Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 18
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 18: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 18. Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare…
4,480 words
Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare da iyayena, ina aiki ina sana'ata ya fiye min wani aure, tuni na cire sha'awar aure a raina da tunani duk wani ɗa namiji. Sai ta kama ce min ai zancen hakan ma bai taso ba domin akwai lokacin da zan zo da kaina ma ina buƙatar in yi auren, don haka gwara nayi abuna tun da ƙuruciyata ba sai lokaci ya ƙure min ba, amma ita zata fi so ma ace na komawa tsohon mijina idan an sasanta akan na kuma wani auren daban, a cewarta gwara na komawa wanda na riga na saba da shi na san halinsa, na ce Gwaggo Marka ba za ki gane rayuwar da nayi a gidan Nazifi ba ne shiyasa kike batun sasanci.
Ni dai haka na baro ɗakin Ummani ina ta faman hawaye, ban ji daɗin fama min ciwon da Gwaggo Marka tayi ba, tuntuni na haƙa rami na binne Nazifi da duk wani abu da ya dangace shi amma shi ne yanzu take min maganar wani wai na koma masa, ai abun da ma ba zai yiwu ba kenan da waninsa ma ballanta shi. To a ƴan kwanakin da Gwaggo Marka tayi a gidan sai naji duk gidan ya ishe ni na gaji, ba don komai ba sai don takurawar da tayi min akan maganar aure yanda kasan auren nawa ya shekara dubu da mutuwa, na rasa irin wasu mutanen da kambaba abu, ta matsawa Abbaa ma akan lallai sai ya ƙyale ni na fara sauraron zaurawan da ke ta suntirin zuwa gurina, shi kuwa yace ai zaɓin a wurina yake idan ina so ai zan sanar da su da hankalina kuma na san inda ke min ciwo, sai ce tayi a'a ai har yanzu ni yarinya ce da ƙuruciyata dudu shekaruna nawa suke, kuma kar ya manta mace ma sai ta shekara arba'in take fara tunani irin na ɗan shekara bakwai. Duk haushinta ya tuƙe ni na ƙosa ta tafi ta bar mana gida, ga shi kome tace sai Kaka ya ara ya yafa dama ƙanwarsa ce, ranar ina jin Abbaa na yiwa Ummani ƙorafin shima ya fara gajiya da maganarta sai kace ita ke ciyar da ni ko kuma ina zaune ne akanta, Ummani tace yay haƙuri kwana nawa ne ma ya rage ta tafi ana gama bikin Hindatu ne.
Ni kuwa dalilin haka sai na tattara kayana na tafi gidan Yashaik, tun da ba dama ayi sallama ace Sa'ida tazo zata ce da yaro jeka kace tana zuwa, kuma ba yanda na iya dole sai na je. Sai da daddare ne Yashaik na ta zuba idon yaga na fito na tafi Maman Yasmin take faɗa masa dalili yace to shikenan ai babu komai, har yake tsokanata yana cewa shima dai akwai wani ogansu a wajen aiki yace zai zo mu sasanta amma tsoho ne don zai yi shekara 70 sai dai akwai dukiya.
Maman Yasmin ta kama cewa,"Allah ya kiyaye ya suttura can yaje wani wajen".
"To ya idan ita kuma tana so fa?". Nayi saurin cewa,"Bana so ma Yashaik".
Yaro ne yay sallama da cewa wai Sa'ida ta zo a waje, kaina na ƙasa na kama mamaki tunda dai ai Ummani ce kawai ta san ina nan, Abbaa kuwa wai ba zai zo yace masa yazo nan ba, to ko Gwaggo Marka ga sani ne? Yashaik ya dube ni yaga ban kai hankalina wurin ba tamkar ba sunana aka shigo aka ambata ba. Ya lura dai da gaske na ƙi jinin Maza yanzu.
Sai naji yana cewa da ni,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?".
Na girgiza masa kai da cewa,"A'a".
Hannunsa ya tsame a cikin kwanon abincin da yake ci. Maman Yasmin ta zuba masa ruwa ya wanke hannu yasa hularsa ya fita. Daga ya leƙa yaga waye kuma shiru bai dawo ba har aka yi isha'i, muka yi sallah muka wuce ɗaki.
Maman Yasmin ta shigo tana cewa da ni,"Sa'ida kin ga Abban Yasmin shiru tun fitar da yay".
Na ɗago kai ina barin linke kayan yaran da na ke yi na ce,"To ko kiran wayarsa za ki yi".
Tace,"Ai kinga wayar tasa nan ya barta, ko kuma can gida ya wuce, Amma dai da can ɗin ya tafi sai ya fara shigowa ya faɗa min, kinga ba sabonsa ba ne kaiwa haka a waje".
Tashi nayi na sanya hijabina na ce,"Bara na leƙa mu gani".
Ina fita ƙofar gida naga ba ya nan, sai na tsallaka wajen masu kankanar ƙofar gidan ina tambayarsu ko sunga wucewasa sai yake shaida min yaga sun fita shi da wani a machine. Ban koma ba na wuce gida, naje ma Ummani ta kama min faɗan na fito da daddare, na ce to ya zanyi naje gidan mata mijinta ya fita a dalilina muma shiru bai dawo ba, tace to shi ɗin yaro ne da za'a kama wani cigiyarsa.
Sai tace ba zan koma na lallamata ta bar ni na fice Abbaa ma bai san naje ba. Na koma na faɗawa Maman Yasmin ɗin tana dai falo ta kasa zaune, kawai sai na tuna nima haka na ke fa idan ya fiata ya jima bai dawo ba, kai na girgiza na koma ɗaki na barta anan a raina ina cewa duk inda yake ma ai zai dawo. Shiru shiru kuma har sha ɗaya da kusan rabi Yashaik bai dawo ba, munyi jugum jugum lokacin don sinitin Maman Yasmin ya hana ni bacci har sai da naji inama ban zo gidan ba.
Can muka ji ƙarar adaidata sahu a ƙofar gida, haka muka yi rige rigen fita ni da ita, yacca ya ganmu hankula tashe sai ya kama dariya yana cewa muyi haƙuri, to yanayin da muka gansa cikin farin ciki sai hankalinmu ya kwanta amma duk mun ƙosa muji ina yaje.
Nan na bar su shi da Maman Yasmin na shiga ɗaki. Washe gari da safe na gama shiryawa zan wuce makaranta sai Yashaik ya kira ni, na zauna gabansa yake faɗa min jiya ai Nazifi ne ya zo wajensa. Gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba na ɗago ido ina kallonsa da jiran jin ƙarashen zancensa.
Kuma lokaci ɗaya na tafi tunanin kwana biyu kenan da muka haɗu da Nazifi ina kan hanyar dawowata daga kasuwar rimi naje na siyowa Ummani kayan zoɓo. Ni na fara ganinsa a cikin mota na zo tsallakowa titin layinmu ashe shima ya ganni, ya fito daga motarsa ya biyo ni ta cikin layin da na shigo ina ta sauri ƙafata har harɗewa take yi kamar zan faɗi.
Ya sha gabana yanda naga idanuwansa sai na rikice a raina haka kawai naji ko shaye shaye ya fara yi, ni dai tsoro duk ya cika ni na ture shi daga gabana ina cewa ya bani hanya, sai ya ruƙo hijabina yana faɗin na tsaya na saurare shi ba abin da na ke tunani ba ne ya kawo shi wurina.
Ni dai duk a hargiste na ke ban san me yasa ganin nasa ya ɗaga hankalina ba na ke jin kamar irin ƴan iskan mazan nan ne suka biyo ni, haka na tsaya ina ta sauke numfashi ya kawo hannu zai taɓa fuskata na bige hannun nasa ina faɗa masa cewar kar ya soma wannan gangancin idan ba haka ba zan masa ihu na tara masa jama'a. Na faɗa masa hakan ina faman huci wanda shi kansa sai da yay mamakin yanayin nawa.
Nace ya bani hanya na wuce sai ya kama faɗin wai dama zai gaya min ne Iyam tana asibiti watanta guda a kwance babu yanda take, yanzu haka ma anata cuku cukun fitar da ita ne za'a yi mata aiki wai ƙashin kwankwasonta ne ya samu matsala. Kaina a ƙasa na ce,"To ni mene nawa a ciki?".
"Ba za kije ki dubata ba?". "Bisa wacca alaƙar da ke tsakani?". "Tsohuwar matar ɗanta mana, kuma surukarta".
Na galla masa harara zan wuce shi don magana da shi ma ɓata lokaci ne a wajena na lura bai da hankali. Sai kawai ya kama cewa,"Sa'ida na zazzo gida Babanki yaƙi saurarena, kuma ya hana ni na ganki, dama so na ke mu zauna ni da ke muyi magana ki sanar musu cewa kina so a mayar da aurenmu, ina so ki dawo gidana ko saboda Iyam Sa'ida, na miki alƙawarin babu abin da zai ke haɗa ni da ke kiyi rayuwarki irin wadda kike so, ba zan takura miki ba, ba zan ci zarafinki ba, kawai ni dai ina so ne ki bawa Iyam irin kulawarki".
"Amma dai baka da hankali da isassan tunani ko, kai wanne irin daƙiƙi ne da ka kasa lissafin rayuwa tsakanina da kai ta ƙare". Nayi maganar cikin doka tsawa ina zare idanu kamar wadda ta fita hayyacinta.
Sai ya shiga takowa zai matso gabana na kuma waro manyan idanuwana ina dakatar da shi da faɗin,"Na rantse da Allah inci ɗaya ka ƙara tsakaninmu sai na ɗauke fuskarka da gigitaccen mari, kuma ka fita a rayuwata kar ka ƙara nuna ka sanni ko tsautsayi ya kawo ka ƙofar gidanmu".
Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faɗin,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faɗa min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki".
Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi".
Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki".
Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?".
Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau.
Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya.
Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faɗa masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje".
Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...".
Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan".
Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan".
Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?.... *B2ƘR23FT5* Yashaik ya katse gajeran tunanin da na tafi akan wanda ya zama silar wannan babban tagomashin da na samu. Yes na yarda Allah ne ya ba ni to amma ta dalilin wa? Tun farko fara kalaminsa na cewa wani ne yaje gida ba a sansa ba Safiyya ce kawai ta faɗo raina, sai dai kuma anya Safiyya zata yi suprising ɗina ta haka? In har ita ce to lallai asubar fari zata kira ni don tana da wutar ciki, duk da suprise ne zata kasa haƙuri sai ta kira ni ta tona kanta.
Maman Yasmin dai sai murna take yi baki yaƙi rufuwa, hannu ta ɗaga sama kawai tana godiya ga Allah, Yashaik yace,"Autarmu ba ki farin ciki ne?".
Nayi figigit na ɗaga ido ina dubansa da fuskata wacca murmushi ya wanzuwa a samanta. "Ina farin ciki sosai Yashaik, kawai dai na rasa ta yanda zan kwatanta murnata, ban san yama zan yi ba, abun da ban taɓa tsammani ba ne Yashaik".
Sai kawai hawaye ya sakko min bisa kuncina, hawayen farin ciki masu sanyi da sanyaya zuciya. "Yashaik amma ka faɗa min gaskiya wane yay min hanyar samun admission ɗin nan? Ni dai ku na ke kawowa a raina kai da Yaya Imam domin kune ku ka dage akan lamarin karatuna, wanda ko da yaushe cikin shige da ficen yanda za'ai na samu gurbin karatu kuke yi. Na kasa yarda da cewar dalilin wani daban da bamu da haɗi da shi na samu, ku ɗin ne dai Yashaik domin kune jigona".
Ya murmusa da cewa,"Kin san idan mune kai tsaye ba zan tsaya ja miki rai ba zan faɗa miki gaskiya, amma na san idan kika ji daga bakin Abbaa za ki fi gasgatawa, yanzu dai ta shi ki wuce kar ki makara".
Kai na girgiza cikin wani irin yanayi na nuna tsantsar farin ciki da jin daɗi na ce,"Yashaik makarantar yau kuma ai ta mutu, da ma voluntry ne saboda haka suyi haƙuri".
Na faɗa ina miƙewa nayi ƙofa, Maman Yasmin tace,"Ehh lallai ne sannu hamshaƙiya, ki kwanar min a gida ba za ki min aiki ba za ki wuce, to dawo ki min wanke wanke, ni babu ruwana da wata Auta". Ta faɗa da sigar tsokana, ni dai ina dariya kawai na fice don Alla Alla na ke na ganni cikin gidanmu, don na tabbatar ba mafarki na ke yi ba.
A soro na samu Abbaa ya fito zai wuce kasuwa shi da Yaya Imam wanda ke riƙe da ledar kayan Abbaa da yake fita da ita. Kawai a lokacin sai naji tamkar na rungume Abbana, amma duk da haka na kasa controlling kaina na faɗa jikin mahaifin nawa kunya tattare da ni, yayin da naji wani irin abu ya tsarga min a dukka ilahirin jikina, tabbas na sani ƙaunarsa ce, soyayyarsa ce, tausayinsa ne. Shima muryarsa na bayyana amon tsananin farin ciki naji ya ɗora hannunsa saman kaina yace,"Ko ranar ɗaurin aurenki ban ga farin ciki da murna irin haka a tare da ke ba Likitata".
A kunyace na zame jikina ina durƙusawa na gaida shi. Ya amsa min as usual yana saka min albarka, Yaya Imam ma na gaida shi. Sai Abbaa yace,"Lafiya ba ki tafi makarantar ba?".
"Abbaa ai ba zan iya zuwa ba ne yau, dama ina ta cewa Allah yasa baka fita kasuwa ba, Abbaa Yashaik ne yake faɗa min wata magana da na kasa gama yarda da ita sai naji daga bakinka duk da shima na san ba zai min wasa ba".
Yace,"Yanzu muke zancen na ki ai da Babarki, dama ina ce sai kin dawo daga makarantar ne, muje to cikin, sai kika ga rabo daga Allah ko?".
Yanda ƙarashen zancen nasa ya fita da wani irin emotion sai naji idona ya cika da ƙwalla, ni kuwa wanne irin rashin kyautawa na yiwa Abbaana, ashe haka na hana shi farin ciki, ƙwarai ba zan yafema kaina ba tun da har na zaɓi farin cikin Nazifi fiye da na Abbaana, kuma Allah ya isa tsakanina da shi da ya riƙe min hakkina na kuɗin makarantata da Abbaa ya bani ya hana ni, ai dama ba kyauta na ce na basa ba, idan da ya bani hakkina da yanzu wata maganar ake a karatuna, amma babu komai ga shi Allah yay min sauyi mafi alkhairi.
Muna shiga ciki na samu Ummani na wanke wanke, tana ganina sai naga itama fuskarta cike da annurin da ya wadatu da farin cikin da ba zai misaltu ba. Na faɗa jikinta ina cewa,"Wai duk ya na ganku cikin farin ciki, kar dai da gaske ba mafarki na ke ba".
Ta tsame hannunta cikin ruwan kumfa tana cewa,"Ai ko mafarkin ne yi adu'a ya zama tabbatace Sa'ida, wannan Al'amari ba zamu so ya tsaya iyaka mafarki ba, jiya ni da mahaifinki kasa runtsawa muka yi saboda farin ciki, wallahi ido biyu muka kwana muna ta adu'a don gani muke kamar mafarki ne ko kuma saƙe saƙen zuci ne da ba'a rabo da shi tun da an saka lamarin karatun na ki a rai".
Buɗar bakina zan magana Yaya Imam ya zunguro ni ganin Zainab ƴar wajen Baba Tijjani ta taho. Muka yi shiru dukanmu ba don komai ba sai don dai ka san irin mutanen da kake tare da su dole ya yi takatsantsan. Muka shiga ɗakin Abbaa, ina maƙale jikin Ummani Abbaa ya kira sunana da cewa,"Sa'ida kinga lamarin ubangiji ko, wallahi yanda ake ta kai komo a karatun nan na ki shiru har na fidda rai na ce ƙila ba ki da rabo, ƙila Allah bai rubuta burina zai cika akan karatunki ba, ashe tuni Allah ya amsa adu'a, lokaci ne kawai zamu jira kuma ga shi ya zo, Allah Allah yasa alkhairi ne".
Duka muka amsa da amin yayin da na ce,"To Abbaa wai shi wanda ya kawo takardun waye?".
Abbaa yace,"Wallahi ban san shi ba Sa'ida, don kansa ma a ƙasa ni ba zan iya shaida shi ba, ga mahaifiyarki nan da na karɓo envelop ɗin na dawo wullar da shi nayi ce na ke irin shashashun samarin nan ne masu aiken wasiƙa, sai ta dage akan cewar a dai duba a gani, shi ne fa da Sa'id ya shigo na ce ya duba ya gani sai yake cewa ai wai takardun makarantarki ne. Na ce ina ai ba zai yiwu haka kawai bamu san mutum ba ya zo ya kawo takarda yace wai ya samar miki makaranta, mu ai ba iyayen banza da wofi ba ne, to sai kuma ga wani ɗan kati a jiki ya ɗauka ya kira lambar sai wanda ya ɗaga wayar yake cewa shi ko menene wani abu dai dareta ne ko?".
Ni da Yaya Imam muna gajeriyar dariya muka ce,"Ehh Abbaa director".
Yace,"Yauwa to dai shi, yay mana bayani yace wani bawan Allah ne da ya saba ɗaukar nauyin karatun ƴan makaranta sai aka haɗa da sunanki a list ɗin, shi Sa'id ma ce yay yana zargin wani mutum da suka taɓa haɗuwa acan makarantar da yaje dubo miki jarabawar intiro ɗin da kika yi...to dai ina ba ki labari shi dareta ɗin sai da muka kusa faɗa da shi saura kaɗan yay zuciya yace an cire sunanki saboda na takura shi da tambaya ina cewa ya faɗa min tsakani da Allah ba cutarmu za su yi ba".
Abbaa yay maganar yana dariya, muma duk dariyar muka yi, yace,"Yo Allah kuwa magana ta tsakani da Allah, yanda duniyar nan ta zama babu gaskiya da amana sai a zo a yaudaremu a cucemu saboda anga abin da muke so kenan mun ƙwallafa rai akan samu, shiyasa ni kuwa nayi ta jefa masa tambayoyi ina yaji tsoron tsayuwa a gaban Allah, ke har da wa'azizzika na dinga masa ƙarshe shima sai ya sakko yana dariya, yace bai ga laifina ba duniyar ce ta lalace. To dai kinga ai sai muka samu fahimtar juna yay min bayanai sosai da na gamsu amma duk da hakan dai na sa Yayyunki su ƙara bincike akai".
Na ce,"Abbaa ai ni da tunanina ma Suprise ɗin Safiyya ne, dama adu'a bata fi ƙarfin komai ba ina ta faɗawa Allah ya bani ta wata hanyar, sai ga shi ma Abbaa an ɗauke maka ɗawainiyar komai karatu kawai zan yi Abbaa".
Haƙoran gabansa tass a waje yace,"To Sa'ida ko da ba'a ɗauke min ko sisi ba ai in har an ba ki gurbin karatun an gama yi min komai, ba ni da shi, ban tara ba, ban bawa wani ajiya ba, amma kuma Allah ne mai yi, ba zai hana ni ba, zai hore min na yi miki duk wata hidima da ta shafi karatunki Sa'ida, ni dai fatana Allah yasa ki fara a sa'a kema na ganki cikin kayan asibiti kina taimakon al'umma musamman talakawa, kuma ina roƙon Allah ya bani tsawon rai naga wannan lokaci, ke kuma yasa miki albarka a karatun. Sa'ida bana mancewa lokacin da za'a haifi Imam irin rashin rashin kirkin da malaman asibiti suka mana akan babu kuɗin magani da alluran da za'a siya, don Allah Sa'ida ki zama me taimakawa ba mai wulaƙantawa ba, kar kuɗi su rufe miki ido ki kasa taimakon al'ummar Annabi".
Na sa hannu ina goge hawayena na ce,"In sha Allahu Abbaa, na maka alƙawari Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana, na gode na gode sosai Allah yay muku sakayya da gidan aljannah, ina son ku wallahi ina sonku Allah yasa kuci moriyar ɗawainiyar da ku ka yi akaina".
Ummani tace,"To mora kuma na nawa Sa'ida, ai mu babu abin da zamu ce da ubangiji sai godiya da ya bamu ƴaƴa masu jin ƙan mu da tausayinmu, ke ma ƴar sana'ar da kike yi da ɗan albashin da ake baki ba ga shi nan ba yaushe rabon da mu sayi sabulu da omo da kuɗinmu, ai Alhamdulillahi Allah ya ƙara buɗa muku ya sawa nemanku albarka".
Abbaa yace,"To yanzu ina kika zaɓa can ƙasar turawan ko kuwa nan dai in dai muka fi kauri".
Kafin na ce wani abu Ummani ta riga ni da cewa,"A'a fa Abbaansu na faɗa maka ta dai yi karatunta anan, ni bana son wannan nisan, ina zamu turata ƙasar waje tana mace a'a tayi a gabanmu ta gama har Allah ya kawo mata mijin aure, ni dai ka ma cire batun bata wani zaɓi na in da take so".
Abbaa yace,"To anji ta bakinki Hajiya Sa'a Babar Sa'ida". Sai ya maida dubansa garen yace,"Ina jinki ƴar albarka ina kike so? Baturiyar za ki koma ko kuwa dai kasar ki ta gado garin hausawa".
Ina wasa da yatsun hannuna na ce,"Abbaa ni ai na bar muku zaɓin duk inda ku ka ce nan zan je, zaɓinku shi ne nawa".
Sai Abbaa ya dubi Yaya Imam ya ce,"Imamu me ka ce? Kun san abin da kuka ce akan karatun nan shi ne, tunda kun fi mu sanin lamuran yanda suke, jiyan Sa'id yace aji ta bakinta tukunna".
Yaya Imam yana kallon Ummani yace,"Ehh ya kira ni ai a daren jiyan muka yi magana, ni da ce nayi ai ba aure ba ne da za'a bata zaɓi, inda muka ga yafi a turata can ɗin kawai. to yanzu tunda ta baku zaɓi kawai ka yanke magana Abbaa, zaka fi mu hange da zurfin nazari".
Abbaa yay shiru na ƴan daƙiƙa, ya numfasa kafin yace,"To da muka dawo daga masallacin asuba na yiwa ƴan uwana maganar, mun tattauna da su akai na faɗa musu duk yanda aka yi kun san sha'ani irin wannan abun da zai je ya dawo ake ji ba wani abu ba. To shi Babanku Tijjani yace idan za'a bi shawaransa a barta ta tafi can ƙasar wajen saboda samun ingancin karatun, namu da na su ba ɗaya ba ne. To Amma ya kuke gani Imam taje can ɗin ko nan ɗin?".
Yaya Imam yace,"Ke ki faɗa da kan ki, can ɗin ko nan?".
Nayi shiru, Abbaa ya numfasa kafin yace,"To ni dai har ga Allah sallar da nayi a jiya ta istikara zuciyata tafi samun natsuwa da fitar taki Sa'ida, kuma dama zaɓin Allah shi muke nema, ni na yarda da ke na kuma yarda da irin tarbiyar da na baki, sannan na yarda da Allah ne me kiyayewa da karewa, wayonmu ko dabararmu ba su zasu mana ba, adu'a ce muna miki kuma ba zamu fasa ba, Allah zai tsare mana ke sannan kema kuma ki tsare mutuncinki. Naga ƴaƴa mata da yawa da suka fita karatun nan suka yi lafiya suka gama lafiya, ni dai roƙona a gare ki kiyi abin da ya kai ki Sa'ida, ba yinmu ba ne yin Allah ne, kuma ya dubemu ne ya dubi kyakykyawar niyayyarmu ta manufarmu akan karatunki, ki taimaka min Sa'ida kar ki bani kunya, kin dai gani irin yanda ƴan uwanki suke ta fafutukar nema miki ta gwamnati ma ba'a samu ba, amma Allah da ikonsa sai ya ba ki rabo a inda bamu taɓa tunani da kai kanmu can ba don sun fi ƙarfinmu, ko ba ƙasar waje za ki fita ba Sa'ida ko anan za ki zauna nasihar dai duka ɗaya ce, idan kika kiyaye sai Allah ma ya kiyaye ki, kin dai sani kaf danginmu babu me ɗaukarki ya kai ki wannan makaranta me tsada ta ɗururuwan kuɗaɗe, to amma da ke abun na Allah ne muna zaune sai ga shi ya kawo miki. Allah yay miki albarka, Allah ya lulluɓe rayuwarki da kariyarsa, ya ba ki sa'a da nasara a karatun nan da za ki fara".
Dukanmu muka amsa da amin, ni dai gaba ɗaya jikina ya mutu. Sai kuma Abbaa ya sake cewa,"Amma kar ki yi maganar da kowa tukunna ki bari sai tafiyar ta kankama, sha'anin rayuwar nan kake ji baka sanin zuciyar wamda kake tare da shi, wani yana nan bai son ci gabanka amma a fuska yana nuna maka ya fi kowa sonka, to ki bar abun da ke sai ahalinki duk wanda za ki faɗawa ki jira zuwa ranar tafiyarki sai ki kira waya kuyi sallama cikin aminci...nan da sati na sama naji ko?".
Na buɗe takardun na miƙawa Yaya Imam ya duba yace,"Ehh litinin ta sama kenan ban da wannan me zuwan".
"To yanzu me da me ya kamata a siya mata, kuma wanne shirye shirye zata yi?".
Yaya Imam yace,"Ai ina ga abun da zata tafi da su ba zai wuce kayan sawarta ba, idan ma da wani abu dai in taje can ɗin ta kira waya ko kuɗi ne sai a tura mata".