Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 16
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 16: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 16. ****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da…
4,473 words
****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da na ke koyarwa. Daga gefe na ke ina bitar littafin muwaɗɗa, ku san awa guda su Malama Mastura na aikin hira akan rayuwar zawarci, dama kusan duk Malamai matan mutum uku ne masu aure amma mu shida duk zaurawa ne, duk san da aka zauna ana hira sai naji suna ta faɗin ƙalubalen da suke fuskanta akan zaman zawarci, cikin gidan iyayensu ba sauƙi haka waje ma babu sauƙi, wasu cikinsu ma faɗi suke har gwara su zauna a gidan auren miji yay ta gallaza musu akan dai zaman gidan da suke yi ana tsangwamar su, ranar da Malama Alawiyya ke bamu labari har ƙwalla sai da nayi wai cikin gidansu kullum mahaifinta sai ya kyareta kuma sai ya goranta mata akan ta kashe aure ta dawo gida ta zauna, haka mahaifiyarta ma bata barta ba tayi ta faɗa mata magana komai nata ta hanata taɓawa har ce mata take tana lalata mata carpet saboda kwanciya, basu san buƙatunta ba komai ita kewa kanta da ƴar ƙaramar yarinyarta da ke hannunta, abinci kawai ake bata shima duk sanda za'a bata sai an mata mita, saboda haka ne ta nemi aikin koyarwar to shima mutane nata surutun yawon ta zubar take yi, Babansu kuma na faɗa mata ai ko aikin me zata yi bata dai da daraja a idon duniya.
Hakan sai yay ta bani mamaki kuma sai naji fargaba ta kama ni, a raina sai na ce to ko dan ni mutuwar auren nawa ban jima ba ne shiyasa hakan bata fara faruwa da ni ba, ni ban san wani abu kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, gaskiya idan na buɗi baki na ce nafi jin daɗin gidan aurena akan zaman zawarcina to sai Allah ya kama ni, ƴan unguwa ne ma dai ke ta gulmace gulmacensu, wataran ma idan na dawo haka daga makaranta har na kanji ana ƙusƙus, Abbaa ma ina jinsa ranar suna hira da Ummani yana faɗa mata an fara surutu akaina ƴan unguwa don haka wataƙila zai yarda ne na tafi can school of nursing jigawan tun da ba a samu ta nan kano ɗin ba.
Gaba ɗaya sai na saka damuwa sosai a raina don tunani bai wuce akan masu magana akaina ba, da kuma a zo nan ba da jimawa ba iyayena su fara min maganar aure don wataƙila ganin ban daɗe a gabansu ba ne, amma kuma sai ya kasance ko da yaushe Abbaa nasiha yake min da kwantar da hankali ta yanda damuwa bata da ikon samun muhalli a zuciyata, kuma da hakan na samu natsuwar ruhi da zuciya matuƙa ganin iyayena na tare da ni, Allah har mancewa na ke da wani suna bazawara ji na ke tamkar ban taɓa auren ba. Yayyuna kuwa babu abin da zan ce da su sai Allah ya saka musu da gidan Aljannah ya ƙara musu buɗi, gata dai iya gata da nuna tsantsar kulawa bayin Allahn nan na yi min, duk san da suka shigo gida sa tambaye ni ban dai da wata matsala ko na ce musu ehhh.
Yashaik da kansa ya biya min kuɗin koyon ɗinki tun watarana da ya zo ya samu muna hirar da Ummani, wallahi ba ai sati ba sai kawai ganinsa nayi da form yace na cike anjima na kai gidan Maman Binta, ranar har kukan farin ciki nayi, to yanzu ɗinkuna na ke tayi kuma Allah yasa min nasibi a kaasuwancin. Duk wata kuwa idan aka bani dubu takwas ɗita a islamiyar da na ke koyarwa ba na riƙe ko sisi tawa yaran Yashaik da Yaya Imam na ke wa siyayya, sauran kuma in siyo omo da sabulun wanka da na wanki na aje mana a gida, Abbaa yay ta faɗa wai na ke rike kuɗina ina adanawa ko na ke siyawa kaina abu, ni kuwa banga amfanin kuɗin ba in har ban musu ba, to me ma na ke da buƙata wacca basa min?
Ranar da na taɓa faɗawa su Malama Alawiyya na taɓa aure ƙaryata ni suka yi wai wallahi kwata kwata ban kama da wacca tayi aure ba, kar nayi wasa da damata na amincewa Malam Isah kawai tunda shi ba ƙaramin yaro ba ne da gaske aurena zai yi babu wasa a maganarsa, ni dai kawai nayi murmushi ban ce musu komai ba saboda Allah ɗaya ya san me na aje a zuciyata dangane da aure wanda ya fita gaba ɗaya a raina, ana hakan kuwa watarana sai Malama Aisha ke cewa ashe da gaske ne ni bazawara ce taji a staff room ɗin Malamai maza ana maganar wai Malam Isah yaje neman aurena ance masa na taɓa aure to yanzu ya janye maganarsa don bai san mene dalilin fitowar tawa ba, shi ne har Malam Amiru ke cewa dama baka shaidar mutum ta fuska, amma ƙila ganin ina da ƙuruciya ne yasa na kaso auren na fito ba zai wuce talaka na ke aure ba abun duniya kuma ya rufe min ido.
Maganar ta tsaya min a rai, da na faɗawa Ummani tace ai sai na toshe kunnena akan maganganun mutane. Yau na dawo daga makarantar na samu wata Kakarmu ta zo, ban ma san da zuwan nata ba don har sai da nayi sallar magriba na fito zan ɗauko abincin rana a kitchen Ummani ke ce min idan na gama cin abincin na shiga ɓangaren Baba Tijjani na gaida Gwaggo Marka. Aje abincin na yi na ce bari na fara zuwa mu gaisa, ina zuwa kuwa na sameta cikin jikoki ana ta hira, da murnarta ta tarbe ni muka gaisa, take min jajen mutuwar aurena wanda sai da ta zo yaune ma take ji.
Sai kuma ta shiga bani baki da shawara akan da na samu manemi nayi aurena kar dalilin mutuwar wannan in ce ba zan kuma aure ba, Umma ta sako baki tana faɗa mata ai ni da iyayena mun ci buri ba lallai na ƙara yin wani auren ba, don ko yanzu haka anata zuwa wajena ma bana fita Abbaa kuma ya ɗaure min gindi da kansa yake fita ma ya sallami mutum. Ai fa sai Gwaggo Marka ta kama faɗa sosai akan abin da Abbaa yake yi sam bai dace ba, idan shi bai sani ba ai ni suke zubarwa da mutunci, ni dai tana farawa hawaye tuni ya fara suntiri bisa kumatuna wanda na jima ban yi ba, tace na tashi muje can taji daga bakin iyayen nawa mene dalilin hakan kuma mene ribar hakan?
Muka tafi da ita muna zuwa ta komar da faɗan kan Ummani wai wannan ba dacewa ba ne, ashe auren nawa ma sune suka shiga suka fita suka tilastawa mijin nawa ya sake ni. Sai da ƙyar Ummani ta fahimtar da ita shi ne fa ta sassauta murya kuma ta dafa kafaɗata ta shiga lallashina.
Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare da iyayena, ina aiki ina sana'ata ya fiye min wani aure, tuni na cire sha'awar aure a raina da tunani duk wani ɗa namiji. Sai ta kama ce min ai zancen hakan ma bai taso ba domin akwai lokacin da zan zo da kaina ma ina buƙatar in yi auren, don haka gwara nayi abuna tun da ƙuruciyata ba sai lokaci ya ƙure min ba, amma ita zata fi so ma ace na komawa tsohon mijina idan an sasanta akan na kuma wani auren daban, a cewarta gwara na komawa wanda na riga na saba da shi na san halinsa, na ce Gwaggo Marka ba za ki gane rayuwar da nayi a gidan Nazifi ba ne shiyasa kike batun sasanci.
Ni dai haka na baro ɗakin Ummani ina ta faman hawaye, ban ji daɗin fama min ciwon da Gwaggo Marka tayi ba, tuntuni na haƙa rami na binne Nazifi da duk wani abu da ya dangace shi amma shi ne yanzu take min maganar wani wai na koma masa, ai abun da ma ba zai yiwu ba kenan da waninsa ma ballanta shi. To a ƴan kwanakin da Gwaggo Marka tayi a gidan sai naji duk gidan ya ishe ni na gaji, ba don komai ba sai don takurawar da tayi min akan maganar aure yanda kasan auren nawa ya shekara dubu da mutuwa, na rasa irin wasu mutanen da kambaba abu, ta matsawa Abbaa ma akan lallai sai ya ƙyale ni na fara sauraron zaurawan da ke ta suntirin zuwa gurina, shi kuwa yace ai zaɓin a wurina yake idan ina so ai zan sanar da su da hankalina kuma na san inda ke min ciwo, sai ce tayi a'a ai har yanzu ni yarinya ce da ƙuruciyata dudu shekaruna nawa suke, kuma kar ya manta mace ma sai ta shekara arba'in take fara tunani irin na ɗan shekara bakwai. Duk haushinta ya tuƙe ni na ƙosa ta tafi ta bar mana gida, ga shi kome tace sai Kaka ya ara ya yafa dama ƙanwarsa ce, ranar ina jin Abbaa na yiwa Ummani ƙorafin shima ya fara gajiya da maganarta sai kace ita ke ciyar da ni ko kuma ina zaune ne akanta, Ummani tace yay haƙuri kwana nawa ne ma ya rage ta tafi ana gama bikin Hindatu ne.
Ni kuwa dalilin haka sai na tattara kayana na tafi gidan Yashaik, tun da ba dama ayi sallama ace Sa'ida tazo zata ce da yaro jeka kace tana zuwa, kuma ba yanda na iya dole sai na je. Sai da daddare ne Yashaik na ta zuba idon yaga na fito na tafi Maman Yasmin take faɗa masa dalili yace to shikenan ai babu komai, har yake tsokanata yana cewa shima dai akwai wani ogansu a wajen aiki yace zai zo mu sasanta amma tsoho ne don zai yi shekara 70 sai dai akwai dukiya.
Maman Yasmin ta kama cewa,"Allah ya kiyaye ya suttura can yaje wani wajen".
"To ya idan ita kuma tana so fa?". Nayi saurin cewa,"Bana so ma Yashaik".
Yaro ne yay sallama da cewa wai Sa'ida ta zo a waje, kaina na ƙasa na kama mamaki tunda dai ai Ummani ce kawai ta san ina nan, Abbaa kuwa wai ba zai zo yace masa yazo nan ba, to ko Gwaggo Marka ga sani ne? Yashaik ya dube ni yaga ban kai hankalina wurin ba tamkar ba sunana aka shigo aka ambata ba. Ya lura dai da gaske na ƙi jinin Maza yanzu.
Sai naji yana cewa da ni,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?".
Na girgiza masa kai da cewa,"A'a".
Hannunsa ya tsame a cikin kwanon abincin da yake ci. Maman Yasmin ta zuba masa ruwa ya wanke hannu yasa hularsa ya fita. Daga ya leƙa yaga waye kuma shiru bai dawo ba har aka yi isha'i, muka yi sallah muka wuce ɗaki.
Maman Yasmin ta shigo tana cewa da ni,"Sa'ida kin ga Abban Yasmin shiru tun fitar da yay".
Na ɗago kai ina barin linke kayan yaran da na ke yi na ce,"To ko kiran wayarsa za ki yi".
Tace,"Ai kinga wayar tasa nan ya barta, ko kuma can gida ya wuce, Amma dai da can ɗin ya tafi sai ya fara shigowa ya faɗa min, kinga ba sabonsa ba ne kaiwa haka a waje".
Tashi nayi na sanya hijabina na ce,"Bara na leƙa mu gani".
Ina fita ƙofar gida naga ba ya nan, sai na tsallaka wajen masu kankanar ƙofar gidan ina tambayarsu ko sunga wucewasa sai yake shaida min yaga sun fita shi da wani a machine. Ban koma ba na wuce gida, naje ma Ummani ta kama min faɗan na fito da daddare, na ce to ya zanyi naje gidan mata mijinta ya fita a dalilina muma shiru bai dawo ba, tace to shi ɗin yaro ne da za'a kama wani cigiyarsa.
Sai tace ba zan koma na lallamata ta bar ni na fice Abbaa ma bai san naje ba. Na koma na faɗawa Maman Yasmin ɗin tana dai falo ta kasa zaune, kawai sai na tuna nima haka na ke fa idan ya fiata ya jima bai dawo ba, kai na girgiza na koma ɗaki na barta anan a raina ina cewa duk inda yake ma ai zai dawo. Shiru shiru kuma har sha ɗaya da kusan rabi Yashaik bai dawo ba, munyi jugum jugum lokacin don sinitin Maman Yasmin ya hana ni bacci har sai da naji inama ban zo gidan ba.
Can muka ji ƙarar adaidata sahu a ƙofar gida, haka muka yi rige rigen fita ni da ita, yacca ya ganmu hankula tashe sai ya kama dariya yana cewa muyi haƙuri, to yanayin da muka gansa cikin farin ciki sai hankalinmu ya kwanta amma duk mun ƙosa muji ina yaje.
Nan na bar su shi da Maman Yasmin na shiga ɗaki. Washe gari da safe na gama shiryawa zan wuce makaranta sai Yashaik ya kira ni, na zauna gabansa yake faɗa min jiya ai Nazifi ne ya zo wajensa. Gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba na ɗago ido ina kallonsa da jiran jin ƙarashen zancensa.
Kuma lokaci ɗaya na tafi tunanin kwana biyu kenan da muka haɗu da Nazifi ina kan hanyar dawowata daga kasuwar rimi naje na siyowa Ummani kayan zoɓo. Ni na fara ganinsa a cikin mota na zo tsallakowa titin layinmu ashe shima ya ganni, ya fito daga motarsa ya biyo ni ta cikin layin da na shigo ina ta sauri ƙafata har harɗewa take yi kamar zan faɗi.
Ya sha gabana yanda naga idanuwansa sai na rikice a raina haka kawai naji ko shaye shaye ya fara yi, ni dai tsoro duk ya cika ni na ture shi daga gabana ina cewa ya bani hanya, sai ya ruƙo hijabina yana faɗin na tsaya na saurare shi ba abin da na ke tunani ba ne ya kawo shi wurina.
Ni dai duk a hargiste na ke ban san me yasa ganin nasa ya ɗaga hankalina ba na ke jin kamar irin ƴan iskan mazan nan ne suka biyo ni, haka na tsaya ina ta sauke numfashi ya kawo hannu zai taɓa fuskata na bige hannun nasa ina faɗa masa cewar kar ya soma wannan gangancin idan ba haka ba zan masa ihu na tara masa jama'a. Na faɗa masa hakan ina faman huci wanda shi kansa sai da yay mamakin yanayin nawa.
Nace ya bani hanya na wuce sai ya kama faɗin wai dama zai gaya min ne Iyam tana asibiti watanta guda a kwance babu yanda take, yanzu haka ma anata cuku cukun fitar da ita ne za'a yi mata aiki wai ƙashin kwankwasonta ne ya samu matsala. Kaina a ƙasa na ce,"To ni mene nawa a ciki?".
"Ba za kije ki dubata ba?". "Bisa wacca alaƙar da ke tsakani?". "Tsohuwar matar ɗanta mana, kuma surukarta".
Na galla masa harara zan wuce shi don magana da shi ma ɓata lokaci ne a wajena na lura bai da hankali. Sai kawai ya kama cewa,"Sa'ida na zazzo gida Babanki yaƙi saurarena, kuma ya hana ni na ganki, dama so na ke mu zauna ni da ke muyi magana ki sanar musu cewa kina so a mayar da aurenmu, ina so ki dawo gidana ko saboda Iyam Sa'ida, na miki alƙawarin babu abin da zai ke haɗa ni da ke kiyi rayuwarki irin wadda kike so, ba zan takura miki ba, ba zan ci zarafinki ba, kawai ni dai ina so ne ki bawa Iyam irin kulawarki".
"Amma dai baka da hankali da isassan tunani ko, kai wanne irin daƙiƙi ne da ka kasa lissafin rayuwa tsakanina da kai ta ƙare". Nayi maganar cikin doka tsawa ina zare idanu kamar wadda ta fita hayyacinta.
Sai ya shiga takowa zai matso gabana na kuma waro manyan idanuwana ina dakatar da shi da faɗin,"Na rantse da Allah inci ɗaya ka ƙara tsakaninmu sai na ɗauke fuskarka da gigitaccen mari, kuma ka fita a rayuwata kar ka ƙara nuna ka sanni ko tsautsayi ya kawo ka ƙofar gidanmu".
Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faɗin,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faɗa min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki".
Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi".
Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki".
Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?".
Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau.
Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya.
Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faɗa masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje".
Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...".
Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan".
Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan".
Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?.... [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR21FT5* Cikin kwanaki jikin Iyam ya tsananta ta zama babu yanda take, kullum suna kan hanyar asibiti, ta koma gidan jiya bata iya komai sai dai ayi mata, daga kwanciya sai kishingiɗe, dama ga jikin tsufa idan ka ganta sai ta mugun baka tausayi, ƴaƴanta ma da suka shiga damuwa duk sun rame musamman Nazifi don ko a baya ma da bai da kuɗi shi ne komai akan ciwon nata, wannan dalilin yasa dole Malam ya haƙura ta koma gidansa. A hakan ma saboda irin magiyar da Nazifi ya dinga masa da ba shi haƙuri, har da haɗa shi da wani amininsa da Malam ke jin nauyinsa, du dai sai da akayi ta fama da shi don sai da ƴan uwa suka shiga maganar, yace shi idan suka takura shi ma sai ya sallameta, lokacin da ta tafi ta tare a gidan ɗan nata ai nuna masa tayi bai isa da ita ba, ta mayar da shi kamar babu aurenta akansa, har faɗa masa take ita ya ƙyaleta, don haka in har zata dawo cikin gidan to shi zai tattara sauran iyalansa su sauya matsuguni tunda dama ba shi ya gina gidan ba, da hakan dai aka ta basa haƙuri ana faman lallashi sai da ƙyar ya sakko ya yarda aka mayar da ita can.
Barinta gidan Nazifin kuma ba ƙaramin daɗi ya yiwa Zahra'u ba, dama sam bata son zamanta a gidan tun ma Sa'ida na gidan, lokacin kawai kirsa ce irin tata don ta samu fada a wajen Nazifi shiyasa bata fito da ɓoyayyan halinta ba akan uwarsa da ƴan uwansa. Yanzu gidan ya zama daga ita sai ƴan uwanta, ƴan uwan Nazifi duk basa tunkarar gidan, waɗanda ba su san meke faruwa ba ma idan suka je basa marmarin ƙara komawa domin ba a yi musu tarba ta mutunci, duk wanda yaje sai ta wulaƙanta shi, yanzu haka kaf dangi baki ya ɗauka Nazifi bai yi sa'ar matar aure ba, babu wanda bai zaginta a cikin danginsa, ko hidima ce ta tashi bata zuwa, in ba yay mata da gaske ba a hakan ma idan taje to a tsaitsaye kallon raini da wulaƙanci zata je ta dawo, wai ƙyanƙyaminsu take bata son shiga cikin ƴan ƙauye.
Gaba ɗaya yanzu Nazifi jinsa yake wani empty, ba shi da natsuwa kwata kwata, ko wurin aiki ya fita hankalinsa na kan mahaifiyarsa, idan ya dawo wurin aiki ma can gidan yake tafiya ba ya dawowa gida sai wajen sha ɗaya, dalilin hakan kusan kullum sai sun yi rigima da Zahra'u waccca ke ƙorafin yana tauye mata hakkinta, ai itama tana da hakkin lokacinsa ba wai ya tattara duka lokacinsa wa mahaifiyarsa kaɗai ba, ga ƴarsa nan har ta fara yi masa ƙiwa.
Wani sa'ilin har fargabar dawowa gida yake yi, ba don komai ba sai saboda masifarta da fitinarta, nema take ta hana shi kwanciyar hankali sam. Kuma ba ya bi ta kan fitinartata domin abin da ya ishe shi shine ya ishe shi, shi kaɗai yasan a halin da yake ciki, idan yana biye mata zata kai su ga haifar ɗa mara ido, a hakan ma don ya tsaya a tsaye ne ya zama namiji a gidansa, yana tsawatar mata kuma tana ɗan shakkarsa idan ya rikiɗe mata, da rainasa ɗin da zata yi tamkar yaronta haka zata mayar da shi. Yanzu ba damar ya zauna waje ɗaya sai ya fara tunanin shi fa da Zahra'u akwai ƙauna me ƙarfi da fahimtar juna tsakaninsu, sai dai bai san me ya lalata alaƙar soyayyarsu ta mata da miji ba, ko kafin aurensu irin yanda take kautatawa ƴan uwansa Allah ne kawai zai biyata, amma yanzu ya rasa me ya canjata lokaci ɗaya, daga ina haka canjin hali da ɗabi'a? Nuna masa take tamkar ita ke aurensa, hakama can gidan su gani suke yi tamkar ai alfarma suka masa suka ba shi ƴarsu, tun da ko ranar da ta kaiwa mahaifinta ƙararsa sai da ubanta yaci masa mutuncin da kare ba zai shinshina ba, har wai yana faɗin ai ƴarsa tana da freedom don haka ya barta tayi duk abin da taga dama a cikin gidan aurenta, kuma dama lokacin da zai aureta ba su yi yarjejeniyar zata yi zaman bautawa mahaifiyarsa ba, saboda haka kar ya ɗorawa ƴarsa wahalar da ba zata iya ba.
Uzuri yay musu domin kuwa zuri'arsu na da ƙarancin ilmin addini, kwata kwata basa martaba aure sai suke nunawa ƴaƴansu ai mijinsu ma bai isa da su ba, kuma ubansu ne jagoran nuna musu yin rashin mutuncin da suka ga dama a gidan aure, shi sai dai ƴarsa ta mulki gidanta ba mijinta ba, da ƴarsa ta ɗan yi complain sai ya kira mijinta ya kama cin mutuncinsa yana faɗa masa bai kai ba, bai kuma isa ba, idan zai iya zama da ƴarsa a yacca ta tsara zaman rayuwar gidanta to ya zauna da ita, kuma babu me sakar masa yarinya ta zama bazawara in har ka auri ƴaƴansa ka aura kenan. To balle dama ita Zahra'u a gidan na su duk ita ce ilimin addini bai wadace ta ba sam, tafi ƙarfi a boko da koyarwar arna rabin rayuwarta duk a ƙasar turai tayi.
Fitowarsa kenan a wanka, bakin madubi ya ƙarasa yana goge sumar kansa da towel, ta cikin madubi yana bin ɗakin da ido, ɗakin kaca kaca babu gyara, kan kujera ma wankin kayansa ne na kwana huɗu da ya cire bata ɗauke su ba kuma ta da niyyar ɗaukewar. Zuciyarsa ta ƙuntata sosai, zai iya rantsewa ɗakinsa yafi sati bai ga tsintsiya ba, ƙamshi kuwa idan ba na jikinsa ba ko na jikinta to ba zai iya tuna rabon da ayi ma ɗakin turare ba, shi abun ma ɗaure kansa yake yi, bai taɓa tunanin mace na sauyawa har haka ba, abun Zahra'u yay yawa kuma ya fara isar sa.
Ransa duk a dagule ya gama shirinsa cikin sky blue ɗin boyel, zagewa yay da kansa ya gyara ɗakin yay fes fes, abun sai ya masa bambarakwai namiji da suna hajara, wai shi ne da da gyara ɗaki yau, rabonsa da hakan tun samartaka. Yana gamawa ya kulle ya fita zuwa ɗakinta, kwance ya sameta tana baccin asarar da ta saba da yake yau weekend babu aiki, ya kai hannu yana tashinta, ta jisa ba wai bata jisa ba ya sani, amma idan zai awa guda yana tashin nata ba fa zata motsa ba balle ta buɗe ido ta san yana yi. Yau kam bata isa yay mata yanda ya saba ba na zaman jiranta har lokacin da ta ga damar tashi, don haka ya buɗe toilet ya ɗebo ruwa yana zuwa ya fetsa mata a fuska, ta tashi a firgice tana faɗi,"Mene haka? Akan me zaka watsa min ruwa? Idan na tashi ɗin me zan baka ne?". Ta faɗa cikin masifa da hargagi.
"Amma ai na faɗa miki tun da sassafe ki shirya zamu tafi asibiti, shi ne za ki zo ki nemi wuri ki kwanta ke da bacci ba ya taɓa isarki, dun kin bi kin zama malalaciya ɗakin mijinki ma ba zaki iya tsaftace shi ba".
Wani kallo ta watsa masa tare da cewa,"Na dai fi ƙarfin ka ce min ƙazama, ɗakinka kuma ba ce kayi baka so ƴan aiki suke gyara maka ba, ni kuwa na faɗa maka ba zan iya stressing kaina da aiki ba, da wanne zan ji ga aikin office ga na gida, kai ko tausaywa mutum baka yi, idan kaga ba zaka iya zama da ɗakin naka a haka ma ka gyara da kanka mana".