
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 5
.....a pa?in "Innallillahi wa inna ilaihiraji un! Abban Ramlah, why did you do this to our daughter?". She immediately burst into tears as if she was not the one who was trying to laugh. Confused and not knowing what to do, I also burst into tears. I said, "Mummy, son of God, I'm sorry. By God, I don't know if the medicine is harmful. Fatima Habib gave it to me. She told me to drink it because people say that I'm not a woman. Every time they say that I'm a bitch. Sometimes they say that I'm a bitch. This statement really hurt me." I wiped my tears with the edge of my cloth and added that "In class, no one cares about me. They say that I have nothing in my body. That's why when Fatima gave me the medicine, I took it... Son of God, forgive me. I will not be angry." Mumy stared at me as if she had been stopped. Her eyes filled with tears, she knew Abba could hear us outside, that's why she didn't say anything. She turned to me with compassion and a calm voice. "God protect you, little one. God protect you from the harm that will befall you. Do you? Stop listening to people's words. You are beautiful, you are better than Billy and Abbas in this house. It's just that you don't look like
SHAFI NA BIYAR
Washegari, idanuna da fuskata sun kumbura, fuskata cike da hawaye. Ina tsaye gaban madubi ina kallon kaina, zuciyata cike da nadama da tsoro. Na fashe da kuka, saboda abinda ya fi bani tsoro shine yadda aka ce maganin da na sha yana da illa.
Bayan sallar asubah, sai ga Abba ya shigo dakina. Da ya gan ni, ya tsaya na ?an lokaci yana kallona, sannan ya juya gefe yana share hawaye.
Abba ne fa wannan! Mahaifina da nake da tabbacin yana matu?ar ?aunata, duk da komai nayi.
"Abba, ina kwana, na ce cikin murya mai rauni."
Sai da ya ja numfashi, kamar mai ?o?arin hana zuciya fashewa, sannan ya ce
"Kije ki Nemi abinda zakici. Anjima kadan zamu je asibiti."
Ya fa?i haka cikin wani irin yanayi da ya cika mini zuciya da wani sabon kuka, sannan ya fice daga dakin ba tare da ya ?ara juyowa ba.
Ina kallon bayansa har ya bace, sai ga Mumy ta shigo. Ta tsaya tana kallona na dan lokaci, kiris ya rage ta kwashe da dariya saboda yadda na koma, amma sai ta daure fuska, ta sunne kanta kasa tana fa?in
"Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Abban Ramlah, me ka yi wa yar mu haka?".
Nan take ta fashe da kuka kamar ba ita ce da can ke kokarin dariya ba.
Cikin ru?ani da rashin sanin abinda zan yi, nima na ?ara fashewa da kuka. Na ce
" Mumy, dan Allah kuyi hakuri. Wallahi bansan maganin yana da illa ba. Fatima Habib ce ta bani. Tace min in sha saboda yadda mutane ke cemin wai ni ba mace bace. Kowanne lokaci sai su ce karmashashiya ce ni. Wani lokaci suce kwaila ce ni. Wannan magana na ci mini rai sosai."
Na share hawayena da gefen zanena sannan na ?ara cewa
"A cikin aji kowa baya kulani. Sai suce wai ban da komai a jikina. Shi yasa da Fatima ta bani maganin, na sha... Dan Allah ku yafemin. Bazan ?ara ba."
Mumy ta zuba min ido kamar wacce aka tsaya da ita cak. Idanunta suka cika da hawaye, ta san Abba yana jinmu a waje, shi yasa bata ?ara ce komai ba. Ta juyo gare ni cikin tausayi da sanyin murya.
" Allah ya kare min ke, auta. Allah ya tsare ki daga cutar da za ta same ki. Kinji? Ki daina sauraron maganganun mutane. Ke kyakykyawa ce, kin fi Billy da su Abbas kyau a gidan nan. Kawai dai baki yi kama da mamarki ba sosai. Amma mamarki cikakkiyar Balarabiyar Jordan ce. Kin taba ganin yadda Mama take, kakarki?."
Na girgiza kai cikin kuka.
"To, mamarki ta fi kyau. Kuma kibar da kike so tana zuwa a hankali. Ai ke kinada jiki, ba kya kallon Billy? Ita ma tana da kiba. Ki kwanta ki huta, bari na hada miki breakfast."
Ta juyo ta fice daga dakin, ni kuma na kwanta ina jin zuciyata na sanyi.
Abba bai ce komai ba, sai kawai ya juya ya fice daga dakin. Ashe dakinsa ya wuce kai tsaye, ya zauna yana kallon bango tamkar mai nazarin wata matsala mai nauyi. Cikin nutsuwa ya ?auki wayarsa, ya kira Yaya Usman.
Yaya Usman ?an fari ne a gidanmu, kuma yanzu haka yana wata ?asa yana ci gaba da karatun wani muhimmin kwas. Likita ne kwararre, cikakken masani a fannin lafiya.
Abba na ?aukar wayar, cikin wata irin damuwa ya ce Usman, kana lapya?
Lafiya lau Abba. Ya Lafiyar gida dai?
Ba lafia ba. Auta ta sha wani magani wai na karin kiba. Ashe kuma yana da illa.
Subhanallah! Ta sha da yawa ne?
A a. Kamar sau ?aya kawai. Amma yanzu muka ji wasu na cewa yana da illa.
To, Alhamdulillah. Idan sau ?aya ne kawai, to babu komai insha Allah. Amma fa ku kaita asibiti a duba lafiyarta. Ka kwantar da hankali kuma ka daina fushi da ita. Gaskiya fa yaran yanzu sai addu'a da hakuri.
Yaya Usman ya ?an yi shiru na ?an lokaci, kafin ya ?ara da cewa
Ka san Auta fa bata da wani laifi. Idan ka ganta da kawayenta zaka gane ita ce karama. Amma tunda ta fara zama yammata, tana jin kamar dole ne ta canza. Haka yaran zamani suke, suna son su yi girma fiye da shekarunsu.
Abba ya dan sosa kai, yana fadin
Au, Usman Auta ce yammata? Yarinya shekara goma sha biyar?
Yaya Usman ya kyalkyale da dariya.
Haba Abba! Auta fa shekararta goma sha takwas ne. Wallahi ba sha biyar ba. Kada ka rage mata shekaru, fa! Ai ma yanzu ita yar shekara sha takwas ce cikakkiya.
Abba ya dan ?aga gira, yana mamakin abin.
Banson karya, Usman. Ta ina tayi sha bakwai?
Yaya Usman ya murmusa, sannan ya ce
To Abba, ai ko mamarta marigayiya, tafi shekaru goma sha biyar da rasuwa. Kaga kenan shekarunta sun jima suna tafiya. Ka karbi gaskiya kawai.
A lokacin, Abba ya jinjina kai, yana murmushi cikin sigar fahimta. Sai ya dafa kansa kamar wanda ya dawo daga rudani, yana sauke ajiyar zuciya.
Yaya Usman kuwa ya ?ara kwantar masa da hankali sosai, ya tabbatar masa cewa komai zai daidaita, kuma zai taimaka wajen ganin an bi lafiyar Auta da kulawa.
Wajen ?arfe goma na safe muka bar gida muka nufi babban asibiti da Abba. Na zauna a kusa da shi a motarsa, amma ba tare da na ce komai ba. Idanuna na kallon titi ne, zuciyata na cike da fargaba.
Bayan dan lokaci, muka isa asibiti. Likita ya kar?e ni da kulawa, ya fara duba lafiyata, sannan ya tambaye ni wasu tambayoyi masu mahimmanci. Daga karshe ya bani wani magani guda ?aya.
Ya jingina da kujerarsa, yana fuskantata, sannan ya ce da murya mai sa nutsuwa
Idan da akwai maganin fitar da nono kai tsaye, da turawa su zasu fara amfani da shi. Amma wallahi, duk abin da suke yi surgery ne, kuma shima yana da matsala. Wannan shan magungunan kari ba komai bane face barazana ga lafiyar ku.
Sai ya ci gaba da bayyana mini illolin amfani da magungunan karin kiba da na breast. Na kasa d aga kai, sai dai na jingina da kujera ina saurare da ladabi kamar wata karamar daliba.
Ya ce da Abba Abba, just two days ne zaki ga yarinyarka ta murmure. Kada ka damu, komai zai daidaita.
Da muka fito daga asibiti, muna cikin mota, sai Abba ya ce To, Auta, me kike bukata yanzu?
Nace da sauri kamar wadda aka jima da dakile mata murya Kayan shafawa da turarena sun ?are.
Abba bai ce uffan ba, sai dai ya nufi babban mall. Da muka isa, ya miko min ATM ?insa yana fadin Sai ki sayi duk abinda kike bukata. Na gode sosai, Abba, na ce, cike da farin ciki.
Na shiga cikin mall ?in kamar wadda aka kawo talla. Na zabi kayan shafawa kala-kala, turare, mai, har da lip gloss da alawa. Na fito da ledodi har uku kamar wata amarya.
Da muka dawo gida kuwa, Mumy na ganina da kayan sai ta cewa Abba mai isa yakaini? Me amfaninta wai? Ai da ita sai takaini Na dan kalli yadda take harara, sai kawai na wuce cikin dariya a zuciyata. "Ai ba ke nagaya ma bukatata ba, bayan wulakancida kikayimun rannan.
******
Tsaye yake a tsakiyar babban bandakinsa wani katafaren wuri mai ?aukar hankali tamkar ?akin sarki a cikin fadar larabawa. Ruwan dumi na sauka daga sama, yana gangarowa a kan fatarsa mai laushi, yana yawo kamar ruwan zinariya.
Bangon bandakin an lullube shi da fale-falen marmara masu she?i, kowanne yana ?aukar hoto idan ka dube shi. Fitilun bango biyu suna bada haske mai laushi, suna wal?iya kamar kyandirori a cikin zauren tsohuwar kasaitacciyar killa.
Turaren wanka na oudh da amber suna tashi a cikin iska, sun cika bandakin da wani irin ?amshi mai nauyi da daraja kamshi.
A gefensa, tawul mai launin shudi yana rataye a kan bakin tagar gilashi, wanda ke duba filin shakatawar gidan.
A jikinsa, ruwan dumi yana sauka da salo, yana wanke gajiya, yana ha?uwa da kwantar da zuciya. Zuciyarsa cike take da shiru ba don bashi da magana ba, sai don mutumin da kalmarsa guda na iya murkushe magana dari.
Shi ne As ad Babangida ?an sarki, attajiri, kuma maigida. zuciyarsa tana saurarar ihun Fiddausi daga nesa.
Sassan gidan suna girgiza da hargowa. Bai ce uffan ba. Bai motsa da gaggawa ba. Ko shakka bai ji ba yasan ita ce. Fiddausi ce fitinanniya marar kunya, yar sarauta amma marar kima. Shi da ita, tuni suka wuce iyakar jin da?i a tsakanin juna.
Sai dai yau... yau ba zai bari ta raina masa iyali ba. Yau zai koya mata bambancin jin sarauta da daukar sarauta a matsayin shinge.
Cikin hanzari, As ad ya gama wanka. Ya fito da zafin sarauta a fuskarsa, ya ?ora hula mai nauyin alfarma, kayan jikinsa na she?i. Fitarsa daga ?akin kamar fitar sarki daga zauren fadar da aka tada saboda rashin da a.
Da ya sauko ?asa, gaban gidan ya yi shiru. Kowa na jiran mamaki ko faduwar magana.
Yana kallo daya da Aishatu, matar da ke zaune cikin fushi amma da ladabi. Bai yi mata magana ba a farko, sai dai ya fuskanci Fiddausi kai tsaye, murya a k asa amma kalmomin sa na da nauyi kamar dutsen guga.
Fiddausi, matata ba sa arki bace. Kuma ba za ki yi ta shiga gidana kina raina min gida ba.
Fiddausi ta fara zaro ido, tana fadin
Yaya ni fa... ni yar uwarka ce...
Amma As ad ya ?aga hannu, bai bari ta karasa ba. Ya ce da ?arfi amma da kwantar da kai irin na masarauta
Babu wata dangantaka da ke da muhimmanci idan har tana tozarta martabar aurena. In kin ?i girmama matata, to ke ma ba za ki samu girmamawa a nan ba. A halin yanzu, ki fita daga gidan nan.
Yaya... yanzu sai da izininta zan gan ka ne? Fiddausi ta fa?a da kuka.
As ad ya daka mata tsawa, murya mai danna zuciya
Idan kika ?ara magana a nan, ba fitar gida ba za ki yi ba har fitar girmamawa! Wannan gida gidan aure ne, gidan ladabi, ba gurin masifa da zagi ba. Ki fita. Yanzu!
Kamar wacce aka zuba mata ruwan sanyi, Fiddausi ta juya da kuka. Ta ja motarta, jiki ba ?wari, ta fice cikin hanzari, tana lumshe ido da hawaye kamar zata tsayar da lokacin.
As ad kuwa ya juyo ya kalli Aishatu. Bai ce komai ba, sai dai ya ?ora hannunsa a kafa?arta cikin nuni na goyon baya da girmamawa. Wannan shine mulki ba da ihu ake gina shi ba, da hali ake ?aukaka shi.
Bata tsaya ko ina ba. Cikin huci da kuka, Fiddausi ta ja motarta da karfi, ta bar harabar gidan As ad. Idonta na cike da hawaye, zuciyarta na tafarfasa da takaici da kishi. Ba don ta zauna a gida ba, sai don zuciyarta ta ?aci fiye da yadda ta saba.
Tana isa gidan babbar yayarsu, tayi horn sau biyu kacal a alamar "Ina nan, kuma bana cikin natsuwa."
Babbar yayarsu ta fito da kanta, tana kallonta da tausayi. Fiddausi ta fito daga mota tana kuka, sannan cikin hayaniya ta ce
Wallahi Ammyn Aliyu, sai na wulakanta Aishatu. Wannan matar tsiya ce! Daman ba zan taba mantawa da yadda ta tozarta Hajjarmu ba. Yanzu yaya As ad yana so ya raina ni saboda ita? Ni fa yar uwarsa ce! Meye yaga a jikinta har yake sonta haka?! Wallahi ko kadan ba sa'arsa bace ba sai faman kore masa mata datakeyi
Yayar ta rungume ta a hankali, tana lallabata kamar yaro. Sanin halin Fiddausi yasa bata tanka da gaggawa ba. Ta bari sai da kukan ya lafa, sannan ta ce da saukar murya
Shikenan, Fiddausi. Ki kwantar da hankalinki. Na kira As ad din, yace yana hanya. Ki zauna ki sha ruwa.
Amma Fiddausi ta buga ?afarta a ?asa, kamar yarinya, ta ce
Wallahi sai na rama. Sai ta gane wannan gidan ba nata bane! Sai na koya mata darasi.
Yayar ta kalleta da ?an bacin rai a fuskarta, sannan cikin kwantar da murya mai cike da nuni tace
Ki kula da lafazinki, Fiddausi. Kin san As ad... yafi wuka kaifi. Kuma ki sani, sarauta ba kishi da ihu ba ce ladabi da natsuwa ne.
Fiddausi ta dan ?aga kai da mamaki, amma zuciyarta bata kar?i fa?an ba. Sai ta zauna tana haki, tana ta shan numfashi kamar wacce aka hana mata iska.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH