Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 6

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 6

.....t to make you happy... and... I feel very dry..." He gave her one last look that combined pity and judgement. He went into the bathroom, a prayer came out of his mouth, he turned on the hot water and poured it into the basin as if he was washing his heart from the confusion it was in. While the water was pouring into his body, his heart told him one thing again: "I want marriage." She calmly walked into the bathroom in the bedroom of the big house, which was full of luxury and odor. After she finished bathing with hot water, she put on a white bathrobe and came out. She found him sitting on the side of the royal bed, clutching his cartier watch. He didn't even look at her. She sat next to him, her heart was full of fear. He didn't look at her. He said calmly. "I already booked everything."

Standalone post1,386 words

SHAFI NA SHIDA

Ayayin da ya daga nar?akkun idanunsa ya zubasu cikin fuskarta, idanuwansa sun ?auki launin dusar rana kamar yadda zuciyarsa ta ?auki zafi mai nauyi. Bacin rai ya bayyana a kowane kwarjinin fuskarsa.

Aishatu ta ?ago kai cike da jin nauyin laifinta, tana jiran hukuncin zuciyarsa kamar wacce ta kusa fuskantar sar?a??en zargi a gaban al?alin kotu.

"Aishatu..." ya ambaci sunanta da sautin da ya sa zuciyarta ta tsinke. "Na fa gaya miki sau nawa ki daina saka abu a gabanki?"

Cikin ra?a mai cike da hawaye tace, "Dan Allah kayi hakuri Habibie... wallahi ba don komai nake sakawa ba, shekaruna sun ja ne, ina bu?atar gyara... kuma abun yana ?ara ni ima ne..."

Yana da?a huci , ya ce da ita "Ni na ta?a ce miki ina son ki saka wani abu a jikinki? Gabanki ba bola bane Aishatu... kuma ban gaya miki sau ?aya ba!"

Yana ficewa daga gado ya ?auki tawul, yana gyara rigarsa cikin fushi. Aishatu kuma ta dur?usa cikin ?asa tana kuka da neman yafiya.

"Habibie please... banson fushinka. I just want to make you happy... kuma... ni naji bushewa sosai..."

Yayi mata wani kallo na ?arshe kallon da ya ha?a tausayi da yanke hukunci. Ya shiga bandaki, addu a na fita daga bakinsa, ya kunna ruwan zafi yana shigewa ?ar?ashin ruwa kamar yana wanke zuciyarsa daga rudanin da take ciki.

A yayin da ruwan ke zuba a jikinsa, zuciyarsa na sake jaddada masa abu guda: "Ina bu?atar aure."

Sanin halinsa da idan ya fito masa bazai saurareta ba, yasa Aishatu mi?ewa cikin nutsuwa, ta shige ?ayan bandakin dake cikin tafkeken ?akin barcin da ke cikin katafaren gidan gidan da ke ?auke da tarkacen alfarma da kamshin ku?i a ko'ina.

Bayan ta gama wanka da ruwan zafi, ta tsane jikinta, sannan ta zura rigar wanka mai launin fari, ta fito. Tana fitowa, ta tarar da shi zaune a gefen gadon royal, yana danne-dannen system ?insa, agogon Cartier a hannunsa na le?owa daga rigar barcinsa. Ko kallon gefenta bai yi ba.

Cike da natsuwa da salo, ta karaso ta zauna kusa dashi, zuciyarta cike da fargabar kada laifinta ya cusa hazo a tsakanin su.

Bai kalleta ba, amma cikin sanyi da izza ya ce, Kiyi kwanciyarki. Gobe flight ?inku da rana ne. I already booked everything.

Ta narke murya da sassauci, kamar mai kokarin tunzura zuciyarsa da tausayi, "I m very sorry Habibie... na yarda nayi kuskure, bazan sake ba wallahi."

Shiru ya ?auki ?akin, sautin Ac ?in dakinsu na tsintuwa kamar yana karanta yanayin zuciyar ma auratan.

Daga bisani ya dago, idanunsa suka ha?u da nata, cike da bacin rai da takaici, yace, But sau nawa zan gayamiki Aysha? Duk abinda kike bu?ata kisha, ki shafa, na barki. Amma wannan saka abu a gabanki da sunan yana ?ara ni ima? Kinsan dame ake yin wa?annan abubuwan? Kinsan irin cutar da zai iya janyo miki? Kinsan ciwon da zai iya ?oye a ciki har sai lokacin da babu magani? Cancer is real fa.

Tana ?asa da murya cikin kaskantar da kai ta ce, Please Habibie bazan ?ara ba. Kayi hakuri.

Ya lumshe idanu, ya dafe goshinsa kamar mai tunani mai nauyi, amma bai ce uffan ba.

A haka ya juyo gefe, ya kwanta. Ita kuma ta na cikin rigar wankanta, ta na kallo kamar karamar yarinya da aka yi wa garga?i. Tana ba shi ha?uri har baccin dare ya ?auketa a gefen gadon, cikin dakin da yake dauke da kamshin turaren Oud Royal da mur?a??en labulen siliki.

Zuciyarsa na faman bugawa da juyayi. Kodayake fushi ne ya mamaye sa tun farko, amma yanzu zuciyarsa na karkarwa da tausayi da bu?ata. Ba wai bu?atar jiki kadai ba, a a bu?atar kusanci, tausayinta, da ?aunar da ke neman dusashewa a tsakanin su.

Ya juya a hankali ya kalleta, tana kwance cikin barci mai nauyi, numfashinta na fita a hankali kamar sautun wa?ar dare. Fuskar ta ta haske a ?ar?ashin fitilar bango, idonta rufe cikin natsuwa, le?enta na ?an motsi kamar tana ?o?arin fa?in wani abu.

A hankali ya matsa kusa da ita. Bai fa?a mata komai ba. Amma zuciyarsa ta cika da salwanta.

Ya ?ora hannunsa a saman kugunta, ya janyo ta a hankali kamar jaririya. Ya rungumota kamar yana ?o?arin ha?a zuciyarsa da nata. Jikinsa ya buga da nata, zafin ?auna ya daki lafiyarsa. Numfashinsa ya fara canzawa, jikinsa ya fara rawar bu?ata, amma zuciyarsa ta hana shi bin bu?atar jiki sai dai ya yi shiru yana jin dumin jikinta.

Sai da ta ?an motsa a barci, sannan ya matseta sosai a ?irjinsa. Le?ensa ya ?an sauka a gashinta, sannan a saman goshinta, yana sauke numfashi mai nauyi.

"Aysha... Ina jin ki fiye da yanda zan iya bayyana... Amma me yasa kike cutar da kanki har kin manta da irin wacce kike?"

Ya dora fuskarsa a ?ugunta, yana jin hawaye na taruwa a idanunsa, amma ya hana su zubowa. A wannan lokacin, ba miji da mata suka kwanta ba zuciyoyi biyu ne da ke neman mafita a cikin dakin da ya cika da shiru, da motsin ?auna, da tambayoyin da babu amsa.

Rana na ?an kaiwa ?arfe takwas da rabi na safe lokacin da Aishatu ta sauko daga saman bene cikin shigar da ta ha?a ladabi da salo. Riga ce mai launin ruwan kwai, mai ?auke da ?an kamshi na turaren Maison Francis Kurkdjian, wanda ko iska na busa daga gabanta, sai ya bar ?amshi a ko ina.

A cikin babban falon gidan dake ratsawa da gilasai masu she?i da fitilun kristal, ta shinfida kayan karin kumallo a teburin girma croissant, omelette, lemo na orange sabo, da shayi mai madara. Komai cikin kayan fure masu kwantar da zuciya.

Yana saukowa daga sama cikin shigar white linen da agogon Rolex a hannu, ta tarbe shi da murmushi. "Good morning Habibie breakfast is ready."

Bai ce komai ba, amma ya zauna yana kallon girman kwazon da ta yi. Duk da jiya sun yi rigima, yau ta taso cikin salo da nuna kulawa irin wadda bata bu?atar magana.

Yana ci, ita kuma tana zaune kusa da shi, tana jiran ya gama. Bayan ya kammala, ya ?an share bakinsa da tissue.

Bayan ya gama karin kumallo, Alhaji As ad ya nufi gidan yayarsa, Mamy, domin da yamma zai tafi garinsu don wata muhimmiyar ganawa da Mai Martaba. Da ya isa, ya tarar da ita tana zaune a falo, abinci kala-kala a kan tebur ba sai an gaya maka ba, za ka gane gidan attajirai ne.

Fiddausi, wacce ke gefe tana zaune kamar tana jiransa, ce ta fara gaidasa da murya a sanyaye. Sai dai bai ma amsa ba, ya karkata ya gaida Mamy da girmamawa. Duk da cewa yayarsa ce, ba ita yake binta ba, amma akwai tarin girmamawa da mutunta juna a tsakaninsu.

Mamy ta kalleshi cike da kulawa, tace "As ad, dan Allah kayi hakuri da halin Fiddausi. Kasan yarinya ce, tana cikin damuwa da matsalolin aurenta. Ko da ta gayamin matsalarta a waya, ni ce na bata shawarar taje ta same ka."

As ad ya gyara zama, ya dan yi shiru na ?an lokaci sannan yace da tsantsar takaici a muryarsa "Fiddausi ce yarinya? Mamy kema zaki biyewa Hajja kuna barin fitsararriya tana aikata abin da taga dama? Bari na gaya miki ko kallon banza kika yi wa matata, wallahi sai na dauki matakin da ba zai birgeki ba. Wannan mugun hali kike ?auka kamar burgewa ne? Yar sarki ce? Mai kudi? To sai ki sani, kasa ce ?arshenmu babu daraja a hakan.

Maganar mijinta kuma, da kin san irin abubuwan da take masa, da kun tofa baki tuni. Ta hada kai da kawayen banza tana tozarta mijinta. Fiddausi ba ta da komai sai raini da wulakanci. Ba ta girmama mijinta, ba ta mutunta shi, balle ta sauke nauyin aure da ke kanta.

Ina gaya muku, mace idan ba ta bin mijinta ba wallahi sallarta da azuminta da hijjabinta, duka wuta ne a gaban Allah. Nagartar mace sharadinta shi ne ta bi mijinta.

Kuma Mamy wai har zagin iyayensa take yi? Wallahi Mamy, wannan ba daidai ba ne. Fiddausi, idan kina ganin abin da kike yi shine daidai, to bismillah ki fice daga gidan. Amma idan kina ganin zaki zauna kina kuntata masa, wanda yake ?aunarki da gaske, to sai na gaya miki, duniya za ta juyo miki.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH