Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 22

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 22

.....what should she do.....she didn't answer him, because she herself was wondering about Khadeeja Muhammad Hammud?,......she stole the look of a man?,why?.....why?. Wanting to protect her dignity and feeling proud, she took her gaze from the data room and returned to the window without saying anything, watching them break through the clouds and go away again in the sky. He just felt that he didn't want to talk and stopped like that, he moved a little and adjusted his sitting position by putting one leg on top of the other, a sitting position that was good for him, and he was showing off another layer of anger that he himself did not have. "What are you watching?" He asked her again how it was just making him happy, but even if you look at the surface of his face, you will not understand that. Her heart pounded again, she frowned and shook her head. "It doesn't matter" She said in a confused state, her soul full of suspicion. He let out a hidden smile. She is not the first woman to have something like this happen between them, but her situation is filled with a kind of compassion and pride like a daughter. He likes this behavior....don't be proud of Izza, for the first time seeing

Standalone post1,696 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 22*

"Kici gaba" Ya furta a nutse yana motsa wadannan kyawawan labban nasa bayan data dauke dubanta kwata kwata daga sashen. Ita sam ba zata bari ba......ba zata aminta ya fahimci koda sau daya ta saci kallonsa ba. Maganar saita tsananta bugawar da zuciyarta takeyi bayan wadda ta tsinci kanta a ciki a dazu,sanda yayi mata kamun ba zata.

Tsuke fuska tayi kadan,sosai takejin ba zata aminta kai tsaye ba.

"Me?" Ta furta cikin qarfin hali da dakiya bayan ta waiwayo tana dubansa,saidai duban bai kasance nakai tsaye ba,don ta sani.....a yanayin ba zata iya kallon qwayar idanunsa ba.

"Kallon" Shima ya bata amsa a yanayi nakai tsaye yana kuma sake kafeta da idanun nan nasa. Yadda ta soma amsa masan da wannan izzar.....da wannan k'i fadin.....da wannan jin isar sai yaja ra'ayinsa.

Yadda zuciyarta ta sake bugawa tare da bata tabbacin ya ganta.....tabbas ya gagganta tana kallonsa. Tun yaushe?,tun kallon farko?,ko ana qarshe ne?. Rasa me zatace tayi.....rasa amsar bashi tayi,saboda ita din kanta tana mamakin ita khadeeja muhammad hammud?,......itace da satar kallon wani d'a namiji?,why?.....me yasa?. Cikin son kariyar mutuncinta da jin izza ta dauke kallonta daga sashen data ajiye kanta ta maida ga window ba tare da tace komai ba,tana kallon yadda suke keta gajimare da girgije suna sake nisa cikin sararin samaniya.

Haka kawai yaji bayason maganan ya tsaya iya haka,ya motsa kadan ya gyara zamansa yana aza qafarsa daya saman daya,wani yanayin zama dake masa kyau,yana kuma sake fidda wata shimfidaddiyar izza dake tattare dashi wanda shi kansa baisan yana da ita ba.

"Me kike kalla?" Ya sake tambayarta yanayin haka kawai yana sanyashi nishadi,saidai ko ga saman fuskarsa ba zaka fahimci hakan ba.

Sake tsananta bugu zuciyarta tayi,ta sake tsuke fuska tana girgiza kai.

"Ba komai" Ta fada cikin yanayi na basarwa,can qasan ranta cike da tuhuma. Boyayyen murmushi ya saki. Ba itace mace ta farko da irin haka ta faru tsakaninsu ba,saidai nata yanayin cike yake da wani irin izza jin kai da kiyaye pride irin na diya mace. Yanason wannan dabi'ar.......kare alfahari da izza ba,karon farko daya fara ganinta tattare da wata diya mace a kansa.

"Kici gaba......amma kuma....." Sai yadan dakata. Dukka kunnuwanta suna gurin,dukka kunnuwanta suna tare da fitar lafazin daga bakinsa. Tsaiwar tasa sai tasa mata wani irin qaguauta taji abinda zaya qarasa fada,amma kuma sai ya yanke maganan daga nan.

"Idan kika kalleni na dan lokaci......" Ya sake dakatawa kaman bayason ya qarasa maganan.

"Bazan qyaleki ki daina ba" Da sauri ta juyo.....wani irin saurin da bata shirya ba. Hakan yakeso dama.......sosai ya riqe qwayar idanunta cikin nasa,akwai abinda yakeso ya gani,kuma ya samu ya gani din,kafin a hankali ya zame idanun nasa.

Numfashi take saukewa a hankali bayan ta maida idanunta ga window,tana jin wata gajiya da tsoro suna shigarta a hankali. Qirjinta yana dagawa,haka numfashinta yana fita da wani irin yanayi kamar wadda tayi gudu.

"Waye shi?,wanna irin mutum ne shi?" Tambayoyi biyun da takejin qaguwar samu amsa sosai a kansu,saidai ta sani a nan kusa bata da wannan amsar......bata dame sanar da ita.

Ya kama ta tana kallonsa… amma maimakon ya dakatar da ita,ya sanya ta son sake kallonsa ne kawai......amma tana tsoron maganansa na qarshe BAZAN QYALEKI KI DAINA BA.....

Cikin qasa da awa daya wani mutum daban take gani ba sheikh haisam ba......ba sheikh muhammad haisam da yake zaune a masarautarsu qarqashin alfarmar mahaifinta ba. Sanda ta farka daga baccin daya dauketa bayan shurun daya ratsa tsakaninsu,shurun da yafi mata sauqin wanzuwa tsakaninsu akan ya sake kamata tana kallonsa......ta farka ta samu kanta lullube da wani tattausan baro,kanta kuma jingine da madaidaicin pillow me taushi,kaman yadda aka sauya fasalin kujerar nata zuwa yanayin da zaiyi supporting kwanciyartata.

Koda ta bude idanun nata a gabanta ta ganshi,ta waiwaya tana duban window din wanda ya gaya mata a tsaye jirgin yake. Koda ta duba lokaci sai taga sun qara kusan mintuna goma sha biyar akan ainihin lokacin da akace zasu sauka.

Ya sauka jirgin tuntuni,ta sani,inde ba babbar lalura ko wata damuwa ba,jirgi baya sab'a lokacin tashinsa ko saukarsa........zaman da sukayi kenan kawai ana jira ta tashi a barcinta ne ko kuma yaya?.

Ta sauke idanunta a hankali a gabanta sanda ya tsugunna da nutsuwa yana daidaita mata takalmanta a gabanta. Wani irin nauyi taji.....nauyi taji sosai ya aza mata. Anya batayi kuskuren fahimtarsa ba?, ba kowanne d'a namiji bane zai yarda yayi lowering kansa.......ya tsugunna a gabanki ya daidaita takalmanki zuwa saitin qafarki don kawai kisa ba. To me tayi masa data cancanci wannan girmamawar?.

"Koyi yake.....koyi yake da fiyayyen halitta" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa sanda yake tuna mata da wani sashe na littafin nan data karanta. Yadda yake hidimawa iyalinsa......yadda yake iya durqusawa matarsa ta takashi ta hau abun hawa S A W.

Idanunta ta lumshe tana jan siririn numfashi tana saukewa. A karon farko ta bishi da kallo,kallon dake narke da wani kalan emotion daga zuciyarta.......kallo me nauyi dake dauke da sinadaran BURGEWA......karon farko daya juya yana takawa tabi faffadan bayansa da kallo tana jin har qasan zuciyarta wata qwayar halitta me suna BURGEWA tana sauka tsakiyar naman zuciyarta.

Welcome to jidda......ta gani a rubuce b'aro b'aro,sanda suke takawa ita dashi kafada da kafada kamar wanda aka bashi gadinta. Ta sauke numfashi me sanyi a karo na babu adadi. Ta dauka a Riyadh zasu sauka......su sake bin mota su shigo makka,saiga wasu irin shimfida shimfidan motoci qirar Rolls Royce Cullinan guda biyu,da tarin Mercedes Benz S-class da suka kusa guda biyar. Jerin motocin alfarma guda shida da suke tsaye cikin tsari.......baya ga mutanen da take hange. Sanye da baqaqen suits kamar yadda aka taresu a airport na Niamey.....sai larabawan da take hanga sanye da farin thobe daya dace da shigar jikinsu sosai tare da bayyana asalin gadon shigar da sukayi.

Koda ba'a gaya mata ba ta gani.......tsaiwar jiransa sukeyi. Duk wanda ke tsaye a gurin dama motocin dake gurin suna jiran isowarsa ne.

Kaman dazun.....kamar a Niamey,yayi taku biyu yasha gabanta,ya kuma rufeta da faffadan qirjinsa ta yadda bame iya ganinta,ya sanya hannuwansa ya gyara yafen mayafinta,ya kuma gyara mata abayar jikinta sosai. Da wani irin sanyi a muryarsa......yana jin kamar yana hadiye wani abu da qyar ya furta.

"Boundaries please" Kaman dai dazun,amma a yanzun tana jin wani abu deep cikin muryar tasa. Bata sani ba.....batasan dalilin duka wannan ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali ya sake ratsa yatsunsa da nata......a hankali ya sake game tafukan hannunsu da wannan yanayin da yake sakawa tsigar jikinta tayi wani irin zubawa har taji kaman karsashinta yana raguwa. Takunsu kusan daidai yake tafiya,suna sake kusantar mutanen da dukkaninsu ke murmushiwa haisam din.

"Assalamu alaikum warahmatullah......welcome your royal highness" Balarabe na farko ya fara fada fuskarsa dauke da wani irin murmushi da zai nuna zallar sabo dake tsakaninsa da haisam din.

Wannan miskilin murmushin......wannan miskilin yanayin dashi ya amsa masa yana bashi hannu shima.

"Royal highness?" Ta maimaita Kalmar cikin kanta tana satar kallon fuskar haisam,wanda yadan taka gaba kadan da ita yana gaisawa da sauran mutanen dake tsaye,fuskar da bata samu cikakkiyar damar kallonta ba sai kwantaccen gashin gefan fuskarsa dake glowing a hasken fitilun da suka cika king abdul'aziz international airport din tamkar allurarka ta fadi ka dauka.

A hankali takejin wannan nutsatsiyar muryar tasa da tasha banban data dukka mazan dake gurin tana ratsa kunnuwanta. Idanunta suna kafe a qasa,tana jin gaisuwarsu tana kuma amsawa a hankali saidai bata daga kai ta kalli koda mutum daya a cikinsu ba,muryarsa da yadda yake magana da yaren da ta rasa gane wanne yare ne kawai ke mata tasiri cikin kunnuwa. Yaren da taji yana mata wani dadi,yana mata kuma kamanceceniya da yaren fullatanci,saidai yafi fulatancin tsari da dadi a kunnuwanta.

Cikin girmamawa daya daga cikin mutanen dake sanye da suit dinnan ya bude masa murfin rolls Royce din yaja da baya da girmamawa. Saidai kuma ya waiwayo gefansa,inda take tsage zuciyarta da kwanyarta suna zurfi da nisa a tunani.

"Bismillah" Yace da ita yana sake bude mata murfin sosai da wani yanayi da taji ya saukar mata da wani izza da girma.

Kowa ya dakata.....komai ya tsaya saboda jiran shigarta mota kawai?,.....kamar a masarautarta ta agadez inda akasan tarin girma da kimarta?.

A hankali ta taka da yanayin takunnan nata dake cakude da qasaita,ta taka motar tana shiga a nutse,ya tsugunna a hankali yana gyara mata abayarta data fito waje,muryarsa da taushi yace.

"Kiyi addu'a......koda bismillah ce" Sannan ya maida murfin ya rufe mata. Ta cikin glass na window din ta bishi da kallo,sanda yake zagayawa zuwa daya side din,da dan murmushi kadan saman fuskarsa yana magana da balaraben.

Ta cikin motar taci gaba da monitoring komai.....motsinsa da yadda yaci gaba da magana dasu. Yadda suke magana dashi cikin girmamawa da qanqan da kai......yadda yake magana dasu da wani yanayi......yanayin da yafi mata kama da yanayin mutumin da ya saba da iko tun daga haihuwarsa.

"Ya salam......wayeshi?" Ta fadi wannan karon a sarari tana jin shakka da kokwanto suna cikata a kanshi.

"Ina buqatar na sani......dole,ba malami bane kawai.....wannan fuskar da muke gani a agadez ba ita bace ta gaske.....wannan mutumin......bashi bane na gaske" Ta fadiwa kanta tana jin qwarin gwiwa. Tana jin zuciyarta na tunzurata......tana jin ya zama dole tayi bincike a kansa.

Sanda take rubuta gajeran saqon tana aikewa,ta dauka zataji tsoro......ta dauka zataji tsoro game dashi ya kamata......amma maimakon wannan wani aminci da nutsuwa takeji. Ta tabbatar sultane bazai aminta har haka da mutumin da ba gaskiya a tare dashi ba,amma duk da haka......tanaso ta sani......tana buqatar sanin koshi waye.......koda ba dogon zama zasuyi ba......amma tana buqatar ta sani.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽