Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 12

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 12

.....his strong hand. However, he had to accept fate. When he arrived at the palace, he went in and greeted everyone, then found a place to sit down. All the royal customs are done, the burial is done with prayers. The priest of the palace said, "The marriage of His Highness Asad and Haneefa, the Fulani woman Maryam, has been arranged for a dowry of five hundred thousand naira." People shouted for joy, but not everyone showed real joy. Some people think that Asad is not very kind in taking care of women, because he has a strong desire for respect. Then each of the enemies smiled, seeing that he also found a wife who would defeat him. When Asad was about to get up and leave the place, the King motioned for him to sit down. As ad bowed his head respectfully. "As ad," His Majesty began with a voice full of pride, "you know, this marriage is a trust for you. Don't forget, she is your sister and the daughter of my favorite in this house, Fulani Maryam. Take care of her as you take care of yourself." As ad he looked at you politely. "So your life is long." The king continued, "I have given permission to open one of your chambers for her. It will be repaired properly, and everything she n

Standalone post2,018 words

SHAFI NA GOMA SHA BIYU.

Gidan Mai Martaba Sarki ya cika da mutane. Kowa na cikin shiga ta alfarma, rawanin sarauta da shaddodi masu walkiya sun cika harabar fada. Manyan baki sun hallara don halartar daurin aure. As ad, ?an sarki, ya fito daga sashensa cikin shadda light blue mai ?aukar ido. Ya sanya hula a kansa, domin ba ya son rawani kwata-kwata yana jin nauyinsa sosai.

Sai dai duk da wannan kyakkyawar shiga, fuskarsa cike take da damuwa. Ba auren kansa ke damunsa ba Haneefa ce, wacce zai aura. Tana ?iya ga Fulani Maryam, autarsu mahaifinsa mai martaba, mace mai zafin zuciya da rashin kirki. Tun yana yaro As ad ya san Fulani Maryam da mahaifiyarsa basu ga maciji ba, kuma Haneefa ta ?auki wannan gaba da muhimmanci kamar gadon kabilanci.

As ad bai ta?a yin za?i ba tun yana ?arami. Umarnin fadar sarauta tamkar doka ne gare shi, kuma ba shi da ?arfin musantawa. Duk da haka, zuciyarsa tana kuka.

"Ba zan ta?a samun mace kamar Ayshatu ba," ya furta a hankali, yana mai shafa sumar kansa da hannunsa mai ?arfi. Duk da haka, dole ne ya amince da kaddara.

Da ya isa fadar, ya shiga ya gaida kowa, sannan ya samu guri ya zauna. An yi dukkan al adar sarauta, ana kabbara da addu o i. Limamin fada ya ?aga murya "An daura auren As ad ?an Mai Martaba da Haneefa yar Fulani Maryam bisa sadaki naira dubu dari biyar."

Mutane sun yi ihu na murna, amma ba kowa bane ya nuna farin ciki da gaske. Wasu na ganin As ad bai da kirki sosai wajen kula da mata, domin yana da tsananin son girmamawa. Sai daidaikun makiya suka yi murmushi, suna ganin shi ma ya samu matar da za ta yi masa galaba.

Da As ad zai tashi ya bar gurin, Sarki ya yi masa nuni da hannu ya zauna. As ad ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa. "As ad," Mai Martaba ya fara da murya mai cike da izza, "ka sani, wannan aure amana ce gareka. Kada ka manta, yar uwarka ce kuma diya ga wacce na fi so a gidan nan Fulani Maryam. Kula da ita kamar yadda kake kula da kanka."

As ad ya ?aga kai cikin ladabi. "To ranka ya da?e." Sarki ya cigaba, "Na ba da izinin a bu?e mata ?aya daga cikin shashenka. Za a gyara shi yadda ya dace, kuma duk abin da take bukata zan sa a zuba mata. Ka tabbatar kana kula da ita kamar yadda ya kamata."

As ad ya amsa da girmamawa, amma zuciyarsa na cike da mamaki da takaici. Waziri ya danyi dariya a gefe, ya ce, "Yallabai, wannan al amari yana bu?atar hikima."

As ad ya yi ajiyar zuciya. "Waziri, ba na ganin zan iya rayuwa da mace kamar Haneefa. Halayyarta tamkar na mahaifiyarta ce." Waziri ya yi murmushi mai ma ana. "Kai dai ka yi ha?uri, Yallabai. Soyayyar sarauta tamkar lauje ne cikin na?i. Ka ?auki wannan al amarin da hikima."

Bayan shagulgulan daurin aure sun lafa, As ad ya koma sashensa, yana tunanin yadda zai iya rayuwa da Haneefa.

Cikin Masarauta, gidan Mai Martaba ya gauraye da murnar daurin auren As ad da Haneefa. Fada na cike da ?amshi da kyakkyawan tsari na sarauta. Fulani Maryam tana zaune cikin wata rumfa, tana tattaunawa da iyalai da danginta. Fuskar ta cike da annuri, tana jin burinta ya kusa cika.

Haneefa na kusa da ita, sanye da al?yabba mai she?i, tana murmushi. Ta kalli mahaifiyarta, tana dariya. "Mama, bari na tafi wurinsa yanzu." Yayarta ta kalleta da tsawa, "Ke Haneefa! Bakida kamun kai ne? A haka zaki je wurin mijinki?" Cikin tsananin fitsara, Haneefa ta watsa mata harara. "Ke kuma, me ya dameki? Ai yanzu ni matar As ad ce!" Fulani Maryam ta gyara zama, ta ?aga hannu. "Ku yi shiru! Ba yanzu ba, ki jira. Ni zan turaki daga baya. Yanzu ki bar wannan zancen."

****

Dare na yi, Fulani Maryam ta shirya cikin ba?ar alkyabba, ta bar fadar cikin wata mota mai ?yalli. Tafiyarta ta kai ta wani wuri mai nisa, can gefen gari, inda tafkeken daji ya mamaye ko'ina. Da ta isa, ta tsayar da motar ta. Ta kalli duhun da ke gaba da ita, sannan ta taka ?asa a hankali.

Ta isa tsakiyar fili, ta dur?usa, sannan ta buga ?asa sau uku da sanda. Nan take, ?asa ta fara girgiza, iska ta canza zafi. Wani halitta ya bayyana mutum kamar ba mutum ba, yana dariya mai razana, idanuwansa ja kamar wuta. Ya kalle ta da murmushi mai ban tsoro. "Menene diyarmu? Me zaki bayar kafin mu saurareki?"

Fulani Maryam ta ciro wata ?aramar ?walba daga aljihunta, tana murmushi mai cike da mugunta. "Ga jinin jikata ga gashinta na ciro. Jikar tawa dake jinya a asibiti. Ba ta da tsari, ba ta da ibada. Halak malak!" Halittar ya danyi tsalle mai ban tsoro, yana dariya. "Mun kar?a! Aikinki ya cika. Me kike so daga garemu?"

*****

Ta gyara rawaninta, ta kwantar da murya cikin izza. "An daura auren diyata da As ad. Ina so ya zama tamkar bawa gareta. Ya ?aunace ta fiye da kowa. Idan da hali, ka fitar masa da mazantakarsa gaba ?aya. Kuma ka yi masa ciwon da zai dinga sassaka shi lokaci bayan lokaci." Mutumin ya tsaya yana nazari, yana mai buga ?asa da sanda. "Aikinki mai wahala ne. Munganshi yana da tsari, yana da ibada. Amma naga wata kafa. Lokacin da sha awarsa ta motsa ko yana cikin tsananin fushi, baya ambaton Allah. Wannan ne lokacin da za mu iya galaba kansa."

Ya fiddo da wani ?an ?aramin ?walba mai ?amshi mai kashe tunani. "Wannan turare za ta shafa a jikinta kafin ta kusance shi. Zai rude da ?auna gareta. Wannan kuma garin abinci ne idan ya ci, gabasa zai mutu har abada. Amma kafin hakan ya faru, sai ta sa shi ya kusance ta gabanta. Daga nan, sai abinda tace masa." Fulani Maryam ta yi dariya mai cike da farin ciki. "Yanzu dai burina ya cika! Haneefa za ta mallake shi har abada." Mutumin ya yi wata dariya mai cike da zafi. "Amma ki kula idan ya samu nutsuwa ko ya yi ibada a lokacin da turaren ke jikinsa, to komai zai wargaje dole sai tana shagalar dashi."

Fulani Maryam ta ?auki kayan tana murmushi, sannan ta juya ta tafi cikin annashuwa. A ranta tana jin cewa yanzu As ad ba zai ta?a samun kwanciyar hankali ba.

Shin wannan mugun shiri zai yi tasiri ga As ad?

******

Da As ad ya koma ?akinsa bayan taron fadar, jikinsa ya yi nauyi kamar an ?ora masa dutse. Zuciyarsa tana cike da tunani, yayin da wani mugun ciwon kai ya fara tasowa. Yana jin tamkar duniya ta nannade shi. Ya cire hularsa, yana shafa sumar kansa, sannan ya nufi bayi ya yi wanka mai sanyi domin samun nutsuwa.

Ya fito daga wanka yana ?an jin sau?i, sai ya kwanta a kan katifar alfarma mai laushi. Ba a jima ba ya fara jin nannauyar bacci na ?aukarshi. A lokacin da yake cikin barcin, sai ya ji wayarsa tana ?ara. Da farko kamar ba zai ?auka ba, sai kuma ya mi?a hannu ya ?auki wayar daga bedside. Ya dubi sunan da ya bayyana akan allon Ayshatu.

Nan take zuciyarsa ta yi wata irin kuna, amma sai ya daure, ya danna kiran. "As-salamu Alaikum," ya furta cikin raunin murya. Jin kukanta ne ya kara ?ara masa ciwon kai. Ya dafa kansa, yana mai jan numfashi. "Habibie... me ya sa? Me yasa?" Ayshatu ta furta cikin kuka mai cin rai. As ad ya katseta cikin sanyin murya. "Ki yi ha?uri, Ayshatu... banda iko ne." Ayshatu ta yi shiru na ?an lokaci, sai kuma ta fashe da sabon kuka. "Yanzu haka za ka bar ni? Habibie... me yasa?" Ya lumshe idanunsa, yana jin tamkar ana tsinke masa zuciya. "Kitayani biyayya, Ayshatu. Nasani, ke yar albarka ce. Banda yadda zan yi." Kukanta ya ?ara ratsa zuciyarsa, amma ta san cewa duk maganarta ba za ta canza komai ba. Ta yi shiru tana shar?ar kuka har ta gaji, sannan ta yi sallama a hankali.

As ad ya jingina kansa da gado, yana jin zafin abin da ba shi da ikon gyarawa.

A gefe guda kuma, a cikin ?akin Fulani Maryam, Haneefa tana ta kai-kawo, fuskarta cike da rashin jin da?i. "Mama, wai bazan je wajensa ba? Tun dazu nake ro?on ku, amma kun hana ni. Wallahi bazan iya jurewa ba, ina son ganin shi!" Fulani Maryam ta kalleta cikin murmushi mai cike da mugunta. "Ki kwantar da hankalinki, diyata. Na san abin da nake yi." Ta mi?a mata wani ?an ?aramin ?walba. "Ga wannan turaren, ki shafa a hannunki kafin ki tafi. Sannan ki rungume shi da ?arfi idan kin shiga. Wannan ne sirrin nasara." Haneefa ta amshi turaren tana murmushi. "Na gode Mama! Yanzu na tabbata zai soni." Ta juya da farinciki, tana shirye-shiryen tafiya.

**** A cikin ?akin Hajja, Fiddausi ta shigo da fuskar ba?in ciki. "Hajja, kina gani kuwa? Haneefa ce za a ba yaya As ad? Wallahi wannan zalunci ne!" Hajja ta yi ajiyar zuciya. "Ku yi masa addu'a kawai, Fiddausi. Ko ni mahaifiyarsa bai saurare ni ba. Wannan al'amari ya riga ya zama doka." Fiddausi ta tura baki, tana fadin, "Amma Hajja, ai wannan auren ba daidai bane. Fulani Maryam fa? Wace uwa ce zata so ha?a zuria da ita?" Hajja ta dube ta da ido masu nuna damuwa. "Ki rabu da maganar nan, Fiddausi. Na fa?a miki tun farko Sarki ya riga ya yanke hukunci. Kaddara ce." Fiddausi ta yi tsaki, tana jin takaici. "Wallahi wannan abu bai min da?i ba." Hajja ta ce, "Ki yi ha?uri, ki bar komai ga Allah. Ba mu da wani za?i."

Sashen As ad cike yake da yalwar dukiya da tsari irin na sarauta. Babban falonsa yana she?i da fitilar zinariya, kujeru masu ?aukar ido suna zagaye da teburin da aka kawata da tulunan furanni. Daga gefe kuma, akwai tagogin gilashi masu tsawo da ke kallon lambun gidan. As ad yana tsaye a gefen tagar falon, yana waya da Waziri, yana tattaunawa da shi cikin murya mai cike da girmamawa.

Yayin da yake cikin wannan yanayi, sai ya ji wani ?amshi mai da?i ya cika falon. Ya dan waigo da kai kadan amma bai ga komai ba, sai ya cigaba da wayarsa. Amma kafin ya ankara, sai kawai ya ji hannaye masu laushi sun zagaye bayansa, suna rungume shi da ?arfi.

Tamkar an zuba masa ruwan sanyi haka ya ji, jikin sa ya yi matu?ar tsuma, zuciyarsa ta buga da sauri. Wani irin ra?a?i ya sauka a kansa kamar an danna masa ?aya. Ya juya da sauri cikin zafin nama, yana ?o?arin tureta, hannunsa har ya ?aga tamkar zai kai mata mari.

Kafin ya kai hannunsa ga fuskarta, sai kawai ta ?ara manne masa, tana rungume shi da ?arfi fiye da da. Jikinsa ya mutu, hannunsa ya yi sanyi, tamkar an cire masa kuzari. Ya kasa dukan ta. Cikin murya mai ra?a, Haneefa ta furta, "Ranka ya da?e..." Bai san lokacin da ya furta "Uhmm..." ba, yana kallonta da idanuwansa da ke kokarin sauyawa gaba ?aya.

Haneefa ta ?ago da kai daga ?irjinsa, tana kallonsa da murmushi mai cike da mugunta da salo. Idanunta suna ?ara narkar da zuciyarsa tamkar an zuba masa ruwan zuma. "As ad... Na kasa samun nutsuwa ne." Yana ?o?arin yin magana, amma muryarsa ta yi rauni. "Haneefa... me kike yi haka?" Ta ?ora hannunta a ?irjinsa, tana wasa mai laushi. "Na san kai mijina ne. Na san cewa dole ne mu kasance tare. Ina son ka."

As ad ya kalli hannunta a jikinsa, zuciyarsa na rawa. Ya yi ?o?arin tura ta a hankali, amma sai kawai ya ji tamkar ?arfinsa na raguwa. Haneefa ta murmusa, ta ?ara lalla?a ta matsa kusa, tana fitar da numfashi a hankali kusa da kunnensa. "Ranka ya da?e, ba na so ka ji damuwa. Ni zan yi maka duk abin da kake so." As ad ya rintse idanuwa, yana jin tamkar wani kulle ya ?aure masa zuciya. Duk ?o?arinsa na tsayayya ya gagara.

Nikam nace As'ad har ankamu Ne????