
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 16
.....Aminatu came in in her expensive sky blue dress, her head bowed. "Mamah, are you okay? You seem to be worried," Aminatu asked, her eyes full of worry. Mamah looked tired and gasped for breath. "I kept calling him, but he didn't answer. I sent him a message and he still didn't answer. Aminatu, you know what I'm running for, right? This is his new wife... she is a member of the Fulany family, Maryam. Since he married her, all care is gone. Aminatu caressed Mamah's hand. "Mamah, calm down. Do you know that our Dad is not like that. Maybe he is in a meeting." Mamah shook her head in frustration, fixing the scarf that had fallen off. "Aminatu, do you know how I feel? Since he married this new woman, I lost my happiness. The man who calls me three times a day, now he doesn't even answer my messages." Aminatu looked at her with sympathy. "Ma'am, be patient and apologize. Maybe they need time. And do you know who married the daughter of the Fulany family, Maryam, an attractive and civilized woman." Mamah frowned, her eyes showing pain. "Aminatu, you don't know how much I love your father. You don't know how my heart breaks. I lost how.....
SHAFI NA GOMA SHA SHIDA
Yammacin Dubai yana kyalli da hasken fitilu masu launin zinariya da fari, ana hango tekun Gulf daga tagogin gida mai hawa biyu na Amina. Gidan yana cikin unguwar Palm Jumeirah, wani wuri na alatu da tsari, inda manyan gidaje ke bayyanar da ?ayatarwa.
Falon gidan yana da salo na zamani kujeru masu launin toka da fata daga Roche Bobois, shimfi?a bisa darduma mai launin beige, da kuma chandelier mai kyalli a tsakiyar falon. A gefen bango, akwai wani babba TV mai fuskar madubi daga Samsung, yana kunna wani shirin na Dubai One
Amina tana zaune a babban falon, ta ajiye wayarta a kan teburin gilashi mai ?auke da tsadaddun furanni na tulip. Yaron nata, Imran, yana tsere- tsere a kan darduma.
Mamah ta jingina a kan kujerar fata mai taushi, ta rungume wayarta cikin damuwa. Har yanzu kiransa bai shiga ba. Ta danna lambarsa sau uku, amma ko ?aya bai ?aga ba. Ta cije le??enta cikin takaici, zuciyarta na bugawa da ?arfi.
Da ?yar ta ji ?aran takalmin Aminatu daga ?ofar falon. Aminatu ta shigo cikin tsadaddiyar rigarta mai launin sky blue, kanta a ?an sunkuye.
"Mamah, lafiya kuwa? Kamar kina cikin damuwa," Aminatu ta tambaya, idanuwanta cike da damuwa.
Mamah ta ?aga kai cikin gajiya, ta ?an furzar da numfashi. "Sai kiransa nake yi, baya ?auka. Na tura masa sa?o har yanzu bai amsa ba. Aminatu, kinga abinda nake gudu ko? Wannan sabuwar matar tasa... 'yar gidan Fulany Maryam ce. Tun da ya aure ta, duk wata kulawa ta ?are.
Aminatu ta dafa hannun Mamah cikin kulawa. "Mamah, ki kwantar da hankalinki. Kinsan fa Dadynmu ba haka yake ba. Wata kila yana cikin taro ne."
Mamah ta girgiza kai cikin takaici, tana gyara gyalen da ya ?an subuce. "Aminatu, kin san yadda nake ji kuwa? Tun da ya aure wannan sabuwar matar, na rasa farin cikina. Mutumin da a rana sau uku yake kiran ni, yanzu ko amsa sa?o na ma baya yi."
Aminatu ta kalle ta da tausayawa. "Mamah, ki daure ki yi ha?uri. Wata kila suna bu?atar lokaci ne. Kuma ki san fa wacece ya aura 'yar gidan Fulany Maryam ce, mace mai jan hankali da wayewa."
Mamah ta tsuke fuska, idanunta suna nuna zafin zuciya. "Aminatu, ba ki san irin soyayyar da nake yi wa mahaifinku ba. Ba ki san yadda zuciyata ke karyewa ba. Na rasa yadda zan bayyana miki. Na ba shi komai soyayya, kulawa.
Aminatu ta saki numfashi, tana ?o?arin kwantar da hankalin mahaifiyarta. "Mamah, ki yi ha?uri. Ki daina tunanin komawa Nigeria, ki tsaya anan ki basu lokaci."
Mamah ta dafe ?irjinta, tana jin yadda zuciyarta ke ra?a?i. "Aminatu, wallahi wannan zafin ya yi yawa. Ni fa matar farko ce! Na san komai game da shi. Na san yadda yake so in kwantar masa da hankali. Amma yanzu, kamar na zama tamkar kango ne babu kowa, babu kulawa."
Aminatu ta sake zama kusa da ita, tana ri?e hannunta. "Ki yi ha?uri, Mamah. Ki tuna cewa soyayya tana da wuya wani lokaci. Amma ina jin cewa Dadynmu zai dawo da kulawarsa da zarar abubuwa sun lafa."
Mamah ta kalli hasken birnin Dubai daga saman bene, tana jin sanyi na ratsa jikinta. Ta duba wayarta, har yanzu babu wani kira ko sa?o daga shi. Ta rufe idanuwanta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Wata mace za ta maye gurbina a zuciyarsa?
Ta tashi tsaye cikin zafi, tana kallon Aminatu da idanu masu nuna kishi. "Aminatu, wallahi ina jin zan koma Nigeria. Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba. Aminatu ta girgiza kai cikin ?o?arin lallashi.
Mamah ta koma ta zauna, tana lumshe idanuwa cikin gajiya. A zuciyarta, tana jin kishin wannan sabuwar matar yana ci gaba da yi mata zafi. Ya Allah, ka dawo min da mijina. Aminatu ta ?an ja numfashi, tana kallon mahaifiyarta da tausayawa. Ko da yake kishi yana ci, amma dole ne Mamah ta yi ha?uri. Auren gidan sarauta ba zai ta?a kasancewa cikin sau?i ba.
****
Babban falon gidan yana da fa?i da tsari mai ?aukar hankali. An kawata shi da fitilun zinariya masu laushi, yayin da bango mai launin ruwan toka ya ?ara wa falon ?aukaka. A gefen falon, akwai wata ?atuwar kujera mai matasai na fata, inda mahaifiyar Khalil ke zaune cikin nutsuwa.
A ?asa, Khalil ya tsugunna cikin ladabi, idanuwansa cike da hawaye da damuwa. Zuciyarsa na bugawa da ?arfi kamar zai rasa numfashi.
Mahaifiyarsa ta kalle shi, tana gyara gyalen kanta. "Khalil, ba wai bana sonka da Ramlah ba ne. Na san kana ?aunarta sosai. Amma mahaifinta... wallahi, baya sonka kwata-kwata."
Khalil ya dafe kansa da hannuwa biyu, hawaye suna kwarara daga idanunsa. "Mamanmu, dan Allah, ki taimake ni. Wallahi ina sonta sosai. Kinsan fa tun tana ?arama nake sonta. Ko da bata gama makaranta ba, ki neman mun aurenta haka."
Maman Khalil ta sauke numfashi mai nauyi, tana kallon ?anta cikin tausayawa. Ta ?an sunkuyar da kai, tana magana cikin rauni. "Khalil, na fahimci yadda kake ji. Amma mahaifinta ya fa?a a fili cewa ko maza sun ?are, ba zai ba ka Ramlah ba. Ina tsoron abinda zai iya faruwa idan aka ci gaba da matsawa."
Khalil ya goge hawayensa da bayan hannunsa, yana ?o?arin saita numfashinsa. "Mamanmu, wallahi zuciyata ba za ta iya jurewa ba. Bansan me yasa mahaifinta baya sona ba. Ina ji a zuciyata cewa ita ce cikar burina."
Maman ta dafe zuciyarta, tana jin yadda kukan ?an nata ke tsaga mata zuciya. "Khalil, dan Allah, ka daina jawo min magana. Ka gane ni ba mai ?arfi ba ce, kuma kasan halin Zainab matar uban Ramlah.
Khalil ya fashe da kuka mai sauti, yana kallon mahaifiyarsa da idanu masu bayyana ra?a?i. "Mom, wallahi bazan iya ba! Nayi ?o?arin mantawa da ita, amma zuciyata ta?i yarda. Ko da mahaifinta baya sona, ki taimaka ki nema min ita."
Ta kai hannu ta share hawayen dake kwance a fuskar Khalil. "Dan Allah, ka gane halin da ake ciki. Kafin a kai ga matsala, gara ka hakura da wannan soyayya."
Khalil ya girgiza kai cikin murya mai cike da ?arfi. "Mom, wallahi bazan iya daina sonta ba. Soyayyarta ta ratsa jikina. Na san cewa tana sona, kuma ban ta?a ganin wata mace da zata iya maye gurbinta ba."
Bayan Mamah ta tashi ta bar falon cikin ra?a?i, Khalil ya zauna a ?asa, yana jin kamar zuciyarsa zata fashe. Me yasa soyayya zata zama haka? Me yasa zan rasa farin cikina saboda banbanci na iyali?
Ya share hawayen da suka yi masa kwance, sannan ya mike tsaye cikin dauriya. "Dole ne in gwada nema daga Babah."
Ya nufi ?angaren mahaifinsa cikin sauri, zuciyarsa na bugawa da fatan samun mafita. Da ya isa, sai ya samu mahaifinsa yana waya. Ya tsaya daga gefe, yana jiran ya gama.
Bayan an gama wayar, Khalil ya tsugunna cikin ladabi. "Baba, dan Allah, ina neman alfarma."
Babah ya kalle shi da nutsuwa. "Me kake nema, Khalil?"
Cikin rawar murya, Khalil ya ce, "Baba, dan Allah, ina neman aurar Ramlah."
Mahaifinsa ya sauke numfashi mai nauyi, yana kallon Khalil da idanu masu nuna damuwa. "Khalil, ka yi ha?uri. Mahaifinta ya riga ya fa?a cewa ko maza sun ?are, ba zai baka ita ba."
Khalil ya lumshe idanu, hawaye suka taru a gefen idanunsa. "Amma Baba, me yasa? Me yasa baya sona?"
Babah ya gyara zamansa. "Khalil, matsalar ba kai ba ce. Matsalar ita ce Zainab marikiyar Ramlah. Kin san yadda take da tsauri da son mulki. Tana ganin cewa ba ka dace da yarinyar ba."
Ramlah tana shigar rayuwar TikTok, tana jin da?in yin bidiyo da wallafawa. Duk da cewa tana jin da?in sabon salon rayuwarta, har yanzu tana ?o?arin neman goyon bayan mahaifinta don biyan ku?in makaranta.
*******
Karfe shida na safe, na kammala duk wani aikin gidan da aka saba. Na gyara dakina, na gyara gado, na share bene mai launin toka. A gefen gado, na ajiye system dina, na kunna don kallon Korean film.
Ina jin yadda labarin ya fara da ?ayataccen salo, amma hankalina ya fara tashi da tunanin TikTok. Ji ya kamata in duba yadda aka kar?i sabon post ?ina na jiya.
Bayan na duba lokaci, sai naga karfe bakwai tayi. Na kashe system ?in, na mi?e tsaye, na nufi bandaki don yin wanka. Bayan na gama, na ?aura gyale mai launin ruwan ja, na bu?e TikTok. Wallahi jiya na tabbatar cewa kaina a duhu yake, na fa?a a raina ina dariya. Ina bu?e feed ?ina, sai na fara ganin post-post na yan gayu. Wasu suna rawa, wasu suna tsokanar juna. Wani video na wata yarinya tana tafi da salon ban dariya sai na yi murmushi. Wasu kuma sai na danna "next" saboda basu birge ni ba. Haka TikTok yake?, na fa?a ina gyara gashina a gaban madubi. To nima fa ba zan bari a bar ni a baya ba! Na ?auki wayata, na danna camera mode. Na za?i wata waka ta Hamisu Breaker wata da ta fi shahara a TikTok. Na kunna duk fitilun da ke dakina, don haske ya fito da kyau.
Na ajiye wayar a kan madubi, na fara rawa a hankali, ina jujjuya idanuwa, ina saitawa da murya. Kai! Na lura da yadda fuskata ta yi kyau sosai a cikin bidiyon.
Na tsaya na kalli bidiyon na, na ga yadda na yi kyau, sai na saki murmushi. Wai shi TikTok din nan yana sa mutum ya ji kamar tauraro. Na sa wasu hashtags kamar yadda Fatima ta koya min #YanGayu #Beautifu l#HamisuBreaker #TikTokTrend. Na danna Post, sannan na aje wayar a kan gado, zuciyata cike da farin ciki. Na fita daga dakin ina dariya, zuciyata na jin da?in wannan sabon salon.
Gidanmu gida ne mai kayatarwa sosai. Abbah yana da kudi, amma ba irin masu saki nan ba. Kowane abu a lisafi yake yi. Gidansa yana da fa?i sosai, an gina shi da salo na zamani. Falo mai tsawo, kujeru masu launin toka da fari, da fitilun chandelier masu ?yalli.Komai a gidan ya nuna cikar arzi?i, amma kuma akwai dokoki sosai. Abbah mutum ne mai tsauri a harkar ku?i. Duk da kuwa muna da komai, sai an yi lissafi sosai kafin a kashe kudi. Na shiga falon, na ganshi yana zaune bisa kujera mai kauri yana karanta jarida. Na yi tsuguno, na gaishe shi da ladabi. "Sannu da safiya, Abbah."
Yayi murmushi ka?an, ya ?aga kai. "Yau kin tashi lafiya?"
"Eh, Alhamdulillah."
Ban tsaya kar?ar komai ba, duk da cewa ina so in yi masa magana kan WAEC da NECO, amma na bari malamin mu ya masa magana. Kar na matsa masa, ko kuma ya ce ba zai biya ba. Na shiga kicin na ?auki ruwan zafi, sannan na koma dakina cikin nutsuwa. Ina kwance a kan gado, wayata ta yi ?ara notifikeshan TikTok. Na duba, sai naga comments suna tururuwa. Wasu na cewa
"Kai Baby Girl! Kina da kyau!"
"Salon ki yana birgewa!"
"Muna son ki sake yi."
Na saki murmushi mai cike da jin da?i. Haba! Ai ba zan tsaya nan ba. Sai Natashi nakara dasawa ?aina camera wannan karan wakar ado gwanja nabi ina dan ram gaji.