Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 15
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 15: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 15. Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
4,357 words
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR20FT5* Nazifi na isowa gida ya tarar da Yaran Yaya har su shida, Maza huɗu mata biyu wai sun zo ramawa uwarsu dukan da aka mata. A falo ya tarar da su sun kafa sun tsare a bakin matakalar bene, Maimu da Zuwaira sai danna uwar ashariya suke me muni suna faɗin idan Zahra'u ta cika ƴar tasha ta sakko taga idan basu nakastata ba yau. Yau sai sun ga wanda ya tsaya mata ba kaki ba ko ubanta ne shugaban sojojin Najeriya sai sun mata lahani kuma sun zauna lafiya.
Mazan kuma suna tare da mahaifiyarsu akan kujera ta na ƙara kora musu jawabai, jawaban da ke daɗa fusata su anci mutuncin uwarsu. Idon Labahani ne ya fara kaiwa kan Nazifi da ke tsaye bakin ƙofa yana kallon su Maimu, da sauri ya zunguri mahaifiyar tasu da sauran ƴan uwansa, da yake suna bala'in shakkarsa duk sai suka natsu Garzali na kiran sunan Maimu da yi musu alama.
Yaya ta miƙe tana faman galla masa harara da cewa,"Ka dawo kenan, to ban tafi ba ina nan mara kunya mara mutunci, wato akan mace yau idonka ya rufe ka manta wacece ni a wajenka ko".
Ko kallonta bai yi ba ya nufi hanyar sama, da sauri su Zuwaira suka matsa masa suna faɗin,"Baba Ƙarami sannu da zuwa".
Babu wanda ya saurara cikinsu ya haye, ya daɗe yana faman kiran Zahra'u akan ta zo ta buɗe masa ƙofa taƙi, sai can tunanin sa spare key ya zo masa. Ƙasa ya sakko ya shiga ɗakinsa, durowan kusa da gado ya buɗa yana bincika maƙullan, sai dai iyaka dubansa babu, kuma nan take Sa'ida ta faɗo masa a rai, saurin kawar da tunaninta yay ya koma wadrobe yana ci gaba da bincikawa nan ma duk babu.
Tsaye yay ya kama ƙugu, Allah ɗaya ya san irin girman ɓacin ran da ke tare da shi, har yanzu kuma ya rasa ma wanne mataki zai ɗauka akan Yaya da Ƴaƴanta. _"Na'am Hubbi, Ohhh na canja musu wuri suna ɗakinka na sama cikin durowan kusa da madubi"._
Rumtse ido yay gam tare da sauke ajiyar zuciya, bai san ta yanda aka yi maganar Sa'ida ta faɗo masa ba a halin yanzu. ya fito ya koma ɗakinsa na sama, yana buɗe durowan ya kwaso maƙullan dukka gidan yana ƙara tunawa da ranar ƙarshe da Sa'ida taje ƙauye ya kirata yana tambayar maƙulli. Ko da ya buɗe ɗakin ya tarar da Zahra'u akan gado ta kifa kai da gwiwo, tura ƙofar yay ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗauki Iman da ke kusa da ita, duban jikin yarinyar yake kamar wanda aka ce masa taji jiwo. Sai da ya tabbatar babu wani ƙwarzanan rauni a jikinta tukunna hankalinsa ya sassauto har yana sauke doguwar ajiyar zuciya.
Shifa a rayuwarsa ta yanzu yarinyar nan ce, idan da ita akwai shi idan babu ita to tabbas babu shi. Ya kai hannunsa saman kafaɗar Zahra'u cikin kwantar da murya yace,"Kiyi haƙuri don Allah". Ture hannunsa tayi tana fashewa da sabon kukan munafurci. Nan fa kuma sai ya ruɗe ya shiga lallashinta yana ta aikin bata haƙuri har da sakkowa ya duƙa gabanta, ita kuwa faɗi take tana sake maimaita masa sai ta tafi gida.
"Na faɗa maka Daddyn Iman ba zan ƙara kwana ba ka sallame ni kawai, ba zan iya da wannan cin mutunci da wulaƙancin na ƴan uwanka ba, kowa ya raina ni basa gani na da girma, Yayyunka su min Ƙannenka su min yanzu kuma tsabar cin fuska har ta kai ga Ƴaƴansu ma, kuma kowa ya tashi buɗar baki sai ya yaɓa min magana yace ba don kana sona ka auro ni ba, ni matar shige ce kuma matar shige bata daraja, tsakani da Allah kayi min adalci kenan idan ka san da haka me yasa baka faɗa min ba na cirewa kaina soyayarka tun da wuri".
Tayi maganar tare da fashewa da kuka sosai a wannan karan kuma na gaske ne, ta goge hawayen tana kallonsa,"To ka bani takardata kawai tunda ka samu dalilin da yasa ka aure ni ɗin, idan ya so sai kaje ka dawo da Uwar gidanka ka bata ƴar taka ni na yafe, Allah ya haɗa ni da mafi alkhairin...".
Saurin kai hannunsa yay bakinta ya rufe,"Haba Zahra'u, wai ke har akwai wanda zai faɗa miki cewa bana sonki ki yarda. Ke da kan ki ya kamata ki ƙaryata hakan ai, kin sani babu wanda na ke so bayan iyayena sama da ke da Iman, na sha faɗa miki zanen ƙaddara shi yasa na fara auran wata kafin ke, kuma ban san wata soyayya ba sai da na aure ki, in ace ni ke da kundin littafin rayuwata da babu wata mace da zan yi tarayya da ita in ba ke ba, ke ɗin nan kin fiya min kowa da komai, kar ki ƙara min zancen wacca muka rabu tarihinta ya riga ya shuɗe a wajena, ni ke kawai na ke kallo a matata ta farko kuma ta ƙarshe, Don Allah don Annabi na roƙe ki ki bar batun za ki tafi, in dai abin da suka miki ne zan ɗauka mataki akai ki bar ni da su, babu wanda ya isa ya taɓa min ke na ƙyale shi".
Kukanta taci gaba, ya hargitse duk ya gigice ya burkice, yafi tsawon awa guda yana famana lallashi kafin tayi shiru tace masa ta haƙura amma ya takawa Yayarsa burki. Ya shiga mata rantse rantsen zai ɗau mataki amma ta bar kukan idan ba haka ba zai sami wata natsuwa ba, shi kukan nata ne ke ɗaga hankalinsa. Fita yay a ɗakin da Iman saɓe a kafaɗarsa, yana fita tayi wata dariya tana tafa hannu, ranta ƙal ta cimma target ɗin farko sai na gaba kuma, ai ta sha alwashin babu boka babu Malam sai ta raba Nazifi da kowa ya zama nata ita kaɗai, shi da duk wani abu da ya mallaka.
Yana sakkowa ya dubi Yaran Yaya da ke zaune a falo, waɗanda ganin nasa yasa suka fara rawar jiki suna raba idanu, ya dube su yace,"Wato a gidana ku ka zo kuna juye rashin tarbiyar da aka ba ku ko? Matata sa'arku ce don ubanku?".
Zuwaira ce tayi dakiyar cewa,"Baba Ƙarami ai ita ce ta fara cin mutuncin mahaifiyarmu, mu kuma babu wanda zai taɓa mana uwa mu ƙyale shi".
Tasss ya ɗauke fuskarta da mari. "Nayi ball da ke a wurin nan, ita Uwar taku idan ta kama girmanta har a tsinka shi? To wallahi duk wadda ta ƙara zuwar min gida tayi ɗiban albarka irin haka sai taga yanda zamu kwashe da ita, banzaye marasa ɗa'a, Kun fita kun bar min gida ko sai na juye muku dukka ɓacin raina".
Ya kalli mazan yace,"Minti ɗaya ku ka ƙara a cikin gidana sai dai yau ku kwana a bayan kanta, kuma ina mai tabbatar muku ba ku da me tsaya muku wajen karɓo ku".
Ɗaya bayan ɗaya suka yi gaggawan ficewa, matan kuma suka ɗauki mayafansu Maimu tayi saurin saɓa ɗanta a baya suka fice da hanzari ba tare da ko sun tsaya sallama da uwarsu ba. Suna fita ya shiga ɗakin Iyam, yana shiga suka yi karo da Yaya da ke niyyar fitowa don ta jiyo shi da yaran.
Kamar bai ganta ba don ko arziƙin gaisuwa bata samu ba a wajensa, ya zauna kan kujera murya ƙasa ƙasa dai kana ji kasan a ƴan ƙunci ake yace da ita,"Sannu da gida".
Itama da irin nasa yanayin ta amsa masa,"Yauwa, ka dawo kenan".
"Na dawo". "To sannu, Allah yay albarka".
"Amin, Allah ƙara girma da lafiya". Sai kuma ya kalleta yace,"Amma Iyam kina da masaniyar fitinar da Yaya ta zo ta tayar min a cikin gida? Fisabilillahi abin da tayi ya dace a matsayinta na babba wacce take uwa a gare mu? Tsakani da Allah ina ita na yin faɗa da matata? Ko da sa'arta ce ai babu daraja sam tayi rigima da ita matsayinta na Yayar miji balle ma ba sa'arta ba ce, kin kusa yin ƴa da ita amma ki zauna ki kama dambe har kina faɗa mata maganganu irin na ƙananun yara marasa lissafi, to gaskiya ni banji daɗi ba, don wallahi tallahi ban da ita ɗin ce kafin zuwana na turo hukuma sun tafi da ita, to taci darajar wata darajar ne kawai, ko ba komai ciki ɗaya yafi gaban wasa. Amma duk da haka zan ɗauki mataki, domin ba zan zuba ido tana haddasa min fitina a cikin gida ba, kawai tun da bata son matata to kar ta ƙara zuwar min gida gaskiya, ta tsaya can iya gidanta idan gaisawa ne na ke zuwa muna yi, kuma ai ga waya idan ma wani abun take buƙata tayi min text don ko yawan kirana ma da take yi ya kamata ta barni haka, kuma ta fita a harkar iyalina ko kallo banza kar ta ƙara yi mata".
Ya maida kallonsa ga Yayar da ke kallonsa da sakakken baki cikin mamaki. "Kuma Yaya yaranku kawai ki ɗauke su ki tafi da su, dama rashin haihuwa yasa na karɓe su kuma yanzu Allah ya azurtani da nawa, na samu matar da zata ke haifa min ƴaƴa don haka na gode da taimakonku da nuna kulawarku. Ba zan ce ban ji daɗi ba haka ba zan ce ba kuyi min adalci ba, kawai dai kije da su suci gaba da rayuwa a gabanku nima kuma sai na ji da nawa da Allah ya bani, In yaso kuɗin da kika karɓa a wurinta sai a bawa yaran".
"Kuɗi kuma?, wanne kuɗi kenan?". Suka tambaya a tare ita da Iyam.
Ya kalli Iyam yace,"Da safe da zan fita na bawa Zahra'u dubu ɗari huɗu akan zata yiwa yaran nan siyayyar sabbin kaya da duk abubuwan buƙatunsu, don har uniform ma tace ya kamata a canja musu, to da ta zo wai sai ta ƙwace kuɗin har tana faɗin ai satar min kuɗin tayi. To tunda bata ganin irin ƙoƙarin da take yi akan ƴaƴansu da ni kaina ɗin da bana banbanta cewa bani na haife su ba, to su ɗauki yaransu kawai dama bani nace a bani ba, ra'ayin kansu ne. Kuma na rantse da Allah Iyam ban da darajar ke da Malam da kuke raye wallahi akan danganta min mata da ɓarauniya da tayi sai nayi ƙararta gaban alƙali, don sai ta faɗi lokacin da ta kamata tana ɗaukar min kuɗi, bana son ƙazafi na tsani mutum me yiwa wani ƙazafi, amma a hakan ma taje ita da Allah don ta ɓatawa iyalina suna, kuma idan ta sake tabbas zan datse alaƙar da ke tsakanimu".
"Ehh lallai Yarinyar nan ta cika makirar mace, wato ƙarayayyakin da ta shirya maka kenan, kai kuma saboda shashasha ne sakatare soloɓiyon namiji an shanyeka har ka hau ka zauna akan tsararriyar magana ta matarka. Banza uban wa yay sanadin auran na ku idan ba ni ba? Kai inda hankali da tunani akanka ma har ka zo kana waɗannan maganganun, wanne gata ne ban maka ba a duniyar nan Nazifi? Ina ce auranka na farko ni na maka lefe, amma shi ne yau akan mace zaka rufe ido kaci mutuncina, to bari kaji baka isa ka hana ni zuwa gidanka ba tun da har mahaifiyarmu na ciki, yara kuma da ta zugaka akan ka mayar da su yanda ta zo ta same su haka zata bar su".
Kaɗa kansa yay yana miƙewa tsaye. "Shikenan kar ki fasa zuwar min gida, Allah Iyam duk abin da nayi mata ita tajawa kanta kuma zan je na sami Malam na faɗa masa abin da ta zo tayi min a gida. Yaran kuma idan ma ba ki tafi da su ba zan kira ubayensu su zo su ɗauke su, tun da na samu nawa babu ɗan wanda zan ci gaba da riƙewa".
Yana gama faɗin hakan ya fice. A daren ranar ya kasa haƙuri sai da yaje har can gida ya samu Malam ya karanta masa duk abubuwan da suka faru, Malam ya kira Yaya ta waya yaci mutuncinta iya gwargwado, ya kuma tsawatar mata akan kar ta ƙara taka ƙafarta gidan Nazifi in ba haka shi da kansa zai ɗauki mataki. Wannan faɗa da Malam yay mata shi ya janyo jin cewa ta rabu da Nazifi ita da shi kuma sai ta Allah, ko mutuwa yay ba zata dubi in da iyalansa suke ba.
Bayan wani lokaci da faruwan hakan Iyam na ɗaki tana ta ƙwala kiran Zahra'u, wacca take falon ƙasa tana kallo kuma tana jin kiran amma taƙi amsawa tayi biris kamar bata ji ba. Tun ranar da akai case ɗin Yaya na zuwa suyi dambe da Zahra'u Iyam ke fama da ciwon ƙafa, farko ba su tsammaci abun babba ba ne ashe ciwon ƙafarta ne ya dawo, dama ƙashin gwiwarta jona mata shi aka yi to shi ne ya daɗa gurɗewa yanzu.
Cikin wata guda da ɗoriya har ta rame saboda tsananin ciwo, kullum ita da Nazifi suna kan hanyar asibiti zuwa gashi da karɓar magunguna. Wanda in ya dawo sai ya barta da Zahra'u a tsammaninsa zata bawa mahaifiyarsa kulawar da ya kamata, nan kuwa bata bi ta kanta in dai ba yana gidan ba taga idonsa, magani ma idan taga dama tana shiga ɗakin zata ɓalla taje tayi floshing ɗin su ba zata bata ba.
Shiyasa Iyam ke shan wuya sosai, bata iya yin komai da kanta sai an taimaka mata, dama sau tari sai dai ta faɗo akan gadon ta rarrafa da jan ɗuwawu tayi abubuwan da zata yi, to garin wannan kifowar da take yi ne ta samu gocewar ƙashin kafaɗa. Tana ta so ta koma can gida Malam yace shi fa bai san zancen dawowarta ba ai bata ma fara gajiya da gidan Nazifi ba tukunna, Ita kuma Zahra'u har da kukanta akan a taimaka a bar mata Iyam zata dinga kula da ita ba zata bari iya ƴaƴanta su kwashe ladan su kaɗai ba, ai itama uwa ce a wurinta, kuma in suka ɗauketa kamar ba su yarda da ita ba ne, dama ga Nazifi ya rantse ya kuma ya rantse duk wacca ta zo masa gida a cikin Yayyunsa da Ƙannensa sai kotu ta raba su, to kuma haka dole ya haƙura duk sati biyu sai suke zuwa dubata sau ɗaya kuma in suka zo za su samu ranar Zahra'u ta gyareta babu ta in da zasu faɗi wani abu na cewa Iyam bata samu kyakykyawar kulawa a gidan Nazifi har a yarda da su.
Yanzun ma banɗaki take ta so ta shiga zata yi kashi ta kasa lallaɓawa ta sakko, shi ne take ta faman kiran Zahra'u amma taƙi zuwa, duk ƙoƙarin da take na riƙe kashin abun ya faskare sai sakinsa tayi a wajen. Ai fa kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani irin ciwo a zuciyarta, yanzu har ita matar ɗan da ta haifa zata ke wulaƙantata haka? Kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa ɗaukar wani mataki, duk yunƙurin da tayi na ganin ta nunawa Zahra'u iyakarta sai taji tamkar an danneta, haka ta rasa ta ina tsoron Zahra'u da shakkarta ya samu muhalli a zuciyarta, Surukarta fa! Isan ba ta isa da ita ba ai ta isa da ɗanta ko? Har dare tana zaune cikin kashi, ga wani azababben ciwon ƙafa da ke damunta, ga uban yunwa don tun shayin da Nazifi ya kawo mata bata ƙara sa komai a cikinta ba, ta rasa yanda zata yi gaba ɗaya.
Bayan dawowar Nazifi ɗakin mahaifiyar tasa ya fara shiga domin dubata, sai dai me? shima tun daga falo ɗoyin kashi ya bugi hancinsa, sai dai bai kawo cewar uwar tasa ce tayi ba. Daga kwance ya sameta ya kunna fitila yana kallonta kwance kamar mara rai, ya tafi da sauri gareta yana kiran sunanta. Sai da yaje bakin inda take ya ankare da dama dama ɗin da tayi cikin kashi. Ya furta,"Subhanallah Iyam ya aka yi haka?".
Kamar zata yi kuka cikin murya mai ban tausayi tace,"Wallahi Nazifi matsuwa nayi ne".
"To amma me yasa ba ki ƙwalawa Zahra'u kira ba, ina wayarki saboda irin haka fa na ce kike barinta kusa da ke ko da zaki kirata bata nan ƙasa sai ki kira wayarta, kuma ita ya akai yau ban sameta anan ɗin ba?".
Iyam tayi wani murmushi me ciwo da cewar,"Wayar ce Nazifi ban an in da na wurgata ba, yau ko ƙararta ma banji ba".
Da matuƙar tausayin mahaifiyar tasa yace,"Bari na kirata ta wanke miki, sannu in sha Allahu kin kusa samun lafiya, likita yaje kawai a fita da ke ƙasar Germany".
Ya faɗa yana ƙoƙarin fita ta tsayar da shi. "Ƙyale Zahra'u Nazifi, kai dai Allah maka albarka da ɗawainiyar da kake yi akaina, yanzu dai kai taimaka min ka raka ni banɗakin sai na gyara jikina".
Kawai a ɗan wannan furucin nata sai ya fahimci da akwai wani abu, don kamar ma muryarta da alamun tsoro a ciki, anya kuwa Zahra'u na kula da ita? Anya tana cika alƙawarin da ta ɗaukar masa kuwa?
Baki ya buɗe zai yi magana ta girgiza masa da cewa,"Nazifi bana so na shiga tsakaninka da matarka ka rabu da sha'aninta kawai, amma dai dole ka haƙura Faty ko Lubabatu wani ya dawo nan wurina da zama don gaskiya ni ɗaya na san a halin da na ke ciki. Matar babu abin da take min a bayan idonka, duk wani rawar jiki daka ga tana yi akaina wajen nuna min so da kulawa to a gaban idonka ne, makira ce ta ƙarshen ƙarshe, Zahra'u idan kasa ƙafa ka fice ko waiwayowa ɗakin nan bata yi, Nazifi matarka halin da nake ciki ma bata duba ta bani abinci ba haka nake yini na kwana da yunwata, kuma banga laifinta ba wannan ɗawainiyar ba kowa zai iya ba sai wanda ka haifa ɗin".
Ran Nazifi ya ɓaci zuciyarsa na tafarfasa ya fita ya bar ɗakin. Ƙwala kiran Zahra'u kawai yake cikin amon tsanin ɓacin rai tun daga ƙasa har ya hau sama. Garam ya banka ƙofar ɗakinta wadda ta firgita ta juyo tana dubansa da cewa,"Innalillahi Honey lafiya?".
"Ashe ba ki da mutunci, ke ɗin dama ba ƴar arziƙi ba ce? Ashe wulaƙanta min mahaifiya kike yi, mahaifiyata Zahra'u za ki ke hanawa abinci? Sannan bata da lafiya ki kasa sauka wurinta kike kulawa da ita kina taimaka mata? Dama ashe ganin idona yasa kike mata abubuwan da ba zan zargi kina cutarta ba, kin san a halin da na zo na sameta kuwa yanzu? Uzurin bayan gida ne fa ya kamata kuma tace ta kira ki kina jinta kika ƙi zuwa gareta, Zahra'u mahaifiyar tawa kika ma wannan wulaƙancin?".
Juya idanu tayi ta ɗauke kai, lokaci guda ta sha mur kafin ta jiyo cikin ɗaga murya ta katse shi da faɗan da yake faman mata. "Kaga Nazifi Dakata! To ni ɗin dama bautar mahaifiyarka na zo yi ne, gaskiya ni ba zan iya wahalar nan ba, haba komai sai dai ayi mata hatta wanka wannan sai an taimaka mata to ni ba zan iya ba, ka ɗaukar mata masu aiki ko ka maida ita gidan mahaifinka ni kam ba zan kashe kaina da bauta ba, kuma wallahi in har ka ɗauko wata cikin ƙannenka da sunan su dawo nan da zama su kula da ita wallahi sai dai in ka sallame ni".
Ta faɗi hakan ta raɓa shi ta fita a ɗakin, barin Nazifi tayi da sakakken baki wanda ya bi bayanta da kallo da maɗaukakin mamaki, gaba ɗaya sai yaji abun wani gingirin gin domin tun da yake zaman aure matarsa bata taɓa ɗaga masa murya ba, haka bai taɓa umartata da ta yiwa mahaifiyarsa abu taƙi yi ba. Amma yau yaga zahirin wacece Zahra'u a cikin kalamanta da ƙwayar idonsa da sonta ya rufe ganin duk wani kuskurenta.
Ficewa yay ya sauka ƙasa da sauri ya koma ɗakin Iyam jikinsa sai rawa yake yi, Yana son mahaifiyarsa so yake ya rabu da ita lafiya. Yana shiga da kansa ya kamata ya shiga da ita toilet yay mata duk abin da ya dace sannan ya fito da ita. Abincinsa ya ɗauko ya zauna gabanta yana bata tana ci, haka tana ci tana zubar hawaye shi kuma jikinsa duk yay bala'in sanyi ya mutu, a zahiri ma ba zai ce ga tunanin abin da yake cikin ransa ba amma tabbas yana jin wani ɗaci a ƙasan ransa. __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA* Halimahz
*LOKACI NE* Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI* Aisha Yabo
*WASA DA RAI* Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200
*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5* "Kai ɗago fuskarka ka kalle ni". Ya ɗago yana duban Malam ɗin wanda ke jifansa da mugun kallo.
"Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...".
"Don Allah Malam ayi haƙuri...". "Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai".
Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa. Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar.
Yinin ranar dai gaba ɗaya haka ya wuni sukuku kamar wani mara lafiya. Bai koma gida ba sai sha biyu na dare ya bar asibiti wajen Iyam, lokacin da ya koma Zahra'u ta rufe ko'ina babu yacca bai yi ba akan ta buɗe ƙofar ta ƙi, kuma ba bacci take yi ba idonta biyu, zai kira ta ɗaga sai tace masa ya koma in da ya fito, ransa ya daɗa dagulewa, ga azababbiyar yunwa kamar bai ci abincin rana ba, kuma da zai taho ba yanda Anty Aisha bata yi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace ya ƙoshi domin idan ya zo a ƙoshe wani tashin hankalin ne na daban tsakaninsa da Zahra'u.
Haka dole ya koma mota ba shi da yanda zai yi, ya buɗe baya yay kwanciyarsa. Ko da Asuba ma bata sakko ta buɗe ƙofar ba sai da safe wajen ƙarfe takwas kana, lokacin zata fita wurin aiki ta fito ko kallon wurin da yake bata yi ba, sai da ta shiga mota ta zo daidai wurin tasa kana ta zuge glass tace masa,"Ai yanda ka ɓarar min da aji kasa na hayo motar haya to ka dinƙi kurɓan baƙin ciki a gidan nan, yauma idan kaga dama kar ka dawo da wuri ka kuma zama a can".
Tana ganin ya buɗe motam zai fito tayi sauri bawa motar wuta ta fice. A ciki ya samu ta kuma barin Iman yauma sai tsala uban kuka take, ba yanda bai da ita ba akan take tafiya da yarinyar in yaso ta samu me raino tace sam ita aiki kawai taje yi can ba zata dinga ɗaukan yarinya tana tafiya da ita ba, tama kusa yayeta na gaji da wahalar shayarwa.
Ko wanka bai iya tsayawa yayi ba kitchen ya shiga ya dafa abin da zai ci, kamar ya san bata ajiye masa ba kuwa, bayan ya gama ya ɗora wanda zai tafiwa da su Iyam asibiti, matan ƴan uwansa kowacce ka ganta da coolern abinci amma shi ban da tasa. Bayan ya fito a wanka ya gama shiryawa ya sanya haƙarƙarinsa akan gado, idonsa na kallon sama kana gani ka san cikin harbawar sakan yay zurfi cikin tunani wanda har sai a iya zuwa ma ayi sata a ɗakin bai sani ba.
Ya jima a haka kafin ya fita falo ya karɓo Iman wadda ke hannun Marawiyya tana ta faman lallashinta, ya zo ya zauna yana mata wasa tuni tayi shiru, can kuma sai tayi bacci ya ɗauketa ya kwantar da ita a ƙirjinsa, cikin shirun da yay sai ya tsinci gimlawar tunanin kiran lambar Sa'ida. Wayarsa ya ɗauko yay dialling numbern, tun ranar da ya saketa dama ya goge duk lambobinta da hotunanta, ashe akwai ranar da riƙe lambartata zata yi masa rana. Haka yay ta gwada kiran lambar bata shiga, sai can a koma ce masa a kashe take, ya jijjiga kai kar dai da gaske kamar yanda aka faɗa masa ta sauya layi ne, aje wayar yay a gefe bayan yanke shawarar zuwa yamma zai je gidan na su, ya san Sa'ida mai haƙuri ce da sauƙin kai, tabbas idan ta gansa zata ji tausayinsa kuma zata yi haƙuri ta dawo gidansa, wanda zai matuƙar son hakan ba don komai ba sai saboda Iyam, domin ya san in ace Sa'ida na nan babu dare babu rana tana kan zaryar asibiti babu gajiyawa babu ƙosawa, kuma cikin bawa mahaifiyarsa kulawa da kyautatawa, kuma atleast zai samu sauƙin damuwar da yake ciki a yanzu na wasu al'amura da ke neman cakuɗe masa, saɓanin Zahra'u da bai ma san ta yanda zai fara sanar da ita ba don babu ta yanda zata fahimce shi, batun sake aure ma kuwa tunanin hakan na zuwa kansa ya ke kaudar da shi amma Allah ya gani ya gaji da halin Zahra'u.