Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 21

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 21

.....let her go forever. Then she felt that her heart was completely broken, and she felt like she needed someone around her, someone who would cry a lot in front of him like a sultan. She doesn't cry in front of anyone......no one sees her tears if you take away the two people, the sultan and my mother, but now she only has the sultan who she will cry in front of and enjoy, where will she find a substitute?, she ended with her unanswered question. Slowly she felt the soft palm of his hand penetrating into hers......slowly, like a snake's movement, she felt his five fingers entering the center of hers.......slowly she felt his hands clasped together as he squeezed his insides so that they began to exchange the warmth of each other's hands. A kind of silence..... silence mixed with calmness is what exists between them, it is what dominates the border plane where they are. Even though the crying did not stop, but she felt a kind of relief that was slowly coming down in her heart. A kind of cold that made even the tears coming out of her eyes come out with a kind of cold. From time to time she felt how he pressed her hand in his, as if he wanted to talk, as if he was persuading her th

Standalone post1,665 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 21*

"YA DAURU.....NA DINDINDIN NE!" Daga can wani sashe na zuciyarsa ya bashi amsa. Bai sani ba,amma ya jima yana hasashe. Tabbas akwai qaddarorin da muke saqasu da farko,amma qarshensu saisu qwace daga sarrafawarmu su shiga saqa kansu da kansu.......ko wannan shiryayyar qaddarar zata qwace daga hannunsa ne?......ta fara saqa kanta da kanta?.

Tunaninsa ya yanke sanda ya soma jin wani abu......wani abu kaman sheshsheqar kuka can qasa,sheshsheqar da ake boyeta ba tare da buqatar kowa ya jita ba. Saidai shi din na dabanne,yana da wani irin kakkaifan ji,wanda zaiyi wahala kayi magana komai qanqantarta ba tare da yajika ba.

Sanda idanunta ke kallon yadda jirginsu yakeyin nisa da niger.......yakeyin nisa da qasar Niamey gaba daya,sai takejin kamar tanayin wani nisa ne na har abada. Kamar tana barin niger ne bari na har abada,kamar akwai nisa da sultane zaiyi mata nisa na har abada. Kamar zata barshi ne na har abada.....shima zai barta bari na har abada din. Sai taji gaba daya zuciyarta ta karye,sai taji kaman tana da buqatar wani a kusa da ita,wanin da zatayi kuka sosai a sake a gabansa kamar sultane. Ba gaban kowa take kuka ba......ba kowa yake ganin hawayenta ba idan ka debe mutum biyun,sultane da mammina,saidai a yanzun sultane kadai take dashi wanda zatayi kuka a gabansa ta more,a ina zata samu madadi?,ta qarashe da tambayarta mara amsa.

A hankali taji lallausan tafin hannun nan nasa yana kutsawa zuwa cikin nata......a hankali da wani irin yanayi ta tafiyar maciji taji yana kutsa yatsunsa biyar tsakiyar nasa yanzun.......a hankali kuma taji ya game hannuwansu guri daya yadan matse cikin nasa ta yadda suka fara musayar dumin hannuwan juna.

Wani irin shuru.....shuru me cakude da nutsuwa shine abinda ya wanxu a tsakaninsu,shine abinda ya mamaye jirgin iyakar inda suke.

Duk da kukan bai tsaya ba,amma wani irin sassauci takeji yana sauka a hankali cikin zuciyarta. Wani irin sanyi da ya sanya hatta da hawayen dake fita daga cikin idanunta suke fita da wani irin sanyi. Lokaci lokaci tana jin yadda yake dan matsa hannunta dake cikin nasa,kamar dai yanason yayi magana ne,kaman dai lallashinta yakeyi ta hanyar motsa yatsunsu dake guri daya da dan matsasu kadan.

Tsahon wasu mintuna,kafin a hankali wannan muryar tasa me laushi da zurfi ta motsa a hankali zuwa cikin kunnenta,cikin yarenta,cikin harshen faransanci da wannnan accent din nasa dake bugar da ita,yake sake saka mata jin tsananin dadin yaren French wanda a baya batasan yana dashi ba sai a bakinsa

"Kiyi kuka idan kinaso,ba rauni bane......amma bame cutarwa ba" Sai taji kalaman sun sauka a kunnuwanta da wani irin banbanci me yawan gaske. Maimakon kuma kukan yaci gaba,a hankali sai taji hawayen suna raguwa suna ja baya da kansu. Yaji komai,duk da baya ganin fuskarta amma yaji yadda ta soma daidaita kanta,yana jin nauyin wannan amanar dake saman kansa......yana kuma fatan ya sauketa har zuwa sanda Allah zaiyi ikonsa cikin lamarinsu gaba daya shi da ita.

“Wani lokaci… dole ne mutum ya bar wuri… domin ya gano inda ya kamata ya kasance.” yayi maganar da nazari masu yawa cikin magananunsa,wanda ya sani,a wannan lokaci ba lallai bane ta fahimci ma'anonin maganarsa ba.

Sosai maganan ya tsaya mata a rai,amma kuma ta gaza sarrafa maganar cikin ranta. Tana jin sanda ya zame tattausan tafin hannunsa daga cikin nata,sai taji yatsunta suna motsi a hankali.....suna motsawa kaman suna shirin riqe nasa yatsun da suke dab da ficewa daga cikin nata.

"Ungo" Ya fada a hankali yana ajiye mata tissue. A hankali ta juyo da fuskar ta don ganin me yake miqa matan,kai tsaye idanunta suka zarce kan fuskarsa suka fada cikin idanunsa.

Ita yake kalla da wadannan idanun da har abada suke tuna mata wadancan ranakun na farko. Wani lokaci idan ta motsa labbanta,sai taji tanason tambayarsa.

"Kaine wannan mutumin?,na wancan ranar daya fara sanyawa na zama mara nasara karo na farko a rayuwata?." Saidai kuma kwarjininsa da izzarta suna cakuduwa su tayar da alfaharinta na diya mace,kaman yanzu saita zare idanunta daga kansa sanda ta fahimci shima ya dauke kansa daga gareta.

"Assalamu alaikum sir....akwai abinda kake buqata?" Ta sake jin muryar wannan matashiyar crew din. Wani abu ta shaqa sosai cikin hancinta,ya kuma tsaye mata a qirjinta cak kaman tsaiwar mashi.

"Me kuma take nema?" Taji tambayar ta zarta cikin kanta. Kadan ta matse yatsunta tanason kauda hankalinta akan komai ma,don batasan abinda yake jan hankalinta ba ga duk motsi da maganan da yarinyar zatayi masa ba.

Ba tare daya amsa mata ba,ya juya kansa a hankali zuwa sashen da take.

"Kina buqatar wani abu?" Ya tambayeta da wani irin softness da yaren French din nan nasa da kullum xai magana dashi sai taji kamar nasa yaran daban yake da wanda ta saba ji. Kai kawai ta girgiza masa,cikin izzarnan tata da sanyin jiki,sannan a hankali ta motsa labbanta tana cewa

"Ba komai" Kaman bazai janye idanunsa daga kanta ba,kafin ya janye din,ba tare kuma daya sake duban crew din ba ya furta.

"Ruwa.......coffee,in akwai buqata sama da haka zaa sanar miki" Ya fada da salon iya taqaice magana irin nashi.

Kai ta gyada,sannan a ladabce ta juya tana barin gurin don cika umarninsa.

Komai daya shafi jirgin.....komai daya shafi tafiyar tasu tana nuna zallar alfarma ne da wata irin tarin izza da dukiya. Wani irin yanayi da tunda take hawa jirgi bata taba riskar yanayi irinsa ba. Shuru ya wadaci gurin.........sanda jirgin ke sake kutsawa cikin sararin subhana. Pilot da crew din da basu da yawa dukka suna bangarorinsu suna ayyukansu.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ta gaza controlling zuciyarta,ta gaza tsaida zuciyarta daga nanata tambayar SHI WAYE?......WAYESHI A AGADEZ......KO NIAMEY da yake da irin wannan alfarmar?.

Private jet.....private pilot.......private crew?. Komai private ne.....komai kuma me kima tsada da alfarma ne.

Tun bayan da ta kawo ruwan,ya tura mata gabanta......ya hada da tissue dukka ya ajiye mata,duk da cewar bata buqaci komai ba. Sai ya gyara kujerar da yake kai zuwa yanayin da zaifi masa dadin relaxing bayansa sosai.

Yayi relaxing din cikin wata nutsuwa yana miqe dogayen qafafunsa dake sanye cikin socks charcoal color da suka dace da shigar jikinsa.

A nutse ya bude briefcase din dake gefansa,ya zaro wani qaramin littafi da duka duka a qiyasinta shafukansa ba zasu haura hamsin ba. Daga kwancen ya sake ragewa gurin da yafi kama da parlor haske,ya koma yayi relaxing sosai yana bude littafin.

Shuru ya ziyarci gurin,wani irin shuru da bai bar mata komai ba sai qamshin turarensa da kuma satar kallonsa da bata shirya ba. Tun bai jima ba ta fahimci karatun yana mata dadi,tun basuyi nisa ba ta gane yadda karatu ke matuqar dauke masa hankali da sakashi a nishadi. Sannu a hankali saita samu kanta da satar kallonsa,satar kallon data zarce mata zuwa wani kalar satar kallo na minti daya zuwa rabin minti sannan ta zare idanunta da sauri a duk sanda taga yayi motsi. Yadda fararen manyan qwayar idanunsa suka rusuna kamar wanda bacci ke son qwacewa.......ta saukar da idanunta a hankali zuwa ga lips dinsa. Wani abu daya fusgi hankalinta.....wani abu data sani ya taba burgeta sau daya tak game da wani jarumi cikin fina finan soyayyan da takan kalla. Wasu irin lips ne masu wani irin shape me daukan hankali,lips din da zai wahala kaga sun bushe,suna da wani irin yanayi dake nuna sulbin da suke dashi koda daga nesa kake,nisan da zaka dauka ma mamallakinsu yana using lips gloss ne saboda qawatashi. Ta saukar da duban nata cikin dabara zuwa ga habarsa. Wani irin beard,kwantaccen saje da gemu daya zama cikakken ado wa fuskarsa. Wasu irin gashi marasa tauri sune kwance sama da qasan labban nasa,suka kuma zagayesu sannan suka hade da kuncinsa zuwa qasan habarsa. Wani irin baqin gashi me daukan idanu da kuma sulbi a idanu ma.....sulbin da haka kawai taji zuciyarta lokaci daya na fusgarta dason taji yanayinsu cikin hannunta. Ta sake maida idanunsa ga cikakkiyar girar dake barazanar hadewa da juna,sai taji wani abu ya zarce ta cikin maqogoranta,ya kuma harba saqon.

"Anya bai fini kyau ba?" Tambayar da ita kanta tasan ta sakata a shakka......shakkar da tabbaci yakeso ya rinjayeta. Ba bala'e'en kyau ya mallaka ba......amma Allah ya yiwa zubin halitta da tsarinsa baiwa da KWARJINI. Komai nasa idan ka kalla yana da wata irin cika da kamala da kwarjini.

Sanda ta dora idanunta kan hannunsa dake riqe da littafin sai taji bugun numfashinta ya sauya na wucin gadi,ta janye idanunta saboda zuciyarta dake gaya mata.

"Kallon bai yawa ba?.....idan yaji a jikinsa fa?" Amma haka kawai minti daya kacal sai taji tanaso ta kalla,tanason ta kalli dogayen yatsun nan da ayau suka ratsa tafukan hannayenta sama da kullum. Tanason taga yatsun da sune na farko da suka fara gauraya da nata yatsun da sunan d'a namiji ya taba hannuwan nata.

Saidai a wannan karon tana shirin janye idanun nata ya kamata da nasa idanun da wani irin sauri da bazata da bata taba kawowa ba. Wani irin kunya...kunya me nauyi da wani irin sanyi taji yana bin kowacce gaba ta jikinta. Zagayayyun fararen idanun da bata taba ganin wani d'a namiji da fararen idanuwa irin haka ba.

Kafeta yayi da wadannan mayatattun idanuwan nasa,idanuwan da suke da wani irin tasiri,ba iya kan mata kawai ba hatta da maza. Yana da wani irin shape ne idanunsa da wani irin tasiri da yawanci ma'abota yawan kallon alqur'ani da hadith kawai ke samunsa saboda kwarjini da albarkar da litattafan ke dasu.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽