Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 22

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 22

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 22: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 22. Ummani tayi karaf tace,"Kaga ni fa ka ƙyale ni da wani zancen…

4,491 words

Ummani tayi karaf tace,"Kaga ni fa ka ƙyale ni da wani zancen sauya gado da kwaba, ka adana kuɗin akwai lokacin amfanin su, haka kawai na tsufa sai kace wata yarinya ace za'a sauyan kayan ɗaki".

Na fita a ɗakin ina cewa,"Ƙyaleta Yaya Al'amin ka yiwa Abbaa gudunmawa idan ya tashi ƙaro aure, ai dama naji ƙishin ƙishin ɗin sun daidaita da Rabi dillaliya".

Karaf naji saukar murfi akaina. Ina dariya sosai na shige banɗaki da gudu, bayan na fito a wanka na shirya tukunna na isa ɗakin Abbaa, ina shiga yace naje mu gaisa da Baba Sabi'u da Baba Tijjani duk sun dawo.

Sai bayan na dawo daga wurin su ne na ci abinci na ƙoshi sannan kuma aka shiga hira, ina ta basu labarin can ƙasar da yanda akayi gwagwarmayar karatu. Sosai iyayen nawa suka ji daɗin yanda ban wani wahala ko na fuskanci ƙalubale mara daɗi ba, dama ƙalubalen dai farko farko ne da ban wani ƙware da iya turanci ba to sai nayi ta jin wahalar yin magana da mutane musamman Malamai, har dai kuma a hankali da Allah ya haɗa jinina da wata Joy Johnsun take cewa haka zan ke ta gwada ko da za'a min dariya, nobody is perfect duk wanda ba yaren uwarsa ba ne to koya yay, da hakan kuma sai ga shi ko a award ɗin speech na ƴan nigeria da aka bayar ina ɗaya daga cikin mutum biyar da aka bawa kyauta, ni ce ta uku sai wani mas'ud da tare muke karatu da shi aka basa na ɗaya.

Na kunce jakata na ɗauko kuɗi na miƙawa Abbaa na ce ga shi ya riƙe, ganin yawan kuɗin sai ya saki baki yana kallona da ayar tambaya. A hankali na shiga masa bayanin cewa,"Abbaa da yake acan su kan bawa ɗalibai kuɗi duk ƙarshen wata mutum ya ɗan siya abubuwan buƙata na karatu da dai abin da mutum ba zai rasa ba, to a ciki Abbaa na ke ɗan cire wani abun ina ajiyewa har suka taru haka, don sai da wani course mate ɗina yazo nigeria na ce masa ya canja min su, da zai koma sai ya tafi min da su.

Abbaa ya mayar da ƙwayar idonsa kan kuɗin yana dubansu da jinjinawa yace,"To Sa'ida nan nawa ne kenan? Tun da na ke a rayuwata ban taɓa riƙe kuɗi masu yawan haka ba, naji su da yawa har danne hannu suke yi".

"Dubu Ɗari biyar ne Abbaa, dama na ce a ciki sai a bawa su Yaya wani abun sauran kuma ku riƙe kai da Ummani".

Murmushi me faɗi naga ya bayyana saman fuskarsa, kafin a hankali kuma ya kai hannu ya goge ƙwallar farin ciki, sannu a hankali ya shiga jero min goiya da sanya albarka kamar zai ƙarar da yawun bakinsa. Ummani kuwa ta ɗaga hannu sama tana godiya ga rabbi, faɗi take yi,"Haihuwa me daɗi, haihuwa me rana, Allah yay miki albarka wannan yarinya ya kawo miki babban rabo, ya azurtaki da mijin marainiya".

Abbaa ya miƙe ya fita zuwa ɗakin Kaka, bai jima sosai a can ba ya dawo ya zauna, bayan ya numfasa yay nisa tare da ce min. "To yanzu Sa'ida ya ake yi kuma wajen neman aiki? Ko kuwa kana zaune ake neman ka?".

Nace,"Ehh to Abbaa zan fara rubuta CV daga nan sai in kakkai muga ko Allah zai sa a dace, sannan akwai hanya ma da ake bi idan Allah ya taimake ka ya haɗaka da mutane na gari sai kaga abin ya zo da sauƙi kuma cikin aminci".

Abbaa yace,"To shi abin da kika faɗa ɗin ya ake yinsa?".

"Bayanai na zan rubuta Abbaa, kuma kaga tun da Allah yasa ma da result ɗin a hannu kuma an samu me kyau ba za'a wahala ba in Allah ya yarda".

Yay ɗan jim kafin yace,"To shikenan Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi, idan Yayunki sun zo sai muyi magana da su naji, amma ban amince ki nemi taimakon wani ko hanya ta wajen wani ba, wannan duk Yayyunki zasu miki insha Allahu, mutane yanzu babu amana ke ba ƙaramar yarinya ba ce yanzu kina da hankalin tunani, idan kika rubuta shi bayanan duk ranar da za ki je kaiwa wajen ɗaukar aikin sai kiyi min magana mu tafi tare, Allah ya taimaka ya ƙara tsare mana ke da mutuncinki".

Na amsa da amin, mun jima muna ta hira da su don har sai ƙarfe sha ɗaya tukunna na baro ɗakin Abbaa, ina shiga ɗakina kuwa sai bacci, yau ko sallar dare ma ban samu damar yi ba sai da ana sallar asuba na farka shima da ƙyar, don har Abbaa ya tafi masallaci ban iya miƙewa ba, dama shi kafin ya tafi sai ya buga mana ƙofa ni da Yaya Al'amin har sai mun tashi mun buɗe kafin ya wuce.

Kwanana huɗu da dawowa Abbaa yace na shirya muje can ƙauye, ni da shi muka je ƙauyen su da na su Ummani muka gaggaisa da ƴan uwa sai da muka kwana biyu muka dawo. Muna dawowa kuwa a washegari na dire a gidan Safiyya da yake itama anan Kano take Nasarawa GRA, mijinta me kuɗi ne ɗan siyasa Babba da ake damawa da shi a wannan gwamnatin. Shekarata biyu a germany aka yi bikin har kusan kuka nayi a lokacin, na so ace ina nan aka yi bikin Safiyya, lokacin nawa tarewa tayi a gidanmu itace akan komai nawa.

Gidanta masha Allah kamar ba a kano ba, kuma Allah ya bata mijin marainiya, yana mugun sonta sosai, ko da ta haihu sunanta ya sakawa ƴar suke ce mata Ilham, to da ke ma dai ƙawarta sai a hankali halinta sai ita tsiya take tsula masa son ranta, Ummansu tana faɗa min tace in ke bata shawara ina yi mata faɗa don ita har ta fara gajiya da halinta. Na dai bata shawara matsayina na amiyar ƙwarai, sai take ce min ita wallahi ban da mahaifanta auren nan ba yinsa zata yi ba, ita soyayyar duk da yake mata ba wani yarda tayi da ita ba saboda tun abun da ya faru akaina take tsoron sharrin kowanne namiji, na ce mata to ai ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, tayi ta adu'a kawai Allah kar ya kawo abin da zai canja daɗin zamantakewar aurenta.

Ranar yini nayi muna shafta ni da ita, don har magriba, zance daya sai ta kama min zancen fitar da mijin aure tunda na gama karatu, yanzu ko aure nayi karyar namiji yace zai wulaƙanta ni, haka nayi ta bagarar da zancenta har ta haƙura ta ƙyale ni, don ko a gida Ummani sai tayi ta cewa,"Karatu ya kammala, Allah kawo aikin yi da mijin marainiya".

Yi na ke kamar ban jita ba idan ta faɗi hakan, Abbaa kuwa kamar zuciyarmu ɗaya, tun da na dawo banji ya ambata min kalmar miji ba, sha'anina kawai ya barni na ke yi babu wani takurawa, don sai in ce abinda na ke a yanzu ban yisa lokacin ƴan matancina ba.

Ga shi dawowata zuwa ake ko da yaushe maneman aure ta ko'ina, ni kuwa nayi mirsisi naƙi fita ko idan Ummani ta lallaɓa ni naje soro na sha zamana tukunna in dawo, ni sam aure ya fita kaina bana fatan ma na sake maimaita shi, na ƙwammaci na mutu da na kara yin aure. Abbaa ba ya sauraron duk wanda ya zo wajensa, sai yace shi a bar masa ƴa ta sarara ai ba a gidan ruƙo take ba balle a ƙwazzafeta.

Haka mu ke ta sana'armu ta siyar da zoɓo da kunun aya ni da mahaifiyata, ga awara ma da na ke yi ƴar order da mutane ke sawa, a rana sai nayi ta dubu biyar sama, masu siyan ma duk yawanci Safiyya ke haɗa ni da su, Maman Khairi zata siyar da firij ɗinta Yaya Imam yace to ya siyawa Ummani tunda ana samun wuta sosai, yafi ayi ta faman siyan kanƙara ko da yaushe. Sana'ar ɗinkina kuwa ba kama ƙafar yaro, gowns na ke ɗinkawa ina ɗorawa a jiji app da instgram, Allah yasa min nasibi a nemana ko da yaushe sai nayi ciniki, kafin na fara ɗora kayan sana'ata sai naja lahaula wala ƙuwwa ƙafa goma tukunna, wannan sirri ne da duk wanda ya riƙe a kasuwancinsa zai sha mamaki.

A gefe ɗaya kuwa Abbaa yasa Yayyuna suna ta fafutukar nemar min aiki, Yashaik ya rabawa mutanensa takarduna sun fi biyar, Yaya Imam ma da nasa jama'ar, shi kansa Abbaa sai da yace na basa file guda biyu ko da wataran a kasuwa zai ji ana hira tun da akwai ƴan harkar siyasa da yawa kusa da teburin su. Ta ɓangarena dai ni babu wani motsi da na ke yi, kawai dai naga su sun tsaya akan lamarin da iyaka ƙoƙarin su sai na barshi na san inda rabo za'a dace.

Ana haka wataran da daddare muna zaune a tsakar gida ni da su Abbaa, har da su Yaya Imam ma da yake duk dare idan suka dawo daga wurin aiki kafin su tafi gida sai sun zo nan sun ɗan jima a wajen iyayensu kana su tafi wurin iyalin su, ana hira Abbaa yana bamu labarin rayuwarsu ta da, ni kuma ina zancen idan na samu kuɗi shagon siyar da kaya zan buɗe, na nunawa Abbaa bidoyin whatsapp na irin yacca mata ke ta buɗe shago, aikuwa kowa ya ƙarfafa min gwiwa da tayani adu'a, Abbaa dai yace ba zai hana ni ba tunda neman halalina ne amma tare da Yaya Al'amin zamu ke zama a ciki, kamar kuma ya shiga zuciyata ya ga abin da ke ciki.

Wayata ce tayi ƙara, na ɗauka ina duba saƙon da ya shigo, kasantuwar datana a buɗe yake sai nayi gaggawan shiga email ɗin na duba, abin da na gani shi yasa ni ƙara tare da dire wayar ina ɗaga hannu sama ina faɗin Alhamdulillah, sai duk hankalinsu yayo kaina nima na maida hankalina gare su ina Kallon Abbaa tare da miƙa masa wayar na ce.

"Abbaa wani asibiti ne suke nemana naje interview jibi".

Yashaik ya miƙo hannu yana faɗin,"Mu gani".

Na basa suka shiga dubawa shi da Yaya Imam, lokacin kuma wani saƙon ke ƙara shigowa ta text message duka dai daga asibiti ɗaya. Ai fa kowa sai murna tare da adu'an Allah sa a dace, Kaka bawan Allah sai ga shi ya rarrafo daga ɗaki yana dogara sanda ya fito shima aka hau murna da shi. Bayan kwana biyu kuwa na shirya da wuri don ƙarfe takwas suka rubuta cewar naje, Daren ranar ban rumtsa ina ta gayawa Allah haka iyayena ma, ƙarfe shida da rabi muka bar gida ni da Abbaa wai gudun kar mu makara azo a samu asara, ni dai da muka je baki na saki ina kallo, to asibiti babba haka na masu kuɗi wa ya kawo ni?.

Ina duban Abbaa na ce,"Anya kuwa nan ne?".

Abbaa ma dai shima da kokonto cikin ransa yace,"Ɗauko takardar da kika curo".

Na fito da ita na ba shi, yace,"To ai sai dai mu shiga tare mu tambaya kinga ba lallai suna jin hausa ba ko?".

Da wannan dan wannan kam, muka shiga tare ya dakatar da wani dattijo yay masa sallama suka gaisa, hausar tasa dai bata fita sosai don haka da ni muka ƙarasa magana cikin harshen turanci. Ya tabbatar mana da nan ɗin ne yanzu haka ma ai an kusa fara interview ɗin nayi sauri na shiga kar layi yay yawa, Abbaa yace to idan ba rabo na ubangiji ba Sa'ida wannan asiti ai sai kallo daga nesa.

Nan ya zauna daga waje yana jirana, suka zauna tare da wancan mutumin. EHA Clinics Kano sunan asibitin anan Lamiɗo Crescent yake. Tsawon kwana biyu na ɗauka ana min gwaji wani babban likita ne me zaman kansa kuma bature ne ma, yawancin Drs ɗin duk turawa ne, nurses ɗin kuwa ƙalilan ne waɗanda suka yi karatu a nageria suma kuma duk ƴan private school ne. cikin ikon Allah kuma duba da ƙwarewata da ƙwazona suka tabbar da cewar sun ɗauke ni aiki tare da su, duk wata za su ke biyana dubu ɗari da casa'in.

Ni dai abun tamkar a mafarki haka naji jin salary amount ɗina, Cikin sati guda na fara zuwa aikin, Abbaa bai yarda da batun night duty ba don ce yay indai zan ke aikin dare to gwara a haƙura da aikin, ya saɓi ƙafa shi da Yaya Imam suka je har can suka ga managern wurin, ya roƙe shi yace masa suna son aikin amma in dai zan dinga aikin kwana to gwara na haƙura, amma idan sun yarda aiki ko ce suka yi na fito da asuba to shi zai rako ni ma kafin lokaci, ya yarda na yini acan ɗin amma shi ban da dare, da haka aka tsara roster ɗin morning and evening duty da ni banda night.

Sai da na jera sati guda Abbaa na raka ni kullum kuma idan lokacin tashi yayi shi zai je mu taho tare, har sun saba ma da mutanen asibitin, hatta managern kansa idan yaga zuwan Abbaa sai yace ya shigo daga cikin office ɗinsa. Watan farko da na ɗauka albashina jiki na rawa na tafi na curo su, ɗari da casa'in cass kuma babu lissafin kuɗin mota da na abinci, suke bamu na mota duk sati abinci kuwa Ummani dafa min take na tafi da kayana. Naira dubu hamsin na cire na damƙawa mahaifiyata, na zare saba'in na damƙawa Abbaa, na kara cire arba'in na bawa Yaya Imam da Yashaik ashirin ashirin, Yaya Al'amin na ba shi goma sha biyar, na cire biyar na bawa Kaka shima, sauran goman kuwa na kaiwa Baba Tijjani da Baba Sabi'u, naira biyar ban sha'awar naci ba a ciki, don tun ranar da na samu aikin na gama kasafin kuɗin.

Aikuwa tsabagen adu'a da albarkar da aka dinƙa sanya min a cikin gidan nan sai da nayi kukan farin ciki. Har da su Umma aka zo ana taya ni murna nayi ta mamaki, na ce wato idan kana da shi sai ayi da kai, idan baka da shi baka kai ba ɗan iska kawai kake. Ummansu Hindatu ma kanta sai da ta faɗa tace,"Ai ko bata so ki don Allah ba yanzu ta soki don abin hannunki, kiga dai tun da kika dawo fa bata saurareki ba".

Ummani tace,"Allah dai ya kyauta kawai". ______________________________ *_Tambayar da zan yi muku, duba da irin rayuwar da Sa'ida ta fuskanta a gidan tsohon mijinta, mu ɗauki matsayin hakan a zahirin rayuwa, babu yanda ubangiji ba ya lamarinsa, shin kuna ganin ubangiji zai iya ƙadartawa ta komawa Nazifi? A bar shi wataƙila yay nadamar abubuwan da ya aikata, sannan yana cikin hali na a tausayawa masa duk da bamu da tabbacin hakan don yanzu bamu san wacce rayuwa yake ciki ba, ko kuma ace ma Allah ya barsa da dukiyarsa amma kuma yay danasani da nadama yana neman dawo da Sa'ida gidansa, kuma mu ƙaddara wataƙila yana da sa hannu a wancan ɗawainiya ta karatunta, haka itama ɓangaren Sa'idan ta zaɓi komawa gare shi...idan hakan ta kasance ya zamu ɗauki al'amarin dukkan mu? Ko ma dai a ganinmu kwata kwata lamari ne da ba zai fara somuwa ba? Kuma a tsumayinku da tunaninku wanne kalar miji Sa'ida zata ƙara aura tun da dai ba zamu so ta ƙare rayuwanta a zaman zawarci ba....ina jiran jin ra'ayoyin ku akan hakan_*

[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR02FT5* Ƙaramin yaro ya shigo gidan yana cewa,"Salamu alaikum a bada zoɓo".

Ummani da ke daga cikin ɗaki tace,"Ana zuwa". Ta fito daidai lokacin tana tambayarsa,"Na nawa?".

"Na ɗari, wai don Allah a bada na roba me kyau".

Tayi murmushi tana cewa,"Ai duk masu kyau ne". Tana saka masa cikin leda wani yaron ya kuma shigowa yace,"Akwai kunun aya?". Tace,"Babu sai gobe idan Allah ya kaimu".

Ta sallami me zoɓo Kaka yace mata,"Me yasa ba ku yi kunun ayar ba bayan kun san anfi son sa".

Tace,"Jiya ne Sa'ida ta dawo a gajiye bata samu damar yi ba".

"To amma ke da ba sai kiyi ba". "Kaka hannun jikar taka sirri ne da shi, akwai zaƙin hannu idan tayi wallahi yafi nawa daɗi".

Kitchen ta shiga ta ɗauko abinci a ƙaramin filas tace da Kaka,"A shigar maka da shi cikin ɗakin ko anan zaka ci?".

Ya gyara zama daga kishingiɗen da yake yace,"Bar min anan cikin ɗakin zafi, nepa sun hana wuta yau".

Ta ajiya masa ta ɗauko ruwa ta aje masa, shi kuma yana ta saka mata albarka don shi kansa kaf matan ƴaƴansa yafi son Ummani, a ko da yaushe yabonta yake yi domin ita ɗin macece ta ƙwarai, yanda take masa tamkar shi ya haifeta. Yashaik ya shigo gidan, a nan tabarmar da Kaka yake ya zauna suna gaisawa, kafin daga bisani ya miƙe ya shiga ciki wurin mahaifiyarsa.

Samunta yay ta fito da kayan sif ɗinta dukka tana linkewa, daga gefe ya zauna yan agaishe da ita ta amsa tana tambayarsa ya iyali. "Me makon ki aika a kira miki Maman Yasmin, yanzu ina ke ina aikin ninkin kaya masu yawa haka".

"Ku dai kun fi so kuyi ta gani na kwance sharaf wuri ɗaya bana aikin komai, haka kawai kuma yarinya na can gidanta tana aikinta sai na aika a tasota, a'a kayan nawa suke gaba ɗaya yanzu zan gama ai. Yau babu in da kaje kenan?".

Ya sauke numfashi yace,"Ban leƙa ko ina ba, gani nayi gwara in ke hutawa lahadin jiki na buƙatar hutu".

"Haka ne, Allah daɗa rufa asiri. Jiya naji ka ce zaku yi magana da Abbaan ku sai ban ga ka dawo ba shiru, ba dai wata matsalar ba ce ko?".

Ya kai hannu yana shiga tayata linkin kayan yace,"Da na ƙyale ne kawai saboda na san ko naje masa da zancen ba karɓa zai yi ba, wataƙila ma raina ya iya ɓaci, sai dai ko ke za ki faɗa masa".

Ummani ta mayar da hankalinta kansa sosai tace,"Menene fa?".

Yace,"Ba fa matsala ba ce". Ya faɗa yanda yaga mahaifiyar tasa ta kafe shi da idanu.

"Dama akan Sa'ida ne ban san me Abbaa ke hange ba da yaƙi bawa zaurawan nata dama, haka kuma gaba ɗaya bai son zancen auren nata ba, amma ni gani na ke bai kamata a biye mata ba, duk da cewar dole auren ya sire mata, amma ai ba zamu ɗauka cewa lallai abin da ya faru a farko shi zai kuma faruwa ba ko kuma yayta maimaituwa, kawai ta ɗauka hakan matsayin jarabawarta ba wai saboda dalilin hakan kuma tace ita ba zata ƙara yin wani auren ba. ita macece ko ai na take ko me take yi duk matsayin da take da shi da aurenta tafi daraja a idon duniya, kuma ku kan ku idan da aurenta hankalinki zai fi kwanciya, kuma sannan shekaru tafiya suke ta yi gaba ba dawo baya zasu yi ba, nan da wata shekarar magana ake ta zata shekara talatin idan da rai da kuma lafiya, to ta gama karatun ta samu aikin yi me za'a ƙara jira Ummani? Baka biyewa maganar mutane balle ta dameka amma ana gudun baki, wani bakin kaifi ne sune masu kambun baka, ni gaskiya na fi ga sha'awar tayi aurenta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ta dage da adu'a kawai Allah kar ya maimaita mata irin mijin baya".

Ummani ta numfasa tace,"Ni kaina da ka ganni wlh yanzu hankalina yafi ga tayi auren, Sa'id idan ta fita aikin wannan wallahi sam sam bana samun natsuwa har taje ta dawo hankalina ba'a kwance yake ba, amma lokaci ne duk dai Abbaan naku na daƙile damar hakan, Allah dai ya kawo mata na gari ya musanya mata da mafificin alkhairi".

"To amin ya Allah. Kuma dama Nura ne yay min magana ɗazu da safe yace abokinsa Ya ganta yace idan ba'a tsayar da maganar wani akanta ba ya gani yana so".

Ummani tayi murmushi me faɗi tace,"Allah sarki, ai na yake to?".

"A can garejin ma su yake shima, kin sansa ma sai dai ba za ki gane shi ba, amma da sallah ƙarama tare suka zo da Nuran ai".

Tace,"To madallah, ai ina ga sai kace masa ya tunkari Abbaan na ku da maganar ko, ya gwada tasa sa'ar ko a kansa dacen yake".

"Ehh to dama ni abin da ma yasa ban masa maganar so na ke na fara bugar cikinta naji ko tana da ra'ayin auren me ƴaƴa".

Ummani tayi gajeriyar dariya tace,"To ita wanne zaɓin saurayi ne da ita yanzu, sai dai kuma wani lamarin na Allah, fatan dai Allah bata wanda yafi wancan".

Da haka suka ci gaba da hirarsu akan maganar Al'amin ma da za'a kai kuɗin aure cikin satin nan, har sai da suka ninke kayan dukka. Shi ya share mata ɗaki ya goge ko ina, yay mata sharar tsakar gida da kitchen suma duk sai da yay mopping, dama sun saba hakan shi da Imam duk sanda suka sameta tana aiki, don shi da yake kusa da suma da sassafe yake zuwa yay sharar soro da ƙofar gida. Bayan tafiyarsa yana zuwa gida kuwa ya aiko mata Yasmin wadda ta shigo tana ta ƙunci wai Kawu yace ta zo tayi wanke wanke.

Da yamma yaro ya shigo tsakar gida yana ta doka sallama babu wanda ya amsa, Ummani na daga cikin ɗaki a kwance kamar a mafarki taji sallaman wajen ƙofan ɗakinta, tayi saurin tashi tana cewa,"waye ne?".

Yaron yace,"Ai ko ni aka yi, wai ana sallama da me gidan".

Labule ta ɗaga ta leƙo tana cewa da shi,"To masu gidan ai da yawa, kaje kace wa ake nema?".

Ba jimawa ya dawo yana cewa,"Wai Malam Salman".

Ummani tace,"Tooo wallahi ba ya nan, amma kace musu yana kan hanyarsa ta dawowa ko zasu jira shi, suna da yawa ne?".

Yaron yace,"Ehh mota biyu ce har da sojoji".

Gaban Ummani ya yanke ya faɗi ya bada rasss, tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin,"Sojoji kuma ɗan nan? An ya ba makuwa ka yi ba kuwa, ko can ɗaya gidan aka aika ka kusa da me kayan miya".

Yace,"A'a ni dai nan suka ce min". "To shikenan je ka kace musu bai dawo daga kasuwa ba sai dare".

Yaron ya juya ya fita ita kuma ta dawo cikin ɗaki, ta kasa zaune tayi tsaye tana tunanin lafiya? Me zai kawo sojoji neman Abbaan su? Sai tayi maza ta ɗauki wayarta ta yiwa Sa'ida flashing, Sa'ida ta biyo bayan kiran, ta ɗaga tana ce mata,"Ke sako min kati zan kira Abban ku".

Yanayin fitar muryan nata yasa Sa'ida cewa"Lafiya Ummani?". "Lafiya lau sauri sako min zan ba shi sallahu ne a kasuwa kar ya riga ya taho".

Within one minutes sai ga shigowan katin ɗari biyar a wayar, ta lalubo sunan Abbaan Sa'id ta kira. Abbaa a lokacin na bakin titi ya ɗaga kiran wanda hayaniyar ƙarar ababen hawa bai barin sa yaji me take cewa itama ɗin kuma bata jinsa sosai, haka tayi ta faman kira ƙarshe sai haƙura tayi, ta fito tsakar gida ta zauna tayi jugum, har sai da ta leƙa ƙofar gidan taga tabbacin maganar yaron, soja ɗaya na tsaye bakin mota da bindiga a hannu, wannan fa yasa ta daɗa tsurewa ta kama safa da marwa a tsakar gida tana ta faɗin Allah sa lafiya.

Bayan kusan rabin awa sai ga Abbaa ya shigo gidan a gaggauce yana ƙwala kiran,"Sa'a! Sa'a! miƙo min babbar tabarma maza maza".

Irin yanda yake ƙwala kiran bana lafiya ba, Ummani ta fito daga ɗaki fuskar hijabi a juye jiki duk sai ɓari yake yi, ganin yanda Abbaan yake shima da ruɗani ta tsaya tambayan,"Abbaa lafiya? Kaga baƙin ƙofar gidan ne kaima?".

Bai amsa mata ba yaci gaba da ɗauraye ƙafarsa da duk tayi ƙura tare da wanke fuskarsa ma. "Ni dai sauri miƙo min tabarmar tukunna, ni kaina ba na ce miki lafiya ko ba lafiya ba Sa'a, amma hankalina duk ya tashi".

"Abbaa to kaje wurin su kuwa? Ko na aika a kira Yashaik yau yana gida bai fita ba".

"A'a ƙyale su Sa'a, bara na fara jin me ke tafe da su sun ce sun jima waje, maza miƙo min tabarmar dai, kin san irin mutanen ba'a barin su da jira".

Ganin ta tsaya kawai ya wuceta yay ɗakinsa ya buɗe ya yayibo tabarma ya fito yay waje da hanzari, duk ya rikice tafiyar tamkar zai kifa ƙasa. A soro ya baza ƙatuwar tabarmar, takalamansa ma a baibai ya saka ya leƙa yana ce musu,"Bismillah ku shigo daga ciki".

Zatonsa iyaka waɗannan sojoji biyun na waje ne sai yaga an buɗe mota manyan mutane dattawan arziƙi suna fitowa, da kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka shaida duniya ta san su ta san da zaman su, matsayi kuma an same shi sai wanda ake kan rabawa, kuma masu faɗa ne aji a ƙasar da suke ciki. Sojojin na basu kariya har suka shigo soron wanda duk Abbaa ya daɗa hargitsewa yana duban tabarmar da duk ta ɗan sha jiki, da shi kansa soron gidan wanda yake ganin sun girmi su ko rakuɓe a cikinsa balle zama.

Sai dai ga mamakinsa babu wani yanayi na ƙyama ko jin kai a tare da su, duk sai yake jin wani iri, bai taɓa yin baƙo yana jin ya ƙasƙantar da shi duba da irin muhallinsa ba sai waɗannan mutanen.

"To ko kujera za a samo muku?".

Ɗaya daga cikin su yace,"A'a babu komai Malam, ai nan ɗin ma Alhamdulillahi ya isa, ga shi duk mun zauna, muna godiya da karramawa".

Sai da duk suka gama zama sannan ya zauna yana mai fuskantarsu, ya ranƙwafa kamar bafaden sarki, da firgicin da ke tare da shi ya shiga miƙa musu hannu wanda a farko sai da yaji shakkar hakan, sai kuma yaga saɓanin fa yanda yake tunaninsu ne domin da kansu suka miƙo masa nasu suna gaisawa da girmama junansu da kuma mutuntawa. Cikin wani yanayi Abbaa da bai taɓa shigansa ba yake kallon tsohon mutumin da ke cewa da shi,"Da ka natsu naga duk ka dabarbarce da ganin namu".

Abbaa yace,"To ai ranka ya daɗe ganin mutane irinku dole mutum ya shiga irin wannan yanayin na ruɗani, ni dai fatana Allah yasa lafiya, Allah yasa lafiya don cikin gida ma kanta iyalina a tsaye take".

Alhaji Sama'ila ya murmusa yana duban Abbaa da kyau yace,"Kar ka samu damuwa lafiya lau, Alkhairi ne ya kawo mu gare ka, saboda haka ka bar tunanin ko ba lafiya ba ne".

Sai sannan Abbaan ya samu ya ɗan sauke ajiyar zuciya ta salama yace,"To masha Allahu, bara a miƙo muku ruwa".

Ya yunƙura zai miƙe sai ga wani baƙon ya shigo, Abbaa ya kalle shi cikin faɗaɗa fara'ar fuskarsa yay saurin miƙewa yana miƙawa Baba hannu yace,"A'a Alhaji Babangida kai ne da kanka a gidan nawa, barka da zuwa".

Baban su Safiyya shima cikin fara'ar da ke wadatuwa saman fuskarsa yake cewa da Abbaa,"Malam Salman ka ganni kwatsam ko, to ya za'ai zuwa ya zamar mana dole".

"Wallahi fa, kar dai kace min tare ku ke da waɗannan bayin Allah'n?".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull