Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 39
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 39: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 39. Ni dai sai kewa ta gida kawai da ta zama dole, banda ina da iyaye…
4,499 words
Ni dai sai kewa ta gida kawai da ta zama dole, banda ina da iyaye a raye ai zai mance ne ma da garin Kano. Iyayena duk sanda muka yi waya da su tambayan farko ya kuke da abokiyar zamanki kafin ya kuke da mijinki zai biyo baya, kuma wannan na san dan sun san yana sona ne banda matsala da shi, ba kuma mayin sallama sai na kaiwa Kudrat sun gaisa musamman Abbaa, kafin yanke kira zai ce min kaiwa Kudrat, ba ƙaramin daɗi suke ji ba da sakamakon canjin da na samu.
Ƙarshe ma Abbaa sai karɓan lambar Kudrat yayi, sai dai naji tace,"Momin Rofi'a ɗazu muka yi waya da Abbaa yace yana gaida ke". Har na ke mamaki ganin fa ni bai kirani ba amma ita ya kirata.
Wata rana kuwa muna cikin kallo sai ce min tayi,"Da safe mun yi waya da Ummani, tana cewa aiken me zata saka a mota a kawo mana nace mata daddawa da kuka".
Ba shiri na juyo ina kallonta nace,"Amma kuwa kin cuce mu, aike tun daga kano mu ƙare a daddawa da kuka". Tana dariya sosai tace,"Idan ba zamu yi amfani da shi ba sai mu koma sana'arsa, za ki kyau da me siyar da daddawa, a bakin gate Paapa zai mana banch". Na kira Ummanin ina cewa ni ban yarda da wannan batun ba, sai ce min tayi ai bani tace zata kawowa ba ƴarta zata kawowa.
Ina cikin wata na takwas Salim ya biya mana saudiya, lokacin za'ai aikin hajji, duk bamu san da tafiyar ba sai da ya rage saura satika, ni dai kamar an tsunduma ni a aljanna haka naji, ita kuwa Kudrat da ke ta jajje normal taji ta. Wallahi tsabagen farin ciki ban iya bacci ba a ranar, kwana nayi ina godewa Allah na, kwana nayi ina zabgawa Salim adu'a, godiyan farin ciki har da su kuka. Yace min,"Mene na kukan kuma, in dai saudiya ne yanzu kika fara zuwanta ke dai Allah yaci gaba da buɗawa".
Kudrat ita da yaran suka fara tafiya amma banda Rofi'at tunda ita a wurina take, ni da shi sai da muka biya ta kano, sai fa lokacin na zo gida tun auren, duk sanda nayi maganar zanje sai yace na bari sai ya samu hutu me yawa sai ya kai ni da kansa naje in yi kamar two weeks, tun ina maganar ina nacin har ma nayi fushi na daina, Ummani ma da na ke mata ƙorafi take ƙara nanata min auren daa sai afi shekara ma ba'a je gida ba.
Zuwan nawa kuwa ba ƙaramin farin ciki iyayena suka yi da ganina ba, musamman ganin na ƙara canjawa kamar ba Sa'idan da suka kai ba, ƴan uwana ma farin cikinsu ba zai misaltu ba. kwana na huɗu ina zazzagawa dangi da ƴan uwa da abokan arziƙi, gidan Safiyya na fara zuwa na yini sai dare ya zo ya ɗauke ni, da yake shi a gidan su Safiyyan yake kwana, naje gidan Hassana Tijjani da Maimuna, duk wanda ya ganni sai yay sha'awata sai yay min murna. Satinmu ɗaya a kano jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki, la'ila ha'illah Allah ya kira duk wani musulmi zuwa wannan ƙasa, ni ban ma san ta yanda zan musalta muku irin daɗin da na ke ji ba, wani irin sanyi me daɗi da shauƙi zaka ji yana ratsa jikinka tun a jirgi, a sanda ƙafafunka kuwa su ka taka ƙasar ji zaka yi gaba ɗaya yanayinka ya sauya, Allah Alhamdulillah, godiya gareka a bisa tarin ni'imomin da ka yi min, a can muka samu su Kudrat su har sun buɗe ido ma don satin su guda.
Na ziyarci ɗakin Allah, na ɗaga hannu nayi kuka nayi kuka, ba kukan rashin wani ahu ba face zallar farin ciki, kuka na ke na tsantsanin farin cikin ganina a gaban ka'aba ɗakin Allah, ga ni gata ina taɓata, Ya Allah! Hawaye kuwa da yana ƙarewa tabbas zai ƙare a sanda na ke gaban ka'aba. A duk sanda na je ƙabarin manzona da kuka na ke barin wajen, ni kawai ji na ke kaman in ƙare rayuwana a gaban wajen, ko da mutane zasu dinga tattake ni suna bi ta kaina, in sallamar in ƙara yi bana gajiyawa. Mun yi aikin hajji lafiya lafiya sai fatan Allah ya karɓi ibadunmu, ai kuwa na yi adu'an Allah ya bani halin da zan kawo Abbaa da Ummani wannan waje, haƙorin makka ai har biyu na saka, wai muna bidiyo da Safiyya ce take to farin shiga kar dai ki dawo mana kina faman yaƙe haƙwara, Ummani ma tace Hajiya Sa'ida haƙorin ya ƙara miki kyau sosai.
Watanmu guda curr da ɗoriya muka fara haramar tafiya, har ga Allah da ni na kawo kaina wallahi ba zan tafi ba, ai nan kuma naga wurin zama, kuka har da su majina zan bar saudiyya. Da saudiya kuwa Dubai muka wuce direct, kaman a zuwa ne Kudrat suka wuce gida najeriya, ni da shi da Rofi'at kuma muka wuce dubai ɗin yace kamar yanda ya kai Kudrat nima hakan ne. Ai ko dai mun yawata a dubai, tun da muka je ba zama kamar wadda taci ƙafar kare, har ce masa nayi dama a can Saudiyan ka bar ni wallahi.
Dubai ma fa ba dai kyau ba, arziqi me daɗi, inda kuɗinka ka sha shagalinka, haka na dinƙa bugawa Salim ƙauyanci yay ta dungure min kai yana ƴar madobi kawai. Ni kuwa da na samu sake a wurinsa bai hana ni fita ai sai na nemi wuce gona da iri, ko yana gida saɓar Rofi'a na ke mu fice inje in ta sakar laɓɓa ina ganin dogwayen gine gine, in ta jido siyayyan kaya yanda na ke kwasan abaya kun ce sana'arta zan fara, haka na yita yawon buɗe ido sai dai muyi waya da shi in ce ina wuri kaza. Aikuwa a sati ukun da muka yi a dubai nayi wani fari kamar me shafa mai, fatana tayi sulɓi sai kace hutu na ke samu, ni dai to ban huta ba sai in ƙasar ce ta amshe ni, yo ban zama ina naga ta zama, yawo kullum ina kan hanya, yay ta mitan in barsa ya dirji soyayya a yanda ya samu hutun aikin nan, nace enaa ai soyayya ka jira mu koma delta, haka yake haƙura sai daren nan amma da safe da rana ina can na tafi galantoyina ni da ƴata, nayi wata ƙiba yanda ku ka san ina shan sha ka fashe, shi kansa Salim sai da yace ko sai yanzu Kunun Tamba ɗin da kusan kullum muke break fast da shi ya fara bin jikina, tunda yana saka ƙiba mutum yay mulmul da shi, Kudrat ƴar sharri har da cewa ko dai surgery naje aka min a kumatu suka yi luhu luhu haka kamar fanke.
Sai da muka yi sati huɗu ciff kafin mu ɗakko hanya, ina ta ce masa yaywa Allah ya tattaromu mu dawo Dubai da zama, me ake da wata lanjeriya, ya biye min kawai da cewa,"To! mu dawo nan ku ga bayan ATM ɗina ko, ko da yake dama ai ga ƴan naija ɗin nan suna ta tahowa aikatau, idan kun ƙarar da ni sai in koma shara da wanke wanke tunda salery ɗin da yawa". Nace,"Allah ya rabaka ya kiyaye". daga nan nace a bar zancen, sai yay ta dariya.
Bamu wuce delta direct ba sai da muka sauka a kano na kaiwa iyayena da ƴan uwana tsaraban Makka da Dubai, aike har da Hassana Tijjani, Salim ya kyauta min muka je har wudil wajenta, ranar tayi farin ciki nima kuma nayi, don gaskiya Hassana tana da matuƙar kirki. kwananmu biyu a kano sannan muka wuce gida. A tsaraban da na yo zan iya cewa gidan su Salim in har a cikin gidan kake ko da tsinke ne kai to ka samu tsaraba daga wurina, kowa yaji daɗin karan da na musu sai cewa suke Allah ya maida ni don na iya tafiya.
Shekarana ɗaya da wata biyu da aure na fara shirin tafiya ƙaro karatu, kamar yanda muka yi da Salim dama yace min ba zai hana ni ba idan ina so, sun yi maganar ma da Abbaa, ko ina na ke so zai ƙyale ni naje kamar yanda ya bar Kudrat itama lokacinta.
Da muka yi waya da Ummani take cewa,"Sa'ida me yasa ba za ki bari sai gaba kya ɗora ba?". Nace,"Ummani ai gwari in yi in wuce wurin kawai, shekaru ƙara tafiya suke, kayi da ƙwarinka zai fi, kuma wata ƙila yanzu ne damar tawa". Tace,"Haka ne, to Allah ya taimaka ya bada sa'a".
Harvard University ita ce makarantar da na zaɓa, da naji kuɗin makarantar sai da na razana, na cewa Salim,"To ko dai kawai na haƙura nayi anan?". Yace,"Babu komai Allah zai yassare, zan yiwa Sir maganar yana da hanya, zai samar mana insha Allah".
Nayi farin ciki sosai, Salim ya ƙara ƙima a idona. Sai a lokacin ma na ke basa labarin wancan lokacin ma da na tafi wani bawan Allah ne ya ɗauki nauyinmu, yace,"Allah sarki ai kuwa ya kyauta haka ake so masu shi su dinƙa aikin alkhairi, sai Allah ya daɗa buɗa musu, Allah ya saka masa da alkhairi".
Na ce,"Amin Mahbub, wallahi ka ga ni dai har yanzu duk adu'ana sai na saka shi a ciki, ko da muka yi aikin hajji ma Mahbub sai da na ta faɗawa Allah na ce ya yalwata dukiyar bawansa kuma ya dawwamar da shi a farin ciki da kwanciyar hankali, yay masa sakayya da gidan aljannah".
Yay murmushi da cewa,"Allah ya amsa Myy kin masa adu'a me kyau, haka ake so ai mutum kar ya zama me manta alkhairi".
Na ce,"Wallahi dai wanda yay maka gata haka ina zaka manta da shi, mutumin da ya kawo maka canjin rayuwa, banda silar ina ni ina taka matakin da na kai. Ni dai Mahbub ka ga har sadaƙa ina yi masa fa, wainar da kaga ina sadaƙa duk friday gare shi na ke cewa Allah ya isar da ladan ai ban iya kuskure ba ko?".
A lokacin kawai sai naga ya dire laptop ɗin da yake dannawa ya rungume ni, ni dai na jima bai min runguma irinta ba, yay shiru kamar me bacci ina ta shafa kansa ni kuma, don naga kamar natsuwa yake so ya samu da hakan, sai can tsawon wani lokaci tukunna na kira sunansa sai ya sake ni yana cewa,"Allah yay miki albarka Baby, na gode sosai da sosai Allah ya jiƙan mahaifanki ba don sun mutu ba, ki ci gaba da masa adu'a da sadaƙan Allah ya amsa ya raba muku ladan".
Na tambayi shi adu'an fa na mene, sai ya manna min kiss yana cewa,"Na soyayyanki ne, Allah ya raya min ke in ga auren Rofi'a".
Nan fa na gyara zama na shiga karanta masa wata wasiƙa kamar yarinya, wai zancen tanadin auren Rofi'a na ke tun yanzu yarinyar da gaba ɗaya shekaranta biyar ne. Shi kuwa sai ya kama dariya yana,"To ko Babar Forida ita me shekara goma sha huɗu ma bata fara zancen aurenta ba sai ke, sannu kin ji".
Ina jina a cikin nishaɗi nace,"Ita Babarta ba sonta take ba, ni kuwa ina son ƴata, saboda haka ka buɗe asusun tari tun yanzu kafin nan da lokacin da zan aurar da ita ka tara min da yawa, Mahbub tsinke ba zan siyawa Rofi'a anan ƙasar ba kaji ma da kyau".
Yay dariya kawai yana cewa,"To Myy Allah ya bamu aron rai da lafiyar kaiwa lokacin, insha Allahu za'a yiwa ƴarki komai kike so, ai Allah ya hore sai dai mu roƙe shi ya ƙaro mana".
Nace,"Amin zamu kai ma in Allah ya yarda, mu da har jikoki sai mun gani, magana ake ta shakara ɗari...Wa yaga surukai sun fara min suntiri a gidan nan, ina ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ina kallonsu ta cikin gilashi, Mahbub ba fa zan bawa yarana munana ba kar ma mummuna ya zo ka tsaya ce masa zaka yi shawara da ni matar gidan, ni dai ƴata me kyau zan aura mata, sai in Babar su Forida ce ban san ba ko ita zata aura musu mummuna, ita ka santa ƴar i dont care ce, ni Rofi'a ta me kyau ce kuma me kuɗi ɗan ƙasar waje, me irin halin Babanta. Yauwa kuma ka shiga tsakanina da Babar su Foridat da ke cewa yarinyata mummuna, zan iya shari'a da ita akan hakan, ba mummuna ba ce ni kuma ban haifi mummuna ba, ban kuma auri mummuna ba duk dai shima ba wani kyan garesa ba".
Aje laptop ɗin yay ya turmushe ni akan gadon yana rufe bakina da nasa, wai na cikasa da magana, kuma zan ƙara maimaita bai da kyau, muka shiga kokawa akan gadon kaman wasu yara, irin wasan da ban san da irinsa ba a baya, haƙiƙa ina son mijina sosai da sosai. An sama min Harvard University ɗin, da zan tafi ni ɗaya na tafi don lokacin Salim na bakin aiki, naje kano na yiwa su Ummani sallama, Safiyya ma naje gidanta Allah sarki tana ta fama da laulayi, a gidan Hajjo na kwana, washe gari na je gidan Mama A'i kafin na dawo. Da zan tafi Maa da Sisters ɗinsa ne suka min rakiya airpot, Kudrat har da hawaye zan tafi na barta da kaɗaici, Rofi'a kuwa da ƙyar muka rabu yarinyar nan Mommy nah kawai take kira, to ni rabuwarmu da ita ne ma ya saka ni hawaye, ga shi Salim yace ba zai yiwu in tafi da ita ba.
Watana takwas a america muna gab da fara exams na kwanta rashin lafiya me tsanani, lokacin Salim yaje min satinsa uku kuwa da zuwa. Yaje ne musamman saboda taya ni murnar birthday, ƙarin shekaran ma da na mance sai ranar ga shi da gift ɗinsa, har ya kira min Yara vedio call na gansu da cake a gaba, Kudrat na cewa suma za su ci na u cake ɗin anan. Ciwo fa ba na wasa ba na kwanta, abu tun ana zuwa asibiti ayi allurai a bani magunguna, ta kai da sai da muka koma haɗawa da tasa tasai iri iri duk sai da na gaji da ɓula ni da ake yi.
Ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa abu kamar ba zan rayu ba, Salim da ke ta son tafiya ya gagara tafiyar sai rubuta takarda yay a wajen aiki, abu dai yaga ba zai kai mana ba daman zaman exams ne ya riƙe ni haka dole na aje semester ɗin muka rankayo muka yo gida. Wuya dai iyaka wuya ina shanta, na koma marabata da matacce numfashi kawai, don komai yi min ake bana iya yin komai da kaina. Hankalin iyayena ya tashi a wannan lokacin ne kuwa dole suka ɗakko hanya suka aje kunya a gefe suka zo gidana, Mahaifiyata har da hawayen tausaya min, Abbaa nah kuwa don bai da yanda zai yi ne amma da sai ya zauna zaman jinyata, ga alkunyan iyayen Salim ɗin da ke ta faɗi tashi akaina ba zai barsa cewa za su tafi da ni gida in jinyar a can ba, duk wanda ya ganni sai yace anyi gwaje gwaje kuwa?
Salim har ya rasa amsar bayarwa ya dinƙa yi, to babu kalar gwajin da ba'a min babu wani ciwo da aka gani ba, general checkup har sau uku aka yi min, a america sai da ya kashe sama da ɗari biyu akan general check up kawai, dama a can aka min sau biyu, ɗayan kuma sai da muka dawo nan. Ciwo ya daɗa ta'azzara ina ta ƙarewa, lamarin ya bawa kowa tsoro matuƙa, sai da ta kai ga an koma yi min maganin islamic don na hausan ma aje shi aka yi, shima bai yi to, duk irin magungunan da yare ke da shi su kansu sai sallamawa suka yi. Sai aka fara tunanin wai ko sammu aka min, haka aka dinƙa banka min hayaƙi wani sai nayi kamar zan shiɗe, gidanmu ya koma gidan Malamai masu ruƙiyya, sauraron ƙur'ani kuwa 24/7.
Watana uku a kwance ina shan baƙar wahala, Mama A'i ita ta zo ta zauna da ni saboda hidimar ta yiwa Kudrat yawa, baiwar Allah nan ita ke min komai, bata samun hutu ga office ga ɗawainiyan yara, kai ai Kudrat ta wuci a kirata kishiya sai dai ƴar uwa, don ni a yanzu ma na fi jinta a jikina fiye da yanda na ke jin Safiyya, tun balle zuwan Ummani da ta mayar da ita kamar mahaifiyarta. Nayi amai ta kwashe, na ƙara yi ta kwashe, ta bani abinci na kasa ci, shi Salim ɗin ma ta fisa ƙarfin halin jinyar tawa, saboda shi hankalinsa ne duk ya tashi gani yake kamar tafiya zan yi na bar su.
Wata rana ciwon ya tsananta min cikin dare haka muka ɗunguma sai asibiti, muna tafe kan titi mota na jiniya matar laftanar ba kanta. Da zuwanmu kuwa aka bamu kwanciya. Karon farko tun kwanciyar tawa da aka min allurai aka sa min drip naji daɗi, lokaci ɗaya wani salamman bacci ya zo min. An ce na jima ina bacci don tun cikin daren nan sai washe gari da rana na farka, farko suna zaton ma ko na mutu ne aka ɓoye musu, likita ya ce musu da raina yau ɗin ne dai aka yi nasara alluran baccin ya kama ni, kuma ƙari ma da daɗin jikin da na ɗan samu.
Naji daɗin jikin nawa kuwa, don da na farka babu ciwon cikin, babu inda ke min ciwo kwata kwata, sai dai rashin ƙwari da ɗanɗanon baki irin na wanda ya sha doguwan jinya. Har ma na samu damar miƙewa zaune da kaina, muna hira da Mama A'i da wata Aunt ɗinsa da Kudrat sai ga shi ya shigo ɗakin, Allah sarki shima duk ya faɗa sosai sai dai yanayin fuskansa bai nuni da damuwa a washe take.
Mama A'i da Aunty Adamma suka tashi suka bamu wuri, Kudrat zata fita ya ruƙo hannunta, kawai sai ya faɗo jikina ya rungume ni sosai yana faɗin,"Myyy Congratulations, Congratulation to us Myy".
Kuma faɗin nasa yay daidai da tsala ihun murnar da Kudrat tayi tana buga tsalle ta dire bayan gama duba takardan da ya bata, sai gata itama ta faɗo jikina sun rungume ni gaba ɗaya sai murna suke. Ni dai mamaki ya kamani kaina ya ɗaure, murna a halin da na ke ciki? a hankali na ke tambayarsu menene. Kudrat ta ɗago a jikina tana faman juyi da takarda a hannu, na bita da ido kafin ta miƙo min hannu tana cewa,"Kinga ban tukwici tukunna". Sai na ɗauke ido akanta na maido kan fuskar Salim da ke ta kallona kamar zai cinye ni.
Kudrat ta zagayo ta bayansa ta kama kafaɗuna tana girgiza ni cikin wani irin farin ciki. "Ki yi murna mana, kin fa warke Mommy, ki sakko ki yi tsalle muyi rawa, ciki ne da ke har na 5months, za'a ma mummuna ƙani ko ƙanwa". Sai tayi shiru kafin ta ƙara cewa,"Amma dai sai na ranƙwashi kan Babyn nan, ya san shi ne yaƙi bayyana kansa yake ta wahalar da mu, sannu Mommyn Rofi'a, tumbin da na ke ta yiwa tsiyan yana cin maiƙon America yana girma ashe Babyn mu ne a ciki".
Hannun Salim cikin nawa yana shafawa ina ga tsabagen farin cikin da yake ciki ne ya hanasa yin magana. Ni kuwa tuni na daskare ina ta kallon Kudrat na kasa wani motsi, sai a hankali idanuna ke ƙiftawa. So na ke na harhaɗo kalamanta in cure su wuri guda su bani ma'anar nufinta, don na kasa fahimtar komai daga abinda tace. babu abinda na gane kuma babu wata kalma da nayi capturing idan ba pregranant ba, Abinda na ke so na gane tana batun cikin wata biyar ko? To cikin haihuwa take nufi ko na cin abinci ko na me? Idan na haihuwa ne a jikin wa yake? Na san dai ba a jikina yake ba, idan kuma a jikin nawa ne to sai in wani cikin na daban ba na haihuwan ba, ina alamar samunsa ma? Ciki har 5month ba alamun fitowansa? To ba dai ni ba domin kuwa na shekara goma sha ɗaya a gidan aure na farko ban taɓa ɓatan wata ba balle ɓarin ciki, haka yanzu cikin aure na biyu ina a shekara ta uku ne kuma tun da na zo ni dai ban san lokacin da na yi ɓatan wata ba.
Fahimtata da suka yi ne yasa shi karɓan takardar ya miƙo min, na karɓa ina sauke ƙwayar idona akansa, sai ya ɗaga min gira yana cewa,"Ba ta yanda Allah ba ya lamarinsa, babu me haƙuri da tawakkalin da baya cin nasara, babu wanda ke miƙa lamarinsa ga Allah ubangiji bai dube shi ba, kuma mafi yawan jinkiri alkhairi ne, ga sakamakon jinkirin Myy, ga sakamakon haƙurin Myy, ga sakamakon tawakkalin Myy, dama na faɗa miki kar mu fidda tsammani, Allah ke bayarwa kuma zai bamu to ga shi ya ƙara bamu, ki gode masa Myy".
Duk da a daskare na ke amma na gane duk me ya ce, sai dai kuma kalamin nasa ne ba na tsammanin zuciya da ganganar jiki za su ɗauka har su yarda. Na dubi takarda a hankali na shiga karanto bayanin da ke nuni da sunan Sa'ida Salman Madobi da ke rubuce a sama, tana ɗauke da ciki har na tsawon wata biyar.
Naji na girgiza akan gadon da na ke, na rufe ido na buɗe, na ƙara rufewa na buɗe har sau uku, na ka kai hannu na mari fuskata kafin na mintsini kaina, ba zan iya gasgata abinda na karanta ba har sai na tabbatar da ba mafarki na ke yi ba tukunna.
"Myy ba mafarki kike yi ba, zahiri ne, kuma a zahirin ma kina riƙe da takardan gwajin da ya bayyana kina ɗauke da ciki, kina ɗauke da halittar yarona a cikinki Myy, kin zama BabynBaby".
To kukan da ya zo min na menene? Kawai dai naji saukar hawaye kafin fitar sautin kuka ina damƙar gaban rigarsa na shiga girgiza kai ina cewa,"Mahbub ciki fa! Cikin haihuwa da ake samu a haifi yaro?, Mahbub ta ina zan same shi? Ni fa bana haihuwa, Mahbub akan rashinta na wulaƙanta, aka tsangwame ni, aka goranta min, aka daina sona, na rasa farin ciki da jin daɗi, 11years ban taɓa ɓatan wata ba ban taɓa ɓari ba, ko a mafarki ban taɓa ganin na haihu ba, sai da aka sauya min suna na koma Juya, Mahbub Dr ba result ɗina ya baka ba, ba nawa ba ne ka mayar mishi ya bani nawa, ka manta a America ma sun duba ba su ga ciki ba, kar mu yarda da wannan ba namu ba ne".
Na ruƙo fuskarsa ina ƙara girgiza masa kai. "Kar ka yarda, ka daina murna Mahbub, ba na so ka saka rai kuma a zo a datse maka farin cikin da aka saka ciki wanda ba zai tabbata ba, ban da ciki, banda ciki Mahbub, ni ɗin Juya ce haka suka faɗa".
Na faɗa da murya me raunin da ke taɓa zuciya, ina fashewa da kuka sosai me ban tausayi.
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR17FT5* Salim ya rumgume ni, hawayena na ta sauka a bayansa, a hankali yake shafa kaina zuwa bayana, kuma cikin natsuwa ya shiga faɗa min tausasan kalamai da suka samar min da natsuwa. Haka na zame daga jikinsa, ina kallonsa da murmushin farin cikin da ba zai misaltu ba nace,"Nima zan zama uwa Mahbub, zan haifa da kaina, zan amsa cikakken sunan mahaifiya, ka tayani godiya ga Allah Mahbub".
Sai sabon hawaye ya sake min shatata, na miƙa hannu na janyo mayafina na yafa, na nemi taimakonsa ya sakko da ni akan gadon. Sallayar da ke kan durowar gefe na ɗauka ya shimfiɗa min, na fuskanci alƙibla na yi sujudu shukur, na jima ban ɗago ba hawaye kawai na ke ina miƙa godiyata ga Allah mai girma da buwaya, mai yin yanda yaso abisa dukkan komai. Sai na samu kaina da kasa ɗagowa har sai da Salim ya ɗago ni, dole na shiga ruɗa ni, domin abinda ban taɓa tsammanin zan samu ba ne, kuma rabon da na cire rai da shi tuntuni.
Ko bayan aurenmu da Salim na nuna masa damuwar rashin haihuwata sai dai shi ata ɓangarensa ko da yaushe yana faɗa min tausasan lafuza ne na kwantar da hankali da ƙara miƙa lamura ga Allah gami da yin tawakkali da duk yanda mutum ya riski kansa a ciki, balle ma ni Rofi'a kawai da suka mallaka min halak malak ta ishe ni wallahi, sai ga shi kuma ashe ina da rabon samun nawa na kaina.
Ina ta ɗokin na karɓi waya na sanar da Ummani ashe tuni Kudrat ta riga ni isar da albishir, Ummani tsaban farin ciki sai da ta ɗauke wuta a sanda ake faɗa mata, domin su kansu iyayena sun fidda rai akan haihuwata, ganin a wannan auren ma cikin shekara ta uku babu wani labari, na su zaton ina daga cikin waɗanda Allah ya rubuta basu da rabon samun haihuwar ne har su koma gare shi. Ina daga zaune kan sallayar na kai hannu saman cikina, farin ciki na ke yi haka kuma mamaki na ke yi, wai ɗan mutum ne a cikina, sai yanzu ma batun rashin yin period ya zo cikin kaina, ni duk wannan kumburin cikin da na yi wallahi ce na ke tumbi ne kawai, don har tsokanata Kudrat ke yi da shi kansa Salim ɗin, to abunda bamu sa ran samu ba ne shiyasa cikinmu babu wanda ya kawo batun ciki a ransa, don har ina ta cewa zan nemi maganin rage tumbi, a lokacin ma har Maman Yasmin na faɗawa take cewa to ai na zama Hajajju ina cikin hutu da jin daɗi ai dole na yi tumbi.
Aunty Adamma da Mama A'i suka shigo fuskoki washe cike da murna, barka suke ta min, Kudrat kuwa faɗi take ai sai na bata tukwici zamu bar asibiti, na ce,"To Madam ai in bayarwar zan yi Paapa zan bawa".
"Noo ban yarda ba woo Mommy, ki bani kawai in ba haka ba kin san dai na san ai na ATM na ki yake".
Dariya nayi sosai, bata barni ba a dole sai da nasa Salim ya tura mata 10k idan mun koma gida zan ba shi, tunda wayata na can. Ni fa banji kunya ba sai da aka sanarwa da su Maa, duk sai naji kamar na nutse, yo ina ta murna kaman zan shiɗe ina na tuna wata jin kunya ma lokacin da muke magana da Ummani da Abbaa. Sai da na ƙara kwanaki biyu a asibitin kafin aka sallame mu, wallahi har a sa'ilin gani na ke kamar daga baya za'a zo ace result ɗin ba nawa ba ne, ko kuma na tashi a bacci naga mafarki na ke yi, sai dai babu ko ɗaya daga ciki rabon nawa ne da gaske Allah ya ba ni, bayan tarin wulaƙanci da gorin da na sha a baya, idan na tuna sai na yi murmushi kawai a fili na furta,"Yau ga Juya zata juye nata rabon".