Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 23

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 23

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 23: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 23. Baban su Safiyya yace,"Tare muke da su, da yake ni uzuri ya ɗan…

4,486 words

Baban su Safiyya yace,"Tare muke da su, da yake ni uzuri ya ɗan riƙe ni a hanya ne shiyasa suka riga ni isowa, tafiyar ai tawa ce ma gaba ɗaya, na ke ce musu ai gida muka nufa su isa kafin na ƙaraso".

Baban su Safiyya ya nemi waje ya zauna yana magana da jama'arsa, yayin da Abbaa ya shiga daga cikin gidan yana kiran sunan Ummani a hankali saboda ana iyo jiyo maganar tsakar gida daga soron. Ummani kuwa na kitchen a lokacin ta rafka tagumi tana jinsa ta taso da sauri tana buɗa masa hannu alamun ya ake ciki.

"To bana ce ba amma dai sun ce lafiya lau alkhairi ya kawo su, don tafiyar ma har da Alhaji Babangida".

"Alhaji Babangida dai?". "Baban yarinyar nan ƙawar Sa'ida, bani sunanta nan, yauwa Safiyya".

Ummani ta sauke nauyayyan numfashi da cewar,"Ohhh har na samu Sa'ida amma da hankalina duk ya tashi ina ta tunanin me zai kawo mana sojoji wajenka, don wallahi har na fara zargin ko matsalar rumfar nan ce".

Yanayin fuskan Abbaan dai gata nan yace,"Samu faranti ki zubo lemu da ruwa".

Ummani ta koma kicin ta ɗauko farantai guda biyu, shi kuma Abbaa ya shiga ɗakin Sa'ida inda firiji ke ajiye ya kwaso kunun aya da ruwa. Yasmin ta shigo Abbaan ya bata faranti ɗaya yace ta kaiwa baƙin waje, Ummani kuma na cewa da shi,"To ai kai musu waɗancan kofunan robar kuwa? Da dai an bar musu a jarkunan? Ko na aika Yusra ta bada kofunan tangaran ɗinta".

"Bar shi akai musu hakan ai sun san inda suka zo". "To shikenan Allah sa khairan ɗin da gaske".

Ta faɗa tana bin bayan Abbaa da kallo har ya fice. Kafin ta shiga daga ɗaki tana cewa bari ta kira Sa'ida ta faɗa mata ko zata siyo kofunan ƴan gayu a hanya saboda zuwan manyan baƙi irin haka, ranar nan ma haka ta zo da ma'aikatan asibitinsu duk sai taji kunya saboda irin farantin da aka zuba musu abinci, to da yake dai baka kunya da matsayin da Allah ya aje ka.

Abbaa ya zauna suna ƙara gaisawa da juna, bayan an taɓa ƴar hira tsakanin Abbaa da Baban su Safiyya sai Alhaji Surajo ke cewa,"Tom Babangida kayi masa bayanin me ke tafe da mu ko".

Baban su Safiyya na jijjiga kai yace,"Ƙwarai haka ne, bama biyewa hirarmu da ba zata ƙare ba, zumunci yay ƙaranci wai don ma Allah ya haɗa kan ƴaƴan namu sunata na su zumuncin".

Abbaa yace,"Wallahi fa Alhajin Allah, da sai a wuce shekaru masu yawan gaske ma ba'a gaisa ba ko ta wayar, zumuncin zamanin sai adu'a sai mutum yayi da gaske zai samu ladansa".

Baban su Safiyya ya numfasa kana ya dubi Abbaa yana yi masa nuni da babban mutumin da ke tsakiya me cikar kamala da dattako, wanda Abbaa zai iya cewa dama tun zuwansu yaji mutumin ya cika wurin da haibarsa, kuma yana da tabbacin ƙamshinsa ne ya gauraye dukka wajen tun daga ƙofar gida har cikin gida.

A hankali Baban su Safiyya yace,"Malam Salman wannan shi ne Major Sadiq Oluwa Ibrahim, Yayar Matata ne uwa ɗaya uba ɗaya domin a wurinsa ma na karɓi auren ƙanwarsa, na kusa da shi kuma kusan mahaifi ne a wurinmu sunansa Captain Adebisi Oluwa...waɗannan kuma duk da kake gani abokai ne sai wancan". Ya faɗa yana nuni ma Abbaa da na kusa da shi yace,"Shi ƙane ne a wajen Major, sunansa Alhaji Mukhtar Oluwa".

Abbaa yana ƙara rissinar da kai yace,"To masha Allahu, madallah dukkanku ina ƙara yi muku maraba, ayi haƙuri dai da irin wajen da aka samu".

Captain Adebisi yace,"A haba dai haba dai muma duk irin namu muhallin kenan".

Baban su Safiyya ya ƙara cewa,"To Malam Salman abin da yake tafe da mu muhimmin abu ne, magana ce babba, kuma alkhairi ne ya kawo mu gareka, sai dai bamu san a yanda zaka karɓi al'amarin ba, duba da cewa mun sake dawowa ne a karo na biyu da buƙata iri ɗaya, amma a wannan karan muna fatan samun karɓuwar tayin mu saɓanin baya da bamu samu karɓuwa ba".

Abbaa yace,"To Alhajin Allah a ɗan warware ni ko, an saka ni a duhu". Ya faɗu haƙoransa a waje fuskarsa washe da fara'a.

Major Sadiq wato Sir kamar yanda ƴaƴansa ke kiransa yay nisa tare da numfasawa, yana daɗa kallon fuskar Abbaa da ke kama da ta Sa'ida sak wadda ya gani a cikin jirgi ranar da zasu kaita makaranta, kafin ya fara magana a cikin birkitacciyar hausarsa ta yarabawa yace,"Ammm Malam Salman mun zo wurinka ne a dalilin Yarona, wato dai mun zo nema masa auren ƴarka da ya gani yake so, idan ba'a rigada an tsayar mata da mijin aure ba shi yana da buƙatar aurenta, aure nan kusa ba tare da anja lokaci ba".

Abbaa ya ɗaga kai a karo na biyu yaywa Major kallo na ƙurulla, sai kawai yaji kwarjinin mutumin ya dake shi, haka kuma nauyinsa ya kama shi, yay saurin ɗauke ƙwayar idonsa akansa yana me ƙara sunkuyar da kai ƙasa yace,"Ina sauraronka Ranka shi daɗe".

Major yaci gaba da cewa,"My son Salim na ɗaya daga cikin manema auren ƴarka a shekarun baya masu yawa da suka wuce, to kuma sai ubangiji ya ƙadarta cewa ba zata zama matarsa ba a wancan lokacin, shi ne a wannan karon ya turo mu gare ku da ƙoƙon bararsa yace a taimaka masa idan har wani bai riga shi ba".

Kan Abbaa ya ɗaure, kafin ya kalli Baban su Safiyya yace,"Alhajin Allah ni ai har yanzu na kasa shaida ɗan namu da kuke magana akai".

Baban su Safiyya yace,"Ehh to da yake a wancan karan ba mune muka zo ba gaskiya, amma ai ba zaka mance yaron da ya kawo kuɗin aure daga baya kuma aka karɓa da cewar ba zai iya jiran yarinya ta kammala karatun da aka ce masa ba, wanda kuma hakan ta faru ne duk ba da son ran zuƙatan kowa ba musamman shi yaron".

Abbaan yayi ƙayattacen murmushi da cewa,"Na tuna, na tuna hakan, to amma shi da yay wancan magana a lokacin baya ai ce na ke an wuce babin...".

Sai yay shiru kamar yanda duk suma suka yi shiru suna kallonsa. Zuciyar Major cike da fargaba da zullumin kar su ƙi amsar tayin su, don shi kansa ya kwaɗaitu wa ɗansa auren Sa'ida. A lokacin ne kuma aka yi kiran sallar magriba, don haka duk suka miƙe Abbaa ya shiga gida Ummani ta zuba ruwa a buta guda biyu ta ba shi ya fita da ita, ta aika Yasmin wurin Umman su Hindatu ta ƙaro buta aka ƙara musu kafin Abbaan ya dawo ya karɓa masu sallaya, ita dai Ummani ganin yanayinsa na yanda yay sanyi kamar jikinsa ya mutu sai duk ta shiga damuwa da fargaba, tana tayi masa magana ma bai tsaya ya saurareta ba.

Don haka da sauri ta ɗauka waya ta kira Yashaik tace idan yana gida yay sauri ya leƙo gidan. Ko a wajen sallah ma babu yanda Abbaa bai yi ba akan wani cikin su ya ja su sallar suka dage masa akan lallai shi ne zai ja su, haka yaja su sallar bayan sun idar kuma suka komo soron suka zauna, Abba ya amso fitila a cikin gida ya saka musu saboda soron yayi duhu a lokacin.

Bayan zaman nasu Alhaji Mukhtar yace,"Malam Salman na san kana tunani ne akan abun da ya faru a baya ko, to idan wannn ne kar ka damu, wallahi tallahi ko a baya Salim ba ya janye maganar aurensa da ƴarku ba ne saboda dalilin da aka faɗa, hasalima danne zuciyarsa yay ya haƙura a babu yanda zai yi saboda nuna masa da tayi na bata sonsa, shi kuma bai zai iya auran macen da bata sonsa ba, yana ganin idan ya nace aka yi auren zaman ba zai yi musu daɗi ba, saboda wannan dalilin a lokacin ya zo ya same ni muka yi magana ya faɗa min duk yanda suka yi da yarinya har ma ya fahimci akwai wanda ita take so, amma bai karɓi kuɗinsa don yay wulaƙanci ko tozarci ba, kum ahatta maganar da akayi a lokacin na cewa ya samu wata matar wallahi a lokacin babu wannan zancen anyi hakan ne duk don samun mafita".

Abbaa ya sake jinjina kai kafin yace,"To da wannan da wannan, don bayanin da ka min yanzu shi ne nake so na tambaya. Sai dai duk da haka akwai wani hanzari ba gudu ba, ƴata ba budurwa ba ce yanzu bazawara ce ita, wataƙila kuma bai san da hakan ba ne".

Baban su Safiyya yace,"Ya sani Malam Salman, ya san komai, sannan shima ɗin ba wai saurayi ba ne da aurensa, bayan aure ma har da arziƙin yara uku...". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR03FT5* Abbaa yay shiru yana nazarin kalaman na su, ba zai ƙi tayinsu ba, domin shi kansa ko a wancan lokacin Salim ya kwanta masa a rai, yafi gamsuwa da shi fiye da duk waɗanda suka zo neman auren Sa'ida, shiyasa ko a lokacin ya yarda ya amince aka karɓi kuɗinsa bisa sharaɗin da ya gindaya na cewar sai ta kammala makaranta, kuma ko a sanda suka zo karɓar kuɗin su bai ji daɗi ba fiye da adadin kalmomin baki, ba wai rashin jin daɗi na sun wulaƙanta su ba kan karɓar kuɗin ba, a'a rashin jin daɗin Ƴarsa ta rasa yaron kirki, yaro me nagarta kamar Salim, yaga haƙiƙanin soyayyar ƴarsa a ƙwayar idon yaron, haka ya tsinci raunin rasata a muryarsa, kuma gamsu ɗari bisa ɗari da irin shaidun da mutane suka yi akansa, ba tare da sanin iyalinsa da kowa ba ya ɗauki ƙafa yaje har garin Anambra state domin yayi kyakykyawan bincike akan yaron da iyayensa kuma duk suka samu shaida mai kyau, dama tsoronsa ɗaya bawa ƙabila auren ɗiyarsa.

To a lokacin da ace shi irin mahaifin da ke tilastawa ɗiyansa abin da yake so ne ko da basa so, to da lashakka Sa'ida bata isa ta auri wani miji bayan Salim ba, to sai dai babu yanda zai yi shi uba ne me son farin cikin ƴaƴansa kuma me son dukkan abin da suke so ko da shi ba ya so in har wannan abu bai kaucewa shari'ar musulunci ba.

A yanzu tarin tambayoyi ne a ransa to amma zai bar su bincikensa ya ba shi amsa, akwai dai damuwa da fargaba a tare da shi. Major ya katse tunaninsa cikin magana me taushi irin ta dattijon arziƙi, yace,"Malam Salman Safiyya ita ta tabbatar mana da babu maganan wani akan ƴarka, bisa wannan dalili muma muka ga ya kamata muyi gaggawan zuwa kar mu makara. Kuma ni da kaina ina baka tabbacin insha Allahu my Son zai kula da ƴarka ba zai ci mutuncinta ba, yaƙini na ke baka akan hakan saboda na san waye yarona".

Da irin waɗannan maganganun Major ya ƙarfafawa Abba gwiwa. Wanda har Abbaa ya dinga jin zuciyarsa na buɗewa da yarda gami da farinciki, sai dai ba zai zama me fatan lamarin ya kasance ba har sai yayi istikara ya kuma sa Sa'ida tayi istikara itama.

Abba yay nisa sannu a hankali ya fara magana da cewa,"Tom ni babu abin da zance sai Allah ya zaɓa mafi alkhairi wa yaran namu. Sannan kamar yanda na faɗa muku ne Ƴata ba budurwa ba ce bazawara ce, saboda haka ni ban da hurumin da zan mata zaɓi kai tsaye domin kuwa shari'a ta bata damar yiwa kanta zaɓi".

Alhaji Mukhtar ya jijjiga kai da cewan,"Wannan haka yake Malam Salman, magana ce me kyau kayi".

Abbaa ya sake cewa,"To madallah, saboda haka ku faɗa masa cewa ya zo ya fara samuna domin ina da buƙatar na gana da shi kafin na basa damar ganawa da ita ƴar tawa su sasanta kansu".

Major shi ya fara cewa,"Tom shikenan zai zo ɗin in Allah ya yarda, muna godiya".

Gaba ɗayansu kuma sai suka shiga yima juna godiya kafin suyi sallama su miƙe zasu tafi, Abba ya shiga ciki ya karɓo leda wurin Ummani yazo ya kwashe kunun ayar da ruwan ya zuba musu a ciki ya raka su da shi har mota. Kamar yanda suka ji daɗi suke ta godiya da irin karramawar da Abbaa yayi musu haka shima ɗin yake ta godiya a gare su. Bayan tafiyar su ya wuce masallaci bai dawo cikin gida ba sai da yayi sallar isha'i.

Ya shigo a lokacin Ummani na daga ciki tana lazimi, yay ɗakin nata ya zauna daga bakin gado, kuma zuwan nasa yasa Ummani idda lazimin nata tare da juyowa ta fuskance tana nazarin yanayin fuskarsa kafin tace,"Abbaa lafiya dai ko?".

Abbaa na duban labulen ɗakin kamar me son karanta wani abu a jikinsa yace da ita,"Ehh to lafiyar zamu ce".

Furucinsa nasa yasa gabanta faɗuwa, ta ɗaga hijabinta ta cire tana aje carbi ta tashi daga kan dardumar ta dawo kusa da shi ta zauna. "Wani abu ne ya faru? Shi Alhaji Babangidan me ya kawo shi kuma mene haɗinsa da su mutanen?".

Ganin duk ta ruɗe Abbaa yay murmushi yana me ɗora ƙafarsa ɗaya akan gado ya fuskanceta, fuskarta ya shafo tare da cewa,"Kwantar da hankalinki matata ta kaina, Sa'adatun Salmanu ba komai ya kawo su ba face alkhairi".

Ummani ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana karayar da kai kafin tace,"Yanzu naji batu, amma da hankalina gaba ɗaya a tashe yake, wallahi ka ganni tun da na zauna Allah na ke ta faɗawa, to ai Alhamdulillahi tunda ba wata matsala ba ce, amma me ya kawo su?".

Abbaa yace"Zuwan na su akan Sa'ida ne".

Cikin mamaki Ummani tace,"Sa'ida kuma? Na shiga duhu me ya faru da Sa'idan?".

"Kinga samu nutsuwa don Allah, zuwa suka yi da batun aurenta...".

Bai ƙarasa ba ta katse shi,"Kamar ya ban gane ba, shi Alhaji Babangidan ya zo maka da wannan zancen kuma ka tsaya sauraronsa? Ya manta mahaifin ƙawarta ne shi ko kuwa ya manta akwai aminta tsakanin matarsa da ni? To ban da ma mutuwar zuciya ina shi ina zuwa neman auren Sa'ida fisabilillahi, kuma kai bai ji kunyarka ba ma".

Tayi maganar cikin Firgicin da ya bayyana a muryarta zuwa ƙwayar idonta da ta fito waje. Wannan yanayin nata da kuma maganar da tayi sai ya bawa Abbaa dariya. Aifa ran Ummani ɓace ta miƙe tana faɗin,"Dariya na baka kenan, to ba zai yiwu ba wallahi, yanda ya zo ya tafi ya tafi kenan babu wani aure tsakaninsa da Sa'ida, hauka ake yi?".

Abbaa yace,"To idan Allah ya ƙadarta faruwan hakan fa? Kuma ina ga ai ba haramun ba ne don ya aureta".

"Allah ma ba zai ƙadarta hakan ba ubangiji ai ya san daidai, kuma nima ai ban ce haramun ba ne sai dai ai akwai duba a lamarin, kuma ya ce ko ka faɗa masa babu wurin shigarsa?".

Abbaa na yin wata dariyar ganin duk tayi kicin kicin yace,"A'a na dai ce masa ya dawo gobe ya ganta, tunda yace yana so a ba shi dama ya shiga jerin zaurawanta ya fara kafa gwamnatinsa da wuri".

Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda na san waye mijina wallahi sai in ce mutumin nan siyeka yayi da kuɗi, yanzu tsakani da Allah sai ka bar Babangida ya auri ƴarka? Kenan kaima a wannan shekarun naka tsofe tsofe zaka iya zuwa neman auren ƙaramar yarinya ƴar cikinka ta kusan nawa? Ko da ike zamu ce ta tadda muje".

Abbaa ya buɗe ba ki da mamaki ƙarara yana dubanta yanda duk ta mayar da maganar gaske. "Ka saki baki kana kallona, to ni dai ba dani za'ai wannan zalunci ba, yarinyata da sauran ƙuruciyarta don tana bazawara ba zai yiwu a laƙaƙa mata auren tsoho ba, daga nan har hizba wallahi, mene wani Babangida daga ya ɗan taimaka mana sai ya wani kwaso ƙafafunsa na marasa kunya yace ya zo neman auren ƴar cikinsa".

Abbaa yace,"Babangida kai tsaye ma babu Alhajin".

"Yo wanne Alhaji bayan ya zubar da girmansa, neman aurar ƴar cikinsa fa yake yi kuma daɗin abin kunyar ma aminiyar ƴarsa".

Ganin fa ta haƙiƙance har tana ɗaukan fushi da shi sai mita take yi yace,"Kinga ke ba ki tsaya kin gama jin bayanin da zan miki ba kawai kin hau kan wata maganar, Aure fa ɗan su suka zo nemawa ba kansa ba".

Ƙyam Ummani ta tsaya ko ƙyafta ido babu. "Ɗansa?". Sai kuma ta dawo ta zauna tana cewa,"Kar dai kace min yaron nan Khalid me hankali, ka san ƴaƴansa maza biyu ɗayan kurma ɗayan kuma shi ne lafiyayye".

Abbaa yace,"To ai bama a nasa ƴaƴan ba ne, ɗan Yayar matarsa ne yaron nan Salim da suka nemi aurenta tun tana budurwa".

Ummani ta ware ido akansa ƙwaƙwalwarta na auna maganarsa kafin tace,"Wai kana nufin yaron da ya kawo kuɗi suka dawo suka karɓa?".

Abbaa ya jinjina kai yana Faɗin,"Ƙwarai shi fa".

"Abbaa sojan nan fa da kace min babba ne da gwamnatin tarayya yake aiki".

"Shi dai Sa'a".

Nan Abbaa ya shiga bata Labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da su Baban Safiyya, Ummani bata jira ƙarashen zancen ba ma ta rangaɗa guɗa a hankali. Ta ɗaga hannu sama tana faɗin,"Allah gatan bawansa, Allah mun gode maka, Allah maji roƙon bawa".

Bakin Abbaa buɗe yake kallonta, mamaki sosai ya kama shi, kar dai abin da ke ransa ne a nata ran itama? Kawai sai yaji tana ƙara faɗin,"Bayan wuya sai daɗi, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, Rabo daga sarkin da ba ya zalunci, bijahi rasulillahi wannan yaron alkhairin Sa'ida ne".

Abbaa yace,"To ke wai kin san yaron nan ne da kike ta farin ciki haka".

"Abbaa ya ba zan yi farin ciki ba, ɗan gidan manya mutane fa, to ni dai wallahi ba don kuɗi ko matsayi ba zaɓin Allah na ke ta nemawa yarinyar nan kuma ina da yaƙinin Salim shi ne Allah ya zaɓo mana, domin kuwa tunda ta fito zaurawa ke ta sintiri akanta ban ji ina farin ciki da zuwan wani ko naji sha'awar ta ƙara yin wani auren ba sai da wannan batu ya afku". Tayi maganar baki dukka a buɗe kamar zai yage saboda murna.

"Yanzu a wacca matsaya ku ka kwana da su? Na san halinka Allah sa suma ba ce kayi su kama gabansu ba, don ni dai ban sani ba Abbaa ko kwaɗa Sa'ida zamu yi muci ba".

Yay murmushi yana cewa,"Ba haka ba ne Sa'a, aurenta na baya ne har yanzu abinda ya faru bai gushe min ba, shiyasa na ke ta jin tsoro ban san da wa zan kuma haɗata ba".

"To ya za'ai na faɗa maka ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, adu'a zamu ta mata ya bata wanda yafi wancan".

"To yanzu dai na ce musu su turo yaron ya same ni zuwa jibi idan Allah ya kaimu saboda bana so a saka wasa a lamarin, sai dai ita ɗin bamu sani ba ko ta amince".

"Kai rabu da ita yanzu ai ba shashasha bace da hankalinta ta san inda ke mata ciwo, a bayan ma ƙuruciya ce ta hanata gane wanda ya kamata ta aura".

****"Maman Nana ni zan wuce". Na faɗa a sa'ilin da na ke ɗaukan jakata ƴar ƙarama na riƙe a hannu. Maman Nana tace min,"To Sister Sa'ida sai Allah ya kaimu, ki gaida gida ki gaida su Ummani".

Na amsa mata yayin da Khadija ke tsokanata da cewa,"Wai ke don Allah ko ki ɗan gwada soliderity watarana ki ce za ki kwana".

Ina murmushi na ce,"To madam indai za ki bar min albashinki na watanni biyu ni kuma zan dinga haɗawa da aikin ki".

"Ehh lallai da ya ke ni bani son kuɗin".

Ina dariya kamar yanda kowa yay na ce,"A'a to ke fa kin je saudiya, ni kuma so na ke nayi nayi na kwashe iyayena na kaisu su sauke farali, kinga idan na samu ƴar 380 duk wata ai tuni zasu wuce umra".

Maman Nana tace,"To Allah dai ya cika buri, ki yi maza kinga Ummani ta bani amanarki yau kin yi dare".

Nace,"Wallahi fa kinga Yaya Imam ɗin ne ma har yanzu bai kira ni ba, ɗazu ya kira nace masa Dr yace in tsaya saboda waccan matar da akai wa operation to ina ga ko tunani yake bamu gama ba".

"To ki kira shi mana". Na ɗan karayar da wuya ina cewa,"Wallahi Maman Nana bana son takura mi shi, komai yake yi yanzu hankalinsa na kaina, Abbaa ne ma yaƙi ya bari na ke komawata ni ɗaya ni banga wani abu a ciki ba".

Suka haɗa baki wurin cewa,"Gata ne suka miki wallahi, mace yar tsaro ce sai da kulawa, ki gode Allah da ya ba ki iyayen da idon su yake akan ki".

"To bari naje, ni na manta ma daga yau nayi off ni da shigowa sai laraba".

Khadija da tsokana tace,"Dama kullum ana ba ki na goron albishir ai dole kike son zuwa aiki kullum".

Sauran pure water ɗin da ke hannuna na jefa mata. Da haka na fito daga Nursing station ɗin, Metrom na zaune muka yi sallama da ita, har na fito compound ɗin asibitin sai gata ta biyo ni tana ƙwala min kira da cewa,"Kinga ajiyar ki kin mance nima zan manta kuma".

"Sauri na ke ta yi kinga ƙarfe tara ta kawo kai, na gode".

Wasu hulunan sanyi ne da safuna Sister Hauwa ke siyarwa daga turkey ake kawo mata, shi ne na siya mana ni da Ummani da Safiyya, da yake safunan ma har da na maza sai na siya har Abbaa da Kaka. Ina tafe zuciyata nata tunanin in kira Yaya Imam ko na ƙyale shi, har dai na fito bakin gate, tunda bai kira ni ba na tabbata wani babban uzurin ne ya riƙe shi, iyaka koƙari suna yi akaina, Abbaa zai rako ni kullum sai mun ci rabin hanya yake komawa, in dai kuma nayi evening to ya sakawa Yayyuna duty yau idan wannan ya ɗauko ni gobe wannan ne zai ɗauko ni.

Ina tsaye bakin gate na buɗe jaka ina laluben wayata sai naji gate man na ce min na matsa za'a wuce. Nayi gefe ce na ke ma ko Dr ne zai tafi sai naga ba motarsa ba ce. Na ɗaga waya na kira Yaya Imam yace,"Kin ganni na taho mashin ɗin nawa ya samu matsala yanzu haka ina wurin masu gyara, kiyi haƙuri gani nan zuwa kin ji".

Nace,"'To Yaya kana ta wajen ina? Na gaji ne wallahi yunwa ma na ke ji".

Yace,"Zan taho yanzu yi haƙuri".

Na kashe wayar ina sanyawa a jaka, na fara tafiyata ni ɗaya cikin tsoron da ya fara kama ni, kafin na gama fita a layin ne Allah ya taimake ni na samu me adaidaita sahu na kuwa yi saurin tsayar da shi, na faɗa masa inda zai kai ni yace na bayar da ɗari takwas. Na shiga ina faɗin Allah ya sauke mu lafiya, ban manta da adu'ar zama cikin mota ba, a koƙarinsa na tayar da babur ɗin motar da ke gefenmu tayi masa horn, na ɗan leƙa na kalla sai naga motar da ta fito daga asibiti ce ɗazu.

Mutumin da ke cikin motar ya fito ya ƙaraso yana cewa me adaidaitar,"Ina kayi?".

Yace masa,"Cikin gari nayi can wajen gidan sarki".

Yace,"Ok to nima can ɗin nayi motana ne kaga ya samu matsala, samun bakaniken da zai zo ma yanzu aiki ne".

Na ɗan saci ido na kalle shi jin yanda yake hausar gwari, kananun kaya ne jikinsa blue riga me dogon hannu da baƙin wando, yasa bakin gilashi da face mask da sam ba zaka gane fuskarsa ba, zubinsa ma ba na hausawa ba ne duk da fuskarsa a ɓoye take. Zan fito ya fara shiga sai naji yace,"Noo shige daga ciki".

Na matsa ciki ya shigo, ƙamshin turarensa ya daki hancina sai naji zuciyata ta motsa, kuma ban aune ba na tsinci gabana da faɗuwa sosai, yatsun hannuna har ji nayi suna rawa, sai da muka yi nisa sosai a tafiya kana na kira Yaya Imam nace masa ba sai yaje ba nama taho, ya gama min faɗansa ya kashe wayar. Ni dai na yita mamakin mutumin ganin bai sauka ba duk da cewa bai faɗi inda za'a kai shi ba, muna tafen ma me adaidaitar ke daɗa tambayarsa yace masa no worry muje kawai idan anzo inda zan sauka zan faɗa maka.

Me adadaitar yake ce masa,"Yallaɓai ko dai baƙo ne kai a garin".

Na jiyo sautin karamin murmushin da yay kawai ba tare da yace komai ba. Muka iso unguwarmu ina ta ma me adaidaitar kwatance har muka zo ƙofar gida, idona ya hasko min Abbaa tsaye a ƙofar gida hannayensa sarƙe a baya, ban san lokacin da na furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shikenan na kaɗe".

Mutumin ya juyo yana kallona me adaidaitar ma ya juyo, duk da banga ƙwayar idon da ke cikin gilashi ba na san dai ayar tambaya ce a cikinta dangane da furucin da nayi. Me adaidatar yace,"Hajiya akwai matsala ne?".

Ai kuwa kafin na buɗe baki Abbaa ya doka min tsawa da cewa,"Ba za ki fito ba ne".

Na haɗiye dunƙulallan yawu, mutumin ya fita nima na fito sai rawar jiki na ke yi, na ciro kuɗi na bawa me adaidaitar na wuce zan iya cewa ina jin yanda ƙwayar ido ta manne a jikina. Muryar Abbaa tuni ta cika kofar gidan da faɗansa akan tahowar da nayi ni kaɗai, ga layin yay tsit ƙarfe tara da arba'in a lokacin, faɗi yake da uban dare na kamo hanya na taho ina matsayin mace, da ba zan iya jiran Imam ɗin ba me yasa ban kira Yashaik ko Al'amin sun je sun taho da ni ba. Hannu ya kawo zai buge ni nayi saurin shigewa cikin gidan, Ummani ma na tsakar gida na shiga tace,"Ya za ki mana haka, ba dole ayi miki faɗa ba ga wayarki anata faman kira ba ki ɗaga ba".

Idona a waje nace,"Wallahi banji kiran ba na sakata a silent".

Abbaa ya shigo yana ci gaba da faɗin,"Idan kika kuma tahowa ke ɗaya sai ranki yayi mugun ɓaci, kuma faɗa min gidan uban wa kika tafi?".

Jikina ya kama ɓari na shiga wallacewa ina faɗin,"Allah Abbaa babu inda na je".

"Ƙarya kike yi in ba haka ba me ya hana ki ɗaga waya? Kin san Allah zan soke fita aikin nan? Ba dai kin yi karatun ba kin samu na tsira da mutunci, to aikin ba dole ba ne zan hana ki".

Tuni na durƙusa ƙasa hawayen idona na neman sakkowa nace,"Wallahi Abbaa babu inda na je, kayi haƙuri don girman Allah".

Uwa me tausayin ƴaƴanta tuni ta shiga bawa Abbaa haƙuri da tausarsa akan yay ƙasa da murya dare yayi, cikin gida ana jinsa haka maƙota ma duk suna ji. Ya watsa min wani mugun kallo da cewa,"Ba zan ɗauki sakarci irin haka ba, kike jira duk dare za'a zo a ɗauke ki, amma wallahi kika ƙara kuskuren tahowa ke ɗaya daga ranar kin gama aiki".

Yana faɗa ya shige ciki, nima na miƙe na wuce ɗakina, Ummani na leƙowa tace,"Abincinki yana ɗakina".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull