Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 13

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 13

.....is divided. There was a little silence in the place, the silence that came only in silence, and it was the same as her entrance. "They have to see... I am still an elephant, nothing has changed," she said from the bottom of her heart. In her heart, she feels that there is this person who is hunting her here....if her enemies are watching her....she will surely show them that an elephant has fallen to the power of a fool. "I am not the one who is being invited..." She said to herself as she braced herself and gave herself confidence. Just when he was sitting six other six. Khadeem....mutallab.....amjad, omar, maleek, naseeb the seventh one went out a little from their circle and was relaxing in a different chair which was a little far from them. He is completely absorbed in the chair, all his eyes are falling on the mini system that is placed in front of him. Since yesterday without anyone's knowledge, Abeer has installed a security device in every corner of the place where the meeting will be held. That's right.....

Standalone post1,533 words

πŸ’Ž *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 13*

Ranace me dumbin tarihi da martaba ga familyn DIORY HAMMANI na aurar da diyar safeena da safiyya,kintsatsen family din da nutsuwa ilimi da kamala suka cikashi,abinda ya taimaka gurin qayatar gurin kenan.

Idan ka hangi morsa safiyya a daidai lokacin......kyautar kudade da sulallar da taketa yi......farincikin dake shimfide saman fuskarta zaka rantse da Allah bata taba baqinciki ba a dukkanin rayuwarta,ko kuma bata ma taba sanin mene baqincikin ba.

A yau tana jinta kamar wadda aka bawa sabon rai dama rayuwar gaba daya. Hakanan ta bangaren nannie......abinda ke kai kawo a ranta yadda suka aurar da falaak da akhnan da aurenta ya kusan zama barazana.....Allah ya kawo lokacin kauda aisa don shehnaz da nata maganan a hannu. Tsakanin su biyun saika gaza tanta ce wace uwar akhnan da shehnaz?.

Daya bayan daya hadimai daga sassan mammina suka fara shigowa,dauke da akwati kwati kanya masu kwana hudu dake lullube da wani kyakkyawan yanki.

Wani shuru ya ratsa gurin kadan,shurun da yazo ne kawai cikin arashi,sai kuma yayi daidai da shigowarta. Da dukka izzarta take takowa

"Dole su gani.....har yanzu ni giwa ina nan,ba wani abu daya canzani" Tayi maganar qasan ranta. Cikin zuciyarta tana jin qilan akwai wannan wanda ke farautarta a nan gurin....idan ma maqiyanta suna kallonta....tabbas zata nuna musu ko giwa ta fadi tafi qarfin wawa.

"Nice me gayyata......bawai wadda ake gayyata ba" Ta fadawa kanta da kanta tana sake kambama kanta tare da bawa kanta qwarin gwiwa

Daga falaak har akhnan din,a yau sai kamanninsu suke nunawa,kamannin da suke tabbatar da nasabarsu da SULTANE MUHAMMAD HAMMUD......Kamannin da suke nuna su din jinin MASARAUTAR AGADEZ ne na gaske.

Daidai lokacin da yake zaune shida sauran 'yan shidan. Khadeem....mutallab.....amjad,omar,maleek,naseeb saishi na bakwai daya fita kadan daga da'irarsu yayi relaxing a wata kujera daban dake nesa kadan dasu.

Sosai ya narke cikin kujerar,dukka idanunsa suna zube saman mini system din dake girke a gabansa a kunne.

Tun jiya ba tare da sanin kowa ba,daga shi sai abeer ya sanya aka maqala na'urar tsaro a kowacce kusurwa ta gurin da za'a gabatar da taron. Yayi ne da nufin samar da cikakken tsaro.....yayi ne don ya tabbatar da cewa yau din gidan ya zamana cikin tsaro. Musamman yau din data kasance sultane ya zabeta,ya zabeta a matsayin ranar da haisam da kansa zai gabatar da ahmad cikin iyalinsa.

"Bansan ko akwai wani shirin ba,bansan ko akwai wani tsarin ba,amma inaso kayimin alfarmar gabatar da ahmad cikin iyalinsa a karo na biyu.....a daren ranar lahadi,inaso a gaban kowa,kowa ya shaida dawowarsa......koda kuwa ka boyemin,jikina yana bani batar Ahmad tana da sila......tana kuma da dalili ba haka siddan ta faru ba.....na kasa nutsuwa muhammad,idan na kwanta fuskar ahmad yana qanqani nake hangowa". Sosai wani abu ya narke a zuciyar haisam din,yasan wannan ciwon a murya da idanun Nanay dinsa.....wannan dalilin ya sanya yakejin lokaci kamar yayi tsaho.....lokacin da zai bata albishir din safeenarta tabar wani reshe.....reshen da gata a gabanta ya kawo mata.

Haka kawai yaji yana ra'ayin monitoring gurin da kansa,amma kaman bazai iya ba saboda gajiyar dake nuqurqusarsa kwanakin. Daga ahmad har Muhammad basason yayi nisa dasu,sukan kashe Lokaci sosai tare dashi,wannan ya sanya saboda ya fara shiga tsakaninsu sosai,suke wani mugun bash in respect tamkar babban wa da kowannensu ya rasa bai samu ba.

Ya zauna gaban masarrafin cameras din,ya kuma bude kowacce shiyya,amma sai ya samu kansa da kashe kowacce camera ya miqawa abeer dake kebance a daki shi dasu beeno,ya zabi fuskar camera qwaya daya......fuskar camera da ta nan ya hangi takowarta tana isowa gurin zaman da aka tanadar musu.

Lafiyayyar atamfa ce a jikinta me wani irin kwantaccen launi mara hayaniya ko saurin jan ra'ayi,saidai kuma yadda ta kwanta a fatarta shine abu na farko da zai fara fusgar hankalinka fiye da kima.

Wani irin sassanyan kyau da karon farko idanunsa suka fara sauka akai......wani sassanyan yanayi......basaraken jikin nan saye cikin atamfar hausawa.....atamfar data zama daya daga cikin suturun da yayi research akai na yankin africa da yaji yana burgeshi sama da komai.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Atamfar dai aka warware,aka dorata daga saman daurin dankwalin kanta wanda aka matse da clip don kada ta sauka,mayafin kuma ya watsu a gadon bayanta da sample din shigar suturar ALKYABBA.

Idanunta.....labbanta.....dama fatarta dukka sunyi wani fresh......blue eyes dinnan sunyi fayau,don ba wani makeup saman kyakkyawar fuskarta sai anihin zallar madarar kyan da duk motsawar da zatayi yake magana akan kansa da madaukakin sauti.

Idanunsa ya lumshe a hankali yana jin wasu abubuwa suna spark cikin kansa,yaja boyayyen numfashi ya aje yana sake ware idanunsa daidai sanda take dab da abun zamanta. Idan har ya gani daidai kamar wadannan siraran labban sun furta

"Bismillah" Ne,sai yaji wani dadi yana sauka har qasan ransa da zuciyarsa. Siraran zara zaran fararen yatsunta da wani lalle me azabar ja ya yiwa ado me fusgar hankali ta sanya tana tattara lullubin saman kanta zuwa gaban rigarta da dinkin ya rufe komai ruf,saidai hakan bai hana bayyanar tudun qirjinta ba daya zauna dasss kaman zanashi akayi ba halitta ce cikin qirjinta ba.

Wani abu me qarfi yaji ya sauka masa.

"Me yasa ba hijab ba?" Ya yana motsa labbansa da qarfi,omar da yadanfi kusa dashi ya waiwayo da hanzari.

"Captain.......magana kakeyi?". Wadannan tsumammun idanun nasa ya daga a nutse ya zubewa omar su,kallon da ya sa ya omar janye dubansa daga kansa,bai kuma sake tankashi ba ya koma cikin hirarsu dasu naseeb.

Sake janye idon nasa yayi,yana sane ya yiwa omar irin wannan kallon,ya fuskanci tun dazun akwai wani magana ne cikin bakinsa.....ko a dazun bai shirya doguwar magana ba bare yanzun da yakejin komai yana sauka daga ainihin saitinsa daga kwanyarsa.

"Halal.....halal ce" Zuciyarsa ta fada masa a sanda yayi zooming fuskarta dab da dab. Daga nan inda yake yana iya hangen wani abu me nauyi cikin idanunta.....kamar kawai qarancin walwala saman fuskarta ta,kamar akwai abinda ke damunta can qasan ranta,hasalima wayarta na tsakanin yatsunta tana jujjuyata tana wasa da ita kawai,bata iya daga kai ta kalli mutane yadda ya kamata.

Haka kawai yaji sha'awar yayi magana da ita......a kwanakin nan aduk sanda zai tunata yana tunata ne da TAUSAYI. Ya yadda cikakkiyar marainiya ce ita gaba da baya ba tare da ita tasan marainiyar bace a karan kanta.

_smile.....its a sunnah_ abinda ya rubuta kenan ya kuma aike mata ya saqon karta kwana,sannan ya maida wayar gefansa ya ajiye yana maida kallonsa ga allon system din.

Akan idonsa saqon ya shiga. Yayi qara kadan,tayi kaman ta share,sai kuma yaga ta bude.

Reaction nata ya nuna sosai......wani irin reaction daya nuna zallar mamakinta a fili. Wadannan blue eyes din tadan bude kadan kafin ta maidasu daidai,ta sake dago wayar daidai fuskarta da alama tanason tantance number waye?.

Murmushi kawai ya subuce masa ba tare daya shirya hakan ba,yanayin sai yaji ya masa dadi. Tsokana......a tsakaninsa kawai dasu maleek irin haka take faruwa.....yau ne karon farko da tsokana ta hadashi da wani jinsi daban ba nasa ba. Wayar ya sake dauka,ya sake rubutawa a gajarce.

_smile mana please_ a wannan karon murmushinsa me sauti ne,saboda yadda yaga gaba daya ta diririce tana waige waige tana kuma sake kallon fuskar wayar tata,kafin ta tabo birra dake gefanta ta qaraso ta kuma rusuna ita kuma ta shiga nuna mata wayar birra tana kalla tana saurare.

Ya fahimci me takeson sanyata tayi sanda ta damqa mata wayar,ta koma ta zauna,saidai duk da wayar tabar hannunta yaga alamar bata nutsu ba,tanata rarraba blue eyes dinta kawai tsakanin jama'a,sai ya sake sauke murmushi yana jawo wayar ya danna Stwiched off ya kasheta gaba daya.

Sai a sannan yaji yadda parlor din ya dauki shuru,ya aro nutsuwa ya azawa fuskarsa kafin ya daga idanunsa ya bisu da kallo daya bayan daya.

Kowa kawai idanunsa yana kanshi,daga sanda yayi wannan murmushin me sauti sai ya dauki hankulansu,yadda yaci gaba da murmushi kadan kadan kuma ya qarasa kashesu gaba daya.

Yana da kirki sakewa da abokansa......amma ba kasafai zakaga yayi murmushi a jere har sau biyu haka ba.

"Lafiyanku?" Ya maze yana jefa musu tambayar

"Kai zamu tambaya captain,ko yau ka fito daga daki a daren farkonka iyakar murmushin da zaka yita yi kenan" Amjad dan kai tsaye ya fadi yana miqewa ya dauki wayarsa,don ya tabbatar tunda ya fadi wannan maganar akwai case ci gaba da zamansa a gurin.

Wani nauyi yaji ya kamashi,saidai bai bari sun fahimta ba ya bisu da tsaki,ya maida hankalinsa ga system din,yana jin kamar bayaso amma haka ya kasheta yana fadin.

"Yana daga cikin kyawun musuluncin mutum,yabar abinda babu ruwansa".

*_KOMAI NISAN DARE_*

*_KOMAI NISAN JIFA_*

*_KOMAI GIRMAN GONA........_*

*AGADEZ PALACE*

*sultane muhammad hammud meeting room*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽