Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 21
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 21: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 21. Mutumin yay saurin matsawa gefe yana ba shi haƙuri tsammaninsa ko…
4,494 words
Mutumin yay saurin matsawa gefe yana ba shi haƙuri tsammaninsa ko me gidanta ne. shi kuma ya kai hannu ya kama hannun trolly ɗin, a hankali kuma a miskilance cikin harshen turanci yace,"Barka da dawowa". Ya faɗa ba tare da damuwar ta jisa ko bata jisa ba, shi dai ya amayar, fushinsa kawai akan me zata fito haka fuska a bayyane kowanne kare da doki ya ganta yajinta burge shi, and just imagine ta tsaya tsakiya idon kowa da ke wajen ya ƙare mata kallo kenan, babu ruwanta bata san marairaice fuskan da take yi ma ƙara fitar da kyawun halittarta yake ba.
"Mtssswww". Guntun tsaki ya fita a ƙasan maƙoshinsa, yana jin kamar ya zaro abar da ke cikin aljihunsa ya daki kanta da ita ko ta san da cewa kan hanya take tsaye ba cikin ɗakinta ba.
Ƙwayar idonsa ta manne a saman fuskarta da murmushin jin daɗi da farin ciki yaƙi ɗaukewa. Waya take yi da ahalinta tana faɗin,"Mun sauka yanzu amma ban hango kowa ba, kuna daga ina?".
Tayi maganar kaman zata yi kuka, wanda sautin hakan ya tafi har can ƙasan zuciyarsa ta motsa. "To Abbaa sai ya ƙaraso Allah ya kawo shi lafiya". Nayi maganar cikin rashin jin daɗi, domin ba haka na so ba, yanda na so ace ina sauka idona yay kwalli da mahaifiyata ko mahaifina, to amma babu komai tunda Yaya Imam da Yaya Al'amin ɗin suna kan hanya, kuma na san duk yanda aka yi kuɗin mota ne ya hane su tahowa gaba ɗayan su.
Na kai hannu ga trolly ɗita sai naji an ja, nayi saurin ɗago ido in sauke kan dogon mutumin da ya fara takawa, da sauri na dakatar da shi da cewa,"Malam jakata ce".
Bai tsaya ba yaci gaba da tafiyarsa, ni kuma ina ta binsa cikin sauri ina ce masa jakata ce yay mistake ɗin ɗauka ne, sai dai ganin bai juyowa ba tunanina ya bani ko bai jin hausa ne tun da yanayinsa kamar ba na bahaushe ba, don haka cikin yaren turancin da ya samu ƙwarewa yanzu a kan harshena na ce masa,"Jakata ce fa kayi mantuwa".
Nan ma dai kamar bai jini ba, sai na ce to ko kurma ne, don haka muna shigowa cikin wata ƴar rumfa nayi saurin shan gabansa da niyyata na masa alama da hannu ya gane nufina. Bisa tsautsayi ƙafata ta gurɗe har na kai ƙasa dalilin ɗan tudun da na buga, wayata ta faɗi na saddaƙar da tayi raga raga, yunƙurawa nayi na miƙe na zauna kan kujerun ƙasan rumfar ina danne wajen da na buge idona a rumtse.
"Sorry please". Buɗe ido nayi na gansa sunkuye gabana kaman zai kai hannunsa kan ƙafata wurin da na dafe sai dai kuma bai yi hakan ba, ya dai ɗauko wayata ya miƙo min. Haka ɗaya naji ƙirjina ya buga sosai, irin bugawar nan da yake a lokacin da mutum ya shiga fargaba ko tsananin tashin hankali na saƙon mutuwa.
Wani sanyayyan ƙamshi ne ke tashi daga jikinsa ya ziyarci hancina, ban san dalilin da hakan ya haifar mini da haɗiye dunƙulallen yawu tare da jin motsawar zuciyata, kuma lokaci guda naji jikina yay sanyi, hannu na miƙa na karɓi wayar ina faɗin,"Thank you".
"Sannu". Ya sake furtawa muryansa can ƙasa.
"Na gode. Dama jakan da ka ɗauka nawa ne ina ga baka lura ba ne". "Na sani, na taimaka miki ne".
"Hope ba ki ji ciwo ba?".
Ina duba wajen na ce,"Ban ji ba". "Sorry na taimaka miki ba tare da izininki ba".
Sai yanzu ya ɗago kansa wanda na san ya kalle ni ne ta cikin baƙin gilashin da idanunsa ke rufe a ciki, babu ta yanda zan iya ganin fuskarsa domin kuwa face mask ya ɓoyeta. Me na ke ji ne? Tamkar na san muryarsa, anya kuwa! Ta ya hakan ma zata kasance? Tunanin da na ke ya yanke ganin ya miƙe yana barin wajen da sassarfa.
Na bi bayansa da ido ina kallonsa, ban san me yasa na ke ganin kamar na taɓa ganin me tafiya irin tasa ba, ba ya ga nan ma ga muryarsa da na ke da tabbacin na taɓa jinta, haka ƙamshin ma kamar na san shi? Sai dai duk me yaja bugawar ƙirjina akan hakan? Waye shi ɗin? Tambayar ƙasan ran nawa ta haɗe da saukar ƙwayar idona akan bayan rigarsa da ke da tambarin S a jiki, ni dai har ya ɓacewa ganina ban ɗauke idona da tunanin wani abu akansa ba.
Wayata na cire key na danna lambar Safiyya, tana ɗagawa tace,"Beb ina ta kiran wayanki ban samu".
Na ce,"To ai sai da muka sauka na mayar da sim ɗina na nan". "Beb can't wait to see you, an dawo lafiya". "Lafiya lau, ina Daughter nah?".
Sautin murmushinta ya fita da cewa,"Ga ta tana bacci, itama ai ta ƙosa taga Mum ɗinta, kina airpot ɗin ina ne yanzu? Kano ku ka sauka ko Abuja?".
"Muna Abuja". Sai yanzu ta ankare da yanayin fitar sautin muryata tace,"Beb lafiya dai? Yaushe rabon da naji muryanki a irin haka, menene?".
Na karyar da wuya ina ɓata fuska na ce,"Kinga fa basu zo ɗaukana ba, kuma tun jiya sai da na cewa Abbaa na tura musu kuɗi sai ce yay a'a akwai kuɗi, kuma yanzu mun yi waya ma yana ce min Yaya Imam ɗin na kan hanya bai ma ƙaraso ba, don Allah haka zan ta zama anan ni ɗaya babu wanda na sani, ga sauran nan duk ƴan gidansu sai ɗaukan su suke yi".
Na ƙarashe maganar idanuna na cika da ruwan hawayen da ke neman zubowa, kawai sai jin ihun Safiyya nayi a gabana ta faɗo jikina ta maƙalƙale ni, nima kuwa ban san lokacin da nayi mata wata runguma ba ina cewa,"Me yasa haka Beb, ni ki daina suprising ɗina irin haka".
Muka saki juna tana bina da kallo da cewar,"Sa'ida ke ce kuwa? Kin ga yanda kika koma na rantse da Allah kamar sake halittanki aka yi, wannan kumatun fa, naga ƙashin wuyanki ko yana nan".
Ta faɗi hakan tana ɗaga jesy hijab ɗin jikina tana aikin taɓa wuyana. "Beb ƙashin ma ya koma, kuturu yarinyar nan anya kuwa karatu kika je kika yi. Ko da yake ai result ɗinki kaɗai ya nuna ba wasa kika je kika yi ba, kin san duk wani handle ena na social media sai da na sa vedion result ɗinki, weldone ƙwaruwata za great first class".
Dariya na ke sosai cikin jin daɗi, ina dubanta na ce,"Amma ya akai kika zo nan?".
"Na san za ki dawo zan ƙi zuwa Beb, haba zance ne ai, muna nan Abuja ma fa tun last week Daddyn Amal ya zo seminer, jiya kina ce min zaku dawo yau kwana ne kawai ban ba a wajen nan, amma ina nan jirgin ku ya sauka na ce bari sai kin kira ni tukunna".
Ina dubanta na ce,"To mu tafi gidan ki idan Yaya Imam ɗin ya zo ya same ni acan, ido yay min yawa duk na kasa natsuwa, kuma wani iri na ke ji, wanne turare ne a jikinki?".
Ta miƙe tana faɗin,"Turaren da kika ba ni lokacin da naje miki visiting...Ke bara dai na fara tofe ki da li'ilafi, Allah Beb gaba ɗaya kin wani sauya, wannan karan kam ai sai miji me tsadar gaske, mijin hawa jirgi sama duk watan duniya, mijin haskawa a tv mijin da ƙasa da duniya ta sansa in sha Allahu".
Ɓata fuska nayi. "Abeg na ce miki ki bar min zance irin wannan, mu tafi ni. Ina ma kika baro Amal ɗin wai?".
"Ke ni ban iya aikin dinƙa yawo da ita tana mota na barta". Na waro ido ina ce mata,"What! Ƙaraman yarinyar za ki bari a mota, Safiyya wai ke kam yaushe ne ranar hankalin ki, ce na ke da kika yi aure kin saitu".
Na faɗa ina ƙara saurin tafiyata tare da tambayarta in da motar tasu take, dama na ƙosa naga Babyn nata don tun da aka haifeta ban ganta ba, sun dai je min ita mijinta lokacin tana fama da laulayi. Kuma can sai na hango Yaya Imam tsaye yana faman ɗaga kai shi da Yaya Al'amin, wani sabon farin ciki ya lulluɓe ni naji kamar na kwasa da gudu na ƙarasa wajensu.
Amma duk da hakan ban fasa gudu gudu sauri sauri ba ina ƙwala masa kira, na bar Safiyya da faman ƙwala min kiran da take yi tana ga motar tasu can, ina ce mata ga Yaya Imam ɗin can ya zo bari na je nemana suke. Ni dai ina zuwa tsananin farin ciki na kasa dakatar da kaina kawai na faɗa jikinsa da matuƙar murna.
"Ke dilla mene haka sakar ni mana, gaban mutane fa mu ke".
Yaya Al'amin yace,"Ah tou ba kun kaita turai ba, ta manta ƴar nigeria ce anan ɗin ma bahaushiya".
Kunya na ɗanji na rissina ina gaida Yaya Imam, kallonsa na ke ina cewa,"Yaya naga ka zama babban mutum".
Hararata yay da cewa,"Malama ina kayan na ki, kar muyi dare a hanya".
Tare muka nufi inda kayana suke, muka ɗauko muna tafe sai ga mota baƙa ta faka a gabanmu, Safiyya ta leƙo tana cewa,"Yaya Imam shigo mu tafi ku barta anan".
Da mamakinsa yace,"A'a Ƙanwata ke da wa?".
Tace,"Kawata na zo tara ai, da ba ku zo ba wallahi Yaya kun barta ta taho da kanta".
Gaisawa suka shiga yi, ya karɓi Babyn hannunta, kusan miti biyar ana tsaye sai hira ake. Wata mota fara ta faka gabanmu, na ciki ya fito saurayi ne baƙi ya zo wajenmu, muka gaisa da shi, yana dubana yace,"Don Allah ku ne ƴan makarantar da ku ka dawo yau?".
Na ɗaga masa da cewa ehh. Sai ya ce min,"Please ko kin san wata Sa'ida Salman?".
Safiyya tayi saurin ce masa,"Ehh ai ita ce ma, lafiya dai ko?".
Sai ya miƙo ticket yana cewa,"A'a dama wannan aka ce na bata".
Ta karɓa tana duba kafin ta miƙawa Yaya Imam tace,"Laa Yaya kaga ma ashe har da kuɗin jirgin masu zuwa ɗaukan su an musu, bamu sani ba. Ke ba'a faɗa muku ba?".
Ina kaɗa kai na ce,"A'a zai iya yiwuwa kuma an faɗa ɗin ina can sakaraftuna na murnar tahowa ban sani ba".
"Ga shi ma yanzu jirgin na ku zai tashi, sai mu koma ciki ai".
Safiyya na tare da mu bata tafi ba har sai da ta ga tashin jirginmu. Tun da muka shiga na ke tawa su Yaya Iman dariyar fama zare ido da suke a cikin jirgi, ba sa banba ɗan kauye yay abin hannu, shi kuma daɗi duk ya cika shi yana faɗin yau ata sanadina ya shiga abin da bai taɓa zato ba, ina ma ace har da Abbaa da Ummani suka taho, gaskiya wannan makarantar tamu sai dai Allah ya biya su kawai.
Haka muke ta hiranmu ina ba su labarin can, du da na ƙosa naga mun sauka burina na ga Abbaa da Ummani kawai. Lokacin da muka sauka a airpot ɗin Malam Aminu Kano messge ya shigo wayata, ina dubawa naga an sa,_"Saura nan ma ki tsaya tsakiyar titin jirgi kina ƙauyanci...gaisuwana ga Abbaa da Ummani".
Dariya na saki ina jinjina lamarin ƙawata, ni na mant ma na tambayeta ko kamfanin sim card ta buɗe ne da duk message ɗin duniya in zata min da sabo take yi, duk da ma first visiting da taje min tana ta rantsuwa ba ita tayi min messges ɗin nan ba ni kuwa na ƙaryatata, to idan ba ita ba waye? _________________________________ *Alhamdulillah! Ƙarshen littafi na jiyu kenan, Littafi na uku zai fara sauka a ranar ɗaya ga watan December insha Allahu, zan ɗan huta na kwana biyu, kuma littafi na uku shi ne ƙarshen littafi na labarin Ƙayar Ruwa, Nagode, Nagode da Soyayyarku, masu siya Allah ƙara buɗi da arziƙi, Allah ya bar zumunci, Ameen* _Kuma kafin mu ɗora zan so jin ra'ayoyin ku, Fitattu Biyar na maku fatan alkhairi.._
*28/11/2023* *Halimahz* 07018098175
*B3ƘR01FT5*
*_Bana jin zan iya fara rubutun ba tare da na ambace ki a wannan fejin ba Takwarata Sadiya Rabi'u, Alkhairin Allah ya isa gare ki da ke da ahalinki, Ya kare ki da kariyarsa, taimakonsa, salamarsa, ya azurtaki da mafirin ciki madawwami. Na gode na gode sosai kuma ina kan yin godiya._* *_Haka dukka mabiya wannan littafi musamman waɗanda suka nuna min ƙauna wajen sanya kuɗinsu su mallaka Allah ya mayar muku da ninkin abin da ku ka kashe, ya azurta rayuwarku da albarka da kariya tare da farin ciki._* ________________________________ Tafiyata kawai na ke tun saukarmu, na bar Yaya Imam da Yaya Al'amin can baya da uban kayana a hannun su, zumuɗina da ƙosawata duk bai wuci na ganni a gida ba gaban Abbaa da Ummani. Adaidaita sahu na tsayar mana, na faɗa masa unguwar makwarari zai kai mu ya faɗi kuɗin da za'a ba shi ban tsaya ciniki ba na ce masa to, Allah ya sani bana son in tsaya ciniki ana kaza ina a'a kaza, musamman ma na kuɗin mota, ga dai shi ni ba ƴar wani ba kuma ba me kuɗi ba, amma a hakan iyayena da suka san halina a wannan fannin duk sanda za su ba ni kuɗin mota da duk iya ƙoƙarin su sai sun nema min wanda su ke ganin zai ishe ni.
Da sauri na buɗe hand bag ɗin hannuna na ɗauko dubu ɗaya da ɗari biyar da yace na miƙa masa, ba na so Yaya Imam ya ƙaraso na ɗora masa nauyi, tun da akwai kuɗin a hannuna gwara na biya, bayin Allahn nan tun da na tafi suke ta ɗawainiya da ni, ban da abin biyan su sai dai adu'an Allah yay musu sakayya da gidan aljanna. Ina tsaye jiran isowar su sai na tuna ma ashe ba guda ɗaya zamu yi ba, dole sai dai biyu, na ƙara tare wani shima ya faɗi abin da wancan ya faɗa take na basa kuɗinsa na ce su ɗan yi haƙuri ga su nan ƙarasowa.
Ni da Yaya Imam muka hau ɗaya, Yaya Al'amin da jakkunan kayana a ɗayar. Da yake Yaya Imam shi ba gwanin hayaniya ba ne shima irina ne, duk sai muka yi wani dunkum a motar, sai ma ni ɗin ce da duk na ke a cikin farin ciki na ke ɗan jan sa da hira, ina cewa Yaya sai naga garin ya sauya min, me adaidaitar da ya ke jiyo hirar tamu shi ma ya sako baki. Muna isa ƙofar gida yanda ku ka san an jefo ni haka na fito daga cikin adaidaitar, Abbaa na ƙofar gida zaune kan tabarma yana jan carbi, ya kafa ya tsare yana jiran dawowarmu, dama Yaya Al'amin sai da ya faɗa yace Abbaa fa ba zai wuce mu same shi ƙofar gida ba ko bakin layi.
Kafin na karasa ga in da yake har ya miƙe cikin tsananin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a gare shi, jikinsa har wani kyarma yake, na tafi da saurina ina duƙawa a gabansa, ƙafafunsa na kama na riƙe ina jin wani irin sabuwar ƙauna da jin ƙan mahaifana, hawaye ya cika kwarmin idona, ban san irin godiyar da zan yiwa mahallicina ba da ya bar min su a raye tsawon wannan lokacin, duk da cewa me tafiya dole tana nan zuwa, haka ban san irin godiyar da zan yi a gare shi da ya bani iyaye nagartattu waɗanda a ko ina ɗa ya shiga zai bugi ƙirji yace shi ɗan wanene ba tare da wani shayi ba, kuma jin hakan yasa a kalle ka da daraja da martaba duk kuwa da cewa su ɗin ba masu kuɗi ba ne.
"Miƙe! Miƙe mu shiga daga ciki ƴar albarka, likita bokan turai madallah, sai godiya ga lillahi".
Tuni ƙofar gidan mu ya ɗinke da jama'a ƴan kallo, yara da manya duk an yi curko curko ana faɗin ƙasar waje taje ta dawo, ta zama likita yanu, duk sai na rasa ma me na ke ji a tare da ni, kalmar Alhamdulillahi ce dai ba zan daina faɗinta ba har na kai ga kushewa. Maƙotanmu kuwa su Malam Sani da Malam Auwal duk suka zo wurin Abbaa suna masa murna nima suna min murna da sanya albarka gami da adu'a. Abbaa ya ciro ɗari biyar a aljihunsa ya kira Yaya Al'amin ya ce,"Kaga ba wa waccan me awarar ka ce ta rabawa yara sadaƙa".
"Na nawa Abbaa?". "Sadaƙa ce Al'amin na dukka zaka ce, niyyar na tare da ni da ɗiyata".
Ya karɓi kuɗin ya tafi, lokacin kuwa matar ke kwashe na cikin kasko, da yake duk magriba ana idar da sallah ta ke fitowa ta fara suya, kuma kafin ka ce wannan an siye ta tashi. Tuni har an gama kai kayana cikin gida, muna shiga daga soro na samu Ummani tsaye na doka tsalle na ɗafe jikinta, itama Allah sarki uwa sai na ji tayi ihun murna har da su guɗa wacca ban taɓa ji tayi ba tana faɗin Alhamdulillah, Allah mun gode maka, muna godiya gare ka da ka kai mana ƴar mu lafiya ka dawo da ita lafiya ka kuma bamu aron rai da lafiya ganin lokacin da bamu tsammaci zamu kai ba.
Daga cikin gida muka shiga in da duk ƴan gidan mu suka firfito, suma carko carko a tsakar gidanmu, dama dai ɓangarenmu tsakar gidan hanya ce don kowa ta nan yake wucewa ya shige sauran ɓangarorin, kowa sai taya ni murnar dawowata yake, kuma kowa ya zo bai min kallo ɗaya sai ya ƙara ya kuma ƙarawa, bayan kallon kyau har da na burgewa ganina sanye da kayan ma'aikatan lafiya. Sai ga Umman su Hindatu ta taho da tafinta tana,"Lale lale oyoyo oyoyo da mutanen ƙasar wajen, ohh ni Haule Sa'ida ke ce kika koma haka, Allah azimun wallahi kamar an canja ki, sannu da dawowa sannu sannu, shikenan abin acas cas mun yi likita a gida".
Ina ta murmushina bakina yaƙi rufuwa na rissina na gaida ita. Yaran ma duk ina murmushi muka gaggaisa da su ina musu godiya da yanda suka nuna min kulawa, sai yau na ke jin ina ma ina da ƙanne da muke ciki ɗaya.
"Sai kika ji haihuwar ƴar uwarki, na ce da Sa'ida na nan ai ita zata karɓi haihuwa". Cewar Umman su Hindatu.
Na ce,"Ai Umma ji nayi kamar nayi tsuntsuwa na taho wallahi, wai ace Hindatu ta haihu bana nan".
"To ya za'ayi, ai kun yi ɗa shima sai yanzu zai ga Babarsa".
Haka dai muka ɗan taɓa hira anan tsaye kafin taja yaranta suka koma sashen su, ina duban Ummani na ce,"Umma fa?". Tace,"Kema kin san hali, ai tun da kika tafi ta daina min magana, ko zata wuce ta tsakar gidan nan sau ɗari ƙala ba zata ce min ba, to ni dai da na fita ilimi bana fasa yi mata sallama, yanzu leƙa can wajen na ta kar dai ki jima balle ranki ya ɓaci, Aniyarta ta baƙin ciki ta tsaya iya kanta".
Girgiza kai nayi ina faɗin,"Allah ya kyauta, ita Umma ana girma rayuwa na tafiya amma tana abu kaman yarinya ƙarama, wa ya san ranar rabuwar da babu dawowa, ni kam ban jin daɗin halin nan nata".
Ashe Abbaa yana jiyo mu sai ga shi ya fito daga ɗaki yana cewa,"Kin ga rabu da ita kar ki je, idan Babanki ya dawo taci albarkacinsa. Shiga ɗakin Kakan ku ga shi can naji yana ƙwala kiran ki".
Allah sarki Kaka, ai kuwa da hanzarina nayi ɗakinsa, ina shiga na same shi kishingiɗe yana firfita, ya ƙara tsufa bawan Allah, na isa gabansa kaina rissine a ƙasa muka gaisa, ashe bama ya gani sosai yanzu dama tun ina can ake ta ce min yana fama da jinya, to da yake dai cuta ba mutuwa ba ce. Na ɗan jima a wurinsa kafin na fito na koma ɗakin Abbaa, na same shi zaune shi da Ummani, an baje min kulolin abinci Ummani na cewa,"Da duk yanda aka yi a ƙoshe kike ko, na ga ba ki halin sabonki ba na ki diro gida ki ce akwai abinci".
Gajeriyar dariya nayi ina cewa,"Kinga ai mun ci abinci a jirgi shiyasa, don ma dai na ce ba zan ci da yawa ba kar na cika cikina".
Ummani tace,"Ohh banda Allah waye zai maka, wai yau ƴar mu ce ta hau jirgi ta keta hazo, to ubangiji yanda ya kira ki tafiya ƙasar turai karatu ya kira mu zuwa ƙasa me tsarki mu ziyar ɗakinsa mu ziyar ci ƙabarin masoyi fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW".
Dukkan mu muka yi salati ga manzon tsira, na zauna ina cewa,"In sha Allahu Ummani indai saudiya ne mun kusa muje, Allah ya bani arziƙin da zan kai ku, amma tabbas a jikina ina jin lokacin ya kusa".
Ita da Abbaa suka haɗa baki wajen furta,"Ilahi ajib".
Sannan muka shiga gaisawa da su, zuciyata sai motsawa take da so da ƙaunar mahaifana gami da tausayin su da jin ƙan su, rayuwa kenan duk sun ƙara girma musamman ma Abbaa kansa duk furfura ta fara yawa, da ka gansa dai ka san shekaru sun ja masa. Ummani tace,"Ai ni dawowarki ta min hajji da umara, ga shi nan tun shekara jiya Abbanki ya siyo ganda saboda ke".
Tuni yawuna ya tsinke na matsa wajen kwanukan ina cewa,"Allah sarki Abbaana na gode Allah ya ƙara lafiya da wadata, fatan dai ba'a kwashe an rabar min ba".
Ummani na girgiza kai tace,"Au wahalar dafuwar ma da nayi ban miki gwaninta ba kenan, to bara na ɗauka na ƙarasa rabarwar".
Murmushi nayi da cewa,"Yi haƙuri Ummanin mu". Tuni na tasa kwano a gabana na fara kaiwa baka don ganda na ɗaya daga cikin naman da na ke so a rayuwata, ko da sallah ni ban fiya ma cin nama ba kamar yanda na ke cin ganda".
Da yake ba wani yawa ne da ita ba dama dai ya siyota ne saboda ni ɗin, don haka tuni na ga bayanta Ummani har na tsokanata da kura kura. Bayan na gama ci ne nake cewa,"Wai yaushe su Maman Yasmin suka yi tafiyar?".
Ummani tace,"Kwana uku da rasuwar kenan, shima Yashaik ɗin ai sai ɗazu da rana ya tafi da yace zai jira dawowarki".
Nace,"Allah jiƙan rai, naji mutuwar iya kuwa". "Da safe sai ki kirata ki mata gaisuwa, kin san ita ta yayeta".
Abbaa yace to naje nayi salloli na kafin yaje masallaci shima ya dawo, na fito sai yanzu na ke ƙarewa gidan namu kallo da yake sun kawo nepa yanzu yanzu, sai naga gidan yay min faɗi kamar ba shi ba, an dai yi masa kwaskwarima ba kamar yanda na tafi na barsa ba, duk jikin bango da ya farfashe anyi siminti, sai irin fasassun tiles ɗin nan iri ɗaya da aka lailaye tsarkar gidan da shi, yay kyau sosai wallahi, gyara yana da kyau a ƙalla ko baka sabunta ba yafi ka bar waje a lalace.
Na idar da Alwala na ke cewa da Ummani wacca ke daga cikin ɗaki,"Ummani wa ya saka tiles ɗin nan?".
Tace,"Al'amin ne wallahi, sun yi aikin gini a wani gida sai me gidan yace ma'aikatan su ɗauka su raba, shi ne bayan sun rarraba shi kuma ya ƙara siya, har fa ɗakina da na ki, ɗakin Abban ku ne kawai ba'a saka ba, yayi kyau ko?".
"Kyau sosai ma Ummani, sai ya ƙara haska gidan". "To yi dai sallar tukunna kya gyaran da aka yi, ɗakinki kamar ba shi ba".
Tsalle na ɗanyi ina murna na ce,"A'a su Yaya Al'amin anyi abin kai iyee, har da ɗakina".
Ɗakin nawa kuwa yay kyau, an yi shafe irin dai ragowa yay aka ɗan gogga, dama tun asalinsa ba fenti siminti ne shima kuma ba ko'ina ba, hatta rufin ɗakin ma an mayar da silin wajen da suka ciccire in ana ruwa ya dinƙa zuba. Allah sarki uwata ta gyara min shi gwanin sha'awa sai ƙamshin turaren wuta yake yi, ƴar yaloluwar katifata ma ta lailaye min ita da wani tsohon bedsheet ɗinta, bani da filo amma har da filo ba zai wuce ko nata ko na Abbaa ta ɗauko min ba. Allah dai ya bani ikon kyautatawa musu, ya kuma basu tsawon rai da lafiyar da zasu ci moriyata.
Bayan na idar da sallah ina ƙarasa karanta suratul yasin da iza waƙa da basu wuce ni duk dare, Ummani ta leƙo tana ce min. "Kinga da na zuba miki ruwan zafi kiyi wanka, ko ba sai kin yi ba?".
Na kai ƙarshen suratul yasin ina cewa,"Zan yi Ummani, jikina duk gajiya".
"To sai ki hanzarta kar ya huce, garwashin ya ƙare kuma bamu da wani gawayin a ajiye, gas kuwa yay tsada idan kin ganmu da shi albashi aka yiwa Yashaik".
Na shafa adu'a na miƙe ina lalubo zani na ɗaura, ita kuma sannan ta shigo tana gyara min net ɗin da aka kafa a jikin taga saboda sauro. "Wallahi Ummani gyaran nan da aka yi yayi kyau, kinga anyi dabara sauro ya rage shigowa".
"Al'amin yay dabarar, ba kiga har bakin ƙofar ya haɗa da net ba a jikin labulen, Abbanki yanzu sai yay kwanciyarsa ma babu net ba maganin sauro".
"An huta ai da cacar siyan maganin sauro kuwa, Su Yaya Al'amin an yi abin arziƙi".
Ta ɗan yi dariya da cewa,"Ke da shi idan ya shigo ya jiki, kyama yi masa Allah sanya alkhairi anje an tambayo masa aure".
Na waro ido waje ina faɗin,"Da gaske Ummani! Tab wace wannan kuwa ta ɗaukarwa kanta halin nurƙufanci". Na ƙyalƙyale da dariya ina sake faɗin,"Tab Yaya Al'amin ni wallahi ban tsammaci ma yana kule kulen ƴan mata ba, dama shiru shirun nan ki kalle su kawai, aina ya samo matar Ummani?".
"Kin ma santa ai, ina gidan Alhaji Saleh nan baya wajen gidan me markaɗe, to jikin gidan akwai gidan farare da ake cewa ana siyar da kunu da awara da safe".
Nace,"Eh eh na gane gidan, da suna markaɗe ko?".
"Ƙwarai nan kuwa, to ɓangaren da suke yin gurasa za kiji ana wajen Baaba tabawa, ai yarinyar jikarta ce ruƙonta take yi".
Bakina buɗe nace,"Ko dai wata za kiga tana biyowa Sajida tafiya islamiya, doguwa fara me ɗan jiki haka, naji kamar ma buzuwa suke ce mata".
"Ai kuwa dai ita ce, su Abbanki har wani daji acan ƙarshen katsina suka je bincike".
Ina kaɗa kai na ce,"Abbaa kenan, hakan ai yana da kyau gudun samun matsala".
Muna haka Yaya Al'amin ya leƙo ɗakin, guntuwar dariya saman fuskata na ce,"Su Yaya ashe an girma an kusa aure".
Murmushi yay yana kawo min hannu yace,"Ki kiyaye ni, ke ai na ke jira ma ki zo ki kwance jaka ki fiddo min lefena dan nauyin akan ki yake yarinya".
"Yaya baka da damuwa kai dai kayi adu'a Allah yasa na samu aiki, in dai aiki ya samu Yaya to lefe sai na maka akwatu biyu da izinin Allah, ai kafi ƙarfin haka ma a wurina, ko me nayi muku ban faɗi ba wallahi. Ga gyara nan ma kayi mana gida yay kyau mun zama ƴan gayu".
Yace,"Kin ga ma gado da kwabarta nace a kaiwa Yahuza kafinta ya siya na cika ayi mata sababbi taƙi yarda".