Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 20
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 20: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 20. Wata huɗu kenan suna ta fama da shi, yace wallahi muddin ta zubar…
4,400 words
Wata huɗu kenan suna ta fama da shi, yace wallahi muddin ta zubar masa da ciki sai sun yi shari'a kuma sai ya saketa kuma ba zai bata Iman ba, to wannan furucin da yay shi ne ta ɗan sassauto amma ba wai don ta haƙura ba, tana nan akan bakanta na sai ta zubar da cikin. Shi ne kuwa ya tattarata gaba ɗaya da duk huruminta ya aje a gefe, ko abincinta ya daina ci, magana ya daina yi mata, ko abubuwan da yake siyowa ya aje cikin gidan duk ya daina, shimfiɗa ma ban da kar ya cuci kansa sai ya ƙaurace mata gaba ɗaya don so yake ya horata ta horu. Kuma sai Allah ya kawo masa hanyar da zai rama ɗin, za'ai bikin Ƙanwarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya daga ita sai ita, Mahaifiyarta ma zata je saudiya duk ya hana yace ba zata je ba, ya kuma rantse da hakan, shi ne ta kira mahaifinta ta kai masa ƙara, shi kuma ya kira Nazifin ya dinƙa zazzaga masa bala'i yana cewa kar fa ya zaƙe da yawa, ya daina ganin don ya isa ne ko ya kai ya ɗauki ƴarsa ya ba shi, alfarma yay masa saboda haka in yace zai zaɓi cuzgunawa ƴarsa to tabbas zai ji sammaci.
Tun da mahaifinta ke shiga huruminsu yay bake bake akai bai taɓa buɗe baki ya maida masa martani ba, idan aka cire mahaifiyarta kowa a familyn na su taka shi yake son ransa musamman ma mahaifin nata, shi har yana faɗa masa banda ƙaddara ma dai ai bai cancanci ya ɗauki ƴarsa ya bawa mara ilimin boko ita ba, wanda ko rubutun kirki bai gama iya ba, ranar kuwa ya kada baki ya maida masa martanin cewa ilimin addini shi ke gaba da na bokon da suke alfahari da tutiya akai, kuma Alhamdulillahi ya samu ko yanzu ƙiyama ta tashi, ko yanzu zai kwanta ƙabari lafiya tun da bai fifita duniya akan lahirarsa ba.
Da wannan su kai ta fafatawa da mahaifin Zahra'un wanda ta kai har yace to shikenan zai ɗauke ƴarsa, shi kuma yace to in har ta fita daga gidansa a bakin aurenta, haka kuma yaywa ƴarsa kashedi tare da jan kunne kar tayi kuskuren zubar masa da ciki idan ba haka ba za su yi shari'a da ita, shari'a irin ta gani kashe ni.
Zahra'u ta sassauta murya tana dubansa tace,"Daddyn Iman kawa girman Allah da manzonsa kayi haƙuri idan laifi na maka, amma don Allah kar kace zaka hana ni zuwa bikin gidanmu ka taimaka min".
Ya isa gaban madubi yana ɗaukan clipper yace,"Ashe shugabar sanin right ta iya bada haƙuri".
Ta rufe ido ta buɗe. "Ni dai ko me zaka kace ka faɗa amma kayi haƙuri ka bar ni naje, ni wallahi na yarda idan naje na dawo ka ware watanni ka hana ni zuwa ko'ina bayan aikina".
Yay wani murmushi kafin yace,"Aikin ma ai kina gab da daina zuwansa, ai yanda kika zaɓi ki baƙanta min haka nima na dinƙi ƙuntata miki kenan, da ni kike zancen wallahi muddin ni ke aurenki sai kin shekara guda ba ki je gidanku ba, za ki sha mamakina".
Aikuwa sai ta miƙe ta baɗawa idonta ƙasa ta kama tafa hannu cikin masifa tana faɗin,"Ƙaryarka tasha ƙarya Nazifi, baka isa ka hana ni zuwa gidanmu ba, baka isa ka raba ni da aikina ba, ka yi kaɗan, idan kuwa kace hakan za'ai nima zaka sha mamakina wallahi wannan cikin na jikina sai na zubar da shi, ba kuma shi kaɗai ba kowanne ciki naka da zan samu sai na zubar da shi kaji ma na faɗa maka".
"To ki ta zubarwa mana, wa kika yiwa in ba kan ki ba, ke ce za ki ƙare a wahala kina shan magani yana lalata miki mahaifa ƙarshe ki zo ki daina ɗaukar cikin, ni kuma daga nan na danƙaro wata matar".
Wani kukan kura tayi tayo kansa zata cakumi kwalarsa tana faman hargagin cewa,"Na rantse da Allah baka isa ka ƙaro aure ba, ni ɗaya zan ci gaba da zama da kai, kuma kayi gangancin hakan ka gani ko wacece sai na kasheta sai naga bayanku kai da ita, kuma ban ga uban da zai hana ni zubar da cikin nan ba ko me za'a yi".
Tana gama maganar ta fita kamar zararra, in few minutes sai gata ta dawo da goran wani magani na hausa da kuma ƙwaya a hannunta, zuba mata ido yay yana kallonta ya kasa hanata har ta ɗiɗɗiki maganin. Jarkan faro guda sai da ta shanye kana ta sauke sai sauke numfarfashi take yi,"Na sha kuma zai zube, na kashe ɗan naka kayi duk abin da zaka yi....".
Cikin tsananin ɓacin rai da ƙunar zuciya yay kanta yana ɗaukar sachet ɗin maganin ya duba, take ya daga waya ya roƙi wani likita da cewa ya hau whatsapp yay masa wani taimako, ya ɗauki hoton maganin ya turawa likitan kai tsaye yace masa ai maganin zubar da ciki ne. Lokaci guda gashin jikinsa ya mimmiƙe, gumi ya keto masa, abun da ya ƙwallafa rai a kai ta zubar masa? Ɗansa na halal ɗan sunnah ba ɗan shege ba? Zuciya ta ɗebe shi ta kai shi ga nufar wadrobe ya buɗe tare da zaro belt ɗin wandonsa. Zahra'u da ke faman zazzaga masifa tana yayi abin da yake tunanin zai yi ba tayi aune ba ya shiga lafta mata belt ɗin ta ko'ina tamkar an aiko shi.
Yaji belt ɗin ma ba zata masa yanda yake so ba kawai sai ya koma sa ƙafa yana bal da ita yana kai mata kutufo da hannu. "Wallahi ba ki isa kin kashe min ɗana ba, idan har cikina ya zube da gaske sai na nakasta ki, sai na barki da mummunan tabon da ba zai taɓa gogewa ba a jikin ki, ko ban kasheki ba sai na zama sanadin da za ki daina farin ciki har abada".
Sai da yay mata mugun duka tukunna ya barta yana huci ba don ya gaji ba ko kuma hakan yay masa. Hankalinsa ne ya tattara ya kaɗa yay asibiti wurin Iyam. Ita kuma ta miƙe da ƙyar cikin wahala tana faɗin,"Kuma wallahi baka duki banza ba, sai ka san ni ka yiwa wannan dukan Nazifi, mugu azzalumi, Allah ya isana da ka cuce ni ka aure ni".
"Dilla can rufe min ba ki, ni da ke wa ya kamata yay Allah ya isa, ban da ƙaddara me zai sa na aure ki, auren bagidajiya mara ilimin addini, kuma Allah ya isa da kika zama sanadiyar da na rasa matata, matar arziƙi...Tun da na aure ki ban huta ba, kullum cikin ganin masifu na ke iri iri, mene a cikin auren na ki banda tarin takaici da nadama, ai tuni na fahimci ba don Allah kika aure ni ba sai saboda dukiyata, kuma kije na sake ki saki ɗaya, kar kuma ki sake ki tafi da ko tsinke da na mallakawa yarinyata, ki aje min yarinya da duk abin da na mallaka mata".
Ya faɗa yana hanzarin shiga banɗaki jikinsa sai rawa yake yi, haka zuciyarsa tamkar zata fito waje saboda ɓacin rai.
"Allah ya isana tun da ka mayar da ni bazawara, wallahi ba zan yafe maka ba sai mahaifina ya ɗauka min fansa".
Tana ta surutanta ya shiga bandaƙi, ko minti biyar bai yi ba cikakke ya fito, shi kansa ya san ba wanka kirki yay ba. Jallabiyar da ya cire ya mayar ya kwashi wayarsa da maƙullai ya fita falo. Can ya sameta tana aikin zage zage tana faɗawa Babanta wai Nazifi yay mata duka har sai da cikin jikinta ya zube, Daddy ayi ƙararsa kotu ba zan yarda ba sai alƙali yabi min hakkina.
Iman tana hannunta ya fizge ƴarsa da ke ta kuka. Sai da yaje bakin ƙofa sannan ya tsaya ya juyo yana kallonta da cewa,"Idan kika bari na dawo gidan nan na same ki ban san illar da zan yi miki ba".
Ya fice a fusace, yacca yake tuƙi kuwa kana gani kasan na cikin motar ba lafiya ƙalau ba akwai matsala ta tashin hankali, ga kukan Iman duk ya daɗa ɗaga hankalinsa wacca tuni ya fara tunanin wacca uwar zai nema mata? Wacece zata kula da yarinyarsa bisa ruƙo na gaskiya da amana? Wace zata bata ingantacciyar tarbiyar da yake fatan yaransa su samu? Wacece zata yi duk iyaka ƙoƙarin wajen ganin sun wadatu da ilimi ta kowanne fanni musamman na addini?
Wayarsa tana ta ƙara yaƙi ɗagawa sai da yaji kiran yay yawa tukunna, ganin likitan Iyam ne sai ya ɗaga da sauri, likitan yace masa zai bar asibiti ne ga result ɗin gwajin da aka masa ya fito, kwanaki ne yay fama da wani azababben ciwon ciki da mara a haɗe har sai da ya saddaƙar mutuwa zai yi. Da ƙosawar yaji menene ya shiga tambayar likitan sakamakon, saboda ko a lokacin likitan yace masa kamar matsalar babba ce amma dai sai result ya fito za su tabbatar. Likitan yace masa ya ƙaraso ɗin dai tukunna amma ya zo da sauri don zai fita ya bar asibitin saboda akwai wani asibitin da zai je zai yi aikin tiyata yanzu.
Kashe wayar yay ya ƙarawa motar gudu, yana shiga asibitin ya miƙawa Fati Iman yace ta goyata, duk ganin yanayinsa kamar ba shi ba a wani rikiɗe suka tafi ruuu suna tambayarsa lafiya. Kai tsaye yace da Yaya,"Zahra'u ta zubar min da ciki, na mata dukan fitar hayyaci na kuma saketa, Yaya ki kirata ki shaida matta kar na koma gidana na sameta idan ba haka ba wallahi ko ban kasheta ba sai na kusa kasheta".
Yana faɗin hakan ya faɗa ofishin Doctor, Yaya ta kama salati tana sallallami, ce take mun shiga uku an ta sake saken aure kenan, Nazifi me yasa ka kasa sarrafa zuciyarka kai kuwa. Yanzu wanne hali Iyam zata shiga idan taji wannan zancen. Shi kuwa yana can gaban likita zaune ya fito da takardun cikin file ɗinsa yana yi masa bayanin cewa.
"Akwai abin da muke kira da Disruptions in hormonal levels, ma'ana dai ka samu low testosterone, sperm production ya ragu sosai wanda dalilin hakan haihuwa ta ɗauke maka, baya ga haka ma still akwai Hormonal Imbalances wato rashin daidaituwar ƙwan halittarka...".
Gaba ɗaya ma sai ya daina ji da gane bayanan da likitan ke masa, to me yay saura da zai ji? Duk sauran bayanin dai akan cutar ne, gundarin ciwon kuma an faɗa masa, kalma ɗaya ya riƙe haihuwa ta tsaya maka ba zaka kuma haihuwa ba! Wannan Kalmar me ɗacin ɗanɗano daga ina haka! Garin ma ya hakan zata faru da shi? Daga ƴar karamar cuta sai binkicensu na ƙarya ya bada sakamakon daina haihuwa?
Bai san wanna tunani zai yi ba kuma bai san me zan iya cewa da danganta maganar likitan akai ba, abu ɗaya ya sani ya ɗaga hannu ya dakatar da likita daga bayanansa, sannan kuma hannunsa na rawa ya zaro wayarsa a aljihu ya danna kiran mahaifin Zahra'u yace masa,"Na mayar da aurenmu Daddy".
Daga wannan maganar kuma sai ya dafe ƙirjinsa da yake jin zuciyarsa na barazanar fitowa waje, har ta kai ga ya faɗo a saman kujera bai sani ba, haka kuma ba tare da sanin nasa ba likita yaji yana ambaton,"Hasbunallahu wani'imal wakil, Astagfirullah ya Allah, tabbas na maka wani laifin da ban sa ni da na ke amsar hukunci ka yafe min Allah na".
Sai ya koma cewa da likitan ya taimaka masa zuciyarsa zata fito. _________________ ₦500 07018098175
*B2ƘR25FT5* Likita ya taso da sauri yayo kansa, ya kama shi ya mayar da shi kan kujerar ya zauna.wani irin numfashi ya ke saukewa me wahala, likitan na ta jera masa tambayar,"Dama baka da lafiya baka min bayani ba, ai you should have let me know, me ka ke ji a ƙirjin naka?".
Bai iya ce masa komai ba kuma ba zai iya cewa da shi komai ɗin ba, likitan yay ƙoƙarin ɗora Stethoscope ya dakatar da shi da cewa,"Bar ni likita bana buƙatan komai, na gode".
Yana faɗin hakan ya kifa kansa kan table, shin me ya aikata a rayuwarsa ne haka da abubuwa marasa daɗi ke ta ƙwallo da shi? A tarihin rayuwarsa yau ita ce rana ta biyu da zai iya cewa ya shiga tashin hankalin da yake jin zai iya haɗiyar zuciya ya mutu ya huta. Kusan mintuna goma yana zaune a hakan yana ta biyo innalillahi a bakinsa, natsuwarsa ma da yake so ya samu ya kasa samunta, kansa yay masa bala'in nauyi wanda in da za'a cire masa tabbas zai so hakan matuƙa.
Bayanin likita ne ke ta faman tariya a cikin kansa, yayin da hoton Zahra'u ke ta haskawa a cikin ƙwayar idonsa san da take shan maganin zubar da ciki, shikenan ta gama da shi, ta cuce shi, kuma ba zai taɓa yafe mata ba, yanzu shikenan kuma shi da wata haihuwar har mutuwa, kawai sai Noor ta faɗo masa, a hankali ya furta Allah ya isa tsakanina da ke Sa'ida da kika raba ni da yarinyata.
Dafa kujerar yay ya miƙe da ƙyar, ya dubi likitan da ƙwayar idanuwansa masu nauyi waɗanda ɓacin rai, tashin hankali, da gangamin damuwa sukawa ƙawanya. Fita yay a office ɗin a daddafe, likita na ta ce masa ya tsaya ya karɓi takardunsa bai ko masa magana ba kawai ya buɗe ƙofa ya fice.
Can ya iske su Yaya zazzaune, tana ganinsa ta shiga tambayarsa lafiya duba da yanayinsa da ya kasa ɓoye halin da yake ciki. "Iyam ta tashi?". Ya faɗa da ƙyar da amon muryar da ya zama tamkar ba nasa ba.
"Bata tashi ba, wai wani abu ne ke faruwa? Me likitan yace maka?".
Ya rumtse idonsa ya girgiza shi, sannan yasa hannu ya shafo kansa. "Ina Lubabatu?".
"Basu jima da fita ba Iman taƙi shiru, taje siyo mata biscuite".
Bai ce komai ba ya nufi ɗakin da Iyam take ya buɗa ya shiga, tana bacci har yanzu, babu wanda zai ga tsohuwar nan bai ji ƙwalla ta taru a idonsa ba, saboda yanda ta rame ta yamutse, ƙasusuwan jikinta na ko'ina ya fito tamkar zasu yi magana, ya ilahi wannan rayuwa Allah ka mana da sauƙi. Gaban gadon yaje ya zauna akan kujera, ya daɗe yana kallon fuskarta, ya kai yatsu ya kara a ƙasan hancinta saboda wani motsi da zuciyarsa tayi na tsoro gani yake kamar bata numfashi.
Sai da yaji numfashinta na fita ya sauke doguwar ajiyar zuciya, ya kama hannunta ya ruƙo ya ɗora a saman kansa. "Na sani a ko da yaushe adu'arki na tare da ni, Allah ya ba ki lafiya ya tashi kafaɗunki".
Da haka ya miƙe ya fita cikin matuƙar sanyin jiki, lissafinsa guda ɗaya ne kawai a yanzu wanda zuciyarsa ta yanke masa shawaran ya siyar da gidansa kawai ya biya kuɗin aikin mahaifiyarsa, wannan ɓata lokacin da jiran tsammanin da yake ko saboda shi sai Allah ya hukunta shi, tana ta shan wuya kullum, ga shi yanzu ma dubu sittin ɗin da suke ci a kullum nema take ta gagara don a yanzu bai da kuɗin na yau da zai tura, sai dai kuma ko me za'ai yau sai Zahra'u ta fito da duk wasu abubuwa da ya mallakawa ƴarsa.
Yana fita Iman da ke hannun Lubabatu tana bata biscuite ta shiga miƙo masa hannu, sai yaji wani sanyi ya ɗan ratsa shi, a ƙalla ubangiji bai jarabce shi ba sai da ya bar masa guda ɗaya. Miƙa hannu yay ya karɓeta ya saɓa a kafaɗarsa, ƙwarai Zahra'u ta shiga hakkin yarinyar da ta yayeta da wuri, har yanzu ta kasa kama wani abinci da zai ke kama cikinta, yarinyar duk a motse kamar me wata cutar. A mota haka yay ta surutai wa yarinyar yana jin sabuwar ƙaunarta na ratsa shi.
Suna komawa gida ya tarar Zahra'u tayi aika aika da haukan da ta ɗorawa kanta, duk wasu gilasai na falon ta farfashe su, ta hargitsa jeran kujerun. Ciki kawai ya wuce yana takawa a hankali gudun kar ya taka kwalba, yana shiga ɗakinsa ma ya tarar ta warwatso masa da dukka sutturunsa, takardunsa da komai na amfaninsa, yay saurin isa ga kan gado ya ɗakko laptop ɗin yana kunnawa yaga taci screen, ya ambaci ƙalu innalillahi da ƙarfi.
Jiki na ɓari ya aje Iman da ke ta shaƙuwa, kuma kafin yay wani motsi sai gata ta shigo ɗakin tana cewa da shi,"Ashe ma kai ƙaramin ɗan iska ne, ai da baka mayar da ni ba, ai da ka sake ni gaba ɗaya shi ne zaka tabbatar da ka isa ka kai, kuma abin da ka zo ka tarar kaɗan ne, wallahi sai na tabbata ka ɗora hannu saman ka kayi danasanin aurena da hujja, ba dai ni ka duka ba, zaka sha mamaki".
Har ta gama surutanta bai ce mata komai ba, sai da zata fita ne yace da ita,"Ki kwashi muhimman kayanki zamu koma gidanmu da zama, zan siyar da wannan a yau".
Wata iriyar juyowa tayi tana ƙunduma ashariya. "Nazifi ka ce mene? Za mu tashi anan? Mu koma gidanku? Na zauna tare da ƙannenka da matan Babanka ka ke nufi? Nooo impossible, ba a kaina ba sai dai kan wata".
"Ok to idan ba kya son faruwar hakan sai ki tattaro duk abin da mallakawa ƴata ki bani na nemawa mahaifiyata lafiya...".
"Kai dakata du Allah! Wai zatonka ni shashasha ce, ka man ce wayayya ka aura ƴar boko me lissafi, to tun da ka bani wannan kadarori na juya komai da nawa sunan Nazifi, kuma kai da kanka ka sanya hannu akai shaidar komai da ka bayar ba naka ba ne ba na ƴarka ba ne nawa ne mallakina ne, baka da iko ba ka da wata hujja a yanzu da zasu karɓa maka, idan ma zaka bar tunaninsu da nemansu zai fiye maka, gida kuma ka siyar ina ruwana, ƙarƙari na koma gidanmu da zama don wallahi ba zan zauna a gidan surukai ba ka zubar min da aji da ƙima".
Ya san dai duk yana jinta da kalamansa, to amma abin da ya kasa ganewa yaushe ya rattaba hannu jikin takardu? Take watarana ta haska masa a cikin ƙwayar idonsa, sun gama gurzar soyayya ko tashi ba suyi akan gadon ba ta miƙo masa takardun tana faɗin takardu ne na neman promotion a wurin aiki, kuma ana neman sanya hannun miji wanda ta hakanne zata iya samu su ƙara mata matsayin da take fata. Shi kuma da murnarsa da azarɓaɓinsa ya karɓa takardun guda biyar ya rattaba sa hannunsa akai mai kyau da aji. Yana ta shi mata albarka yana faɗin ɗaukakarta ai tasa ce.
Tunaninsa ya tsaya cak jin ta wullo masa abu a jiki, ya kai idonsa kan ATM har guda biyu, ya ɗauka yana juya su kamin ya kalleta ya miƙe cikin hanzari da ƴar guntuwar murnarsa sai kuwa furucinta yay daga daga da guntuwar murnar da ta ziyar ce shi. "Babu ko sisi a ciki domin kuwa duk na tura su cikin asusuna, wacca hujja zaka nunawa banki na cewar ba kai ka tura ba? Kuma sannan da kake maganar zaka siyar da gida, ka manta da cewa har da shi ka sanya hannu a takardarsa na cewa ka mallakawa Noor? Motarka ita kawai ta maka saura Nazifi baka da wani sauran abu da zaka yi tunƙaho da shi, kuma ban yarda ba saki tsakanina da kai ma ya zama dole, domin kuwa na lura da cewa kamar babu ta kamaka, ni kuma ba zan iya zaman aure da talaka ba, ba kuma zan bar maka ƴata ba dole zan tafi da ita domin ba zan bari rayuwarta ta tagayyara ba a wurin wanda bai da kuɗin ɗawainiyar kansa ma balle ta ƴarsa, ingantacciyar rayuwa na ke sowa ƴata da zata tashi cikin gata da jin daɗi da rayuwar cikin daula kamar yanda na so ba yanda ubanta ya ta so ba, shiyasa na ƙwace komai na ka kafin ma tsautsayi yaja ka ga samun wasu ƴaƴan ba tare da ni ba ya zama an raba dukiyarka da ba da ƴaƴana kawai ba, kuma kamar yanda ka faɗa ne Kuɗinka shi yasa na aureka ban da haka kai kanka ka san idan ba shaye shaye nayi ba nayi rayuwar ƙasar waje da kwalin degree na me aji ace na ɓige da auren namijin da ko satifiket ɗin primary bai da shi".
Kalaminta ya ƙona ransa,"Ki je duk wata cutarwa da kika yi min ke da Allah domin kuwa kin zalunce ni, mayaudariya azzaluma, sannan ki sani ko za ki mutu igiyar aurena ba zata sauka daga kanki ba, kina nan tare da ni, kin zubar da ciki ko? To ki sani ni kuma a yanzu ba zan ƙara haihuwa ba, haihuwa ta tsaya min".
"Na shiga uku, kenan idan ina tare da kai ba zan ƙara haihuwa ba, ina burin haihuwan ɗa namijin da na ke da shi? Na rantse da Allah baka isa ba Nazifi sai ka rabu da ni sai ka sakeni, ba zan zauna da namijin da ba ya haihuwa ba, ga talauci ga rashin ƴaƴa inaaa".
Ta faɗi hakan tayo kansa kamar mahaukaciya tana cewa lallai ko ya saketa ko tayi masa rauni, shima yay saurin tashi ya ɗaure Iman a bayansa tare da maketa ta faɗa gefe ya fita a ɗakin yasa makulli ya kulleta.
*BAYAN SHEKARA HUƊU* *Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.*
Ƙarar saukar jirgin da ya jiyo na shawagi a ƙasa yay sanadin lumshe idanuwansa, wanda hakan yay nasarar bayyanar da zara-zaran gashin idonsa da kuma motsawar laɓɓansa masu taushi, kaman wanda yay mugun gajiya haka ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, yay saurin mayar da p-cap ɗinsa haɗi da daidaita zaman baƙin gilashin fuskarsa, sai fuskan ya ƙara ɓoyuwa ta yanda ba zaka yi saurin shaida shi ba, kewayyan sajensa me haɗe da gemu kawai kake iya haskowa kaɗan.
Bugawar sakan ɗaya, biyu, uku ya buɗe idanuwan nasa daga lumshen da suke tare da ɗan juyasu yana jin wani sanyayyan abu na biyowa ta babban yatsansa yana shiga jikinsa. Idonsa ya sauka akan agogon hannunsa, agogon ya buga ƙarfe huɗu da rabi daidai na yamma, kuma lokacin yay daidai da gama shawagin jirgin da ya taso daga ƙasar Germany zuwa ƙasarmu ta nigeria, kansa ya ɗaga ya mayar da dubansa ga inda jirgin ya sauka, idonsa na kalle masa mutanen da ke fitowa daga cikin jirgin sannu a hankali, kallonsu yake yi sosai ya kasa ko da ƙifta ido, duk ya ƙosa yaga fitowar halittar da idanunsa ke jira, haka kuma ya kasa ɗauke ganinsa daga wurin duk da irin yacca yake jin wani taraddadi na fizgarsa, zuciyarsa faɗa masa take kamar ba zaka samu ba ka haƙura kawai.
Bayan fitowar passengers da dama, gabansa ne ya yanke ya faɗi, zuciyarsa ta harba fat fat a lokacin da ƙwayar idonsa ta sauka akan kyakykyawar halittar da ke sakkowa a yanzu, hasken jikinta kaman jini ya tsarto, kai ba ka ce ƴar nigeria ba, sakkowa take yi daga matattakalan a hankali kuma cikin natsuwa, doguwar fuskarta na bayyana baiwar fara'ar da Allah ya bata, fuskar da kana gani kasan babu wata damuwa a tare da ita illa zumuɗi da ƙosawar son kasancewa da mafi muhimmanci wasu mutane a rayuwarta.
Tun fitowanta a jirgin kanta a ƙasa yake, riga da wando ne a jikinta na uniform ɗin nurses ɗin ƙasar germany blue colour, sun matuƙar mata kyau tubarakallah ma sha Allah, a gefe ɗaya kuma tana gyara zaman sarƙar hannunta. Ta ɗago fuskarta tana kanne ido alamun haske yay masu yawa duk da rana ta ɗanyi ƙasa a lokacin. Cikin takun tafiyar da take me ɗaukar hankali da burgewa trolly ɗin da take jaye da ita ta cije wanda hakan yasa ta gurɗewa tayi saurin duƙawa.
Gurɗewan nata ya taɓa zuciyarsa ya miƙa hannu da sauri da niyyar tareta daga yunƙurin faɗuwar da take neman yi, sai kuma ya ankare da cewar tazarar da ke tsakaninsu me yawa ce, kuma hakan ya haifar da rashin jin daɗi a tare da shi, bai kamata hakan ta kasance ba, alƙawarinsa ne na gyara kuskurensa zai tsaya tare da ita kowanne yanayi da motsinta ba tare da ya bari wani abu ya sameta ba, katanga ya ke so ya zamar mata, katanga ta kariya, hakana zai zame mata madafar da zata kaance ko da yaushe tana dafawa ba tare da kuka ko baƙin ciki ba, nasa alƙawarin ne a wannan karon wanzuwar tabbataccen farin ciki a fuskarta da duniyarta har ranar da zai daina numfashi, ba zai bari wani abu ya taɓata ba, haka ba zai ƙara gangancin maimaita kuskuren da yay a baya ba.
Iskar bakinsa me ɗumi ya furzar, kansa ya sunkuyar ya leƙa cikin motar da yake jingine a jiki, ƴarsa da ƙanwar ne zaune a ciki, sai ya kai ƙwayar idonsa yana duban fuskar ƙanwar tasa, da wani yanayi sirrantacce a saman fuskar tasa, a hankali yace da ita,"Kayan sun mata yawa".
Sai yay shiru for seconds kana ya ƙarasa maganar da cewa,"zan taimaka mata".
Da murmushi me burgewa a fuskarta da ke nuna nata jin daɗi da farin cikin da ke neman zarce nasa tayi knooding masa kanta kawai. "But be carefull Mr Man".
Leɓbansa ne kawai suka motsa, alamu na son yay murmushi sai dai hakan bai samu ba, domin kuwa a yau ɗin karo na farko da yake jin wani abu me kama da tsoro na kama shi, wanda a matsayinsa da sanin waye shi ɗin bai kamata tsoro ya nemi ya masa farmaki ba. Ya miƙa hannunsa cikin motar ta miƙo masa face mask ya saka, ya ƙara gyara p-cap ɗinsa ya zuba hannayensa cikin aljihun rigar sanyin jikinsa, fuskarsa ta rufu ruf kamar mara gaskiya, ya sake leƙa kansa cikin motar yana duban Ƙanwar tasa da cewa,"Yayi?".
Haƙoranta na gaba suka bayyana dalilin siririyar dariyar da tayi, ta ce,"Ko ni ba zan iya shaidaka ba, balle kuma ita, duk da wani connection ɗin yafi gaban tunanin mutum".
Da dogon yatsansa ya lakuci kumatunta, sannu a hankali kuma ya fara takawa yana tafiya yana jin wani irin yanayi na shigarsa, farin cike yake, farin cikin da zai iya cewa ya girmi nata da duk wani masoyinta makusancinta.
Hanzarin tafiyarsa ya ƙara na gient ɗin namiji kamarsa. "Excuse me". Ya faɗa da amon muryar da ya fito da ɓacin rai, haka ma ɓoyayyar fuskarsa na bayyana zallar kishi da jin haushin mutumin da ya isa gabanta da niyyar taimaka mata ya karɓi trolly ɗin so that taji da jakunkunan hannayenta.