Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 41

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 41

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 41: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 41. *B3ƘR19FT5* Muka koma gida na ci gaba da rainon Ayman cikin…

4,451 words

*B3ƘR19FT5* Muka koma gida na ci gaba da rainon Ayman cikin kyakykyawan kulawa, Mama A'i na tare da ni har muka yi arba'in, na ƙara samun cima me kyau. Sai bayan mun yi arba'in naje kano, ranar muka tafi gaba ɗaya har Mama A'i, Kudrat kawai muka bari a gida don gaba ɗaya da yaran muka wuce, ba jirgi muka hau ba a mota muka tafi, daga can gidan su Salim aka turo mana da direbobi biyu, Babban motan ƙiran Land Cruiser Prado a cikinta ne ma ake fita da Maa, muka shiga ciki gaba ɗayanmu, tawa kuma Lexus RX 350 wadda Salim ya bani ranar suna sai muka zuba kayanmu a ciki ɗayan direban ya biyo bayanmu, kuma saboda yawon arba'in da zanyi idan munje can ɗin shiyasa muka yi tafiyan motan, Salim yace sai direban yake kai mu duk inda zamu je tunda ban riga na iya motar ba, shi bai son ake masa yawon hawan mota da jaririnsa duk ya kwaso ƙura da iskan hanya.

Zuwana gida kamar a cinye ni, Ayman kuwa tunda yaje hannun Yaya Al'amin sai da ya kusa awa guda tukunna ya dawo da shi, har da zolayansa na bari yay yawo da ɗan gidan ƴan gayu masu kuɗi, matarsa na zaune ya nuna mata yana cewa,"Irin wannan me kyan za ki haifa idan kin tashi, ki yi ta saka shi gaba kina kallo har su tafi".

Ummani ce ta kora shi a wajen tana faɗin,"Mara kunya". Naji daɗin yanda na samu labarin matar Yaya Al'amin, da yake lokacin da aka yi bikin ina America, ɗakina Yaya Al'amin ya gyara ya haɗe da nasa wanda aka shigo da shi ta ciki, don Ummani ce tayi bata so ya matsa a kusa da ita, Matar ita ma me kirki da ita Ummani tace wallah ji take kamar tana tare da ni, iya ladabi da biyayya da taimakawa dai Buzuwa na yi mata, ita dai Ummani kam tayi dacen surukai saura kuma matar Abbayo, shima Allah ya haɗa shi da ta gari.

Ranar dai Ayman ya sha jagwalgwalon hannu, wannan ya ɗauka wancan ya ɗauka, manyan nan maƙota ƙawayen Ummani ai ba su jira gari ya waye na shigar mu ba, shigowa suka dinƙa yi suna sun zo ganin Hajiya Sa'ida da Balaraben Ɗanta. Tun zuwana baki yaƙi rufuwa, haka murmushin fuskata yaƙi ɗaukewa, duk wanda ya ganni sai ya ƙara kallona ya ce,"Masha Allah".

Gida kuwa mamakin yaren da bakina ya kama suke. Ummani ta ce,"Gaskiya Sa'ida kin yi ƙoƙari, yo wannan idan ni ce ta ina zan fara iya wannan yaren, ni fa ɗazu da kuna yi da yaren gani na ke kamar ba ku san me kuke cewa ba".

Na ƙyalƙyale da dariya na ce,"Ummani kuma fa ba wahala, nima fa da na je ban taɓa tsammanin zan iya ba wallahi, wahalarsa na dinga gani, shima da yaga naƙi mayar da hankali na iya sai ya daina min turancin ya ke min yaren, kuma fa Ummani kin san maƙasudin iyawar?".

Ina dariya na ce,"Haushi yaji yace to ya daina magana da turanci a gabana shi da Kudrat, da yare za su dinƙa yi ko na dinga tsarguwa naji haushi".

Ummani ta kama dariya,"Ai kin ga yay maganinki".

"Wallahi fa Ummani tuni na zuciya, don haushi na ke sosai naji sun sauya yare a gabana, ba shiri kuwa na dage na koya nima, to yau da gobe ga shi ma idan ina yi sai ace nima su ce ba bahaushiya ba".

"Haka ne, ai ni dai wannan aure na ki Sa'ida abin jin daɗi abin alfahari, ke dai ki ci gaba da biyayya da ladabi, ki kuma tsaya akan gaskiya, ki kama danginsa kamar na ki, matarsa yanda ya ke so ku zauna ki fishi ƙoƙarin ganin ma kun zauna a hakan kin ji".

Na ce,"Insha Allahu Ummani".

Muka bar tsakar gida muka koma cikin ɗakinta. Muna cikin hira Buzuwa ta shigo ta duƙa tana cewa,"Anty Sa'ida ko yaran za su mu kwana a can".

Na kalli Ummani bata saka mana baki ba. Na ce da ita,"Ba takurawa Buzuwa?".

"Ah babu Anty Sa'ida, ai akwai waje". "To shikenan".

Sai da muka gama cin abinci da yaran kana na shirya su, Rofi'a ba zata ba dama, maƙale mata ce, Isioma da Forida na turawa Buzuwa can, da ma mun taho da manyan barguna guda biyu tunda na san yanda gidan namu yake. Ai har sha ɗaya muna ta hira da Ummani, zazzaɓi ya rufe Ayman, ina faɗawa Ummani tace,"Yo ba yasha ɗauka ba ai dole yay zazzaɓi, kin san jikin jarirai, don ma ya fara zama mutum".

Ai kuwa ba shiri na ɗau takarda na rubuta sunan magani na bawa Mustafa Ƙanin Hindatu yaje chemist ya siyo min. Duk rigimansa yau dai shiru kaman ya san mun zo baƙunta, na ba shi maganin yana sha kuma sai bacci, da yana ta wuntsil wuntsil ɗinsa. Ban kuwa faɗawa ubansa bai da lafiya ba, don faɗa ne zan sha ƙarshe ma ya rage mana kwanakin da muka zo yi. Washe gari can gidan Hajjo muka fara zuwa, muna ta waya da Safiyya na ce min ba zan zo ba sai na gama tsufa a garin.

Mun zazzaga ƴan uwa da abokan ariziƙi ni da yarana, wani wurin in muka je har tambaya ake wai ƴaƴan kishiyar tawa barin gidan tayi ko mutuwa tayi. Kwana goma muka yi a Madobi har da matar Yaya Al'amin muka tafi, ita ce me jigilar goyon Ayman, idan ya zo hannuna to nono zan ba shi, ƴan uwan Ummani da na Abbaa ƙalilan ne ban je musu ba, ai kuwa jikina ya faɗa min, haka na yi ta faman shan maganin ciwon jiki, Yaran kuwa sometyms har ƙorafi suke ba ya Rofi'a mage uwar son jiki, shi kansa direban da ke jigilar yawo da mu sai da yaji a jikinsa, da muka je madobin can ya zauna masaukinsa a gidan Baba Audu suna kwana tare da ɗansa Muzammil.

Watanmu guda currr a kano, ranar da zamu koma sai da naji kamar kar mu tafi, Salim ne ya zo zamu wuce tare da shi, ya dawo daga Ekiti sai ya biyo ta nan ɗin, yara da suka gansa murna kaman me, ranar har cikin gidanmu ya shigo, sun kanainaye shi sun hana sa ma zama, Abbaa na tsokanar su ai anan za'a tafi a barsu, Salim ɗin ma yana murmushi ya ce dama ai an barwa Ummani su. Da goma sha tara ta arziƙi haka muka bar gida, iyayena sun cika ƴaƴan Salim da abubuwa, Yashaik ma babban kwalin choculate haka ya siya musu, ga yaran da shiga rai da saurin sabo, ba wanda bai kewansu ba da zamu tafi.

Da muka biya ta gidan su Safiyya Umman su hanamu tafiya tayi a ranar sai da muka kwana, na yi tawa Salim dariya kuwa, ya azalzalo ni daga gidanmu mu tafi shi kewata yake yi, kuma mun je yaywa Umma sallama ta riƙe mu, ni dai har ya fita a falo dariya na ke masa, ga babu damar mu kwan tare da shi a gidan, haka dole ya haƙura ya riƙe yunwarsa.

To haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar min, idan na kalli kaina sai nayi mamakin yanda na koma, Allah ya kai ni matakin rayuwar da ban taɓa haskowa kaina ba, dama an ce nasarar mahaƙurci da wanda aka wulaƙanta ba ta zuwa a ƙarance, har godiya na ke ga Allah da ya rabo ni da waccan rayuwar ta gidan Nazifi ya musanya min da mafi alkhairinsa.

Watan Ayman goma sha huɗu na fara sabon laulayi, na faɗa sabuwar duniyar murna da jin daɗi, wallahi ban ƙi ba ayi ta bani, ina so mijina ma kuma na so, don mun tara da yawa ba zamu gaji da su ba, mu abun alfaharinmu tun da ko Annabi ce ya ku hayayyafa domin na yi alfahari da ku. Wannan karan kuwa na wahala nayi ciwo fiye da wanda nayi lokacin cikin Ayman, sai dai shi wannan gwajin farko aka gane ciki ne, bai ɓuya ba kamar na Ayman. Ba shiri na yaye Ayman, ranar har da Kukana sai kace rabamu za'ai, na sha tsiya kuwa wurin Mahbub da matarsa.

Wajen Kudrat Ayman ya koma dan ita ce uwar Yayen, kan kace me kuwa yaro yaje hannun kulawa sai ga shi yay ɓul ɓul da shi, har wata ƙiwa ma yake min, na ce lallai ne Ayman ka riƙa ka riƙe. Sai in ya so ne ma wataran idan ƴan rigimar na kansa to fa sai ya zo wajena za'a samu salamar kuka, dama shi indai kuka ne ya iya, har ce na ke da Mahbub kai kuwa wanne irin kuka kayi da kana yaro, yay dariya ya ce ke dai wanne irin kuka kika yi, ni ai da an ganni anga salihin bawa.

Na sha wahala fiye da yanda baki zai faɗa da wannan cikin, don sai da ta kai ga mun tattara mun bar ƙasar mun koma America da zama, saboda in samu kulawa me kyau a wajen ƙwararrun likitocinsu na can, wannan lokacin kam da Umman Batula muka tafi Allah sarki da ke mijinta ya rasu satin sunan Ayman da komawarsu. Ni kam har ina rubutawa Ayman wasiyya a diary, gani na ke kamar ba zan kai ba, bai zama lallai na haife abinda na ke ciki ba, ko da na haife ɗin to wataƙila ƴar uwata Fillo zan bi, in mutu in bar yaran da mahaifinsu, haka duk na karaya shiyasa sai na bi na rame saboda fargaban da ke tare da ni, ai kuwa hawan jini da ya kamani ni kaina da aka faɗan sai da na jijjiga, a matsayina na likita na san irin wannan hawan jinin babbar matsala ce ga rayuwar bawa, haɗari ne babba.

To amma a hankali da ke ina ta samun kalaman kwantar da hankali daga Mahbub, ga kuma iyayena suma da ko da yaushe cikin waya da su muke suna min kalaman ma su wanzar da natsuwa sai na fara daina damuwa da sanya tunani. Har cikina ya shiga wata bakwai ban daina fama da ciwo ba, wannan cikin kam ɗan ƙarami da shi ana ta cewa mace zan haifa, kuma yana cikin wata na bakwan ne ƙoƙarin shiga na takwas na haife tagwaye na bakwai ni dukka maza, wannan lokacin ma kamar wancan da kaina na haihu kuma lafiya lau, sai dai ban yi dogon naƙuda ba kamar na haihuwan Ayman, wannan yini guda nayi na gama. Yaran sai a machine aka saka su, saboda yanda aka haife su ɗin ƴan ƙananu da su, ni har tsoro ma suka ba ni, ce na ke ko ba su da kyan halitta ne, sai da aka tabbatar min da lafiyarsu lau tukunna hankalina ya kwanta, in ta kuka tunma da naga an raba ni da su an kai su can wani ɗaki daban acan ake rainon su.

Bamu komo najeriya ba nan muka zauna, Maa suka zo ita da su Kudrat da yaranmu, suka sauka a wani babban apertment, Ayman yana ganina yaron ko inda na ke bai zo ba yana maƙale jikin Kudrat, haka na figo shi bai san ina nan cikin ciwo cike da kewarsa ba, duk motsina tunaninsa na ke, ramar da na yi har da ƙulafucinsa da na saka a raina.

Wannan lokacin ma na ga gata da tarairaya wurin mijina da mahaifiyarsa duk da kasancewar ina kwance a asibiti, basa tafiya sai dare ƙarfe sha biyu, kuma duk inda takwas na safe yake sun tattaro sun taho asibitin, tare da su zamu yi break fast, Tagwayena in aka ciro su a machine aka kawo min haka na ke kwantar da su a ƙirjina cike da tausayin su da ƙaunarsu da ke bin kowacce jijiya ta jikina. Cikar sati da haifan twins ɗina aka musu raɗin suna, Babban shi ne Abubakar Sadiq wanda ya ci sunan mahaifin Salim za mu ke ce masa Ajmal, ƙaramin kuma Umarul Faruq shi kuma yaci sunan sahabin Annabi ne, sunan yaren su Chidera da Kanayochukwu.

Wannan karan kam babu taron suna sai dai mun yi shagali iyamu yamu. Yo mene maraban ba mutanene kawai babu, amma batun kashe kuɗi ina kan gadon an kashe su, asibitin nan babu wanda bai samu rabon ordan snack ɗin da aka yi ba, shanu uku Mahbub yasa aka yanka aka soya akai ta rabon nama a asibitin. Sai da yaran suka cika kwana arba'in kafin aka yi discharging ɗina daga asibiti lokacin sun ƙara ƙwari, kuma wani ikon Allah a lokacin ka gansu ba zaka ce bakwaini ba ne, kamar mu guda da Umarul Faruq komai nawa ya ɗakko, Ayman da Ajmal kuwa zaka tsammaci tagwaye ne saboda tsananin kamansu, kuma sune kana ganinsu kaga kamannin mahaifinsu. Bamu dawo najeriya ba saboda ganin likita da na ke kai yaran, Kudrat da ma bayan suna suka koma da yaran saboda makaranta itama da wurin aikinta, Maa itama sai bayan sun tafi ta tafi, amma Ayman anan aka barsa wajena, sai da muka yi wata takwas a America sannan muka dawo najeriya, ba ƴaƴana kawai ba hatta Umman Batula ta sauya kamar ba ita ba, fata taji canjin yanayi.

Kan gado na ke zaune ina sawa Ajmal kaya, sa kayan da muke ta fama tun ɗazu, ya ƙi tsayawa sai yawo yake da ni, da yake haka yake gagaraf garaf, kwai ƙarfin tsiya, da kuzarinsa shi kam ba irin sauran ba, har cewa ake ko shi ne zai gaji Babansa ya zama soja. Ban isa fa na ajesa ba, tun bai cika wata biyu ba yake mirginawa, yanzu kuwa bana karambanin ma barinsa kan gado in tafi, tsab zai murgina ya wuntsilo daga kan gadon ya barni da ɗora hannu aka, in shiga uku da jaraban Babansa. Shi ɗin ranar yana hannunsa ya kwantar da shi akan kujeran falonsa, wai miƙewar da zai yi ya ɗakko abu kan dispenser sai jin yaronyay ya timo ƙasa, Allah ya so da katifansa a gefe ya faɗo kanta, kuma ko a jikinsa ba kuka, to ranar da a wajena ya faɗo sai nayi kuka saboda ihun faɗan da zan sha. Umarul Faruq kam ba ruwansa, yanda na kwantar da shi hakan zan zo na samu kayana, idan ba wai bacci yay ba ya juya gefe, yanzu haka yana gefena a kwance salihin bawa in kunji ana cewa, da ace shi na ke sawa kaya muka ɗau lokacin nan da yanzu Ajmal na nan ya ɗagan dubaidar rayuwa da kuka, inaa ai shi bai yarda na barsa, ko bacci zai yo to sai dai fa yayi shi a bayana ko a jikina, shan nonosa kuwa har yay yawa don yafi Ayman, duk ya bi ya zuƙeni yaƙi bari nayi ƙiba, ko saboda shi ba zan bari su shekara biyu ba zan yaye su.

*B3ƘR20FT5* Mahbub na zaune ƙasa kan carpet ya na gyarawa yara computer ɗin su da ta lallace, Ayman na tare da shi sai ƙiriniya yake masa yaƙi barsa yay aikinsa da kyau. Sai buga masa gwaranci yake yi. Ai ni kam na gode Allah da ya ban Ayman, yay ta haɗa min shirgi ko gajiya bai yi, idan mace ne ai na huta ina ga shekara biyar zan fara sata ɗora tukunya, wuyarta in gama gyara insha Allah kafin in waigo yayo min ɓari, idan kuwa kitchen na shiga duka durowoyin nan sai ya buɗe murafansu.

In ta faman mita ina ni ya ishe ni sai in sa ai masa rubutu ya nutsu, Mahbub yace in ƙyale masa yaro lafiya ce ba zan takura masa ɗa ba, har da shi bai ma ga fitinan da yake yi ba, na ce yo ina zaka gani ka tafi ka barmu da shi. Ile kuwa ranar sai ga shi yay masa ɓarin takardu kuma ya zauna akai ya saki fitsarinsa. Ranar kuwa na yita ƙunshe dariyata, sai basarwa yay bai faɗa ba dai ya ɗauke shi ya kaiwa Babarsa, itama can ai gata da shi jiki duk manja tana faɗin,"Can kuje ku ƙarata, daga shiga kicin na ɗorasa saman island ya kifo min da manja da kayan miya gaba ɗaya, Babansa na gari ya dawo yanzu in banu yace ina sane na barsa ya kifar, daɗin ma kayan miyan ba su shigar masa ido ba da ina ga jaraban Babansa sai tasa na bar gidan yau".

Ni dai na ta musu dariya, Ayam ɗina idan yay fitinar sai dai kawai in girgiza kai na ce,"Allah ya gyara min kai".

To yanzun ma da Baban nasa ke aikin sai bi ya ke yana kwaso min kayan durowan su Ajmal yana kawo masa, shi kuma ya biye shi suna ta hiran, in ya kawo ya karɓa yace,"Yauwa Ayman ɗina to na gode sannu da aiki".

Tun yana biye masa sai da ya dawo ya koma ce masa,"Je kai wa Mommy". Can da ya ƙara kwaso kayan wankinsu sai ya zauna ya leƙa fuskan shi yana cewa,"Toda". Ban san lokacin da na tuntsire da dariya ba, shima Mahbub ɗin dariya ya saki yana ce masa,"Na'am ɗan gidan Soja, Allah yay maka albarka ka ji yaron kirki, sannu da aiki, kwanta ka huta haka ai ka gaji".

Still ina dariyan na ce,"Ka ga idan baka hana shi faɗin sunanka haka ba wataran haka zai gatsa maka shi a gaban mutane".

"Ah to mene dan ya faɗa ba sunan Babansa ba ne".

Nayi ajiyan zuciya a raina inawa mijina adu'a gami da kyakykyawan fatan alkhairi. Haƙiƙa ina alfahari da tsintata cikin rayuwar wannan bawan nasa, idona naji ya cika da ƙwalla wadda ba ta komai ba ce face farin ciki, a kullum adu'a na ke wa uban ƴaƴana Allah yasa ya gama da duniya lafiya, ya raba shi da iyayensa lafiya, kuma ya sadamu da juna har a aljannah, ya kuma dawwamar da shi cikin farin ciki, ya ba ni ikon saka masa da irin alkhairan da yay min a rayuwa, na san ba zan taɓa iya biyansa ba sai dai na kimanta wajen kyautata masa da dukkan buƙatun da ya zo min da su.

Ba faɗa ko saɓani ya haɗamu fushin na ɗan ƙalilan ɗin lokaci ne, to idan ma faɗan ne dama akan ƴaƴansa ne zaka ji yana yi, ko sun yi ta'adi an musu faɗa sun kama kuka, ko ya zo ya tarar da Oga Soja yay ɓari to fa in ya fara sai ko ina ya amsa a gidan, yace ai muna kallonsa muka barsa yay ɓarnan, sai kuma azo a dame shi da ya siyo ya siyo.

"Myy wannan gyaran yafi ƙarfina, sai dai a barsa zan turo mai gyara ya zo ya duba musu, ko a siyo musu sabuwa dama wannan ɗin ai ta jima, sabuwan ma dai zan siyowa Farida Isioma da Rofi'a sai a gyara musu wannan ɗin, Ni wai garin ya akai ma suka lalata, abar da take saman table ya akai ta kifo".

Kallonsa nayi duk don yaji bakina ne fa, ai ya san wanda ya lalata musu ɗin, so yake nayi magana yace ba wani nan rashin adanin yaran ne, alhalin Foridat na iyaka ƙoƙarinta akan adana abinsu, amma Ayman da fitina bai barin masu komai, sun kunna abar suna kallo ya ɗauki lemu ya sheƙa musu akai, kuma ko a jikinsa bai san ma me ya aikata ba, ai kuwa ya ɗalu a wurin Forida. Kudrat ta ce da ni bakinmu alaikum ya tasu. To yanzu da zai ji an daki Ayman ɗin mun shiga uku da faɗa, Forida kuwa sai ya iya bugunta ƙila ma yace ba zai gyara musu ba ita ɗin ma ba zai siyo mata sabuwan ba, ba ya so sam a taɓa masa Ayman, shi ke ƙara tunzura shi ma yayta cewa,"Yayi Oga soja".

Ɗaukan Ayman yayi suka fita, ba jimawa ya dawo shi ɗaya, ya kuma ɗaukan Umarul Faruq ya fita da shi, ai ganin hakan na fahimci inda ya dosa, haka zai kwashe su duk ya kai ɗakin Yara. Ya dawo yana faɗin,"Wai ba ki gama ba shi ba ne".

Don in tsokane shi na ce,"So na ke ma ya gama sha na bar maka shi in tafi aikina, yau eba na ke so na mana, kar ɓomo ɗin can da na jiƙa ya lalace".

Killer smile yayi yana hayowa kan gadon, kuma kamar Ajmal ɗin ya sani ya saki nono. "Kin gani shi ma yaro ya san lokacin Babansa yayi, ita ma Eba sai ta jira a sallami me gidan".

Yana dawowa ya faɗa kan gado tare da jawo ni jikinsa, nan da nan kuma labari ya sauya salo. Naga alama so yake in kuma ɗauka tun ban yaye su Umarul Faruq ba.

*Bayan Shekara Bakwai.* Ƙaramar ball ɗin da tayi shawagi a sama ta faɗo ƙwal a saman fuskar mutumin da ke zaune bakin Sahad Store na Mandawari kano. Ya dafe fuska cikin jin zafin buguwan, kuma kafin ya kai hannu ya kama ball ɗin ta gangara ta kifar da kwandon kayan gyaransa, kayan duk suka watse a ƙasa.

Ba zafin ƙwaluwar ba ma, bin hanya ya bibya tsinto kayan alhalin mutane na ta faman wucewa, wani ma sai ya take shi bai lura ba. Ya ɗago ransa a ɓace yana kai dubansa ga ɗan ƙaramin yaron da ya doka ball ɗin, Rofi'a da ke tsaye kusa da ƙanin nata tayi ƙwafa tana gyaɗa kai ta shiga ƙwala kiran,"Mommy! Mommy! Mommy!".

Hankalin Sa'ida yay can bata jita ba ma, sai da Isi'oma ta taɓota tana cewa,"Mommy kinga yaran can ko, kalle su fa acan baya, Mommy wai haka kullum za muke tafiya sai mun yi nisa muke ganinsu a baya, a ke barin su a gida kawai".

Na ɗaga kaina don kai dubana gare su sai na jiyo Rofi'a ɗin na cewa,"Mommy Ayman ya ƙwalawa me gyaran takalma ball".

Raina ya ɓaci sosai, na rasa irin Ayman sam ba ya ji indai akan ball ne, nayi faɗan nayi har na gaji, kawai duk wurin da ya samu doka ball yake da dogayen ƙafafunsa irin na Babansa, kuma ba'a isa azo fita ba sai ya saka rigiman lallai sai da ball ɗinsa zai fita, a hana shi a rasa kwanciyar hankali da faɗan ubansa, na ce hakan ba kyautuwa ba ne yace babu ruwana kar na ƙara hana masa yaro yin abinda yake so.

Kuma har yana cewa Ayman ɗin ka doka ball ɗinka duk inda ka ga dama, wanda ya fasa taɓa min ɗa bai cika isashshe ba, kayi ball a inda kake so Babanka soja ne Kakanka Soja ne Yayan Babanka soja ne kaima kuma soja ne.

To wa ya san yanzun ma ko yana wajen, tunda ajiye mu kenan da yayi mun dawo daga rakiyan Ummani da Abbaa airpot za su tafi Umaran da na biya musu. Shi ne ya aje mu nan in yiwa yaran su Yashaik siyayya zai je gidan sarki ya dawo sai mu wuce, yau ɗin muka shigo garin kuma kai tsaye filin jirgin muka wuce, da yake shekaranmu biyu kenan da komawan mu can Abuja, tun ma da muka koma ɗin bamu wani zazzo kano ba tun bayan rasuwan Kaka, Allah sarki Kaka har yau mutuwarsa na taɓa ni, duk da an sha zaman duniyar.

Cike da takaici na girgiza kai na kalli Isioma nace,"Kula da yaran nan ina zuwa". Na faɗa ina tafiya na barta da Umarul Faruq da Ajmal. Ai fa tunda ya hango tahowata ya falla a guje yay jikin wani mutumi ya ƙanƙame shi, ga fitina ga shegen tsoron bala'i, idonsa duk yay wurƙi wurƙi ai ya san dole ma sai na murɗe masa kunne, yanzuma yasa hannu ya rufe kunnuwan dama haka muke da shi. Ni ban da yaci sunan Abbaana ma ai zane masa jiki zan ke yi.

Mutumin ya ɗauke shi yana dariya da jin sha'awan yaron a ransa, Rofi'a kuma sai dariya take yi na mugunta dama sun saba a tsakaninsu, shi yay mata dariya idan irin hakan ta taso itama tayi masa, gata dai da ƴan uwanta mata amma sun fi shiri da shi, duk wata kitumurmura tare su ke yi, in ce an dai ji kunya Yayar kawai.

"Mommy wallahi ki zane shi, sai da ina ta ce masa kar ya buga kar ya buga yaƙi jina, da zan ƙwace ma yace min sai ya faɗa ni da Paapa, ni kuwa na ƙyale shi don na san faɗan Paapa, haka kawai ya zo yana cewa kar in ƙara bugun masa ɗa, dama duk an fi sonsa ai".

"Ina wanda ya bugawa ɗin?". Na tambaya idona akanta ita ɗinma kamar na kwaɗeta, ba damar mu fita sai suke tsayawa a baya, kuma har a gaba zan tasa ƙeyarsu amma kafin na farga sun zilla sun koma bayan, sai mun ci uwar tafiya kan in ankare Isioma tace min,"Mommy ga Tom and Jerry ɗin can a baya".

Rofi'a ta kai hannu tana yi min nuni da mutumin da ke tattara kayan gyaran takalman nasa yana maida su cikin kwandon, sai naji tausayinsa ya kama ni don da gani yana cikin wani hali na neman taimako, amma ɗan albarkana ya daddage ya buga masa ball, abar da take da shegen zafi ni kaina ranar da ya ƙwalo min ita sai da na kusa ƙwalla.

Na gyaɗa kai ina niyyan in tafi inje in basa haƙuri sai kuma dai na fara tunkaran wajen wanda ya ɗauka Ayman, haka kawai ban sansa ba bazan bar masa yarona ba, wani abu ya faru na zo na shiga uku, ubansa ma sai yay min bulalai ya ɗaure ni, ya haka Family sakat sai an nemo masa ɗansa.

Muka gaisa da mutumin yana cewa,"To ya za'ai ai haka yara suke sai haƙuri, kar ayi masa faɗa please kuma kar a duke shi, zai daina wataran, bari naje na bawa shi mutumin haƙuri".

Kaina na ƙasa na ce,"Shikenan na gode". Ya tafi tare da Ayman ɗin wai ma don kar ya bar min shi in duke shi, yana riƙe da shi a hannunsa, na bi bayan mutumin da ido har ya kai ga wajen me gyaran takalman.

"Mommy ɗauke ni". Ajmal ya faɗa cikin nasa rigiman, ba zai barni na huta ba ai, ya girman ma shi bai yarda da kowa ba, shi ko Umarul Faruq dama indai da Isioma bai da damuwa.

Na duƙa zan ɗauke shi daidai lokacin kuma da Nazifi ke ɗago kai ya kai dubansa ga Babar yaron da mutumin yaje basa haƙuri yay masa bayani, me idanunsa za su gane masa? Kamannin da ba zai taɓa mancewa ba ne ba fa, fuskar da ya ke ta son gani ce fa, a wani razane yake kallonta har ya kuma yar da kwandon gyaran takalman suka watse a ƙasa, baki a buɗe ya kasa rufewa.

Zuciyarsa ta shiga harbawa fat fat kaman zata fito waje, kafin a hankali laɓɓansa su haɗe da furta sunan Sa'ida. Tambayan farko da ya fara shiga ƙwaƙwalwansa ita ce,"Yaran waye a hannunta?".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull