Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 40

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 40

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 40: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 40. Naji ƙwarin jikina sosai kuwa don asibitin babban asibiti ne sun…

4,353 words

Naji ƙwarin jikina sosai kuwa don asibitin babban asibiti ne sun iya kula da mutum. Maganar farin ciki ba a batunta ta ɓangaren ƴan uwa da abokan arziƙi, Family ɗin su Salim kuwa ka rantse karon farko kenan da Salim zai samu haihuwa, ashe su haka suke farin ciki da tarairayan mace idan tana da ciki ko da kuwa haihuwa ta ɗari zata yi, sai da na zama kamar wata ƙwai ɗanya saboda yanda ake ririta ni tun balle me abu da abunsa mijina abin ƙaunata.

Ƴan uwansa haka suka dinƙa zuwa yi min sannu, sai kowa ya zo an ce masa ciki ne sai yace au da ciwon ƴan gayu na ke aka sa su tasowa suyi tafiyayya. Yara kuwa ko da yaushe suna tare da ni suyi ta kallon cikin suna faɗin,"Mommy yaushe za ki bamu Baby?".

Rofi'a kam ai ko bacci zamu yi yarinyar nan kanta na kwance kan cikin wai kar a ƙwace mata Baby, idan ranata ne yana wajena sai fa in tayi bacci ne zan mayar da ita ɗakin su Foridat ta kwan a can, dama haka muke da ita ko da yaushe ita tafi son bacci a wurina, Kudrat tace,"Ke kike shagwaɓata shiyasa take miki abinda taga dama ai, ke ƴa mummuna amma ki ta wani faman ji da ita".

Na ce,"Ehh komai za'a faɗa a faɗa, baƙin ciki kashe maƙiya".

Tasa dariya da cewa,"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, da Baby ya zo zamu ƙara juyawa mutum baya aradu".

Nima ina dariyar na ce,"Kar ki manta hajajju kullum ciki azkar muke, kuma bakinmu li'ilafi da yasin ko da yaushe, kinga kuwa haka zaku buga ku barmu, kuma indai muni yasin a fuskar ƴaƴanki ya tare".

Cikin wasa da raha muke zancenmu, ni dai Kudrat ba kishiya ba ce a wurina ƴar uwa ce, kuma har zuciyata haka na ke jinta, don ƙwarai da mata za su daure a danne kishin zuciya to za'a zauna lafiya tsakanin kishiyoyi, ba faɗa ba tashin hankali, to ba kowacce mace ba ce kamar Kudrat musamman a wannan zamanin tunda ko a iyayenmu na da ai zamu gani, lafiya suke da kishiyoyinsu sai kaga har a rasa banbance ƴaƴan wance da wance tsabar haɗin kai. Kuma zuciyar kowa fess ake zama ba wadda ma ke tsayawa sauraron zugar mutane, Sai dai fa duk da hakan muma don mun samu jarumin miji ne tsayayye a cikin gidansa, mijin ƙwarai da bai nuna banbanci tsakanin iyalinsa, mijin da bai fito ya nuna fifikon wata ba, shiyasa na ke jinjinawa Mijina domin ya cika namijin ƙwarai.

Sai da naji daɗin jikina sosai babu wani ciwo da ke takura ni sannan Mama A'i ta koma gida. Ita da taji daɗin zaman ma so tayi har sai na haihu, Abbaa yay ta faɗan to zaman me zata yi, bacin ma makaranta zan koma. Ni kuma gani nayi zaman me zan yi dama tunda lafiya ta samu, ba wani wahalallan laulayi, saboda haka na yanke shawaran komawa makarantana, ranar da Mama A'i zata koma sai da naji kamar na bita, rabona da gida tun dawowarmu daga saudiyya.

Tsaye na ke gaban madubi ina duban kaina, Salim da ya fito daga toilet ya tsaya ta bayana ya rungumeni yana tusa hannayensa cikin rigata ya shiga shafa cikina. Ina kallonsa ta cikin madubin na ce,"Ranka ya daɗe Sir".

Yay min cizon wasa a wuya kafin ya amsa,"Na'am ranki ya daɗe Momin Unborn".

Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata saboda daɗi. Na kai hannu saman kansa ina cewa,"Godiya ga Allah da ya bani ɗaya tamkar ya dubu, mijina abin sona abin alfahari da tunƙahona, jarumin da ya fi dukkan maza, gaishe da kai jigona, matakalar kwanciyar hankali da farin cikin iyalinsa, Allah ya bar mana kai ya faranta maka, ya bani ikon sanyaka farin cikin da nima kake sanya ni a ciki".

"Thank you for the praise Momin Huɗu". Ya faɗa yana manna min kiss a kumatu. Na juya idanu da faɗin,"Mahbub ko goma aka bani wallahi ina so, zan yi murna in farin ciki, ba zan ji wahalan kulawa da su ba, ba zan kasa tarbiyantar da su ba, Mahbub ƴaƴa Rahma ne kai ka faɗa min da bakinka, kawai dai idan suka zama huɗun to haihuwa tare da kai".

Siririyar dariya yay da cewa,"Ni in haife su ta ina Myy?".

Hannu na kai na zungure shi ina faɗin,"Ta nan, haihuwan na zuwa zai buɗe".

"Ohhh kiji daɗin cewa na buɗe da yawa ko, ko da yake na fanjama neman maganin maza, in tsuke irin yanda kike tsukewa kina sawa na fita a hayyacina".

"Abu me sauƙi kenan, ƙarƙari ka fito da kuɗi, zan haɗa maka maganin da sai ka shekara kana min surutan da yafi wanda ka ke yi, maimakon Myy zan mutu sai dai ka koma cewa Myy na mutu daɗinki ya kashe ni".

Na faɗi hakan muna dariyan jin daɗi da shi. Zaunar da shi na yi kan stool na shiga shirya abina, ba na taɓa ƙosawa da yi masa wanka da shirya shi. Ina gyara masa gashi yake min zancen komawata makaranta, duk da ba'a son ransa zan koma ba ɗin, babu yanda bai yi da ni ba akan na bari sai na haihu na koma har fushi yay, ni kuwa ban ga amfanin zaman ba tunda dai lafiya na ke, me zan jira kuma haka kawai sai na fara tara yara kuma karatun ya zo yana min wahala, duk da shekara uku ne na gama.

"Myy; Mommi(Kakarsu) ta ce to ba zai yiwu a barki ki tafi ke ɗaya ba, Anty Adamma zata zo sai ku wuce tare, ita zata zauna da ke saboda taimakawa da kulawa".

Nayi knooding kaina da gamsuwar hukuncin da Mommi ta yanke na ce,"Ba damuwa ai Mahbub, ina yiwa Mommi godiya da kulawanta".

"To yanzu kin gama haɗa komai? Flight ɗin 9 za ku bi".

Na ce,"Ni kam na gama duk shirina". Sai na marairaice na zauna saman cinyarsa na shiga roƙonsa. "To Mahbub don Allah kaga tunda ba ni ɗaya zan koma ba har da Aunty Adamma ka bari na tafi da Rofi'a, kaga dai ba kyau raba uwa da ƴa, Allah baka san irin ciwon da na ke ji ba a zuciyata idan na tafi na barta nima har kuka na ke yi, kana kallo idan na tafi duk ramewa take yi".

Ido ya zuba min yana kallona kawai, sai na ƙara marairaice masa kaman zan yi kuka ina faman roƙo. Gira ya sosa kana yace,"Shikenan ku tafi ɗin, amma ai kin san dai this session za'a sakata school, yanzu idan kika tafi...".

Bakinsa na toshe da kisss, sai da na tsotsi abina son raina kafin na barsa ina murza kunnensa na ce,"Kai dai ba ka yarda mu tafi taren ba?".

Yana kallona da idanunsa da suka canja kala saboda tsokano shi da nayi ya ɗaga min kai kawai. Na miƙe akan cinyar tasa ina cewa,"To idan munje can zan saka ƴata a school nima dama na ƙagara ta fara zuwa makaranta, bakinta ya ƙarasa buɗewa a can".

Fizgo ni yay sai kan gado,"Ki tsokano ni sannan ki nemi hanyar ficewa".

"Mahbub to zan haɗa kayan Rofi'a ne fa". "Tab idan kunje can kya siya mata wasu, amma yanzu madara za ki bani, anjima fa za ki tafi ki barni".

"Za ka takurawa BabynBaby fa". "In ji wa? Abinda zan yi lafiya zai ƙara masa ai kin fini sani".

Soyayyarmu muka dirza ni da shi, haka muka yini cirr a ɗaki ni har kunya ma naji, don Aunty Adamma ta zo tana ta kiran waya amma mutumin nan ya hana ni fita wai bai ƙoshi ba na ƙyale shi, Baby yasa na ƙara yin daɗi ji yake kamar zai zauce. Ƙarfe takwas na dare Mahbub ya kaimu airpot, da Rofi'a na tafi ƴan uwanta na ta jin ba daɗi, musamman Isioma da ita ma ke ta roƙonsa Paapa nima a tafi da ni please.

Komawata America can ni ɗin ma haka aka samu ƙwararran likitan da ke bani kulawa wanda har gida yake zuwa, na faɗa musu ni yanzu bana jin ciwon komai, sun ƙi yarda a haka Dr ke ta cin kuɗinsu, tunda na tafin kuma Salim bai da natsuwa akai akai yake zuwa, ya zo yay ta ririta ni cike da so da ƙaunata a gare shi, haka kuma ya daki bidirinsa, ni kam ban hana shi abinda yake so. Cikina na da wata bakwai ya bayyana sosai, don har ya kai wata shida ba zaka taɓa cewa ina da ciki ba, anata cewa ƙaramin ciki garen, wanda ba su sani ba ma cewa suke tumbi ne, amma ikon Allah shigarsa wata bakwai sai ka rantse ina cikin watan haihuwar ne.

Kuma babu wani ciwo da na ɗinka fama da shi tun farkon ciwon da nayi, kawai dai na kumbura ne kamar an zuba min yeast, har bana son kallon kaina a madubi wallahi saboda munin da nayi, Safiyya sai tayi ta kunna ni wai ai ance idan mace tayi muni idan tana da ciki to mummuna take haifa, ai kuwa nabi na damu da maganar, yo wake son haifar mummuna, sai da Salim ya kirata yaci ƙaniyarta tukunna ta shafa min lafiya. Sai dai shi kansa tsokanata yake da girman cikin, idan ya zo America yaje school ɗakko ni haka zai ta min vedio yana daga cikin mota, ni kuwa ina tafe ciki a gaba wurjanjan har kunya na ke ji, don dai ba yanda zan yi ne karatun ya zama dole amma da babu inda zan ke fita har sai na haihu.

Yau ya zo ɗaukana, ban san ya sauka a ƙasar ba, don bai faɗa min ba, mun dai yi waya yake cewa tunda mun kusa dawowa ba lallai ya ƙara zuwa ba shima suna bakin wani babban aiki ne, na fito daga gate ɗin makarantan ina tsaye ina jiran taxi, sai gani nayi mutum ya leƙo yana,"Madam turtsitsi shigo na rage miki hanya".

Ban mamakin ganin nasa ba don dama na san ba zai iya haƙurin ɗaukan lokacin da ya faɗa ba bai zo ya ganni ba. Na shiga motan ina cewa,"Mijin turtsitsi ya da zuwa ba sanarwa".

"To a kora ni mana ace ba'a son ganina ba'ai murna ba".

Cikin shauƙi na sarƙafo hannuna a nasa ina kwantar da kaina a kafaɗansa na ce,"Ni a wa na ce ban murna da ganin miji na gari ba, ina sonka mijina idan na ganka sai in rasa kalar farin cikin da na ke riskan kaina a ciki, banda ƴar uwata ma kaima ai ka san ba zan ke barinka ba".

"Umm matata nima kasa sukuni na ke idan bana tare da ke, shiyasa za ki ga bini bini na taho gareki, ba takura miki na ke ba wallahi ƙaunarki ce tayi min yawa, ina sonki mace ta gari me ladabi da biyayya, Allah ya ba ki aljannah ko don biyayyan da kike ma mijinki".

Na ƙanƙame shi ina amsawa da,"Amin ya Rahman". Sai yace,"Rofi'a fa?". Na ce,"Ai akwai school bus, yanzun ma na san an maida ita".

"Weldone Hajiyar Doller, ki zuba uban kuɗi kisata a wannan makarantan me tsada, ni da Kudrat ta faɗi mani fa ban yarda ba".

"Amfanin kuɗin uwa tayiwa ƴaƴanta hidima musamman ta ɓangaren ilimi". "Haka ne, Allah ƙaro miki masu albarka, yanzu ban aron dubu ɗari biyu".

Ina dariya sosai na ce,"Ɗari biyu jal". "Madam ai ba a naira ba, ina nufin dala dubu ɗari biyu". "To ka sha kuruminka Sadauki, tunda ka ba da wannan ajiyar mene ba za'a maka ba, ka san mu hausawa mun ce yaba kyauta tukwici, so ba bashi za'a baka ba, kyauta ma za'a baka".

"Lallai na kusa in zamar miki ɗan maraya kiyi ta jiƙani da doller, Madallah da ke Hajiyan doller Allah ƙara lafiya da buɗi, aci gaba da taimakon marayu".

Da jin daɗi mara misaltuwa na amsa da,"AMIN Hubbi nah, ba ni ɗaya ba har da kai".

Kiss yay min a gishi sannan yace,"So'ida wallahi nayi matuƙar jin daɗin yanda kika so ƴaƴana, wallahi ban san ta yanda zan misalta miki daɗin da na ke ji ba akan ɗaukan yarana matsayin na ki da kika yi, haƙiƙa kin ƙara samun fada a zuciyata, kin ƙara samun gurbi me girma a raina, Allah yay miki albarka".

Satinsa uku da tafiya muka yi hutu, washe garin ranar da na dawo gida na fara naƙuda a tsaitsaye a tsaitsaye, ni ban ma ɗauka itan ba ce nayi zaton dai ciwon mara ne haka tunda ina ɗan taɓawa. Sai da na faɗawa Kudrat yanda na ke ji tukunna tace ai naƙuda ce. A ranar kuwa aka turo mana wata dattijuwa a cikin matan uncles ɗin Salim, da yake da muka sauka direct Aunty Adamma Anambra ta wuce. Suka yi suka yi mu tafi asibiti na ce su bari ba haihuwar ba ce, Kudrat har taji haushina wai zan nuna musu ni likita ce kenan na san aikina.

Kwanana uku ina naƙuda a asibiti kafin Allah yasa na sulluɓo ƙaton Jaririna, yo ba dole ciki yay girma ba, kunga yaron kuwa masha Allah, godiya sai ga lillahi domin kuwa lafiya lau da ga ni har yarona, wayyo dama haka ake ji? Ni dai da aka bani yaron ji nayi kamar na tsaga ƙirjina na ɓoye shi a ciki, shi da mahaifinsa kamar an tsaga kara saboda tsananin kama, naji daɗi kuwa domin burina ne haihuwan kyakykyawa, bakin yaron ɗan ƙarami gashin ido har saman fuskarsa, take kuwa na shiga tofe abinda da ayoyin ubangiji, na tauna dabino a baki na zuba masa ruwan a bakinsa. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR18FT5* Zo kuga murna wurin Salim, Yana Abuja lokacin aka kirasa ƙarfe uku na dare, amma bayan asuba sai ga shi ya sauka. Runguma babu kalar wadda ban sha ba a wajensa, kiss kamar zai cinye ko'ina na jikina, farin cikin da yake nunawa zaka ce ko don saboda haihuwar daga gare ni ne, a'a shi haka yake yau ko da Kudrat ce zata ƙara haihuwa iyaka farin cikin da zai nuna kenan da kuma kulawar da zai bada.

Ina kwance kan gadon shi yana gefe zaune da Babyn a hannunsa, da na motsa zai ce,"BabynBaby menene? Me kike so? Wani wurin ke miki ciwo? Faɗa min menene me kike so kin ji matata ta gari abar ƙaunata".

Sai dai kawai nayi murmushi na kaɗa masa kai in ce,"Babu komai Paapa, lafiya lau na ke, kai kawai na ke so kuma gaka a tare da ni".

Hannuna ya daɗa haɗewa da nasa da Babyn, ba zan iya ce masa ina jin ciwon mara sosai ba don sai ya bi ya tashi hankalinsa, ni kuwa ba na son ganin mijina a wannan yanayin, na fi son ganinsa a irin wannan yanayin da na ke ganinsa a yanzu riƙe da ɗansa na tsantsar farin ciki da annashuwa.

Sai yamma aka sallame mu muka koma gida. Jego na ke me cike da daɗi, gata ta ko'ina an mayar da ni tamkar ƴar gwal, miji yanai ƴan uwansa na yi, nawa dangin na min, kwanana biyu da haihuwan Mama A'i ta ƙara dawowa ita zata min zaman wanka, ni da ta zo ce na ke da kayan fara sana'a ta taho, wai ashe kayan barka da jego ne kawai aka tulumota da su ta kawo min, dama tun kan haihuwar naji Ummani na faɗin an haɗa sabulu wanka, to ashe har dakan yajinta tayi botikin fenti guda biyu.

Ga kayan sanyin jariri na injin saƙa me kyau, set har huɗu don ana zuwa ma da su na cire sky blue colour ɗin na cewa Mama A'i a saka masa kayan Kakarsa. Zannuwan turame kuwa masu sauƙin kuɗi kala shida, abinka da ƴar gidan me siyar da su, banda manyan atamfa da kowacce zata yi dubu bakwai guda huɗu, da sabbin hijabai na ɗinkin zama ni, ga falle falle na wankan jariri guda uku shima, ga zanin goyo na saƙa shima me kauri guda biyu, ko ba'a saka masa kayan sanyi ba aka goya shi da iya shawul ɗin ai ya isa yaji ɗumi, zoben azurfa kuwa ina gani shima na san daga Abbaa ne, takalman jarirai guda uku suma masu kyau haka ya siyawa jikansa. Turarukan wuta kuwa masu bala'in ƙamshi na jego manyan kwalabe huɗu suma, da humran jariri, kai wato ina nan ashe Hajiya Ummanita na can tana shirin saukar jika. Yashaik da Yaya Imam kuwa kuɗi suka tura min, da zolayarsu suka ce,"Duk da ke Hajiya Sa'ida ce amma dai ga wannan a siyawa ɗan mu turare, Allah yay masa albarka".

Naji daɗin kyautan na su sosai, muka yi waya da Ummanin ina zuba na ce,"Ummani ina zan kai wannan yajin da aka kawo?".

Ta ce,"Yo ai dama na rabo ne ba kawo miki aka yi ki tasa a gaba ki ta ci ba, ki bayar a aika gidan su nasu ne, idan wani zai zo ga na ku ke da Kudrat sai a taho muku da shi. Abbaanku ya ba da rubutu za ki gani ke da jaririn za ku dinƙa sha, wannan baƙin zaren kuma a ɗaura masa a hannu saboda bakin mutane, azurfar ma yace ki saka masa ita ma ta baki ce naji ance jikan nawa kamar balarabe, kinga ba ma zauna ba".

Na kada baki na ce,"Ai Ummani na iya haihuwan ɗa, ki gode Allah na haifa miki jika me kama da larabawa, sai ma dai kin gansa tukunna za ki ji kamar ki riƙe".

Tana murmushi ta ce,"Ina zan riƙe shi uwarsa tayi ƙarata".

kai ni dai ban san haka na ke ƴar gata ba sai da na haihu. Maa bini bini ta kira ni ta ce,"Daughter ya kike da Jikana?". In ce mata muna cikin ƙoshin lafiya. Ana gobe suna ƴan uwana suka zo, Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Saudatu, Umman Batula, Hajjo, har da ƴaƴan wajen Hajjo Juwan da Safna, ƴaƴan wurin Baba Tijjani kuwa babu ko mutum guda, na rasa ranar da zasu gane duniya ba wurin zama ba ce su daina jin haushinmu suna gaba da mu, amma abin na su gaba gaba ma yake yi, musamman ma da suka ga yanda na koma da irin mijin kece rainin da n ake aure, duk sai suka ƙara ƙullatarmu ni da mahaifiyata, mu kuwa duk basa gabanmu. Ni dai naji daɗin ganin iya wa'annan ma da sua zo matuƙa, ranar har rasa inda zan tsoma raina nayi saboda daɗi.

Har ranar suna ban san da wanne suna Mahbub yaywa jaririn huɗuba ba, tunda na haifesa na ke ta tambayansa wanne suna ya saka masa sai yay murmushi yace,"Myy ki bari ai sai ranar suna ake faɗa ko".

Na ce,"To ai dai ka san wanda zaka saka tunda ka masa huɗuba, ni ba Mamansa ba ce, tsakani da Allah sai ace nima sai ranar da kowa zai ji nima zan ji".

Ya ce,"To me ɗa, ai kaɗai kika yi aikin haihuwan, sunana ne to nasa amma sai ranar naɗin suna kema za ki ji, da ake min gori da ban bayar ba a haifa ne, kima gode min ki ban kyauta na iya jefa ƙwallo a raga".

Dukan wasa kawai na kai masa a ƙirji, duk nacin da na saka masa sai da na haƙura. Ina ɓata fuska na ce,"Kuma ma idan suna mara daɗi ne ka saka masa idan ba sai ka ƙara yanka rago ka sauya masa ba".

Ranar sunan bayan ya dawo daga masallacin asuba, ina ɗaki na fito a wanka kenan, sai ga Rofi'a da gudunta ta faɗo jikina, na ɗauketa ina cewa,"Rofi'a na haneki wannan gudun, tiles ɗin nan bai da amana akwai santsi, wa ma ya tasar min ke da wannan farar asubar?".

Cikin gwarancinta tace min,"Paapa yace kije yanzu, Mommy yau a goya min Baby".

Na ɗaga mata kai,"Ehh za'a goya miki".

Na ajiyeta, na karɓi jaririn a hannun Mama A'i da ta gama shirya shi, ɗan albarka ba dai kuka ba da tsotso, daga karɓarsa har ya farka a barcin da ya fara zai yi halin kukan. Na yafa babban towel akaina ban tsaya shiryawa ba, ni kam ban ɓata lokaci wajen amsa kiran mijina, na fita a ɗakin ina ta yiwa yarona wasa duk da uban kukan da yake tsalawa, ni dai hakan ma daɗi yake min, ina kallonsa da murmushi ina shaƙe ƙamshin turaren da aka fesa ma kayansa masu kyau.

Yana zaune kan carpet ya baje alawan suna da biscuite na same shi, hannu ya miƙa ya ɗakko filo yasa min na zauna akai, ina gaida shi bai amsa ba ya hauni da faɗan bar masa yaro da nayi yana kuka. Ni kam ban jin daɗin wannan faɗan nasa wallahi, yana gani fa duk yaron ya ruɗa ni amma ce yake ina ɗaukar hakkin yaro. Ina gyara zan ba shi nace,"Mahbub ka fa san halinsa da kuka, yanzu na fito a wanka na karɓe shi hannun Mama A'i, kuma wallahi bacci ma yake yi fa, na taho zan zame zani ne a hanya ina ba shi".

Wani kallo yay min da cewa,"A waje kike, ba cikin gidanki ba ne, zanen ai ba duka za ki kunce ba ko".

Ni dai ganin ya hasala na shiga ba shi haƙuri, kuma a hakan saboda yaron yaƙi kama nono nan ma ban tsira ba laifina ne. "Myy ba na son irin haka, bana jin daɗin kukan yaron nan wallahi, ke idan ni ina da nonon basa ma kya ga ina miki faɗan ne balle har kike cin magani kina turo ba ki gaba".

Kamar zan kuka na ce,"To kaga fa yaƙi kamawa".

"Ta ina zai kama dama, har yanzu kin kasa koyar yanda za ki dinƙa ba shi, wannan rashin imani ne kawai, na rantse miki idan ɗana ya samu matsala akan rashin samun ruwan nono idan ranki yay dubu sai ya ɓaci".

Idona ya ciko da ruwa kawai na saki nonon ina ce masa,"Ai sai ka basa da kanka tunda kai ka fini iyawan".

Ya galla min harara yana kama nonon ya saka masa a baki, kuma da gasken ne ya fini iyawa, ni ko da yaushe haka muke fama wajen saka masa a bakin, kuma idan na tashi in rufe masa hanci, ko bai niyyan kukan ba sai ya tsanyare dalilin hakan, Mama A'i tayi ta faɗa kamar zata buge ni.

Ina aikin ɓata fuska kan faɗan da yay min ina kallon yanda ya riƙe nonon da kyau ya saita yaron na ta sha abinsa, na jisa yana cewa,"Suna yaci, me zamu dinga ce masa?".

Lokaci guda na bar fushin, na bar kallona daga kan jaririna na dube shi ina murmushi na ce,"Sunan wa yaci?".

"Ke dai ina ruwanki, laƙabi kawai na tambaye ki".

Na san ba zai wuce sunan mahaifinsa ya saka ba, na dubi yaron ina kallonsa cike da wannan soyayyar da take daban da kowacce soyayya wato soyayyar uwa, na shafo sumar kansa ina cewa,"Ayman yayi?".

Sai shima ya ɗora nasa hannun saman nawa muna shafa kan yaron a hankali yace,"Da yare kuma muce masa Emeka".

Nace,"Wow, to Mahbub baka faɗa min ainihin sunansa ba ai". Ya manna gefen fuskarsa da tawa cikin kunnena ya raɗa min,"Sunan Abbaa".

Ban san sanda na juyo gaba ɗaya ina sakin Ayman ba in fuskanci mahaifinsa. "Mahbub sunan Abbaa nah ka saka?".

Ya jijjiga min kai yana shafa fuskana, na rungume mijina cikin hawayen farin ciki da jin daɗin da suka shiga sakko min. Godiya na ke masa ina kwarara masa adu'a iri iri. Wallahi sai na ƙara jin sabuwar ƙaunarsa ta kama ni, darajarsa da kimarsa da mutuncinsa sun daɗa hauhawa a idona, ina ƙara alfaharin samunsa a rayuwata, ta kai ga har na fashe da kuka wanda ba na komai ba ne sai tsantsan farin ciki. Ban ma iya tashi naje ɗakina ɗakko wayata ba, da wayarsa na kira Abbaa na shaida masa Salim yay masa takwara, Abbaa shima yaji daɗi sosai.

Cewa yake,"Da gaske Salman yay takwara Salman, ai kuwa mun gode da wannan kara da aka yi mana, Allah ya albarkaci rayuwan Salman yasa ya zama mahaddacin alqur'ani".

Na haɗa su a waya Abbaa na ta saka masa albarka da adu'a, irin adu'an da har sai da jikin Salim yay sanyi.

Nima ɗin adu'a na ke daɗa masa ina cewa,"Allah yasa ƴaƴanka su zama masu jin ƙanka". Ƙarfe goma muka shirya muka tafi can gidansu Anambra, da ke a can ne za'a yi taron sunan, gida ya cika maƙil da jama'a, kuma iyaka familyn su ne ba wasu ba, sai abokan wajen aikina, to sai jama'ar Kudrat ma da ta yo gayya guda ita uwar ɗa, sai ƴan uwana da ba su wuce ƙirgen yatsun hannu ba. Ranar dai anyi shagalin suna iya shagali, taro na gani a fada na a buga a jarida, kuma an buga ɗin kuwa, yau an wayi gari Sa'ida Salman da yarona Salman sun kafa tarihin shiga jaridar duniya.

Na yi shigan suna na haɗuwa, in saka in cire kace sabuwar amarya, ni da yarinyata Rofi'a shiga iri ɗaya muka dinƙa yi, haka itama Kudrat da yaranta, ashe har anko tayi mana ban sani ba sai a ƙarshe da taro ya kusa watsewa ne take cewa to ga ankonmu har da Mijinmu, haka muka yi shigan irin kayan yarensu na saƙi, mun yi kyau sosai aka mana hotuna, Paapa daɗi ya cika shi baki sam yaƙi rufuwa.

Ni dai kyautuka sai in ce har gajiya da karɓa nayi, na samu kyauta Ayman ma ya samu, yo kayan da Ayman ya samu ai har ya girma ba zai saka wasu ba, gaskiya dangin Salim sun yi a rayuwa, dangin mutunci dangin karama, dangin bugar ƙirji, yau ko ba na jikina ba zan wa mace kwaɗayin shigowa cikin wannan ahali na ban girma.

Bamu tafi ba sai washe garin ranar suna, lokacin zamu tafi mun jewa Sir sallama ya bani takardun fili ɗauke da sunan Salman Salim Sadiq(Emeka Oluwa), sai naji sunan ya ƙara burgeni, mallakin ƙaton fili kyauta daga kakansa, ashe haka suke, idan suka samu ƙaruwan jika sai kakansa ya mallaka masa kadara me girman gaske, to shi Baban su Salim jikokinsa duk filaye yake ba su kuma manyan filaye, da yake gaskiya ba wani talaka a familyn kowa da rufin asirinsa iya gwargwado, sai dai mahaifin su Salim ɗin duk yafi su kuɗi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull