da ita.

Kuma muna dawowa gidan Ummani ta ɗora min ruwan zafi nayi wanka, ta bani abinci da kanta na ci na ƙoshi, ta mulke min jikina da maganin ciwon jiki, Abbaa ya fita chemist ya siyo maganin ciwon jiki ya ɓallo ya bani na sha, da kansa yace na shiga ɗaki na kwanta nayi bacci sosai, a lokacin kallonsu kawai na ke tayi a raina ina ayyana ko me ke zuciyoyinsu? Shin abin da ke raina shi yake ransu na game da zaman gidan Nazifi? Ko kuwa akasin hakan ne?

Sai da Ummani ta zungureni ta kama min faɗan bata son ina nisan tunani irin haka, kafin nan na miƙe na shigo ɗaki na kwanta, ina kwanciyar sai bacci, baccin da ya haddasa min mummunan mafarkin ina maimaita rayuwa a cikin gidan Nazifi. Numfashi na ja na sauke na ce da Ummani,"Mafarki nayi ne".

"To mafarki da zaka yi adu'a sai ka ƙwala ihu haka, kin ji yanda ƙararki ta bani tsoro kuwa. Kai haba Sa'ida ban san ki da haka ba, To me kika gani a mafarkin?".

Ido na ɗaga ina kallonta sai nayi ƙasa da kaina ban ce komai ba. "Ko ganinki kika yi a can bursun ɗin? To ya kamata ki cire tunanin hakan a ranki, Allah ba zai kuma kawo miki ƙaddarar hakan ba, ki yi ƙoƙarin mantawa ma gaba ɗaya tun da dai har Allah ya fidda ke, Ko kuwa me kika gani dama?".

Na girgiza kai ban ce komai ba. "A'a fa baki za ki buɗe ki min bayani".

"Ummani a gidan Nazifi na ganni, wai na koma can". "A'a to kuma shi ne sai aka yi me? Mene da can ɗin?".

Ba shiri na ware idanuna akanta ina cewa,"Ummani sai na soma komawa to?".

"Banda ta cewa sai abin da Kakanki da Abbaanku suka yanke. Amma dai ki zama cikin shiri kin san duk dare suna iya cewa ki tafi. Mafarki kuma daga yau kar ki ƙara ihu irin haka adu'oi ne iri daban daban akanki kin san su, irin haka ba sai ki janyowa kanki matsala ba idan ma wani sharrin ake nufarki da shi ya sameki".

Tana gama faɗin hakan ta fita ta barni. Ai a wurin na silale na zauna ina hawaye, wai komin dare zan koma gidan Nazifi? Ba ni na miƙe ba sai da aka yi kiran magriba tukunna naji muryan Ummani na faɗin,"Ki fito kiyi alwala ga ruwan ɗumi nan na zuba miki kar ya huce".

Tashi nayi cikin mutuwar jiki na fita, ina alwala ina lissafi, matsawar aka ce na koma gidan Nazifi to wallahi sai dai ko na tsaya a titi mota ta bige ni, ko kuma nayi tafiyata ƙauye, ai ni da Nazifi kuma har abada, mun gama zama da shi haka kuma na gama ganinsa, ko a lahira bana fatan ƙara ganin ko da inuwarsa, a yanzu haka na san ba zai taɓa waiwayata da sunan cewa na koma gidansa ba, to nima haka ba zai taɓa jin motsina ba, idan naga take taken su Abbaa na in koma ne to zan nemi wani wajan, shi kuma duk sanda ya gaji ya aiko min takarda ta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull