
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 23
..... as if everything is in his environment, as if there is nothing strange in his situation, as if this is his normal daily life style. Slowly the elevator stopped, he still did not look at her, he walked slowly and extended his hand to her. She stopped and looked at the smooth palm of one of his hands extended to her, and his eyes were on his phone, it seems that both his hands and both hands are skilled in using the phone. She looked at the palm of his hand very much, for the first time she felt it in her hand instead... This life.... is not like that of a poor person" she said in her heart, except that she was clearly unable to control herself. It is fear that should come now, the fear that is more powerful. The silence that he felt from his eyes fell on her, and their eyes were mixed with each other. "Let's go?" He said gently, putting his hand in his pocket instead of continuing to extend it to her. She was following him again, showing his every move. Her mind was divided again.
LU'U LU'U (The diamond)💎 HUGUMA BOOK 03///PAGE 23 Cikin awa daya da mintunan qalilan suka qaraso. Babban hotel dake dab da harami wato raffle makka palace.Ta sake daga idanunta tana daban hotel din. Daya daga cikin hotel din data saba sauka duk sanda zataje umara. Yana mata dadi,yanayin tsari tsaro kulawa dama komai nashi dabanne. Hotel ne na masu iko.....sarauta sama hannu da shuni a kowanne bangare na duniya."Raffle?" Ta sake nanatawa wani mamaki me girma da nauyi yana danne zuciyarta,zatonta da zarginta kuma a kansa yana sake ninkuwa.
Fuskarsu cike da alamu na sanayya, tashi fuskar kuma a sake da wani irin yanayi dake nuna nutsuwar da Allah ya yiwa ruhinsa baiwa da ita.Direct suka zarce zuwa elevator da zai rage musu tsahon tafiyar. Ko a ciki numfashi take ja kadan kadan tana sake satar kallonsa. So take taga wani abu daya sauya a tattare dashi amma babu. Shidinne dai......sheikh muhammad haisam din da suka taho tare daga agadez har zuwa makka din. Ba wani reaction nasa daya sauya, kamar komai yana kan muhallinsa ne, kamar ba wani baqon abu cikin lamarinsa, kamar dai normal daily life style dinsa kenan.A hankali elevator din ya tsaya, still bai kalleta ba, ya taka a hankali yana miqa mata hannunsa. Tsaiwa cak tayi tana duban lallausan tafin hannunsa daya miqa mata, idanunsa kuma suna kan wayarsa, da alama koda hannu daya koda hannayensa biyu dukka ya qware wajen sarrafa waya. Tafin hannun take kalla sosai, a karon farko taji wani tafi jinsa cikin nata hannun maimakon...
Wannan rayuwar.....ba irin ta talaka bace" Ta fada a zuciyarta,saidai har a fili ta gaza mallakar kanta. Tsoro ne yake kamata zuwa yanzu,tsoron da yafi na dazu qarfi.Shurun da yaji ya sanyashi daga idanunsa ya zube a kanta,take idanuwansu suka gauraye da juna. Ya dan zuba mata ido yanason karantar abinda yake cikin ranta,amma saita kawar da kanta tana jin tsoro da shakkarta suna qaruwa."Muje?" Ya fadi a tausashe yana maida hannun nasa cikin aljihun jubah dinsa maimakon ci gaba da miqa mata shi.A nutse take biye dashi tana sake karantar sa takunsa. QASAITA kowanne motsi nasa nunawa zallarta. Hankalinta ya sake rarrabu Sashen da suke nufa.....bata taba sauka a wani bangaren ba,wannan block din ma bata taba hauroshi ba.Bullowar wani balaraben matashi ya sanyata janye hankalinta kadan. Kaman sauran ma'a...
kammala ibadarta ta wuce.Bakin qawatacciyar qofar ya taka,ya matso da executive access card dinshi jikin qofar,tayi 'yar qaramar qara ta bude kanta da kantaIdanu akhnan ta sauke a hankali akan card din,adon gold din dake jikinsa na dabanne. Wani irin minimal design me daukan hankali. Ta aza idanunta akan embossed name din dake jikiAlsaamit shine sunan dake rubuce a jiki,akwai wani tiny emblem a jiki. Qawataccen crown me jan hankali sosai da daukan idanu.Tura qofar yayi,ya soma takawa zuwa ciki.Saita tsaya cak, qafafunta kamar sun qi motsi Cikin iikinsa yaji bata biye dashi,ya tsaya da tawa ya waiwayo da manyan fararen idanun sa yana dubanta.In salon bada sassauqan umarni.
Shima nasa fararen idanun ya zuba mata,sannan ya sauke numfashi a hankali yana maida wayarsa aljihu still bai dauke idanunsa daga kanta ba."Ki shigo" Ya fada da wani irin coolness yanayinsa yana nuna hankalinsa kwance yayi maganar.Ci gaba tayi da duban labbansa ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba. Haka kawai taji qwalla tana cika mata idanu,saita motsa labbanta a hankali."Ban tambayeka shiga ba.....waye kai?" Ta sake fada har ga Allah tana jin tsoro duk da ta sani tana amintaccen muhallin da ba kamarsa duk duniya. Amma ta sani,duka wannan.......dan wadannan,tsarin tafiyarsu.....private jet......wannan suit din duka ba aikin sultane bane. Tasan kudin da zasu sauka da farko,tasan jirgin da zasu bi duka ta bakin shehnaz......amma a yanzu sabanin komai take gani.Idanma sultane ne.....tun daga private jet zuwa wajen girmamawa tarba da karramawa
ma'aikatan hotel fa?."Ba gurin tsaiwa kiyimin tambayoyi bane nan" Sai ya daga hannunsa yana mata nuni da ciki kamar yana mata magana ne cikin ikon dake cakude da nutsuwa."Ki shigo" Ya rufe da fadin hakan cikin nutsuwar nan tasa.A hankali taji qafafunta suna saki,ta soma motsawa tana takowa zuwa ciki.A nutse ya saka hannu ya maida qofar ya rufe,sannan ya soma bin bayanta a hankali. Cak ta tsaya sanda yake tsaiwa Shima"Me yasa na yarda na shigo?,me yasa bance ba?" Ta tuhumi kanta. Saita daga blue eyes da sauri ta waiwaya tana sake dubansa."Ka fara bani amsa.....waye kai?". Idanu ya sake zube mata kawai yana karantarta ta cikin nutsuwa,tsoro,karaya duka yau yake...
da sauri ta waiwaya tana sake dubansa."Ka fara bani amsa.....waye kai?". Idanu ya sake zube mata kawai yana karantarta ta cikin idanunta. Rauni, tsoro, karaya duka yau yake gani cakude cikin shudin idanun gimbiyar agadez din a yau. Kafaffiyar gimbiyar nan wadda ta bawa maza da yawa kashi......kafaffiyar gimbiyar nan wadda bata sauka daga kan ra'ayinta......kafaffiyar gimbiyar nan da batasan tsoro ko sauya tsari ba.Lumshe mata idanun yayi yana budesu a lokaci guda, wani abu daya sake bayyanar da zanuun kyanshi."Zan baki amsa" Sai ya dakata."Amma ba yanzu ba" Ya cikashe maganarsa."Sai yaushe?" Ta sake fadi da alamu wannan dabi'ar tata ta kafiya ta motsa.
kanta,ya tara takawa a nankali yana nufar daya daga cikin qofofin dake cikin luxury living room din,ya budeta a nutse,ba tare daya kalleta ba yace."Ga dakinki.....ki shiga ki huta,ki kuma shirya nan da awa daya zamu shiga haram". Daga haka ya juya a nutse yana sake bude daya qofar dakin,ya taka a nutse yana shigewa ciki.Wannan mutumin?... meye ainihinsa?,Sheikh? businessman?,royalty?,Ko dukka?toh fa......masu karatu.....a samu wani ya taimaki akhnan ya bata satar amsa......ya gaya prince ne.....dan sarkin Ethiopia da kansa k tunani da canki canki ya qarasa zautata 😂😂😂muje zuwa mutane na