
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 13
...how did his daughter's upbringing begin? Mumy said again, "Son of God, Abba, forgive me. I myself was surprised, but you gave her a chance to correct her mistake. You know the children now, they often make mistakes but they also need guidance." Abba was relieved, he was saddened by what had happened, but he also felt that Mumy's words had an effect on him. But his heart is happy. He thought, "Did I make a mistake in educating her? Why did she do this?" ** The next day, in the morning, my body is still aching, especially the headache that started in the morning. I know I have sinned, that's why I haven't slept since midnight. I went to home treatment, even though the drug that Fareed gave me in lemon juice did not release me, I was tired and sick. However, I mustered up the energy to tidy up, wash the toilets, and clean the toilet. Seeing that it was almost six o'clock in the morning, I went to Billy's room to ask her what I would cook for her. That's when I heard her laugh, she was smiling happily. Surprised, I stopped and listened to what she was saying. "Oga, what pill is this girl taking? You know she didn't even take it from her hand. As for me, I've never taken anything lik
SHAFI NA GOMA SHA UKU
Adaren nan Abba gaba ?aya bai kwanta ba. Bakaramun hankalinsa tashi yayi ba, domin tunanin abin da ya faru yana ta faman yi masa yawo a zuciya. Bai ta?a tsammanin za ta aikata irin wannan abu ba. A zahiri, bai iya ganewa ba ko da mafarki ne ko gaske. Ya da?e yana tunani kafin ya mi?e ya watsa ruwa, sannan ya koma kan dadduma ya ?ora sallah, yana neman nutsuwa da natsuwa a cikin zuciyarsa.
Mumy ce ta taso daga ?aki, tana lura da yanayin Abba. Ta san cewa lallai wannan lamari ya dame shi sosai. Ta zauna kusa da shi, cikin tausayi da natsuwa ta fara magana, "Dan Allah Abba, kayi ha?uri. Ai bata ta?a aikata haka ba, wannan ne na farko. Kasani, yaran yanzu, ba za ka iya musu ba. Kawaye ne ke jan su da wa?annan abubuwa. Ka yafe mata, dan Allah."
Abba bai ce komai ba, kawai sai ya cigaba da addu'o'insa cikin natsuwa. Bayan ya gama, ya kalli Mumy da kyau, yana jin nauyin maganar da take yi. Zuciyarsa na bugawa, yana ji kamar zuciyarsa ta tsinke saboda takaici da kuma tunanin yadda tarbiyyar 'yarsa ta fara ?aci.
Mumy ta sake cewa, "Dan Allah, Abba, kayi ha?uri. Ni kaina na yi mamaki, amma ka ba ta dama ta gyara kuskurenta. Ka san yaran yanzu, sukan yi kuskure amma kuma suna bu?atar shiriya."
Abba ya ?an numfasa, ya na jin ba?in cikin abinda ya faru, amma kuma yana jin maganar Mumy tana yi masa tasiri. Sai dai zuciyarsa tana ?unci. Yana tunani, "Ina nayi kuskure ne wajen tarbiyyarta? Me yasa ta aikata haka?"
** Washegarin ranar, da safe, jikina har yanzu yana ciwo, musamman ma ciwon kai da ya tashi tun da asuba. Na san na yi laifi, shi yasa tun ?arfe hu?u ban sake yin bacci ba. Na shiga gyaran gida duk da cewa kwayar da Fareed ya zubamun a lemo bata gama sakina ba, ga gajiya da ciwon jiki. Duk da haka, na tattara ?arfin guiwa na gyara ko'ina, na wanke bandakuna, sannan na ?ora abin kari. Ganin ?arfe shida na safe ya kusa, sai na nufi ?akin yaa Billy don tambayarta abin da zan dafa mata. A lokacin ne na ji dariyarta, tana kyalkyala cikin jin da?i. Cikin mamaki, na tsaya na saurari maganar da take yi. "Oga, wai wace kwaya ce yarinyar nan tasha? Ka san ko daga hannunta bata yi ba. Ni fa ban ta?a shan irinsu ba, yau na sha wata sabuwa. Gaba ?aya ta kasa ?aukata, baccin ma ban yi ba." Na ji zuciyata na tsinkewa. Na furta cikin tsoro, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un." Na dafa kirjina, ina tunani, "Kenan da gaske shaye-shaye take yi? Ko kuwa wani abu daban ne?" Amma ba wannan ne kawai ya fi tayar min da hankali ba, sai dai maganar da ta sake yi.
"Ai na gaya maka, wallahi sai na lalata rayuwar Ramlah. Soyayyar da mahaifina ya nuna kanta fiye da ni, sai ta zama masa ajalinsa. Ina so ka bani kwayar da zan dinga zuba mata cikin abin shanta. Lokaci ka?an, shaye-shaye zai kama jikinta. Duk gidan nan, ni tafi yarda da ni. Nifa na fi kowa nuna mata kulawa. Kai dai kawai ka kawo. Ko Mumy bata isa ta nuna mata irin kaunar da nake nuna mata ba." Gaba ?aya jikina ya mutu, hawaye na zuba a fuskata. Na koma kitchen cikin sauri, na fashe da kuka. "Wannan wace irin ?addara ce? Yaya billy ce ke shirya wannan mugun nufin akaina? Na yi zaton itace mafi ?auna a gare ni a gidan nan!" Cikin wannan halin ne, Mumy ta shigo kitchen ?in, ta ga ni ina goge hawaye. Ta ce cikin kulawa, "Yar albarka, har kin tashi? Na san ba halinki ba ne wannan. Kidaina damuwa da fa?an Abba, kinji? Ai inda kikaje ba wani abu ba ne. Haka yan gayu sukeyi. Kin san Abba bai waye ba. Ni da kin gaya min ai da sai na ce kije gidan Abbas ki kwana. Kema yakamata ki zama yar gayu ai." Na rasa abin cewa, zuciyata na ?ara tsananin ra?a?i. "Shin Mumy bata fahimci cewa da gaske Fatima tana nufin cutar da ni bane? Ko kuwa itama tana cikin wannan ha?in bakin?" A cikin wannan tunanin, na san cewa ba zan iya dogara da kowa ba yanzu. Dole ne in nemi mafita kaina, kafin lamarin ya wuce gona da iri. "Amma ta yaya zan yi? Kuma wa zan nema ya taimakeni?" Mumy ta gyara murya, tana dubana cikin yanayi na nuna kulawa. "Kinga kawarki Fatima, tana son ki zama yar gayu. Bakya ganin yayarki ai? Macce sai da gayu. Mazan ma sun fi son yaran da idonsu suka bu?e."
Sai na ji wani irin karsashi ya shige ni, zuciyata tana raya cewa gaskiya Mumy ta fa?a. Tunda a makaranta ma haka suke cemin, wai ni marar wayewa ce. Na ji kamar idan na bi shawarar Fatima, zan zama kamar sauran 'yan mata. A hankali na ji kwarin gwiwa ya fara shigata.
Mumy kuwa, tana hawa sama sai ta fa?awa Abba, "Abban Ramlah, ni dai ina da shawara. Yarinyar nan kadaina bata ku?in kashewa kwata-kwata. Ya zama na ?an?ane mata, ta ji da?in wahala, shi zai sa ta ?ara nutsuwa."
Abba ya yi shiru na ?an lokaci, sannan yace, "Ai tun da, daman ina tunanin haka."
Na je gaishe shi, bai amsa ba, duk da yadda na ri?a ba shi ha?uri. Na ji zuciyata ta tsinke, duk da haka sai da na fito muka tafi makaranta da Malam Idi.
A makaranta, na yi niyya ba zan kula Fatima ba kwata-kwata. Amma sai ga ta tazo tana bani ha?uri, abin mamaki kuwa sai na ji na yarda da ita. "Ai Mumy ta ce min Fatima masoyiyata ce, tana so in zama cikakkiyar yar gayu," na raya a zuciyata, duk da cewa na san halayyarta ba ta da kyau.
Yinin ranar, sai tiktok kawai take yi a wayarta. Lokacin da aka fita break, sai na fara jin cewa hakan ma yana da kyau, duk da farko ban kula ba. Sai da aka tashi sannan ta sake bani ha?uri, na kalleta cikin rashin gamsuwa nace "Kinsan masifar da kika janyo min gida kuwa?"
Ta fashe da dariya, tana cewa, "Au, har yanzu ba a daina miki fa?a ba? Lallai!" Na tsaya ina kallonta da mamaki, sai ta ce "Gobe idan na zo, zamuje gidan malami. A rufe bakin iyayenki baki, su daina ce miki komai akan duk abin da kike yi. Ki huta da wannan fa?an!"
Na ji kamar an tsikare ni, zuciyata ta tsinke da tsoro. Fatima ta shige mota ta bar makaranta, ni kuma na zauna a bakin hanya ina mamakin maganar da ta fa?a. "Gidan malami? Rufe bakin iyaye? Wannan wani irin shiri ne haka?"
*******
Kafin ya ce komai, Haneefa ta kai hannunta ta shafi sumar kansa da laushi. Wani irin ra?a?i da nishadi suka ha?u suka mamaye shi. Jikinsa ya yi sanyi gaba ?aya. Idanunsa suka fara lumshewa tamkar yana jin da?in abin da take yi. Ta sunkuya a kan kunnensa, tana saukar masa da numfashi mai dumi. "As ad... Na san ba ka saba da wannan ba."
Sai ya ji zuciyarsa na rauni, jikinsa na narkewa, tamkar wani abu yana tasiri cikin zuciyarsa. Haneefa ta ?ora kanta a ?irjinsa, tana wasa da wuyan rigarsa. "Kada ka kore ni, ranka ya da?e... Na jima ina mafarkin wannan daren." Maimakon ya yi magana, sai kawai ya lumshe ido, numfashinsa na fita a hankali.
Haneefa ta lura cewa tasirin maganin ya fara aiki. Ta yi murmushi mai cike da nasara, sannan ta ?aga fuskarsa a hankali. "Ranka ya da?e, ina son ka..." Ta furta a hankali, tana shafa gefen fuskarsa. As ad ya yi ?o?arin fa?ar wani abu, amma muryarsa ta yi rauni sosai. "Haneefa... ki... ki barni..." Sai ta ?aura yatsunta a le?ensa. "Shiii... Kada ka ce komai. Ni zan kula da kai."
Ta dinga murza hannunta akan ?irjinsa, tana shafawa cikin salo na bariki. Jikinsa ya fara rawar sanyi, idanunsa sun sauya daga tsayayyen mutum zuwa tamkar wani marar ikon tsayayya. Ta ?aura kansa a cinyarta, tana murza gashinsa, sannan ta rafka masa wata dariya mai kashe zuciya.
"Ka bar komai a hannuna, mijina." Kafin ya ce komai, sai ta yi wani irin motsin birgewa, ta ?ora hannunta a gadon bayan wuyansa, tana murzawa cikin sanyi. As ad ya runtse ido, yana jin tamkar wani zararre. Kowane motsinta yana narkar da jikinsa.
Kowane motsin Haneefa na narkar da shi. Yana jin tamkar an daure masa tunani, duk wata tsayayyar zuciya ta gushe. Yana jin tamkar bawan da aka rufe a keji. Ta yi murmushi mai cike da mugunta, sannan ta kai bakinta kusa da kunnensa. "Zan kasance da kai duk daren nan. Ko da ace ka kore ni, ba zan tafi ba."
Ta kai hannunta ta ?an murza gemunsa, sannan ta sunkuya tana ra?a a kunnensa. "Kai ne jarumi na... Yau zan nuna maka banbancin matan gida da 'yan bariki." Kafin ya ankara, sai ta dinga girgiza jikinta a hankali kamar mai ra?a?in zumudi, tana kwantar da kanta a ?irjinsa. Numfashinsa ya yi nauyi, yana jin tamkar zuciyarsa zata tarwatse.
As ad ya kasa magana, yana jin zuciyarsa na kuna da sha awa marar misaltuwa. Sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa na ?o?arin bijirewa, amma yana jin raunin da ya gagara tsayayya. A wannan lokacin, Haneefa ta rungume shi sosai, tana lalla?a shi kamar jariri.
Bayan ?an lokaci, ya yi ?o?arin janye jikinsa, amma ta sake manne masa. Sai kawai ya daina ?o?arin tsayayya, yana jin wani irin yanayi na murmur?iyar zuciya. "Ni naki ne... Haneefa..." Ya furta cikin rauni, tamkar wanda aka kwashewa tunani. Haneefa ta yi murmushi mai cike da farin ciki, ta dora kanta a ?irjinsa, tana jin cewa burinta na fara cika.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH