Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 13
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 13: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 13. Muna zaune ne tsakar gida muna cin abinci Abbaa ya dawo, muka yi…
4,480 words
Muna zaune ne tsakar gida muna cin abinci Abbaa ya dawo, muka yi masa sannu da zuwa ya zauna. Walida ta taho da gudunta ta faɗa jikinsa tana faɗin,"Abbaa sannu da dawowa, an dawo lafiya?".
"Na dawo lafiya lau ƴar albarka, me kika ci haka duk kika ɓata bakin ki?".
Kunnensa ta kama ta raɗa masa magana, Sai kuma ta ɗora yatsa a leɓenta tana cewa,"Amma fa kar kayi magana ta ji".
Dariya nayi Abbaa ma yay dariya. Ummani ta fito daga kitchen tana cewa,"Babanki zai shigo gidan ne ai biyana kayana zai yi. Yarinyar nema kike ki ɓalla min jari ta ƙarfi da yaji".
"To ai Abbaa yace shi ya ba ki jarin". Ta faɗa tana ƙara maƙalewa jikin Abbaa. Shi kuma yana tayata Ummani dai na mita akan shanye mata alawar yaran da take siyarwa, ta sauya wajen ajiya yafi sau nawa amma sai Walida ta bi ta ɗauko. Bayan gama cin abincin Abbaa ya dube ni yace,"Ke ya jikin na ki?".
Fitar amon muryarsa kamar na me fushi da ni hakan yasa na ɗaga ido na ɗan dube shi kafin na ce,"Da sauƙi Abbaa".
"Babu wani waje da kike jin ciwo?".
"Ehh Abbaa". Na faɗa kawai amma ba wai don hakan ba ne, a zahiri cikin ƙashina ciwo na ke ji sosai.
Muna nan dai zaune ita jiran naji Abbaa yay min maganar Nazifi ko maganar tafiya amma naji shiru bai yi ba. sai na ɗan fara jin tsoro don ban san ko yana so ya gwada hankalin yakamata na ba ne. Ummani ma da muke tare muna magana jefi jefi saboda shirin da take ji a radiyo itama ban ji tayi min wani zance ba. Da Kaka ya kira ni kuwa ba ƙaramin kaɗawa ƴaƴan hanjina suka yi ba, na yi hanzarin miƙewa ƙafafu a sanyaye nayi ɗakinsa, ya gama cin abinci lokacin na raɓe daga can gefe ina ce masa gani.
"Ya jikin ki ɗin". Ya tambaya ba tare da ya dubi in da na ke ba. "Da sauƙi". Na faɗa a hankali.
"Allah ya sauƙe, an siyo miki magungunan?". "Ehh Abaa ya kawo min tun da rana". "To shikenan tashi kije. Ko akwai wata matsala?". "A'a babu Kaka". "To Allah yay albarka". "Amin Kaka sai da safe, Allah ya ƙara lafiya". Na faɗa ina tashi na fita.
Da Abbaa ya dawo ya shigo ɗakin Ummani, ina kwance kan gadonta na miƙe ina masa sannu da dawowa, ya amsa yana cewa,"Ungo maganin sauro, ko an samu net ɗin?".
"Ehh an samu amma ya ɓuɓɓule Anty Khairi tace zata aiko a kawo wani to ban sani ba ko sai zuwa anjima idan Yaya Imam zai shigo".
"Imam ai ba zai zo ba ƙarfe tara yanzu, saka maganin dai ɗayan ai zai isa har gari ya waye ko?".
"Ehh Abba, an gode".
Na karɓa ina miƙewa na fita na basu wuri duk da Ummanin sallah take. Ɗakina nayi na kaɗo sauro waje, na manta ma ɗazu da suka kawo wuta na bawa Hindatu wayata ta saka min caji, ko da yake ban gama dawowa hayyacina ba balle hankalin ya kai ga wata waya, sai yanzu da daren yay kuma na ke tunanin haske ga basa kawo wuta cikin dare. Ummani ce ta miƙo min ashana da ƴar ƙaramar toci, muka yi sallamar sai da safe kafin nan na rufe ƙofa na kwanta.
Washe gari da safe duk yanda na so na taya Ummani aiki ta hana ni, sai ce tayi tun da naci abinci na dai yi wanka na kwanta ba cikakkar lafiya garen ba. Sai bayan ta gama aikinta tas sannan ta zo ta zauna, ina ta jera mata sannu ina cewa ban ji daɗi da bata barni nayi aikin ba.
Abbayo yana zaune a ɗakin yake maimaitawa Ummani irin wulaƙancin da suke sha idan suka je ganina a bursun, iya ƴan kwanaki bakwan da nayi a ciki wulaƙancin da suka sha yafi miliyan, yace sau tari sai sun taho sai yaga Abbaa yana share ƙwalla. Ni dai duk abinda yake faɗa ina jinsu, wani na yi yaƙe wani kuma na buɗe haƙora kamar mai yin dariya amma a zahiri ban san ina yi ba, kawai dai na san ko da yafiyata ce kawai zata ragewa Nazifi ya shiga aljanna bana jin zan yafe masa, a silarsa naga hawayen mahaifina, a silarsa naga hawayen mahaifiyata, a silarsa ya hana kowa nawa kwanciyat hankali. Kaɗan kaɗan na ke jin ciwo haka, sai na ɗora hannu a kan ƙirjina saboda yadda naji kamar zuciyata zata faɗo ƙasa.
Ummani ta lura da ni tayi saurin tasowa tana cewa da Abbayo,"Buɗe sif ɗin can ka miƙo magungunta, da yake ba sanin ciwon kanta tayi ba bata sha ba ni kuma ina ta zuci zucin nayi mata magana".
"Ta ma ci abinci ne?". "Eii taci, ai sai da Abbaanku ya sata gaba ta sha shayin da aka kawo daga gidan Yashaik tukunna ya fita, ka santa da gardamar cin abinci".
Sai bayan ya miƙo mata maganin tukunna ta dubi fuskar Sa'ida taga idanunta a rufe. "Au bacci kika yi saboda kar ki sha maganin, to tashi".
Kaka da ke isowa ƙofar ɗakin ya ɗaga labule, yake tambayar Ummani jikin Sa'idan yaga bata leƙa wajensa ba, tace,"Da sauƙi jikin nata yanzu ne ma naga tana ɗan dafe ƙirjin, maganin zata sha kuma sai bacci ya ɗauketa".
"Barta tayi baccin ko ya ya ne zata ji sauƙi a jikinta tunda ta jima bata samu yin ba, idan ta tashi sai ta sha amma ta bar wasa da shansa akan lokaci ai taji bayanin likitan ko".
"Eiii ai ko da muka dawo ma sai da na ƙara gaya mata". "To Allah ya sawwaƙe, Kai zo ka saka min kujera a ƙofar gida".
Har dai na kwana biyar a gida babu wanda yay min zancen tafiya, ni yanda ma suke nuna min kamar ko na dawo gidan ne, zancen ma bana jin suna yi ko kaɗan, sau tari idan naji kiran Abbaa ko Kaka sai na tsammaci zancen zasu yi min sai kuma naji lafiyata ce dai za'a tambaye ni sai kuma ace ban da wata matsala? Aikin gida kuwa ƙememe Ummani bata barina nayi sai tace ina buƙatar na huta, ai kuwa ina hutawar don bacci na ke sha abuna a hakan ma don ban samu tabbacin yanda na ke so ba.
Yau ina zaune ɗaki mun gama waya da Safiyya, wacca itama ke tambaya ta ko su Abbaa sun min maganar komawa na ke bata labarin komai, mun jima muna hira kafin muyi sallama wanda na ke mata godiya akan taimakonta gare ni, har ta haɗa ni da Baba ma a waya. Bayan gama wayarmu na ɗakko reza ina yanke farce ina bin suratul Yusuf da na kunna. Muftahu ne ɗan wajen Baba Tijjani ya leƙo ɗakin nawa yana ce min naje Abbaanmu na kirana.
Da hanzari na aje rezar na saka hijabina. suna zaune shi da Ummani na shiga, zama nayi daga gefe kaina a ƙasa, gabana sai faɗuwa yake saboda sanin cewa kiran muhimmi ne daga yanayin yanda na samesu. sai dai tsorona da fargabata bai wuce ayi min zancen Nazifi ba da komawa gidansa.
Bayan Abbaa ya numfasa ne yace da ni,"Kun yi waya da mijinki?".
"A'a Abba". "Bai neme ki ba tun ranar?". Na ɗaga kai,"Ehh Abbaa".
Sai ya kalli Ummani yace da ita,"Akwai wanda ya zo cikin yaran nan?".
"Anya kuwa, na dai ji kamar maganar Yashaik da safe a ɗakin Al'amin".
Sai Abbaa ya sake dubana yace,"Me yasa ba ki taɓa karanta min irin zaman da ku ke yi ke da mijinki ba?".
Nayi shiru na kasa cewa komai har sai da ya ƙara min magana kana na ce,"Abbaa ban san ta in da zan fara bayani ba ne, sai kawai na bar komai a matsayin me wucewa. Ban taɓa tsammani zata kaimu ga lamarin da ya faru ba".
Na faɗa ina jin tahowar kukan da na kwan biyu ban yi ba. "To za ki koma gidan nasa?". Da sauri na kaɗa kai ina cewa,"A'a Abba ba na so na koma".
"To ai koma kin ce za ki koma ba komawar za ki ba, don ranar da mahaifiyarki ta faɗa min dukka halin da kike ciki na yanke hukuncin cewar zamanki da shi ya ƙare. ni duk ban san haka al'amarin yake ba, tunanina irin ƴan matsaltsalu ne dai na gidan aure da aka saba fuskanta shiyasa ko da yaushe na ke cewa kiyi haƙuri, ashe abun yay ƙamarin da muka shiga hakkinki tunda bamu taɓa ba ki damar yi mana bayani ba, kuma da sai ki rubuto min ko a takarda ne tun inda baki ne katse ki na ke yi, amma kiyi haƙuri".
Wayarsa ya ɗauko a aljihu, yana ƙoƙarin kiran Yashaik sai ga shi ya shigo, ya gaida su nima na gaida shi tukunna ya nemi waje ya zauna. Zamansa ba wuya Yaya Imam ma ya shigo, shima bacin sun gaisa ya zauna yana tambayata ya sauƙin jikina na ce masa naji sauƙi.
Abbaa ya dubi Yashaik ya ce,"Ina ka nufa yanzu?". "Ehh to daga nan dai zan je makarantar su Yasmin zan biya kuɗin makarantarta".
"Kai fa Imam?". "Ba ni da wajen zuwa Abbaa". Ya faɗa wanda na san ba hakan ba ne, haka yake a ko da yaushe idan iyayensa suka tambaye shi me zai yi ko ina zai je sai yace babu saboda biyan tasu buƙatar.
"Yauwa to kasa kunne da kyau ka jini. Ka kira Nazifi kace masa ya aiko da takardar sakin Sa'ida, ya aiko da takardar sakin Sa'ida a yau ba sai wani lokaci ba, kar ya aiko min da takarda me ɗauke da saki ɗaya ko biyu, saki uku na ke so ya aiko min da shi, ka faɗa masa ya gama zama da ita har abada".
Yaya Imam ya ɗauki wayarsa yana cewa,"Yanzu kuwa Abbaa, ai don kar nayi gaban kaina ne dama amma tun ranar da kotu ta sallame mu na so ya rubuta takarda a lokacin ya bayar, to da naji kayi shiru yasa na dakata don ban san me ka shirya ba".
Ni na karanto masa lambar wayar, ashe shi tuni ma ya goge lambobinsa, kiran farko ya katse na biyu da na uku ma haka duk ba'a ɗaga ba, sai da ya ƙara na biyar ɗin kana aka ɗaga, muryarsa daga can a daƙile yay sallama, Yaya Imam ya amsa masa da cewa,"Saboda amsata wajibi ne ban da haka baka isa na amsa maka ba, nama yi mamaki da har ka san ya kamatan sallama, ai ce na ke ka manta da addinin gaba ɗaya. Anyway ka kore watsatstsen tunanin da ke ranka akan kirana, ba kiran da aka saba yi da ba ne, lafiya shiru har wannan lokacin baka aiko da takardar sakin Sa'ida ba?".
Wani makirin murmushi yay irin na marasa mutuncin nan yace,"Mun yi da ita zan saketa ne? Idan ma tunanin hakan ne akanta to ta cire shi domin ni ba zan saketa ba, kuma ka faɗa mata ko ta gama zaman gidan ko ba ta gama ba ta tattaro ta dawo yau, dama ba bisa izinina ta tafi ba, kuma zata dawo ta same ni".
"Kaga dakata, magana na ke maka ta dole zaka saketa, ka rubuta takarda a yau ka aiko mana da ita".
"Imam ka ke ko? Ba zan taɓa yin abinda kuke so ba, Sa'ida sai dai ta ci gaba da rayuwa a gidan naku haka amma ba zan saketa ba, kuma ni da ku mu zuba mu gani".
Ƙit ya kashe wayarsa kuwa. Abbaa ya fara magana cikin kakkausar murya, kana jin yadda amon ta yake fita hakan zai tabbatar maka da yana cikin tsananin ɓacin rai,"Babu wani mahaluƙi Wanda ya taɓa tozarta mu kamar wannan yaron! Babu Wanda ya taɓa wulaƙanta zuri'a ta irin wannan yaron, me yake jin kansa? Yaushe ya taka matsayin da zai ci mutuncinmu haka? saboda yana taƙamar yana da kuɗi...".
"Taƙamar dai yana da tsiya da iskanci, kuɗinsa ɗin banza da wofi, mu ba irin talakawan da zamu bari mu wulaƙanta ba ne, ba ƴan tsiya ba ne mu amma tabbas zan nuna masa ƙaryar iskanci yake, zan nuna masa mun shallake gaban tunaninsa". Cewar Yaya Imam.
Sautin kukana ne kawai yake fita a hankali, kaina bisa cinyar Ummani, sai faman goge min hawaye take yi, jikina ya yi zafi rau kamar wuta. Idanu na kawai na rufe gam saboda da zarar na buɗe su sai su riƙa haskomin abubuwa barkatai. Muryar Ya Imam na tsinta a cikin tunanin da nake yi yana faɗin,"Abba kayi shiru ka daina ɗaga muryarka akan wanda bai gaji arziƙi ba, ka bar lamarin komai a hannunmu, duk yanda zai yi sai ya bata takardar saki ko shi ya fi kowa taurin kai a duniya, nasa kaɗan ne zan nuna masa ƙaramin mara mutunci yake, ni ubansa ne a taurin kai, zan gwada masa wallahil azim Sa’ida tana da Yayye masu tsaya mata kuma ƴar gata ce, na baya ma da yay rashin sani ne shiyasa har ruwa ta sha".
Yashaik ya ce,"Ki bar kuka ke kuma, ai kuka ya ƙare maki, kar ki ji komi ki kwantar da hankalinki zama da Nazifi ne kin gama shi... Ko ya ba da takarda ko kuma daga nan har kotun ƙoli wallahi".
Yaya Imam yace,"Kotu zaka kai shi? Ka shirya ɓatawa kanka lokaci kenan, ai yanda Abbaa ya buƙaci takarda a yau tabbas a yau ba sai an kwana ba zai rubutata ko da yana rubutu jini na zuba a hannunsa, zan je har inda yake karɓowa, idan yay min garda wallahi zan raunata shi ne kuma na tilasta masa ɗaukan takarda da biro ya rubuta abin da muke so".
Yana faɗin hakan ya miƙe yana saka wayarsa cikin aljihu, kafin ya nufa ƙofa Ummani ta dakatar da shi tana cewa,"Imam dawo, dawo kar ka tafi a zuciye ina tsoron zuciyarka Imam, gwara ayi abun nan cikin maslaha idan bai bayar ba sai muje gaban alƙali, amma kaga yana ji da kuɗinsa kar abu ya kwaɓe mana".
"Je ka Imam, karɓo takarda sakin ƙanwarka a hannun Nazifi shi zai tabbatar min da kai jinina ne na gaske". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR17FT5* "Kai kuma kaje ka gama da makarantar Yasmin ɗin". Abbaa yace da Yashaik wanda ke tsaye shima jikinsa na tsuma saboda fushi da ɓacin rai.
Ummani tace,"Abbaa na faɗa maka idan yaran nan suna cikin yanayin ɓacin rai ka daina saka su aiwatar da ɗaukan mataki, kaga ba'a san me zai je ya dawo ba. Yanzu dai da ka dakatar da Imam ɗin ka san halinsa kar ya zo yay masa dukan illah mu kwana a ciki".
"To ke kina zaton ko dukan mutuwa Imam zai yi masa zan ji daɗi ne? Ai a duniyar nan babu wani hukunci da za'ai wa Nazifi na ji sanyi a raina. Sakar min ƴa shi ne kawai zai ɗan ragen raɗaɗi, amma batun hukunci wannan sai mun haɗu a kotun Allah, ban da lokacin ɓatawa na yin shari'a da shi a duniyar nan".
Sai ya dube ni yace,"Ke me kikewa kukan to".
Cikin sabon kukan da ke zuwar min na ce,"Abbaa ba na son komawa gidansa, Abbaa Nazifi ya zalunce ni da yawa, tun da na aure shi ban huta ba Abbaa, ina jin tsoro kar yaƙi bani takardata".
Yanda amon muryan Abbaa ya fita ni kaina sai da na tsorata musamman da naji furucin da bai taɓa yunƙurin yi ba. "Malama daina kuka ki share hawayenki, ki kuma kwantar da hankalinki, saki ne kamar yayi shi ya gama, ko da zan yanke hannun Nazifi ne sai na yanke ya rubutu sakin ki...".
"Subhanallah". Ummani tayi saurin katse shi. "Abbaansu don Allah ka sanyayawa zuciyarka ruwan sanyi, ai duk ba sai ta kai ga an fusata irin haka ba, shi kansa ai ya gaji da ita ko ba'a tursasa shi ba dolensa ne ma zai bata takardarta, amma ka daina batu irin haka".
Kansa kawai ya jijjiga yana ƙurawa waje ɗaya ido ba tare da yace da ita komai ba. Ummani ta zame kaina a bisa cinyarta ta miƙe tana faɗin,"Bara naje na ɗora girki, Me za'a dafa?".
"Kar ki girka da ni sai naga yanda hali ya yiwu". "To Allah ya kyauta". Fita tayi, ni kuma ina nan zaune hankalina duk yaƙi kwanciya, tsorona Allah tsorona Nazifi yaƙi sakina, Abbaa yace na tashi na tafi kuma in ban daina kukan ba sai ya saɓa min ya mayar da ni can gidan da kansa tunda ya lura kukan na ke so, to gwara na koma inda zan ke yi kullum da hujja.
Ko da Ummani ta sauke abincin rana kasa ci nayi, babu yanda bata yi da ni ba na ce mata na ƙoshi, Abbaa kuwa yanda ta aje kwanonta bai kalli inda yake ba, sallar azhar kawai naga ya fita, tunda ya dawo kuma ya zauna ban da jijjiga kai da girgiza ƙafa ba abin da yake yi. Sun yi waya da Yaya Imam yafi sau ƙirgen yatsu, shi kuma yana can office ɗin Nazifin wai ba ya nan amma ya tsaya jiransa ya dawo, Abbaa dai yace to karka dawo min gida sai da takardar sakin ƙanwarka. Ana haka Yashaik ya dawo shima ya ce ai yaje har can gidansa bai same shi ba, Abbaa bai ce komai ba sai Kaka ne ma yace,"Lallai yaron nan ya wuce tunaninmu a rashin mutunci, ƙila sai mun ɗauka hukuma mun masa shigar dare".
Ni dai ina kallon fuskar Abbaa yay wani irin murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa. Ganin yanda na takura kaina Ummani ta ce,"Ke zo ki kitse min kaina".
Tare muka fita da ita daga ɗakin Abbaan, muna kitson tana faɗa min na kwantar da hankali na saki raina nayi walwalata, na riga na san waye mahaifina tunda har ya furta yau to sai in ba ya numfashi ne abin da ya faɗa ba zai aiwatu ba, kuma na san su waye Yayyena su kan yi duk iya ƙoƙarinsu akaina wajen ganin sun nema min ƴan ci sun kuma faranta min.
Ta shiga bani labarin ai lokacin da na kirata na shaida masu abin da ke faruwa ta zayyanewa Abbaa komai, shi ne ya fusata yace yana raye bai ga wanda zai wulaƙanta masa ƴa ba sai Nazifi ya sake ni kuma sai ya kai ƙararsa kotu an bi min hakkina, kuma in sha Allah Nazifi na raye zai ga ƴaƴana da ɗaukakata.
Gama kitsonmu kenan yaro yay sallama yace ana kiran Sa'ida a waje, da mamaki ni da Ummani muka maimaida abin da ya faɗa, sai Ummani tace da shi,"Kaje ka ce waye".
Yaron ya koma sai ga shi ya dawo yana faɗin wai mijinta ne ya zo, ta shiryo za su tafi. Kusan tare da Ummani muka girgiza kai a raina ina faɗin lallai Nazifi ya raina ni ya raina gidanmu. Ummani bata ce komai ba ni kuwa na miƙe na fita, ɗakina na shiga na yafo mayafina na nufi hanyar fita sai Abbaa ya fito yana cewa da ni,"Ina za ki?".
Kaina ƙasa Ummani ta fito tana ce masa,"Wai Nazifi ne ya zo ya ce taje su tafi".
Abbaa yace,"Madallah da ɗan marasa kunya, to kije ki same shi ki karanta masa duk wasu shiƙa shiƙan cin mutunci da ke cikin kanki sannan ki juyo ki dawo, ki tabbatar kin gusar da ɓacin ran saman fuskarki da maganganu masu zafi da tsayawa a rai".
Ina fita na same shi daga cikin mota ya hakimce, yana ganina yay biris yana jiran na ƙarasa, minti ɗaya, biyu kawai sai na juya zan koma cikin gida sai ji nayi yana,"Malama dakata". Amon muryarsa ya fito tamau.
Na waigo lokacin da yake isowa inda na ke. Yana faman haɗe rai yace,"Ɗan aiken bai faɗa miki saƙon cewa ki fito tafiya zamu yi ba".
"Shi ne ai na fito naga wanne mara zuciyar ne, ashe kai ne Nazifi, me ya kawo ka ƙofar gidanmu?".
Bai expecting furucin hakan daga gareni ba don haka ya tsaya kallona kafin ya ce,"Saboda ba ki da hankali kin baro gidan aurenki kin zo kin nemi wuri kin zauna, tukunna ma bisa izinin wa kika taho nan ɗin?".
"Bisa izinin waɗanda suka isa da ni, ka san ai ni ban gama watsewa ba ina jin maganar mahaifina. rashin hankali kuma ai yana wajen wanda babu zuciya a ƙirjinsa. Kai Nazifi ban da ma baka da kunya har ka iya tako ƙafa ka zo ƙofar gidanmu kace na koma gidanka, gidan da babu arziƙi babu mutanen arziƙi a cikinsa, gidan butulu rainon butulu, To bari kaji na faɗa maka sai dai wata Sa'idan a gidanka amma ba dai ni ba, babu abin da zai maida ni gidan mutumin da bai tsotsi arziƙi ba sai tsiya, mun rabu rabuwa ta har gaban abada, sai ka jira haɗuwarmu a kotun Allah. Yanzu miƙo min takardata da ka kawo min sannan ka juya ka bar mana ƙofar gida bana son sake ganinka idan ba haka ba sai nasa yara sun maka cin kashin da kare ba zai shinshina ba".
Wani kallo yake min da ke nuna tsantsar ɓacin ransa da takaici. "Ni kike faɗawa magana haka?".
"An faɗa maka, an faɗa maka shayinka na ke yi, ai ko a ba ya darajar biyayya wa iyayena yasa na rangwanta maka, ban da haka abin da zan maka dabba aka nuna maka aka ce ka wulaƙantata Nazifi ba zaka soma ba. Kuma gidanka ne na baro shi kenan ko ba tsayawar ahalina, sakina ya zamar maka dole balle kuma sun tsaya min, zaka bani takardata ko kuwa zaka nuna min kare ya cinye zuciyarka?".
Duk maganar da na ke yi ina yi ne cikin rawar murya da taruwar hawaye a idona wanda ban san na menene ba, sai dai sam na hana bayyana duk wata faka da zata nuna rauni a tare da ni.
Yana jijjiga kai kaman ƙadangare yace,"Ko za ki mutu ba zan sake ki ba Sa'ida".
"Haka nima ko zaka hauka ce ka bi bola Nazifi sai ka sake ni, ai ba ma sai na rantse ba don ayau zaka san an isa da kai a gidan da ka raina mutanan cikinsa. Ban da ma ƙaddara da jarabawa ina ni ina zama matar illiterate irinka, talaka irinka da ko ubangijinsa da yay masa ni'ima bai iya gode masa ba balle ya godewa wacca da kuɗin gumin mahaifinta aka samu ceto rayuwar uwarsa, a lokacin da ƴaƴan da ta haifa su kasa yi mata komai...Ai kin banza ƙwaƙwalwa babu komai sai tarin jahilci, yo jahilci mana tun da an karanta ba'a anfani da shi, matacce mai matacciyar zuciya, babu komai a tare da kai sai tsiya, wallahi na godewa ubangijina da bai sa na haɗa zuri'a da ƙaramin mutum irinka ba, kuma dama ubangiji ba azzalumin bawansa ba ne shiyasa ya hana ni haihuwa tare da mutum mara daraja irinka, don abin jaje ne ga duk ɗan da zai nuna Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin uba, haka abun kunya ne ga macen da zata nuna Nazifi a matsayin miji, ni kuwa yanzu tsakanina da kai tamkar nisan sama da ƙasa ne...".
A zafafe ya kawo hannu zai wanke ni da mari yay rashin sa'a tawa zuciyar tafi tasa kusa, aikuwa bai farga ba na damƙe hannunsa na ɗauke shi da marin da sai da ya kifa ƙasa.
Na ƙyasata yatsu ina nu na shi na ce,"Somin taɓi na maka, idan ka ƙara kuskuren ɗaga hannunka a gabana wallahi sai na maka wanda yafi wannan muni...kuma ka bani takardata na ce kafin na ƙarasa yaga maka rigar mutunci".
Yana dafe da kuncinsa Yashaik ya iso wajen. ya duben yace,"Me ya fito da ke wajensa?".
"Zan faɗa masa ne ya kwashe ƙazaman ƙafafunsa masu dattin zunubi ya bar mana ƙofar gida, wadda ya ke tunanin zata koma masa ba ƙaramar mutum ba ce ita kamar shi ƙasƙantacce kuma wulaƙantacce mara ilimi".
"Shiga cikin gida". Yashaik yace da ni. Na watsawa Nazifi wata muguwar harara naja dogon tsaki da cewar,"Ka jira lokacin da zaka yi ƙuncin da yafi na saman fuskarka a yanzu, ka kuma jirayi lokacin da zaka burkice da nemana akan na yafe maka, itama ta gida ka faɗa mata hakkina ba zai barta ba gwara ta zo tunda wuri ta duƙa ta nemi yafiyata kafin duniya ta fara ƙwallo da kai da ita da magoya bayanku".
Na shiga cikin gida ina jin Yashaik na ce masa ya ba da takarda kawai ya tafi babu wanda ke son ganinsa takarda kawai su ke so, ba su da lokacin ɓatawa da shi. Murmushi Nazifi yay me kama da na yaƙe yana sosa gemu, yaywa Yashaik kallon wulaƙanci kana yace,"Kuna ta in saketa in saketa, ban ga fa wanda ya isa ya tilasta min ba, yin kaina na ke babu me saka ni yin abin da ban niyya ba, idan kuma kuna da karfin ƙwata sai ku ƙwata...kuma ka shiga ka faɗa mata ta fito mu tafi don ban gama wahalar da rayuwarta ba".
Yashaik ya girgiza kai yace,"To shikenan kar ka bayar, idan mu ka je gaban Alƙali ka maimaita hakan, zamu haɗu a kotu a karo na biyu".
"Hhhh to shikenan muje zuwa, in dai kuna da kuɗin yin shari'a ku buga da ni".
Ana haka Imam ya ƙaraso, da ƙyar ya iya tsayawa ya kashe machine ɗinsa saboda tafarfasar da zuciyarsa take yi musamman na ganin Nazifi a ƙofar gida, ƙofar gidan ma har yana kai yatsa ƙirjin Yashaik ya nuna shi. Ko maƙulli bai tsaya cirewa ba ya tafi da sassarfa yana zuwa ya damƙi hannun Nazifi da ke nuni da Yashaik, ya barƙala shi yana faɗin,"Wallahil azim ko Sa'ida ka nuna da yatsa a gaban idona sai na karya ƙasusuwan hannunka...Ka zo da abin da muka umarceka ko kuwa sai na sassaɓa maka kamanni tukunna ka shiga hankalinka ka bi umarninmu".
Maganar yake gaba ɗaya ma ya mance da ya barƙale hannun Nazifi, sai da Yashaik ya taɓa shi tukunna ya sakar masa yana dukan ƙirjinsa tare da tankaɗa shi baya. Hayaniyarsu ta fito da Abbaa wanda ya leƙo cikin dattakunsa yace,"Sa'id kaga ku shigo daga ciki saboda maƙota da jama'ar unguwa".
Imam na kallon Abbaa yace masa,"Mu shigo da shi ciki?".
Abbaa yace,"A'a ku barsa dolensa ma zai shigo da ƙafafunsa, ai da sauran tunani akansa da har ya gane ya zo da ƙafafunsa na marasa mutunci".
Abbaa da Yashaik suka shiga ciki, yayin da Imam yake ma Nazifi wani mugun kallo da cewar,"Ka ci sa'a da kaga yanda zan maka ɗaukan saman ka, kuma ka shigo mana gida a gadarance sai kaga yanda zan kwarfe ƙafafunka ka baje a ƙasa".