
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 14
.....her soul?" I took a breath and smiled fakely. "Alhamdulillah." She adjusted her bed laughing. "Your bed is more comfortable than mine, that's why I slept here. Are you back from school?" I nodded, my heart full of wonder. "Yes, I'm back." She laughed. "I just made a milkshake, I put yours in the fridge." I frowned playfully. "Did you make a milkshake? How are you Billy, did you work today?" She looked at me with laughing eyes. "Yes! My body is hurting, but I woke up." I smiled weakly, but my heart was full of doubt. Why is Yaya Billy showing such care today? I know that in the past she didn't help much. I was in this thought, and then Mumy sent her to the door and came in quickly. She slapped Yaya Billy hard. "You too Billy! Now won't you help? Do you have Ramlah to sit and do nothing?" Yaya Billy got up from the bed in a hurry. "My body hurts, Mumy." I quickly stood up politely. "Mummy, I will help." She looked at me with a look full of hate. "And you came to sit down, I was born so that I would cook for you? Shameless! My chest is nothing but I feel like you are the same as everyone else?" I felt something cut in my heart. Before I did.....
SHAFI NA GOMA SHA HUDU
Na dawo daga makaranta cikin gajiya, na shiga gida a hankali, na ajiye jakata kusa da ?ofar palo. Cikin falon, na hango Mumy tare da kawayenta biyu, Anty Faiza da Anty Maryam, suna ta hira da dariya. Na tsaya a bakin ?ofa, zuciyata cike da gajiya.
Na sunkuyar da kai, na tsugunna cikin ladabi. "Ina yini Mumy, ina yini Anty Faiza, ina yini Anty Maryam."
Mumy ta daga kai tana kallona da wani kallo na rashin jin da?i. "Ke kuma da kika dawo, ba za ki cire takalminki ba? Sai ki shigo da datti?"
Na ?an ja numfashi, na sunkuyar da kai cikin jin nauyi. "Yi ha?uri, Mumy."
Anty Faiza ta saki murmushi tana cewa, "Ba komai, Ramlah. Yarinya ce ai." Mumy ta ja tsaki, ta ci gaba da hirarta. Na mi?e a hankali, na nufi dakina, zuciyata cike da damuwa. Me yasa Mumy ke yi min haka?
Ina shiga daki, sai na hango Yaya Billy kwance a kan gadona, tana latsa waya. Na tsaya daga bakin ?ofa ina kallonta cikin mamaki.
Ta ?ago kai, ta saki murmushi mai rauni. "Sannu da dawowa, Ramlah. Ya makaranta?"
Na dan ja numfashi, na yi murmushi na karya. "Alhamdulillah."
Ta gyara kwanciyarta tana dariya. "Gadonki ya fi nawa dadi, shi yasa na kwanta anan. Kin dawo daga makaranta kenan?"
Na gyada kai, zuciyata cike da al'ajabi. "Eh, na dawo."
Ta ?an yi dariya. "Dazu na yi milkshake, na ajiye miki naki a cikin fridge."
Na ?an tsuke fuska cikin wasa. "Ke kika yi milkshake? Yaya Billy, yau ke kika yi aiki kuwa?"
Ta kalle ni da idanuwa tana dariya. "Eh mana! Ai jiki na ciwo, amma na tashi nayi."
Na yi murmushi mai rauni, amma zuciyata tana cike da shakku. Me yasa Yaya Billy ke nuna kulawa haka yau? Na san dai a baya bata cika taimakawa ba.
Ina cikin wannan tunani, sai ga Mumy ta turo ?ofa ta shigo cikin hanzari. Ta daka Yaya Billy da harara. "Ke kuma Billy! Yanzu ba za ki taimaka ba? Ko sai ke da Ramlah ne ku zauna babu aikin yi?"
Yaya Billy ta tashi daga gadon cikin shagwaba. "Ai jiki na ciwo, Mumy."
Na yi saurin mi?ewa cikin ladabi. "Mumy, zan taimaka."
Ta kalle ni da wani irin kallo mai cike da tsana. "Ke kuma da kika zo kika zauna, haihuwata kika yi da zan dafa miki abinci? Mara kunya! Kirji ba komai amma jin ki kike daidai da kowa?"
Na ji wani abu ya tsinke a zuciyata. Kafin na yi magana, sai kawai na ji mari ya sauka a kumatuna. Na ja da baya cikin tsoro, na yi ?asa da kai, hawaye na neman kwacewa.
Mumy ta daka min tsawa. "Ni ce uwarki da za ki tsaya kina kallona haka? Ki shiga ki dafa mana tuwo! Asararriya mara tarbiyya!"
Na sunkuyar da kai cikin jin kunya da ra?a?i, na kasa cewa komai. Yaya Billy ta kalle ni tana murmusawa da tausayawa, amma na san a zuciyata dadi takeji.
Na yi ?o?arin mayar da hankali kan littafina, amma duk lokacin da na ta?a kumatuna, zan ji ciwon marin da ta yi min. Hawaye suka cika idanuwana, zuciyata tana ?o?arin fashewa. Me yasa Mumy za ta mare ni haka? Shin na yi mata wani babban laifi ne da ban sani ba?
Na kalli milkshake ?in da Yaya Billy ta kawo min, yana nan a gefen gado, amma zuciyata ta kasa kar?ar cewa Yaya Billy ta yi wannan wahala don ni. Ko dai akwai wani abu a ciki? Na ji tamkar dakina ya yi min zafi, don haka na fita farfajiyar gidan, na zauna a karkashin bishiya, ina duba littafana da wayata. Amma babu kati, babu kudi. Na zauna cikin damuwa, ina tunanin yadda zan yi.
Bayan na gama aikin kicin, na fito tsakar gida ina duba littafina, amma hankalina a tashe yake. Cikin wannan yanayi, sai na ji sallama daga bakin kofa.
"Assalamu alaikum."
Na dago kai cikin mamaki, sai naga Khalil tsaye yana murmushi. Ya na?e hannuwansa bisa kirjinsa, yana kallona da wata fuska mai kulawa.
"Wa'alaikumus salam," na amsa cikin sanyi.
Ya zauna kusa da ni. "Ramlah, lafiya kuwa? Kamar kina cikin damuwa."
Na kauda kaina gefe. "Babu komai."
Ya girgiza kai, yana dubana da kulawa. "Me ke damunki? Makaranta ce ta wahalar da ke?"
Na saki murmushi mai rauni. "Ba komai, kawai na gaji ne."
Khalil ya kai hannu ya kama nawa, yana kallona da idanu masu cike da tausayawa. "Ba zan gaji da faranta miki rai ba. Kin sani."
Na sunkuyar da kai, ina jin wani irin sanyi a zuciyata. Khalil mutum ne mai kirki, amma ban taba sanar da shi matsalata ba.
Muryar Yaya Billy ta katse hirarmu. "Auta, ga nakinki cuppino."
Na juya, sai naga ta aje kofin a gabana tana murmushi. "Nagode, Yaya Billy."
Khalil ya kalle ni. "Wannan fa?"
"Cuppino ne, Yaya Billy ta yi."
Ya mi?a hannu zai ?auka. "Ni zan sha."
Na yi saurin ri?e hannunsa. "A'a, Khalil. Bari na kawo maka wani."
Ya yi murmushi. "Kin san ina son komai daga hannunki."
Na kasa fa?a masa gaskiya. Na bar shi ya ?auka, zuciyata tana tsalle kamar zata fado daga kirjina.
Ina tsaka da zama a bakin kujera, ina jin yadda zuciyata ke bugawa da sauri. Tun da Khalil ya tafi, ban samu natsuwa ba. Me zai faru idan cuppino din da Yaya Billy ta yi yana da matsala? Me yasa ta dage na sha, duk da ta san ban saba da irin wannan abin sha ba?
Kawai sai na ji nayi ya billy tace. "Auta, kin sha kuwa?" Na yi saurin juyowa. "Eh, na sha Yaya Billy." Ta kalle ni tana murmushi, sannan tace, "Kin ga, bacci nake ji wallahi." Ta sake dariya sosai, kamar yadda ba ta saba yi ba. Na dan rike hannuna cikin damuwa. "Me ya sa kike dariya haka?" Ta harare ni tana dariyar nan da ke cike da gulma. "Wai ni yar kauye ce ko? Ba na saba da irin wannan ba." Na saki murmushi na karya, sannan na ce, "A'a, ba haka nake nufi ba." Ta gyada kai.
Ina zaune ina daddanna wayata cikin sanyin jiki, sai na jiyo muryar Abba daga waje. Ya amsa sallama cikin gajiya. Na yi saurin gyara zama, na sunkuyar da kaina.
Yaya Billy ta mike cikin sauri tana gaishe shi. "Abba sannu da dawowa." Abba ya amsa a hankali yana kallonta da kulawa. Amma ni kuwa ko motsi ban yi ba. Sai naji zuciyata ta kara tsananta bugawa.
Momy ta fito daga daki tana gyara mayafinta. "Abba, yau ka dawo da wuri." Abba ya gyada kai, ya zauna a kujerar roba mai lankwasa. "Eh, aikin ya kare da wuri." Na yi kasa da kai, ina kokarin guje wa idon Abba. Amma duk da haka, na san zai lura da ni. Momy ta ja kujera ta zauna kusa da shi, tana kallona daga sama har kasa. "Abba, kayi ha?uri, amma gaskiya ne sai ka raba Auta da Khalil. Kamar yadda kayi a baya. Ba mu so ya rika hure mata kunne."
Abba ya ?ago kai yana kallon momy da mamaki. "Me ya faru kuma?" Momy ta ja tsaki. "Ka san fa Khalil yana son Ramlah tun suna yara. Yanzu har ya fara zuwar mana gida, yana neman lalata tarbiyarta." Na dago da sauri, idona cike da kwalla. "Momy, wallahi ba haka bane..." "Yi shiru!" Abba ya katse ni da tsawa. "Kina musun abin da momynki ke fada? Na ce ki tsuke bakin ki!" Na yi saurin rufe bakina, hawaye na sauka bisa kuncina.
Abba ya kalle ni cikin fushi. "Na kara ganin ki da wannan yaron, wallahi sai na ci ubanki. Bazaki sakamun ciwo ba!" Na ji zuciyata na tsananta bugawa, hawaye na gangarowa kamar an bude famfo. Baki na na rawa, amma ba zan iya cewa komai ba. Momy tace . " Hakan Yayi dai dai Abba, kai hakuri. Auta zata gyara halinta." Abba ya girgiza kai. "Ai dama na ce, na kara ganinta da shi, saina karya lagonta. Ke Ramlah, tashi ki bani wuri!" Na mike cikin sauri, na rasa inda zan sa kaina. Yaya Billy ta saki wani murmushi da bai kai fuska ba, tana cewa, "Auta, kin ji ko?"
Na fita daga falon da sauri, ina jin yadda zuciyata ke wani irin zogi. Na samu waje kusa da kofar daki na zauna, na jingina da bango, na ci gaba da kuka.
Na dafe kaina ina kuka a hankali, domin kada su ji. Duk lokacin da Abba ya nuna fushi, zuciyata tana karyewa. Ba don komai ba, sai don na san cewa ba zan iya kare kaina ba. Me yasa ake kallon Khalil kamar wani mai lalata tarbiyar mutane? Khalil dai bai taba cewa mun komai ba sai na kirki. Shi ne kawai wanda yake kokarin faranta mun rai, amma ga shi yanzu, ana ganin laifi ne ma ya gaishe ni.
Na daga kaina, na kalli kofar falon. Sai na ji muryar Abba yana cewa, "Wallahi Yalwa, idan har kika bari wannan yaron ya ci gaba da zuwar mun gida, saina dauki mataki. Ni ba zan dauki wannan rainin hankali ba." Ashe abba yakira Maman khalil ce yana mata maganganun nan.Na ji momy tana cewa, "Yanzu haka, sai dai mu kara tsaurara mata, ko da yana nufin raba su gaba daya." Yaya Billy ta kara cewa, "Ai kuwa hakan yafi." Na tsinci kaina cikin kuka mai karfi, ban iya daurewa ba. Ji nake tamkar ana tsaga zuciyata da wuka. Muryar Yaya Billy tana dariya cikin radadi ya kara rikita ni.
Sai kawai na mike cikin rawar jiki, na koma cikin dakina, na fada bisa gadona ina ta kuka. Na rufe kaina da filo, ina jin yadda kalaman Abba da momy ke ci gaba da dokar zuciyata. Me yasa ake mun haka? Me yasa ba wanda yake fahimta ta yanzu kullum ci?in laifi nake?
Bayan wani lokaci, na tashi daga gado. Na ji yunwa tana damuna, amma bana jin wani abu zai shiga cikina. Duk lokacin da aka yi mun fada haka, na kan rasa sha awar cin abinci. Na tsuguna a bakin gado, na jingina da bango ina ta tunani.
Na tuna lokacin da na kasance karama, Abba yana ?aga ni sama yana murmushi. Momy kuwa tana bani alewa tana cewa, "Autar momy ce." Amma yanzu duk abin ya canza. Na rasa inda na yi kuskure.
******
Washegari da safe, na tashi da kyar. Jikina duk ciwo yake kamar an dakeni. Na zauna bakin gado, idanuwana na kallon rufin daki. Tunani ya cika kaina: Idan ban samu kudin makaranta ba, ya zan yi? Abba dai ya riga ya ce ya daina bani kudi.
Na tashi a hankali, na yi aikace-aikacen gida cikin sanyin jiki. Bayan na gama, na fito falo don gaida Abba. Na tsugunna a gabansa cikin ladabi.
"Abba, ina kwana."
Ya ?an dube ni sama da ?asa, sannan ya gyara zamansa a kujera. "Lafiya kalau."
Na yi shiru, zuciyata na bugawa kamar zata fado. Da na ga zai tashi, sai na ce cikin rawar murya: "Abba... kudin makaranta."
Ya tsaya cak, ya juya yana kallona da fuska mai nuna ba?in ciki. "Ke kike neman kudin mun? To biyar dita! Na daina baki kudi, wallahi. Ki nema daga can."
Na ji wani sanyi ya ratsa zuciyata. Na daure na ce, "Abba, kayi ha?uri. Ba zan kuma tambaya ba."
Ya yi tsaki, ya kama hanyar fita daga gidan. Na tsaya a wurin kamar an dasa ni, hawaye suna cika idanuwana. Me yasa rayuwa take min haka?
Na koma dakina cikin sanyin jiki, na zauna bakin gado, na dafe kaina. Idan Abba ya daina bani kudi, ya zan yi? Na ?auki wayata, amma babu ko sisi a ciki. Na ?auki system dina da wayata, na sa su cikin jaka, zuciyata kamar zata fadi. Na fito daga gida da kyar, ina tafiya kamar wacce bata san inda take nufa ba.
A hanya, na ji tamkar zan zube saboda babu abin da na ci tun jiya. Na daure na taka da kyar har na isa makaranta.
******
Ina shiga aji, na hango Fatima tana tsaye kusa da kujerarta, tana duba wayarta. Da ta ganni, sai ta taho da gudu tana dariya. "Ramlah! Yau kam kin sha kyau!"
Na saki murmushi marar ?arfi. "Fatima, barka da safiya."
Ta kalle ni da kulawa. "Lafiyarki kuwa? Kamar wacce aka daka."
Na yi murmushi na ?arya. "Babu komai, kawai na gaji ne."
Ta yi dariya tana gyara ?an kwalliyar bakinta. "To yayil? Kinga ni fa nayi sabon saurayi a TikTok!"
Na zaro ido cikin mamaki. "Sabon saurayi kuma? A TikTok?"
Ta daga kai cikin jin dadi. "Eh mana! Wallahi yana l sau?in rayuwa. "Kamar zan shiga TikTok nima. Ko zan samu irin kyaututtukan nan."
Fatima ta bushe da dariya. "Ai sai ki fara wallahi. Mu dai muke jin dadi."
Na dubeta cikin mamaki. "Fatima, wannan saurayin fa? Ya kika yi har ya fara sonki?"
Ta ?an murmusa. "Ba sai na yi komai ba. Kawai rawar TikTok ce, da ?an jan baki kadan, sai ki ga mabiya suna tururuwa."
Na girgiza kai. "To ai banda kati."
Ta fiddo kati daga jakarta, ta mi?a min. "Ga wannan, 5K ne. Ki saka data, sai ki bude account dinki. Wallahi kina da kyau sosai, zakiga mabiya suna tururuwa."
Na karbi katin cikin jin kunya. "Nagode, Fatima."
Ta ?ora hannu a kafadata tana murmushi. "Ba komai, Ramlah. Wallahi idan kika yi trending, zaki ga yadda rayuwa zata sauya.
Na kunna system dina, na duba yadda ake bude TikTok account. Fatima tana dan nuna min yadda ake yin rawar da take yi, tana ?an motsa jikinta cikin salon jan hankali. Na rike haba ina dariya. "Yanzu haka kawai ake samun mabiya har 300K?"
Ta gyada kai tana dariya. "Eh mana! Ki dinga bazawa 'capacity,' kiyi trending."
Na yi shiru ina tunani. Idan har TikTok zai sa in samu mabiya, kuma daga nan na samu kudi, to me zai hana na gwada? Amma zuciyata tana jin tsoro. Ko ba dai wannan ba ne mafita?
Fatima ta kamo hannuna tana cewa, "Ramlah, ki daina jin tsoro. Ba zaki yi komai ba face dariya da ?an jan baki. Ki ga yadda mutane za su fara yabonki."
Na sauke ajiyar zuciya. "To zan yi kokari."
Ta saki murmushi. "Ki gwada kawai. Idan kika yi trending, zaki gane."
Na rufe system dina, zuciyata cike da ru?ani. Wannan shawarar TikTok ta fara shiga raina, amma har yanzu zuciyata tana tsoron abin da zai biyo baya.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH