Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 42

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 42

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 42: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 42. Kuma kamin wata tambayar ta sake gifta masa idanunsa sun haska…

3,574 words

Kuma kamin wata tambayar ta sake gifta masa idanunsa sun haska masa kamannin yaran maza dukka uku a cikin idanuwansa. Ba sai ya nemi ƙarin bayani ba, kuma ba sai an faɗa masa ba, ko makaho ya shafa yaji ya san wa'annan kyawawan yaran maza tubarkalla masha Allah na ta ne. Kawai sai ya tsinci saukar hawaye a saman kuncinsa, haka yaji ƙafafunsa na neman gaza riƙe shi, yay saurin ja da baya yana jingina da bango.

Rayuwa kenan, wacca ya wulaƙanta ya tozarta ya gorantawa ita ce ke tsaye haka a gabansa, gata nan ta zama mace cikakkiya mai aji da ilimi da wayewa, wadda ta taka matsayin da shi bai taka ba, kallonta yake daga nesa kallon da ya san tafi ƙarfin ya isa wurin da take, da dukkan nuni ta samu kowanne kalar cigaban rayuwa da ake nema, shi kuma ga shi cikin wata rayuwa na halin ƙaƙa na ka yi, halin rayuwar da cin yau ke masa wahala balle na gobe, godiyarsa ɗaya ma ya samu Allah ya jiƙansa ya sawwaƙe masa manyan basukan da ke kansa, banda haka yana jin da zuwa yanzu kam yana can bursun zaman da babu lallai ya fito.

Ya kai hannu ya share hawayensa, ba kowa ya tuna ba sai mahaifiyarsa wadda Allah yaywa rasuwa shekarar da ta wuce, kuma a yanzun haka ya tuna da lokacin da suke tare da Sa'ida ne, irin kulawar da ta bawa mahaifiyarsa abar ƙaunarsa, irin hidimar da ta yi mata, saɓanin matar da ya sake aure wacce zai iya cewa ita ta zama silar ajalin mahaifiyarsa, don ita ta zubar da karkashi bata gyara wajen ba Iyam ta zo ƙofar ɗaki tana ƙwala masa kira, sai Marawiyyan ta fito tana mata rashin kunyar da ta saba, dama bata girmama mahaifiyarsa sam yo auren ma da ƙaƙa aka yi, ita ta aure shi ma don bai da kuɗin auren, to haka kullum take cikin jawa uwarsa kunne na kar ƙara zuwar mata gida tana kiran ɗanta, idan son ganinsa take ta dinƙa kiransa a waya ya zo gida ya sameta.

Kuma a ranar da takewa Iyam wannan hargowan lokacin ya fito daga ɗaki da niyyan cin mutuncin Marawiyyan kawai sai ya tadda ta tunkuɗa Iyam baya ta zame akan wannan ruwan karkashin, shikenan daga ƙwaluwar da tayi a ƙasa kuma sai ciwo, ba magana ba motsi. Akai neman kuɗin maganin aka rasa a sa'ilin har sai da ya tuna da alkhairin Sa'ida gare shi, sanda suna tare da ta ɗauka kuɗin makarantarta ta siyar da kayan ɗaki ta ba da kuɗin maganin Iyam har aka mata aiki, haka da sanda yaje asibiti aka ce masa yanzu ta tafi ga kuma kuɗin da ta bayar, ranar yay kuka iya kuka, yayi nadama da danasanin wulaƙanta Sa'ida da yayi a rayuwarsa, ya kuma ji takaici da baƙin cikin sauya kyakykyawan halinsa da yay, ga shi Allah ya nuna masa ƙarshensa, ya tozartata ya mata cin kashi ita da ƴan uwansa akan rashin haihuwa ga ta can cikin gata ita da yaranta.

Idanuwansa suka rufe yana jin zuciyarsa na masa ciwo, sai yay murmushi yau ga shi ɗanta ya ramawa uwarsa abinda yay mata, sai ya kai hannu ya shafo wurin da ball ɗin ta ƙwalu, daga jin zafin ball ɗin ma ka san me shegen tsada ce. Ya buɗe idanu a hankali yana kai dubansa gare su, ganin yanzu saɓanin na ɗazu, yanzu tana tare ne da mijinta wanda ya fito daga cikin arniyar mota, tana karanta masa ƙiriniyar da Ayman yayi har tana yi masa nuni da inda Nazifin yake tsaye.

_"Nazifi Allah kar ya ƙara nuna min kai a rayuwata, Allah kar yasa na ƙara tozali da fuskarka har na koma gare shi, macuci azzalumi"_

Kalaman nata na wancan lokacin suka haska masa cikin kai, a ƙasan ransa yace haƙiƙa Allah ya amsa miki adu'anki, ga ki ga ni, har kina iya nuna ni daga nesa amma idanuwanki ba su samu damar ganina ba. Hawaye suka daɗa sakko masa masu zafi, a hankali ya duƙe a ƙasa zai kwandon gyaran. Ɗagowan da zai yi kuma Salim ya ƙaraso wajensa, ganinsa ɗin sai da gabansa yay mugun duka, har yana saurin ja da baya. Salim ɗin na dubansa da murmushi yace,"Ba wani abu ba ne".

Nazifi ya haɗiye yawun wahala, jiki na rawa ya ce,"To ai ranka ya daɗe ganinku ne akwai furgici, Allah yasa lafiyar". Ya faɗa da tsammanin ko Sa'idar ce ta faɗa masa abubuwan da yay mata ya zo ya kama shi.

"Ranka ya daɗe ni dai wallahi ba mai laifi ba ne".

Yay maganar cikin rawar murya da ruɗewar ciki. Still da murmushi fuskan Salim ya ce,"Ni ne Mahaifin wannan yaron, Mahaifiyarsa na faɗa min rashin jin da yay ne".

Da saurin murya da na jiki Nazifi kamar zai duƙa masa yake cewa,"Laa ai babu komai, yaro ma shi da yake wasa, ball ɗin kuma ai kayana ta buga ba ni ba, batun haƙuri ma ka bari kawai ranka ya daɗe, don Allah a bari ba sai an bayar ba".

Foridat ta ƙaraso wajen tana cewa,"Paapa Mommy tace ga takalmin Ajmal a gyara masa, zai shiga mota ya gurɗe ƙasan ya ɗago kaɗan".

Da Salim na shirin ya ce a ƙyale kawai a siya masa wani tunda store za su shiga, sai kawai ya bari Nazifin ya gyara ɗin shima ya samu wani abun, tunda ba lallai yay ciniki ba fitowarsa. Shi kuwa Nazifi mamaki ne ya kama shi jin suna yare, ƙarya yake yace bai ji burgewan su ba musamman ma Sa'idan da Ƴaƴanta, yanda ta buga shigan alfarma ga haƙoran makkanta sai ƙyalli suke daga nesa.

Hannu na rawa ya jawo kwandon kayan gyaran ya karɓi takalmin hannun Forida ya shiga gyara, ya gama Salim yay yay da shi ya karɓi kuɗin gyaran yace a'a su barshi, takurawan da Salim yay masa dole tasa shi miƙa hannu biyu ya karɓa. Ya shiga zura hannu cikin aljihun koɗaɗɗun kayansa lalubo canji.

"Ranka ya daɗe bari na ɗan samo canji a can, da yake ba a samu an yi cinki ba ne tun fitowan nawa".

Ya faɗa sai faman buɗa haƙwara yake duk a ruɗe, ya bi ya dabarbarce, Salim da fara'ar nan tasa ya ce,"No barsa kawai ka riƙe gaba ɗaya, idan na koma da shi ma Madam faɗa zata yi ban barwa mabuƙaci kamarka ba, Allah ya bada sa'a".

Dubu ɗaya ce sabuwa fil, amma haka Nazifi ya zube ƙasa yana ta jera godiya. "Na gode, Na gode ranka ya daɗe, Allah ya raya iyali, Allah ya ƙara matsayi da ɗaukaka, Allah ya jiɓanci al'amura".

Salim yaja yaransa suka tafi, ya so da cash a jikinsa da yawa ya ɗan yi masa ihsani don ba ƙaramin basa tausayi yayi ba, abin a taimaka masa ne tabbas, sai dai bari su fito daga siyayya sai ya cire kuɗi a ciki ya basa, tunda yaga kamar nan ɗin ne wajen zaman sana'ar tasa, duk da masu sana'an gyaran takalman ba su fiya zama wuri ɗaya ba sun fi bin hanya suna kaca cau kaca cau. Nazifi na kallon Sa'ida daga nesa gwanin ban sha'awa ita da iyalinta, Sa'idansa ta zama matar manya, ji yay kamar ya bisu, kamar ya isa gabanta ya duƙa ya ƙara neman gafararta, yana kallo suka shiga cikin Sahad Store ɗin, fuskarta da ta mijinta cikin nishaɗi da farin ciki, ga wani bayyananiyar soyayyar junansu da ka kalle su.

Jiki a matuƙar mace ya juya ya shiga ta wani ɗan loko, bai yi tafiya me nisa ba ya isa wani gajiyayyan gida, ƙofar langa langar gidan duk a farfashe ta lanƙwashe. Iman da Ƙanwarta Mubina na can ƙofar wani gida suna wasan ƴanta, suka kwaso a guje ganinsa ya dawo don ya hana su yawo, su kuma rashin jin daɗin zaman gidan ke sawa su fice. To matar gidan jarababba ce, ta daka ta kuma daka, su yi kukan ta kima musu uban aiki, abinci sai taga damar ba su ma, tayi ta musu gorin ai uban na ku me gyaran takalma da kwasan kwata bai kawo ya aje ba, don haka ba zan ba ku ba, sai in su ci sa'a ne wataran ta ke ɗan tausaya musu ta ba su.

Duk sun yi furkai furkai da su, da ganinsu ma ka san ba su yi wanka ba, riga daban ɗan kwali daban, rashin uwa ma dai gaban ƴaƴanta babu daɗi. A tsakar gida suka sameshi ya zauna bakin rijiya ya zabga tagumi, suka shigo a tsorace kar ya dake su ko faɗa. Iman me wayon ita ta lura da kaman kuka mahaifin na su yake.

Ta ƙarasa da sauri ta zauna kusa da shi tana faɗin,"Baba sannu da zuwa". Kallon su kawai ya tsaya yi, tausayinsu ya kama shi. Iman ɗin ta zare masa hannun da yay tagumin tana cewa,"Baba ka daina tagumi, kuma naga kaman hawaye ka ke yi, Baba wani abu ne ya faru?".

Numfashi ya sauke, cikin dabara ya goge hawayensa don ka kaɗan ba ya so yaransa ke ganin cikin irin yanayin nan. "Ina ku ka je?". Tayi ƙasa da kanta a hankali tace da shi,"Baba muna ƙofar gidan Malam Musa muna wasa".

Murza fuskarsa yay. "To kun samu abinci kun ci?".

Suka girgiza kansu a tare alaman a'a. Ƙwalla ta daɗa cika idonsa yana zura hannu cikin aljihunsa ya zaro dubu ɗayan da Salim ya ba shi. Ya bawa Iman ɗin yana cewa,"Ku je kantin Gambo ku siyo taliya ƴar hausa ta ɗari uku, sai manja na ɗari, sai ki haɗa abinda za ku daka yaji".

"Tom Baba". Suka faɗa suna miƙewa cike da murna, sai dai suka je soro Mubina ta dawo tana cewa,"Baba na siyo biskit don Allah?".

Kai ya ɗaga mata,"Ehh ki siyo idan akwai canji".

Cikin wani irin yanayi da shi kaɗai ya san a halin da zuciyarsa take ya goge hawayensa. Idanunsa hoton iyalin Sa'ida kawai ke haska masa, yaranta tsab tsab da su cikin shiga ta alfarma, yara kamar larabawa kaji ina ma naka ne ko ka sace ka gudu. amma ga nasa yaran kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin jaka. Ba su daɗe ma da dawowa hannunsa ba don ba su cika shekara ba, Zahra'u ta kawo masa su zata yi aure, tun rabuwar da suka yi bata ƙara aure ba sai yanzu, to mijin da ta aura yace ba zai riƙe ƴaƴan da ba nasa ba, ta dage ta tafi da su gidan Kishiya ta sakota gaba da sharri da makirci, a dole ta tattaro yaran ta kawo masa abinsa, ga su nan cikin rashin galihu makaranta ma ya kasa saka su.

Marawiyya ta fito daga ɗaki, ganinsa ta wurga masa wani matsiyacin kallo tana jan tsaki tare da ɗaukan buta ta shige banɗaki. Haka suke zaune da shi sam bata ganinsa da daraja, ina ma yake da gashi idon da zai samu arziƙin gaisuwa daga wurinta. Dama ita taji ta gani tace da shi su rufawa juna asiri, tunda shima bai haihuwa ita kuma taƙi auruwa sai gantalin zawarci take, ba namijin da ke iya zama da ita, shi kuma saboda yaransa ma ya yarda saboda ya samu me riƙe masa su, to ashe ma gwara bai auren ba ya zauna ya riƙe yaransa a gidan su.

Tashi yay jiki a matuƙar sanyaye ya shiga ɗan akurkin ɗakinsa, ya aje kwandon sana'arsa, ya saki yagalallan labulen ɗakin sannan ya kaɗe saman tabarmar ya kwanta idanuwansa na kallon rufin kwanon ɗakin da hasken rana ya shigo ta ɓulolin jiki. Samun kansa yay da rufe fuska da tafukan hannu yana fashewa da kuka, komai na rayuwan baya ne ke dawo masa daki daki, haɗuwansa da Sa'ida, Shaƙuwansu, matsayin da aka ɗaukesa a gidansu kamar ɗan gida, soyayyarsu, aurensu, rayuwar auren da suka shimfiɗa a farko, halin tsananin da ta zauna da shi, irin sadaukarwar da tayi akansa, halaccinta gare shi, samun arziƙinsa ta dalilinta, ɗaukakar da ya samu, wulaƙantata ɗin da yay kamar kare, ƙofar da ya bawa ƴan uwansa na cin zarafinta, mayarsheta baiwar da mahaifiyarsa tayi, gorin rashin haihuwar da ya dinƙa mata, ƙazafin da yay mata, rabuwar aurensu, halin da ya fara faɗawa, abinda Zahra'u tayi masa, zaman kurkukun da yayi, mutuwar mahaifiyarsa zuwa yau da Allah ya nuna masa ita tun bayan shekaru goma sha biyar, ya ganta a mataki na matsayin da bai taɓa tsammanin zata je ba, ya ganta cikin kwanciyar hankali da farin cikin da shi bai sameshi ba sam.

Kawai sai ya daki kansa a cikin kayan wankin da yay matashi da su, ya shiga kukan da babu sauti, a hankali muryansa ke fita da,"Allah ka yafe min wulaƙanta rayuwar baiwarka da nayi, Allah na roƙe ka kaji tausayina kasa Sa'ida ta yafe min, Allah ko dan yaran nan guda biyu da ka bani mata ka bani halin da zan inganta rayuwarsu, na ba su ilimi da irin gatan da jin daɗin da ƴaƴa ke samu wurin mahaifinsu".

Yana tsaka da hakan su Iman suka yi sallama a ƙofar ɗakin nasa, yay saurin tashi zaune yana goge fuskarsa, sai da ya saita kansa tukunna ya ba su izinin shigowa. Suka shigo Mubina na tafiya wajensa ta faɗa jikinsa, Iman kuma ta duƙa ta miƙa masa kuɗin da cewa,"Baba ga shi ɗari biyu da hamsin ne ya ragu, na taho da gawayi ma, Anty ta hanamu taɓa mata nata".

Sai dai yay namijin ƙoƙari wajen hana raunin da ke tare da shi fallasa a gabansu. "To kun siyo komai?".

"Ehh Baba, gawayin zaka haɗa min, kuma naga kaman baka da lafiya".

Tayi maganar cikin jin tausayin mahaifin nata kamar zata yi kuka. "Ɗagani Mubina in je in haɗa muku wutar can, ko ba kya jin yunwa ne?".

Tana wasanta a jikinsa tace,"Ina ji mana Baba, yau fa bamu ci abincin safe ba ka manta, sai da muka je can gidanku fa Amarya ta bamu ƙosai guda biyar, suma ya ƙare lokacin Yaya Iman ce ma tace mun ƙoshi bayan sai da Baba Adamu yace zai bamu kuɗi mu siyo wainar fulawa".

"To yanzu dai ai ga shi za'a dafa, irin taliyar ma da kike so, sai kin ci kin ture ƴar lelen Baba".

Tare da shi suka fita, Iman ta ɗakko masa kujera ya zauna gaban burkoti, dama basa iya haɗa gawayin sai dai shi ya haɗa musu. Sai hira suke masa wanda hiran na su ne ya ɗebe masa kewa, Mubina na tambayarsa yaushe za su wurin Mominsu, yace to sai yasa kati a waya sai ya basu su kirata su ji. Duk da ya san abu ne me wuya don ko da wasa mijin Zahra'u bai yarda yaran suje gidansa ba, yace hakan a bakin aurenta, ita ganin ta ɗebi shekaru da yawa ba auren yasa ta ke lallaɓa igiyan aurenta.

*****Sai dare Mahbub ya zo ya ɗauke mu a gidan Safiyya, can muka yini yau kam, ita ma yaranta huɗu dukka mata, ga dai wani cikin nan da muke ta sa ran zuwan namiji. A mota muke waya da su Abbaa ina alhazawan baɗi insha Allah, don so na ke idan suka dawo a Umra to aikin Hajji ma ayi da su, yanzu haka ma na haɗa kuɗin mutum ɗaya saura na mutum ɗaya, kuma kafin zuwan lokacin Allah zai hore in haɗa, na fi so suje dukka su biyun

"Mommy ina bindigan da Mami ta ba ni". Ayman ya faɗa yana zuro kansa ta tsakanin kujeran motan, ni ban so Safiyya ta ba shi bindigar ba duk da ta wasa ce ni bana so, ko da yake Babansa ma ba shi ta gaske yake yi. Nayi masa shiru kamar ban jisa ba. Umarul Faruq ma ya kama cewa,"Mommy nima ai Mami ta bani jirgi irin wanda Paapa ke hawa". Shima na masa shiru, Ajmal kuwa sai taɓo Mahbub yay ya ce,"Paapa har da ƙatuwan mota Mami ta bani nima".

Na girgiza kai muka haɗa ido da Mahbub, ya ƙaramar ariya yana cewa,"Hmm duk ma za ki fitowa da yara kayansu ne, sai aiwa yara kyauta ki riƙe".

"Naji, ni ɗazu ma ban baka labari ba, sirikata ta kira ni wai don Allah asa musu rana suna so zasu zo ayi maganar aure".

Murmushi yay da cewan,"Wacce surukar taki, don naga duk kun tara surukai, ƴaƴan gaba ɗaya kun bayar da su".

Nayi dariya da maganar tasa, daga cewa za'a haɗa Ayman da ƴar gidan Safiyya Iftihal shi ne tsaban sharri wai duk mun bayar da su. Na ce,"To dai Allah zancen gaskiya na ke maka, ina saurayin Forida likitan nan na Abuja, to Mamarsa ce ta kira ni".

Dariya yay yace,"Sai ku yi magana da Hassanarki ai, lokacin da ku ka fara barin yarinyar zance sani nayi, wallahi ni dai gaskiya na ke faɗa muku ku daina munafurtata".

Haka muke ta hiranmu da shi cikin nishaɗi, hankalin yaran ma duk ba ya garemu suna baya suna vedio call da Ummani, shi kuma nan shafo cikina yake yana faɗin,"Daren yau zan samar da uku kyawawa".

Na doke hannun nasa ban biye masa ba na maida kallona kan titi. Don na fara tsoron yaran nan, kwanaki Ayman rutsa ni yay na gama shirya shi zasu tafi school wai sai na masa irin kiss da hug ɗin da na ke ma Paapa, to ga Umarul Faruq nan ma daga na sumbace shi a goshi sai yasa min darun irin wanda na ke ma Paapa shima a lips. Na waiga na dubi yaran, kallonsu na ke duk cike da so da ƙauna, kafin na maido da dubana ga mijina wanda na tsare da kallo har sai da ya kawo yatsu sai tsole min ido, ina dariya na sauke ido ina ƴar dariya, wayata na buɗe maimakon shiga whasapp ɗin da nayi niyya sai kawai na ɓige da kallon kaina a kan screen ɗin wayar, ni da Ajmal da Umarul Faruq da Ayman da Mahbub. Rayuwa kenan, Allah mai yanda ya so, ga shi dai yau ya haskaka rayuwar Hajiya Sa'ida, ya haska ni da hasken da ban taɓa zaton samunsa ba. Haƙiƙa ba ka fidda rai da duk abunda yake na Allah ba na wani bawa balle yace zai hanaka.

Na sauke numfashi, annurin fuskata na ƙara washewa, na faki idon yarana na kaiwa Mahbub kiss a kumatu, ya waro ido da cewan,"So kike muyi accident akan titi". Ina siririyan dariya na ce,"Ina sonka Mahbub, Ina sonka Miji na gari, Ina sonka ɗan aljannah, ina sonka Abu Ayman da Ajmal da Umarul Faruq, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan kwana, ya dawwamar da mu a cikin farin ciki da jin daɗi har abada".

"Amin ya hayyu ya qayyum Ummu Ayman Wa Ajmal Wa Umarul Faruq Wa Sauma Wa Nasrin".

Ya faɗj hakan yana min ƙayataccen murmushin da ke nuna shimfiɗaɗɗiyar soyayyata a fuskarsa, tare da kamo hannuna ya riƙe yaci gaba da tuƙin a haka. _______________________________ *_ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! Dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin talikai majiɓincin al'amuran bayinsa...A yau 15-Dec-2023 na kawo ƙarshen labarin ƘAYAR RUWA Book 1-3, wanda na fara rubuta shi a ranar 1-Oct-2023, labarin da ya samu rubutu, wallafawa, ƙirƙira, tacewa daga gare ni Halimatus-Sa'adiyya H Zakariyya(Halima.hz), ina roƙon Allah nah da ya bani ladan faɗakarwar da nayi a ciki ni da waɗanda suka karanta ba ki ɗaya, sannan ya yafe mana kuskuren da na rubuta kuma ku ka karanta._*

*_Sannan ina miƙa godiya da gaisuwar ban girma na musamman gare ku Masoyana, waɗanda suka yi dafifi wajen sanya kuɗinsu su mallaki wannan labarin nawa, na sani tabbas ƙauna da cancanta ne yasa hakan, na kuma miƙa jinjinata a gare ku, tare da roƙon jalla wa'azza ya ninka muku abinda ku ka kashe, Allah ya faranta muku yasa wa halal ɗin ku albarka...Ina mana fatan samun dacewa a rayuwarmu, iyayenmu waɗanda suka rasu Allah ya jiƙansu da rahmarsa, wa'anda ke raye kuma Allah ya ƙara musu lafiya da nisan kwana, ya kuma sa suyi kyakykyawan ƙarshe mu da su baki ɗaya._*

*_Ba ya ga haka zan yi amfani da wannan dama wajen neman yafiyar duk wanda na ɓatawa bisa kuskure ko kuma cikin sani, tafiya ce da muka yita miƙaƙƙa, ɗan Adam ajizi ne, zai iya zamana na ɓatawa wani cikin tafiyar, ba fito na fito muka yi ba, ba cecekuce ba, koma dai ta ya ta kasance ina roƙon ku da a yafi juna don Allah, nima idan akwai wanda muka taɓa samun saɓani haƙiƙa ban riƙe shi ba, batu na yafiya ne kuma na yafe sai fatan Allah ya yafe mu gaba ɗaya._*

*_To ban sani ba ko zan ƙara fasowa nan gaba da wani sabon labarin, amma dai zai zama da kamar wuya gaskiya, dalili kuwa sau ɗaya na ke rubutu a shekara, to ban ce ba amma dai ku fi dakona a tafiyar team fitattu biyar na gaba wato next October 2024 idan Allah ya kaimu. Na bar ku lafiya, Halimahz taku ce domin ku ɗin nawa ne, ku ɗin mutane ne na musamman a gare ni, idan ba ku sani ba ku sani ina yi muku son so fisabilillah._*

*_Ƙofar aika saƙo gare ni ta lambar wayata a buɗe take gareku a ko da yaushe, sai dai don Allah kar aji ba daɗi idan aka samu jinkiri na bayar da amsa, kun dai san yanda al'amuran suke, dole sai mun dinƙi yiwa juna uzuri, uzuri yana da matuƙar daɗi a rayuwa, ko shawara na ta shi bayarwa na kance da mutum ka zama mai yin uzuri a rayuwa. Murmushi ɗauke a fuskata na ke cewa da ku Bissalam, Saduwar alkhairi._*

*Tauraro nawa za ku bawa labarin?*

Halimahz 07018098175

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull