Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 19
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 19: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 19. Kawai sai naji jikina yay sanyi, na fara tunain yanzu idan na…
4,444 words
Kawai sai naji jikina yay sanyi, na fara tunain yanzu idan na tafi sai fa na shekara uku kamar yanda na ke gani rubuce a jikin takardar. Anya ba zan fasa tafiya can ɗin ba duk da nima dama nafi so ta fita ɗin, to amma ya zan yi Abbaa har istikara yayi zaɓin Allah kuma ya nema, Allah yasa zuwana can ɗin babban alheri ne.
Yashaik ya zo Abbaa ya jaddada masa akan kar ya manta yaje can Emorate ɗin yaga Director ɗin ido da ido sannan yay bincike sosai akan lamarin. Ina komawa ɗaki na ɗauka wayana na kira Safiyya, bacci take yi a lokacin amma jin albashiri ɗin da na zo mata tuni ta warsteka tana cewa,"Ke ba na son wasa da feelings ena".
Nace,"Wallahi Tallahi da gaske nake yi miki".
Wani ihu tayi tana faɗin,"Wow what a great news Beb, admission a germany kuma nursing wow Beb am so happy for you wallahi, wanda yay miki silar nan ubangiji Allah ya haɗa shi da dukkan alkhairan duniya, ina ma zan gasa na masa kyauta. Yanzu yaushe ne ake batun za ku tafi don naji wata cousin ena ma na maganar tafiya can?".
"Sati na sama Beb, amma dai za ki zo kafin na tafi ko?".
Shiru ta ɗanyi kafin tace,"Da wuya na zo nigeria cikin week ɗin nan, kin ganmu muna Saudiya mun je Umrah jiya muka tafi, amma kar ki damu kina makaranta zan kawo miki visiting".
"To ƙawar arziki Allah ya amince sai na ganki, ki faɗawa Umma ma kin ji".
Da yake dai Safiyyar tawa sai a hankali sai ce ta min,"Ke wacce Umman mun yi faɗa da ita fa ba ma magana, ki kirawota da kan ki".
Kai na girgiza na ce,"Allah ya shirya min ke wallahi, yanzu da Umman ku ka yi faɗa?".
"ƙwarai aure ma zan zuga mijinta ya ƙara, ba dai ganin bata da kishiya ba ne yasa duk take takura min akan sai nayi aure ba, ki ji fa jiya tutsiye ni tayi wai lallai sai na bata lambar My ta kirawo shi ya zo anyi maganar aure".
"To mene abin laifi a ciki Beb, ai da gaskiyanta ke fa da kanki kin faɗa min yanda kike ta shan surutu a family na ku akan kin ƙi aure, kuma kin ga idan ke ba kya damuwa ita Umma dole zata damu, burin kowanne fa iyaye ne su ga sun aurar da ƴarsu wallahi hankalinsu yafi kwanciya".
Daga yanda naji tayi shiru na san jina kawai take, ma'ana in gama mu ɗora da wani zancen. "Kika min shiru".
"Ina jin ki ai, ni an faɗa miki irinki ce da maganar mutane ke damuna, wanda ya fasa cewa nayi kwantai yaci uwatas, idan mutum shi ke ci da ni ko a makwamcinsa na ke kwana duk ya ƙwace...ni na faɗa mata ta toshe kunne daga duk abin da zata ji, aure lokaci ne idan ya zo duk ƙina da shi fa sai nayi kamar mutuwa yake, ni dai kawai a min adu'a don wallahi tun a kanki na ke tsoron maza Sa'ida, Nazifi ya girgiza duniyata, amma ɗan bantan uba ai very soon zan girbe abubuwan da ya shuka, Allah ubangiji ya kawosa gabanki yana kuka".
Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Sai na kwantar da murya ina mata nasiha ina bata shawara akan dai ta tsaya ta fidda mijin auren shi yafi, tun da tana da masoya masu sonta tsakani da Allah, kuma tayi karatun nan har ma tana da aikin yi to me ya rage mata kuma? Fitar nan da take tayi a har business ɗinta sai surutu ake akai to baka san bakin wani ba.
Mun daɗe muna wayar da ita kafin muka yi sallama bayan ta haɗa ni da Ummaa a confrence call, wallahi Safiyya ƙawar ƙwarai ce muna gama wayar sai ga alert ɗin 30 tayi min wai gudunmawarta na tafiya makaranta. To cikin satin gaba ɗaya sai na zama cikin shire shirye, Abbaa kuwa kace zai min sabon aure sai faman siyo min atamfofi yake da shadda yana cewa na ɗinka abina duk da ba masu tsada ba ne, sai yace wai dai idan naje can aga ƴarsa fes fes da ita. haka Yaya Imam ma da yake yanzu turaruka yake saidawa da kayan kwalliya ya kwaso min kaya ni duk sai na ke jina ma kamar nafi kowacce mace gata da samun dacewar family, Yashaik kuwa shi ne da siyo bandir ɗin littafai da biro da ɗinko min hijabai.
Hajiya Ummani kuwa ina gefe ina mata dariya, ta jidi uban shinkafa kusan rabin buhu tasa aka yo taliya ƴar murji kwano biyar wai na tafiyata, har da su ɗauko tsohon risho da muka daina amfani da shi tun da kalanzir yay tsada, ta wanke shi tass ta saka a bakko leda. sai da Yaya Al'amin yace mata ai duk ba'a tafiya da su tun da ni cikin hostel zan zauna ba gida zan kama ba, ko su man abinci ma duk ba'a tafiya da su, yaji ne da maggi kawai, sai ta siyar da shinkafar dama da cuku cuku ta haɗa kuɗin ta siya, ta aika kuɗin ƙauye a auno mata barkono kwano goma za'ai farin yaji da na daddawa, ni dai dariya kawai na ke yi, a gefe guda kuma ina ta jin tausayin iyayen nawa, ba damar suji kuɗi hannunsu sai su ce na tambayo me ake tafiya da shi a siya min, Ummani da taji kuɗi hannu sai ta ban tace sauri je ki rimi su ba ki haɗin maggi, haka ta daka min maggi kusan toba biyar irin manyan nan na zuba spices.
Ana saura kwana uku tafiyar tamu Abbaa yace na shirya naje ƙauye muyi sallama da ƴan uwa na can, tare da shi muka je muka yini acan sai dare muka dawo, wallahi ranar duk sai naji tamkar sallamar ƙarshe na ke da mutane. Ana gobe zan tafi na jajje gidan ƴan uwanmu na amana suma na musu sallama, maƙota ma duk na shishshigaa su duk tare ma muka shiga da Ummani, kowa muka je sai ya tayani murna yay min adu'a.
Da daddare ina ɗaki kwance na gama haɗa komai nawa nayi lamo ina ta tunani daban daban, sai naji ƙwala kiran Yaya Imam, na fito na same shi ya miƙo min leda baƙa babba, na buɗe naga takalma ne masu kyau da ƙarko guda huɗu ya siyo min, na gwada duk suka min nayi ta masa godiya har da ƙwallata. Bayan sun yi sallama da su Ummani zai wuce gida yace min,"Goben kin ga ƙarfe bakwai suka je jirginku zai tashi, don Allah sai ki daure ki kammala koma daren yau da kin yi asuba ki fito da kayan ki, na yiwa wani me adaidaita maƙocinmu magana daga masallaci zamuyo nan ko gida ba zan shigo ba".
Na ce,"To Yaya". "Kar fa sai mun zo ki dinƙa tsaye tsaye".
Da haka ya fita. Ummani tace,"To tun da haka ne kinga shiga kiwa mutanen gidan sallama ba'a zo ana tashin su da sanyin asuba ba".
Wucewa nayi ƙafafuna a matuƙar sanyaye, na fara shiga ɓangaren Baba Sabi'u na jima a can shi da Umman su Hindatu suna ta min nasiha, wacca ta ƙara sanyawa jikina ya mutu duk nayi la'asar, kafin na fito na tafi ɓangaren Baba Tijjani, nan dai Baban ne yay min faɗansa da nasihohinsa, Umma kuwa kyaɓe baki tayi kawai tace Allah sa ayi abin da aka je yi, ƴaƴanta kuwa babu wanda yace min ci kan ki, saɓanin ƴaƴan Baba Sabitu da naga ƙauna cikinsu har da masu kuka.
Kaka ma a daren muka yi sallama da shi, daren dai ni ban wani runtsa ba, kamar yanda zan ce Abbaa da Ummani ma duk basu runtsa ba don ina jiyo sautin maganarsu cikin dare sanda na fita alwala. Da asuba ana idar da sallar asuba Abbaa ko shigowa gida bai ba sai ga adaidai na horn a ƙofar gida, cikin sauri kuwa na fita gudun mita irin ta Yaya Imam, Yaya Al'amin ya bani wani agogo yace amma idan na tashi dawowa na taho masa da na ƴan gayu nace an gama Yayana, lokacin Abbayo ya kira waya shima muka yi sallama da yake ya koma can Ibadan ɗin tuni.
A ƙofar gida muka tsaya sai da muka jira Abbaa ya dawo wai ya tsaya ne ayi sadaƙa. Haka muka ɗunguma muka tafi airpot, Yaya Imam a adaidaitar da Kayana suke, ɗayar da Yashaik ya aro kuma shi ke tuƙa mu da ni da Ummani da Abbaa da Yaya Al'amin, Ummani dai tun da muka taho take ta matse hawaye, nima kuma kukan bai zo min ba sai da muka je aripot ɗin.
Duk ƙin tafiya suka har aka gama clearing ɗinmu, lokacin da aka kiramu na tashi kenan sai naji wayata tayi ƙara ina dubawa naga an turo min saƙo ta gmail ɗina daga wani banki wai suna taya ni murnar buɗe doller account da su. na aje mamakina a gefe na tafi wurin ahalina muna sallama, nan kuka ya ƙwac e min sosai har da su majina, da ƙyar na iya juyawa na bar wajen shima sai da naji ana ta sanarwar nan da mintu biyu jirgi zai tashi, Abbaa yace,"Sa'ida je ki Allah yay miki albarka ya tsare hanya, kina sauka ki kiramu ɗin kin ji, Imam yay miki canjin kuɗi yace suna ƙaramar jakar da Babarki ta baki babu yawa dai duba ashirin ne daga baya in sha Allah za'a karo miki, Allah yasa ki dawo ina da tsawancin kwana".
Ƙafafuna naji suna neman kasa ɗaukata su tafi da ni, saƙo ya kuma shigowa wayata, cikin gudu gudu saurin tafiyar da nake na duba sai naga saƙo daga wata lamba ta ƙasar waje, cikin harshen turanci da cewa. _"Safe flight, Allah ya tsare hanya, a maida hankali a karatu first class muke so, a kula don Allah, amanar kanki"._
Har na shiga cikin jirgi ina murmushi don na san bani da wani me min messge irin haka sama da ƙawata Safiyya, sosai na ƙara jin sonta da ƙara ƙudurin kyautata mata idan har Allah ya ida nufi burina ya cika. Awan mu shida zan ce keman a jirgi muka sauka a ƙasar Germany, lokacin da na fito daga jirgin na kalla garin na shaƙi iskar sai naji tamkar komai mafarki ne, Allah kenan, ko da wasa, ko a tunani ban taɓa haskowa kaina zuwa irin wajen nan ba. Hatta tsohon mijina da yay kuɗin bai taɓa lissafin cewa zai kai ni saudiya ba ma, dama ita kawai na ke da burin ace yau na hau jirgi na ziyarci ɗakin Allah na kuma kai ziyara ƙabarin manzona. Kawai sai naji sabbin hawaye sun sauka a kuncina, ba na baƙin ciki ba ne ko damuwa ko kewar ahalina, a'a kawai ji nayi nasa rai da rabon zuwa makkah, kuma ina ji a jikina nan kusa ubangiji zai kira ni.
Muna zaune ka wasu kujeru mu da muka zazzo daga nigeria ƴan makarantar, sai ga wani farin mutum dogo gashinsa kamar na larabawa, ya duba ƙaramin katin hannunsa yana tambaya wacece Sa'ida Salman Madobi, sai na ce masa gani yace an ce ya zo ɗaukana ne, sai na dubi sauran ƴan uwan tafiyar tawa, na ce su taso mu tafi sai yace ai ni kaɗai ɗin dai. Kamar ba zan tafi ba duba da cewar ya za'ai mun zo tare kuma duk makaranta ɗaya can zamu nufa ya zaman ni kaɗai ace an zo ɗaukana, sai wani Saurayi cikinmu yake cewa naje kawai ai ba wata matsala ba ce. Nace to nan na nunawa mutumin kayana, ya kwasa sai rawar jiki yake yana kirana da Madam, yana saka kayan a both ɗin mota zai haɗa da wata green ɗin jaka sai nace masa ba tawa ba ce, sai yace min a'a tawa ce an ba shi ya taho min da ita, amma gata ma na riƙe a hannuna.
Na karɓa na shiga motar da adu'ata, duk na ƙosa na samu sarari na siya sim na kira gida na sanar musu mun sauka, ai ko ina cikin wannan tunanin sai drivern ya juyo yana bani layin waya yace na saka, na karɓa na saka da murnata ina ta masa godiya kuwa, ni dai a tsammanina tun da ya bani ai ƙila kyauta ne ake rabawa ɗalibai. Ba'ai minti biyar ba da ɗora layin naga shigowar saƙo da cewar,_"Fatan an sauka lafiya, Allah ya bada abin da aka zo nema"._
Wani sanyayyan murmushi na yi a fili na furta,"Zan kira ki ƙawata, ina son ki Allah ya bar mu tare".
Wayar na aje gefe na buɗe green ɗin jakar da na ke ta tantamar tawa ce, sai dai ina buɗewa mamaki ya kamani matuƙa da uban kuɗin da na gani a ciki wanda aka rubuta Euro a jiki, sai na ɗauko kai zan wa drivern magana na ce masa wannan ba tawa ba ce, sai maganar ta maƙale dalilin shigowar wani cikin motar wanda ya zauna a gaba, kansa da p-cap fara kansa a ƙasa ya kuma sanya face mask.
Gabana naji ya yanke ya faɗi ba tare da sanin dalili ba, ina aikin zare ido naji an jefo min abu jikina, ɗaga idon da zan yi na duba sai naga face maske ce, Drivern kuma sai ya katse tunanin da na ke da cewa,"Madam kisa face mask saboda zamu tsaya ne a shopping mall makaranta ta ba da umarnin haka".
Fuskata a ɗaure na ke duban drivern, so na ke nayi magana to amma ina tsoro tun da ba hausa zan yi masa ba, kar nayi turancin nayi kwaɓa, to amma haka dole na dage na tattaro guntun turancina na ce masa,"Shi baƙon da ka ɗauka bai san darajar ɗan Adam ba ne da zai wurgo min abu jiki, ko ba zai ba ni da hannu ba ai sai yace na ɗauka".
Sai ya kama ba ni haƙuri, ni kuwa duk da haka naƙi ɗauka sai ma cilli da nayi da shi gefe, muka iso bakin wani babban mall motar tayi parking, motar ma bata gama tsayuwa ba na gaban ya fita cikin sauri ya shiga mall ɗin, ahi kuma drivern yace na fito na shiga ciki duk abin da na gani na ke na ɗauko makaranta ta riga ta biya kuɗin.
Na fito ina jin ƙafafuna na harɗewa, haka na tsaya kusan minti biyu ina ƙarewa wajen haɗaɗɗan mall ɗin kallo kafin a hankali nayi bismillah na fara takawa. Ina hawa kan step na biyu na duba saƙon da ya shigo wayata wanda ke cewa _"Mace me daraja bata yawo a ƙasar sai da face mask, ki ke rufe fuskarki kin ji"._ Murmushi nayi kawai na juya motar na ɗauko face mask ɗin yayin da na ke bin bayan kiran lambar Safiyya. ____________________________ ₦500 07018098175.
*B2ƘR24FT5* Nazifi ne zaune a ƙasa kan carpet, gefensa mug ne da ruwan tea a ciki wanda yaji haɗin kayan ƙamshin shayi yake kurɓa a hankali a hankali, yayin da laptop ke kan cinyarsa sai takardu a gafen hannun hagunsa duk a barbarje. Wayarsa da ta yi ƙara ya dakatar da danne dannen da yake cikin laptop ɗin, ya ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa yace.
"Wallahi kuwa ka ganni na kusa minti ashirin akanta na dai kasa fahimta, amma kuma na yi ƙoƙarin shigar da wancan document ɗin na dukka bayanan kamfanin, na samu Madam tayi min aikinsa, shi wannan ɗin ne dai na ke so zuwa anjima idan na fito sai ka duba kuma ka koya min saboda gaba ko".
Daga can ɓangaren aka yi magana kafin shi kuma ya ƙara cewa,"Oak oak tom shikenan babu matsala duk yanda ka gani ɗin dai zai yiwu, tun da ni ba sanin harkar na yi ba kuma na yarda da kai ɗari bisa ɗari, na san ba zaka jefa ni hanyar da zan cutu ba. Amma kamar nawa ka ke ganin zasu iya ba ni bashin?".
Shiru na ƴan sakanni yace,"Biliyan ɗaya! amma Alhaji Sunusi kana ganin zan iya requesting hakan kuwa? Basu yi yawa ba? Ka san yanda sha'anin kasuwancin yake duk ya taɓarɓare kar azo in karɓi kuɗi masu uban yawa ba fata ba azo a samu matsala".
Ya kuma yin shiru na kusan minti uku yana sauraron na cikin wayar kamin yace,"Ehh ai shi ne abun dubawar da na ke faɗa maka. Ka san girman Allah Alhaji Sunusi kwata kwata ba zan ce maka ga ta inda nayi asarar waɗancan kuɗin ba, duk buge bugen lissafi da bincike wallahi na rasa ina miliyan ɗari da hamsin ta shiga, to amma ka san kowanne bawa Allah na jarabtarsa, na bar hakan matsayin ƙaddara sai adu'an Allah ya mayar min da alkhairi, ƙila wani mugun abun ne ma yake shirin faruwa da ni sai Allah ya kare hakan lamarin ya sauka akan dukiyata".
Ya ƙara yin shiru sannan yace,"Amin ya Hayyu ya Qayyum, kaga har yanzu wallahi cikin iyalina da iyayena babu wanda na faɗawa, bab na so su shiga damuwa, ni kaina haka dai ina rayuwa ne kawai, tunda ka san duk wata ɗawainiya ta ahalina akaina yake, ƙannena da kowa nawa da ni suka dogara, idan suka ji cewan na rasa komai nawa zasu shiga tashin hankali...Amma dai mahaifina zan sanar da shi a yau ɓoyewan bai da amfani, muna da su a raye dole mu buƙaci adu'arsu, ta hakan Allah zai ɓullo da mafita. Yanzu ka nemi waɗanda zaku yi maganar sayan waccan plazar ta Kabuga, ka san ita kaɗai ta rage min dama, a ciki na ke so na fitar da kuɗin da za'ai wa mahaifiyata aiki sauran kuma kaga sai a wari wani abun da ko shago ne a buɗe kafin su banki su bamu aron kuɗin sai a tayar da kamfanin shinkafar".
"Yauwa na gode fa, ina godiya sosai da sosai Alhaji Sunusi, Allah ya bar zumunci. A gaida iyalin".
Daga haka wayar tasa ta ƙare ya ajiyeta gefen gado, laptop ɗin ya kashe kana ya shiga tattara takardun gabansa yana shirya su. Sai bayan ya gama ne ya ɗauki wayarsa ya danna lambar Yaya, ta ɗaga yake tambayarta sauƙin jikin Iyam tace masa kamar dai kullum don yauma ko buɗe ido bata yi ba, yanzu ma take shirin ta kira shi sun jisa shiru yau bai leƙo ba.
Da muryan bayyana tarin damuwa yace mata,"Na ɗa tashi ne da uzuri amma jimawa kaɗan zan leƙo, ko da Iyam ɗin zata farka ta tambaye ni kya ce mata lafiya lau ba wani matsala aiki ne ya ɗan tsare ni".
Yayan tace,"To shikenan".
"Jiyan da ta farka ta samu taci abinci kuwa?".
Yaya da ke kusa da Iyam tace,"Wallahi bata ci ba, ta dai ce tana son ferfesun kifi to kuma kaga dare yayi a lokacin, ka ma fa san likita ɗazu da ya zo ce yay sai an saka mata robar abinci".
Ya furta kalmar innalillahi yana jin wani gumi na tsatstafo masa, duniyar gaba ɗayanta yaji ta ƙara yi masa nauyi aka. a sanyaye yace,"Allah ubangiji ya kawo mata sauƙin da ba za'a kai ga hakan ba, yanzu bara na kira Lubabatu sai na tura mata kuɗi tayo cefane ayi mata ferfesun, ƙila idan ta farka ɗin ta samu ci, yanzu ma dai zan gaggauta na taho".
Tace,"To shikenan. amma ya ku ke ciki da maganar iyayen Zahra'un?".
Ya sauke numfashi kana yace,"Yaya lamarin na su dai sai haƙuri, amma ni na faɗa musu ina kan bakana babu wanda ya isa ya raba ni da abin da Allah ya bani".
Itama ta numfasa murya a hankali tace,"To Allah ya kyauta, amma lamarin nasu akwai son zuciya da rashin addini, yanzu dai kai zaka ta iya bakin ƙoƙarin ka shawo kan matarka kasan mu mata akwai daru idan lamari irin haka ya tashi, sai an ta faman lallashi tukunna".
Ya shafi kansa da cewa,"Ai Yaya Zahra'u ma gaba ɗaya bata jin wani rarrashi wallahi, shiyasa na faɗa mata idan ta gaji ne to ta faɗa min kawai na sawwaƙe mata, ni ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, rabona da samun kwanciyar hankali a cikin gidan nan wallahi Yaya har na manta, idan na tuna ma abin da na miki kan sharrin da tayi miki kar kiji yanda raina ke sosuwa".
Yaya tace,"Allah ya kyauta wancan kuma ai ya wuce, hannunka bai taɓa ruɓewa ka yar, ciki guda muka fito kuma na fika hankali da shekaru da sanin yakamata, kaga ni ba zan bari zumuncinmu ya taɓu ba.... Yauwa jiya muna magana ma cajin wayar tawa ya ƙare sai yanzu zancen ya faɗo min, Kai Nazifi me ya shiga cikin kanka har kake tunanin dawo da Sa'ida gidanka?".
Yay shiru bai ce komai ba. Ta sake cewa,"Magana na ke maka, kai kace kana neman shawara ko ba haka ba".
Ya murza goshinsa kuma haka kawai sai yaji wani abu ya motsa a ƙirjinsa kan yace,"Kawai dai Yaya na ji ne ina so na dawo da ita ba tare da sanin dalili ba".
"To wallahi ka sauya tunani ka yiwa kanka faɗa, me ya kai ka? Allah ya rabaka da ƙaya kuma ka ke neman sake janyowa kanka masifa, yo masifa mana zama da wadda bata haihuwa duk da Allah ya baka me haifa maka yanzu, to ni dai in har na kai na baka shawara ka cire tunanin dawo da ita, in ba haka bayan kashe maka ƴa da tayi ta dawo wannan karan zata ƙarasa kashe maka mahaifiya ne kaima kuma ta kassaraka ta barka gaya, don ba zaka yi aune ba zata kwashe duka dukiyarka tun da dai bata haihu ba".
"Tom shikenan Yaya, dama daɗin shawarar kenan, ni ban yi wannan tunanin ba. sai na shigo asibitin".
Suna gama wayar ya kwantar da kansa jikin filo yana kallon saman ɗakin, zuciyarsa cunkushe take yana ta aikin tunanin yanda zai samu mafita, mafita akan abubuwa da yawa da suka tsaya masa yanzu ciki kuwa har da son dawo da Sa'ida, ita ɗin kuma hr yanzu ya kasa gane dalilinsa na so ya dawo da ita gidansa, duk da cewa da yaje yana faɗawa Yayan Shago cewa ya taimaka ya shige masa gaba kan shawo kan iyayen Sa'ida ta dawo gidansa, Kai taye Yayan Shago yace shi kam ba da shi ba, ai dama ba'a sanin darajar abu sai an rasa shi, ya kasa gane Sa'idan na da muhimmanci a wurinsa sai yanzu ne saboda bai da kunya bayan duk irin wulaƙancin da yay mata sannan zai ce zai dawo da ita.
Iska ya furzar me zafi daga bakinsa ya sauka akan gadon, wadrobe ya buɗe ya shiga kwaso tsaffin kayansa da zai bayar, wadrobe ɗin duk tayi kaca kaca sai tashin tsamin jiki da na turare da ya haɗe wuri ɗaya, ya girgiza kana saboda takaici da ya maƙure shi, ko da wasa Sa'ida bata taɓa haɗa kayan da ya cire da wankakku, kuma idan kaya sun isa a ɗauka a bayar da kanta zata ɗauko tace Hubbi wannan sun isa a bayar kafin su ƙarasa mutuwa, amma zai iya cewa bai taɓa ganin hannun Zahra'u a cikin wadrobe ɗinsa ba da sunan gyara masa kaya ko ɗakkowa tun bayan da ta gama na marmarin amarci.
Yana cikin haɗa kayan ne kuma ya tuna da kiran Lubabatu da zai yi, cikin hanzari ya ajiye kayan hannunsa ya ɗauko wayarsa ya kirata, ya sanar mata cewa zai tura mata dubu huɗu tayi sauri ta siyo kifi tayi ferfesunsa ta kai asibiti. Gama wayar tasu yay daidai da shigowan Zahra'u, yanda ta shigo fuska a haɗe shima kuma ya haɗe tasa fuskar zaka san ba a shiri da juna an samu saɓani. Ta zauna kan kujera tana kallonsa tace,"Wai yanzu da gaske ka ke ba zanje bikin nan ba?".
Tayi maganar tana girgiza ƙafafu haka kuma tana faman jijjiga kai alamun dai ranta a matuƙar bace yake, sannan ta shiryawa rigimar da duk ya taka.
Bai ko kalleta ba balle ta saka ran zai amsa, ya sunkuya ya ɗauki Iman da ta fara rarrafawa can zata tafi yo ta'adi, wasa ya shiga yi mata, ba zai taɓa iya musalta yanda yake matuƙar kaunar ƴarsa ba, yana son fiye da kowa da komai nasa, irin son da bai haɗa shi da komai ba, haka yana matuƙar godiya ga Allah da ya ba shi ita ya ke kuma kan ƙara basa wasu. "Daddyn Iman magana fa na ke maka kayi banza kamar baka jini ba".
Ido ya ɗaga ya kalleta, sai yay murmushin da shi ɗaya yaji sautin kayansa kana yace,"Sai na rubuta a takarda na bi ko'ina a cikin gidan nan na manna tukunna za ki gane abin da na ke nufi kenan".
Sai kawai ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya, kuka sosai irin na cin rai. "Me yasa za ka zaɓi hakan a matsayin hanyar ƙuntata mini, ko laifi na maka ai bai kamata ka huce akan hakan ba".
Barin Iman yay ya miƙe ya yana tuɓe jallabiyarsa, bai da lokacin biye mata shikam, ya fi gane ya mayar da ita mahaukaciya tayi ta zuba a duk san da irin hakan ta motsa. faɗa suke yi sama da watanni, dama tuni yana ta fushi da ita yana jin haushinta akan nuna rashin sanin darajar iyayensa da muhimmancin su, kwata kwata bata nuna damuwarta da kulawarta akan rashin lafiyar mahaifiyarsa, ta mayar da shi wani ɗan iska sauna sai dai ta shirya tayi fitarta aiki, haka idan zuwa anguwa ne ya kama tana kan gaba wajen fita, amma ko da sau ɗaya bata taɓa dubansa ba tace zata je asibiti wajen Iyam, haka ko da tursasata yayi akan su tafi ranar sai sun yi tashin hankali tun daga kan tafiya zuwa dawowa. Ga shi yana buƙatar kuɗi ƙememe taƙi ta ba shi wani abu a cikin kuɗaɗen da ya riga ya mallakawa su Iman tun kafin haihuwarsu, a cewarta yanzu ai ba nasa ba ne ko auro ba zata ba shi ba balle yay iko da su ganin yana ubansu. Sannan ta zo ta Yaye Iman yarinyar na da wata goma wai ta gaji da bata nono ita ba zata bari nonota ya zube ba, ya rabu da ita a wannan ganin yarinyar bata kuka kuma tana shan madarar da aka basu a asibiti sosai da zai kama cikin yaro.
Kuma kwatsam bayan nan saboda bata da hankali tana batun zubar masa da cikin da Allah ya ƙara basa tana faɗin ita ba zata iya haihuwar kwanika ba, bata shirya mata ba, ya za'ai ƴarta ko wata goma sha biyar bata yi ba ace ta samu wani cikin, ba hauka take ba yanda ta tsara sai bayan shekara bakwai kafin ta sake samun wata haihuwar, bata yi aure don ta saki jiki tayi ta zuba ƴaƴa ba kamar wata kaza, don haka ko me zai yi sai ta zubar da cikin.