Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 14
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 14: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 14. Ya faɗa yana shige ciki ya barsa tsaye sanƙanƙan. Zuciyar Nazifi…
4,499 words
Ya faɗa yana shige ciki ya barsa tsaye sanƙanƙan. Zuciyar Nazifi na jin wani ƙullutun baƙin ciki, shi babu babban takaici ma a wurinsa sama da irin yanda suke masa magana da nuna isa. Yay murmushin leɓe ƙasan ransa yana maimaita furucin Abbaa _,"Zai shigo da ƙafafunsa"._ shikenan zai gani shi da su waye a sama, itama kuma Sa'idan zata ƙwammaci kiɗa da karatu akan maganganun da ta faɗa masa, ba dai zata same shi gida ba ne.
Juyawar da zai yi sai ganin Malam yay ya sauka a daidaita sahu, ido waje yake kallon mahaifin nasa da son sanin manufar zuwansa. Har Malam ya ƙaraso ƙofar gidan bai ɗauke ido akansa ba haka bai iya cewa komai ba, mamaki ya ƙamar da shi cike da tsoron abin da ya kawo mahaifin nasa. Sai da Malam ya shiga soron gidan kana ya ɗago murya da ce masa,"Ban kai ka ganni ka biyo bayana ba ne mara mutunci da bai gaji arziƙi ba, ni dai nayi danasanin haifarka".
Ya haɗiye yawu yana rissinar da kai tare da bawa Malam ɗin haƙuri. Ashe da dalilin Abbaa na cewa zai shigo da ƙafafunsa, amma kuwa Malam bai kyauta masa ba domin ya so ya nunawa Abbaa cewa bai isa ba yayi kaɗan. Ba don ya so ba ya taka ƙafafunsa cikin soron cike da baƙin ciki da takaici. Ina kaɗa miya a kitchen na jiyo sallamar Malam ɗin na taso da sauri na fito, ƙasa na duƙa ina masa sannu da zuwa, ya amsa gaisuwata yana saka min albarka tare da adu'a wadda naji daɗinta sosai har cikin raina.
Nayi masa iso ga ɗakin Kaka na ce,"Bismillah ka shiga". Sannan na wuce Nazifi wanda nayi tamkar ma ban taɓa sanin me zubin halittarsa ba, na tofa masa yawun bakina a ƙafafu ya san da cewar ƙyamatar ma ganinsa na ke. Kitchen na koma na ci gaba da aiki, bayan kusan minti goma sha Yaya Imam ya shigo ɗakin Ummani ya same mu da cewa,"Tashi ki je ana nemanki".
Na miƙe gabana na faɗuwa na saka hijabina na bi bayansa. Na shiga da sallama na nemi waje na zauna da girmamawa a gare su, Nazifi na tsakiya Malam sai zazzaga masa masifa yake yana zaginsa. "Dilla Malami tashi kaje ka ɗauko abun rubutu, kuma ka haura mintuna biyu za ka sha mamakina".
Yana ƙunci haka ya fita, Malam yana ta bani haƙurin abubuwan da suka faru, yana faɗin shima ba zai taɓa yarda da komawata gidan Nazifi ba, kuma ban kyauta masa ba da na kasa yi masa kallon mahaifi wanda ba zan iya kai masa kukana ba. Nazifi ya dawo da takarda da biro ya zauna gefe da ni, kamar an watsan wuta haka nayi saurin ja baya da shi don ko kusa ba na son ganinsa ma balle jinsa kusa da ni.
Abbaa yana dubansa yace,"Kaga darajar mahaifinka fa kaci har ka ɗauka mintuna masu tsayi haka a cikin gidana. Ban da haka niyyata kana shigowa su Imam su saka rubutun da baka so kuma su fitar da kai cikin ƙalilan ɗin mintuna".
Kansa ya ɗago ya kalli Abbaa yace,"Abbaa ba na son sakinta, zai fi kyau a sulhunta mu...".
Yaya Imam yace,"Ka san Allah ka bar ganin Malam a zaune anan idan ka kuma musu da abin da mahaifinmu yace zan jaka waje na farfashe bakinka, na lura yanda ka raina naka iyayen haka ka ke ganin zaka raina na kowa".
Yay maganar yana tasowa daga inda yake zaune yay tsaye akansa, ni dai ban kallesa ba ban kalli inda yake ba, amma ina da tabbacin yanda na tsorata da amon muryan Yaya Imam ɗin haka shima ya tsorata wanda shine dalilin fara rubutunsa akan takardar babu shiri.
Yana gama rubutawa ya kallo inda na ke ya kira sunana da muryar da tayi kama da masu neman taimako. Ƙin ɗagowa nayi tamkar ban ji kiran ba, sai da Malam yace,"Sa'ida karɓi".
Na ɗago ina bin takardar da yake miƙo min da kallo, kafin na kai hannu na karɓa. Kuma wai saboda bai da cikakkiyar kunya har yana faɗa min,"Ba da son raina na sake ki ba, ki sani zan iya maida ke a kowanne lokaci".
Ni dai idona na kan farar takardar da ke ɗauke da rubutun cewa _"Ni Nazifi Bala Mai Kalwa na saki Sa'ida Salman saki biyu"._
"Na sake ki saki biyu, da sauran igiyar aurena akanki".
Ya ƙara faɗa min da baki yana miƙewa zai fita Yashaik yace masa,"Butulu kawai wanda bai san mutunci ba mutunci bai raine shi ba balle halacci. Tun kana tsummanka baka da komai ka addabi rayuwar yarinya sai da ka aureta hankalinka ya kwanta, kuma kai ne yau ka wanko ƙazaman ƙafafunka a gaban idanun mutumin da ya dinga tallafar rayuwarka da jarin sana'a ka sakar masa ƴa, kai a ganin ka kaine da riba ko?, to bari kaji Sa'ida itace da riba domin tun farko daman taimaka maka tayi ta aureka ba don kun dace ba, kuma da sannu zaka girbi abin da ka shuka don Allah ba zai barka haka ba sai ya saka mata".
Fuskarsa ta nuna yaji zafin maganar, ya tsaya yana duban Yashaik yana sauke numfashi. Abbaa ya doka masa tsawa da cewa,"Dalla can fice ka bar min gida kafin nasa a fitar da kai".
"Ta zo ta kwashi kayanta da wuri".
Ina saurin buɗar baki nayi magana Kaka ya riga ni da cewa,"Kai ne matsiyaci kai kayanta suka dama, ba ta biɗar ko tsinke a wannan tsiyataccen gidan naka, ka adana su domin amfanin wataran...maza ɓace mana da gani".
Yana fita Malam ya shiga bawa su Abbaa haƙuri, Abbaa yana babu komai, shima yana cewa fatan wannan abu mara daɗi ba zai shafi zumuncinsu ba, Abbaa yace zumunci ai sai tsakanina da kai Malam Bala, amma babu matarka babu matata, haka babu ƴaƴanka babu ƴaƴana. Kuma ka jawa ɗanka kunne ko da wasa kar yay gigin sake bibiyar ƴata idan ba haka lallai ba zai ji daɗina ba.
Kaka yana kallona yace,"Tashi kije".
Na fita ƙafafuna a matuƙar sanyaye, da gudu na shiga ɗakin Ummani na faɗa jikinta, kawai sai na fashe da kuka sosai, kukan da na rasa na farin ciki ne ko kuma akasinsa. Ummani ta karɓi takardar hannuna ta karanta a hankali ta furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kafin ka shiga lallashina tana cewa,"Daina kuka, in sha Allah wannan rabuwar taku alkhairi ce gare ki mara misaltuwa, in sha Allahu ba za kiyi kukan zawarci ba sai dai ma ganin ranarsa tun da har gidan aurenki ya tauye miki abubuwa da dama".
Ni dai kuka kawai na ke yi, cikin idona babu wani abu da ke haska min face dukkanin rayuwar da na shafe tare da Nazifi tun daga ranar farkona na siyan rake a wajensa har zuwa wannan rana da ya miƙo min takardar sakina a gaban mahaifina. A hankali na furta,"Allah na roƙeka kasa ƙarshen jarabawar kenan". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR18FT5* Tun daga wannan rana da na karɓi sakina a hannun Nazifi na shiga wani sabon babin rayuwa. Ni kam sai dai nace Alhamdulillahi don bana wani fuskantar ƙalubale da zan ce gwara zaman uƙubar gidan aure akan zaman zawarcin da nake yi a gidanmu, duk da a baya naji tsoro sosai duba da yanda na ke jin mutane na kambaba tashin hankali da musibar da ke cikin zawarci.
Ko kusa ba na fuskantar kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, ba ya ga sabuwar soyayya da tsantsar kulawa ma da iyayena da Yayyuna ke ba ni, ko da yaushe cikin nuna damuwarsu gare ni suke na me na ke da buƙata, motsi kaɗan me na ke so, hatta mahaifiyata ba ta so ma na ke aikace aikace. Umma da yaranta ne ma suka so su saka ni gaba da habaici da yada magana wai na kaso aurena saboda ina so nayi yawon zawarci irin na ƴan iskan mata, wani sa'ilin kuma su ce rashin haihuwa yasa aka sako ni, ni dai bana taɓa daga kai na dube su haka ban taɓa nuna na san suna yi ba, Ummani ma bata taɓa bi ta kan Umman ba duk da irin maganar da take yada mata me zafi wai ai da ban kaso aurena na fito ba saboda yanzu dai babu wanda zai aure ni sai dai na ƙare a haka tunda bana haihuwa, kuma ga shi ma ban da karatun boko mazan yanzu kuwa wayayyiyar mace suke aure, saboda haka ya kamata ta saka ido akaina saboda kar na fara yawace yawacen banza don ranar nan ma taji wajen masu shayi ana faɗin daga mutuwar aurena ko gama idda ban yi ba na fara yawon iskanci.
Aikuwa ran Ummani ya ɓaci da maganarta, suka kama hayaniya har sai da Kaka ya fito ya tsawatar musu, Ummani tace to lallai fa yaywa Umma tsakani da ni babu ruwansu da zaman da na ke yi a gidan, su ɗauke ido akan ƴarta idan ba haka duk abin da tayi mutum shi ya siya da uwar kuɗinsa, a daren ranar kuwa Kaka ya tara dukka gidan Iyaye da Ƴaƴa ya jawa kowa kunne, yace duk wanda ya kuma ɗaga ido ma ya kalle ni ya furta kalaman bazawara sai ya bar gidan, Abbaa ma yace duk wanda bai ɗauke idonsa akan ƴarsa ba lallai zasu yi rigima ta ban mamaki, to tun sannan fa na samu salama a wajensu, babu ruwansu da ni nima babu ruwana da su, Umma ko magana ma bata min idan na gaida ita sai ta min banza, saboda haka kwata kwata ma na daina ko zuwa ɓangarenta, iyakata wajen Umman au Hindatu.
Hankalina ya kwanta bani da wata damuwa, daga na ci sai na kwanta sai hira da mahaifiyata, wanda hakan ke ƙara kawar min da duk wani tunani da zai iya fama ciwon da ke a zuciyata, hatta Safiyya da suka zo ita da Hassana Tijjani sai da suka min tsiyar wai har na fara kumatu, kuma wanne man bleaching na ke shafawa, wanda kuwa duk ya san batun mutuwar auren sai yace Allah ya saka min, da can bai san bana haihuwar ba sai yanzu da yay kuɗi shi ne zai juya min baya.
Abbaa kuwa watana ɗaya ya fara bani ƴan kuɗaɗe ina ajiyewa duk sanda ya fita ya dawo, yace da zarar na kammala iddah sai na koma makaranta na ci gaba da karatuna kafin Allah ya kawo mijin aure, ni kuwa a zuciyata babu wani lissafi na aure, ai tuni na gama faɗawa zuciyata na gama yin aure kuma, buri na bai wuce rayuwata ta inganta ba, na koma makaranta nayi karatu sosai na samu gogewa nima na zama cikakkiyar mace ƴar zamani mai ji da kanta, sannan na samu aikin yi me gwaɓi wanda zan tallafawa mahaifana da su kan su Yayyuna da sauran al'ummar musulmai.
Wata rana muna zaune Yaya Al'amin ya zo yana faɗawa Abbaa cewa akwai scholership na school of nursing jigawa, abokinsa ne suke bayarwa yay masa magana yace zai yi magana a gida idan an yarda sai ya karɓawa ƙanwarsa, Abbaa dai yay shiru bai ce komai ba ni kuwa ina ta murna, bayan kwana biyu da maganar hakan sai Abbaa ke cewa a'a ba ya so nayi nisa, in ace dai nan school of nursing ne ta kano kusa kusa sai ya bar ni na tafi, amma shi ba ya son in da zanje na zauna ba zai samu kwanciyar hankali ba.
Makaranta dai kowacce iri ce indai a kano ce to za'a sama min na je, wacca zan ke zuwa ina dawowa amma ba ta kwana da zan yi nesa da su ba. Ranar da na fita a iddah Yaya Imam ya zo da zancen cewa ya tambaya min wata makarantar islamiya anan farkon layinmu zan ke zuwa ina koyarwa kafin na koma makaranta, nayi murna sosai da sosai nayi ta masa godiya, a washegarin ranar kuwa na fara zuwa.
Da ɗan kuɗin albashin da suke biya muka ja jarin kunun aya ni da Ummani, Abbaa ne ma yaje har makarantar almajirai ya samo almajiri bisa izinin Malaminsu, idan aka taso su ƙarfe goma zai zo ya ɗauka kular ya fita titi kafin ƙarfe ɗaya ya ƙare har ya dawo, kuma Alhamdulillahi sosai ake ciniki Allah kuma ya saka mana albarka, da kuɗin sau tari ma ake cefane idan Abbaa bai da kuɗi.
****Yaran duk sun fita hayyacinsu tamkar wasu marayu marasa galihu, yanda ka san basu da uwa ba su da uba a raye, zaune suke a falo sun yi jungum jungum, kana ganinsu kasan muguwar yunwa ce ke ƙwaƙularsu kuma ba su da yanda za su yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu ba za su yi bala'in baka tausayi, rabon su da abinci tun guntun biredin da suka samu suka ci da safe, shima Abbansu ne ya rage ya kira su suka ɗauka ba don bai san ba su ci ba sai don ƙara musu.
Iyam ta fito a ɗakinta ta samesu tana cewa,"Kun duba kitchen ɗin babu sauran garin kwaki?".
Atika ta buɗe ido ta kalleta a wahalce tace,"Babu fa na faɗa miki, tunda Anty Sa'ida ta tafi kinga an kuma kai wani abu cikinsa ne, idan kina da kuɗi ki aika a siyo mana indomie kawai, ai akwai sauran gawayi a baya, kuma gaskiya ki faɗawa Abbaa kawai Anty Amarya ta cire girki da mu tun da bata son bamu, sai muke yi da kanmu ko Anty Faty ta dawo nan".
Ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla tare da dafe cikinta. Rumana dai na gefe bata iya cewa komai ba sai kallo da ido, ko da yaushe haka take bata da bakin magana, yarinyar ta rame sosai duk tayi ƙashin wuya tayi baƙi saboda wahala. Iyam ta zauna kan hannun kujera ta rafka tagumi, can kuma ta miƙe tayi ɗakinta tana cewa,"Bara mu gani".
Ɗakinta ta wuce tana faman laluben kuɗi, duk kuwa da cewa ta san ba ta da ko da sile, amma tausayin yaran yasa duk ta kiɗi me, ita ba ma ta kanta yunwa kam har ta saba zama da ita, Nazifi bai damu da bata kuɗi ba yanzu saɓanin da kullu yaumin naira dubu biyu zuwa uku sai ya ɗauka ya bata duk sanda zai fita, idan ma ya mance bata mantawa Sa'ida kan bi shi ta karɓo ta bata duk da a lokacin tana tsaka da tsangwamarta, to in ace da kuɗin da sai suke samu suna siyo wani abin suna ci da rana.
Wata huɗu kenan da tun bayan sakin Sa'ida al'amura suka canja a cikin gidan, ga ɓangaren masu son zuciya ba za su faɗi gaskiya ba amma tabbas shi kansa gidan da yana magana zai faɗi cewa anyi rashin nagartacciyar mace.
Zahra'u irin rayuwar hutun da ta taso a gidansu ita take yi a cikin gidan, bata son yin duk wani abu da zai wahalar da ita, girki kuwa dama ita ko a gida ba yinsa take ba sai ma da za'ai aurenta ne Yayar Mamanta ta takura akan sai ta shiga catering school, a babu yanda zata yi shi ne taje ta koyi girki, kuma ita babu wani abu da take ƙiwan yi sama da girki, balle da taga tana da uwar kuɗinta miji ma ya sakar mata ATM saboda haka kashewa cikinta kawai take da ciye ciyen order, hatta shi kansa tafi yi masa ordern abinci ta juye a flask a zuwan ita tayi, dama tana da chef ɗinta a hannu duk ranar da ta tashi zata ce da ita ga abincin da za'a mata zuwa yamma a kawo mata.
Tafiyar Sa'ida babu jimawa ƴan aiki suka yi tafiya ƙauye kuma har yau ba su dawo ba, ita kuma ganin akwai su Atika yasa bata damu kanta ba don dama bata shiri da yin shara da sauran ayyuka. Ita abin da ta sani taci ta kwanta ta danna waya, ranar da take da fita aiki ta fita, yarinya tayi kuka ta bata nono ta sha, idan goyo ya kama ta sauka ta miƙawa Kakarta ita, share share da wanke wanke da goge goge kai duk wani aiki na cikin gidan ta tattara shi ta barwa Rumana da Atika, yaran basa hutawa sam domin kuwa duty ta raba musu, da zaran Nazifi ya fita idan weekend ne zata tsawatar musu akan su yi aikinsu da gaggawa kafin ya dawo daga masallaci, idan kuma working days ne nan ma ba zata taɓa ko tsinke ba har sai yaran sun dawo a makaranta suyi aiki, idan ranar zata fita aiki zata ce musu idan ta dawo ta tarar ba su gyara wuri ba sai ta sumar da yaro.
Batun abinci kuwa dama ba'a magana, ba ko da yaushe suke samun ci ba har na safe kuwa, gwarama na dare wannan ta kan basu kullum shima kuma saboda Nazifi yana gidan ne, amma da safe in suka shirya za su wuce makaranta zata kaɗa musu worning da cewa kar su kuskura su nunawa uban ruƙonsu basu yi breakfast ba, dama ta faɗa musu ba ubansu ba ne uban ruƙonsu ne dan haka ko Abbaa da suke ce masa kar ta ƙara jin sun kira shi da haka, suke faɗa masa irin sunan da sauran suke kiransa Baba Ƙarami, idan nasa yaran sun tashi za su ke ce masa Daddy.
Duk wannan abun ba su kaɗai ba hatta Iyam bata ragwantawa ba, yanda ba zata bawa yaran abinci ba haka itama ba zata bata ba sai na daren dai, kira idan Iyam zata yi mata sau dubu miliyan ta amsa mata guda ɗaya tayi mutunci, kuma Iyam bata isa ta sakata aiki ba, kai tsaye zata faɗa mata ɗanki na ke aure ba ke ba, idan ma har ta samu arziƙin ta tanka mata kenan, don tafi gane ma taja mata tsaki ta wuce ta barta.
Yanayin yanda ta ke takunta ba ƙaramin shakkarta suke ba, ita kanta Iyam tsoron Zahra'u take ji ba kaɗan ba kamar wadda ta asirce, gidan kuwa tsakani da Allahnta ya isheta ta gaji da zaman gidan Nazifi, don ko kaɗan Zahra'u bata mutuntata bata ganinta da daraja, magana ma idan zata yi mamta murya a sama kamar da sa'arta take, ga babu damar komawa gida don tun ranar da aka yi sakin Sa'ida Malam ya kira ya faɗa mata cewar kar ta sake ta ƙara ko da zuwar masa gida ne, tunanin dawowar shi kuwa ma kar ta soma a lokacin da sha'awar hakan ya taso mata, sai san da yaga dama yace ta dawo tukunna.
Duk lamarin da ke faruwa babu masaniyar Nazifi tun da ba zaman gidan yake ba, duk da dai ya lura da canjin wasu abubuwan amma sai ya ɗauke ido bai maida hankali akai, hakan ma kuma saboda kar yay magana ne Zahra'u tayi fushi don ko kusa ba ya son yin abin da zai ɓata mata rai a cewarsa ita Uwar Ƴaƴansa ce, ba ta cancanci ɓacin rai a wurinsa ba tunda ta basa abin da ya shekara da shekaru bai samu ba.
Tana kan gado kwance tana bawa Iman nono, gefe ɗaya kuma waya ce a hannunta take dannawa, tayi ƙiba ta ƙara fresh, kaɗan kaɗan take murmushi. aka turo ƙofan ɗakin aka shigo, kasancewar tayi nisa akan danna wayar sai sam bata ji alamun shigowa ba.
Atika ta maƙale daga bakin ƙofa tsoro duk ya cikata, shayin yin magana take yi don ko magana ce suka yi zama tashin hankali ne, tace suna cika mata kunne idan ba Kakarsu ko uban ruƙon su zasu wa magana ba to ita su daina mata magana suna saka mata ciwon kai. Shiyasa ko da yaushe idan suka zo wurinta sai su raɓe a bakin ƙofa tana musu kallo ɗaya za su fice da sauri kafin ta sakko ta faffale yarinya da mari.
"Anty". Ta kuma kiran sunan a karo na uku tun shigowarta. tana shirin juyawa ta fita sai taga Zahra'un ta miƙe zaune tana gyarawa Iman kwanciyarta. Aje wayarta tayi a gefenta sannan ta ɗaga kai ta kalli Atika tace,"Zo nan".
Yarinyar ta tafi a hankali cikin sanyin jiki gami da bala'in tsoro, tana zuwa Zahra'u ta cafkota tare da ɗauke fuskarta da mari, cikin wata gigitacciyar tsawa da ta amsakuwa a ɗakin tace,"Don ubanki ban hana ki shigo min ɗaki ba, ban ce kome ne ba ku jira ni na fito, uban me zan miki da kika zo kina damuna da kira?".
Cikin rawar jiki Atika da tuni hawaye suka wanke mata fuska saboda zafin mari tace,"Anty kiyi haƙuri don Allah".
Zahra'u ta kama kunnenta ta murɗe sosai har sai da yarinyar ta fashe da kuka. "Durƙusa ƙasa da ubanki, na kira ki kin zo kin min tsaye saboda ba ki da ɗa'a".
"Don Allah kiyi haƙuri ba zan ƙara ba". "Idan kika kuma shigo min ɗaki me zan miki?". "Ki yi min duka". "Ba duka zan miki ba kakkarya ki zan yi, me ya kawo ki yanzu?". "Dama yunwa muke ji, cikina ciwo yake yi".
Ai tana rufe baki ta fara jin saukar duka a jikinta. "Shegiya munafuka masu kashe aure, wato so kike ya dawo yace bana baku abinci ko, ina guntuwan taliyan daren jiya da na baku, ko Kakar taku cinyewa tayi bata rage muku ba?".
Maganar take tana tsutsula mata wayar caja. "Ba magana na ke miki ba, na ba ku abinci ko ban ba ku ba?".
"Kin bamu Anty, mun ci mun ƙoshi kiyi haƙuri don Allah ba zan kuma zuwa na ce miki ina jin yunwa ba, don Allah kiyi haƙuri wayyo Allah na, Anty na daina dama Iyam ce tace na zo na roƙe ki".
"Kina ban haƙuri kina min kuka, to idan kinga na bar dukanki kin rufe min baki, kuma kije kice mata ba zan bayar da abincin ba idan so take ku ci ta fito ta dafa muku, zaman ɗanta na ke yi ba zamanta ba, kin ji me na faɗa miki ko kuwa?".
Ai kuwa babu shiri Atika tasa hannu ta toshe bakinta tana faman susar jiki, da ike da ɗan haskenta jijiyar goshinta ta fito tayi raɗau, idonta yay jawur duk ga shatin wayar nan ya fito a jikinta. "Sai na ce ki tashi ki fita sannan za ki tashi, in ci gaba da dukan na ki kenan, shegiya makira me kama da ƴaƴan aljanu, wai yunwa ku ke ji, don uwarki da ta kasa riƙe ki sauran taliyar da na ba ku da safe ubanki ne ya cinye, to wallahi ko za ku mutu cikin gidan nan ba ku isa nayi girki akanku ba sai dan son raina, shima kuma sai naga dama zan ba ku...kin fice min ko sai na tashi na take ki dangin tsiya da jaraba".
Da sauri kuwa ta miƙe har tana kifawa ta ƙwala goshi akan gadon ta fice da gudu. Sai da ta fita ta buɗe baki ta saki kukanta, tana zuwa ɗakin Iyam ta faɗi a ƙasa tana burgima. Yaya wacce ta zo babu jimawa ta miƙe da sauri tana cewa,"Ke lafiyar ki?".
Yarinyar cikin kuka mai ban tausayi take cewa,"Anty ce ta zane ni".
"Duka? Me kika yi mata tayi miki wannan mugun dukan haka? Ji fa yacca fatarki ta farfashe, kutumar bala'i anya Zahra'u ta taki hanyar zama lafiya da mu kuwa".
Yaya ta faɗa tana waigawa ta kalli Iyam wadda tayi shiru cikin damuwar abun, tace da ita. "Iyam kin ga fa yacca Zahra'u ta daki yarinyar nan".
Iyam tace,"Uhmm ai ki bari kawai, Zahra'u ta zama abin da ta zama, yanzu bata da kirki sam, gaba ɗaya ta sauya daga Zahra'un da kika sani a baya, ni kaina ban isa ba yanda kika san ba uwar mijinta ba, ranar nan ma kusan kawo min hannu tayi saboda na ɗaga mata murya na ce ta gyara ko nasa ɗana ya koya mata hankali".
Nan ta kwashe komai take faɗawa Yayan, wacce ɓacin rai yasata cewa,"Ba ta ba ku abinci? Shi kuma Nazifin yana ina?".
Iyam ta haɗa hannaye alamun bata sani ba kafin tace,"To ina na ke ganinsa ma balle na masa bayani, yanzu fa idan ya shigo ya gaida ni da safe shikenan sai wata safiyar, dawowarsa ma bana sani don ba ya shigowa yace min ya dawo, idan na aika yara su kira shi sai dai yay ta cewa gashi nan ga shi, ita kuma.ta ƙware a makirci duk wannan iya shegen da take yi a gabansa bata yi mana, ke idan ya wuni a gidan ma sai tayi tamkar zata cinye ni".
Yaya ta waiga ta kalli ƴarta Rumana da ke kwance kan gadon Iyam ta dafe ciki, idonta a rumtse tana cije fuska. miƙewa tayi ta fita a ɗakin Iyam na ta kiranta akan ta dawo ta dawo, bene ta nufa sai ga Zahra'u na sakkowa.
"Ke ashe ba ki da mutunci, ba ƴar arziƙi ba ce, saboda ba ki darajarta uwarki shine za ki dinga wulaƙanta tamu uwar, kuma tsabar ba ki da imani har kike bar mana uwa da yara da yunwa, so kike ciwon yunwa ya kama su, ko ke kika kawo abincin da har kike da ikon hana su, banza mara mutunci". Tayi maganar cikin faɗa sosai.
Zahra'u tayi mata duba na rashin mutunci tace,"Kin san wani abu? Na ɗaga miki ƙafa iyaka yau amma ko don gaba ki kiyaye ɗaga min murya ko kuma ki kwantata lamari da mahaifiyata, sannan kar ki ƙara zagina ni ba banza ba ce, idan kika yi kuskuren hakan za ki gane banbancin aya da tsakuwa. Sannan da kike maganar na wulaƙanta muku uwa ta dai wulaƙanta kanta, ban da wulaƙanta kai da aurenki da gidanki, mijinki da ransa da lafiyarsa ki kwaso ƙafafu ki taho ki tare a gidan ɗa...abinci kuma ba su suka aje ni ba, don haka girki zan yi shi me kawai na bawa wanda ya aje ni a gidan, idan sun ga basu iyawa su tattara su koma gidan ubansu tunda su ba shegu ba ne, idan kuma shegu ku ka haifa sai naji bayani don haka kawai ba za ku ɗebi ƴaƴa ku lalaƙa masa ba, ke koma shegun ne a yau ki tattara garanku ki wuce da su domin ban shirya ruƙon ɗan kowa ba, aikin wofi kawai ba ki da aiki ke kenan kina kan hanyar gidan ƙani sai jace wata tsohuwar bazawara".
Hannu Yaya ta kawo zata mareta aikuwa Zahra'u tayi saurin riƙeta tana yin wurgi da hannun nata, ta ɗaga yatsa tana nunata da cewa. "Ko wannan tsohuwar ta gefenki bata isa ta ɗaga hannu ta mareni ba bare ke karan kaɗa miya Yayar miji". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu