
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 19
..... the journalist was recording the interview, after giving a pause to the signs that were showing that he was going to stop, he smiled. "The people of Agadez and Niger must be proud of your existence among them. But if you don't mind, can we know the origin of your roots?" He spoke and the sound echoed in the meeting room. She felt a kind of dummmm in her head, her heart was beating so crazy that she felt like she was looking for my neck, then she quickly controlled herself and remembered the number of cameras in front of her and let out a smile. "I think you haven't been in Agadez for a long time.....or are you a stranger?" He looked at her, then smiled and said. "God help you......I am fully born from Niger......from my tenth grandfather until today.....we just want to hear it from your mouth" Kai said, trying to hide her anger on the boy, because in her mind she felt as if he had said a bad word to her. "I'm like you, I was born here, my grandmother and grandfather..... I don't know any other country after this... not other people after the people of my country, Niger....... this makes me very jealous of my people" She finished with a smile. They went and took it all togethe
๐ *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 19*
Bata dauka haka yawan adadinsu yake ba sai data fito zuwa gurin,fitowartata kamar waa shugabar qasa hasken camera ya fara haskawa tako ina na masu qoqarin daukan hotonta.
Har qasan ranta taji dadi.....har qasan ranta kuma taji ta sake fashewa da wani irin taqama izza da alfarma,sai data zauna sannan kowa ya zauna suka sake miqa gaisuwa bisa wakilcin mutum daya.
Ta amsa musu da salon amsawarta dake dauke da izza da kuma son nuna ita din macece me kirki,kuma ita ta kowa ce,daga bisani ta basu dama,wanda kuma ya kasance shine me wakiltarsu gurin mata tamabayoyi ya matso ya soma gabatar da kansa.
Tambayoyi ne daya bayan daya suia fara mata kan irin ayyukan da ita kanta take gudanarwa al'ummarta. Daya bayan daya take zaqulo dukka ayykan da tayi,manyan ayyukan da dukkaninsu tana yinsu ne saboda ta sake kafa kanta......tana kuma yinsu ne saboda biyan wata buqata ta qashin kanta.
Sai da suka shafe sama da sa'a guda kowanne gidan jarida yana nadar hirar,bayan data dakata alamun da suke nuna takai aya,sai ya saki murmushi.
"Dole al'ummar agadez dana nijer gaba daya su dinga alfahari da wanzuwarki a cikinsu. To amma kuma idan ba damuwa,ko zamu iya sanin asalin salsalar tushenki?" Yayi maganar da sautin daya buga amsa kuwwa cikin dakin taron.
Wani irin dummmm taji cikin kanta,zuciyarta ta wani irin mahaukacin bugawa da har taji kaman tana neman amayota ta wuyanta,sai kuma tayi saurin controlling din kanta sanda ta tuna adadin cameras din dake gabanta ta saki murmushi.
"Ina zaton baka dade da shigowa agadez ba.....ko kuma kai din baqo ne ko?" Idanu yadan zuba mata,sannan ya saki murmushi yana cewa.
"Allah ya taimakeki.......cikkaken haifaffen nijer nake......tun daga kakana na goma zuwa yau.....kawai dai munaso muji daga bakinki ne" Kai ta jinjina tana qoqarin boye fushinta akan yaron,don a ranta sai takejin kamar baqar magana ya gaya mata.
"Ni dinma kamar kai,haifaffiyar nan ce kaka da kakanni.....bansan wata qasar ba bayan wannan......basan wasu al'ummar ba bayan al'ummar qasata ta nijer.......wannan ya sanya nake tsananin kishin mutane na" Ta qarashe da murmushi.
Tafi kuwa suka dauka gaba daya,abinda ya bata relief sosai taci gaba da binsu da murmushi tana addu'ar tambayar ta tsaya iya nan,saidai fatanta da addu'arta basu cilla ko ina ba wata tambayar ta sake shigowa.
"Naji dadin wannan amsar taki,saboda a guraren hira daban daban,wasu na yad'a qarairayin kamar ke din baquwar haure ce iyaye ko kakanni suka shigo" Kai ta gyada cikin nutsuwa.
"Tom....naji dadin haduwarku da adadi me yawa haka......yau zan tabbatarwa da duk me kokwanto qasata da asalina" Saita waiwaya tana duban tafisu,tayi magana da ita qasa qasa,tafisu ta tashi ta wuce,ita kuma ta maido hankalinta kansu.
"Ku jira lokaci kadan,zan baku takardun da zaku yada don kauda wannan zargin daga zuciyar kowa" Ta qarasa fada tana murmushi,duk da zuciyarta cunkushe take da haushin yaron daya tsiro da tambayar,kuma wani irin zargin me qarfi taji ya d'arsu a ranta game dashi,gwara ta nuna musu cikakkun takardunta don kashe wannan rade radin da bataso yayi nisa ko kadan.
Ci gaba tayi da amsa tambayoyinsu na daban,har zuwa sanda tafisu ta qaraso gurin.
"Miqa musu su shaidawa duniya" Mammina ta fada tana murmushi.
Kai tsaye kuwa tafisu harda tuntuben da mammina ta yaba dashi,ta kuma fassarashi dukka cikin saurin isar da saqonta ne ya kawo hakan ta miqawa dandanzon 'yan jarida takardun.
Sannu a hankali suka bude takardun,cikin qasa da mintuna uku suka fara zagayawa a tsakaninsu,wannan ya duba ya miqawa wannan,sai wasu daga cikin su suka fara daukan hotunansu suna miqawa 'yan uwansu.
Ko kusa ko alama bata kula ba,saboda sauran tambayoyin da take amsawa wani d'an jarida daban daya karbi ragamar tambayoyin,har sai da taji kamar sautin maganganu qasa qasa ya fara tashi a gurin.
Idanunta ta aza a kansu,takardun sun fara nisa daga mutanen dake gaba gaba zuwa baya.
"Bakusan a inda kuke bane,bada hujja zai zama kuna yawo da takardu masu muhimmanci haka a tsakaninku?" Tafisu ta fada cikin tsare gida,ta kuma fadi abinda mammina keson fada musu kenan.
"Kiyi haquri.....wani abune yadan rikitar damu,banbancin bayanai ne,bayanan da uwargida ke fada yasha banban matuqa da bayanan jikin takardar" Ya fada bayan ya karbo takardun yana sake kallonsu a hannunsa.
"Kamar yaya?" Mammina ta samu kanta da yin tambayar kai tsaye ba tare data jira tafisu tayi mata tambayar ba.
"Kiyi haquri ki sake dubawa ranki ya dade......takardu ne na qasar Ethiopia,cikakkiyar shaida.....shekarun haihuwa takardar haihuwa ta asibiti original ba jabu ba,harda sanya hannun shugaban qasar dake tabbatar da takardun na asali ne daga tushe ma". Batasan ta miqe ba,batasan kuma ta isa gaban tarin cameras din dake zagaye da ita ba ta, saka hannu ta fusgi takardun cikin fushi.
Gani take qarya kawai yake mata,gani take kawai ya fada ne saboda ya rikitar da ita,ya fada ne saboda alamunsa sun nuna akwai mummunan quduri a tattare dashi.
A birkice take kallon takardar kamar wadda bata taba karatun boko ba. A gigice take bin rubutun daki daki tana karantawa. Takardar zama haifaffiya kuma mallakin qasar Ethiopia ce tabbas a hannunta,kamar dai yadda dan jaridan ya fada da farko.
Idanunta ta daga tana duban tarin tulin 'yan press din da kowannensu shima ita yake kalla. Ta bisu daya bayan daya da idanu. A qalla sunkai mutum ashirin,daga mabanbantan gidajen tv dana radio. A cikinsu batasan adadij mutanen da suke da hoton takardar ba. Batasan adadin mutanen da suka watsa hotunan a take daga daukarsu ba,don ta tabbatar,babu ta yadda za'ayi labari me dumin gaske irin wannan ya shiga hannun d'an jarida ya kwana lafiya.
"Ranki ya dade......nace kodai akasi aka samu?,zaki iya mana cikakken bayanin ya akayi haka ta faru?" Ya sake cusa mata tambayar yana saita camera dinsa.
Idanu ta zuba masa da wani irin wulaqantaccen kallo. Ta sani.....taba d'an jarida abune me hadarin gaske,bashi kadai bama harda iyalinsa gaba daya,koda shi daya ne a guri ballantana gurin cike yake da abokan aikinsa?.
"Ayimin afuwa.....wataqila takardun sun cakuda da wasu,zan nemeku idan komai ya daidaita" Abinda ta fadi kenan,bata kuma tsaya jira ba,bata tsaya jin tarin tambayoyinsu ba ta juya a gaggauce tana wucewa. Tana iya jin muryoyinsu suna jefa tarin tambayoyi mabanbanta,to amma ko tsaiwa qafafunta ba zasu iya ba ballantana ta fuskancesu.
"Tabbas..... Akwai wanda yayimin kutse dakin ma'ajiyar sirrina......tamim!!!!.....zaka mutu,tabbas zaka mutu idan baka bincikomin abinda ke faruwa ba,bayan komai a hannunka yake?!" Ta fada cikin qaraji kaman wata tababbiya. Cikin kanta da ranta takejin tabbas idan har an taba wannan dakin......to bata da wani sauran qwarin gwiwa. Ta jima tana saka ranar da zata shiga ta kwashe wasu kaya a ciki ta qonesu amma sai ta manta.....don ta tabbatar wanzuwarsu a tare da ita mugun hadari ne,duk da tasan tayi kafuwar da babu me banbareta cikin agadez. Ko bayaga haka,idan an matsanta banbareta,to bomabomai ne zasu dinga fashewa daya bayan daya da sunan sarkinsu dama diyar da yafi qauna duk duniya.
Hannunta har rawa yake sanda ta karbi takardar da tamim ke miqo mata sanda yake shigowa dakin da wani irin kwantaccen tsoro saman fuskarsa. Jikinsa dukka rawa yake,kaman yadda haqoransa ke haduwa kaf kaf kaf saboda tsananin tsoro kaika dauka wanka aka masa da ruwan qanqara.
*_Bismillahir Rahmanir rahim_*
*_Wamay yihinullahu fama lahu mimmukrim_*
*_Alaisallahu bi khafin abdah?_*
*_SHEIKH MUHAMMAD HAISAM MOTI ABA JIFAR IBRAHEEM the silent one_*
Duk da cewa sakin layin qarshe na takardar kawai ta fahimta.......wani irin girgiza zuciyarta tayi. Sunan IBRAHEEM kadai wata babbar barazana ce ga zaman lafiyarta......ballantana ta ganshi hade da sunan da dazu dazu ta gama bankwana dashi cike da farincikin ya tafi babbar dama ta samu a gareta.
*_Shin ubangiji bai isarwa bawansa ba?_*
*_Dukkan wanda Allah ya wulaqanta lallai bashi da wani wanda zai girmamashi_* wannan sune fassarar abinda ke rubuce a tarin tulin takardun nan" Tafisu ta fada tana sake nutsa hannunta cikin takardun da dukkaninsu rubutu daya ne a ciki,kuma sune suka maye gurbin duk wani file da a cikinsa a baya can muhimman takardunta ne a ciki.
"Innalillahi......na shiga uku!" Ta samu kanta da furtawa,a karon farko da rauninta ya bayyana muraran,ta sulale tana zama dabas a gurin a gaban tamim da tafisu tana manta meye ma matsayinta!!!.
โ โ Karo na farko a rayuwarta da takejin wani namiji haka dan da dab kusa da ita. Karon farko kenan da takejin wani irin kariya da tsaro suna bibiye da ita. Dukkan wani taku nata qwaya daya da zata sauke zaya sauke nashi a tare da ita,hakanan koda wani sashe na mayafi ko abayarta ya tattare tana iya jin yadda hannunsa ke kaiwa gurin ya gyara zamansa sosai a jikinta.
A duk sanda yayi hakan......wani abu daban yake saukarw a jikinta da ruhinta.....wani yanayi takeji na izzar da bata tana jin makamanciyarta ba.
Tun daga faarfajiyar airport na agadez bata sake saka falaaq da maleek a idanunta ba,bawai don ta damu ko akwai sabo da shaquwa me yawa ba.....aah,haka kawai lokaci lokaci sai zuciyarta ta gaya mata a yanzun bata da wani sama da falaaq din.
Blue eyes dinta ta daga a nutse ganin ba wani cikowa ko mutane.......karo na biyu wani mamakin ya kasheta bayan wanda ta shiga a airport na agadez ganin private jet din da daga ita saishi ya daukosu ya kuma ajiyesu a nan Niamey din.
"Private terminal?" Ta fadi a hankali idanunta akan private jet na biyu da suke tunkara wanda yasha banban da wanda ya kawo su Niamey din.
"Me yake faruwa?" Ta furta can qasan ranta.
"Alfarma ce dashi haka?" Ta sake tambayar kanta da kanta daidai sanda sauran ma'aikatan dake gurin suke gaidashi cikin tarba ta musamman da kuma girmamawa,saidai duk maganan da suke kaman a agadez da wani yare ne da bata jinsa bata kuma ganewa,amma yanayin girman da suke bashi sai abun yake sake jefata cikin duhu.
_yanzu kika fara shiga duhu akhnan?,ko baki fara shiga bama?_
*_yan uwana masoyana assalamu alaikum warahmatullah_*
*_gaisuwa da fatan alkhairi,biki gareni na sisters dina har biyu,ina neman uzuri da afuwa idan har kuka jini shuru laraba alhamis da juma'a,duk da zanyi dukkan qoqari tuquru naga ban tsallake muku kwanakin ba in sha Allah,saboda halin rayuwa da yanayin biki,amma koda page bibbiyu ko daya daya ne ya samu zan qoqarta kada na barku haka_
_na gode muku qwarai da gaske,in sha Allah huguma ba zata baku kunya ba_๐๐ฝ๐๐ฝ