Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 17

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 17

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 17: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 17. Ta faɗi hakan tana neman komawa ta kwanta ya dakatar da ita,"Ke…

4,440 words

Ta faɗi hakan tana neman komawa ta kwanta ya dakatar da ita,"Ke dalla malama mene hakan wai, zaman jiranki zan ta yi sai lokacin da kika ga damar shiryawa tukunna".

"To wai Nazifi idan na sakko nayi maka mene don Allah, me zai kaimu asibiti alhalin lafiyata ƙalau kaima lafiyarka ƙalau haka ma ƴarmu lafiyarta ƙalau".

"Amma ai na faɗa miki cewar yau da asuba an kwantar da Iyam ko, ke kwata kwata ba ki san abin da ya dace ba, me yasa kika zama mara mutunci ne, na ki iyayen kawai ke da daraja da ƙima a wurinki nawa kuma kin raina su kin mayar da su mutanen banza".

"Ni dai kar ka ce zaka zagi mahaifana, kuma kar ka ƙara ce min ban da mutunci, asibiti ne ba zanje ba a yanzu kayi tafiyarka kawai, idan na tashi na biyo bayanka, ni kenan kullum ina kan hanyar asibiti zaman jinyar suruka".

Tayi maganar tana komawa ta kwanta. "Ke ba fa zai yiwu ba, na rantse da Allah Zahra'u idan ba ki sakko kin shirya mun tafi ba in ranki yay dubu sai ya ɓaci, Me kika mayar da ni ne, sakaran miji shashasha wanda sai yadda matarsa tayi da shi, to wallahi ba zan ci gaba da ɗaukar halin iskancinkin nan ba, ni ke aurenki saboda haka dole ki bi umarni na kuma ya zamar miki dole ki girmama min iyaye, yanda sauran matan ƴan uwana ke zuwa su zauna a asibiti tare da mahaifiyarmu haka kema, ki sakko ki shirya mu tafi"

Yay maganar cikin tsawa da ɗaga murya na gaske, wanda har sai da ita kanta ta tsorata da yanayin da ya ke neman rikiɗe mata. Tana ƙunƙuni ta sakko a gadon ta shiga toilet wai sai ta sake yin wanka du dai don ta ɓata masa lokaci. Shi kuma ya fita yana ɗaga kiran waya. Bayan kusan minti goma sha biyar ya leƙo tsammaninsa ta gama shiryawa sai gani yay a sannan ne ma take wa Iman wanka, gajeran tsaki yay na takaici kafin yace da ita,"Kuma na ce ki bani ATM ko".

Tayi kamar bata jisa ba sai da ya ƙara yin magana tukunna tace,"Wai wanne ATM?".

"Ban sani ba, ke dalla na gaji da rainin hankalinki, zan tambaye ki ATM ɗinki ne uban me zan a shi".

"Amma ai na faɗa maka babu ko sisi a ciki ko, duk na kwashe kuɗin na siya mata kadarori, dama kaima ai ba naka ba ne na ƴaƴana ne to mene kuma abin zuwa ka dinga takura min da cewa na baka. To ni duk na siya musu kadarori don babu amfanin aje kuɗin kawai ana zuba musu ido, kuma ni ATM ɗin ma tuni ya ɓata nayi duban duk ban gansa ba, sai blocking nayi".

"To me ya hana kiyi shawara da ni kafin yanke hukuncin hakan, ko ƴar taki ce ke ɗaya".

Shiru tayi masa taƙi cewa komai. Sai da ta gama shiryawa tukunna ya sake ce mata. "To ki tura min kuɗin da na saka a ciki jiya don da sune za'ai amfanin asibitin Iyam".

Ta buɗe baki da cewa,"Amma to Daddyn Iman baka faɗa min ba tun lokacin da ka tura, ai ni suna shigowa na turawa Mami su nace a siyawa Iman zoben gwal, naga ba account ɗinka ba ne ban tsammaci kuɗinka ka saka ba".

Kallon ba ki da hankali yay mata kamin yace,"Zoben gwal? Da duka miliyan ɗayan? Zahra'u wai me yasa ba ki san ciwon kuɗi ba ne, ba fa zuwa na ke na tsinko kuɗin nan ba, ko tsinkowar na ke ai da wahala, akan wanne dalili za ki siyawa ƙaramar yarinya zoben gwal mene fa'idar hakan, anya kina da hankali kuwa, kuma ban faɗa miki cewa na samu matsalar account ba sai naje nayi babban gyara".

Ta ɓata fuska tana mitar. "Ni don Allah Daddyn Iman ka daina yawan min faɗa akan irin haka, mecece miliyan ɗaya a wurinka Allah na tuba, cikin dukiyarka aka taɓa miliyan ɗaya me aka cira, amma a kwanakin nan sai wasu abubuwa ka ke yi akan kuɗi kamar wanda bai da su".

Ƙugu ya kama da hannu ɗaya yana jijjiga ƙafa, ya fara zirga zirga ya rasa me ke masa daɗi. Ita dai tsayawa tayi tana kallonsa kafin tace,"Wai lafiya?".

Nunfashi ya sauke me nauyi yace,"Wuce muje".

Gaba tayi yana biye da ita a baya, har suka shiga mota bai daina mita ba akan kuɗin da ta taɓa, da yacca take ɓarnatar masa da dukiya saboda bata san zafin nemansu ba. Earpice tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da faɗan da yake ta mata tunda suka taho, kuma ba zata iya ci gaba da jin maganarsa da yake na zata basa takardun filayen da duk tace ta siya ai ba hauka ake a iya waɗanda ya mallaka musu ma ya ishe su, ko kuma ta basa na Noor tun da ita ta mutu.

Har dai suka je asibitin bata ƙara ce masa kanzil ba tun bayan ce masa da tayi Daddyn Iman ka koyi son kuɗi yanzu ko baka da shi sai haka.

Zuwansu aka fara bari a shiga ɗakin da Iyam ke kwance, Zahra'u ya bari ya tafi can office ɗin likita shi da Yaya Babba da Yayan Shago. Su Yaya duk suna nan zaune bakin ƙofa an zabga tagumi, Zahra'u ta miƙe ta shiga ciki, babu wanda ta kula a cikinsu tun da ta zo, Jamila matar Yaya Babba ma da tayi mata magana shareta tayi.

"Ina wuni". Iyam na kallonta cikin wahalar ciwo tace,"Lafiya lau Zahra'u, kuna nan lafiya".

"Lafiya lau, sannu Allah sawwaƙe". "Amin na gode Allah yayi muku albarka". Tana maganar ne tana kallon Iman da Zahra'u kewa wasa tana ta ɓaɓɓaka dariya.

Nazifi ya shigo bayan sun gaisa ya shiga tambayarta yanayin yanda take jin jikin, yana kuma faɗa mata yanda suka yi da likitocin akan wataƙila sai an fita da ita waje acan za'a yi mata aikin ƙashin kwankwasonta, bai dai san yanda zai mata bayanin kuɗin da ake nema ba don duk wanda zai faɗawa cewa bai da adadin kuɗin da aka nema sai an ƙaryata shi. Sai yay jugum da ka gansa dai ka san yana da tarin damuwa a tare da shi wadda ke neman fin ƙarfinsa, Iyam ta lura da hakan ta tambaye shi ko wata matsalar ce yace ciwon nata ne kawai damuwarsa.

Sam Zahra'u ƙin zama tayi a asibitin, shi kuma yace wallahi bata isa ta bisa ba tunda bata da mutuncin da zata iya zama a asibiti wurin mahaifiyarsa, saboda haka yana fita itama ta fito yana bakin titi yaga ta tari napep ta hau. Abun duniya duk ya ishe shi, jikinsa har wani ɗumi yay kamar me zazzaɓi. Ya rasa dalilin da yasa cikin ƴan kwanakin nan zuciyarsa ta addabe shi da tuna masa irin azabar da ubangiji ya tanadarwa wanda bai kwatanta adalci ba tsakanin matansa, ya sani ba wai bai sani ba ubangiji ba ya barin mijin da duk ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, jiya har da mummunar mafarki yay da har yau ya kasa gane ma'anarsa balle yasan in da ya dosa da musababbin yinsa.

Kai tsaye gida ya wuce, yana zuwa ɓangaren Malam ya nufa. Sai da ya jima zaune yana jiran Malam ɗin kafin ya fito, bayan sun gaisa ne kansa ƙasa ya rasa ta inda zai fara magana. Malam dai kallonsa kawai yake yay guntun murmushi irin na su na manya yace da shi,"Ka zo ka saka ni gaba, da wani abu ne? Ko jikin mahaifiyar taku ne".

Ƙeya ya ɗan sosa kan yace,"Dama Malam akan waccan maganar da na maka ne kwanakin baya". Yay maganar cikin kame kame.

Malam yace,"Wacce magana kenan, abubuwan da yawa bana iya tunawa ba".

Sai ya ɗago ya kalli mahaifin nasa kaɗan kafin ya kuma sadda kai ƙasa, shi kansa nauyin maganar yake ji to amma babu yanda ya iya haka dole yace,"Amm Amm akan maganar Sa'ida, na maka magana tun kafin ta fita idda sai baka ce komai ba, to yanzu ina so ne na shiga sahun manema aurenta don Allah a shige min gaba".

Malam yay masa wani duba na baka da hankali, so yake ya mayar da shi mutumin banza, tun ba'ai wata biyu da rabuwan auren ba yake ta masa zarya, haka yay ta damunsa da kira shi lallai yana so zai dawo da matarsa. Malam kuwa bai basa fuska ba sam hasalima ranar farko da ya fara yi masa maganar sai da yay masa tatas to da yake ɗan yau ne baka haifi halinsa ba saboda rashin kunya bai fasa masa maganar ba, shi kuwa ko gani yay iyayen Sa'ida ma za su kuma basa ƴarsu ai sai ya hana.

Har da zuwansa wajen Amarya itama zai kama ƙafa da ita ta taya shi shawo kan mahaifin nasa da ike idan tasa baki a magana Malam kan yarda, dan ko cikin matansa ma yafi shawara da ita. To itama dama sam bata ji daɗin rabuwar auren ba, don a lokacin ji tayi da ace ita ta haifi Nazifi babu abin da zai hana bata masa duka ba don bai wuce duka a wurinta ba. Shi yasa ko da yaje mata da zancen komen yana magiyan akan ta roƙa masa Malam tace masa,"Babu ruwana Nazifi ba za ka haɗa ni faɗa da shi ba kuma kaja mahaifiyarka ta zo tana jin haushina, kana dai ganin a irin yanda ku ka rabu da yarinyar nan ni ban ma zaton zaka iya cewa zaka mayar da ita ba, wallahi ce na ke ka shafeta a babin rayuwarka".

Sau biyu yana zuwar mata da ƙoƙon bararsa taga kamar dai duk hankalinsa a tashe yake, sai ta basa shawaran cewa yaje gidan su Sa'idan ya samu mahaifanta ko ita ya nemeta ya bata haƙuri idan ta haƙura shikenan sai su sasanta kansu amma ita ba zata iya saka baki a sha'anin ba, babu ruwanta kar ta zo tayi baƙin jini kuma ya janyo mata faɗan kullum a wurin Malam.

Lokacin jinsa yay tamkar zai hauka, bai san dalilin da yasa tunanin Sa'ida da al'amarinta da shi ba ya addabesa, tun da ya rabu da ita bai yi danasani ba balle nadama, imfact ji ma yake kamar ya rabu da wata ƙaya ne, kuma dama bai san ma shi ba sonta yake ba sai da ya auri Zahra'u, to a yanzu ma da suka rabu ba wai don yana sonta ne zai mayar da ita ba, ba don tausayi ko don ya wulaƙantata ba kamar yanda ya sha alwashi lokacin da aka tilasta masa sakinta, a'a haka kawai zuciyarsa ke faɗa masa cewa ya dawo da ita kamar hakan na da amfani a gare shi, kamar yana da buƙatarta musamman ma idan yaga halin ciwon da mahaifiyarsa ke ciki. Har magana yay da abokinsa Hamisu shima yace bai da shawarar da zai basa ta wannan ɓangaren, bai kuma isa ya tunkari Iyam da zancen ba, su Yaya ma duk ba zasu goyi da bayan hakan ba shiyasa ma babu wacca ya tunkara da maganar a cikin Yayyun nasa, balle yanzu ma da basa wata hulɗa da Yaya gaba suke a tsakaninsu.

Sai daga baya yay amfani da shawaran Amarya yaje gidan su Sa'idan har sau biyu sai dai ya rasa ta yanda zai aika a kirawo masa ita, idan ma ta fito bai san me zai ce mata ya kawo shi wurinta ba. zuwansa na uku ne kuma suka haɗu da Abbaa ya dawo daga masallaci, lokacin Abbaa har ya shiga soro sai ya dawo ganin baƙuwar mota a ƙofar gidan, bai ma san Nazifin ba ne don har ya fito a motar ya durƙusa a gabansa suka gaisa bai ɗauka muryarsa ba.

Kuma hakan sai yasa du ya diririce, Abbaa ma yay zaton ko cikin zawaran da ke zuwa wurin Sa'ida ne sai da yace masa shi ne tukunna Abbaa yace,"Ohh to lafiya, me ya kawo ka gidana?".

Babu kunya kuma yake faɗawa Abbaan abun da ya kawosa wai so yake a basa dama ya shiga cikin manema auren Sa'ida. Abbaa ya dakatar da shi cikin ɗaga murya,"Hala sai da ka maku kafin ka zo ko? Manta irin rashin mutuncin da ka shuka mana kayi ne? Ko saboda wancan lokacin ban ce da kai komai ba shi ne ka samu zarafin dawo min gida saboda baka da ta ido...Ai Kai dai ba zan taɓa mancewa da butulu ba irinka, Nazifi lokacin da ka shigo rayuwar ƴata cikin gata da jin daɗi ka sameta, duk da burin da na ke da shi akanta haka na haƙura lokacin da ka nemi auranta na aura maka ita saboda ina maka kallon ɗana wanda zai kula da rayuwar ƴata ya ingatata, ashe ashe kai ɗin baƙin mijici ne ban sani ba, na baka amanarta ka ɓige da cin zarafinta da wulaƙantata saboda kayi kuɗi, har sai da ta kai ta kawo ka mata ƙazafin kisa ka ɓatata a idon duniya, kuma tsabar ka isa ka zo har gabana ka sakar min ita, sannan yazu saboda kai fitsararre ne ka sake ɗebo ƙafafun rashin kunyarka ka zo wurina kana roƙon na baka damar ka mayar da ita, ai ko a baya abin da ka aikata mata rashin sanar da ni ne da wallahi sai nayi shari'a da kai...Ka saki ƴata kuma kun rabu, ba zan lamunci raini da iskancinka ba wai zaka sake aurenta, to bara na faɗa maka in dai batun mayar da aurenku ne ka bar tunaninsa domin lamari ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, ni ba sakaran uba ba ne da zan ƙara yarda ƴata ta komawa wanda bai san darajarta ba...don haka kayi gaggawar tashi ka bar min ƙofar gida kafin na kira Imam ya fito yay maka dukan saɓa kamanni, ina ga rashin dakuwar shi ya baka lasisin dawowar mara kunyar banza da wofi".

Ya faɗa yana kallonsa cikin fusata. A lokacin gaba ɗaya kasa yin wata magana yay haka ya kasa ɗagowa ya dubi Abbaan, kansa a sunkuye ya miƙe yana jin ƙafafunsa a sanyaye ya koma mota ya bar wajen, duka abin da Abbaa ya faɗa masa bai ji zafi ba kuma bai ji haushinsa ba, sai dai duk yanda zai yi zai yi wajen ganin ya dawo da Sa'ida gidansa.

Malam ya katse tunaninsa da cewa,".... __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA* Halimahz

*LOKACI NE* Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI* Aisha Yabo

*WASA DA RAI* Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5* "Kai ɗago fuskarka ka kalle ni". Ya ɗago yana duban Malam ɗin wanda ke jifansa da mugun kallo.

"Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...".

"Don Allah Malam ayi haƙuri...". "Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai".

Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa. Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar.

Yinin ranar dai gaba ɗaya haka ya wuni sukuku kamar wani mara lafiya. Bai koma gida ba sai sha biyu na dare ya bar asibiti wajen Iyam, lokacin da ya koma Zahra'u ta rufe ko'ina babu yacca bai yi ba akan ta buɗe ƙofar ta ƙi, kuma ba bacci take yi ba idonta biyu, zai kira ta ɗaga sai tace masa ya koma in da ya fito, ransa ya daɗa dagulewa, ga azababbiyar yunwa kamar bai ci abincin rana ba, kuma da zai taho ba yanda Anty Aisha bata yi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace ya ƙoshi domin idan ya zo a ƙoshe wani tashin hankalin ne na daban tsakaninsa da Zahra'u.

Haka dole ya koma mota ba shi da yanda zai yi, ya buɗe baya yay kwanciyarsa. Ko da Asuba ma bata sakko ta buɗe ƙofar ba sai da safe wajen ƙarfe takwas kana, lokacin zata fita wurin aiki ta fito ko kallon wurin da yake bata yi ba, sai da ta shiga mota ta zo daidai wurin tasa kana ta zuge glass tace masa,"Ai yanda ka ɓarar min da aji kasa na hayo motar haya to ka dinƙi kurɓan baƙin ciki a gidan nan, yauma idan kaga dama kar ka dawo da wuri ka kuma zama a can".

Tana ganin ya buɗe motam zai fito tayi sauri bawa motar wuta ta fice. A ciki ya samu ta kuma barin Iman yauma sai tsala uban kuka take, ba yanda bai da ita ba akan take tafiya da yarinyar in yaso ta samu me raino tace sam ita aiki kawai taje yi can ba zata dinga ɗaukan yarinya tana tafiya da ita ba, tama kusa yayeta na gaji da wahalar shayarwa.

Ko wanka bai iya tsayawa yayi ba kitchen ya shiga ya dafa abin da zai ci, kamar ya san bata ajiye masa ba kuwa, bayan ya gama ya ɗora wanda zai tafiwa da su Iyam asibiti, matan ƴan uwansa kowacce ka ganta da coolern abinci amma shi ban da tasa. Bayan ya fito a wanka ya gama shiryawa ya sanya haƙarƙarinsa akan gado, idonsa na kallon sama kana gani ka san cikin harbawar sakan yay zurfi cikin tunani wanda har sai a iya zuwa ma ayi sata a ɗakin bai sani ba.

Ya jima a haka kafin ya fita falo ya karɓo Iman wadda ke hannun Marawiyya tana ta faman lallashinta, ya zo ya zauna yana mata wasa tuni tayi shiru, can kuma sai tayi bacci ya ɗauketa ya kwantar da ita a ƙirjinsa, cikin shirun da yay sai ya tsinci gimlawar tunanin kiran lambar Sa'ida. Wayarsa ya ɗauko yay dialling numbern, tun ranar da ya saketa dama ya goge duk lambobinta da hotunanta, ashe akwai ranar da riƙe lambartata zata yi masa rana. Haka yay ta gwada kiran lambar bata shiga, sai can a koma ce masa a kashe take, ya jijjiga kai kar dai da gaske kamar yanda aka faɗa masa ta sauya layi ne, aje wayar yay a gefe bayan yanke shawarar zuwa yamma zai je gidan na su, ya san Sa'ida mai haƙuri ce da sauƙin kai, tabbas idan ta gansa zata ji tausayinsa kuma zata yi haƙuri ta dawo gidansa, wanda zai matuƙar son hakan ba don komai ba sai saboda Iyam, domin ya san in ace Sa'ida na nan babu dare babu rana tana kan zaryar asibiti babu gajiyawa babu ƙosawa, kuma cikin bawa mahaifiyarsa kulawa da kyautatawa, kuma atleast zai samu sauƙin damuwar da yake ciki a yanzu na wasu al'amura da ke neman cakuɗe masa, saɓanin Zahra'u da bai ma san ta yanda zai fara sanar da ita ba don babu ta yanda zata fahimce shi, batun sake aure ma kuwa tunanin hakan na zuwa kansa ya ke kaudar da shi amma Allah ya gani ya gaji da halin Zahra'u.

****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da na ke koyarwa. Daga gefe na ke ina bitar littafin muwaɗɗa, ku san awa guda su Malama Mastura na aikin hira akan rayuwar zawarci, dama kusan duk Malamai matan mutum uku ne masu aure amma mu shida duk zaurawa ne, duk san da aka zauna ana hira sai naji suna ta faɗin ƙalubalen da suke fuskanta akan zaman zawarci, cikin gidan iyayensu ba sauƙi haka waje ma babu sauƙi, wasu cikinsu ma faɗi suke har gwara su zauna a gidan auren miji yay ta gallaza musu akan dai zaman gidan da suke yi ana tsangwamar su, ranar da Malama Alawiyya ke bamu labari har ƙwalla sai da nayi wai cikin gidansu kullum mahaifinta sai ya kyareta kuma sai ya goranta mata akan ta kashe aure ta dawo gida ta zauna, haka mahaifiyarta ma bata barta ba tayi ta faɗa mata magana komai nata ta hanata taɓawa har ce mata take tana lalata mata carpet saboda kwanciya, basu san buƙatunta ba komai ita kewa kanta da ƴar ƙaramar yarinyarta da ke hannunta, abinci kawai ake bata shima duk sanda za'a bata sai an mata mita, saboda haka ne ta nemi aikin koyarwar to shima mutane nata surutun yawon ta zubar take yi, Babansu kuma na faɗa mata ai ko aikin me zata yi bata dai da daraja a idon duniya.

Hakan sai yay ta bani mamaki kuma sai naji fargaba ta kama ni, a raina sai na ce to ko dan ni mutuwar auren nawa ban jima ba ne shiyasa hakan bata fara faruwa da ni ba, ni ban san wani abu kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, gaskiya idan na buɗi baki na ce nafi jin daɗin gidan aurena akan zaman zawarcina to sai Allah ya kama ni, ƴan unguwa ne ma dai ke ta gulmace gulmacensu, wataran ma idan na dawo haka daga makaranta har na kanji ana ƙusƙus, Abbaa ma ina jinsa ranar suna hira da Ummani yana faɗa mata an fara surutu akaina ƴan unguwa don haka wataƙila zai yarda ne na tafi can school of nursing jigawan tun da ba a samu ta nan kano ɗin ba.

Gaba ɗaya sai na saka damuwa sosai a raina don tunani bai wuce akan masu magana akaina ba, da kuma a zo nan ba da jimawa ba iyayena su fara min maganar aure don wataƙila ganin ban daɗe a gabansu ba ne, amma kuma sai ya kasance ko da yaushe Abbaa nasiha yake min da kwantar da hankali ta yanda damuwa bata da ikon samun muhalli a zuciyata, kuma da hakan na samu natsuwar ruhi da zuciya matuƙa ganin iyayena na tare da ni, Allah har mancewa na ke da wani suna bazawara ji na ke tamkar ban taɓa auren ba. Yayyuna kuwa babu abin da zan ce da su sai Allah ya saka musu da gidan Aljannah ya ƙara musu buɗi, gata dai iya gata da nuna tsantsar kulawa bayin Allahn nan na yi min, duk san da suka shigo gida sa tambaye ni ban dai da wata matsala ko na ce musu ehhh.

Yashaik da kansa ya biya min kuɗin koyon ɗinki tun watarana da ya zo ya samu muna hirar da Ummani, wallahi ba ai sati ba sai kawai ganinsa nayi da form yace na cike anjima na kai gidan Maman Binta, ranar har kukan farin ciki nayi, to yanzu ɗinkuna na ke tayi kuma Allah yasa min nasibi a kaasuwancin. Duk wata kuwa idan aka bani dubu takwas ɗita a islamiyar da na ke koyarwa ba na riƙe ko sisi tawa yaran Yashaik da Yaya Imam na ke wa siyayya, sauran kuma in siyo omo da sabulun wanka da na wanki na aje mana a gida, Abbaa yay ta faɗa wai na ke rike kuɗina ina adanawa ko na ke siyawa kaina abu, ni kuwa banga amfanin kuɗin ba in har ban musu ba, to me ma na ke da buƙata wacca basa min?

Ranar da na taɓa faɗawa su Malama Alawiyya na taɓa aure ƙaryata ni suka yi wai wallahi kwata kwata ban kama da wacca tayi aure ba, kar nayi wasa da damata na amincewa Malam Isah kawai tunda shi ba ƙaramin yaro ba ne da gaske aurena zai yi babu wasa a maganarsa, ni dai kawai nayi murmushi ban ce musu komai ba saboda Allah ɗaya ya san me na aje a zuciyata dangane da aure wanda ya fita gaba ɗaya a raina, ana hakan kuwa watarana sai Malama Aisha ke cewa ashe da gaske ne ni bazawara ce taji a staff room ɗin Malamai maza ana maganar wai Malam Isah yaje neman aurena ance masa na taɓa aure to yanzu ya janye maganarsa don bai san mene dalilin fitowar tawa ba, shi ne har Malam Amiru ke cewa dama baka shaidar mutum ta fuska, amma ƙila ganin ina da ƙuruciya ne yasa na kaso auren na fito ba zai wuce talaka na ke aure ba abun duniya kuma ya rufe min ido.

Maganar ta tsaya min a rai, da na faɗawa Ummani tace ai sai na toshe kunnena akan maganganun mutane. Yau na dawo daga makarantar na samu wata Kakarmu ta zo, ban ma san da zuwan nata ba don har sai da nayi sallar magriba na fito zan ɗauko abincin rana a kitchen Ummani ke ce min idan na gama cin abincin na shiga ɓangaren Baba Tijjani na gaida Gwaggo Marka. Aje abincin na yi na ce bari na fara zuwa mu gaisa, ina zuwa kuwa na sameta cikin jikoki ana ta hira, da murnarta ta tarbe ni muka gaisa, take min jajen mutuwar aurena wanda sai da ta zo yaune ma take ji.

Sai kuma ta shiga bani baki da shawara akan da na samu manemi nayi aurena kar dalilin mutuwar wannan in ce ba zan kuma aure ba, Umma ta sako baki tana faɗa mata ai ni da iyayena mun ci buri ba lallai na ƙara yin wani auren ba, don ko yanzu haka anata zuwa wajena ma bana fita Abbaa kuma ya ɗaure min gindi da kansa yake fita ma ya sallami mutum. Ai fa sai Gwaggo Marka ta kama faɗa sosai akan abin da Abbaa yake yi sam bai dace ba, idan shi bai sani ba ai ni suke zubarwa da mutunci, ni dai tana farawa hawaye tuni ya fara suntiri bisa kumatuna wanda na jima ban yi ba, tace na tashi muje can taji daga bakin iyayen nawa mene dalilin hakan kuma mene ribar hakan?

Muka tafi da ita muna zuwa ta komar da faɗan kan Ummani wai wannan ba dacewa ba ne, ashe auren nawa ma sune suka shiga suka fita suka tilastawa mijin nawa ya sake ni. Sai da ƙyar Ummani ta fahimtar da ita shi ne fa ta sassauta murya kuma ta dafa kafaɗata ta shiga lallashina.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull